episode 14

AURE UKU

(a hospital romance)

      By

Chuchujay

    ✍🏽

Ga masu san a tallata musu hajarsu

09058191213.

Episode 1⃣4⃣

    A yarda umaimah ta figi motarta Allah ne kawai Ya kaita gida,

A lokacin da ta tafi rasa abunyi paki yayi amma yana bukatar wanda zai hana umaimah zuwa italy,

Kallan Hindu yayi yace"babu wanda zaki kira ki faɗa masa cos she cant go to italy, zan ji da komai ."

"Ƙaramun murmushi tayi tace "do you love her that much"?

"Shafa kansa yayi yace "with My life".

"Murmushi tayi tace"tana da soft heart  and im sure a zuciyarta kana da wani soft guri kawai ka bata maganin attitudes ɗinta "

Ka fahimceni?

Murmushi yayi yace "zai gwada ."

Wayanta ta ciro ya kira Yaya Abubakar dan kaf gidan shine take da numbern sa shima ɗan umaimah ta tab'a ƙiran sa a wayanta ne.

Ringing ɗaya Ya ɗauka,

Bata b'ata lokaci ba wajen sanar masa abunda Ya faru tiryan tiryan,

Godia yayi mata yace yanzu zai kira daddy sannan Umaimah baza taje italy' ba.

"Tana gama wayan Paki yace "bari na bita, Yana ƙorakin shiga motar sa tayi folding hannun ta tace "dan saurayi idan ka tafi ni wanene xai maidani gida?"

Sosa kai yayi yace "im Sorry dan Allah,"KB Zan barka nan ina nan dawowa.

Shi da Hindu suka nufi gidan su umaimah .

A bakin gate ɗin tamfatsetsan gidan Paki yayi parking motar sa ,

Kallan sa hindu tayi tace bari na maka iso a maimakon Umaimah i know she wont mind.

A tare suka shiga ,kai tsaye part ɗin umaimah suka nufa ,dama ita ba gwanar kula maƙiyan umaimah bace a gidan ,

Sannan bata damu da shiga ta main gidan ba ,kofar da zata sadata da sashenta kawai take nufa.

Tsayawa Paki yayi a bakin kofa,

Juyowa tayi ta kallesa tace "yadai?"

Dan Sosa kai yayi yace "i think ba dai dai bane na shigar mata guri kai tsaye bata san da zuwa na ba".

"Karamun murmushi Hindu tayi tace "kar ka damu You're not going to find her naked i promise".

Ƙasa yayi da kan sa cikin jin kunya,

Gaba tayi yana biye da ita a baya,

A cikin wani tamfatsetsan falo suka tsaya,

Babu alamun ta dan haka hindu tace 'bari na ƙarasa inda idan kaje you might actually find her naked dan nasan yanzu haka tana chan tana shirin tafiya italy' cikin rashin sanin masu hanata na hanya.

Zama yayi yana Mai Jin nauyin maganar Hindu wadda ya kula ita ko a jikin ta,

Yana wannan zaman Nameer Ya shigo duba da shi yanzu ba zuwa makaranta yake ba ,yana shirin wucewa Abuja.

"Turus Nameer yayi lokacin da yaga Paki,"

Da murmushi Paki Ya kalle sa yace"Big boy ."

"Haɗe Nameer yayi yace"im not a boy,i Am a man Cos a sashen mu nine babba kuma protector ɗin mami , "Mai kake yi anan.

Faɗaɗa murmushi Paki yayi cos fushin Nameer a gurin umaimah Ya kwaso shi,

Yana Mai kokarin magana muryar umaimah ta katsesa a yayin da take fitowa daga sashen da Hindu tayi hannunta dauke da jaka tana faɗin"Hindu kima daina koƙarin tsayar dani 'fa,wallahi Habib sai Ya kwashe kashin sa a hannu tunda dai shi bai gaji mutunci ba,"Wallahi sai yaga kalar wulakanci na da bai tab'a gani ba.

'Mami Habib?

Mai yayi miki,

Mai Habib ɗin yayi miki.

