BABI NA SHA BAKWAI

BABI NA GOMA SHA BAKWAI

Amaryar daddy dai ta iso, gangariya da ita. Aunty Fatima mace ce kyakkawa, ga son mutane 'yar jihar Katsina ce ta taba yin aure Allah yayi wa mijin rasuwa amma bata taba haihuwa ba. A nan Abuja Daddy ya ganta gidan wanta wanda abokinsa ne har suka daidaita.

An tafi Malumfashi a can aka dauro auren. Mummy kam a wannan lokacin ta gama amincewa ta rasa wannan fadar da ta taso, don haka ta zuba idanu. Gashi dai an mayar mata da mukamin zuwa dakin maigida tun kafin auren amma kishi da fushi suka hanata lekawa. Da ta tada rikici ne ta dage sai dai Daddy ya ajiye Aunty Fatima a gidan sa na Zaria ba zata zauna gida daya da ita ba.

Daddy kuwa yace "Idan har kina son zama kan 'ya'yanki dole ki bi tsarina, kuma bana son wani tashin hankali a gidannan , duk wacce tace fitina zata haddasa min, to kofa a bude take" hakan yasa ta ja bakinta tayi shiru, fi'ili iri-iri dai tana ganin shi. Amma bata da bakin magana, ita ta kula ma sai lokacin girkin Anty Fatima ya zagayo a karshen mako sai yace mata sun tafi Zaria, ko kuwa wani garin daban, hakan ba karamin tayar mata da hankali yakeyi ba, wai yau itace kishiya zata gwadawa juya miji? Wai rayuwa juyi-juyi don haka ba yanda ta iya. Wani lokaci tana kokawa yarta halin da take ciki "gaba daya na fada miki ya zama kaman wani zararre, wani abun idan yanayi ma kaman wani karamin yaro a dole ya auri mai karancin shekaru 'yar zamani."

"Ato ai ke kika ki shawarata da tun farko ko kafa bata taka cikin gidanki ba, bare ki ga abun takaici."

"Hmmm wai inji mai ciwon hakori, ai ni Yaya Lantana yanzu tsoron yin wani abun nakeyi, na tsorata da Mahmoud, wannan karon muddin ya san da saka hannuna a al'amarin gidan sa to kashina ya bushe. Dadin dadawa nayi a kan Halima, amma kiga ba aje ko ina ba aikin ya warware duk da dai da farko anyi nasara. Na tsorata da wannan lamari. ke dai ku tayani addu'a Allah ya dawo da hankalinshi kaina, don naga alama wannan Fatimar 'yar duniyace da gaske takeyi"

"To shi kenan tunda kince haka"

Suka yi sallama da yaya Lantana ta shiga tunanin wasu dabarun, haka kawai a zo a sameta da miji a kwakwabe shi, bayi da wata katabus sai abunda mata tace masa? oh ni Juwairiyya ashe abun haka yake?

******

Inna dai baki har kunne saboda ranar Uwani tana hanyar zuwa ganin gida, su Amina kuwa an kasa zaune an kasa tsaye, can anjima an leka waje an sake dawowa ciki, duk dai gadin isowar Uwani ake tayi. Wannan tahowar, Malam Hassan ne ya kaisu filin jirgi sai dai maimakon taga sun bi yanda taga sunyi a tafiyar su Turkey, yau wani karamin jirgi taga Sagir ya nufa, ita dai binshi takeyi a baya, masu iniform din kusa da jirgin suna gaisheshi, shima ya gaida su, sannan suka shiga jirgin. Yanayin tsarin cikin jirgin ma ya banbanta da wancan, an shigo musu da kayan su, nan dai taji kaftin din yana bayanin tashi, Aneesa ta dubi Sageer tace masa "yaya har za a tashi banga mutane sun zozzo ba?"

Hannunshi ya saka cikin yatsunta "Mu kadai zamu tafi, shatar jirgin na dauka mana"

"Uncle Sagir gaba daya? Me yasa?" ta fada cikin dafe kirji da zare idanu.

"Saboda ina son ki san matsayin da kike dashi a rayuwata. kuma saboda zan iya"

Nan dai tayi shiru, tun ba da tafara ji yana zagaye tafin hannunta da dan yatsarsa ba. Ba a dauki lokaci ba suka isa filin jirgin jihar Gombe dake Lawanti. Nan suka tarar da wani abokin huldar Sagir yazo tarbar su.

