Part 23
Yau takama Saturday gaba dayan su suna gda Safwaan na bedroom din sa yana bacci safa kuma gyaran gda ta shiga gaba daya ko Ina ta gyara sae kyalle yake da kamshi(Mata Banda kazanta dan itace abu na farko dake fara haddasa fada tsakanin ki da mijinki ki zama Mae tsafta a koda yaushe)
Bayan ta gama ta shiga kitchen da daura breakfast kunun gyada da kosai ta musu bayan ta gama tayi wanka ta shirya cikin riga da wando na parkistan colour red and lemon green tayi kyau abunta wayar ta ta dauka ta sakko kasa bayan ta zauna ta kunna data ta fara chatting.
Ganin har kusan 10 bae tashi na yasa ta shiga dakin sae da ta fara gyara parlour kafin ta wuce bedroom dinsa ganinsa a kwance ya rungume pillow tsam a jiki abu yasi bata dariya toilet ta shiga ta wanke shi tass fitowan ta yyi dae² da tashin sa idon sa ya ware akan ta kana yace yau kuma ta Nan Kika billo da asirin naki toh ta Allah ba taki ba
Dariya ta shiga yi sosae karda kire ciki kallon ta kawae yatsayi dan shima kansa yasan ga mishi kyau sosae muryarta ta dawo dashi daga tunanin da ya tafi tace hmmm Ka taba ganin anyima abunda ba'a so asiri ka sake tunanin dae Ni tashi na gyara dakin inaso zan fita.
Wani kallo ya watsa Mata tace Kae dude irin wnn kallon kodae wankan ya maka ne ta fada tana juyawa wani iri yaji a jikinsa da ba safa bace ba abunda zae hanashi rungumar abunsa dan gaba daya ta tafi dashi.
Tabe baki yyi yace hmmm a haka ne kike ganin kin hadu gsky da dijen kyauye kikayi kama.
Tsaki tayi tace hmm fadi gsky dae ai ko makaho ya shafa ya sani wlhi da ya ma'aruf ne da yanzu ya min pics da yawa Yana fadin wow my bby kinyi kyau Kae Allah ka barmu da masu son mu dae.
Wani haushine ya kama safwaan lkc guda ya damkota yace repeat wat u just said
Cikin rashin tsoro ko ta maimaita manne ta yyi da bango ya hade bakin su guri daya Yana kissing gaba daya ya fita hayyacinsa safa kuma sae neman kwace kanta takeyi amma ba hali sae da ya samu nutsuwa kana ya saketa ya juya ya nufi toilet.
Mutuwar tsaye tayi a gurin tana mamakin wnn abu da kayar ta tashi ta Shiga gyaran daki har ta gama bae fito ba hakan yasa ta dawo parlour ta zauna cike da tunanin abunda ya Mata.
Bayan ya gama shiryawa ya fito kae tsaye dining ya wuce ganin haka yasa itama ta mike cikin yansin jiki ta isa dining din sae da tayi Saving dinsa kana ta deba nata ta zauna gaba daya taki bari su hada Ido shi kuwa ko a jikinsa a ransa yace na ganoki yarinya yanzu da kinmin rashin kunya ta wnn hanyar zan kamaki.
Bayan sun gama ya dauki key din motar sa zae fita tace ya dan Allah ka ajiyeni gidan su mommy.
Kallonta yyi yace Zaki fada Mata ne abunda na Miki
Da sauri ta dago tace aini bana fadan sirrin dake tsakanina na mijina.
Wani dadi yaji amma ya fuske yace waye mijin naki. Da sauri tace yi hkr yayana nake son cewa yace better. Muje
Ganin zata fito da Dan karamin Vail din kayan jikinta yace ba inda Zaki je koma na fasa da gudu ta koma daki ta dakko hijab harda niqab ta saka shi dariya ma ta bashi. Gefen mai zaman banza ya zauna yace ita zatayi driving din ba musu ta karba suka tafi.
