episode 25&26

AURE UKU

               (a hospital romance )

                  By chuchujay

                wattpad :@chuchujay

https://whatsapp.com/channel/0029Va9RLKT2P59fHSa7Ia1j

Join My whatsapp channel inda Zan baku noorurrahman kyauta.

Yes paid novel ne amma Zan baku shi a channel ɗina kyauta,

Just follow and share i want audience domin baku.

Episode2⃣5⃣➡2⃣6⃣.

   Baki ɗaya haka nan Umaimah ta karasa ranarta a sukurkuce,bata san kasancewar paki a tare da ita ba Ya kamata sosai sai a yau da kwata kwata bata ji sa ba ko tagansa,

    Motar yaya Abubakar da ta gani a gida Shine Ya tabbatar mata da yana gida ,

Parking motar ta tayi a gefen tasa ta nufi sashen sa kai tsaye,

Tun a ƙofa taganshi yana shirin shiga,

Yana ganin ta Ya faɗaɗa fara'ar sa yace "umaimah Kin dawo kenan,"

Murmushi tayi tace" wallahi yaya na dawo and ganin motanka yasa nazo na gaishe ka cos na kwana biyu ban ganka ba,

Shiga yayi tana biye dashi a baya,

A falo ta tarar da iyalan sa ,da gudu yaran sukazo gareta suna mata oyoyo inda mahafiyarsu ke ta mata fara'a tana Mai faɗin dama wai kina gidan nan umaimah,yaushe rabon da na saki idona?

    Zama tayi tana Mai faɗin"maman sultan baza ki gane ba fitar ce da sassafe wani lokaci bana shigowa sai dare Chan,".

"Gaskiya dai Allah Ya taimaka ,aikin ku Ai sai ku,

Bari na kawo miki abinci,

Da saurinta tace "a'a Aunty Im okay dama nazo magana ne kawai da yaya Abubakar."

    Ƙaramun murmushi tayi tace "bari na baku guri dan tsakanin ki da yayanki sai Allah"

    Bayan tafiyarta Ya Kalleta yace "umaimah Allah yasa lafiya,"

Murmushi tayi tana Mai Wasa da hannunta tace"Yaya dama ina san magana da kai ne,ko nace ina san na nemi shawarar ka saboda ina tsoran nayi abunda zai dameni,wasa ta cigaba dayi da hannunta Kafun tace"Yaya I've found someone ,i mean wanda yake san Ya Aureni and im not against it,

I might sound somehow amma yaya Im loving the idea saboda ive fallen for this guy,

Sannan yaya bai tab'a Aure ba and He's just a month older than me,

Shine babban abunda nake tsoro sabida abunda mutane zasu ce,wasu zasu ga kamar Im selfish ina ƙokarin jansa cikin rayuwata bayan nasan ko Aure bai tab'a yi ba,amma yaya abunda nake ji a tattare dashi ko akan Hafiz banji ba,sannan yana mun soyayyar ni kaina takan bani tsoro,

Ban san Ya zanyi ba,

Duk abunda na fuskanta a rayuwa ta a wannan karan bana ganin komai sai alaƙata dashi

    Shiru Yaya Abubakar yayi bayan takai ƙarshen zancen ta Kafun yace"a ina yaran yake ,ɗan gidan wanene".?

Licking lips ɗin ta tayi tace"Yaran Admiral Muktar paki ne"

    Riƙo hannun ta yayi yace kali nan umaimah,eh nasan abun sound somehow amma it doesn't matter ,nasan dole mutane zasuyi magana kamar yarda kika ce amma abu mafi muhimmanci Shine muddin idan zuciyarki ta kwanta dashi ta yarda dashi ki saurareta ,saboda you deserve some happiness Sannan yaran nan bake kika masa dole Ya soki ba ,shine yaji yana sanki kuma ya amince zaiyyi rayuwar sa dake so Allah wadai duk abunda mutane zasu faɗa.

    Babban farin ciki na Anan Shine ,yarda baki  sare da Aure ba,bakice a'a ba saboda Hafiz ma Ai yazo maki da soyayya,nayi farin ciki mutuƙa da kika saka a zuciyarki ba kowane Ya zama ɗaya ba sannan da ikon Allah jikina Ya gama bani a wannan karan baza muyi dana sani ba,

Duk abunda ke saki farin ciki umaimah nima yana sani ,and a rayuwata bani da buri da Ya wuce naga kinyi settling down a gidan mijinki,abu ɗaya Ya hanani magana wanda Shine gudun yarda zaki ɗauki maganar ,amma tunda yau da kanki kike so na miki Alƙawari zan tsaya miki kamar koda yaushe,

Duk wani damuwar ki in dai ina da maganinta Zan maki,Just say the word,and kar ki damu i will talk to daddy .

    Murmushi tayi tace "nagode yaya ,kai ɗan uwa na gari ne,ina jinka a zuciya ta,ina ƙaunar ka saboda ka damu da damuwata kamar ciki ɗaya muka fito ,ko iya abinda na samu a gidan nan ke nan na godewa Allah.

