episode 6


AURE UKU

(a hospital romance)

              by

    Chuchujay

Episode 6⃣.

  Wai ni kam imamu yaushe zaka kawo mana mata ne gidan nan ,mun gaji da wannan gafara san banga ƙaho ba ,gaka dai geme geme kana shirin bawa talatin duka amma kamar an maka ƙwari Ko budurwar Arziƙi baka da ita,

Muntari ?

Ko ni ƙadai abun yake damu ne ,ga dai nan usama matarsa ciki na biyu ne da ita,nan ga inteesar cikin fari gare ta ,kanwar ka ma kenan ,idan kuma ba so yake na mutu banga jininka ba ,ko kuwa baka da lafiyar mazantaka ne.

"Tari Paki Ya fara saboda kwarewar da yayi,ummu(mahaifiyarsa)ce ta miƙa masa ruwan da ta zuba zata sha tana Mai shafa masa baya".

Tsaki Nana tayi tace "karyar soyayya kike nuna masa Habiba,idan da soyayya ki sa shi yayi Aure itace karshen kauna idan kuma ba maganar da na faɗa ta rashin lafiyar mazantakan bace Ko kuma leƙeleƙe.

Affan ne Ya aje spoon ɗinsa Ya tashi a gun yana mai jin takaicin Nana"Ai kamar jira take ta koma kansa tana cewa" yo kaji mun shegen yaro,dan inawa Yayanka faɗa shine abun yayi maka ciwo?"To dake ni,

Kaima ai yaci ace ka fara maganar Aure shekara ashirin da ɗaya kaida wannan Mai ido a loƙon"

Haɗe rai Afnan tayi tace"nifa nana tunda nazo gurin nan ban miki magana ba,ke shikenan baki san a zauna lapia daga wannan sai wannnan".

Wani salati Nana ta rafta ta kalli mahaifinnasu tace muntari kana ji Ko?

Dama ai ance yarinya idan ta balaga ta fara nono da jini shikenan sai tana ganin dai dai take da kowa ,

Yanzu 'dan Allah muntari sabida tsabar ta'ada ta kafurai da kuka daura ma kanku Shine ke hanaku killace ƴaƴanku ,to wallahi muddin ni na haifeka kuma na isa da gidan nan da mutanen dake cikinsa to dole a aurar da yaran nan uku ,sun isheni ,ga rashin ɗa'a ga rashin kunya da rashin girmama na gaba dasu wanda suka koya gun uwarsu,

Fuu Affan Ya bar gurin a yayin da Afnan tace "Ai sai kizo ki mun Auren tunda akan ki nake zaune a Gidan nan ,in dai fitina ne kin iyata saƙo saƙo, kece ba ga Ummu ba baga mu ba ,mene muka tsare miki ne ?

Kuma ai Abbi kika haifa ba mu ba,

Tsawar da mahaifinta ya daka mata yayi dai dai da kukan da Nana tasa tana Mai faɗin"Ai shikenan muntari tsakanina da ƴaƴanka kuma sai duka ,kwana kaɗan Ya rage su fara mun duka ,dama waccan figaggen yaran Apan Mai zubin jijiya yafi kowa haye mun sai kuma ita Apinan ɗin 'dan idan ban ƙaryaba har bangazata ta kusa yi jiya"

Duk da sanin halinta da Abbi yayi bai hanasa cewa da Afnan ta bata haƙuri ba,sanin mahaifin nasu baya wasa da abunda Ya shafi nana yasa tace"kiyi haƙuri Nana ,sannan Ai Allah yana kallon,mu kuma shaidane ban bangaje ki ba kikace na kusa bangaje ki amma kije na yafe miki ladan haihuwar Abbi da kikayi,sannan ni ba sunana Apinan ba ,ba kuma sunan Affan Apan ba idan baki iya ba kice Hassan da usaina tunda su nasan bazai maki wahala ba".

