Part 12



..... Alhmdllh su safa an isa Bauchi lpy bayan an gama kwashe kayansu daga cikin mota kowa ya ja nashi zuwa masaukin shi Tasleem da safa a room din da ke kusa da na ya Haleema suma yada zango ko ina fes kamar masu gdn basu tafiya ba da kafin su iso

Siblings sin Saheeb (mijinta) sunzo sun gyara gdan tare da masu aiki ga kuma girki mae rae da lpy akan dining.

  Wanka  sukayi  tare da sallah margrib da isha'e bayan sun fito suka ci abinci kafin suka koma daki suka kwanta dan sun gaji over.



*************************

A gdan su kuma bayan tafiyar su Safwaan ya wuce garden ya zauna yana aiki da system dinsa Rafeeq kuma ya tafi hospital.

Nabeela na zaune a parlour ita da mommy suna kallo sae ta mike tace "mommy ni zan tafi sae kuma na sake lekoku*

Mommy tace "da wuri haka zaki tafi  ki bari driver ya maida ke mana" tace "aa mommy sauri nake kuma gashi sae na tsaya cafe sae anjima"

Mommy tace" toh ki gaida gida"

Bayan fitar Nabeel bata tsaya ko ina ba sae garden tun a zaune ta same shi ya dora kafa daya kan daya dayan hannun sa na rike da roban Chapman dayan kuma yana kan laptop din da ke kan kafar sa.

Guri ta samu ta zauna smiling tayi tace"Weldon ya Safwanna"

Bai dago ya kalleta ba kuma baice komai ba ya cigaba da aikin sa ita kuma Nabeela tayi tuna nin ko baiji bane ta kara cewa"ya Safwanna sannu da aiki"

"Sannu" kawai  yace shima kamar an masa dole zata kara yin mgn yace"see Nabeela am busy now so just live"

Marairaice fuska tayi tace"ya Safwanna mai yasa kullun idan na zo gurinka kake min haka koba komai aini yar uwar kace wlhi bana jin dadi gaba daya dan Allah ka dai na"

Bai dago ba kuma baice komae ba ya cigaba da aikin sa ita ko ta dora da fadin"haba ya Safwanna mai yasa kake neman illatar min da rayuwa ko dan kaga ina son kane dan Allah ka taimakamin kar na rasa raena ban San ya zanyi wnn dawainiyar sonka dake hanani bacci ba kullum dan Allah ka....."

Bata kara sa ba yace"shiiiii tashi ki tafi "

Wani kuka mai tsuma zuciyar mai sauraro Nabeela ta hauyi sae da ta tsagaita tace"dama ai zan tafi dama nasan kafi San bare a kaina shiyasa ma kafi sake mata fuska dan Allah ka gaya min mai safa tafini da shine da har kake wulakan tani akanta" kukan da ya kara zuwa mata ne yasa ta kasa karasa mgnr

Ajije laptop din yayi ya kalleta yace"ki daina wahalar da kanki Nabeela mgnr kuma nafi son safa akanki bana son kara jinta kuma...

Bata bari ya karasa ba tace"ai dama baza ka so ka sake jinta ba tunda...."

Itama bata karasa ba ya daka mata tsawar da tasa hanjin cikinta juyawa"ke karki gaya min sheet ko dan kinga ina lallabaki ne da alama kin manta gaban wa kike ne snn karki kara min mgnr wata anan idan ma sonta nake ina ruwanki toh let me tell one thing u re not my type so karki kara gangancin zuwa inda nake". Yana kaiwa nan ya figi laptop dinsa ya wuce.



Za a tayi agurin tana ta rusa kuka saida tayi mai isarta snn ta miki jiki ba kwari ta fito. A compound ta hadu da mommy a tsaye cikin dasashshiyar  murya tace"mommy na tafi" bata jira jin amsar ta ba tawuce.

