episode 15&16


AURE UKU

(a hospital romance)

         By

Chuchujay ✍🏽

    Episode 1⃣5⃣➡1⃣6⃣

    BAYAN SATI BIYU.

"Mami ina ta cewa kiyi haƙuri amma mami kina ta ignoring ɗina gashi zan tafi".

"Banza ta masa a karo na ba iyaka Kafun tace"zo nan Nameer,"

Babu musu Ya ƙarasa gare ta Ya zauna a gefen ta fuskar sa gwanin ban tausayi,

"Kallan sa tayi na ɗan wani lokaci tana Mai jin soyayyar sa da tausayin sa kafin ta jawo sa jikinta ta rungume sa tsam,"

"Raba jikin ta tayi da nasa tace"Nameer ina san ka sosai nasan ka san wannan,and yanzu Abuja da zaka wuce ,kasa ma ranka karatu kaje ,"

Study hard Nameer ,i want to be proud of you ,kar kasawa ranka wai baka da kowa achan gurin ,kaje ne dan kayi karatu,

Sannan ina so Nameer kasan irin abokan  da zakayi hulɗa da saboda rayuwa ce zaka je kayi sabuwa and i hope you wont disappoint me  ,

And last abunda nake san faɗa maka ,Abunda ka faɗa last time bana san Ya Maimaita kan sa dan Allah Nameer ,you're hurting me with your words,sannan duk wanda kaga Ya kashe mutum a duniya to karshen sa baya kyau Kafun akai ga lahira,

Na tabbata baza kaso mamin ka ta shiga wani hali ba saboda i will die without you,

I need you ,Nadiya and Abdallah also needs you,

So please Nameer bana san wannan zuciyar da kake yawanyi.

Rumgume ta Ya kuma yi yana Mai shesheƙar kuka Kafun yace "mami baza kizo muje tare ba,?"Its a flight 'fa minti kaɗan zaki dawo,

Shafa kansa tayi tace"Nameer i promise you first visiting ni zaka fara gani,".

Murmushi yayi wanda Ya bayyana side dimples ɗin sa yace "mami i will make you proud i promise".

Kissing forehead din sa tayi tace "Allah yayi maka Albarka".

Da gudu nadiya ta shigo tana Mai faɗin"Hamma Nameer daddy fa yana chan yana jiran ka,and yace tare zamu tafi,. "

Kallan ta umaimah tayi tace dake?

Kaɗa kai tayi tace"Eh,daddy yace muje tare Cos i was crying ,mami muje da Abdallah?"

Kaɗa mata kai tayi tace "A'a Abdallah bazashi ba amma ke ɗin kije ."

To mami"ta faɗa da dauki Kafun ta fita a falon tana murna zata raka Nameer abuja. "

Tare dukkan su suka je Airport dan raka Nameer,

A dawowa ne ta bawa shatu Abdallah suka bi motan da su daddy suka zo wanda Aunty sadiya ke tuƙawa a yanzun suka koma gida,ita kuma tayi CITY HOSPITAL.

SATI BIYUN DA SUKA GABATA.

    Kamar yarda daddyn umaimah yayi mata alƙawari within 48 Hours aka kamo Habib daga wani ɗan ƙaramin ƙauye Mai suna Cosò cikin garin italy ,

    Last garin da bai tab'a tunanin za'ayi tracing ɗinsa a gurin ba.

"Lokacin da aka dawo dashi nigeria da fari sai da yayi gardama akan bashi da hannu akan abun da Ya faru,amma da yasha matsa babu shiri yayi confessing ."

    Babu irin roƙon da baiyyiwa umaimah ba akan ta yafe masa ko dan darajar Nameer amma tace "Ai da yasan da darajar Nameer bazai ƙokarin zubar mata da daraja ba."

Sosai Ya daku,Kafun aka kaisu court ,zaman ƙwana daya aka kaisu gidan maza.

"Ta bangaren daddy kuwa Ya yanke Alaƙa da mahaifinsa dan a cewar sa Ya kasa saka Habib a hanya tunda tun fari Ai Ya musu Kashedi".

"Bangaren asibiti kuwa ,bayan Abun da Ya faru ta samu ƙwaƙwaran kira daga board,"Kamar bazataje ba amma Hindu ta lallashe ta Akan taje.