"Na gode, Haruna."

Haruna ya rike hannun Sagir sukayi musabaha "Ah, ba komai yallabai. Ga motar nan, direba zai kai ku duk inda zaku je."

"Zamu wuce tare ai ko? Saboda akwai maganar da nake so mu tattauna"

"To ba damuwa." Haruna ya sallami direban, yace ya je da motarsa zasu hadu a cikin gari.

Ya zo zai zauna a mazaunin direba ne Sagir yace "bari kawai na jamu" ya mikawa Sagir key din sannan ya koma kujerar gefe.

Aneesa dai tana zaune a baya banda daukin ganin Innarta ba abun da takeyi. Tana jin su Sagir suna ta bayanin kasuwancin su. Wani dadi ne yake cike fal a zuciyarta musamman idan ta dubi wannan mutumin da yake magana yana juya kamfanoni da aikace-aikace, da ma'aikata da maqudan kudade wai idan ya juya farat daya, shi nata ne dungurgum mai sonta ne kuma me iya mata komai don ganin farin cikinta ya kuma share mata kwalla. Ita da ba kowan kowa ba amma Allah ya dagata ya kaita wannan matsayin, ba abun da takeyi sai dai ta godewa Allah. kullum kuma addu'a takeyi Allah ya bata ikon kyautata masa ta kuma soshi kwatankwacin yanda yake sonta koma fiye.

Lokaci-lokaci a tsakanin hirar Sagir da Haruna, Sagir yakan kalli madubin motar su hada ido da Aneesa, wani murmushi take masa wanda shi kadai yasan tasirinsa a tare dashi.

Misalin karfe uku suka shiga Kunuwal, sun samu tarba mai kyau. Bayan sun tattauna da Haruna, Sagir ya ajiye shi a Gombene sannan suka wuto. Dakinta na kuruciya ta ajiye kayanta tayi Sallah. Bayan sun gaisa da Inna ne ta koma falo wurin Sagir. "uhmm har wani dadi kikeji irin kin ga Innarki ko? to idan kun gama gaisawa sai ki fito."

Aneesa ta dafe kirji ta marairaice fuska tace "iyaka ganin gidan kenan? ko hira fa bamuyi da ita ba, ban je wurin su Mama ba, sannan kuma banga Falmata ba..."

"to naji shikenan, baki ga danginki ba, kiyi hakuri yau dai ki huta, gobe idan na juyo sai a zagaya dangin dani ko?"

Nan tayi ajiyar zuciya ta sake fuska "wai! har ka tsoratani na zaci da gaske kakeyi komawa zamuyi"

"Idan kince mu koman ma ai zamu iya."

Da sauri tace "Na yafe, ni kam ina nan kai dai ka sauka lafiya"

Sagir ya rike baki "oh haka ma zaki ce ko? ba komai zamu tattara mu koma ai, ni zan wuce yanzu"

"Har kaci abinci?"

"Eh yanzu mukaci da Malam Habu" sai da yazo tafiya Aneesa taji wani iri.

"Allah ya kiyaye hanya, to goben da karfe nawa zaka zo?"

Sagir ya kura mata ido tayi narai-narai da idanunta "Wata zatayi kewata kenan." Da sauri ta rufe idanunta tace "Nifa ba haka bane, kawai ina son na sani ne saboda na shirya da wuri ba kace zamu fita gaishe-gaishe ba?"

"to naji, kaman da yamma yayi ai. Sai ki shirya min beta."

Aneesa tunaninta daya yaya za ayi ta zauna har sai gobe da yamma taga Sagir? "Allah ya kaimu."

Yasa hannu ya janyota barin jikinsa sannan yace "sai da safe." A hankali ta shaki kamshin jikinsa ba tare da tace masa komai ba ta juya cikin gida abinta.

Ranar hira suka raba dare sunayi da Innarta, tana bata labarin karatunta da kuma rayuwar Abuja. Nan ta fito da hotunan da sukayi a Turkey ta nunawa Inna. Ta bata labarin wani zuwan da Sagir yayi da ita Lagos har kamfanin su na can sai da ya kaita ya kaita wurare daban-daban na bude idanu kafin su dawo. Inna kuwa farin ciki ne fal a zuciyarta ganin yau ga Uwaninta ta samu cikakkiyar rayuwa, ta auri mutumin da ya ke darajata ya kuma san mutumcinta.

