BABI NA SHA TARA

Assalamu alaikum, da fatan kuna lafiya. Ina godiya da addu'o'inku gareni, alhamdulillah ina samun sauki.

Gobe da jibi bazan samu yi muku update ba, don haka yau ga double update da fatan kuna jin dadin labarin.

And I need your prayers my next release is coming out soon  HALIN GIRMA pray for its success please.

Thanks for the love and support, keep the comments and votes coming, and share share share!

BABI NA GOMA SHA TARA

Tana sallah, ta sauka don ta shirya abun karyawa, ta san sammako Sagir zaiyi zuwa Zaria. Abun haushin da ya dameta ma shine tayi kokarin taga ta tashi da fushin rashin tafiyarta amma ta nemi fushin ta rasa sai ma wani jin dadi da takeyi idan ta tuna duniyar da Sagir kan iya kaita a duk sanda ya so. Tana gamawa ta koma dakinta ta sha wanka ta ci kwalliyarta kaman ba ita bace jiya ta ci kuka. Tana saka dankunne ne ya shigo dakin ya tsaya daidai kanta ya rungumota ta baya. 'yar cikin danyar shaddace mai ruwan madara a jikinsa da alama bai sa garen bane, sai kamshin sa na musamman dake tashi a jikinsa. "Yau baza a tayani karyawa bane?"

"Yanzu daman zan sauko, kayi hakuri."

"Fushi ya kare kenan." Duk da ba sosai take jin haushin sa ba sai ta sadda kai kasa tace "Wane ni yin fushi da kai Uncle Sagir, tunda har kace ai shike nan magana ta wuce. Duk yanda na so tafiyar nan bai kai son ganin na bi umarnin ka ba."

Ya dubeta cikin so wannan yarinyar akwai iya kalami "Tunda kince haka, na baki umurnin kema ki shirya sai mu tafi tare"

Da sauri ta juyo ta fuskance shi idanunta suna bayyana farin cikin da ta tsinci kanta "Da gaske?"

"Eh, amma idan kika dade wurin shiryawa kuma na tafi na barki"

Da sauri tace "Ai ma a shirye nake, mayafi kawai zan dauka da jakata." cikin murna ta makale masa wuya.

"Idan baki sakeni ba daga ni har ke bazamu tsira wurin Aadil da Sameeha ba don zamu rasa daurin auren." Da sauri ta sake shi ta rufe fuskarta cikin jin kunya. Ya mike tare da lakace hancinta ya bar dakin. Kafin kace meye ta shirya ta fito fes da ita cikin wani lace mai launin koren ganye da aka masa ado da ruwan hodar da ta turu (Fuchsia pink), ta fito da lafaya da ta shiga dashi sosai ta nada.

Ba abun da zata cewa Aisha domin kuwa ita ta koya mata wannan shigen. Ita kanta ta yaba da kwalliyar tata a madubi. Ta nemi takalman da basu fiye tsawo sosai ba ta saka, jakarta kuma serviette ta jefa da wani setin kayan kwalliya na kamfanin l'oreal, lip balm, turarenta na channel, sai wayarta da chewing gum mai kamshi.

Tun daga kan matakala tana saukowa a hankali Sagir ya bita da kallo yana mamakin yanda a da yake mata kallon karamar yarinya ya gagara kallon macen da ke gaban shi, yanzu ko zuciyarsa har wani alfahari takeyi da samun mace kamar Aneesa. Suna karyawa rabin hankalin Sagir na kanta, ta kula da hakan ne yasa ta kara yauki tana cin abincin kaman bazata ci ba can tace ita ta gama.

"Haka zaki na zama da yunwa? kin san jiya ma ba wani abun kirki kika ci ba, sannan yanzu zaki kama hanya amma ba za ki sa abu a cikin ki ba?"

"Na koshi, bana son zuciyata tayi ta tashi ne a mota shi yasa."

"To shi kenan, amma muna isa ki nemi wani abu ki sa a cikin ki"

Ta amsa mishi a sanyaye. Bayan ya kammala ne yace wa Malam Hassan ya fito da mota, "Sun dauki abincin su ai?" Sagir ya tambayi Aneesa

"Eh tun da na gama na kira Musa ya dauka musu."

Sagir ya jinjina mata, kullum yana tausayin yanda take aiki cikin gidan nan ya kissima maganar a ransa yana gani zai yi magana da Hajiya ko za a samu wadanda zasu rinka taimaka mata da aiki don yanzu ga wahalhalun ciki ga karatu abubuwan zasu mata yawa.