Muryar Nameer ta ziyarce ta cikin wani irin fushi ba kamar na yaro ba.

"Turus tayi Kafun ta tako gareshi tace"Nameer yaushe kuka dawo kai da daddy"?

"Yanzun nan ya bata amsa Kafun Ya sake cewa "mami Mai Habib yayi miki".

Durƙusawa tayi dai dai tsayin sa tace "Nameer na faɗa maka ba sau ɗaya ba ka daina kiran sa Habib He's your father for God sake. "

Ture hannunta da ta dafa kafaɗarsa yayi yace"mami he's not My father ,na faɗa miki ba sau ɗaya ba shi ba daddy na bane ,i might be using his name amma mami we are not related."

"He lost that right mami a long time ago, ki faɗa mun abunda BASTARD ɗin nan yayi miki and i swear i will kill him.

"Babu wanda yayi tsammanin Abinda Ya biyo baya,sosai umaimah ta ɗauke Nameer da mari Mai zafi idanunta cike da kwalla tace "who taught you that"?

"Uban wanene Ya koya maka wannan?"You're  calling your father a bastard har kana cewa zaka kashe shi.

"Ni na koya maka wannan?"

Tana kokarin sake marin sa hindu tayi saurin shiga tana cewa 'a'a Bulama.

Sai a lokacinne ta kula da paki wanda ya janye Nameer daga gurin.

"Sake nuna Nameer tayi da yatsa tace "i raised you to be better than that,"ko mene ke tsakani na da mahaifinka tsakanina da shi ne amma baka da right ɗin zagin sa har kana ikirarin zaka kashe sa.

Kwace wa yayi daga hannun Paki Ya nufi hanyar da zata sadasa da inda ɗakinsa yake Kafun yace "amma mami ina da right ɗin tsanar sa and you can not do anything about that, i hate him and idan na girma na tsincin Ya miki abunda ban sani ba yanzu i will kill him,saboda you're  My World .

Da gudu ya shige,

Zaman ɗirshen tayi a kasa tana Mai cewa "shekarun sa sha ɗaya kawai fa,"He's just 11,and ina Kallan tsanar mahaifin sa akan idanun sa,why me?

Mai yasa kaddarata zata zo da haka?

Yaro ƙarami amma a cikin kwayar idanun sa akwai kiyayya.

"Habib shine wanda ya fara ja mun komai saboda duk da ba dan 'ina san shi na aure sa ba Atleast da yana da decent life i will get to adjust,amma yayi ruining komai ,sannan bai tsaya anan ba After 11 years yake san b'ata mun rayuwa".

"Mene laifina Hindu?"

What's My fault?

"Yarda nameer yake yanzu Ya kike tunanin zai kasance idan nan gaba yaji labarin abun da yake faruwa a yanzu?"

Nasan da ace daddy bai jama ƴan gidan nan kunne ba akan abunda suke yi ba da za'a samu mai faɗawa Nameer abun da yake faruwa ,

Sai kuma maine zai faru?

Kuka sosai ta fashe dashi.

Kukan da take haka paki yake jinsa har cikin ransa ,

Idanunsa ne suka fara kawo ruwa dan akan umaimah da damuwarta ya manta da Mai ake kira Dakiya da jarumta,

Zuciyarsa ce ta ƙara karyewa da Ya fahimci a gidan mahaifinta ma ita da yaranta bawai zamane ake dasu na soyayya ba.

Juyawa yayi ya fita dan idan Ya cigaba da tsayuwa bai san maine zai faru ba.

Rungume ta Hindu tayi bayan fitar paki tana Mai lallashin ta,

Zumbur Ta miƙe tace"sai naje italy' na kamo habib nasa an wulaƙanta mun shi a kasar nan,".

"Baza kije italy' ba."