Kafun taji wata masifar ta Nana ta bar dining Area ɗin ,

Kallanta ta mayar kan Imam tana Mai binsa da idanu a yayin da ya maida hankalinsa yana Mai cin Abincinsa cikin nutsuwa,

Cike da fitina tace "tuzuru ba magana ne,"

Still bai Kulata ba Ya ɗauki cup d'in chapman ɗin da ummu ta zuba masa Ya shanye yayi hamdala,

Kafun Ya kalli mahaifiyarsa yace "ummu gaskiya sai an tara mata dubu tukunna za'a samu mace mai irin girkinki,gaskiya Abbi Ya iya zabe ,kalar hannunki kalar abincinki".

Ai kamar Nana na jira tace"inji ubanka,ina dadi a abincinnan duk an cika kafu zabo duk da ansan likita ya hanani ci dole sai an kasheni kuma wallahi nan gani nan bari kabewar kan kabari,a hakan kuma zaka ƙare Kana santin abincin uwarka bana matarka ba,"Ai kuma ka shiga uku dani yanzu tunda Auranka Ya zungureni sai anyi zaka samu sauƙina.

Tashi imam yayi yace Ummu ,Abbi sai da safenku,Nana ke kuma zan kawo maki wani magani Uku,safe ,uku rana, uku dare.

Har ya kai hanyar da zata sadashi da bangarensa yanajin ƙananun kuka da masifar Nana wai Ya kirata tab'abbiya ,dole yasa ummu tashi sabida ruwan diban Albarkar da Nana ke mata wai ta haifa masu yara irin yaren ta marasa kunya kafurai.

    Mahaifin Imam Alhaji Muktar Paki mutum Paki ne dake cikin kaduna ,ta wani bangaren kuma mutanen Adamawa,a Adamawa Ya tashi 'dan nan Ya tarar da iyayen sa amma hakan bai hana sunansu na PAKI tasiri ba,su Biyar iyayensu suka haifa maza huɗu mace ɗaya inda maza biyu suka rasu Ya rage saura su uku,

Sai Ya zamana shine babban gidan.

Naval Officer  ne wanda yake da matsayin admiral ,

A wani Zuwa da yayi America birnin New york Ya hadu da Habiba wadda take half Nigerian Half NewYorker ,mahaifinta ne ɗan nigeria mahaifiyarta kuma yar newyork,'dan Haka yaren hausa a bakinta kamar tana ƙasar,kasancewar su achan ɗin bai hanasu bin addini ba da hanya Mai kyau,

Su biyu ne gurin iyayen su ita da yayanta Areefullah,

A lokacin da Alhaji muntari Ya kawo maganar Aurenta Nigeria gida ba ƙaramun balli mahaifiyarsa hajja Hanne(Nana) ta tayar ba akan sam sam bata yarda Ya Auri kafura ba ,

Ƙarfin mijinta da kuma biyayyar da take masa ce tasa wannan Aure Ya ɗauro amma 'fa habici duk inda ta zauna,

Bayan rasuwar mijinta wani ciwo da tayi ta tattara ta koma gidan Alhaji Muktar a lokaci ummu na da cikin imam ,babu irin zagin da bata sha gurin Nana duk da irin wahalar da tasha da ita duk da itama jinyar da take na ciki 'danma intisar wanda imamu kebi tana 'dan kama mata,

Irin mitar Nana da halayyar ta a dole ummu ta saba tun tana sawa a ranta har ta saba musamman da ta lura da babu abunda zatayima Nana ta burgeta 'dan tun filazal ta nuna bata santa,

A Haka dai suka cigaba da rayuwa har Allah Ya azurta ummu da yan biyu Affan da Afnan,

Duk da halin Nana hakan bai hanata jin jikokinta a ranta ba kar ma ace imamu wanda duk jarabarta bai cika Kulata ba ,

Duk ranar kuwa da Abbi Ya dawo daga Abuja Ya bani da korafe korafe na an mata kaza an mata kaza kullum a haka take,

    Tayi nacin san ta sakewa Abbi Aure amma abun yaci tura 'dan duk yarda tabi sai Ya bulle dan shi baya da lokacin mata biyu,bama wannan ba shi yana san matarsa ita kadai kuma ta ishesa haka zalika ƴaƴa biyar ɗin da ta haifa masa Ya gode Allah duk da Allah ne bai sake basu rabo ba.

