BABI NA SHA DAYA
Alhamdulillah, i'm feeling better now, so here is a long update.
Thanks for the love n support
keep sharing voting and commenting.
BABI NA GOMA SHA DAYA
Ana gobe za a basu hutu ne Sagir ya dawo gida da albishir wa Aneesa. "Ki shirya zamuyi tafiya, wani aiki ya taso min a kasar Turkey, tunda kunyi hutu ai inaga ba amfanin ki zauna ko?"
Mamaki ne ya hanata cewa komai, wai yau ita Uwanin Inna ce zata kasar waje? Kasar wajen ma tare da Sagir da bayi da lokacin komai?
"Baki ce komai ba, ko bazaki je ba?"
Aneesa ta shiga rudani ta rasa me zata cewa Sagir "A'a ba haka bane, kawai dai..."
"Kawai dai baza ki iya bin umurnin mijinki ba?"
Ita tunaninta ya shallake nan ya tafi wata duniya daban da take matukar tsoro, tabbas idan wannan tsoro ya karasa shigarta ba tantama ta san zata samu babbar matsala.
"Zan iya, kuma a shirye nake"
"Gobe bayan kin dawo makaranta zamuje a miki intabiyu na visa, tunda na karbi fasfo (passport) dinki wurin Daddy."
To kawai ta bishi da shi, ita dai ba daga nan take ba.
Bayan komai ya kammala ne cikin sati biyu suka hada jakkunan su ya kaita tayi wa Daddy sallama, sannan sukayi wa su Hajiya ma sallama.
Dawowarsu gida ne tace "Uncle Sagir, sai dai su Inna basu san da tafiyar tamu ba"
Ya dubeta da kyau sannan yace "Ki kirasu a waya mana kuyi sallama, muna dawowa sai na kaiki in sha Allah"
Ranta ba haka ya so ba, amma ba yanda ta iya ta amince ganin ba walwala a tare da ita yace "ko kin fi so ki basu labarin Istanbul a waya? Kinga idan kinje sai ki nuna musu har hotunan ki a can"
Nan dadi ya kamata, ta masa godiya. Tana cikin karasa shirin akwatintane na trolley ya shigo dakin nata, yanzu ta rage jin tsoro idan ta ji shigowarshi don haka da wuri ta tambaya ko yana son wani abu ne?
"A'a, ci gaba da shirin ki."
kasancewr kwana biyar yace zasuyi yasa ta dauki kaya kala shida saboda sha'anin tafiya, da kayan bacci kala uku sai kayan ciki da ta diba, comb da brush da dan abun da ba a rasa ba"
"Ki dau kaya masu nauyi don wannan lokacin a wurin su ana dan taba sanyi" Yana kallon yanda take nade komai take jera shi kaman wata mai aikin kirkire (artist).
Baya gajiya da kallonta, duk da tsoronsa na sake barin zuciyarsa ta wahaltu yana ganin ya fara rasa ragamar yin hakan dangane da Aneesa shin kuwa zata iya samun wuri ta zauna? Sai yake jin tamkar ya gama wancan jinyar sai yana samun wani karfin zuciya da nishadi a tare da Aneesa. Fatan shi daya Allah ya sa kar ya sake kuskure.
Malam Hassan ne ya kaisu filin jirgi, har suka shiga jirgi Uncle Sagir ne ke rike da akwatinta ya bar mata 'yar jakar hannun da take rike da ita. A hankali ta ke kula da duk inda suka tsaya me akeyi a wurin, don wannan ne karo na farko da zata shiga jirgi koma da tazo filin jirgi. Maimakon taga suna shiga inda mutane suke duruwa, sai taga sun haura ta sama inda daddaikun mutane ke shiga wurin. Nan Aneesa taga wata duniya a cikin jirgi. Tana kankame da jakar hannunta sai waige-waige takeyi cikin dabara tana kare wa komai kallo, kaman daga sama taji uncle Sagir yace mata . "Kinyi shiru da yawa me kike tunani?"
Sunkuyawa tayi cikin jin kunya "babu, kawai..."
"Kar kiji tsoro ba komai, ga wannan idan jirgin zai tashi ki tauna ba abunda zakiji" ya mika mata buttermint a hannunta, garin yin hakan hannunshi ya taba cikin tafin hannunta mai laushi. Nan take taji tamkar wacce akayiwa shokin. Sagir kuwa yana lura da canjin da ya gani a tare da ita, ya yi murmushi ya mayar da hannun shi ya zauna, har aka fara sanarwar daura damara. Ganin kar ya kara matsawa kusa a kuma ta dazu sai yace "ki duba" ya gwada mata yanda zatayi da nashi damarar kujerar. Da aka zo tashi ne ta damki kujerarta ta tauna mintin bakinta, amma duk da haka sai da taji a cikin ta.
