Part 17





Washe gari da safe ummi ta kira safa room dinta tace"safa bana son asamu matsala yau kiyi duk abunda ya kamata karnaji kuma kar na gani kin dae ji na fada miki"

Tace"insha Allah ummi ba abunda zae faru"



Da misalin karfe 5pm aka shirya zuwa *CROSSING OF THE SWORD*

Gaba dayan su sanye suke cikin wando na soldiers da white polo shirt da aka rubuta *ASHWAAN* a jiki to masu son sanin mae *ASHWAAN* yake nufi yau zasu sani .

Asalin sunan Safa Aysha idan readers basu manta ba toh idan aka hada farkon sunan safa *ASH* sa mu dauko na karshen na safwaan wato *WAAN* zae bamu  *ASHWAAN*. Hope kun gane.

Wannan abun ba aikin kowa bane sae Rafeeq da Tasleem ba safwaan ba har safa taji dadin wnn sunan.

Make up din safa na yau yafi na saran ranakun kyau kallo daya zaka mata ba sae ka kara na biyu bah wando tasa da riga fara shape dinta ya fito figure 8  sae wasu takal ma hills sosae masha Allah kawae na iya furtawa.

Kallon kanta tayi ta mirror tace "gsky ya Hafsah bazan iya fita haka ba kalli fa yanda wandon na ya matseni duk shape din jikina ya fito"



Ya Hafsah tayi dariya tace"hkr zakiyi sis kinji"

Tasleem dake bakin kofa tace"hmm manya masu kunya da dae an daura aure duk wata kunya fita zatayi"

Ya Hafsa tace"mara kunyar banza naga ke yanzu kin lalace ko"

Dariya kawae tayi ta fita. A kasa safa ta same su duk sun shirya ita kadae ake jira.

A compound motoci sukayi parking ana jiran amarya da kawayenta su fito. Tunda daga nesa safwaan ke kallon safa wani tsartsar yaji tundaga yatsan kafansa har cikin brain dinsa.

Gaba daya tafiyan ta ya canza sbd hills din da tasa. Wani frnd dinshi da suke cikin motar yace"masha Allah komae yaji zamzam"

Ran safwaan in yayi dubu ya baci fita yyi daga motar fuuuuuuu yaje inda su mom faty ke tsaye yace" mom ya za'a yi dan Allah yarinyar nan ta fita cikin mutane haka gsky ta canza kaya"

Mom faty tace"kayi hkr bafa a daura aure ba "

Yace"ehh duk da dae haka"

Tace"toh gsky ba wani kaya  da zata saka yanzu dan daga na dinner sae na walima suka rage kuma kasan tun daga Dubai muka dinko su so kaga  ba yanda za'a yi"



Ba San yaso ba ya hkr ya koma mota.  Bae jima da zama ba sae ga tawargarsu safa mota aka bude mata ta shiga a hankali ta zauna.

Kamshin turaren da safwaan yaji ba karamin daga masa hankali yyi bah. Ya dauke kansa ya maida ga kallon window.



Bayan kowa ya shiga aka fara tafiya. Ba Wanda yace ma wani kala shiru kawae kake ji kowa da abunda yake kiyastawa a ransa. A haka har suka isa. Tasleem ta fito da frnds din su suka nufo motar da safa ke ciki bayan sun bude Amani tace"matar soja ae sae ki fito ko"

Marairacewa tayi tace"wlhi bazan iya fita a haka ba Allah"

Safwaan ya tabe baki yace"dama kina da kunya haka toh mai yasa tun a gida baki ce a canza miki bah"

Banza ta masa tafi fuuu, ya ciza lips dinsa ya fito a bakin kofa suka jera gaba dayan su, safwaan sae wani shan kamshi yakeyi itadae safa bata masan yanayi ba. Ta hanyar da zasu bi an shinfida wata red carpet sae kuma wash soldiers dinda suka rike sword sunyi crossing dinsa ta tsakiyar gurin suka bi, Tafiya suke mae cike da kasaeta su Tasleem dake baya suka dinga watsa musu shine2 da kuma wani spray mae kumfa.