A parlour suka tarar da su ummi harda su Nabeela da mom faty da ya Hafsa bayan sun gaisa Nabeelah sae harara take watsama ma safa ita kuma da ta kula da haka sae ta manne jikin safwaan ko kunya babu firar su sukayi har aka kira sallah suka tashi duk suka tafi domin gatar da ita.
Safa da taga Nabeelah ta bi bayan safwaan zuwa waje itama ta fito da gudu tana fadin ke Ina Zaki bi mijina da Kika biyo bayansa gaba dayan su tsayawa sukayi shi safwaan abun mamaki ya bashi sae kallonta yake.
Tace ke tamba dadda me na biyo mijina waje
Nabeelah tace Ashe tamba daddin na da yawa
Safa taceni ba tamba dadda bace kuma mijina ba tamba dadde bane kuma Allah ya masa katanga da kaidunki bazan jaka akuya kinci karya kin kwana da yunwa Ramin kura sae ya'yanta
Nabeelah tace da sannu akuya ke akuya ke shiga Ramin kuta ta cita da yaki sannan ta tarwatsa yayanta ta mallaki karagar ikon gudanar ta rayuwarta.
Safa tace wlhi na Miki kashe da nakarshe duk na Kara ganin ki ko sahun mijina kin biyo sae na bata miki rae banza Mara zuciya
Nabeelah tayi dariya tace Ni nariga na kadu ba abunda Kika isa kimin Ni murucin kan dutse ce ban fito ba sae da na shirya. Rana ce Ni tafin hannu yyi kadan ya shafe haskena a ko ina.
Safa tace hargagin damusa bai isa ya razana ya'yan kura ba kamar yanda atishawar kuda bazata iya fasa tulu bah. Dan haka ki fita harkar mijina
Nabeelah tace hmmm abun kamar da wuya kidan ganga da lauje.
Safa tace duk Wanda yaso musaya raina nashi yayi ban ga laifinki ba Dan na Miki mgn baki ji ba ko iyayen da suka haifeki ai musayar yawu kike dasu.
Nabeela tace Ni cila kowa ce mai cilanin lalata idan ban lalata Miki aure ba zan lalata mijinki domin Ni Nabeela kafar anugule ce Mae lalata miya.
Safwaan da ranshi ya gama baci akan maganar Nabeelah ta karshe ya daga hannu zae kwada Mata Mari safa tayi saurin rike tace haba ur Excellency barta kawae ai tsanyar kura ba'a bama kare dillancin kamar yadda sama tayiwa yaro nisa sae dae ya daga kae yyi kallo kuma kifi kuma kifi da kaska basa zama waje daya ko ana Sarar bushiya a tsallake bushiyar kuka.
Cike da bacin rae Nabeelah tace hmmm da wae Marina zakayi akan wnn abun na fa girmeta kuma nafika kusanci da ita ko ba komae Ni Yar uwar kace ta jini ma kuwa. Ke kuma Bari na gaya Miki na riga na kone ba abunda Kika isa kimin
Safa ta makalema safwaan tace dama Yana iya da abunda ya kone inji kishiyar wuta mu munfi karfin ki kuma ke da safwaan sae dae a mafarki.
Nabeelah tace bazan iya juran cin fuska daga gareki ba sbd mai tirken yaki baya daukan wargi.
Safa tace ke da mutane sun San cewa ke kwatace ko wane jaki dabba naki ne da bazaeyi kuskuren hada hanya dake ba.
Nabeelah da ranta ya gama baci ta daga hannu zata kwadama safa mari safwaan ya kire Mata hannu tareda Bata maruka masu kyau guda biyu.
Mutanen gda dake gurin suna kallon kamae tuna suka fara draman su sukaji hayaniya suka fito Tasleem ta sa dariya har da kyakyatawa tace nagode tawan ta kalli Nabeelah tace duk Wanda baeji bari ba yaga oho.
