episode 21&22
AURE UKU
(a hospital romance)
By
Chuchujay ✍🏽
Episode 2⃣1⃣➡2⃣2⃣
Gaskiya Dr Bulama bazan iya Wanchan Aikin na cyst ɗin chan ba ,patient Ɗin 'fa Hiv positive ce Fa,
Gaskiya i cant risk it kawai idan zakiji shawarata muyi mata transfer ko kuma mu ɗorata akan magani,
Gaskiya bazan iyawa Mai HiV operation ba ,
Sauke glasses ɗin dake idanun ta umaimah tayi ta kalli Dr maryam dake ta faman mitar abun,
System ɗinta ta juyo tana mai Kallan Dr maryam kafin tace "Dr maryam ki kalla da kyau,cyst ɗin matar nan yayi girman da idan ba'a cire ba zai zama cancerous,
And 'dan kawai tana da Hiv shine baza'ayi mata aiki ba?
Wanne policy ne Ya hana ,?
Shikenan shi kuma Mai HIv ba mutum bane baza ayi masa aiki ba idan yana neman a cecesa? "
We have precautions to follow kema kin sani,to menene zai sameki dan kin mata Aiki,bana tunanin zaki mutu.
Okay naji its okay,kar kiyi i will take the lead,you can leave My cabin.
Tashi umaimah tayi 'dan zuwa nurses station ,alamu tayiwa farouk Da yazo,
Babu musu Ya taso yazo,cikin serious tone tace "zamuyi wa matanan aiki ,nasan baka da komai in schedules naka ,Dr maryam baza tayi ba so we are taking over ASAP arrange my team and prepare the operation theater,na tura maka details ɗin patient ɗin ,"
SOME HOURS LATER.
Ko wannen su dake cikin OR ɗin sanye yake cikin gowns da aprons ,eyes wear,da face shield saboda gudun splash na jini,ko wani fluid na jikin mara lafiyan,sanann kowannen su hannunshi sanye da glove,
Tsaye umaimah tayi akan Patient ɗin Kafun tace "Intern students This Patient is HIV positive, and zamuyi mata Aiki mu cire ovaries cysts ɗin da take dashi,so beware of needles injury, scalpels ko wani sharp object ɗin ,so Aikin nan tare zamuyi its high time ,ku kula needles Are not allowed to be bend da hannu,ko cirewa jikin syringe,
Puncture resistant container ta nuna tace duk used abu na disposing Ya kasance anan. "
Nurse farouk dake gefanta ta kalla wanda tasan He's Good at his work and komin menene tsananin risk na Aiki zaiyyi indai tana gefen sa ,itace tsananin yardar da sukayi da juna,
Kaɗa mata kai yayi Kafun tayi murmushi,
Paki wanda tunda ya shigo asibitin bai sata a idanun,sa ba sai da aka kirasu ,har cabin ɗinta Ya gama zagayen duniya bai ganta ba,
Matsawa gefenta yayi cos shima Ya yarda indai da risk to Ya same su a tare.
Murmushi tayi ganin abunda yayi,
We are performing laparotomy instead of using laparoscopy since the cyst is large,
Alamu tayiwa Nurse farouk wanda Ya fara bata kayan aiki tayi makin large cut a tummy ɗin patient ɗin wanda take jini Ya fara fita,
Komai Ya dawo visible gareta tana gani a haka ta ciro Cyst ɗin,tasa a container ,miko hannu da tayi yasa paki dake adoring ɗinta mika mata abunda Zatayi staples ,
Kallan Dr Munnir tayi wanda yayi saurin ɗauke ido dan kar tace yazo yayi dan haka kawai ta maida hankalinta wajen staples ɗin.
Bayan ta gama tace"our surgery is done,"
Nurse Fatima take this Cyst and ovary to the lab a duba ko cancerous ne,amma im positive its not ,cos idan Ya zama cancerous ne we will have to remove her womb,.