Haka nan ta shirya taje,baki ɗaya board ɗin asibiti ne suka hallara dan tattauna abunda Ya faru ,

Zaune ta tarar already Paki har yaje,

Murmushi tayi masa lokacin da ta haɗa ido dashi,

Ɗauke nasa yayi kamar ma bai san da ita a gurin ba,

Tunani ta fara ko sun faɗa masa wani abu da bai dace ba .

Ta rasa dalilin da zaisa ana kiran board meeting dashi,

Ita likitan asibitin ce shi kuma Intern ne its okay ma idan ance yayi abune da za'aiya reporting ma school ɗin sa ,amma Ai case ɗin is close tunda an gane menene gaskiyar Al'amarin ,Shin mene dalilin kiran nasu?

    Board President ne yazo cos dama shi kaɗai ake jira.

Sake maimaita abunda Ya faru yayi Kafun yace "Dr Bulama i heard zaki aje aiki" .

    Ƙaramun murmushi tayi tace"with All due respect sir,

Im offended a yarda kayi Narrating whole situation ɗin nan,

But its okay what's done is done i Just hope lesson ɗin yaje ,

And yes im resigning from HERE.

Ɗaure fuska tayi cos tasan halin su dukkan su yan rainin hankali ne sannan meeting ɗinnan akwai wani motive ,

    "Dr Bulama im pleading on case ɗin Jabir dan Allah kiyi haƙuri ki janye case ɗin da kika ƙara akan sa na harassment  Abun yayi masa yawa imagine kece a shoe ɗin sa ya za kiyi.

"Wata irin dariya tayi tace "Mr director ,bazan taba zama a shoe ɗin Nephew ɗinka ba ,shi munafiki ne ni kuma ba munafuka bace,bazan taba yin abunda yayi min ba ga wani,"

"Sannan idan baka manta a lokacin da na yafe masa case ɗin harassment da defamation of character na yi tunani ba ɗan iska bane wanda ba a bawa isashen guidance ba,

    Nayi tunanin kuskure ne ,ashe wautace ,so bana tunanin yanzu 'dan na kara da case ɗin akan sa wani abu ne."

    And yes idan na janye masa wannan case ɗin kaga za'a iya bashi licence ɗinsa na aiki wanda ni bana san hakan,

"Amma yanzu kaga an kwace masa lisisi aikin likitanci na shekara goma sha biyu,mene yafi wannan dadi?"

Im Happy that's All that matters ,i don't Care about him .

I didn't spare My baby daddy ,wanene Jabir.

Dukan table ɗin tsakiya ɗaya daga cikin board members ɗin tayi tace"watch it Dr Bulama,you're the youngest here,Mai kika sani?"

Mai kike taƙama dashi da kike fama da wannan arrogant and rude attitude ɗin,

You're just 29 act your Age.

"Cikin sanyin rai umaimah ta kalli matar da Akalla zata yi arbain ,tace"im the youngest ,im the fastest,i'm intellectual,

Na ɗauki ciki guda Uku a womb ɗina ,na haifa ,ina kan raina,less time, but teaching them the best ethics ,and yea Less i Forget kar kice ban faɗa Maki ba,

I Am a single mom. "

Duk wannan yayi girma ga ƴar shekara Ishirin da tara,so Mai yasa Zan Acting Age ɗin when abunda yake kaina yafi karfin age ɗin?

       " Snr Dr Halisa ,cikin mutuntawa ina san na faɗa miki cikin shekarunki Arbain da wani abu na tabbata bakiyi experiencing abunda nayi experiencing a rayuwa ba,this is not the first time da kike poking hancin ki cikin abunda Ya shafe ni,

Kin zata lokacin da kike faɗawa Director ina sleeping da board members ban sani ba?

    "Kar mu fara allura ta tono garma,"

Sannan abu na ƙarshe ,im no hypocrite .

Da shi nake taƙama.

"Gyaran murya president ɗin yayi yace"ba shi Ya kawo mu ba please".

Kallan Dr halisa wadda tayi gum umaimah tayi tace"nima nasan haka Dr halisa ce kamar bata san da hakan ba."

  "Dr Bulama your resignation is rejected tun kafin ki kawo cos i have talked with the management this hospital need you,

Dan Haka on behalf of All the board muna tura miki Apology na abunda Ya faru ,hope You will accept this Apology".

Shiru tayi na wani lokaci idanun ta akan Paki wanda yaci mur kafin tace "ina fatan kuna sane da bani kaɗai akayiwa laifin ba,"Har da Imam paki.