Ummi da itama ranta ya baci ta ja hannun safa zata tafi da ita safwaan ya rike tareda girgiza Mata Kae hakan yasa ta sake ta tayi cikin gda.
Mommy ma abun ya mata dadi Dan bata son hali irin na Nabeelah gaba daya tarbiyyanta ya baci har ta fara bin maza. Mom faty kuma batace komae ba dan tasan halin yarta.
Kowa ya watse ya barsu a gurin safa kalli safwaan tace ya sake ni zanje nayi sallah kaema ka tafi masjid kallonta yyi yace Zaki min baya Ni a gda. Smiling kawae tayi ta damka ma Rafeeq hannunsa suka wuce masjid.
Nabeelah kuma ko cikin gda Bata koma ba ta wuce gda cike da bacin rae tana tunanin wane mataki zata dauka akan safa Dan ita ta kowane hali sae ta auri safwaan.
Wayarta ta ciro ta kira wata frnd dinta Sarah tace tana so ta kaita gurin malamin ta amata aiki akan safa.
Hmm Allah ya shirya mu yasa mufi zukatanmu gaba daya ya kare mu daga Rudin duniya Ameen
^^^^^^^^^^^^^^^^
Da dare yyi bayan daddy ya dawo suka gaisa suka tafi gda.
Da sauri ta shige dakinta saboda yanda take Jin maranta na ciwo dama ta riga da tasan wata yazo karshe kan gado ta fada tana ta juyi ta dafe mararya tana zuba kuka kamar ranta zae fita.
Safwaan da yashi ya tararda bata parlourn ya haura sama Jin kukanta yasa shi shiga dakin akan gda ya hangota lkc guda ta fita hayyacinta gaba daya da sauri ya karasa gurin Yana tambayar lpy kuka kawae take ta kasa magana.
Ganin hannunta akan mararta ya tabbatar mishi da menstrual pain ne ke damunta a hankali ya furta period time dinki ne yyi Kae ta daga masa alamun eh tsaki yyi ya fito ya koma daki wayar shi ya dakko ya kira Rafeeq ya sanar dahsi halin da ake ciki ba bata lkc sae gashi shida Tasleem sun karaso.
Bedroom dinta suka nufa direct allura Rafeeq ya hada yace ma safwaan ya riketa dan wlhi bazata tsaya bah.
Tsaki yyi yace amma gurin rashin kunya itace a gaba gaba smiling kawae Rafeeq yyi yace gsky koh nine a matsayin ta abunda tayi dazu shi zanyi sbd na kare mijina daga sharrin yanmata
Tsaki yyi yace dama halinku daya da ita Allah shirya ku toh.
Bayan an Mata allura suka dawo parlour suna fira kusan Bari akan abunda ya faru dazu ne Basu bar gdan ba sae kusan 10pm dakin ta ya koma ya samu tayi bacci blanket dinta ya rufeta da shi tunawa da maganar Rafeeq yyi akan cikin dare zae iya tasowa hakan yasa shi kwanciya kusa da ita bayan yyi wanka.
Cikin bacce yaji ta mirgino ta dawo kusa dashi gaba daya ta matseshi a jikinta bae an Kara ba yaji tana wani irin marayen kuka kamar ranta zae fita lallashinta ya shigayi gaba daya bataji Bata gani hannunsa ta kama ta dora kan cikinta tana matsawa kan kirjinshi ya dorata ya dinga shafa Mata maranta wani irin Kara ta saki lkc daya ta fara bleeding heavily Jin saukan abu ka jinka sa yasa maidata kan gado ya kunna bulb din dakin ganin jini a jikinsa yyi tsaki tareda fita dakin. Sae da ya canza riga ya dawo a inda ya barta ana ya dawo ya tadda ta toilet ya kaeta ya dawo dakin ya dauki pant da pad ya kaemata da taimakon sa ta gyara jikinta suka dawo daki sae faman sannun yake mata Basu kwanta ba sae da ya canza bedsheet din gadon.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top