Part 14

Bayan kwana biyu daddy ya shirya tafiya shida uncle  Hassan zuwa Chad amma bae gaya ma kowa Chad din zashi bah haka ma Rafeeq ba gaya ma kowa ba idan dae sun matsa yace musu ae wayar shice ta fadi kuma suna aikin da baza a iya kiransu ba kuma dajin babi network amma sunyi waya ta hanyar ogansu yace komae lpy.

Daddy ma da zae tafi sae yace musu Spain zashi gurin wasu kaya da za'a shigo dasu.

-----------

Safwaan kam yana samun kulawa sosae dan tuni ya farfado su daddy ma da suka je satin su biyu suka dawo saboda ogansu yace zasu iya tafiya nan da wani sati zasu sallame shi ya dawo gda.



*A WEEK AFTER*

Tsaye muke a airport nida Mrs BB muka hango wani hadaddaen guy sanye yake da wata white polo da wandon soldiers sae kuma rigar da ya daura a waist dinsa itama ta kayan kakin ce wata yar jaka ce rataye a wuyansa da ya riko da hannu tafiya yake cike da izza da kasaita.  Mrs BB tace anya ko neeshar bazan ma gayen can mgn bah (hmm nidae b ruwana kar ayi daedae da allurar sojojinsa ta taso ya mazgeni nayi nan😂😂🏃🏃)

Rafeeq kadae yazo daukan shi bayan sunyi hugging din juna da tareda gaisawa suka shiga mota suka wuce   gda.

Bayan sun isa gda suka gaesa da su baba mai gadi da sauran ma'aikatan gidan tareda mishi ya jiki.

Yana saka kafarsa cikin parlourn mommy Tasleem dake bayan kofa ta mae wata irin muguwar runguma tana fadin"oyoyo Heart❤"

Rankwashi ya kai mata akai dan ta dan tsoratashi

Baki ta turo tana cewa"haba ya saf daga dawowar ka"

Yace"ehh din kin wani tsorata mutane"

Tace"ashe dae kae ba cikakken soja bane tinda har kaji tsoro" ta karashe mgnr tana dariya🤣🤣

Yasa hannu zas kamata amma t gudu🏃

Yace"naughty girl ashe kina da tsoro zaki shigo hannu ne"

Gaba daya parlourn aka sa dariya kara sawa yyi inda su daddy suke bayan sun gaisa  suka masa ya jiki .ummi tace "son ga abinci a dining yana jiranka"

Yace"dearest bari nayi wank n dawo"

Safa da tajo yace dearest ta tabe baki kawae

Mommy tace"toh  hmmm harda wani suna dearest kuma yanzu"

Ya shagwabe fuska yace"mommyn yara kin sa mana ido nida ummina"

Sukayi dariya gaba daya ya leemat tace"ya saf har yanzu baka girma ba duk da ka kai ga yara"

Ya kalleta yace"naga kin rainani zaman ki gidan nan kwana biyu karki ga dan kinyi aure harda bby kimin rashin kunya"

Daddy yace"aikin banza ai ta girmeka yanzu tunda har ta riga aure kuma ta haihu kayi zuciya ka fito da mata kafin karshen she kara amaka aure"

Cikin shagwaba yace"ummi kina ji ko"

Ummi tayi smiling tace"kyalesu ai aure lkc ne dashi idan Allah ya kawo mata sae ayi Allh dae y baku ta gari"

Suka amsa da ameen

Tasleem tace"nida twinie zamu dauki nauyin sisters and friends day kuwa"

Wata uwar harara ya sakar mata hakan yasa tayi shiru ya kalli safa yace "baki iya gaisuwa bane"

Shiru tayi tana wasa da zoben da ke hannun ta

Yace"toh na dawo lpy ban mutu ba dam nace miki mutum baya mutuwa sae lokacin shi yyi"

Mommy tayi dariya nan ta bashi labarin duk abunda ya faru bayan sun dawo daga airport jinjina kae kawae yyibya mike tsaye yace"bari nayi wanka na fito"



Sukace to.

*_"_"_"_"_"_"_"_"*

Baku tambaya ina masoyan safa bah hmm

A gdan su ya ma'aruf kam mom ta matsa akan ya fito da matar aure tunda ta hada shi da yara da yawa yace aa amma kuma har yanzu bae gaya ma kowa safa yake so ba dan har yanzu itama Bata taba furta tana son shi bah



*:::::::::::::::::::::::::::*

Ya kabeer kum tunda yaga alamun safa kamar bata son shi yasa y janye sae dae suna shiri sosae fiyeda da yace yana sonta hakan yasa ya maida akalar kan Asma'u kawarsu Alhmdllh har ansa date kuma.