Suna tafe a mota taji Sagir yana waya da angon, wai su Uncle Aadil ba dama yau murna ba acewa komai. Suna gamawa tace "Na san Uncle Aadil ji yakeyi kamar sha daya bazatayi ba a daura auren. Tun shekaranjiya zumudi waya kan waya, har Sameeha ta daina dauka"

"yanzun ma cewa yakeyi yaya har yanzu bamu taso ba? kin san mutum idan ya hadu da abun da yake so to fa ba a cewa komai." Ta dubeshi tayi murmushi.

Sun dau hanyar Kaduna radio ke ta aiki a motar, Sagir ya rage muryar shi yace "shi wannan ba a sa shi a zauna a gida ne sai idan za a fita?"

Ya sa yatsu biyu yana murza lafayyar jikinta. Aneesa tayi dariya tace "Ba a sawa, ai zai takura mutum."

"Gashi kuwa ya miki kyau." Ya fada yana kallon cikin idanunta, da sauri ta boye fuskarta a cikin garenshi.

A hankali ya rada mata "Malam Hassan yana ganinki ta madubi" ba shiri ya sa ta matsa gefe yana dariyarta. Cikin nishadi suka isa, zuwansu kofar gidan Daddy har an dan fara taruwa, don haka ba tare da sun sauka daga mota ba, Sagir ya jira malam Hassan ya fita sannan ya dauki bandir din dari biyar-biyar yace "Ga tukwuicin kwalliyar yau, duk da dai biki za a tafi a ka yi ta."

Aneesa ta yi wannan murmushin da tasan Sagir yafi so tace "Duk da biki zanje, na san da Uncle Sagir dina a gefena shi yasa nayi. Na gode, Allah ya kara budi ya dada rufa asiri, ya kuma biya maka dukkan bukatunka na alkhairi." Wannan maganar da ta fada masa sai da ya janyo mata samun rabonta, riko habarta yayi ya bata kwakkwayar tukuici a baki, sannan ya sake ta. Aneesa ta juya taga ko da me ganin su amma ganin duhun glass din motar yasa ta sauke ajiyar zuciya. Ta rike mabudin motar ne yace mata "ki kula da kanki fa, sannan don Allah kina shiga ki nemi abu ki ci."

Ta fita daga motar zuciyarta a cike fal da farin ciki, dakin mummy ta fara zuwa ta gaisheta. Mummy ta amsa ba yabo ba fallasa bare yau tana farin ciki zata aurar da diya. Ta bi Aneesa da kallo ganin yanda ta kara wani haske da sheki, ga shiga ta alfarma nan a tare da ita ko ba komai ta san ta samu kwanciyar hankali. Haka take fata Sameeha ma ta zauna lafiya da mijinta.

Tana shiga dakin amaren su Sameeha da Aisha suka fara mata tsiya, "kinga manya masu tafiya cikin class, ba a tahowa da yaku bayi sai an jira oga ya tako baya"

Aneesa tace "sai kuji dashi ai, Sameeha ke kiji da fargaban barin gida kina biyewa wadannan."

"Zuciyata fal da farin ciki wani fargaba ya saura?"

"Za ma ki gane kuren ki ai, yanda ya bi ya matsu yaga an taru an shafa an watse sai kin shiga hannu zaki gane shayi ruwa ne"

Aisha ta sa dariya sannan tace "Anty Aneesa yaya banga an shigo da jakarki ba. Ko ke bazaki wuce Jos din bane"

Aneesa ta gyara zama tace "hmmm ke dai bari abun dogon labari ne. Bari kiga na sa maasa a ciki na ko zanji daidai, har wani jiri nakeji"

"uhm-uhm wannan jiri jirin dai kam sai a hankali"

Aneesa tayi fari da idanu tace "fulakon abinci nayi nazo ban koshi ba gashi yanzu yunwa na tambayata ki rike fassarar ki"

Sameeha tace "Aisha ki rabu da ita idan tayi tsami zamu ji."

Da misalin karfe sha daya da minti goma aka daura auren Sameeha Mahmoud da Aadil Yahaya. Farin ciki ya rufe duk wanda ya halarci taron bare wadanda akayi taron don su. Ana gama daurin aure angwaye suka wuce inda aka tanada domin yin reception nasu. yayin da a cikin gida kuwa sai shirye-shirye akeyi na tafiyar amarya da masu kaita Jos don dama kususu kam da su aka daura aure. Kasancewar iyayen Aadil a can suke za a wuce da amarya can a karasa biki kafin nan kowa ya watse, yawanci jama'a daga Zaria kowa zai koma gidansa mutane kalilan aka ware wadanda zasu raka amarya Jos din.