Girgiza kai mommy tayi dan tasan akan danta take wnn kukan kuma tana tsaye a gurin ta ga ya wuce fuuuu kamar zai tashi sama baba maigadi ne ya katse mata tunanin da takeyi leda ya bata ta koma cikin gida



«»«»«»«»«»«»«»«»«»«»«»«»

A bangaren mutanen Bauchi kuma basu tashi bah saida asuba shima Kiran wayar da ya shigo phone din safa ne ya tashe su Ya kabeer ta gani yana yawo akan screen dama tasan shine da kullum shike fara tadasu daga bacci.  Tasleem tayi tsaki tace"mayu kawae sun bi sun addabi mutane suna bacci mtssww" taja tsaki tana mikewa    toilet ta shiga tayi alwala ta fito itama safa bayan ta gama waya ta mike tashiga tayi alwalan ta ta fito kara'atanul fijir suka fara yi kafin a kira sallah bayan sun gama kowace ta dakko wayar ta ta fara karatun Alqur'an wnn training din ummi ne dan tun basa so har yabi jikinsu.  



(Uwaye ya kamata mu kula da tarbiyar yaran mu sosae koya musu ibadah da sauran abubuwa akan mu yake idan kika saba ma yaranki da tashi cikin dare suyi sallah haka zaibi jikin su musamman yan mata da samari idan kika ga cewa da kin tafi koma wa zasuyi su kwanta sai ki tsaya a gurin kuyi sallahr tare haka ma raka'atanul fijir da kuma karantun asuba yafi komi zama kan mutum saboda a wnn lokacin kwakwalwarsu a bude take ba hayaniyar da ta shiga kansu . Ku kula da azkar dinsu saboda azkar din safiya d a yamma babbban makamine haka ma daily prayers dinsu dan Allah Dan ba kowane yaro bane idan kika ce je kayi sallah zaiyi wasu saedae kawai suyi alwala su labe suce sunyi sallah dan Allah iyaye akula da tarbiyar yara

Allah ya kama mana)

Bayan sunyi sallahr asuba suka koma kwanciya bacci basu tashi ba sae kusan 10:57am a  da Ya Haleema da Saheeb bayan sun gaisa Ya leemat tace "breakfast dinku na dining dan tun dazu na leka na gani ko kun tashi  na samu kuna bacci"

Smiling sukayi tare da wuce wa dining din bayan sun gama cin abinci suka dawo parlour ya leemat kadae suka tarar dan Saheeb ya fita zauna wa sukayi suka fara fira cikin nishadi.

Ya leemat tace"wai baku tashi aure bane sai kun tsufa"

Tasleem tace"kinji ya leemat ai saida kuka gama uni kafin kukayi aure to muma haka"

Ya leemat tace"hmmm dan muna kasar da ba tamu bane amma da ba haka ba idab kuna da mazajen aure kuyi abunku in yaso sae ku karasa karatun acan din yafi dan kun San yanzu sai a hankali"

Safa tayi smiling tace"Allah dai ya kawo nagari"

Suka masa da ameen

Ya leemat tace"safa bana ji jiya Nabeela na fadin ki kula da soyayyar su ba hakan na nufin ya Ma'aruf ke yake so kenan "

Kasa tayi da kanta tana wasa da yatsun hannun ta ya leemat tace"feel free mana am ur elder sis"

Safa tace"ya leemat mutum uku ke sona bayan ya ma'aruf akwai ya kabeer elder brothern Amani snn kuma akwai wani lecturei dinmu muna kiransa da sir farouq"

Ya leemat tace"toh safa decision ya rage naki ki zabi wanda yafi kwanta miki a rai"

Safa tace"ya leemat wlh bana jin son kowa a raina ya Rafeeq yace nayi salatul istikara kuma nayi amma dae ba abunda ya canza kuma gashi sun dame ni kowa so yake nace ina sonsa "

Ya leemat tace"toh Allah kawo mafi alkhairi"

Suka amsa da ameen ya leemata tace"Tasleem kin fada ma mommy cewa Rafeeq kike so ko kina nan da bakin halinnan na zurfin ciki"

Tasleem tayi dariya tace" aa amma kin San mommy da saurin harbo jirgin mutum tuni ta gano ai"

Ya leemat tace"toh Allah ya kaimu lokaci musha biki"

Suka amsa da amin suka cigaba da firar su







Haka suka cigaba da zaman gdn cikin jin dadi har Saheeb ya maida ya leemat gd haihuwa tare da su safa