    Gyara zaman sa yayi yace "ni dake umaimah Ai ciki ɗaya ne,ko baki san uba ɗaya ne ciki ɗaya ba?

Kar na kuma ji kince ba cikin mu ɗaya ba ,da ni dake da umar da usman da Aliyu duk cikin mu  ɗaya,it doesn't matter hallayyar su a kanki amma ni nasan suna ƙaunar ki suna kaunar ki ,kawai wani abu ne Chan na banza yake tare musu nuna maki,wa kike tunanin yake samun sa'a kamar tamu?

Duk wanda Ya samu ƙanwa irin ki abun yayi alfahari da ita ne,kinsan yarda kaina yake ƙato idan naji abokai na nace wa "Ai Abubakar yayan young beautiful surgeon  umaimah Bulama ne,sai kiji na kasa riƙe kaina 'dan har rawa yake kamar zai faɗi,its a real show up ".

    Dariya tasa tace"yaya!!!"ɗan hira suka tab'a Kafun tayi masa sallama ta wuce ,.

Haka nan taji kamar an sauke mata dukkan wata damuwa ,ɗaura ɗamara tayi da zuciyarta wajen nunawa paki soyayyarta ,kamar yarda yayanta Ya nuna mata "Fuck the society as far as she's Happy "

Koda ta shiga sashen su Abdallah da Nadiya sunyi bacci Shatu kawai ta tarar a falo tana kallo,

Tana ganinta tace"sannu da zawa Adda,zama tayi kan kujera tana Mai cire takalmin ta Kafun tace"baki kwanta ba,

    Hamma tayi tace "wallahi Adda wai ina jiran shigiwarki ne ko zaki nemu wani Abu,"

"Shatuuhh!"Idan kina jin bacci Just go to sleep ki daina cewa zaki jirani ko zan buƙaci wani abun ,Babu abinda zan buƙata ,idan ma inaso zanyi da kaina ,Ai kina ma ƙokari in kina mun haka bazan na jin daɗi ba ,kefa yar uwata ce ba yar Aikina ba,

Please!

    Murmushi tayi tace "kiyi haƙuri Adda ,a rayuwa ta kullum burina bai wuce naga na kyautata maki ba,kin san a yan uwan mu kece mace ta farko data fara ɗauka na ta jani jiki cos kowa maganar sa ɗaya ni nayi sanadin mutuwar shifaɗo ,bani da sa'a ,kowa yaki zuwa Ya nemi Aurena kamar wata Mai kanjamau,shiyasa a rayuwata yanzu Kin bani abunyi ,cos kula dasu nadiya ina jinsa har raina ina kaunar yin hakan,suna mutuƙar bani farin ciki.

    Kallanta umaimah tayi taga yarda tayi bul bul ta ƙara kyau ,Dafata tayi tace"shatuh i want the best For you sannan na ɗaukeki badan wani abu ba ace ma saboda Aikina and su nadiya na bukatar wani,amma nima ina bukatar ki kusa dani,and insha Allahu zaki gani ,sai na maki Auren kece raini ,Auren da masu yan gutsiri tsoma akan ki zasu ji kunya,"And yanzu ma maganar da nake miki na sama miki Niva open university kina gida zakiyi karatun ki,exam kawai zai kaiki,

So insha Allahu monday bana komai zan dauke ki muje muyi komai,.

    Cike da murna ta rungume ta tace "nagode sosai Adda ,Allah ubangiji Ya faranta miki Ya shira maki yaranki."

Shafa kanta tayi tace ameen ya rabbi,

    Wanka tayi bayan ta shiga ɗaki taci abinci ta jawo system ɗinta tana ɗan wani research ,a hankali takan duba wayarta taga koda saƙon paki ne Amma shiru,kamar ta sake ƙiran sa amma tayi ƙokari ta danne zuciyarta gudun kar ta bada kanta,

A hakan nan ta gama abunda Zatayi ta kwanta amma tunanin ta baki ɗaya Ya karkata kan paki ,bacci b'arawo ne kawai Ya ɗauke ta tana Ayyana yarda yake.

   

    Washe gari kasancewar bazata Aiki ba yasa ta joining yan gidan breakfast duk da kuwa yaya usman da umar sun fita,

Bayan sun gama cin abinci tana ƙoƙarin tashi daddy yace "umaimah ina san magana dake mai muhimmanci ,kizo sashena,,"

"Maganar baza'a iya yinta bane a cikin mu sai anje sashen ka Alhaji?"

Maganace dai ta budurwar zuciya da ɗiyar ka take da ita sannan baki ɗaya bata san ta tsufa ba dan haka zuciyarta take mata kwaɗayin Abunda yafi karfin ta,Ai naji jita jitar sannan wayar da kayi jiya ta tabbatar mun ba jita jita bane.

