Part 19
*A WEEK AFTER*
_*20th September*_
Sanye yake cikin wata dakakkiyar farar gezna da tasha dinkin sirfani baki sae hular sa itama baka takalmin sa ma bakake ne hannun sa na sanye da agogon Rolex maganar kamshi Kam ai ba'a mgn wow Masha Allah Safwaan kenan cikakken namiji mai cikakkar kamala da kwarjini son kowace mace kin Wanda yarasa.
Rafeeq dake bakin kofa yasa dariy yace "kaga angon Aysha safa kaima da kanka kasan kayi kyau irin wnn kallon da kake bin kanka dashi"
Safwaan ya tabe baki yace kanka akeji
Rafeeq yace my guy kayi kyau sosae ga kayan sun zauna jikin ka
Dariyan gefen baki yayi yace ba daga kayan bane daga mae kayan ne
Dariya Rafeeq yayi sosae yace Allah baba
Safwaan yace na kula fah ka rainani da yawa
Duka Rafeeq ya kaimshi yace Kae dan iska nine ma na raina ka bayan na baka good 2 weeks ko ba haka ba mijin kanwata kake Kae inda Kara aika kirani Yaya wlhi
Safwaan yace eh naji what ever ma dae Kae ka sani
Fita suka yi suka tarar da sauran frnds dinsu a parlour.
Kiran daddy ne ya shigo wayar Rafeeq bayan sun gaisa yace likita bokan turai wai Kun fito kuwa
Rafeeq yace eh daddy gashi nan zamu fito daga gida yanzu
Daddy yace toh kuyi sauri kunsan by 12:30pm ne
Yace inshallah
Kallonsu yyi yace guys daddy ne fah ya kira wae ko mun fito ku tashi mu tafi.
Bayan Sallahr Juma'a liman ya shaida auren *Safwaan Mas'ud* da *Aysha Muh'd Karamat* a bisa sadaki naira dubu hamsin gaisuwace ta biyo baya mutane sae Allah Sanya alkairi suke musu
Rafeeq ya koma gefe ya kira Tasleem bayan ta dauka yace bby an fah daura aure
Tace da gaske ya feeq
Yace ehh
Ajiye wayanta yyi dae² da shigowar baba Hure kakarsu da ta haifi ummi
Guda ta rankada ta na rawa Tasleem ta taya ta suna wakar Aysha ta zama matar Safwaan💃
Wani zazzafan hawaye ne suka rika wanke fuskar safa kuka take yi kamar ranta zae fita
Baba Hure tace yau Ni naji sakarar banza daga an daura auren ki sae kisa kuka maimakon kiji dadi
Cikin kuka tace ehh nayi kukan ai bata baci ba sae a maeda auren kanki
Baba Hure tace kunji min ja'irar yarinya toh bari naje na samu uwar taki
Har ta kai bakin kofa kuma sae ta dawo ta zauna kusa da jikarta ta janyota jikin ta tayi ta fara rarrashinta da bata baki
Su Kam su Tasleem sunyi jukum² kowa da abunda yake sakawa a ranshi
*^•°^•°^•°^•°^*
Safwaan Kam ba'a mgn daurewa kawae yakeyi amma deeply ji yake kamar ya kama da 🔥 (🤣🤣my guy taka don finish oo) lol
Bayan sun dawo gida part dinsu suka wuce bayan sun gama abunda zasuyi suka fito zuwa cikin gida. Aunties dinshi sae faman tsiya suke mishi kowa da kalar zolayar da take binshi dashi yake kawae yake musu dan shi kadae yasan abunda yake ji
Ummi ce tashiga part din mommy sunci ado kayansu iri daya daka gansu kasan naira ta zauna
Da ya leemat taci Karo a hanyar kitchen tace yauwa Haleema dan Allah ku fito da kanwar ku gasu son nan a waje
Tace toh ta nufi dakin su Tasleem
Zaune ta same su suna ta faman bama safa hkr da har yanzu kuka takeyi
Tace musu su fita gaba dayan sukayi waje
Zama tayi kusa da ita tana rarrashinta sae da ta tabbatar da tayi shiru da dakko kayan makeup ta mata yae simple bayan ta gama ta dauko mata wani less ash da yasha dinki da red dinki doguwar riga bayan tasa ta daura mata head dinta shima red sae sarka da dan kunni suma duka red haka ma takalmanta. Bayan ta gama shiryata tafito tsab da ita ta feshe fa da turaruka masu azababben kamshi.