Filin jirgin Murtala Muhammed dake Legas suka fara zuwa inda zasu shiga jirgin da zai wuce kai tsaye dasu zuwa Istanbul, a wannan filin jirgin kam taga sun shiga bangaren da yafi girma fiye da wanda suka baro a Abuja, Sagir ya mata bayani ta wannan banagaren ake jigila tsakanin kasashe (international) wanda suka shiga kuwa a can Abuja na tsakanin garurwan gida ne Nijeriya (local flights). Sun shiga jirgin Turkish airlines inda zai dauke su ba tsayawa har babban birnin Istanbul.
Aneesa dai ba abun da ya fi damunta irin yanda kyawawan mata masu sintiri cikin jirgin nan suke ta kai kawo a kansu, a zuba wancan a kawo wannan, tana jin bacci amma bata son ta dauke idonta kan Sagir, don taga har wani murmushi yake musu tukun musamman wata da ta faye zuwa ta gurinsu, ta tambaya ko me Uncle Sagir yake so shi kuma ya juyo yace "Aneesa, a kawo miki tea?"
A hankali ta girgiza kanta, don bata son ta faye dura ruwa a cikinta, gudun kar taji fitsari bata san yaya zatayi ba, tunda bazata iya ce masa tana jin fitsari ba don haka ta kame bakinta.
Duk maitarta na ganin kartayi bacci sai da ta runtsa saboda jiya bata samu isasshen bacci ba.
A hankali taji muryar da tayi sanarwa dazu tana ce musu sun kusa iso (Istanbul Ataturk Aiport), a hankali ta bude idanunta taga kanta da rabin kafadanta gaba daya a jikin uncle Sagir yake, da sauri ta nemi dagawa amma sai ta samu ya mata kawanya da hannayensa karfafa. Ganin ta motsa ne yasa a hankali ya cire hannunsa daga bayanta suka hada ido, ya gyara zama ita kuwa ta gyara mayafinta.
"kayi hakuri, nayi bacci ne ban san..."
Lumshe idanunsa yayi yace "ci gaba da baccinki saura minti ashirin a isa." nan ta duba gefenta window ne taga abun mamaki gari kaman a mafarki ko ina wuta ne dau a kasansu. "a'a zan yi kallo"
Wajen awowinsu shida a jirgi nan take mutumin nan ya sake sanarwa akan sun iso masaukinsu, zasu fara sauka kowa ya daura damararsa. Ai duk da damarar da jirgi ya sunkumesu yayi kasa dasu Aneesa ba shiri ta cafko hannun Sagir, idanu rufe har saida suka taba kasa aka tsaya sannan ta kula da irin wawan rikon da tayi masa, da Sauri ta sake shi. Ya dubeta yace "Aneesa mai tsoron jirgi" nan da nan ta rufe fuskarta ai yau kam ta saya wa kanta abun zolaya.
Kasancewar ba su da wani kaya sosai, sun sauka da kayayyakinsu basu dade ba Sagir yayi waya, nan take suna fitowa suka samu motar otel tana jiran ta daukesu, kasancewar ya bukaci hakan. Cikin minti arba'in sun isa masaukin su, Aneesa kuwa kallo takeyi tun daga airport har suka shiga mota zuwa isarsu masaukinsu inda taga an rubuta Hilton Istanbul, sannan ta sararawa kallon titi. Da ikon Allah, wani shudin kati (blue card) kawai taga ya mika musu ba tare da ya biya kudi ba, ya bada wani shaida na takarda da (password), suna shigarwa taji sunce "sannu da zuwa Mr. Daggash muna maraba da kai a otel din mu muna kuma maka fatan zaman jin dadi." Nan da nan taga an hau hidimarsu ana karramasu, yanzu a wannan babbar kasar ma Sagir wani babba ne?
Nan dai taga wani mutumi mai sanye da inifom yazo ya kwashi jakkunan su. Aneesa dai duk inda Sagir ya jefa kafa ya daga nan take saka nata, kyaun garin ya wuce tunaninta kaf. otel din ma maza da mata sai kai komo sukeyi, sai da suka shiga kororon (corridor) da zai dangana su da dakin da aka basu ne tukun ta ga jama'a sun ragu.
