episode 13

AURE UKU

(a hospital romance)

  By

Chuchujay

Episode 1⃣3⃣

Wannan episode ɗin nakune masu comment inajin daɗin sharhin ku❤

     CITY TEACHING HOSPITAL

7:00am.

    Idan bawa na cikin fushi a yanayin fuskar sa idan ka kalla zaka tabbatar da wannan fushin da kuma kimanin adadin sa,

"A yanzu ma idan ka kalli fuskar umaimah zaka tabbatar da irin fushin da yake cinta Ya wuce lissafi Ainun ,"

"Cikin takun ta na isa da izza take takowa cikin asibitin ,

Sanye take cikin Doguwar Abaya navy blue ,kafafun ta cikin Gucci heels Black ,idanunta kuma cikin sun glasses na ralphs ,

Idan ka Kalleta sai ka kuma kallan ta,tayi kyau ainun amma a kan fuskar ta babu annuri. "

Gefen ta Hindu ce bayan  su kuma tare da jami'an tsaro  guda biyar ƙwarara waɗan da suka san Mai suke.

Kai tsaye ciki ta shiga suna biye dasu ,

Kowa da kus kus ɗin da yake akan abinda yasa ta kawo yan sanda asibitin,

Turus tayi lokacin da taga Paki a inda take da burin zuwa tayi rashin mutunci da sojoji guda uku sun kamo ƙwalar Dr jabeer zasu fitar da shi ,

    Ƙarasawa tayi tace Mai ke faruwa anan?

"KB ne Yayi charaf Ya amshe yace"ga wanda Ya dora clip ɗin nan online san nan mun zo gareshi ɗan san tabbatarwa yana mana ƙaryar bashi bane,dan haka zamu tafi dashi chan inda Ya kamata mu ɗan rarrashe shi."

    "A hankali ta taka gaban Dr jabir tana Mai cire glasses ɗin ta tace "nan asibiti ne kuma gidan marasa Lapia na tabbata basu buƙatar damuwa ,

A yanzu ni nazo da arrest warrant,kun san duk hukunci bazai wuce na police ba ,amma inaso waɗan nan handsome And hot soldiers' ɗinna mu su ɗan lallasar mun shi.

" a gabana Ya faɗa mun abunda na masa da Ya hassada wannan gagaruwamar tsanar dake tsakani na dashi  .  "

"Kallan yan sandan da tazo dasu tayi tace "

    Inspector Na fahimci abun na gida ne amma zan neme ka idan da yuwar hakan .

"Murmushi Inspector ɗin yayi yace "ba damuwa hajiya im at your Service a koda yaushe ,just give me a Call,".

"Godia tayi masa Kafun tace Sai na sake nemanka".

"Dan Allah umaimah ki saurareni ,sabani ne muka samu tsakanin mu, Kin manta tsakanina dake Ai min sassanta taya za'ayi kuma na maki ba dai dai ba?"dan Allah kar ki bari mutanen nan su tab'ani

Dr Jabir Ya faɗa a ruɗe.

Ƙaramar dariya tayi tace "to banace ba ,amma nima ai bance zan maka wani abu ba ,cewa nayi za'a lallab'a mun kai a tambaye ka dalilin da yasa ka ɗora ba komai ba ,menene na tsorata haka nan.

"Kallan sa Hindu tayi in a disgusting manner tace "gaka dai ka haɗu amma a kasan zuciyar ka baka haɗu ba "i mean menene ribar ka? ".

"Dafata Umaimah tayi tace bari idan muka je aka lallab'a mun shi zai faɗi ribarsa,".

Kallan ɗaya daga cikin soldier ɗin da kamar jira yake tayi tace "My brother a ɗauke sa muje a lalaba shi,"

"Kamar kuwa yana jira Ya suresa a kafaɗa ,ihu Dr Jabir yake yana faɗin dan Allah ta rufa masa asiri ".