*-:-:-:-:-:-:-:-:-:-:-:-:*

Sir farouq kam harda kwatawa asibiti ciyon zuciya ya kamashi hakan yasa iyayen sa suka dauke shi suka maida shi gda lkcn da aka gaya ma safa hankalinta ya tashi sosae lallae bazata taba mantawa dashi ba a rayuwar ta..





*°^°^°^°^°^°^*

Bayan ya fito daga wanka ya shirya cikin kananan kaya sae baza kamshi yake parlour ya shiga ya iskesu suna fira dag nan gaba daya suka wuce dining dama shi ake jira bayan su Tasleem sinyi serving kowa aka fara kwasar girkin da ummi ta musu  suna cin abincin suna fira banda safa da ra hadiye rae ba alamun annashuwa a fuskarta.

Tasleem data kula da hakan tadan zungure ta ke kin manta a gaban su daddy kike fah"

Ta danyi smiling tace"kekin San mutumin nawa ya dawo"

Tasleem tace"amma da baya nan kinata kewarsa"

Tsaki tayi da yasa kowa a gurin saeda ya kalleta da alamun tambaya

Idan akwae abunda safwaan ya tsana bae wuce tsaki ba hararta yyi itama ta hararesa tareda kauda kanta gefe.

Ummi tace"princess mai yasa ki yin tsaki"

Dan smiling tayi tace"umki cikina ke ciwo"

Ummi tace"shine zae saki tsaki karki kara"

Tace "insha Allah"

Daddy yace"data kinsha magani"

Tace"ehh daddy"

Yace"toh Allah kara sauki"

Ta amsa da amin

Tasleem kam sae dariya take kasa² abun ya kara bama safa haushi ta mike zata bar gurin mommy tace"dota karki cemin kin koshi"

Tace"ehh mommy"

Mommy tace"to me kika ci anan"

Tace"laaaa mommy ae naci da yawa ma fah"

Mommy tace"dama ke ba son abinci kike bah"

Dariya tayi tace"a'a mommy Allah ae yanzu ina ci da yawa"

Mommy tace"Allah ya shiryeki"

Tace amin



*°•°•°°•°•°•°•°•°•*

Washe gari gari da misalin karfe 4:30pm  duk suka fara shirye²n zuwa event din da za'ayi banda safa dake kwance cinkin blanket.

Tasleem ta gama shiri taga safa bata niyar tashi ta shirya kuma ta mata mgn amma ta mata banza.

Dakin mommy ta shiga tsaye ta sameta a bakin mirror tana saka sarka Tasleem tace"mommy safa bata shirya ba kuma na mata mgn amma ta min banza maybe idan keki je zata tashi"

Mommy tace"ni na rasa gane kansu ayi mutane suna zama gda daya amma basa shiri kullum kara rura wutar fadan suke Allah ka shirya min su"



Tasleem tace"amin"

Tare suka fita suna shiga mommy taje kan gadon ta yaye blanket din ta taba wuyanta taji jikin ta warm acikin sigar lallashi mommy tace"dota ciwon cikin ne har yanzu"

Ta daga mata kae alaman eh

Tace"sannu bari akawo miki  lepton kisha kinji sae kisha magani kinji"

Tana fita safa ta mike tna dariya tace"kai wlhi naji ddi, kinga yanzu am not going anywhere"

Wani haushi da ta kaici ya kama Tasleem tace"toh wlhi bari naje na gaya ma mommy"

Safa ta sakko daga kan gadon da gudu tace"Dan Allah twinie kiyi hkr kin San ba shiri muke da ya saf ba plss dan Allah🙏🙏



Tasleem tace"to shknn matar soja amma  ko ba dan ya saf ba ya kamata kije saboda kina son soja sosae"

Bayan da ta iya dole ta shirya kaya iri daya suka saka sunyi kyau sosae dan Tasleem cewa tayi sae ta mata makeup.

A parking space suka tarar da mutanen gdan su gaba daya.  Daddy da su mommy mata daya Rafeeq da sauran ma mota daya.