"Me kikace Aneesa? Ko dai da na barki a Abuja?" Sagir ya fada cikin zolaya. Da ta gane wasa yakeyi sai tayi murmushi, don ta gaji baza ta iya dariyar ma mai karfi ba, dadin dadawa tana jira taga yau yanda za a kwashe, don dai tun a falon da suka baro a can kasa (reception), ta kula da makullin kati na daki guda a ka bashi amma tana zaton ko zai kaita ne ya koma ya karbi nashi don haka sai bata damu ba, ganin mutumin nan da ya kwaso musu kaya ya ajiye duka jakukkunan su a dakin sai ta fara tsinkewa da al'amarin "yau akeyin ta yaya zan fara kwana a daki daya da uncle Sagir?"
Sagir ya kunna mata ruwa yace "ki shiga ciki a toilet akwai ruwa ki watsa kiyi alwala kafin nan zan sauka na karbo wasu lambobi a kasa"
Ya fita ne saboda ya san bazata sake ba idan yana dakin. Sagir na fita ta karewa dakin kallo an kawata shi iya kawatawa gadone lafiyayye a bangare guda yayinda aka ajiye kujeru biyu kusa da wani makeken windon da ya bude zuwa waje, can ma wani gurin shakatawar ne. Bayan ta gama kallon dakin ne ta shiga bandakin tayi wanka tayi brush sannan tayi alwala, nan ne taji dadin jikinta, tana fitowa mai kawai ta shafa ta burma kayan baccinta ta fesa turare sannan ta maka hijabi, sai dai bata san ina ne alqiblar ba don haka ta samu bakin gado ta zauna tana jiran dawowar Uncle Sagir.
Can sai gashi ya shigo, ganinta da yayi a zaune yace "sorry, na dade ko? ga alqibla nan" ya nuna mata hade da bude jakarsa ya fito mata da 'yar sallayar da sai da ya ware ta sannan taga girmanta. sai da ta tada sallah sannan ya shiga. Ta biya sallolinta duka kasaru sai magriba ne ta yi shi cikakke. Tana sallame isha ne Sagir ya fito daga bandakin, kallo daya ta masa ta sunkuyar da kai saboda yanayin da ta ganshi da towel a jikinsa bata sake motsi ba sai da taji yace ta bashi sallayar.
Yau ita kam nata ya sameta a garin mutane, ba irin tunanin da batayi ba har ta gwammace tayi zamanta a Abuja da ta san haka masaukin su zai kasance. Yana idarwa aka buga kofar su, Aneesa taga ya mike ya tafi bakin kofar ganin wannan jallabiyar a jikinsa taga ya yi kyau. Sai kuma tace "ko wa ya san muna nan daga shigowar mu har yayi bako?" bata ida tunaninta ba sai taga ashe Sagir abinci yasa aka shigo musu dashi. Yace idan ta idar ta zo su ci abinci.
"Meeting dina gobe da jibi ne idan Allah ya kaimu, amma idan kina so zan wakilta miki wanda zasu raka ki ganin gari, a cikin hotel din nan ne zamuyi meeting din a dakin taron su, tare da wasu masu zane, (architects)"
Ita wa ta sani a garin nan da zai hadata da su? Sannan yaushe ta iya yaren su? Da wannan tunanin ne tace "a'a ba komai zan zauna kawai idan ka gama taron sai mu fita tare."
"sarkin tsoro kawai" ya fada yana kallon abincinsa.
Aneesa tace "yaya akayi mutumin falon kasan nan ya san sunan ka bayan banji ka fada masa ba?"
Sagir yayi murmushi "Baki ga na mika masa wani kati ba?"
"eh,"
"Sunan shi Hilton hhonors, tun daga Abuja na biya komai, yanda ba zan yi tafiya da kudi mai yawa a hannuna ba, su kuma can suka turo musu sunana, da randa zan iso da kwanakin da zanyi da sauran abubuwa."
"hmm shi yasa naga mutumin yana ta murna da zuwanka wato ya san kai babban bakon su ne kenan"'
Ta bashi dariya yace "ni ba kowa bane, ko ke idan kina da wannan katin zasu kula dake sosai, musamman idan kina yawan sauka a otel din nasu"
Aneesa ta kama baki sannan tace "Tab, wane ni Uwanin Inna"
Sagir yayi dariyar da ya dade bai yi ba "wane ke Uwanin Inna? to ai Aneesan Sagir kam zata iya ko?"