Suka fito tana rike da hannuta su Amani dake tsaye a gurin suna jira duk suka taka musu baya har compound din gidan mutane sukayi caaaaa kansu kamar zasu hade amaryar.
Tun fitowar su safwaan ta zuba mata Ido ko kyaftawa ba yayi tayi mai kyau sosae a ranshi yace she is beautiful amma bata da kunya " dan karamin tsaki yyi ya kauda kanshi ganin sun kawo dap dasu.
Pics akayi tayi kamar ba gobe bayan an gama ya laeemat ta ja hannun su biyun suka tafi part din daddy nan ma pics akayi dasu ummi bayan an gama suka tafi ya rage daga amarya sae ango da frnds dinsu ya leemat ce ke nuna musu yanda zasuyi har aka gama.
Harda mutanen da ba'a gayyata ba duk sun zo irin su nernerh da sauran members din Ashwaan Hausa Novel yan kibiyar kaddarra da Kainuwa fans tun daga 1 har 10 duk sun zo suma sun laba dan ace wae sunje bikin ba lbr aka basu bah 🤣LoL
Da misalin karfe 6pm aka shirya kai amarya safa gidan angonta safwaan
Daddy, mommy, ummin Ammi, baba Hure ,mom, da safa sa uban gayya safwaan. Zaune suke a parlourn daddy Yana musu nasiha ya kalli safwaan yace
Safwaan ga amanar Aysha nan na baka, idan ka yarda ka cutar da ita koda bayan rainane ban yafe ba, kanwar kace kuma kasan bada son ranta akayi auren nan ba dan kawae lpyr ka ne ta yarda ta aureka. Ka tun bayan mu bata da kowa Kaine babba ka rike girman ka duk lkcn da ka ganta cikin damuwa kayi kokarin musanya mata da farinciki kuma kar kaga dan na hada wnn auren ka samu damar wulakanta ta ka zama mai hakuri a kowane lokaci kuma dan Allah ka rike amanar da na baka nasan inashallah sannu a hankali komae zae wuce dan a koda yaushe nayi istikara inuwar Aysha kadae nake gani a tare dakae
Ya juya ya kalli safa yace ke kuma Aysha na sanki da hakuri toh ki Kara akan wnn bana son jin wani tashin hankali ki zama Mae biyayya a kowane lkc kinsan aljannarki tana kasan kafar sa Allah ya muku albarka ya baku zuri'a dayyaba" duka suka amasa da Amin
Sauran ma duk sun musu iya nasu safa Kam Banda kuka ba abunda takeyi ji take dama kabarinta za'a kaita da yafi mata akan a kaita gidan mutumin da baya kaunar ta kokadan.
Daukarta sukayi suka kaita dakin mommy bayan kowa ya fita mommy ta maida kofa ta rufe zma tayi kusa da safa tace daughter Mae yasa kike kuka kamar anmiki mutuwa ko auren ne baki so da safwaan
Girgiza kanta tayi alamun aa
Mommy tace toh shknn yi shiru kinji idan baki son safwaan ne sae insa a raba auren yanzu sae a bashi Nabeela tunda dama ita tana son shi
Tace aa mommy dan Allah
Mommy tace toh ya isa kukan yi shiru kinji. Inaso ki zama mai rike sirrin mijinki karki yarda ki gwad fada ma koh da ummin kice abunda ke tsaka nin ku ki zama Mae tsafta duk da nasan ke training di nace amma kira akan Wanda na sanki dashi kinji
Tace inashallah mommy
Wataeda ta dakko ta bata tace gashinan mayan gyaran jikine kar ki zubar kinji Allah muku albarka ya kauda duk wata fitina da zata bullo
Tace ameen mommy ngd
Rufe mata baki tayi tace u deserve all all dis daughter
Smiling tayi ta rungumeta sae sabon kuka rarrashinta mommy tayi bayan ta tsagaita kukan ta ja hannun ta sae dakin ummi tana ajiye ta ta juya ta fita tareda rufo musu kofar
Nasiha Mae ratsa jiki ummi ta mata tareda addu'a .