Sai da Aneesa ta zo kwanciya ne duk tunanin Sagir ya bi ya dameta, ko yayi bacci yanzu? ko me yaci da dare? ko a ina zai kwana? duk dai tambayoyin da suka isheta kenan.

Har ta dan fara bacci taji wayarta na kara ta duba taga maigidan ne, cikin zakuwa ta zauna kan katifarta ta sa wayar a kunne. A tsanake cikin sassanyyar murya tace "Assalamu alaikum"

Sagir ya amsa mata "har kinyi bacci ne? na zaci har yanzu anata hira da Inna"

"Mun yi hirar har mun gama na yau kam, kowa ya shiga. yaya gajiyar ka?"

A hankali Sagir ya rufe idanu ya budesu "akwai gajiya, yau kam idan na kwanta bazan tashi da wuri ba, kashe wayoyina ma zanyi ko zan samu na dan huta"

"ya kamata kam, yaya kayi da abinci?"

"Bayan kin ki ki biyoni ki dafa min." Aneesa tace "sai na bi ka Gombe don kawai na ma girki, bayan gaka da jama'a da wuraren cin abinci?"

"oh kin fi son nayi ta yawon cin abinci ko?"

"Ba haka bane, naga dai yaushe nazo gidan ne ma?"

"Tunda kince haka to ki shirya gobe idan nazo zamu koma."

"Don Allah kayi hakuri, laifin me nayi? nayi kewar gida sosai ba kace zaka barni nayi sati daya ba?"

"Na fasa, ki zauna da shirinki kawai"

"Yau na ga ta kaina don Allah My dear kayi hakuri"

"yanzu kam na tabbatar sai za ayi lallami ake kakaba min my dear din nan, naki wayon. Haka kawai zaki sani kwana ni kadai bayan gaki minti ashirin a kusa dani"

Kunya ya rufe Aneesa tace "naji zan na ce maka My dear kullum, amma don Allah ka barni nayi sati sai na koma, idan kana so ma ka tafi Abuja ka ci gaba da sabgoginka sati nayi sai na taho"

"Na barki ki taho da wa?"

"Ba sai na shiga mota ba."Aneesa ta fada ita kanta tana auna zancen.

"Ke ma da gangan kika fada. Sai da safe kuma ki zauna da shirinki"

Yana fadan haka ya kashe wayar, yau ita kam ta bo'esu yaya zatayi da wannan mutumin daga wasa sai magana ta koma gaske, tsakaninsa da Allah yanzu kwana daya zai barta tayi?

Haka ta hakura da tunani ta kwanta bacci. Da safe tana shiryawa gidan Falmata ta doka sammako, Falmata kuwa murna ne ya cika ta fal. Dama labari ya isota akan aminiyarta ta iso gari. Aneesa ta taya Falmata shirya yaranta sannan suka zauna sai hirar yaushe gamo sukeyi.

"Ni meye labari ne, kinga yanda kikayi bulbul kika canza?"

"kai aminiya ke dai da son zance kikeyi"

"A'a yanzu dai na san Sagir ya bar dawainiya dake an koma ji da juna"

"hmm, Falmata kenan ai al'amarin Uncle Sagir sai shi, wani ji da juna kuma?"

"Ban gane ba?"

Aneesa ta yi ajiyar zuciya tace "ki ga dai tunda akayi bikin mu yanzu kusan shekara kenan sai yanzu nazo ganin gida amma wai sai yace kwana daya zanyi bayan ya sa min ran zan fi haka dadewa"

Mamaki ya kama Falmata "to, kika san ko da akwai abun da ya sa shi canza shawara?"

"Ba wanin nan kawai dai nayi subul da baka na tambayeshi yaya yake kula da kanshi shi kadai. shi kenan wai na shirya yau idan yazo zamu juya, ni ban san wani irin ra'ayi bane dashi. Lokaci daya sai ya juya kaman wani mai juju"

"Ni banga meye abun tada hankali ba anan, tunda shi yaso kizo yanzun kuma har ya kawo ki da kanshi, don yayi ra'ayin ku koma ai bazai kawo sanadin fada ba, a ganina kiyi kawai yanda yace. Idan kika masa gardama gobe kuma kika bukaci zuwa gidan kina ga zai yarda ya bari ki zo?"