Yana fadan wannan kalmar dukkan su sukayi shiru, Aneesa na mamakin matsayin da Sagir ya bata a zuciyarsa yayin da shi kuma yana mamakin kansa da ya furta wannan kalami, amma ance magana zarar bunu. Don haka ba yanda za ayi ya mayar, jin dakin yayi shiru da yawa, yasa ya mike ya daura farantan a kan tebur din turo kwanuka ya ajiye wa room service a bakin kofa.
Aneesa kam yanda ya tashi a haka ya barta ta gagara motsa koda dan yatsa. "idan kin kammala zaki iya hawa kan gado ki kwanta ni zan kwanta nan kan kujera."
Aneesa ta dubi kujerar ta dubi tsawon Sagir tasan ko idan ya kwana a kai da ciwon jiki zai tashi gashi suna da taro gobe, don haka tace "Ba zaka takura ba? ga nan gado a dakin?"
Dubanta yayi cikin shakku amma da ya ga bata damu ba sai ya rage wutan ya shiga kurkure baki ya dawo ya samu tana kwance a kasa ta sa pillow daya, har yanzu dai da wannan hijabin sallar tata.
"Ban gane kin kwanta a kasa ba?"
Aneesa ta hadiyi wani abu don tsoro sannan tace "kai baka san a kasa nafi yin bacci ba? duk randa na kwanta kan gado sai naji jikina yana min ciwo"
Sagir ya gane manufarta don ya saba ganinta tana kwana kan gado, jin haka sai bai ce mata komai ba, ya hau kan gado ya kashe fitilar dakin. "Amma kin san ko matan limamai ba su bacci da khimar ko?"
Ya bata dariya amma, tana tunanin yanda zata cire ta kwanta da rigar baccin jikinta kawai, da yaga bata motsa ba yasa yayi shiru ya barta. Aneesa tana jin yayi shiru ta zaci yayi bacci ne, ta mike ta cire lufayyar ta dauki abun rufuwa daya ta lullube jikinta, sannan tayi addu'ar bacci.
Lumshe idanunsa yayi yana murmushi, shi zai ga karshen wannan kulafanci da akeyi.
Tsabar gajiya, bata ji tashin Sagir ba sai da ya idar da sallah ya tasheta. Zabura tayi "har Safiya tayi?"
"Eh, kin san harda canjin lokaci zai sa lissafin lokacin ya koma baya"
Mikewa tayi ta manta da ma wani wasan buya da takeyi ta wuce bandakin, sai da ta shiga ta ganta a madubi tukun ta tuna. haka ta makale a toilet. Sagir yajita shiru ne yasa yace "Aneesa lafiya?"
"Eh"
"Naji ki shiru ne lokacin sallah fa yana fita"
Ta rasa me zatayi can sai dabara ta fado mata tace "Don Allah dan miko min khimar dina uncle Sagir" ya san abun da ya boye ta kenan, yana dariyarta a ransa ya mika mata khimar din. Tana fitowa yace "in dai a haka zamuyi kwana biyar din ashe kina da jan aiki" Ai shikenan abun da take jira kenan tsoro ya karasa bunne ta. Da kyar ta tattaro natsuwar ta tayi sallah, ta samu yana faman aikin sa na komfuta. Bai jira ya karya ba ya shirya cikin wasu 3-pieces suit mai ruwan toka yace mata "nayi magana karfe goma za a kawo abincin ki, ki leka tukun ki ga waye ne ki kuma tambaya, idan sun baki kika rufe kofa, kar ki budewa kowa sai kinji muryata."
A sanyaye ta amsa, don ita ya kara tsorata ta da kyar ta tambaya "Suma a nan ana satan mutane?"
Ya mata kallon kasake "ko zaki gwada ki gani? Ana fada miki abun da zakiyi kina tambaya ko ana satan mutane, ina ne babu ta'addanci a duniya?" wannan Sagir din dai tana da matasala dashi har gwamma Sagir din jiya.
Haka sukayi kwanaki biyu kullum da safe idan ya shirya sai da yamma yake dawowa, kafin ya dawo kuwa akwai kofa ta cikin dakin su da yake hango waje anyi wurin zama, nan Aneesa take zama ta sha kallon ci gaban wannan babban birni, ga furanni masu sanyin kallo a cikin korayen lambuna, mutane kowa na sabgar gabanshi. Idan ta gaji da kallon waje ta dawo daki ta sha kallo a tv, duk da dai ba son kallon takeyi ba. Yana dawowa ya dauketa su fita gari. Aneesa dai ta bawa ido abinci, randa zasu fara fita ne ta gama shirin ta tsab, sai Sagir ya dubeta sama da kasa yace "Wannan wani irin kauyanci ne haka?"