Masoyan ta kuma kullum cikin kiranta da nuna mata zallar sonda suke mata sukeyi  kuma gashi next week zasu koma skl inda zasu jame da sir farouq



★★★★★★★★★★★★

A bangaren Safwaan ko tun ranar da Nabeela ta kara zuwa gdn washe gari ya shirya zuwa Spain ya dawo yau washe gari su safa suka dawo daga Bauchi



№№ *A WEEK LATER* №№





Su safa suka koma skl kuma a wnn satin ne ya leemat ta haifi santaleliyar yarta mace gaba daya gdn cikin farin ciki suke dangin Saheeb ma ba'a barsu a baya bah 

Saheeb ya taka rawar gani sosae dan tsayawa fadan irin abubuwan da ya kawo wa bby da mamanta bata lokacine

Bayan sati akayi suna yarin ya taci sunanta Maryam (sunan maman Saheeb kenan) suna kiranta da little M



*TWO DAYS LATER*

Around 9pm daddy ya kira safwaan parlourn sa bayan sun gama magana daddy yace"yanzu Chad din zaka tafi gobe"

Safwaan yace"ehh daddy "

Daddy yace "toh Allah ya kaimu ya kuma sa ayi a sa'a " ya amsa da ameen  suka cigaba da firarsu



Washe gari da safe Safwaan ya shiga part din mommy ya mata sallama ta mishi addu'a da kuma fatan samun nasara ita dae har ga Allah badan daddyn su ya matsaba da safwaan bai zama soja ba dan tana tsoron wata rana a kawo mata gawar danta

Bayan ya fita part din ummi ya wuce bayan sun gaisa ta hada mishi breakfast yaci da ya fito zai tafi ta mishi addu'a da fatan nasara.  Fitowanshi keda wuya yaci karo da Rafeeq safa da Tasleem Rafeeq yace "yane guy ka shirya mommy tace mu kaika airport since sisters dinn naka are free today are we good to go"

Safwaan ya daga kafada alamun no problem kayanshi kawae Rafeeq ya dauka mishi suka shiga mota suka fara hanya bayan tsawon lokacin da aka dauka ba mai cewa komai sae Rafeeq yace" nikam wai yau kun gaida yayan ku kuwa"

Tasleem tace"morning ya saf"

Yace"morning amma saida na roka"

Tace"tace pardon"

Rafeeq ya kalli safa yace" ke baki iya gaisuwa bane"

Turo baki tayi tace"morning ya saf"

Baiko kalleta ba yace"morning"

Rafeeq yace"bro yaune zaku fita operation din"

Safwaan yace"I think so shi yasa shi yasa kaga ina sauri sbd kar ace yau kuma kaga ban huta ba"

Safa tace"dan Allah ya saf ina zuwa wlhi ina so inga yanda soldiers ke operation plsss ta hade hannu alamun roko🙏

Safwaan yace"toh ki zama soldier mana yanda zaki fi gani da kyau toh bari kiji wnn abun tsakajin mutuwane ko rai kawae ki mana addu'a kinji"

Ta share kwallan da ya zubo mata tace "promise ya saf"

Gaba dayan su dariya sukayi suna jin jina irin wnn son da safa kema soldier haka  bayan sun isa airport safwaan ya kalli Rafeeq yace"feeq am good to go" suka sauka dukan dan an gama komai har an fara Kiran perssengers tsayawa yyi suyi ban kwana ya kalle su yace"ni fa zan wuce need ur prayers and ladies amaida hankali ga karatu okay"

Tasleem tace "ok bro"

Itakam safa kuka ne yaci karfin ta sae gaba daya suka maida kallon su gareta Rafeeq yace"sis what are u crying 4 sis harda shesheka"

Cikin kuka tace"ya ganin nake shima idan ya tafi ba zae dawo ba irin na abban princess"

Safwaan ya matso kusa da ita yace" ba'a mutuwa sae lokaci yyi kuma insha Allah zan dawo ras kinji sis"

Ta daga kai yace toh"wipe ur tears"  tasa hannu ta goge fuskar ta

Rafeeq yace"wae ka manta tafiya zakayi ne"

Yace"aa bye"

Yawuce suna daga ma juna hannu har suka daina ganin sa suma suka shiga mota sae gd

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top