episode 1
AURE UKU.
By
CHUCHUJAY ✍🏽
EPISODE 1⃣
KIRIKIRI MAXIMUM PRISON LAGOS STATE NIGERIA.
A kullum zaryarta zuwa prison ɗin yana mutuƙar bata mata rai ,
Bata jin wani tausayi ko rashin jin daɗin abunda yake faruwa da shi duk da irin ɗinbin san da tayi masa a baya,
Ta sa a ranta akan cewa kaddarar sa ce,duk wani wanda zai nuna mata rashin dace wa akan bibiyar sa Ya bata takardar sakin ta Kallansa kawai take sannan bata sawa a ranta domin ta gama yarda da yarda ɗan Adam yake da hallayyarsa,
Cikin handcuff Dukkan hannayen sa biyu Haka aka rako sa ,kallan sa kaɗai yakan sa mata faɗuwar gaba ,hakazalika a yanzu haɗa ido kawai da tayi dashi sai da Taji mumunar faɗuwar gaba Ta kawo mata ziyara,
Abubuwan da suka faru tsakaninta dashi take suka fara tariyo mata ,danne su tayi dan tafiyar su babu abinda ya haifar mata sai tashin hankali da dana sani,
Kallanta ta mayar gareshi dan ta gama yarda a yau sai tabar kirikiri da sakinsa akanta,
Glass Mai Kauri ne tsakaninsu Wanda yake ɗauke da bulloli Shida,telephone ɗin dake sakale a gefenta ta ɗauka ta kara a kunne yayin da shima yayi halkan,
Magana ta fara "Hafiz nazo ka bani takarda ta dan Allah mu daina bata lokacin juna kodan zaman mu na farko kan ka chanja Mai ɗan dadi duk da yaudara ne, ka sakeni dan koda ace huƙuncin ka ba kisa bane ta hanyar rataya ,koda kuwa ace za'a cire duk wani charges akan ka,Hafiz bazan taba sake zama da Kai ba.
Kukan da yasa shine abunda yayi mutuƙar bata mamaki,tasan wanene hafiz mutum ne Mai mutuƙar juriya da jarumta ,amma a yau yana mata kuka dan kawai tana masa maganar Ya sake ta,
Shiru tayi tana Mai jin kukan nasa ta cikin telephone ɗin a yayin da yake ratsa dukkan wani sasshe na jikinta,
Ina ma hafiz bai zabi tarwatsa rayuwarsu ba ,ina ma ba'a kamasa da laifuka mafi munin wanda aka kamashi dashi ba,
Ina ma!
Tana kokarin cire telephone ɗin dan bazata iya cigaba da jin kukansa ba ta tsince muryarsa yana cewa"UMAIMAH dan Allah dan Annabi kar ki takura mun na sake ki,ni mutum ne Mai laifuka da dama a wajen ubangiji, kila yamun Rahma sakamakon mutuwa da zanyi a matsayin mutum mai Aure,"Ke mutuniyar kirkice UMAIMA ,a dukkan rayuwata ban taba Auren mace Mai kamala da haƙuri ba kamar ki,ke maratussalaha ce ,ke macece yar Aljanna,Mai tausayi da jin kai,dan Allah UMAIMAH kimun wannan Alfarmar guda ɗaya duk da kuwa ni Azzalumine a wajenki.
Bata san lokacin da ta kwace da wani irin kuka ba Mai mutuƙar cin rai,
Take duk ikirarin da take na rashin jin tausayinsa Ya kau dan ta tabbata koda a ce babu soyayyar sa a tattare da ita tasan tabbas yana da soft spot a wani gurbi na zuciyarta,
Tana kokarin cire telephone ɗin yace"UMAIMAH bana so na mutu,Ina mutukar tsoran zuwa na haɗu da mahaliccina,bana so umaimah ,Ina san na rayu na dai dai ta tsakanina da ubangijina na rayu da ɗana wanda shi kaɗai Allah Ya bani,sannan babban farin cikina ta tsatsanki Ya fito,"Amma kash kaico na ,bani da wata damar ,nayi wasa da wadda Allah Ya bani ,nayi fatali da kyautar ni'imar da yayi mun saboda san zuciya da kwaɗayin duniya wanda a yanzu Ya kaini Ga dana sani,
UMAIMA gobe za'a rataye ni ,gobe zan mutu,babban tsorona kenan,a razane nake da Ya zamana nasan ranar mutuwa ta.