Nan da nan idanun Aneesa sukayi narai narai "Yaya zaki kama ki bunka wani hijabi kamar wa'azi zaki je?"
Ranta ya sosu amma sai ta danne tace "Uncle Sagir ni haka na saba shigata, suma baka ga suna saka nasu irin kayan ba?"
"To kema ba sai ki sa irin nasu ba?"
"Idan sun zo kasar mu irin nawa suke sawa ne?"
Jin haka Sagir yayi shiru, domin duk da kasancewarta mai karancin shekaru tunaninta mai zurfi ne, yana son mace mai tunani (he likes smart women). Haka ya hakura suka fita, idan ya juya ya ganta kamar zatayi swimming a cikin hijabin don rashin kaurin ta sai yayi dariya.
Da suka fita ya kaita masallacin Sultan Ahmet, wanda aka fi sani da shudiyar masallaci (Blue mosque) saboda launin adon da akayi wa masallacin, musulmai da wanda ba musulmai ba duk ana bari su shiga ziyara sai dai an fi zuwa lokacin da ba na yin sallah ba saboda cunkoson jama'a. Abun da ya bata mamaki shine yanda taga wasu mata sun zo da wanduna kai ba dankwali amma taga da suka zo shiga ma'aikatn wannan masallacin sun basu dogin gyaluluwa suka rufe kansu da wuyansu sannan suka shiga. Bayan sun fita ne ta ke fadawa Uncle Sagir abun mamakin da ta gani shine ya mata bayani har wanda ba musulmai ba ana bari suyi ziyara a nan.
Sunyi hotuna awurin kafin su wuce wani kayataccen wurin cin abinci. An dai ajiye abincin Aneesa kam sai kallon nata takeyi ta gagara tabawa, don wani abune kanana a cikin koko bata sanshi ba, amma taga Sagir ya daga ya kai baki ya cinye abun ya ajiye kokon. Ganin bata taba nata bane yasa Sagir yace "Akwai dadi dai, ki ci mana"
Kai ta girgiza masa, tana ganin abu baki baki wani dadi zai yi? Nan yace "Bude bakinki"
Ta juya tana duba gefensu da bayan su yaya zata bude bakinta kowa yana ganinta? Sai da ya sake nanatawa sannan tayi yanda yace nan ya daga kokon ya sa mata a baki yace "Ki hadiye," Abun mamaki sai taji abun ya wuce sulub, gashi yana da dandanon gishiri gishiri. Tissue ya dauka ya goge mata gefen bakin ta, hakan yasa Aneesa tayi saurin sunkuyar da kai cikin jin kunya, daga bisani tana jin dandanon abun da ya bata a bakinta, ashe dai yana da dan dadi sai da yaga ta dau dayan ta ci ne yace mata "Oysters kenan kika ci." Tayi murmushi tana nanata sunan abun a bakinta, nan dai aka kawo musu green Salad aka kawo musu wani abincin kuma na Turkawa, har dai tace ta koshi.
Daga nan hotel suka koma, sai washegari ne yace "akwai wurin da nake so ki gani, amma kuma a cikin ruwa za a kaimu kina tsoron ruwa?"
Aneesa ta zaro idanu, tana tunani yau har ina za a kaisu sai a ruwa? "A'a bana tsoro, a Kunuwal ina zuwa Rafi."
Sagir murmushi yayi saboda wannan ruwan wane Kunuwal gaba daya bare rafin dake cikinsa. Waya taji yayi sannan yace ta shirya su tafi, wata doguwar riga ta saka mai ruwan daurawa ta nada farin gyale a kanta ta sa fararen takalman da basu da tsawo, a wajen dakin ta samu yana jiranta shi kuma T shirt ce marar nauyi a jikinsa sai wandon chinose da flat takalma. Suna fita wajen otel dinsu sai taga ya nuna mata abun da zasu shiga motar doki ne (luxury coach) ta daga idanu ta dubi Sagir, yayi mata murmushi, nan suka shiga mai musu bayani sai yi yakeyi, sun bi ta Golden Horn, wanda Sagir yace mata wannan shi ya raba garin kashi biyu, bangare daya na cikin Nahiyar Europe daya bangaren kuma yana nahiyar asiya. Abun ya bawa Aneesa mamaki matuka.