Shigowa ammi tayi tace to uwar amarya muzo tafiya da ita
Wani sabon kuka safa ta saka musu dakyar ta rabata da jikin ummi da itama hawayen takeyi
My abokiyar fada ontop tace dama itace za'a kaiwa safwaan niko nace hmm nan baki San ko waye Shiba koh!!!
Fita sukayi da ita compound hmm Tasleem kuka safa kuka hugging din junan su sukayi da kyar aka raba su mota suka shiga daga nan sae gidan amarya
Tsayawa fada muku yanda gidan ya hadu bata lkc ne na baku dama readers kowa ya kiyasta
Parlourn kasa anyi decorating dinshi in a matured colour babu kalar da baza ku samu a ciki ba amma golden yafi yawa bau tsaya wani saka komae kala daya ba a,a kowace kala akwae.
Haurawa da ita sukayi sama suka nufi dakinta da ita kana shiga parlour ne da komae nasa army green and golden ne.
Kan makeken red and golden royal bed dinta suka direta har lkcn amarya kuka takeyi.
Da misalin karfe 9pm aka fara shirye²n zuwa dinner(toh fa suko kudin ne ya musu yawa haka naga har yanzu ba'a gama event din ba🤔)
Kusan kowa ya shirya ya Hafsa ce ta shigo tace"safa ta gama shiryawa"
Suka ce a,a
Tace toh idan ta gama tazo makeup artist din na jiranta
Pheena tace toh
Makeup din yau tasha bamban da na kowane event fadar tayi kyau ma zunubi ne ga wani fitinanne kamshi dake tashi jikinta rigarta black da ratsin golden head dinta ma golden ne sae wata dankareriya sarkar zinari dake wuyanta takalminta hills ne da tsayinsu 6 inches ne.
Masha Allah amaryar safwaan kin hadu.
9:28pm aka fara Shirin fita parking space din gidan mota motar dake dae² kofar gidan aka nufi safa da ita tun kafin ta shiga ciki kamshin turaren ta ke mishi welcome bayan ta zauna aka rufe musu kafar . Da kamshin turaren su ya hadu sae ya bada wani kamshi Mae dadi Mae sanyi gaba da yansu kowa da abunda yake sakawa a ranshi.
Sun fita titi street light ta haska sae Satan kallon ta yakeyi ita bata ma San Yana yi ba dan hankalinta na kan window
Wayar shi ya ciro ya shiga danne² shi unexpectedly yaji ta fado jikinshi sakamkon bogulas dinda suka hau.
Wani yarrrr yaji tundaga yatsan kafarshi har cikin brain dinsa itama safa haka da sauri da daga shi tare da basarwa.