"Hannun sa Ya dunƙule yana feeling less a gurin ,"Murmushi Director yayi yace "we Are very sorry Imam Paki,"

President Ya Karb'a ta hanyar faɗin ,shima yana bin mu cos abinda ma'aikacin mu yayi Ya kusa lalata masa career ɗin sa and babban Abunda dama muka gama yanke shawara Shine,za'a cire sa daga ƙarkashinki dan gujewa jita jita irin haka,musamman wadda ake cewa kuna soyayya.

"Tana kokarin magana paki Ya katseta ta hanyar faɗin,"Dr Bulama i can talk for My self,

Gyara zaman sa yayi a karo na farko yace "with all due respect Inajin daɗin aiki da Dr Bulama i refused to be switched saboda ba Wasa nazo yi ba ,likita anan yayi koƙarin bata mun suna and i know the law i can sue this hospital for All i care,

So banzo na zauna anan ba dan ana mun Kallan kaɗan.

"And yes Ba soyayya muke ba ni da Dr Bulama nine nake soyyaya da ita, rumours ɗin kusan gaskiya ne amma Zan muku ƙarin haske ,

"Ni nake san Dr Bulama amma its a one sided love,im confessing a nan saboda babu wani protocol da ya haramta mun san Dr Bulama,

And ina faɗa ne to clear duk wani confusion,

Cos i know im not in the wrong,so im begging With the board and All the staff akan kowa Ya fita issues ɗina ,its gonna take me a year here, then im out.

Sannan ni Aiki nazo yi ba wani abu ba,sannan soyayyar da nakewa Dr Bulama bazata tab'a shiga tsakanin Aikina ba.

Haɗe hannayen sa yayi biyu Kafun Ya tashi ya fita ba tare da Ya damu da abunda zai biyo baya ba.

    "Shiru gurin ya ɗauka kowa na ciki shock ɗin confession ɗin Paki,karma ace Dr bulama wadda tafi kowa shiga 'dan bata taba tunanin Paki zai yi hakan ba,sannan tana Mai jiyo fushi a maganar sa.

"Haɗe rai tayi cos bata shirya amsa abunda zasu faɗa ba musamman yarda kowa yake kallanta tasan akwai masu magana.  "

"Cikin haɗe ran ta miƙe tace ,Apology accepted and i will put paki in the right place,pardon his attitudes ".

"Da haka ta fice a board room ɗin inda ta bar su da maimaita Ya akayi."

"Kai tsaye neman Paki ta fara,

"Good morning Dr bulama,Aisha shareef ta gaisheta a yayin da take hangen imam,

"Ɗan tsayawa tayi ta kalleta Kafun tace"morning and yes ki kiramun Paki kice masa ina nemansa a cabin ɗina.

A cabin ɗinki?

Aisha ta tambaya da wani irin tone.

"Har umaimah tafara takawa ta tsaya ta juyo ta kalleta musamman jin da yayin da Aisha tayi maganar".

"Dan daga girar ta guda ɗaya tayi tace "Kina da matsala da hakanne?"

"Saurin kaɗa kai Aisha tayi 'dan ita kanta bata san ma maganar ta kwace mata ba".

"Juyawa umaimah tayi ta bar gurin tana Mai jin wani irin yanayi Akan Aisha wanda ta kasa fassarawa,"Tafi mai dashi a jinin su bai haɗu ba .

"Tafi minti nawa a zaune tana jiran Paki amma yaki zuwa,"Sai da ta fara tunanin ko Aisha bata faɗa masa tana kiran sa ba ,

Tana kokarin tashi taje ta samesa Knocking ɗIn sa da ta haddace ya mata sallama.

"Bayan Ya shigo ya tsaya a tsaye yace"Dr Bulama Kin kirani and Na tsaya stitching  ma wani patient ciwo ne as per Nurse Farouk instruction".

"Kallan sa tayi da kyau jin yarda yake mata magana kamar bashi ba, "

Alamu ta masa da hannu tace "zauna"

Cike da kafewa yace"im okay Dr and Dr Kaseem yana nemana idan babu damuwa ina san ki faɗa da sauri,idan ba urgent bane kuma naje na dawo".

"Cikin sosowar rai tace Imam paki have a seat bana san na sake repeating kaina, "

Kamar bazai zauna ba amma sai Ya zauna ɗin yana Mai Kallan gefe.