Kuma dai Falmata ta fadi gaskiya, don haka Aneesa ta sallamawa ranta shi kenan zata bishi, amma ba haka ranta yaso ba sam.

"To daman ke kam ai Innarki kike son gani kuma kin ganta kun gaisa, sai gidan Mama da sashen su Mairo idan banda nan ki fada min ina kike da shirin zagawa?"

"Tabbas kinyi gaskiya hakan ne kawai, naji shawararki zan bishi mu koma."

"ke kam ban fada miki ba dai Garba ya samu aiki a Gombe."

"kai haba? na muku murna kwarai, kice ana ta shirin kaura kenan. Shi kenan su Aliyu zasu shiga makaratar su a can"

"in sha Allah, hakan dai muke fata, yanzu dai rikicin da ake ciki Innarsa ta dage wai sai dai ya barmu a nan yana zuwa yana komawa, wai yanda baya shayina idan muka tafi sai yanda na yi dashi a can, kin taba jin irin wannan maganar? yau ina ni ina raba shi da mahaifiyarsa?"

"Haka Inna Dadayon ta fada?"

"Shi yasa ma, baki ga na daukantu kan maganar tafiyar ba, ni dai ina ta addu'a Allah ya zabar da abun da yafi alheri."

"Ameen, wannan shine babba, ki bashi shawarar ya bita a hankali har ya samu ya rabu lafiya da ita, kin san sha'anin iyaye. Kar yaga kaman baki damu ba, daga baya yazo yayi dana sanin yin hakan ya daura miki laifi, kuma uwa uba idan tayi fushi dashi to kin ga fa masifa na iya aukuwa, shi yasa a rabu dai lafiya a hankali Allah yasa ta fahimta."

"Hakane, Ameen." ta kawo wa Falmata zani sai kuma yaranta ta kawo musu 'yar kanti masu kyaun gaske. Sai godiya aminiyarta  takeyi

Sai kusan azahar Aneesa ta koma gida, ta taya Innarta aikin abinci, suna cikin aikin ne tace "Inna, daman ina son na fada miki ne yace yau idan yazo muka je gaida su Baba zamu koma"

Inna tayi shiru kadan sannan tace "ba dai Abujan kuke da shirin komawa ba?"

"ban dai sani ba, sai idan ya zo zamuyi magana dashi."

"To Allah ya kawo shi lafiya" Aneesa ta amsa a ranta, daf la'asar ne tayi wanka ta dauro alwala sannan ta zo ta shirya a cikin leshi marar nauyi mai kalan shudi da digodigon baki, ta fito fes da ita sai shanawa takeyi. Inna dai dadi ne fal a zuciyarta ganin Uwanin ta na walwala, hakan yasa ta kara godewa Allah. Wajen karfe hudu aka ce musu Sagir ya iso, Aneesa ta shiga kai masa abinci ta samu sai hira yakeyi da Muhammadu kaninta.

"Ya cika ka da surutu ko?"

Sagir yace "A'a Muhammad fa abokina ne, kuma hira mukeyi ba ruwanki, kinaga har motar katakonsa ya ban kyauta?"

Muhammad ya fita daga falon da gudu.

Aneesa ta dubi Sagir tace "Ina wuni?"

"lafiya kalau, yaya shan gida?"

A tsume ta amsa saboda har yanzu bata huce ba kan maganar tafiyarta. Ya kula da ranta a bace yake don haka yace

"wani abu ne ya faru naga kaman kina makoki?"

Murmushi tayi kadan sannan tace "ba wanda ya mutu, yanzu Uncle Sagir don Allah baza ka bari na kara ko kwana biyu ba?"

"Au daman a kan wannan maganar ce kika wani hada rai? Ai na gama magana ni dai, idan kin shirya ki zo muje gidan Baban mu gaishe su"

"To kaci abinci kafin nan"

Ta tashi cikin sanyin jiki ta dauko khimar dinta sannan tayiwa Inna sallama, akan zasu je su dawo. Suna fitowa taga ya nufi mota, ita kuwa ta fara takawa ganin haka yasa ya girgiza kai ya rufe kofar motar sannan ya bi sawunta. "Baza ki ce min da kafa kike son tafiya ba sai kawai kiyi gaba? ko dan ni ban san gidan ba?"

Tana shiru bata ce masa komai ba, suna tafiya a hankali ba tare da ta kula shi ba har suka isa gidan Baba, sun samesu duka a gida.