Bayan Azahar ne Sagir ya kira Aneesa yace ta same shi a falon Daddy. Sai da ta kara gyara fuskarta ta fesa turare mai sanyin kamshi sannan ta tafi falon. Da shi da angon ta samu a zaune "Wai yau Uncle Aadil buri dai ya cika, ina fatan dai baza a sake cewa 'yar uwata bata da natsuwa ba?"

Aadil ya sa dariya yace "ke kuma zamuyi haka dake? Ai wancan tsohon zance ne. kin ga yanzu kin kara samun matsayi daga kanwa kin koma babbar yaya."

"A to gwamma mu sani ne ai, Allah ya bada zaman lafiya ya kawo zuri'a dayyiba."

Aadil ya amsa da Ameen. Sagir ya dubeta yace "kinci abincin kuwa?"

Nan da nan ta kara kasa da murya cikin wani salo tace "eh naci."

Sagir ya kula da hakan da tayi sai dai sunyi rashin sa'a ba su kadai suka gane hakan ba, Aadil yace "Bari naje na sallami su Buhari suna waje."

"To ba matsala"

Aadil na fita Sagir yace "Yaya to zamu iya tafiya ko?"

"Sun kusa tafiya ko zamu dan jira mu ga tafiyar su?"

"To shi kenan, idan sun tafi sai ki sameni a mota. Baki dai sake hararwan ba ko?"

Kai ta gyada masa,"Dazu Malam Hasan ya shigo da wata jaka yace a bawa Sameeha, tana mika godiyarta, Allah ya saka da alheri"

Sagir yace "Ameen, ba komai" Ta mike zata fita ne dai-dai lokacin Aadil ya shigo yace idan ta shiga tayi musu magana su fito.

"Kai Uncle Aadil, za dai akai maka matar" Nan suka sa dariya ta koma cikin gida.

Biki dai anyi shi lafiya baki kuma kowa ya koma gida lafiya an bar ango da amarya da halayensu.

Suna komawa kuwa ranar litinin ta ci gaba da zuwa makaranta, Hajiya ta sama musu wata mata da zata na tayata ayyuka, a hankali Aneesa ta gwada mata komai.

Sau da yawa idan ta dawo daga makaranta ma zata samu Iyatu ta gama ayyuka. A ta bayan kicin dama akwai dakuna, daya daga cikin dakunan Iyatu take amfani dasu. Yayinda masu gadi da su Malam Hassan suke can Boy's quaters

Aneesa ta gama rajistar dukkan jarrabawan da zata zana saura watanni uku a fara jarrabawa, don haka ba wasa karatu sosai takeyi. Amma da zaran Sagir na gida to zata tattara komai ta ajiye a gefe domin lokacinsa ne. Hankalinsu ya kwanta da juna kuma tunda take bata taba dagowa Sagir maganar Ummi ba, haka shima bai tambayeta ba duk da yasan ta samu labarin.

********

Ranar asabar da safe ne Khazeena ta kirata a waya hankalinta a tashe tace "Aneesa ke kam ga Sameeha a gida sai kuka takeyi babu yanda ba ayi da ita ba ta fadi me ya sameta taki magana. Yanzu dai Daddy yace ya nemi wayar uncle Aadil inaga yana kan hanya ban san me ya faru ba. Ki kirata ki gwada tambayarta ko zata fada miki"

Aneesa nan take taji zufa ya feso mata hankalinta ya tashi, me zai faru da har Sameeha zata koma gida wata biyu da aure? Kai wannan babbar matsalace don haka da sauri ta shiga dakin karatun Sagir ta same shi.

"lafiya dai Aneesa? yaya na ganki haka?"

Cikin tashin hankali ta fada masa abun da yake faruwa "Aadil ya taba fada maka suna da wata matsala ne?"

Sagir yayi shiru yana tunani, "Babu, ki kwantar da hankalinki koma meye ne a tsanake za a warware shi."

Aneesa dai hankalinta yafi bata suje gida suji me ake ciki amma Sagir yace tabari sai abu ya lafa tukun na.

Suna zaune a falon Sagir da yamma sai sukaji buga kofa, Aneesa ta zabura daga cinyar Sagir inda tayi wa kanta matashi, ta nemi mayafinta sannan ta je ta bude kofar. Mummy ta gani a tsaye a wurin. Jikin Aneesa dai ya bata ba kalau ba.