                                **********

Bangaren umaimah kuwa koda ta koma gida tun a parking space yaya Aliyu ya tareta,

Rabawa ta gefensa tayi zata wuce dan bata san masa rashin kunya sannan bata san ƙarar da energy Ɗinta akansa 'dan yau da batu Ta dawo wanda dole ayisa yau 'dan ita bata da time da safe kafun kuma ta yi Aikin kwana gwanda tayiwa tufkar hanci.

Wani mari yaya Aliyu Ya ɗauke ta dashi wanda yazo mata a bazata,

Juyowa tayi ta kallesa Idanunta Ya kawo ruwa hannunta dafe da kuncinta tace"mari 'fa Yaya Aliyu,you slapped me".

Cike da masifa yace"na mareki ɗin Ko zaki rama ne?

Ba dai ke kinyi wuyan da zakina wa matata gorin haihuwa ba wallahi nan gaba bulala Zansa na zaneki mara tarbiyya kawai sakariya wadda ta kasa killace kanta guri ɗaya gidan miji,menene Amfanin ƴaƴa irin naki masu uba daban daban ke ba akuya ba".

No this can't keep on,

da gudu ta yi ciki tana faɗin Daddy?

Daddy Daddy im leaving this house.

Cike da tashi hankali Alhaji Bulama Ya miƙe ganin yarda ta shigo tana kuka tana kiran sunsa ,

Lapia?

Ya tambaya yana Mai rike hannunta,

Cikin kuka tace "Daddy gidan nan zan bari nagaji da gidannan,ace ni da gidan ubana ni da yarana bamu huta ba ,Daddy abunda akewa su Nameer a gidannan is too much for kids there age ,sannan ba wannan ba yanzun nan 'fa marina Ya Ali yayi."

Mari?

Daddy Ya faɗa da mutuƙar mamaki.

"Sai ki fadi Mai kika mashi Ya mareki Ai ba wai kawai kizo kice Ya mareki ba ,jiyan nan gabana babu ko kunya kika yiwa matarsa gorin haihuwa,

Hajiya ta faɗa tana Mai kauda kai ".

Cikin rufewar ido Umaimah tace"dama Ai hajiya zakiga nawa laifin amma baza kiga nasu ba tunda ni bake kika haifeni ba amma dake kika haife ni bazaki ƙi fadar bangren da matar Ya Ali ta fara mun gorin zaman Aure ba ,sannan dake kika haifeni bazaki tab'a faɗawa yarana cewa ubansu daban dabanba sannan uwarsu ta kasa zaman Aure ba,baza kuma ki taba barin yan uwansu suna kwararsu ba ko kuma matan ƴaƴanki,

Yara kanana baza kuna wasa da mental health ɗinsu ba,

Amma yayi dama ba gidan ne baki so na zauna ba?

Zan bar miki ki zauna  ke da ƴaƴanki,

Fita tayi a ɗakin, tana jin daddy yana ƙwala mata kira amma ta ƙi sauraransa 'dan marin Aliyu Ya kaita bango,

    A Sashen yaya Abubakar ta ɗauko su NAMEER ,taji daɗi yarda bata tarar da yaya Abubakar ba,bata tsaya sauraran maman Sultan ba ta sakasu cikin mota ta ,kamar jira take gate man Ya buɗe mata ta figi motar zuwa titi.





Wattpad:chuchujay

AREWA BOOKS

https://arewabooks.com/book?id=653305e91c06f4783fc2ef84

Facebook:https://www.facebook.com/groups/805959663295457/?ref=share



CHUCHUJAY ✍🏽

TBC.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top