"Kafun kace mene an taru ana kallan su ana kus kus,"

"Motarta suka shiga tare da Hindu yayin da su Paki  suka saka Dr Jabir a motar da suka zo da ita".

"Umaimah na ƙokarin tada mota Hindu tace "girl baza ki bawa guy d'in chan chance ba kuwa ?"He have the qualities and kalli fa yarda Ya nuna damuwar sa akan ki ,yanzu haka kina kallo ke yake kallo yana jira yaga motan ki kawai Ya tashi,

Hes a real gem ƙawata.

"Kallan paki tayi ta glass ɗin gaban motar ta taga da gaske Kallan nata yake ,Sniffing tayi tace "ba abun mamaki bane yarda Ya saka effort akan case ɗin nan ,kar ki manta ba ni kaɗai bane jiki har dashi,"

"So yana yi ne dan kansa shima,And he might be a gem, ko yana nuna kulawarsa aikaina ko wani abu,"

"Kar ki manta A mazan da na Aura nayi Auren soyayya ,And it was a very beautiful moment kafun nazo na gane kuskurena so dont Judge BOOK by its cover".

"Kaɗa kai tayi tace "ƙwarai we shouldn't Judge BOOK by its cover so shima Paki kar ki judging ɗin sa according to what you faced,"

"Wani abu deep inside me yana faɗa mun Paki Alkhairi ne sannan karki manta har Hafiz Ya mutu yana san ki ,kawai dai shi hanyar da Ya ɗauka dan yin rayuwar sa ne ba mai kyau ba ,amma kema kin san yana sanki,"

Allah Ya jiƙansa da Rahma.

"Tashin motan umaimah tayi bata ce mata komai ba ,Motar da aka saka Dr Jabir ta bi ganin sun yi gaba ,tana kallo ta mirror Paki Ya shiga motar sa Ya biyo su.

"Kallan ta Hindu tayi da ta kula da wanda take hange tace "you're young umaimah kar ki cutar da kan ki ,just Listen to your heart and fuck the society ".

"Ba dai tace mata komai ba ta tashi motar ta ,ganin bata ce komai ɗin ba yasa Hindu yin shiru amma tasan a zuciyar Umaimah tunanin abunda ta faɗa mata ɗinne Take".

"Gate ɗin wani ware house aka buɗe musu suka shiga,

Dariya umaimah tasa lokacin da ta faka motarta ta kalli Hindu wadda ke mata kallan "dariyar Mai kike " Kafun tace "Kin san mai nakewa dariya

",wata dariyar ta kuma sakawa Kafun tace "

"Idanun Jabir nake hangowa kilan yayi shiru ne dan yaji ina faɗin a lallab'a mun shi ,ai kuwa zai sha lallaba dan a idanun soldiers' ɗin chan ma ƙiris suke jira.

     "Tana kokarin fitowa a motan paki yazo Ya buɗe mata kofan motan idanun sa cikin nata,itama ɗin shi take kallo,

Ganin Ya tare bakin kofar yasa Hindu buɗe side Ɗinta ta fita tana Mai murmusawa,

Kallan sa take itama shiɗin ta ke kallo taƙi ce masa ƙala,

Tsugunnawa, yayi kan gwiwar sa  yace "abunda kika ce akan ko ina da hannu akan Clip ɗin chan yanzu Kin tabbatar da bani da hannu,And Koda wanda na sani ne muddin da hannun sa ciki bazan barshi ba sannan soyayyar da nake miki Mai tsafta ce,ba wai ina sha'awarki bane,ƙaunarki nake.

"Bana fatan abunda zai b'ata maki suna duk ƙanƙantar sa,ba kece ba a clip ɗin chan amma kasancewar Fuskar ki ciki ba ƙaramun soya mun zuciya yake ba,"

"Dafa saitin zuciyar sa yayi yace "wani irin ƙuna haka nake jin zuciya ta ,"

Ƴar ƙwallar dake shirin zubowa a gefen idanun sa Ya goge yace "wallahi tallahi Umaimah ina mutuwar sanki ,wallahi ina miki san da bana yiwa kaina.