"Mummy sannu da..."

"Rufe min baki munafukar banza munafukar wofi, ai ni daman nasan za ayi haka, ki hada jini da Halima ki zama baki da sharri?"

Kan Aneesa ya daure me ya kawo wannan maganar kuma?

"Mummy ki shigo ciki muyi magana..."

Sagir yana jiyo hayaniya hakan yasa ya mike ya fito bakin kofa ganin Hajiya Juwairiyya abun ya bashi mamaki kwarai.

"Ni me zan shigo nayi a gidanki? kinji dadi kin haddasa min fitina da tashin hankali a gida hankalinki ya kwanta, kina tunanin zaki tauna taura biyu ki share ko? To ina son ki san kinyi kadan."

"Hajiya me yake faruwa ne? kiyi hakuri ki shigo ciki ayi magana a tsanake ai hakan bai dace ba."

"Ni zaka fadawa abun da ya dace da wanda bai dace ba? Ai wacce ya kamata ka fadawa wannan tana karkashin inuwarka kuma ta dade tana damfararka amma son da kake mata ya rufe maka idanu."

Ran Sagir ya fara baci, wani irin abu ne mata zaki baro gidanki kizo kina tayar masa da hankalin iyali sannan ga ma'aikata suna kallo.

Da kyar ya samu ya lallaba Mummy ta shigo karamin falo ta zauna.

"Hajiya, kiyi hakuri daga bisa dukkan alamu an bata miki rai, amma ina son na san wai me yake faruwa ne?"

Aneesa na gefe banda hawaye ba abun da takeyi.

"Abun da yake faruwa shine matarka tana nema ta kashewa 'yata aure"

Maganar ta daurewa Sagir kai ba shi kadai ba harda Aneesa, "Ban gane ba. Wani abu Aneesa ta fadawa Sameeha?"

"Baza ka gane ba, Abokin ka dai amininka da ka rike a matsayin dan uwa soyayya yakeyi da matar ka"

Sagir ya zabura cikin fushi jin wannan kalma abakin Mummy amma kuma ya dakatar da kanshi jikin sa na bari yace "Hajiya, kin san ina baki dukkan girman da ya dace na bawa mahaifiyar Aneesa, amma ina son ki san wannan irin zance bai kamaceki ba. Don haka duk abunda Aneeesa ta miki wanda bai miki ba, ke matar babanta ne zaki iya kiranta ki fada mata, amma ki wanke kafa ki zo gidanta ki daura mata irin wannan sharrin a gabana mijinta wannan bazan lamunta ba don haka idan bazaki damu ba don Allah ki koma gida."

"Da kyau, ai ba haka banza ba. Zasu barka haka ne? yau ni kace na fita na bar maka gida, zan fita amma ina son ka bincika wannan maganar da kyau, domin kuwa 'yata da idanunta ta ga kwakkwarar shaida kan cewa lallai mijinta yana son 'yar uwarta kuma matar abokinsa"

Aneesa kam tsabar girman wannan rikici ta kasa kwatanto tashin hankalin da ta tsinci kanta. Kuka kawai takeyi jikinta na tsuma. Mummy na fita Sagir ya ja kofa ya rufe ya dawo ya samu Aneesa. "Ki daina kukannan haka,"

"Wallahi my dear ban san me yasa mummy wannan maganar ba, ban san me kuma take magana a kai ba, kai shaida ne tun da nake ban taba son kowa ba sai kai. yaya ma za ayi da aurena na so wani da namiji bayan mijina?"

Tana kuka tsakaninta da Allah yayinda take mamakin irin wannan fitina da Mummy tazo dashi. Sagir ya rungumo Aneesa jikinsa yana rarrashinta "Ya isa haka, na san an samu misunderstanding ne amma koma meye ne zan warware shi. kiyi hakuri"

Cikin kuka ta daga masa kai, to amma me zai sa Sameeha tayi wannan tunanin har tayi yakinin cewa tana da kwakkwara shaidar da zai nuna haka? Bayan hakan ma ta bar gidan mijinta da kwatakwata watan su biyu da aure? dole akwai wani abu mai daure kai a wannan al'amari.

Sagir yana tabbatar da hankalin Aneesa ya kwanta ya ce "Ni zan fita, zaki zauna a nan ko na kaiki gun Hajiya?"

"ba komai sai ka dawo."