Hajiya ta faɗa tana Mai ƙora tea ɗin ta,

    Ƙaramar dariya Aliyu yayi yace "Ai ni umaimah ban tab'a sanin kina da san zuciya haka ba sai yau,ina ke ina yaran Admiral muktar ,dama dai ace babban ne ya iya maneji dake amma wanda bai taba Aure ba kuma tsaranki Ai Kema kinsani ba sai an faɗa maki ba ,san zuciyarki a fili yake sannan duk wanda yajiki yasan desperation ne ke damun ki kwana nawa aka gama yawo da sex clip ɗin ku a duniya sannan yanzu wata maganar Aure ta bayyana . "

    "Ai baka san wani abu ba Ali,ita dama sa'a ba ga kowa take ba,ka kalli umaimah a gurin nan ,bazan boye maka ba tafi kowa sa'a a yaran daddy ,i mean ka duba rayuwarta da kyau, a wannan karan ma sai gashi Allah ya kara buda mata sa'arta ta samu mutum irin imam paki,ba san zuciya bane ,rahmace ta ubangiji,Ya kamata ace ka gane hakan,

Yaya Abubakar ya faɗa kamar ba shi Ya faɗa ba cos abincin sa ya cigaba daci calmly.

    Tsaki Hajiya tayi tace "kaji haushi Abubakar Ai ,indai akan umaimah ne  nana Surbajo Kafun ta tafi ta barbaɗa maka "

Dukan dining table ɗin da daddy yayi ne yasa ta saurin yin shiru,nunata yayi da yatsa yace "na faɗa maki ba sau daya ba ,ba biyu ba akan ki daina saka Surbajo a haukan ki amma baki ji ko?

Zamu samu matsala fa,ki kiyaye sannan kai kuna Ali da kake faɗin san zuciya kaima kaso zuciyar ka haifu,.

Kai daddy !!

Matar yaya Ali ta faɗa a karo na farko tunda aka fara abin 'dan tun gargaɗin daddy babu wadda tayi gigin sake shiga shirgin umaimah ballantana yaran ta,

    Tashi daddy yayi yace umaimah oya ,

Babu musu ta mara masa,

Zama yayi yace zauna umaimah ,

Babu musu ta zauna tana Mai narenare da ido 'dan abinda Ya faru a wajen Ya ɗan tabata,wai ace danginka ne ke adawa da kai.

    Cikin sakin fuska yace "umaimahn daddy menene baki faɗa mun ba?"

Shiru tayi ba tace komai ba ,kallon idanun ta yayi yaga sun ciko da kwalla,

Ajiyan zuciya yayi yace "kalli nan umaimah im not against duk wani abu da kika zab'a kuma kika ji a ranki Ya miki,Just go for it koda zai maki zafi daga baya, at least Ya saki farin ciki daga farko".

    Daddy bama zai sani baƙin ciki ba,kamun addu'a ,na zab'i Paki and wallahi daddy ba san zuciya bane ,abunda zuciya ta ke so ne sannan ban amince da zab'in ba sai da na tabbata da hankali na Ya kwanta,and daddy inaji a jikina he's not like Hafiz ,'dan Allah daddy support me i want this.

    Shiru yayi yana karantar yanayin ta,tabbas Umaimah ta tafi akan wannan yaran da bai sani ba dan ko magan nan bai kai mata ba amma ta kare,cikin san jawo da hankalin ta garesa yace "umaimah bai tab'a Aure bafa.sannan ke Kin tab'a Aure,yaranki uku fa,."

    Cike da kwarin gwiwar da bata san tana dashi ba tace "daddy Annabi Muhammad (SAW)Nana khadija ya fara Aura kuma she's even older ,daddy anan ma ban girmi Paki ba,babu inda addini Ya haramta Aurena dashi,"Daddy please kaine kawai kwarin gwiwata and jikina yana bani imam alheri ne a rayuwata,

Ta karasa maganar tana Mai nare nare da ido.

    Ajiyan zuciya yayi mussaman ganin Yarda umaimah ta fito masa a mutum,tabbas soyayyar ta rufe mata ido,sannan shi he's looking out for her,baya san tazo Ya yaudareta kamar Hafiz amma ganin yarda bataji nauyinsa ba yasa shi cewa"shikenan princess ɗin daddy,duk abunda kika zab'a nima ina tare dashi sannan ina Addu'ar Allah yasa Shine zai rufeki ko ki rufesa,"Jiya mahaifin sa ya kirani yamun maganar so i thought kawai irin random mutane ne musamman scammers shi yasa ban tsaya jin sa ba nace masa wrong Number ,amma yanzu tunda naji ta bakin ki zan kirasa a sa rana mu haɗu ayi magana sannan ina san ganawa da shi yaran.

    Cikin kasa da kai tace"daddy sunan sa Imam",

Dariya yasa yace jaira"to imam",

Haka suka cigaba da zantawa tsakanin ɗiyar da tayi shaƙuwa Mai tsanani da mahaifinta .

************



Su umaimah an kamu 'fa,😂oh ba kunya.

Bakina da goro.

Chuchujay ✍🏽

TBC.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top