Shiru tayi tana Mai kallan sa ta glass d'in da Ya rabasu,hannunta tasa ta dafa glass ɗin a dai dai inda Ya ɗora hannunsa ,
A hankali ta shafa tana Mai tuna yarda ya nuna mata soyayya kamar zai cinyeta a wata biyu na Auren su,
Lumshe idanunsa yayi wanda suka faɗa saboda tsantsar masifa yace"kar ki bawa ABDALLAH labarina idan Ya girma,bana san yasan babansa failure' ne a rayuwa sannan na yarda da zaki bashi tarbiyya Mai kyau,kar ki barshi Ya rabi dangina dan na bar miki shi halak malak,dangina ba mutanen da zanyi Alfahari dasu bane Kema kin sani sune mafarin jefani cikin wannan masifar,ina so idan da dama ki raini ABDALLAH Ya zama cikakken Mahaddacin Qur'ani ,Ya zama malami akasin mahaifinsa,"
Idan Kinje gida a side drawer dake gefen gadona na aje cheque na milliyan goma ,ki ɗauka ki juya ma ABDALLAH ,wallahi tallahi ba ta hanyar banza na samesu ba,kuɗi ne masu tsafta babu gurbaci a cikinsu,
Kisa Abdallah yana mun Addua ,Kema idan har da dama zan samu a gurinki bazan ki ba, duk da nasan abun zaiyyi wuya duba da yarda na cutar dake a rayuwa.
Ina mai mutuƙar baki hakuri akan ki yafe mun,Allah Ya baki miji Umaimah wanda yake salihi, Ina Mai miki addua ki Auri miji nagari ba irin mazajen da kika AURA GUDA UKU BA.
Allah Ya haɗa fuskokinmu da Alheri.
Nagode Allah yayi miki Albarka.
A Yarda ma'aikatan suka kawo sa haka suka ƙara tasa keyarsa dan komawa da shi kurkukun da suka dauko shi,
Buga glass ɗin tayi wanda hakan yasa shi tsayawa,ma'aikatan basu ja ba dan sukan bawa wanda yayi expire dama duba da duniyar ma barinta zaiyyi baki Ɗaya,
Roban take away ta ɗauko daga jakarta wanda bata san dalilin da yasa ta zo dashi ba,ɗaya daga cikin ma'aikatan ne Ya zagayo Ya karba,Ya juya zai tafi tace masa"ka faɗa masa Na kawo masa favorite dambun naman kazan da yake so sannan ni na soya,sannan insha Allahu indai na dena masa Addua to numfashina ne Ya yanke daga jikina,sannan zai Alfaharin abunda zai tafi Ya bari."
Wani irin kuka ta fashe dashi a yayin da taga yana mata murmushi lokacin da aka aika masa da Saƙonta,da sarsarfa ta tashi tabar gurin tana Mai Kallan yarda aka maidashi har a lokacin murmushin na akan fuskarsa,
Kuka take sosai a motarta tana Mai jin wani irin zafi a cikin kirjinta,tabbas rayuwar Hafiz babbar Aya ce ga mutane .
WACECE UMAIMAH ?
DR UMAIMAH USMAN BULAMA,
Ƴa ɗaya tilo a gurin Amaryar Alhaji usman bulama,
Alhaji usman bulama mutumin Zaria ne wanda zama Ya kaishi garin ADAMAWA YOLA garin FULANI tushen kunya,
Alhaji Bulama sharraren mai kuɗine wanda ake lissafawa a cikin dumbin masu kuɗin duniya ba kasa kawai ba,
Architecture ne wanda Allah ya habaka a hanyar domin irin tsabagen basirarsa,
A irin buɗin da Allah yayi masa har Construction company (BULAMA CONSTRUCTION COMPANY) ne dashi wanda suke samun kwangiloli masu dama wadda sai da rabanka ma suke karba.
Matan Alhaji bulama biyu,hajiya zuwaira itace uwar gida wadda ta haifa masa yara huɗu dukka maza babu mace ko daya.
