episode 11
AURE UKU
(a hospital romance)
By
Chuchujay ✍🏽
Episode 1⃣1⃣
Kuka yake kamar ƙaramun yaro wanda Ya sa,dafasa yace "Paki kuka kake akan abinda kasan ba kayi ba?"Haba Paki ,
Be a man mana kasani zamu gano wanda yayi abun nan mene damuwar kuma?
"Ture hannun KB yayi Ya dawo yana Mai facing ɗinsa yace "man ba wai ina yiwa clip ɗinann bane kuka,
Ina kukan yarda naga baƙin ciki a idanun umaimah ,KB she's heart broken And hurt ,And kasan menene ,She is mad At me thinking im behind this saboda sammy,
I mean wanene ma Ya kira sammy gurin nan,
Mai yasa daga ganin mutum baka sanshi ba zaka fara zaginsa who on earth does that, ?
"Juyowa yayi yana Mai goge hawayensa yace "look KB Muddin idan na gani da hannun sammy a abunnan trust me She wont like me Cos wallahi zata ga worst of me ."
"Ajiyan zuciya KB yayi yace "so bama damuwanka ke damun ka ba damuwar wata ce"?"
"Man kasan wannan Abun can ruin your career?"
"Ba tare da Ya kalli KB ba yace"aw kai ta career na ma kake ?"Kalli nan Kb bari na takaice maka muddin idan Umaimah na cikin farin ciki Ya ishe ni komai a rayuwa.
"I don't Care about anything else".
"So yanzu ka kira friend ɗin ka richard j nasan he's Good a wannan fannin and nasan shi kaɗai ne wanda zan yarda dashi please KB ina san wankewa Umaimah sunan ta her reputation cant be damage just like that ".
"Da mamaki KB Ya kura masa ido jin bama ta image ɗin sa yake ba na wata yake ."
"Dafa sa yayi yace "calm down Paki you're My brother and bana wasa da abunda zai shafe ka,and yanzu tunda kasa umaimah a rayuwarka itama zan ƙokari na mayar da damuwarta tawa".
"So chill man ina trying layin Richard bana samun sa amma right away zan je gurin sa and sameera tace mun ta wuce gida".
"Da wani irin kallo Paki ya kalle sa yace wane gidan,?"
Dama tana da gida a garin nan ne?
Last i remember bata da gidan zama a garin nan,ko tayi gida ne ban sani ba?.
"Ɗan Sosa kai KB yayi yace "well Ai kasan gidan da take sauka idan tazo Adamawa,tana gidanku ."
"Ƙaramun tsaki Paki yayi yace"No tazo taje hotel ko ta bika gida sabida wallahi idan tana gidan mu ina kallanta haushin Abunda tayiwa umaimah Shine zai dameni and wallahi one word Akan umaimah zai sa na mata wulaƙanci. "
"Yar dariya KB yayi yace"'dan me sameera zata bini gida when kasan mummy da daddy ma yanzu haka basu gida ni ɗayane,"
"Kai kuwa dama ta saba tunda ga Afnan.
kuma ai gidanku ba baƙonta bane dan ta samu karbuwa gurin nana ,and please paki kar ka bari idanunka su rufe akan soyayya kamanta alaƙar abotaka,
Bai kuma ce masa komai ba 'dan ya sani akan umaimah zai manta da kowa da komai.
Yana wannan thought ɗin aka aiko masa sammaci daga director,
Baiji komai ba ya tashi Ya tafi,
Chan Ya tarar da umaimah wadda ko kallan sa batayi ba sannan ga dukkan alamu taci kuka ta godewa Allah saboda yarda idanunta sukayi ja.
"Samun gurin yayi Ya zauna yana Mai gaida director ɗin wanda Ya amsa masa babu yabo babu fallasa ".
Kallansa director ɗin yayi yace "imam paki what's going on?"
Ku faɗa mun gaskiya saboda kunga dukkan ku ahalin gidan mutunci ne ,we can settle this with the truth,this clip is too real to be fake.
"Dukan table ɗin gaban sa Umaimah tayi tana mai mantawa dashi wanne a gurinta Kafun tace "i told you director na faɗa maka that clip is fake,amma idan Bazaka yarda dani da abunda nake cewa ba ,i will Send in My resignation letter ,its that Simple.
"Ba sai ka kira mu tare ba 'dan ka ci mun mutunci ,na faɗa maka countless time with out Number that He's just an intern dake ƙarkashina And nothing more ,ba Mai bina bayani tunda duk wanda nayi bai gamsar da ku ba".
"Kafun a fara board meeting akaina zan aje aiki a asibitinnan its not that hard ,"
But for God sake director ka daina dagewa aka lallai sai ka lallata mun image shi kuma ka bata masa career ɗin da Ya fara with All due respect.
"Tana kai karshen maganarta Ta tashi tafita a office ɗin ba tare da ta damu da kiran da director ɗin yake mata ba."
"Kallan director paki yayi bayan fitarta yace"sir video ɗin nan editing ne its fake sannan ka bani 24hours zan kawo maka tabbacin haka ,sannan ka daina kokari bata sunan Dr bulama kun daɗe tare da ita Ya kamata ace kana cikin masu shaidarta da hallayanta ".