Haka suka ci gaba da tafiya lokaci lokaci Aneesa take satan kallon Sagir. An nuna musu wuraren tarihi da dama sannan suka je Bazaar wato kasuwar su ta gargajiya nan ne suka sauka a motar dokin nan, Sagir ya rike hannunta kamar karamar yarinya, sai shiga layi-layi na kasuwar sukeyi. Ba abun da babu, kama daga kayan kamshi, kayan yaji, da na abinci da na sakawa da duk wani abun da mutum zai bukata, domin kuwa makekiyar kasuwace, ita dai duk ta takura da rike mata hannu da Sagir yayi, amma ta kula shi ko a jikinsa. Wannan yasa ta dan saki jiki kadan.
"Yaya sai tafiya mukeyi ban ga kin ce kina son komai ba."
"Ni ba abunda nake so," ta fada daidai lokacin da suka tsaya wurin kayan kwalliya na mata irin su dan kunne da sarka ta gargajiya. Sagir yace "Tunda ba abun da kike so ni ki zo na nuna miki me nake so." Nan yayi cinikin wata sarka mai kyau tana da fararen duwatsu, yana dauka kuwa taga sarkar ta mata kyau don haka ta amince ya saya mata. Daga kasuwa kuma sun shiga dokin su inda ya kaisu bakin ruwa, suna isa wurin da zasu shiga motar ruwan, ta san wannan ruwan azimun ne ba zata hada shi da na Kunuwal ba.
Suna tafiya Sagir na mata bayanin sunan wurare, wasu ta rike wasu kuwa jinsa kawai takeyi, ita dai ta san yau tana ganin kyaun duniya. Suna iso wata gada ce ya nuna mata wani gini "Nan shi ake kira Rumeli fortress," suna wuce kasan gadan kuma yace Kinga wannan, masarautu ne da aka gina su da zallar marble" Aneesa dai ta sha kallo, domin kusan awa uku sukayi ana yawo dasu a gari, har aka mai dasu bakin gaba inda abun hawansu ya maidasu Taksim square, ko da suka koma, hotunan da akayi ta daukanta da U. Sagir tayi ta kallo abunta.
Ana washegari zasu koma ne suka fita sayayya, wani babban mall ya kaita Istanbul Cevahir, a nan suka shiga wani shago yace ta dauki duk abun da take so, sannan idan taga abun da zatayi tsaraba dashi ma ta dauka.
Sun shiga kantuna sunyi biyar. Amma har suka fito Aneesa bata ga Sagir da komai ba sai turare, ita kuwa sai da aka turo kayan da ta saya a keke, bayan sun ajiye kayan a masauki sauka sukayi wajen cin abincin otel din su suka ci abinci sannan suka koma masauki don kimtsa kayansu, don jirgin su da safe zai tashi tun cikin dare zasu tafi filin jirgi.
Tana shirya kayan a babban akwatin da suka saya ne Sagir yace mata "Har kina shirya kayan baki nuna min sayayyar taki ba?"
Murmushi tayi tace "Ni ban sayi komai ba"
ya dubeta ya dubi kayan dake gabanta "kina nufin duk wannan sayayyar baki daukawa kanki komai ba? To na su waye wannan kayan?"
"kaga na sayawa Aisha, Sameeha da su Khazeena, na sayawa Kamaal, da su Hamdiyya, wannan kuma na 'yar kawuna ne wannan na Azhaan. Sai wannan na Abba da Daddy..." haka ta ci gaba da lissafa masa, hatta Musa mai musu shara da su Baba Saratu sun samu tsarabar Turkey amma Aneesa bata sayawa kanta komai ba. Abun ya bashi mamaki, a tunaninshi duk kayan da ta gani sun burgeta ne shi yasa tayi ta daukawa kanta, ashe ita duk jama'a ne a ranta yarinyar tana da kyakkayawar zuciya, zata mori zama da jama'a. Sagir yace "an taba haka mutum yayi tafiya bai sayawa kanshi komai ba?"
"wa yace maka ban sayi komai ba?"
Ta sa hannu a jakarta ta dauka masa kyamarar da sukayi ta daukar hoto tace "Ga babban kyautar da ta fi komai, a kullum na kalli wannan zan tuna zuwata nan garin amma, duk wadannan abubuwan zasu iya kodewa ko su bata ko na kyautar wata rana"
"Hakane kinyi gaskiya."
Suna filin jirgi ne suna jiran a kirasu Sagir ya mike yace "ki jira ni a nan, ina zuwa yanzu kar ki motsa ko ina."