Ɗaga kai tayi 'dan ganin Mai maganar,

Da gudunta ta ruga gareshi ta faɗa jikinsa tana Mai faɗin"Daddy".cikin kuka,

Shafa ƙanta yayi a hankali  kana ya raba ta da jikin sa ya kamo hannunta Ya zaunar da ita kan kujera Ya zauna a ƙasa hannunsa cikin nata .

shi kaɗai yasan irin raɗaɗin da yake ji a zuciyarsa idan yana ganin umaimah ciki hali irin wannan.

gefen ta yaya Abubakar yazo Ya zauna shima yana jin dama zai iya ɗauke mata kuncin dake damunta Ya maida kansa.

Daddy ne yace "umaimahn daddy,"Ni kaɗai nasan abunda nake ji idan ina ganin hawayenki,jikina yana bani Nana surbajo bata farin ciki dani a duk inda take saboda i failed her,

"Nine na ja miki komai sabida ni na haɗa Aurenki da Habib a karo na farko sannan na haɗa a Karo na biyu,"

Ki yafe mun umaimah ,soyayyarki ce ta rufe mun ido nayi tunanin gata ne na miki.

Saurin goge hawayenta tayi tace"daddy mana,ni baka mun komai ba ,hasalima dalilin Auren na samu ƴaƴanda wasu ma da kuɗi suke nema amma sun rasa,"Ni'ima ce Allah yayi mun a lullube kuma ina gode masa a kullum daddy,

"Idan ka cigaba da ɗorawa kanka laifi ni Bazan iya yafe wa kaina ba,"Ƙaddara tace da babu wayau ko dabarar da za'isa na tsallake ,

Mene kuma abun daɗin daddy?

Ina da rayuwa kuma ina da lafiya shine yafi komai .

Murmushi yayi ɗan yana san yaga da kanta ta lallashi kanta wanda a Yanzu tayi sannan Ya gamsu da ƴar ɗiyar sa Ta girma .

Goge mata ƴar karamar kwallarta yayi yace "nan da awanni 48 za'a kawo mun Habib har gida ba sai Kin wahalar da kanki binshi italy' ba,"

Ba italy' ba ko ina ya buya a cikin duniyar nan ina da yarda zanyi a ɗukafar dashi gabanki sannan ban shirya sassauta masa ba ,tunda bayan shekara goma sha ɗaya bai ƙasa a gwiwa ba yazo dan bata miki,

Nikuma na shirya yaƙi da duk wani Mai saki kuka yarinyar daddy.

"Murmushi maganar da yayi ta karshe tayi ,"

Daddy ya kamata ka gane yarinyar nan ta girma fa yaranta uku fa amma Bazaka ɗaina shagwab'a taba .

Yaya Abubakar Ya fada.

Murmushi daddy yayi yace "ai ko duniya umaimah ta tara tana nan a yarinyar daddy."

A haka suka gama lallashinta Kafun suka tafi,

Bayan Ya rage daga ita dai Hindu a ɗakin ne ta kalleta tana tunanin ta inda zata fara tambayarta ina Paki,

Ɗan shiru tayi Kafun tace "ke dawa kika dawo"im sorry na barki ke ɗaya."

Ƙaramun murmushi Hindu tayi tace"kawai kice mun ina Imam paki,"To Inajin Ya wuce.

"Ya wuce kuma?"

Kallanta hindu tayi tana mai san gintse dariyarta tace "kina da matsala da hakan ne?

Ɗan haɗe rai tayi tace "ina tambayane kawai ɗan Ya shigo har falo ba ba tare da izini na ba."

Dariya Hindu tasa aranta tace "munafuka kina so kina yanga".

*********

   Kwance take kan Gadonta da dare tana Mai tariyo abubuwan da suka faru a yau,

Tunanin Paki Shine abinda yafi damun kwakwalwarta dan duk yadda taso ta cire sa ta kasa.

"Yau yazo sannan yaga wani bangare nata da ba kowa Ya sani ba,

A lokacin tsintar kanta tayi da kasa yin shiru na abinda yake damunta 'dan Nameer Ya riga da Ya gama tabo mata damuwarta,

Tsakanin ta da habib kiyayya ce amma bazata taba bari tsakanin sa da Nameer Ya zama kiyayya ba duk girman lefin da zai mata.