"Ƴar da kike nuna kamar zamana cikin soyayyar ki abune mara dacewa, da ace da yarda zanyi na cire soyayyar ki da na yi Ɗan na faranta miki rai ,

Wallahi umaimah ina sanki da yawa babu abunda Ya dameni da past ɗin ki ni present ɗin ki ne a gaba na,

Kiyi haƙuri idan soyayyata tana b'ata miki rai .

Tashi tsaye yayi ya juya yana Mai goge idanun sa,

Ba tare da Ya juyo ba yace"And na manta ban faɗa miki ba ,guy ɗin da yayi editing Clip ɗin yana ciki shi muka fara kamawa Kafun Ya sanar mana da Dr Jabir Ya bashi kuɗi masu yawa yayi editing amma bashi yayi uploading ba ,sannan an cire clip ɗin daga dukkan websites,".

"Juyawa yayi Ya taka Ɗan shiga ciki,"

Baki ɗaya taji kamar an cire mata wata laka a jikin ta,

Kalaman sa ne kawai ke mata yawo a kwakwalwa ,haka nan ta tsinci jin zafi a zuciyarta ta dalilin hawayen sa da ta gani,

"Tafi minti goma zaune a motan Kafun ta tashi tabi bayan sa ,

Tun kafin ta shiga take jin ihun Dr Jabir yana ƙarb'ar warb'a hannun sojojin.

"Zaune ta tarar da Hindu gefe guda tana Mai juya wayarta ,gefe guda kuma KB ne shima zaune sai Paki dake chan gefen Wanda yayi editing Clip ɗin wanda yasha Ɗan banzan duka ,daga gani sai da yasha luguɗen tsiya Kafun ya faɗi sunan Dr Jabir.

"Kallan matashin yaran tayi tace "nawa suka biyaka?"

Bakin sa kamar ansa goruba saboda kumburi kafin yayi mata alamu da hannu.

"Ƙaramun tsaki KB yayi yace 500k fa,just 500k Ɗan kawai Ya b'ata sunan wasu ba tare da yasan Mai zai biyo baya ba,"Guy you messed with the wrong people.

"Zama tayi akan kujerar dake facing Paki wanda koda wasa yaƙi bari su haɗa ido,"

Kallanta ta mayar kan Dr Jabir tace "ku tsaya da dukansa haka",

"Matsawa tayi daf dashi tace "you're a very good doctor ,ina tuna lokacin farko da na fara aiki da kai,it was amazing saboda yarda mukayi aiki hand in hand,"

"I have been dreaming naga na samu likita da yasan abunda yake a kusa dani,"I wanted to work with you again and again saboda kasan Mai kake.

"Ban sani ba ,a lokacin da kazo kace kana sona da wane motive kazo but i told you i wasn't interested da mutunci nayi rejecting offer ɗin ka idan zan tuna ,amma ka dauke sa something else,ban san mane Ya maida soyayyar da kace kana mun ba ta koma kiyyayya  ,"

"Ko 'dan tun farko wani abu ne dama ka shirya?"

"I wasn't understanding sudden diss ɗin ka akaina , "Bani da wani riƙo da nake dashi akan ka,

I don't hate you,

Nasan kilan you're just jealous of me And kana tunanin connection Ya kawoni nan,but i told you ranar a office ɗin Director ,ina matsayin da nake, da gumina,da hawayena ,da jinina .

Da kasan gwagwarmayar da nasha Kafun nazo nan Bazaka ma fara tunanin kaini ƙasa ba.

"But you decided to,ba tare da kayi tunani sau biyu ba kwakwalwarka ta baka wani banzan shawara na ɗora edited clip ɗin nan da Intern ɗina ."

"Kasan kuwa abunda ka aikata?"

Kasan girmansa kuwa ?