Bayan sun isa Rafeeq yaja hannun safa suka koma geje yace"ki saurari abunda zan fada miki da kyau Aysha"

Daga face dinta tayi ta kallesa taga ba alamun wasa a face tace"ya feeq kaene yau ka kira sunana"

Yace"ehh idan muka shiga ki nuna ma mutane u re safwaan's fiance za'a saka miki ribbon indicating u re so special to him zaki zauna a high table so behave ur self and do as I said pls"

Tace"toh ya insha Allah "

Yaja hannun ta suka koma gurin sauran

Jerawa sukayi tare suka shiga hall din bayan kowa ya zauna aka fara da national anthem bayan an gama akayi speech daga nan aka fara Kiran wadan da za'a karama girma.

Bayan sun fito wani mutum na gani dauke da wani decorated tray  a hannu daka gansa kasan karamin soja ne duk matarsa tazo sae ta saka masa sabon  star tare da dan jawabi.

Da a kawo kan safwaan sae ya kalli safa dauke kanta tayi ta maida dubanta ga star din da zata saka mishi matsawa tayi kusa dashi idon ta na kasa tace"ya saf dan duko tsayina ba zae kae bah pls"

Dan rankwafa yyi ta cire masa old star din tasa masa new one.

Microphone din ta karba jikin ta ya fara rawa cikin muryar ta mae dadin sauraro ta fara mgn in britit" congratulations; well done  is your hard-working dat brings u upto dis level u re today.

You are on the road to success, u re on d way to progress, hope u will put more effort, i wish u a successful leadership and may Allah continue to guide and protect u against ur d evil ones. I really appreciate ur hard work my husband"

Tafi kawae kake ji rap³ sae daya daga cikin ma'aikatan gurin yace ta tsaya za'a masu  pic. Pics aka musu sosae Rafeeq ma saida ya musu da phone dinsa haka ma Tasleem ta Musu  har a wayar  safa din  mutanen gurin ma duk sun dauka dan  ta matukar burgesu haka aka cigaba da gudanar da event din cikin gin dadi ba a gama bah saw 9pm.

Bayan an gama kowa ya fara Shirin tafiya gida tunda suka shiga mota ba Wanda yyi mgn har tafuya tayi nisa

Rafeeq yace"gsky lil sis u really killed me kinga yanda kika yi kamar kece matar tasa da gaske kai am really impressed "

Safwaan ya tabe baki yace"saunawa zan gaya ma ka dae na hada ni da wnn yar 300level din she is not my type karma kasa ta fara jin wani abu game dani"

Cikin tsiwa safa tace" ai dama ni bance ka aure ni bah da zaka wani ce kae baza ka auri yara bah Dan Allah ka dakko yar shekara 1000 matsalar wa. Sannan kuma karka kara kirana da yarinya dan ban maka kama da ita bah yara a bayan uwarsu kawae kake ganin su yanzu ma wlhi darajar  Order hafl dina kaci da ba abunda zae na bata lokacina har na tsaya sama wnn banzan abun. Kuma jira kaji wlhi nafi karfin auren ka dan banma kama da da kalar matar da zata aure ka bah wae ma......."

Bata karasa ba Rafeeq ya daka mata tsawa"are u stupid dat u will be telling ur elder such kind of words"

Zata yi mgn yace"I don't want to here anything from u just keep ur mouth shut"

Shiru tayi bata kara cewa komae ba har suka isa gd. Koh gyara parking bai gama bah ta bude mota ta fita fuuuuuu.

Dariya Tasleem take ba kakkaurawa hakan ya harzuka Safwaan ya daka mata tsawa"ke ubanwa kike ma dariya anan"

Hadiye dariyar tayi Rafeeq yace"haba mana bro cool down ka gama da safa shine zaka sauke haushin ka akan ta toh wlhi enough is enough kar allurar sojojin ka ta sauka kan matata"

Tsaki kawae safwaan yyi ya fice shima.

Rafeeq ya kalla Tasleem yace"bby dawo gaba"

A kunyace ta koma gaban ta zauna reverse yyi suka fita daga gidan gaba daya.

Rafeeq yace"bby wae yaushene zaki zama mallakina hakurina fa ya fara karewa "

Smiling kwai tayi ta maeda dubanta ga titi Rafeeq yace"answer me now"

Tana kallon window tace"in d next 10years to come"

Parking yyi abakin titi yace"to sae mu jira anan har shekara goman suyi"



Zaro ido tayi waje a shagwabe tace"Allah wasa nake maka"

Muryar ta ya kwaikwaya ya maimaita abunda tace

Dariya kawae tayi tana rufe fuskarta da bayan hannun ta.