"Ƙaramun murmushi Director yayi dan Ya kasa yarda wai editing ne ,amma jin abunda paki Ya faɗa yasa yace yaji ya bashi 48hours.
Sallama yayi masa Ya fita yana Mai jin kansa na masa wani ciwo,
**
Ina shegiyar take ,
Nana ta tambayi sameera a lokacin da suka shigo harabar asibitin,
"Riƙe kugu nana tayi tsakiyar asibitin tana Mai ɗaga murya tana cewa "ina karuwar da ta lalata min jika ,dama na faɗa Ai akwai dalilin da yasa imamu ƙin kawo mata gida ashe wata kafurar ke sakuce sa,to wallahi yau ko ni ko ita.
A hankali mutane suka fara maido da hankalin su kan Nana,
Dr maryam ta ƙaraso garesu ganin yarda Nana ta rike ƙugu tace "baba akawo stretcher ne " ?
Da masifa Nana tace "ubanta da uwarta za'a kawo,"
Kafun Dr maryam ta farga Nana ta chakumo wuyanta ta fara yanka mata mari tana Mai faɗin"Allah Ya tsine miki,gaki ɗai ba wani kyau ba amma Kin iya kai yaro ƙarami gado ki lalata".
"Rike hannunta sammy tayi tace "nana ba ita bace ba".
Kallan Dr maryam tayi hannunta cakume a kwalarta Kafun tace "Aw Allah yar nan?"
Ni nace wannan tayi muni da yawan da gurin da zai bi ɗin ma ba zai dadin ba,
Sameeratu ki kaini gurin makirar,
"Hannu Dr maryam tasa ta banbare na Nana tana Mai jin zafin zaginta da tayi da kuma na marinta,"Cikin fushi ta kalli sameera tace "ina fatan kin san nan ba asibitin mahaukata bane da zaki kawo mana mahaukaciyar da ta kwace har tana mari".
Cike da rigima nana tace"la la la la,nice mahaukaciyar,""Kinsan wanenen ɗana kuwa a najeriya ,
To billahilazi yau sai kinsan Kin kira uwar baban soja mahaukaciya,
"Sake riƙe Dr maryam tayi ƙam ƙam tana Mai faɗin bari na kira muntari sai ki kira uwarsa mahaukaciya kiga abunda zai same ki.
Tana kokarin danna kiran idanun sameera suka sauka kan umaimah dake kokarin shiga cabin ɗin ta .
Jawo hannun Nana tayi tace 'Nana ga karuwar chan,
"Babu shiri nana ta saki Dr maryam,ta nufi umaimah gadan gadan,"
Yan kallo suka fara bata guri dan kowa yayi tunanin mahaukaciyar ce,
Umaimah na kokarin buɗe kofar cabin d'in taji an jawota baya an dauke ta da mari,
"Dafe kuncinta tayi da mamaki tana Kallan Nana kafin hankalinta Ya kai kan Sameera,"
"Sauke hannun da ta dafe kuncinta tayi tace"baba wato yarinyarki taje ta ɗauko ki ba tare da taji kashedin da nayi mata ba Shine ta sa kika mareni tunda ku Naga alama tunanin marin mutum a jiniku yake baku tunanin Mai zaije Ya biyo baya"
"Zan yafe maki darajar tsufanki saboda ina da abinda Ya dameni ,Kallan Nurse farouk tayi tace "kira securities su rakasu farouk"
Ta juya zata shiga nana ta sake finciƙota zata mareta ,
Charaf umaimah ta rike hannun sosai wanda sai da nana tajishi har kashinta Kafun tace "Kaka kije gida ki huta ".
Sakar mata hannun tayi ,take idanun Nana suka kaɗa sabida haushin umaimah tamata iskanci da jika ta hana shi Aure sannan ta mata rashin kunya,
Sake kwaƙumo umaimah tayi ta kama hannunta ta kafa mata haƙorinta wanda yasa umaimah saka ihu.
NANA!
Muryar Paki tayi ƙara a gurin,
Da gudu Ya karasa Ya raba bakin Nana da fatar umaimah wadda har Ya fasa.
Kama hannun umaimah yayi cikin firgici,
Kwacewa tayi kamar Ya sa mata wuta ta ɗauke masa fuska da mari .
Yin kan Nana tayi tana cewa kinsa cizan nan nawa zai iya ja maki balai,Kallan hannun umaimah ta kuma yi taga yarda ya gatsa tace "wallahi kinci darajar tsufanki,"
Da wallahi sai na daki sauran haƙoranki ɗinann sun zube.
Da ihunta tace "farouk "call the Security,kar ta je tana cizan wasu.
Cike da ihu nana tace "mune tsaran kasa dan ubanki, kuma bai tsaya anan ba."
Cikin Muryar zuga sameerah tace"kana kallo Dai paki yarda matar da kake ɗaga jijiyoyin wuya take cima kakar ka mutumci babu ko tunanin tayi jika da ita "
Juyowa umaimah tayi ta kallesa wanda Ya tsaya cikin tashin hankali,
Takowa yayi yace DR Bulama muje a wanke maki ciwannan,
Wani Kallan banza ta bashi ta raba ta gefansa
.
Manage
IM having test tomorrow but nayi kokarin baku kuyi hakuri da wannan.
Chuchujay
Tbc
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top