Bayan sun zauna aka mike tsaya domin national anthem bayan an gama suka zauna. General ya tashi yyi dan jawabi daga nan sauran manyan sojoji sukayi nasu. Bayan an gama kuma aka bukaci ganin amarya da ango bayan sun fito aka kawo mata wanidan tray ta dauki wata Yar flower ta saka mishi abun ya matukar birge mutane sosae.  Bayan nan safa ta samu gift da yawa daga ciki ko harda keyn mota godiya tayi sosae da nuna jin dadinta . Taro yayi taro abun sae son barka..









          *D_DAY*

Washe gari Friday, tunda safa ta tashi ta rasa meke mata dadi a duniya. Gashi gdn ya cika da mutane . Mommy ce ta shigo dakin taga alamun basuda niyar yin wanka tace"dota taso muje kinji naga wadan nan basuda niyar yin wanka yau"

Kamar zata yi kuka  mike suka fita . Bayan tayi wanka mommy ta bata wani material sky blue gown tasa sae takalmin da sarka duk  silver  light make up aka mata amma tayi kyau sosae. Daki ta koma koh da tashiga ta samu wasu daga cikin frnds dinsu sunyi wanka suna shiryawa.

Zama tayi kan gado ita kadae tasan abunda ke

damunta. Wata Yar yarinya karama ce ta shigo direct gurin safa taje tace"aunty amary wae inji ya Rafeeq kizo"

Tace"ok toh kice ina zuwa"

Ta kalli Tasleem tace"dan Allah muje ki rakani"

Tasleem tace"ba inda zani banyi wanka ba yarinya"

Ta marainiyace tace"yanzu b mae rakani". Suka ce ehh  jiki a sanyaye ta mike gabanta sae faduwa yakeyi ta fita.







♠♠♠♠♠

A bangaren Safwaan kuma koh da Rafeeq ya shigo daki ya tarar da safwaan kwance yana bacci hani'an duka ya daka .asa yace"dallah malam tashi kasan karfe nawa yanzu zaka kwanta ka saki gandar lebe kana bacci"

Tsaki safwaan yyi yace "wlhi ni har na ma na manta"

Rafeeq yace"ai dole kamanta mana toh wlhi daddy na jiranka a parlourn sa"

Ai da sauri ya fada toilet yyi wanka. Bayan ya fito yaga wata gezna sky blue da tasha sirfanin nevy blue dinki yyi kyau sae hula zanna bukar sae wrist watch dinsa Rollex silver colour Rafeeq dake gefe yace"dallah malam ba kallon kayan zakayi ba sawa zakayi" tsaki kawae yyi ya dauki kayan. Ya shirya tsaf cikin shaddar yyi matukar kyau sosae kallon kansa ya tsayayi sae wani smiling yake . Kiritt Rafeeq  ya dauke sa photo dariya yyi yace"gsky nayi kyau"

Rafeeq yace"hmmm shekin angonci ne kake yi malam baka g komae ba sae ka ida shiga ciki tukun"

Duka ya mae masa ya kauce yace"Dan isaka kawae"

Fita sukayi inda suka tarar da sauran frnds dinau dake parlourn tsokanar sa suka shiga shidae iy karsa smiling.

Part din daddy suk fito da niyar zuwa sae ga Tasleem cikin tashin hankali tace"ya feeq ina safa dinda ka aiko a kirama"

Kallonta yyi da mamaki yace"ni ban aiko a kirata ba"

Tasleem tace"muna fa zaune a daki yar gudan Ammi tashigo tace kana kiranta so tace in rakata nace bazanje dan alkcn banyi wanka ba so kuma tundaga nan bata dawo ba "



Rafeeq yace"kun diba cikin gd"

Tace "ehh"

Yace"kirata kiji mana"

Tace"ga phone dinta anan"

Innalillahibya dinga maimaitawa safwaan dake tsaye yace"toh ku tambayi su mommy mana"

Tace "kowa fa na tamabaya"

Part din mommy suka nufa direct da ta gansu cikin tashin hankali ta tmbay lpy Rafeeq ne kadae ya samu ya mata bayani. Mommy ma takira daddy ta gaya masa abunda ke Faruwa yace gashi nan hanyar gda.



Hankalin mutanen gda ya tashi gaba daya amarya ta bata bat........

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top