Ƙaramun murmushi tayi tace "trust me anan gurin zan nuna maka ƙarfin izzar kuɗi ,'dan bayan sun gama chasa mun kai,za'a kaimin kai Asibitin kaje gaban board members ɗin da kasa suke nuna mun dan yatsa ka wanke ni".

"Ɗagowa tayi ta kalli Paki wanda yayi saurin ɗauke idanun sa akan ta tace "shima ka wanke sa,then i will Call the press ka tabbata ka b'ude kazamin bakin ka kai da wanchan abun then i will decide your fate ɗan ban shirya yafe maka ba nan kusa.

"Tashi tayi tace ina waje ku chasa munshi kamar yarda ake chasa shinkafa amma ku tabbatar baku taba bakin sa ba dan dashi nake san yayi magana,".

Wayar tace ta hau ruri,Director ne ke kiran ta,tana ƙokarin ɗauka ta tsinci muryar Dr Jabir yana faɗin"bani na kawo idea ɗin ba wallahi".

"Juyowa tayi tana Mai ƴar ƙaramar dariya tace"kana nufin kace mun ba kai da wancan abun bane kawai a cikin wannan haɗakar?"

"Takowa tayi tace"its getting more interesting ,faɗa mun wanne shegen ɗan iska ne ɗayan,

Wayartace ta sake ƙara,

Daga masa hannu tayi tace "ɗan tsaya".

"Dagawa tayi tasa a handsfree tace "director ina ji,barka da rana ,ina fatan ƙalau.

"Cikin sassauta murya yace"Dr bulama ina kika kai Dr Jabir?"

Don't do anything illegal with him,kar ki saka kanki ciki matsala,you will answer to the board.

"Gyara zama tayi kamar yana kallanta tace"mr Director sir,ina fatan wanda Ya faɗa maka bai faɗa maka da hukuma nazo ba,Hukuma suka tafi da Jabir dikko har iri biyu,"

"Akwai Dodanni da malaikun duniya a ciki,sannan ni zakanyyar da zan cinye duk wanda yayi ƙokarin Wasa da jelata,".

"Bana tsoran kowa a board ,i told you zan miƙa resignation letter na,kar ka manta sunana UMAIMAH USMAN BULAMA, diya guda ɗaya tilo a gurin attajirin Mai kuɗi nan,USMAN BULAMA"Idan kaga na tab'o nice naso na tab'u,nasan zakace nayi taƙama ko?

"Ƙaramar dariya tayi tace wani lokacin sai da haka"

Na faɗa maka zan kawo maka wanda yayi editing wannan clip ,sannan Next time dear Mr Director kar ka fara yanka huƙunci ba tare da ka san gaskiyar abin ba,

"Gaskiyar kuma gata nan gaba na,muna nan tare da Dr Jabir muna wasan chess and two men down,

Ina fatan ka iya chess kuma kasan me ake kira da two men down,

So na zubar da biyu guda ɗayane nake ƙokarin saurare ka Katseni ta hanyar kira.

"Kallan Dr Jabir tayi tace "maza gaisa da Dr mr director sir sai ka sanar damu wannan Strong opponent ɗin mu sai mu shirya Cos nasan kilan black horse ne ".

"Cikin sheƙewar muryar Dr Jabir yace Hello sir"

Murmushi ta kumayi tace Dr Director kaji Nephew ɗinka ko?

Na'am?

Yafaɗa ta ɗaya bangaren wayan.

Ƙaramar dariya tayi tace "aw Sorry na manta ashe ba baka san nasan Nephew ɗinka bane ba Dr Jabir,"

Well a ranar da ka nema masa yafiya a gurina ranar nasan wanene shi a gurin ka,

Ina fatan ba kaine Black horse ɗin mu ba,?

"Well muna sauraranka Dr Jabir ,sweet uncle ɗinka ne Ya saka ka ko kuma wani mastermind ɗin ne da yafi kawun ka zarra da yayi tsautsayin taka ɗiyar BULAMA?"