Fita tayi ta barsu su karasa inda tana sa kafa paki Ya saka,
Apron da Face wear ɗinta tayi disposing ,wash room ta shiga bayan ta cire gloves tana Mai saurin wanke hannunta throughout,
Bayan ta gama ta fito,
Gabanta Ya bayyana yana Mai faɗaɗa mata murmushin sa yace"i Love everything' about you Dr Bulama,"
Juyawa tayi ganin mutane na wucewa tace"Paki mutane zasu jika 'fa,"
Ƙaramar dariya yayi yace"I dont Care ,su jini,ko Kin manta abunda na faɗa a gaban management,ina sanki,and bazan daina ba ,sannan a da ni kaɗai nake yi amma yanzu mun zama mu biyu,"
Kaɗa kai tayi ta fara takawa zuwa cabin ɗinta inda shikuma yake binta a baya,
Kowa kus kus ɗin yake saboda maganar da yafaɗa na yana santa Ya fito waje ,wasu su zageta wasu kuma suji haushin ta saboda samun Paki dan akwai masu crushing akan sa da yawa.
Zama tayi kan kujerarta yayin da Ya zauna a wadda take facing Ɗin ta yana Mai ƙin ɗauke idanun sa akan ta,
"Akwai wani abu a fuskana?"ta tambaye sa tana mai ɗaga masa gira,
Dan rufe idanun sa yayi kana Ya buɗe yace"kyanki da yake ɗaukar hankalina a kullum ,Shine a fuskarki,."
A kalla yasata murmusawa na babu adadi,dan Cije lebenta na ƙasa tayi tace "baku da wani abu da zakuyi ne yau".?
Shafa kwantaccen sajensa yayi yace "Well duk Abunda zanyi yana tare dake Kin manta kece ogata,sai yarda kikayi dani,komai nawa na ɗamƙa miki ,sannan duk inda kika saka ƙafarki nan Zan saka tawa,"
And yauwa inasan san na tambayeki,
Ina fatan kina nufin duk wani abu da kika faɗa jiya gaban su Ummu,cos ummu ta gama saka rai dake ,haka zalika siblings ɗina,
Kowa yana sanki amma babu wanda ya kaini sanki,so please kar ki janye maganar ki na jiya duk da ina da yaƙinin dan Nana kikayi amma na tabbata Wani bangaren gaskiya ne,
Kallan sa tayi cikin ido tace"yanzu idan nace kazo ka Aure ni zaka iya?
Dafe zuciyar sa yayi yace"cikin bugun zuciya,i want to wife you sannan inasan muyi 30 years a ɗakin mu Im not joking cos duk Abunda Ya shafe ki ni bana ɗaukar sa abun Wasa,ko gobe kikace na Aure ki Zan yi ,trust me im loaded,
Ƙaramun murmushi tayi tace "Im not After your money kaima ka sani ba,and i Just dont want to rush things' dan haka you will have to court me,Ya kamata kasanni sosai nima nasan ka ,like da dislikes ɗin ka da nawa,and a side ɗina bani da matsala ,side ɗinka ne " .
Karshen maganan ta kai tana san ganin reaction ɗin sa Kafun tace "Im Sorry idan jiya na wuce iyaka".
Yar Dariya yayi yana Mai tuna abinda Ya faru jiya Kafun yace "Well indai kin yarda dani,kin kaini gida a matsayin wanda kika zab'a zakiyi rayuwa da then nana baza ta zama matsala ba."
Ɗan kasa tayi da murya kafun tace "beb ɗin ka fa".
Fahimtar da sameera take yasa shi darawa yace"na jiyo kamshin kishi,Well sameera bazata taba zama threat tsakanina dake ba cos ke nake so ,sannan ni tsakanina da ita babu wata alaƙa ta soyayya,kawai alaƙace ta zumunci bayanta ba wata ,sanann tana internship ɗinta ne a sydney private hospital wanda na Uncle ɗinta ne and saboda tace a gida nan ɗin zata shi yasa suka barta,
Sannan gidan mu sun bata masauki ne saboda sun ɗauketa an zama ɗaya duka daga Family ɗinta,
Dan shiru tayi tana nazari ,ba wai tana tsoran Sameera bane,amma tabbas tasan akwai sauran rina a kaba,
Fitar da tunanin sameera tayi a kanta kafun tace"you have to try hard to impress me 'fa paki cos na wuce stage ɗin da puppy love zai burgeni, "Can you handle me.