Mutane kance soyayya da sa rai da yayi ga ɗiya mace ne ya sashi ƙarin mata amma a zahiri kuwa ba haka bane,
Soyayyar Bafulatana Nana Surbajo dake yawan kawo nono Companin sa ita tayi masa mugun kamu duk da kuwa yanayi kamar bai taba kula da ita ba a yayin da ita bama tasan yanayi ba duba da shi ɗin mutum ne da ganinsa sai ka cike Paper.
Da yake Allah Ya kaɗara matarsa ce bai kasa a gwiwa ba wajen bincike akanta inda Ya gano daga rigar da take yaje ma iyayenta da maganar Aure tun kan Ya furta mata soyayya.
Iyayenta ba masu tsaurin ra'ayi bane dan haka suka bashi dama Ya nemi soyayyar nana surbajo duk da yarda danginsu suka masu Cha akan zasu bama dan yankan Kai diyarsu tilo.
Ba wani wahala Ya sha ba Ya samu Auren surbajo wanda kwata kwata baiwa uwargida zuwaira daɗi ba amma babu yarda zatayi da yin Allah dan haka abun ya kullu yarda Allah yaso.
A shakara Allah Ya Azurtasu ɗiya mace wadda taci suna UMAIMAH,sosai Alhaji bulama yayi mutuƙar murna wadda tasa shi fitar da zakka Mai mutuƙar tsoka,
A duniyarsu ta shahararrun masu kuɗin babu wanda bai san da samuwar UMAIMA ba da kuma irin Adadin ƙaunar da yake mata dan baya iya boyewa,
Wannan ƙaunar da yakewa UMAIMAH ba karamun damun hajiya zuwaira take ba da yayanta uku, cikin yaranta Abubakar,usman,umar,Aliyu,Abubakar babban danta ne Kawai yake jin Umaimah a cikin zuciyarsa kamar uwa daya suka fito amma sauran kuwa ba karamun saka masu kiyayyar umaimah da uwarta tayi ba.
A haka umaimah tayi ta girma cikin soyayya da kulawa duk da kuwa irin tsangwamar da take sha gurin uwar gidan Alhaji bulama da yaranta uku,
Tun kafun tasan menene kiyayyar har ta fara ganewa tasan mema kiyayyar ke nufi.
A lokacin da ta shiga shekara goma sha biyar Allah yayi ma mahaifiyarta rasuwa sakamakon brain cancer da ya sameta,babu irin kudin da Alhaji bulama bai kashe ba dan kawai Nana surbajo ta warke amma abun yaci tura,
Tun rasuwar Nana surbajo Umaimah ta ci buri kuma ta sawa ranta sai ta zama surgeon,
Da wuri ta fara makaranta sabida irin kaifin kanta,tana da shekaru goma sha biyar ta kammala karatun secondary school ɗinta ,
A shekarar da ta zagayo ya kai ta harvard university inda ta fara karatunta na liktanci,
Babu irin kauɗin da hajiya zuwaira batayi ba akan Kai umaimah Harvard da akayi amma yayi kunnen uwar Shegu da ita, umaimah na shekara ta uku a Harvard mahaifinta yaje Ya ɗaukota,
Bata tambayesa dalili ba d'an tasani idan da wanda yake san cigaban ta bai wuce shi ɗin ba sannan ta yarda duk wani decision da zai yanke akanta mai kyau ne.
Bayan dawowarta Nigeria tayi mutuƙar mamaki da taji wai ansaka ranar Aurenta da Habib Aliko yaran Aminin Daddynta,
Koda Daddynata yayi mata magana akan Aurenta da Habib nuna wa tayi duk abunda Ya yanke akanta dai dai ne muddin karatunta bazai tsaya ba,
Tasani Daddynta Ya chanza amma bata saka wa ranta komai ba,baƙaramar rawa Hajiya zuwaira ta taka na wajen Auren Umaimah da Habib d'an ita ta haɗa komai.
Yaya Abubakar kaɗai ke bata baki yana Mai nuna mata Auren ma ba matsala bane sannan bazai shiga rayuwar karatunta ba tunda Daddy Ya jaddada ma Habib d'a mahaifinsa kan zata cigaba da karatun ta and baya buƙutar su ɗauki nauyi zaiyyi komai,
Haka nan ya Auri Habib inda Ya ɗaukota daga garin adamawa ya kawota kano,
DE ta samu a TURKISH MEDICAL SCHOOL inda ta dora daga inda ta tsaya.