Ji tayi wani irin yanayi na rashin dadi Ya ziyarceta,

Cikin kulawar da bata san tana da ita ba tace "akwai abinda ke damunka ne,"Zan ma Farouk magana Ya dubaka.

Murmushi yayi kafin yace "a makarantar mu nine must brightest student,sannan na fita da First class, bangaren medicine kenan kama ai kinsan ba abun Wasa bane,so ina da capability ɗin ganewa idan bani da lapia ko a'a bana buƙatar kowa.  "

"Haka nan taji yayi mata wani irin kwarjini a karo na farko,"

Dan har tana hada in ina a maganarta musamman yarda taga Ya kuramata ido da wani irin yanayi,

Sauke idanun ta tayi saboda yarda taji Idanunsa na mata a cikin nata.

"Wani irin murmushi yayi yace"Dr Bulama Stop making me feel less,i can fight for me,ni namijine da yasan right ɗin sa,im not some coward ,and yes im not scared 'dan nace ina sanki cikin gurin Chan mai cike da mutanen banza ".

Ai ba laifi nayi ba ko sab'awa mahalicci ,ina sanki kuma har gobe ina sanki, and nasan kinajin wani abu a zuciyarki a tatare dani,

Musamman idan ina tare dake ,idan kikaji muryata nasan zuciyarki na bugawa da sauri,

Sannan idan baki jini ba nasan kina kewata.

Amma Zan ɗaga miki kafa tunda kamar ina zaƙewa da yawa,duk lokacin da kika gama tattara shawararki akaina ni a kullum ina tare dake ,sannan maganata da nafaɗa na barin field ɗin nan idan har bakiji wani abu na soyayyata a tatare dake ba nan da shekarar da Zan bar nan then na maki Alƙawari zan aje mafarkin zama surgeon .

"Yana gama maganar sa Ya tashi yakama Hanyar fita ,yana ji tana masifar Ya dawo bata gama dashi ba and how dare he zaina Wasa da mafarkin sa akan soyayya."

Banza Yayi mata,tun ranar Ya chanza Mata baki ɗaya ,tun tana wa kanta excuse akan baya damunta har zuciyarta ta yi ƙarfi wajen karyata ta 'dan sosai take jin abun har ranta ,musamman a yanzu da taga wani kusanci da Ya shiga tsakanin sa da Aisha shareef musamman idan tana musu lecture.



*

Cikin sati biyun nan halayyar paki ba karamin damunta take ba,cos a yanzu tunanin sa yana ɗaya daga cikin abunda yake hanata sukuni,

    Kafun Hindu ta wuce tasha faɗa mata tana san paki ne wanda take shan mur tace Ai karyane ita ba sanshi take ba amma a yanzu tana neman ta ƙaryata kanta.

"Kai tsaye bayan Ta raka su Nameer Airport tayo asibitin,

Tunda ta shiga take san ta sa idanunta akan Paki amma bashi babu alamun sa,

A ranar koda taga babu shi bata tsaya basu wani lecture ɗin kirki ba,

Bayan ta gama suna fita,tace "Kabir ashir."

Juyowa yayi yayin da ta masa alamu da hannu akan yazo,

Babu musu yaje yana Mai boye karamin murmushi a zuciyar sa yana faɗin "shege paki yasan Mai yataka.

"Kamar kuwa yarda yayi expecting yana zuwa tace paki 'fa".

"Dan Sosa kai yayi yana san tuno yarda Paki Ya shirya masa kafin yace"Ai Dr Paki yana gida bashi da lapia sosai,"

"Cikin reaction ɗin da bata san tayi ba tace "bashi da lapia kuma?"

Mene yake damunsa?

And idan baya da lapia mai yake a gida?

Boye dariyar sa yayi yace"Ai yana Chan kuma rashin lafiyar sosai yake amma ko ummu bata sani ba 'dan yana part ɗinsa a kunshe".

Cikin damuwa tace "and kake nan Kana faɗa mun when Kana abokinsa,idan shi baya san lafiyansa Ai akwai masu so".

"Na'am ?"KB ya tambaya bayan sarai yaji abunda tace,

Wani irin kallo ta bashi musamman da ta fahimci abunda tace,

Tashi tsaye tayi tace ,

"Kaini Gidansu."



*********

So jiya baku samu update ba cos banji daɗi ba ,

But im Good.

To munje gidan Muntari ɗan Nana Mai abun mamaki,

Team# pakiumaimah

Kuna kusa?



Chuchujay ✍🏽

To be continued .

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top