A sanyaye ta amsa masa can sai gashi ya dawo, tana ganinsa tayi wata ajiyar zuciya wato dai duk yanda take jin tsoron Uncle Sagir shine komanta a kasar da bata san kowa ba sai shi, wani dadi taji ya lullubeta da ta ga ya dawo ya zauna a gefenta.
Bayan dawowarsu, Sagir ya ci gaba da al'amuran kasuwancinsa kaman yanda ya saba, Aneesa kuwa randa suka dawo washegari taje gidan Daddy ta bawa kowa tsarabarsa. Kowa yaji dadi yayi godiya, amma mummy yanda kasan kyautan kashi aka kawo mata, don yanzu kam ta daina boye kin Aneesa da takeyi kiri-kiri take kinta. Hatta Zaheeda da bata kula Aneesa sai da tayi murna da kyautar agogon da ta kawo mata mai dan karen kyau. Ko da Sagir ya zo daukanta su tafi Hajiya Juwairiya bata masa godiya ba. Sai da Daddy ya dawo ne suka nuna masa tsarabar ya kira yayi godiyar.
Haka su Aisha duk sunji dadin tsarabar da Aneesa ta kawo musu duk da kuwa zuwa kasashe ba bakon abu bane a wurinsu, domin lokuta da dama acan suka fi yin hutun su, zata bada na Azhaan ne ta wurin Hajiya Sagir yace mata "ki bari cikin karshen mako na sama zamuje Kanon in sha Allah sai ki kai musu da kanki"
Aneesa tayi shiru saboda a tunaninta kafin hutunta ya kare zasu je Kunuwal, watakila ya sake shirin tafiyar ne ko kuma daga Kanon su wuce.
Ranar asabar sai ga Sameeha tazo gidan Aneesa, kwarai tayi mamaki amma kuma dadin ganin 'yar uwarta ne yasa bata jima cikin mamakin ba, bayan sun gaisa ne Sameeha tace "yaushe zaku koma makaranta?"
Aneesa tace "saura sati daya hutun mu ya kare, wani abu ne?"
"A'a kawai daman ina so nazo ne na koyi wasu abubuwa a wurin ki,"
Maganar ta daurewa Aneesa kai, tace "Baba saratu bata nan ne?"
"Ta na nan, kawai zaman gidan ne ya isheni, kullum Daddy kara fita hanyata yakeyi, kuma mummy ta kasa shan kanshi, ban san me zanyi da rayuwata ba, hakan yasa naga ko auren ma nayi ban san yaya zanyi zaman auren ba tunda ban iya komai ba."
Tausayin Sameeha ya kama Aneesa, "addu'a zakiyi tayi a hankali, hankalinsa zai kwanta, ya saurareki har ma ya koma miki kaman da. Kuma batun tunanin da kikayi ki koyi abubuwa wannan shine daidai. Amma kuma kinsan mutum bazai magance matsalarsa ba ta hanyar guje musu. Ki zauna a gida ki koyi komai ki canza shafin rayuwarki, abun da kikayi a baya kuskure ne kuma kin gane kuskurenki. Don haka ni na san idan daddy ya gamsu kin gane laifin ki, da kanshi zai mayar miki da rayuwarki. Idan kuma kina gani kin fi son ki yi ta gujewa rayuwar ki ba laifi sai nayi wa Uncle Sagir magana ki zo mu zauna"
Sameeha ji kawai tayi hawaye suna gangaro mata "Aneesa kiyi hakuri da duk abun da na miki, na nuna miki kaskanci ba sau daya ba, amma na san hakan ba daidai bane kiyi hakuri, sai dai bana tsamman daddy yana sona yanzu, kaman yanda Hamza ya gujeni haka kowa zai gujeni"
Aneesa ta jinjina maganar "kowa ai yana bukatan damar gyara abubuwa, don haka kiyi hakuri komai zai wuce, zan fadawa uncle Sagir ko zai bamu shawarar abunyi"
Sun dan jima har zuwa azahar har ta taya Aneesa aiki kadan sannan ta ce zata koma. Tana fita kuwa sai ga Sagir sun shigo shi da Aadil, ta dawo suka gaisa sannan ta fita.
Ta kawo musu ruwa ne Sagir yace "yau me yake damun kanwar taki naga ta yi sanyi?"
Aneesa tayi murmushi "maganarce dai ta kullum"
Aadil yace "Haba nima zance wannan ba ita bace Sameeha, sai dai naga wannan a natse"
"Uncle Aadil a ido na kake kiran 'yaruwata haka?"
