Part 9
Washe gari da safe su Tasleem suka shirya zuwa gdan su Amani Ali driver ne ya kaesu suka ce ya dawo dau Kansu da yamma amma a gdn su Asma'u zaka same mu
Yace"tho"
A parlourn kasa suka tarar da hajiyan su Amani bayan sun gaesa suka tambaya koh Amani na nan
Hajiya tace "ehh tana dakin ta"
Tashi sukyi suka haura sama bedroom din Amani suka wuce direct koh da suka shiga kallo suka same ta tanayi duka safa ta kae mata a tsorace ta mike zaune sae suka saka dariya zama sukayi kusa da ita
Tasleem ce ta fara Ciro phone dinta ta nuna na ma Amani safa ma ta ciro nata ta nuna mata bata fuska Amani tayi tace "shine kukayi waya baku fada min bah" ta karashe maganar kamar zata yi kuka
Dariya suka sa gana daya sae itama ta dauko wata waya akan side bed drawer dinta Tasleem ta fara karba tana fadin"wow sis Cong"
Tace "tnx"
Safa ma karba tayi ta duba tace "laaa ke ma irin iPhone dinmu ce amma taki golden"
Tace"ehh ya kabeer ne ya bani jiya"
Murna suka taya ta nan suka shiga lbr sae guraren karfe 3 suka fara shirye2 zuwa gdn su Asma'u bayan sun shirya suka fito compound dan kiran driver Mae gadi ne yace musu Hjy ta aike sa ana cikin haka sae ga ya kabeer ya fito daga part dinsu ya nufo part din Hjy ganin su da yyi ne yasa shi tsayawa gaeda shi su Safa sukayi ya amsa cikin fara'a
Amani ta marairaice tace"bros dan Allah ka kaemu gdn su Asma'u mana"
Kallon ta yyi yace"OK ina zuwa bari na shiga wurin Hjy na fito"
Ba jimawa ya fito suka shiga mota bayan sun hau titi ya kabeer sae kallon safa yake ta mirror yana smiling ta daga alaman hakan ta dauke kae ta koma kallon hanya
Bayan ya ajiye su sukaSauka gaba daya shima ya kabeer fitowa yyi ya kira Amani ta dawo baya su kuma su Tasleem suka shige abunsu
Ban ta je kusa dashi yace"sis dan Allah Ki bani no din frnd din nan taki"
Kallon mamaki ta masa tace"wacce daga cikin su"
Yace"doguwar"
Dariya tayi dan tasan safa yake nufi dan ta danfi Tasleem tsawo kadan tace"oh safa"
Sunan ya maemaeta kafin yace"eh ita"
Dariya ta koma yi tace"ya wlhi tana da Wanda take so"
Ido ya zaro waje yace"an tsaida mgn?"
Tace"aa ya iyayen ta ma basu San dashi bah"
Ajiyar zuciya ya sauke yace"yoh ae wnn ba matsala bace tunda dae ba'ayi mgnr gemu da gemu bah kawae ki bani zan san yanda zan shawo kanta"
Tace"tho ya nidae bazan bada bah kaga nayi nan" ta karashe mgnr tana tafiya
Jayo ta yyi ta dawo baya marairace fuska yyi yace" pls sis ki taimaka wlhi ina sonta sosae"
Dariya ya bata amma ta gimtse tace" tho da sharadi"
Da sauri yace"ina jinki yar galadima"
Tayi yar dariya tace" zaka samin credit din 5k a phone dina"
Da sauri yace"indae wnn ne na yarda yan zuma kuwa"
Phone dinsa ya ciro nan take ya mata transfer din 5k ta jin alert tayi hugging dinsa da sauri ta ciro phone dinta ta fada masa no safa godiya ya mata yana fadin"dat's my lil sis ya Shiga mota ita kuma ta shige cikin gdan su Asma'u tana jin jina lamari na yayan nata
Koh da tashiga ta same su a tsakar gd sbd ba NEPA dakin Maman su Asma'u ta wuce direct bayan sun gaesa ta fito ta shiga dakin su Aunty Raliya ta gaedasu
Tsakar gdn ta dawo ta zauna Tasleem ta kalle ta tace" wae
Ke mae kika tsaya yi a waje tun dazu
Dariya tayi tace" ni da ya kabeer ne bari idan kin hau online zan fada miki
Tsaki safa tayi tace"ai a haka zaku kare munafukae kawae"
Dariya kawae sukayi suka cigabada firarsu inda Asma'u ta nuna ma Amani phone dinda ya Rafeeq ya bata da kuma laptop din da safwaan ya bata murna ta taya ta sosae
Sae bayan sallahr isha mommy tasa Safwaan yaje ya dauko su dan ta aiki Ali driver gdan mom faty kanwarta
Bayan da safwaan yaso haka ya daure yaje wayar Tasleem ya kira tace masa suna gdn su Asma'u kwantance ta masa na gdn ba dadewa koh sae gashi ya iso