Bayan sun isa hall dinda za,ayi event din kowa ya fito banda su safwaan da ke jira a bude musu kofa
Har tasa hannu zata bude yace malama ki bari azk a bude
Kallonshi tayi taga hankalinsa baya m kanta sai ta koma ta kafe jikin kujera
Tasleem ce ta bude mata shi kuma Rafeeq
Jerawa suka gaba dayan su amarya da ango na tsakiya
Hannunsa ya miko mata jiki a sanyaye ta saka nata aciki lumshe ido yyi dan jin taushin hannun nata kamar na jaririn da aka haifa yau. Tafiya suke kamar wasu 🌟 daka gansu kasan sun dace da juna shima safwaan bakar gezna ce a jikinshi da tasha dinkin sirfani golden
Wakar poko ta kiss dinel kawae ke tashi bayan kowa ya zauna aka fara gudanar da dinner
Rafeeq ne ya bada biography din safwaan Tasleem kuma tayi na safa
Rawa akayi sosae bayan sun gama aka kira amarya da ango
Wow gurin da suka tsaya pic dinsu ne a kasa na ranar frnds and sisters day an rubuta *ASHWAAN* a kasa. Tsaye kawae suke har gwanda safa tana dan juyawa. Da gangan safwaan ya taka safa.
Dan Kara tayi kadan tace haba safwaan me haka zaka wani takani.
Ko kallonta baeyi ba yace yau kuma ni kike Kira safwaan toh bazan dauka ba cox am not ur mate kin gane ko
Smiling tayi tace aiko ada dan nayi batan kaene amma yanzu da duhu ya yaye haske ya bayyana sae na gane ashe na Kara girman da zan kiraka da sunan da aka rada ma karfa ka manta matarka ce ni yanzu ba kanwarka ba idan ka manta toh na tinama kauta understood
Mutanen gurin sunyi tunanin mgnr arziki ce sukeyi dan face dinsu dauke da smiling nan kuwa basu san Tom and Jerry din fada sukeyi ba
Karin kudi kawa ake musu bayan sun gama frnds din amarya suka jata.
Step dance dinda suka yi practicing sukayi da wakar skeleton move
Safwaan kallon ta kawae yake a ranshi yace dama bata da kunya haka nan da nan kishin shi ya motsa yanda mutane ke daukar ta a waya bae San iya Ina zae tsaya ba .
(Na rantse ka banj laugh safwaan🤣)
Haka aka cigaba da dinner tareda daukar pics kamar ba gobe
Harda mutanen da banyi tsammani ba na gani
Aljana Aisha fans grp
Real nana Aysha fans ma duk sun zo
Haka ma menene matsayina Najeeb fans da Waye Shazama duk sun zo Kainuwa fans ma duk sunzo to ballantana su uwayen gayya Ashwaan Hausa Novel ai ba,a mgn.
Sae around 12 aka gama kowa ya koma gida su ya leemat da frnds din safa da wasu kannin mommy suka raka safa gida
A bangaren Safwaan kuma suna barin gurin dinner guda ya koma yayi kwanciyar sa.
Rafeeq yyi dashi akan ya tashi su karashi firrr yaki wayans hi ya ciro ya kira mommy yace "mommy wlhi ga safwaan nan nayi² dashi ya tashi ya tafi gda amma firr yaki
Tace bashi wayar
Karba yyi cikin sanyin murya yace maman safa Ina jinki
A fusace mommy tace safwaan tashi ka tafi gidan ka bana son shashancin banza umarni na baka ba shawara ba
Yace haba mommy kema kin San...
Bai karasa ba tace wlhi idan baka tashi ba ranka sae yyi mummunan baci daga nan ta yanke wayar ta tana mamakin hali irin na safwaan lallai safa zakiyi fama Amma zan tayaki da addu'a inshallah
Mikewa yyi ya fito parlour Rafeeq na bayanshi key din motarsa ya dauka frnds dinshi suka ce mu fito kenan
Ko kallonsu baeyi ba ya fita mara mishi baya sukayi suka fita gaba dayanshi.
Tunda ya hau titi Rafeeq yaga alamun bashi da niyar tsayawa dan haka yyi parking ya siyar musu kaza da fresh milk.
Suna shiga Tasleem ta leka ta window da sauri ta juyo tace guys ga sunan ku shirya
Sakko da amarya parlour sukayi suna zama sas gasu sun shigo bayan sun zauna sunata barkwanci sunkai kusan 30mins safwaan yace kunga malamai guf nyt ku tashi ku tafi dan wlhi na gaji da yawa.