Bayan Daddy ya nemi ganin Aadil ne domin jin musabbabin rikicin daga wurinsa sai ya kira Sameeha, Anty Fatima da Mummy a falon shi yace "Ke sameeha nayi magana da mijinki, kuma ya shaida min duk abun da kika fada. Amma kuma ya min wani bayani mai gamsarwa, don haka ina so ki saurareshi ku fahimci juna."

Mummy tace "meye abun fahimtar juna, yarinya taje ayi ta cutar ta. Tunda ya fito yace baya son 'ya ta shikenan ni ina son ta"

"Juwairiyya idan rai ya baci ai ba aso hankali ya gushe, don haka nake son ki kwantar da hankalinki"

Anty Fatima tace "hakane"

Mummy ta banka mata harara ita bata ga meye wannan takeyi a falon nan ba, abu bai shafeta bama sai ta sa kanta duk kuma Daddy ne ya daure mata gindi.

"Abun da nake so dake Sameeha ki saurare shi ya miki bayanin komai. Anjima nake son ki shirya ki koma dakinki."

Sameeha ta dago ta dubi Daddy "Allah Daddy bazan iya zaman gidan ba."

"Wani irin maganace haka, ba za ki iya zaman gidan ba gidan wa zaki zauna? ko an gaya miki haka ake zaman aure, daga kin samu matsala da mijinki sai fuuu ki tafi gidan ku?"

"Daddy ai gaskiyarta ce, yaya za a dake ta a hanata kuka?"

Jin haka Daddy yace su tashi shi kam ya gama magana suyi abun da suke so.

Sagir yana fita Aadil ya nema. Suna haduwa yaga yanda abokin sa ya shiga wani irin yanayi.

"wai me yake faruwa ne? Hajiya ta zo gida dazu tana wasu maganganun da ban gane kan su ba, yaya aka yi har haka ya faru ne?"

Aadil yacewa Sagir ya zauna, "Lafiya kalau kawai dai wani dan rashin fahimta aka samu daga wurin Sameeha"

"Ban gane dan rashin fahimta ba bayan yarinya tana gidansu. Ba dai korarta kayi ba ko?"

"A'a sam da kafarta ta tafi"

"Wai me yasa baza ka fada min asalin me ya faru bane? me yasa Hajiya taje tana zagin Aneesa wai zata kashe mata auren 'yarta?"

Aadil yayi shiru ya rasa ta inda zai fara fuskantar aminin shi da wannan bayani mai rikitarwa, wanda ya hana shi bacci na darare masu dimbin yawa. Don haka yace "kar ka damu komai zai wuce, kai dai kawai ka san cewa duk abun da yaje ya dawo ni bazan taba cutar da kai ba ko na maka abu na kaskanci. Ka wuce komai a wurina Sagir, ka daga ni daga babu ka kaini matsayin da nake a yanzu duk abun da nake takama dashi ko 'yan uwana suke takama dashi Allah ya sa ta sanadinka duk na samu hakan don haka kar ka bari wani abu ya shiga tsakanin wannan."

Sagir dai kanshi ya kulle me yasa Aadil zai na irin wannan maganar? Sai dai idan abun da hajiya ta fada... inna lillahi wa inna ilaihirraji'un

"kana nufin duk abun da Hajiya ta fada gaskiya ne?"

Aadil yayi shiru ya rasa amsar da zai bawa Sagir, sai ji kawai yayi hawaye suna gangaro masa ya kau da kai gefe ya goge su kafin ya juyo yace "Duk wannan a baya ya faru kuma ya wuce, sannan kuma ina son na fada maka Aneesa bata san komai ba akan maganar nan..."

Sagir idanun sa a runtse ya mike daga kujerar ya dakatar da Aadil "Tun yaushe kake son matata? kafin auren mu ko sai da na aureta?" Sagir ya matsa kusa da Aadil ya cakwamo wuyar rigar sa yana jijjigawa "Abun da zaka saka min dashi kenan Aadil? Matar da na aura kake so? ka shigo gidana ina nan da bana nan kuyi hira kuyi wasa da dariya ashe kana da wata manufa a tare da kai? Haba Aadil a matsayin dan uwana na dauke ka. Ka bani mamaki ka kuma bani kunya you disgust me!" ya sake shi har sai da Aadil ya tafi tagal-tagal kamar zai fadi.

Sagir ya bude kofa ya fita Aadil ya bi bayanshi yana kiransa amma ran Sagir ya kai makura wajen baci.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top