Tare suka fito gana dayann su harda Asma'u ta kofan da safwaan yake ta zagaya knocking tayi yyi winning glass din kasa cikin sanyin ta tace" ya safwaan ina yini"
Da sakin fuska yace"lpy Asma'u ya gd da su mama"
Tace "lpy ya naga sako na gode sosae Allah ya kara budi da arziki"
Yace"ameen karki damu kema ai kanwata ce"
Tayi smiling tace"toh ngd ya saeda safe"
Yace"Allah tashe mu lpy "
Ta amsa da ameen
A bangaren su safa kuma da sauri Amani da Tasleem suka shiga baya dan basaso idan safwaan ne zae yi driving su shiga gaba ba yanda safa ta Iya dole ta shiga gaba sae da suka fara sauke Amani kafin suka wuce gda
Bayan kwana biyu Abba ya shirya ma su Ummi tafiya zuwa qauyen su domin gaeda dangi dan tun bayan da akayi shari'a basu kara zuwa bah
Bayan kwana biyu suka je da safa Tasleem Ummi da rafeeq dan ya dauki hutun 1 week a hospital
Tarba ta mutunci aka musu a gdn su Ummi dan a can suka yada zango
Washe gari suka shirya domin zaga dangi duk Indi suka shiga nan2 ake dasu har gdn baffa Sani suka je gaeda inna larae itama tarba ta mutunci ta musu dan tuni ta nema ga fara a gurin su bayan sun gaesa rafeeq yace" inna ina su hydar ne"
Tace"Rafeeq rabonda na saka hydar a ido tun bayan wata biyu"
Ido ya zaro yace" toh ina ya tafi"
Tace"yana Lagos shida dan uwansa"
Yace "toh Allah dawo miki dasu lpy"
Tace"ameen"
Sae karfe 5pm suka koma gd haka suka dinga yawon dangi ko ina sun leka
Bayan sati suka koma gd
Bayan kwana biyu Safwaan ya koma Enugu dan yana da aiki sosae a gaban sa
*SOME YEARS LATER*
Abubuwa da yawa sun faru ciki koh harda fara zuwan su safa university dan sun samu admission gaba daya su kuma department din su daya inda suke karatun pharmacy shi yasa suke zuwa tare
Haka ma shakuwa ta fara shiga tsakanin safa da safwaan dan yanzu ba kamar da ba ya dan gare miskilancin sa ita koh dama safa kawae saukin kae Rafeeq ma yayi mamakin sakkowar da Safwaan yyi daga zuwan sa Enugu
A bangaren Tasleem kuma shakuwa da soyayya sae kara karuwa yake tsakanin ta da Rafeeq har ta kai da Abba ma yasan suna son junan su yyi matumar farin ciki da faruwan hakan.
A gefen ya kabeer kuma ya bayya na ma safa kansa da kuma irin son da yake mata ita dae bata ce masa tayi accepting ba kuma bata ce masa bata son sa bah
Abdul_waheed ma ya matsa mata akan yana so ya turo magabatan shi idan yaso ta karasa karatun a gdn sa amma taki yarda dan tafi so sae ta gama karatu tayi aure dan haka dole ya hkr da zancen
Yau ta kama Monday run safe su safa suka shirya domin zuwa skl
Da suka isa direct hall dinda suke lectures koh da suka shiga ba lecturer aciki guri suka samu daga gaba suka zauna bayan 15 da shigowar su sae ga wani young handsome guy ya shigo a shekaru ba zae wuce 27 to 28 fari ne dogo da doguwar fuska Mae dauke da bakin sajen sa da yasha gyara sae kyalli yake he dressed in milk and coffee jampa
Introducing kansa yyi yace" Am faruoq Yusuf by name and I will be taken u physics 101 but for a while"
Ya gyara tsayin sa yacigaba da cewa u know in every society there must be some rules and regulations governing them, firstly u don't tolerate coming to d class late if I enter b4 u den u will not enter
Hence i hate noise and last but not d least I gave test anytym I wnt and if I give u assignment I will be collecting it any tym I decided am I clear" suka amsa da yes sir
Lectures sukayi na 2 hrs snn suka fito masjid suka je dan basu da lectures sae bayan sallahr azahar hakan yasa sukayi zaman su a can matan class din su kuma sae mgnr haduwar new lecturern suke
Bayan sallah suka cafeteria suka ci abinci da suka gama suka nufi hall din su dan sun San halin lecturer din idan ya shiga toh ba mae shiga bayan sa sae 6pm suka koma gd a gajiye .......
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top