Dariya sukayi gaba dayansu Habeeb yace ai dama tafiya zamuyi yanzu ma kuwa.
Rafeeq ya kalli Tasleem yace bby mukam idan lkcn auren mu yyi ba Wanda zaizo rakoni
Smiling kawae tayi kanta na kasa
Safwaan yace zaka fara koyawa yarinya rashin kunya tun yanzu
Dariya sukayi gaba dayansu suka mike ya musu rakiya har waje
Rafeeq yaja hannun safwaan suka koma gefe
Safwaan yace malam me haka
Rafeeq yace ba komae kasan ni doctor ne so pls kabi yarinyar nan a hankali dan nasan matse kake yau
Dukanshi yyi yace dan iska kawae
Dariya kawae yyi yace gsky ne dae
Kawayen shi sukace amarya Allah y bada zaman lpy mu dai zamu tafi kuma inshallah kafin mu tafi gobe zamu leko. Sae da safe
Rike hannun Tasleem tayi tana girgiza mata Kae tace twin sis dama ba Sona kike yi ba dama duk abunda kike fada a kaina karya ne dama akwae ranar da Zaki iya tafiya ki barni.
Kowa tsayawa yyi Yana kallon drama dinsu
Tasleem da hawaye ya wanke mata fuska tace don't worrybsis even if we are far distance our heart will still link together, I promised u I will come tomorrow. Hugging din juna sukayi suna kuka
Sun ba kowa tausayi Rafeeq ya matsa kusa dasu yace haba sisters what is this princess kiyi hkr gobe ni da kaena zan kawo Miki ita
Dagowa tayi tace promise
Yace I do
Rakasu tayi har bakin mota Rafeeq ya Mika ma safwaan ledar kazar da ya siyo yyi tareda yima motarsa key suka bar gidan.
Suna shiga gidan safwaan ya ajiye ledar ya wuce room dinshi itama safa room dinta tashi sae da tayi wanka tayi nafilanta yanda ta saba
Shima safwaan wankan yyi bayan ya fito ya sakko kasa da niyar kashe wutar duka parlourn sae ta tarar da ledar da ya ajiye inda ya barta
Tsaki yyi toh sae nace ta dauka ko kuwa tsabar rainin hankali ne.
Dauka yyi ya kashe bulbs din ya nufi sama.
Room dinta ya nufa ko da ya shiga ya tarar da ita kan sallaya tsayawa yyi har ta idar cilla mata ledar yyi yace gashi nan karkije kice ma daddyna hanaki abinci
Ko kallonshi batayi ba ta cigaba da azkar dinta buga kofar dakin yyi ta tintsire da dariya .
Banza tayi da ledar ta hau gado ta kwanta bacci yaki zuwa sae faman juyi takeyi a gado alamun yunwa Dan rabonta da abinci tun daren jiya
Sakkowa tayi daga kan gado ledar ta dauka dauka ta nufi kitchen dan ta dakko plate da cup.
Safwaan kuma bayan ya koma dakinshi ya kwanta phone dinshi ya dauko ya duba messages din da suka shigo wayar sa bayan ya gama yayi game da ya gaji ya ajiye juyi yake kan gado ga wani matsanancin ciwon da mararsa keyi mikewa yyi ya nufi kitchen dan dafa tea
Murda handle din kofar yyi haka yyi daedae da itama ta fito sae jin kanta tayi a jikinshi ta dago tace ya saf mai kuma ya kawo ka kitchen yanzu
Fuska daure yace dama mutum da gidan shi har sae an tambaya mai ya kawo shi kitchen
Smiling din yake tayi tace Allah huci zuciyarka
Ta juya ta tafi abunta kallonta ya tsaya yi Yana kallon hips dinta a hankali ya lashe baki sae da ya dae na ganinta ya shiga kitchen din ya dafa ruwan zafi da lime dinshi da ya saba sha
Niko nace hmmm kana da mata amma ka tsaya whalar da kanka😒🤦♀
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top