Duƙan desk ɗin dake tsakiya tayi cikin wani irin tsananin fushi dan taje maƙura.

"Jin yayi shiru ne yasata nuna sojan da yafi ko wannen su girma da murɗewa tace"

Mr hot soldier, daga gani a training ɗin da ka samu kana haɗawa da Gym ba,Cos you look build i must say.

"Murmushi soldier ɗin yayi yace 'i work out twice a day".

"Tsaki paki yayi yace "And who asked you sau nawa kake working out ?"

Ba wannan Ya kawo ka nan ba.

"Ƙasa yayi da kansa cikin girmama Yace Sorry young master .  "

"Dan karamun murmushi Hindu tayi lokacin da ta hango kishi karara a idanun Imam paki,"

"DR Bulama don't do anything you'll regret, "Muryan director ta wayar Ya karade store room ɗin,

Murmushi tayi tace "naso na manta kana speaker fa,"Well idan Nephew ɗinka Ya buɗe baki yayi magana bazai samu ƙarin duka ba akan wanda yasha ,Amma idan Ya zab'i yayi shiru ni kaina Ban san Mai sojojin nan da suka gino ba zasuyi masa ,

And bana tunanin akwai abunda zan dana sani,amma jabir kuwa yana kan yi.

Daga ɗayan bangaren Director yace "Jabir kayi magana mana wenene yasa ka" .

Fashewa da kuka yayi yace"na yarda ina mutukar kishin yarda Allah yayiwa Dr bulama ƙokari da sanin kan Aiki,idanuna sun rufe har na kasa gane menene dai dai."

"Idan ina ganinta ji nake kamar na hadiye zuciya na mutu ,i Am a second best a asibitin nan and i cant lose to a woman,i wanted to be the first best amma Dr bulama ta shiga mun gaba ta tsole mun ido, "

"Da gaske lokacin da na nemi yafiyarta i mean it amma kwatsam tsohon mijinta HABIB ya kawo mun offer ɗin kaita ƙasa And da haka ma Ya bani 3million sabida da fari naƙi amince wa ".

Dukkan wannan idea ɗin sa ne and tun ranar yabar Nigeria ,ji tayi baki ɗaya jikinta Ya hau karkarwar bacin rai Cos bata taba sanin Habib zai mata abu har haka ba,Cos a tunanin ta ita uwar dansa ce ko dan ɗansu baya Kai wannan limit ɗinba.

"Cin Kwalarsa Paki da Ya tako gurin jin Ya ambaci Habib yayi yace"idan kayi ƙarya ka yarda dani zan cire girmanka na babbalaka na bawa kare kai.

"Cike da tsoro yace "wallahi tallahi ba ƙarya neke masa ba Ai akwai transaction ɗinsa da wayan da mukai."

Yanzu yana ina"paki ya tambaya,"

Kafaɗa mana Jabir"director Ya faɗa".

Yana itally ,

Ya faɗa yana Mai fashewa da kuka.

Cikin wata irin sassanyar muryar broken heart tace "ko birnin sin yaje sai na kamasa na saka an hukuntasa ".

Mikewa tayi ta fita a store room ɗin tana Mai ignoring kiranta da suke.

Da gudu paki ya bita da gudu,

Da ƙar ya kamo hannunta ,

Chak ta tsaya ,

A hankali ta juyo idanunta ciki da hawaye tana Kallan idanun paki wanda Ya Marairaice mata da ido yace ,you cant drive a wannan yanayin sanann ina zaki.

Itally,

Ta bashi amsa tana Mai ƙokarin shanye kukanta Kafun tace "let go of me".

Saurin sakar mata hannu yayi kamar shocking Ya kamasa,

Tana ganin haka ta ruga motanta.

Ko takan Hindu dake ihun ta tsaya batayi ba tayi wani mugun reverse ta fita.



*

Mun tai itally kamo habibu🥵🥵

Chuchujay ✍🏽

TBC.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top