Haɗe hannayen sa biyu yayi yace "ban fito ba sai da na shirya sannan ki yarda dani idan nace maki,bazaki tab'a tsallake soyayyar Paki ba."Kashe mata ido ɗaya yayi a ƙarshen maganar sa wanda Ya sakata giggling kamar wata high schooler,
Buɗe kofar da akayi ne yasata saurin juyawa akan kujerarta tana Mai Kallan desktop ɗin dake gefen ta cikin Mazewa,
Nurse farouk ne,haɗe rai tayi tace "yaushe kafara shigo mun babu Knocking ,"Ƙaramun murmushi yayi dan Ya fahimci abinda yake faruwa,
Aje file ɗin dake hannun sa yayi yace "ayi mun afuwa to,file ɗin patient ɗin chan ne hardcopy na kawo miki kamar yarda kika buƙata,".
Na barku lafiya ,da murmushi a fuskarsa Ya fita.
Bayan fitar sa Paki Ya Kalleta yace"masoyiyata ki daina ƙokarin boye soyayyarmu dan yanzu abunda nake faɗa miki,kowa a asibitin nan yasan ina sanki,sannan a yanzu ma na sake ɗaura ɗamarar sanar da kowa soyayata gareki,
Tashi yayi yana Mai blowing mata kisses da hannu ,Kafun Ya kama hanyar fita yana Mai faɗin we are going out for dinner yau since yau kina night ne".
Kaɗa kanta tayi bayan fitar sa dan rabonta da jin yanayin da take ji game da paki tun kan Hafiz.
A hall ɗin da suke zama Ya tarar da KB tare da Aisha shareef suna hira ,tana ganinsa ta washe masa haƙora tace "paKi ina kaje ne tun ɗazu ina nemanka since operation ɗin chan bangan ka ba,"
Zama yayi kusa da Kb yace "nace zance ne."
Cikin rashin jin daɗin furucin nasa tace ,zance mana,naje zance gurin macen dake haukata mun lissafina a kullum idan na saka ta cikin idanuna,
Ina tare da Dr Bulama tun ɗazun ,da kyar na iya yakicewa na taho saboda nasan yanzu Zatayi abu Mai muhimmanci ne.
Da mamaki ta kalle sa tace"dama wai paki jita jitan nan ba karya bane,kai yanzu baka jin kunya ma?tayaya zakayi soyayya da bazawara wadda tayi Aure daya daya har uku ,har da ƴaƴanta fa,
Amma kai ka kalle ka young,handsome and rich,Mai zai hana ka kalli matan dake gabanka.
Shima da mamakin furucin nata yace "kina nufin yan mata irinki Zan kalla?kalli nan Aisha,I hope ban baki wrong signal ba,sannan with All due respect bana san kina faɗan abun banza akan Umaimah raina zai na baci naji bana san magana dake ,and yes ke ba irin matan da nake so bace ,irinta nake so dan haka respect it please."
Dauke kai yayi da Ya gama maganan sa dan ta ɗan Sosa masa rai,
Tashi tayi tace "kayi hakuri ban faɗa bane da wani abu,"
Bayan barinta gurin KB ya kallesa yace "mutumina why mana,Mai yasa zakayiwa Aisha magana a haka ne saboda Allah."
Haɗe rai yayi yace"gwara nayi rejecting ɗinta tun kafun ta ɗauki hope ɗinta da nisa,ni one woman man ne,one army"
Dariya KB yayi yace "zaka sani ne duk ranar da Nana ta mayar da kai sameerah and umaimah man".
Ƙaramun tsaki yayi yace"bismillah ɗin ta tasan halina ai".
Dariya sukayi a tare kowa da abun yake tunawa na Nana.
***
Kamar yarda Ya faɗa da dare Ya fita da ita romantic dinner,
Duk yarda take tunanin Paki Ya wuce nan gurin saboda yarda yake narkar da ita a soyayyarsa ba a magana,har asibiti ya maida ta cikin kulawa yana mai nuna mata matuƙar soyayyar ta da yake yi.
Sai wurin 9 Ya shiga gida,
Yana ƙokarin shiga sashensu yaji An ambaci sunansa da muryar da ya Jima bai ji a zahiri ba illa a waya.
A/N
Mundai kusa Aurawa paki umaimah and nan zamu tsunduma tafiyar Aurenta da paki,daɗi ne ko akasin haka?.Nidai nace daɗi ne kufa?
Ku cigaba da bina kun sharhi dan ina mutuƙar kaunarku da sharhinku❤
Chuchujay ✍🏽
T
B
C.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top