Aadil ya sa dariya ya daga hannayen sa "kiyi hakuri kar na rasa gidan zuwa cin buda baki, kin ga azumi ya kusa zagayowa"
Sagir yace "To laifi ne don ya fadi gaskiya? Nima ban taba ganin ta haka ba sai yau"
Aneesa ta hada rai ta tashi ta bar falon, tana kicin tana jiyo su suna tattauna wata kwangila don haka da ta gama kan tebur ta ajiye musu abincin ta wuce dakinta don ta huta, tana kwance tana tunanin al'amarin Sameeha ne Sagir ya shigo dakin, da hanzari ta nemi dankwalinta zata daura, ya zauna a bakin gadon yace "Aadil ya wuce, meye ne naga kin razana da na shigo?"
Hannu ta sa ta mutsuke idanunta "Nayi nisa ne a tunani shigowar kan ta sa ni firgita"
"hmm tunanin Sameeha? ko tunanina?"
Ta zaro idanuwa "ni kuma me zai kaini tunanin ka, bayan yanzu na barka lafiya a kasa"
"Don ina lafiya sai baza ayi tunani na ba? yau kam na san matsayina." zatayi magana ne Sagir yace "To tunda ba tunani akeyi ba na Sameeha akeyi kenan, me ya faru?"
Nan dai Aneesa ta fada masa abun da ake ciki da yanda sukayi da Sameeha. "naji komai, kuma yanda kika fada mata gaskiya ne, abunyi ki ban kwana uku zan san meye abunyi zan kuma samu Daddy in sha Allah akan maganar"
Cikin fara'a ta rike hannun Sagir tana masa godiya a lokacin ne ta kula da dankwalinta da ke hannunta ashe bata daura ba.
Yana kula da ita don haka ya shafa gashinta yace "Haka kawai kina da gashi mai kyau sai ki k'i nunawa mijinki ya gani kullum kiyi ta maka lufaya kamar wata matar liman"
Idanunta ta runtse tace "Uncle Sagir bana so."
"wai ni yaushe aka yanka min ragon suna uncle ne a gidan nan, tun ina dauka kina kwaikwayar su Khazeena ne har abun ya zarce ya zama a ko ina ma haka ake ce min. so kikeyi wataran a ganmu tare ace wannan kam mijin ma ya mata tsufa da yawa har uncle take ce masa?"
girgiza kai tayi "to ai..."
"To ai meye? daga yau na soke uncle a gidan nan, sai dai wasu su fada amma ke kam Sagir kawai ya isheki."
Yana shirin tashi ne tace "emm Uncle Sag..." kallon da ya mata yasa ta gagara karasa "to ai ni bazan iya fada bane"
"to shikenan ki sa min wani sunan banda uncle, meye maganarki?"
"Daman ina so na tuna maka ne batun tafiya Kunuwal din, sai mun dawo Kano ne zamuje ko kuwa kafin mu tafi?"
"ki dai saurara tukun"
Abin da yace kenan ya fita daga dakin.
Bayan ta kammala ayyukanta ne ta kulle ko ina, da yake Uncle S... oh Sagir ya fita inda yake zuwa kullum da har yau bai fada mata ba, sai tayi wanka ta dauko daya daga cikin english wears dinta, riga da siket ne wanda Khazeena ta rakata suka sassaya a wani plaza, bata cika sa su ba, saboda tafi jin dadin atamfa. Bata sauko kasa ba a falon sama ta zauna ta dauko hotunan su na Turkey tana kallo, tv kuma nata aikin watso labarai, ta dai kunna ne daman don ya taya ta hira. Kamshin turaren sa taji sannan ta gane yana tsaye a kanta ne, tana juyawa sukayi ido hudu.
"Banji shigowarka ba, sannu da dawowa"
"Wataran za asace ki, kin kure muryar t.v sannan kin rike wani aikin a hannu kina ta faman yi."
"Tsoro nakeji shiyasa na kunna don ya tayani hira."
"o, yanzu kam na dawo ki kashe komai sai ki sameni a daki"
Aneesa ta mike tsam ta fara tunanin yau kuma wani laifin tayi ta ga ta kanta. Tunda take bai taba cewa ta shiga dakinsa ba ko aikanta bayayi dakin, idan yana gida kuwa yafi so ya kadaice shi kadai a can don haka bai taba kiranta ba. Cikin fargaba ta maida hotunan dakin ta, ta adana a durowa sannan ta dauki mayafinta ta nufi dakin Sagir.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top