Gyarawa Abdallah kwanciyarsa tayi daga kan cikinta dan yanzu baya yarda yayi bacci idai ba a gurinta ba a gurinta ɗin ma a jikinta,

Murmushi tayi tana Mai kissing goshinta a zuciyarta tana Mai faɗin"ko me kaikuma Zan faɗa maka akan naka mahaifin idan ka girma?"

Ta dai san baza ta tab'a faɗawa Abdallah mahaifinsa ɗan blood money bane komai rintsi,sannan Zatayi duk yarda Zatayi taga abun bai bibiyesa ba Tayi Wannan alwashin.

Addua tayi masa tayiwa kanta ,

Tana rufe idanunta paki Ya cigaba da dawo mata,

Jin tunaninsa zai addabeta yasata jawo wayanta ta shiga numbernsa da tayi saving da INTERN I'P .

    "Murmushi tayi a yayin da zuciyarta ke ingizata akan ta kirasa,"

Har ta danna zata ƙirasa Tayi saurin fita kamar an tsikare ta.

"Karshe ta tsinci kanta da tura masa message "thank you for everything'."

Tafi karfin minti nawa tana duba wayarta taga ko ya maida mata amma shiru,a haka har bacci b'arawo Ya kamata.

Bangaren Paki kuwa.

    Yana fita a sashen umaimah ya fita a gidan baki ɗaya,motar sa Yashiga ,kai tsaye gida Ya nufa yana Mai jin zuciyarsa na Tafasa,

"Yana ƙokarin haurawa sama yaji muryar nana na faɗin"an dawo daga kokerar ne?"

Shine kake fama sanɗa kamar b'arawo?

Ba tare a Ya Kalleta ba yace "Alhamdulillah ba'a Sino's biggest super market aka kamani ba da hannuna maƙale a baya ina zazzare ido kamar an ƙaɗa bera a buta ba".

Ki barni yar da kika ganni nana dan Allah.

Har Ya haura saman yana jin banbaminta da bala'inta na yau da kullum.

Kai tsaye ɗakin ummu Ya nufa,

Yana knocking sau ɗaya ta bashi izinin Ya shigo,

Zaune Ya tarar da ita tana duba wani file,

Zama yayi kan stool Ya gaida ta,.

"Amsashi tayi tana Kallansa kafin tace lafiya dai ko?"

Naga ka dawo da wuri.

Saukowa yayi daga kan stool ɗin Ya zo kusa da ita ya zauna yana Mai ɗora kansa a kafaɗarta Kafun yace"Ummu zuciyata zafi take mun".

Cikin rikidewa tace "wanne irin zuciya kuma muna zaune kalau Imam?"

Hawayen dake maƙale a idanun sa ta hango,cikin tashin Hankali tace"tashi muje asibiti imam ba abun Wasa bane wannan harda kuka?"

"Ƙaramun murmushi yayi yace dama akwai likita da zai mun magani ummu,".

Dafa sa tayi tace Imam kasan dai baka da wanda zaka faɗawa damuwarka sama dani ko?

"Just tell me ni da kai zamu gyara komai ,"i promise,akan clip ɗin chan ne,hope baka da hannu ciki?

"Dan ajiyar zuciya yayi yace an kama waɗanda suka dora ma".

Ajiyar zuciya tayi tace Alhamdulillah "Wallahi yarinyar jiki na raina ,na ji tausayinta Sosai".

Tsintar kansa yayi da murmushi dan yasan mahaifiyarsa ce zata fara ƙarb'ar umaimah.

Haka nan Ya barta ba tare da Ya faɗa mata komai ba yana Mai jiran lokaci.

Yana tsaka da tunaninta da  halin  da Ya barota yaga saƙonta,

Kamar an sashi a aljanna musamman da Ya tabbatar tayi saving layinsa kennan.

"Har zai replying huɗubar Hindu ta dawo masa, "

Haka Ya dane zuciyarsa ba tare da Ya mayar mata saƙon ba duk yada yaso kuwa.



Chuchujay ✍🏽

T

B

C.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top