Tun ranar da aka kaita gidan HabIb tasan ba mijin Arziƙi bane 'dan a buge ya shigo ,bai tsaya anan ba kuma a ganawarsu ta farko raping ɗinta yayi wanda yaji mata ciwo sosai,tashin hankalinta bai fara ba sai da tasan Habib manemin mata ne sannan kuma ɗan giya ,bata sanar da kowa ba take zaune dashi a Haka musamman da taga yarda Daddynta ke mutuƙar yaba hankalinsa 'dan munafukine na masifa saboda baya taba nuna shi 'dan iskane gaban iyayenta,a Haka har rabo Ya shiga tsakaninsu ta haifa masa yaro na miji wanda yaci suna NAMEER,
NAMEER na da shekara ɗaya Habib ya saketa sakamakon dawowa da yayi gida a buge suna zaune da NAMEER a falo 'dan kawai tayi faɗa da mita akan Ya daina shigo musu gida muddin giya bata sake sa ba,
Cikin maye Ya mata saki uku wanda a musulunci ma ta saku,
Daga baya Ya dawo yayi ta naci akan shi bai saketa ba amma Daddynta yayi masa koran kare sannan Ya ƙwaci NAMEER ɗin da Ya kwallafa rai akai wanda mahaifin Habib bai jaba 'dan baya san alaƙarsa ta baci da Alhaji Bulama.
Kamar wasa bayan iddarta Daddy ya sake introducing mata BILAL shima dai yaran Abokinsa,
Abun ne Ya dameta duba da Ko Auren ta na fari bata gama Alhini akai ba amma wai Daddyn Ya kawo maganar Auren ta da wani,wanda shima kamar Habib ba sanshi take ba,
Kuka ta ɗingawa Abubakar Akan ita bata san Auren Bilal 'dan Auren ma bata so baki daya ,she's just 21 amma ace wai har Zatayi Aure na biyu,
Baki abubakar yayi ta bata akan zai je ya samu mahaifinsu yayi masa magana,
Koda yawa Daddyn nata magana sai cewa yayi Ai hajiya zuwaira taje wajen malaminta dake mata Addu'a Ya tabbatar mata muddin Umaimah ta zauna babu Aure zata lalace kuma babu wata nasara da zata tabayi a rayuwa shi kuma bazaya taba barin ɗiyarsa tilo guda ɗaya ta tagayyara ba,
Ƙara yarda yayi da Lallai daddy yana san umaimah to extent that yama rasa inda zaisa Alƙibilar tunaninsa,'dan ko shi da yake ɗan Umma yasan maganar ta ba dai dai bane duba da kalar tsanar da take wa UMAIMAH ɗin ,kawai dai tace tana so ta bar mata gida,
Kara bawa umaimah hakuri yayi a karo na biyu inda ta yarda da Auren BILAL wanda yake da mace ɗaya,shima kuma mazauninin garin kano 'dan Haka Ta dora karatunta inda ta tsaya.
Duk da tarin kuɗin mahaifinta hakan bai hana kishiya da miji da uwarsa galaza mata ba,gida ɗaya suke baƙi dayansu,
Karatun ta ne basu so amma kuma babu yarda zasuyi dan basu suke ɗaukan nauyin Karatunta ba sannan yarjejeniya ce akayi Mai zaman kanta,a Haka tana wannan rayuwar ta sake samun ciki cikin shekarar su ta biyu da Aure duk da bata so ba amma Haka nan Ta ɗauki dangana,
Duk wani wulakanci da take gani gidan Bilal dannesa tayi Ko yaya Abubakar bata faɗawa ba 'dan faɗan ma is pointless 'dan tasan babu mai duba mata kar ma ace Daddy zaice kawai Zaman Auren ne bata so.
Hankalinta ta mayar kan karatunta wanda take samun nasarori sosai a ciki,gefe guda kuma tana kula da NADIYA yarinyar da ta shiga tsakaninta da BILAL Yar shekara,
Saukinta kawai NAMEER YARO DAN SHEKERA UKU a lokacin yana gurin Matar Yaya Abubakar "Sadiya" wadda ke nan cikin mansion d'in Bulama 'dan bai yarda Ko wanne ɗan sa Ya fita da iyalinsa daga gidan ba ,duba da gidane duniya guda.
CHUCHUJAY ✍🏽
To Be continued.
Follow,share,like and share.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top