*№№№№№№*

A bangaren safa kuma room dinsu ta wuce direct tana shiga ta fada toilet tayi wanka bayan ta fito spray kadae ta fesa ta dakko nyt wears dinta riga da wando ta saka ta dakko socks da hand gloves da hularta bobble hart tasa sbd garin akwae sanyi.  Bayan ta gama shirya wa tayi sallah ta koma kan gado ta kwanta..

-------

Safwaan ma wanka yyi bayan ya fito yaje gaban mirror yana goge kansa da karamin towel kalaman safa kadae yake tunawa smiling din gefen bakin yyi ya fesa spray ya shirya ya fita



Bayan su Rafeeq sun dawo part din ummi suka shiga bulbs din parlourn akashe amma TV a kuune take Rafeeq ya kunna wutar parlourn tsaki sukaji anyi hakan yasa Rafeeq zuwa gurin safa din sae yaga safwaan a kwance yace"aa bro na u off d lyt sbd kana kallo"

Tsaki kawae yyi ya juya Rafeeq ya karba ledan hannun Tasleem yace ta kira safa tace toh tana shiga dakii itama wanka tayi bayan ta fito tayi sallah ta saka irin kayan baccin safa. Kan gadon taje ta tada safa tsaki tayi tace"lpy kika tadani"

Tasleem tace"ya feeq ne ke kirn ki"

A tare suka fito parlourn bayan sun zauna Rafeeq ya jowo ledan da ke kan cetre table ya mika musu Tasleem ta karba ta bude ta dakko ice cream da shawarma ta bama safa ita m ta dakko nata.

Safa tace"wae dama sbd wnn ne aka tadani"

Yace"eh n tuna lkcn da kina yarinya ne bakya bacci saw abbah ya dawobya kawo miki I've cream shine na fita na siyo miki"

Turo baki tayi tace"toh ai yanzu na girma"

Yace"ehh amma ba sosae ba"

Dariya kawae tayi ta dauka ta fara sha nan suka fara fira dan ita bata masan safwaan na gurin bah.. fira tayi fira sae dariya suke kamar ba dare bah Rafeeq ya fada wata mgn hakan yasa safa tayi wata irin dariya mai hade da ihu.

Tashi safwaan yyi ya daka mata tsawa"ke bakinda hankali ne kike ihu haka kamar baki San dare yyi bah"

Tace"wlhi da hankalina dan kawae kana bacci shine zaka ce kar muyi fira ai saw ka koma dakin ku mana"

Kallonta kawae yyi ya mamakin yanda ya barta take gaya mishi mgn son ranta.. Mikewa Rafeeq yyi yace angel gud nyt and sweet dreams". Snn ya kalli safwaan yace"bro sae ka shigo"

Safa tace"dama ita ai zka cemata sweet dreams".

Yanda tayi mgnr ya bashi dariya itama Tasleem saida tayi safwaan ne kawae baeyi ba wae shi a dole baya son raini. Rafeeq yace"Allah shiryaki" tace "ameen"

Bayan tafiyar Rafeeq Tasleem ta shige daki safa kam tace ita dole sae tayi kallo tunda suka tada ta bayan tafiyar su Safwaan nason kashe wuta amma yakasa mata mgn juyawa yyi yana kallon sofan da yake kwance a kae.

Kusan 30mins ba Wanda yyi mgn sae safa dake ta faman jera tsaki hakan yasa safwaan mekewa yace"ke  wae akwae ubanda yace ki tsaya ne dazaki dinga ma mutane tsaki"

Safa tace"naga ikon Allah ka tashi kaje part dinku mana"

Zaeyi mgn kenan aka dauke wuta zubur safa ta mike tace"Dan Allah ya saf kunna min flash din wayar ka in tafi dakin mu"

Banza ya mata kawae ta miki ta fara lalubar hanyr karap ta fada kan sofan da yake kwance kusan 1min suna a haka tace"dan Allah ka kunna min flash dinka intafi daki" tureta yayi ya tashi bayan ya kuuna flash din wayar sa ita kuma ta tafi daki da gudu.

A nan ya zauna ya kasa tashi yaje daki  bayan an kunna generator sae kawae ya gyara kwanciyar sa ana Dan ko motsi kadan ya kasa yi haka ya dinga juyi har washe gari........

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top