"to wai kin jita, wato har gida zaki jawo min shi ki nuna min ko? To naga dai ko haske na bayi dashi bansan me zaki nuna min ba" Duk suka yi dariya, bayan an gaisane Aneesa tace bari ta je sashen Mairo su gaisa, nan ta bar Sagir suna ta hira da Baba.

Mairo ta biyo Aneesa suka gaisa da Sagir sannan suka musu sallama akan su kam sun wuce "sai idan sun samu dogon hutu kuma in sha Allah sai mu taho" Sagir yayi wa su Baba bayani.

"To yayi kyau, Allah ya kara hada kanku ya baku zuri'a dayyiba." Nan Ya cika su da alheri sannan suka fito suna barin gidan Baba, Aneesa ta kara sauke kai kasa tana takunta dai-dai Sagir yace "don nazo garinku shine kike nuna min hali?"

Da sauri Aneesa ta juyo ta dubeshi "Nifa ba hali nake nuna maka ba, kayi hakuri idan kaga kaman hakan ne."

"To meye ne?"

"Ba komai, ya wuce. Muje kar dare ya mana"

"Kafin nan ki kaini rafin da kike zuwa da Falmata."

Aneesa ta dube shi ta tuna lokacin da ta bashi labarin rafin kukanta. War haka kuwa wurin gwanin ban sha'awa ne. Don haka suka dau hanya suka gangara a hankali. Suna isa taga Sagir ya nade hannayensa a kirji yana kallon wurin cike da sha'awa ga korayen ganyayaki ga iska mai sanyi, zata juya ne ya sa hannu ya rike nata, tayi saurin juwaya tana waige-waige "uncle Sagir mutane zasu ganmu fa'

"Meye to don sun ganmu, ba hannun mijinki kika rike ba? idan kina so ki kara kwana shi kenan, sai na jiraki gobe mu koma hakan ya miki?"

Aneesa murna ya cikata fal, amma kuma sai tayi tunanin wata kila yaga yanda ta bata rai ne yace haka don taji dadi. Nan da nan tace "Ba damuwa, mu koma yau din kawai tunda hakan kake so. wani lokacin sai na zo na kwana biyu"

Sagir ya sake hannayenta suka juya zuwa gida.

"Amma Uwani yanzu zaku dauki hanya? yanda garinkun nan yake da nisa?"

Aneesa tace "Inna a zuwa ma fa da jirgi muka taho, amma yanzun ban san ko yau zamu wuce ba"

Inna tayi shiru sannan tace "Ke dai ki maida hankali, ki kula da mijinki, ba ruwanki da damuwa da abun hannun sa duk abun da ya baki ki gode masa ki kasance mai masa addu'a kar ki kuma takura masa ko ki fitine shi don kin ga komai kike so yana miki. komai na rayuwa a sannu ake cimmashi"

"Naji Inna na gode, zan kiyaye."

"Kije kuna yin dare."

Aneesa kaman tayi kuka nan taji da ma tacewa Sagir din ya tafi, amma haka dai ta daure tayi sallama dasu sannan ta shiga mota. Bayan ta cika kowa da tsarabarshi.

Sai da suka dau hanya Sagir yace "kuka kikeyi? ko mu juya ne?"

Girgiza kai tayi da sauri, parking yayi yace sai tayi shiru su ci gaba da tafiya, ta goge hawayenta.

Maimakon taga sun dauki hanyar fita gari sai taga ya shiga cikin gari, wani gida taga sunje mai kyaun gaske daga gani ma sabo ne gidan. Bata tambayeshi ko ina suka zo ba tunda taji sunyi waya da Haruna abokinsa sai ta zaci ko gidan sa suka zo. Amma bayan sun sauka sai taga Sagir ya fidda makulli ya bude gidan.

"Ba za ki shigo bane?"

Nan ne Aneesa ta fahimci ashe ta tsaya ne kaman hoto, daman ba yau bane zasu wuce Abujan ya hanata zama da Innarta? Tabbas yau ta gane kuskurenta.

Tana zaune bayan ta idar da Sallah, Sagir ya aika musu abinci mai kyau ita dai mamaki ne ya hanata cin abincin, har yau tana kwatanta yawan arzikin Sagir a ranta amma duk randa ta kayyade yawanshi sai ta ga ya wuce tunaninta, wai yanzu gidan da suke ciki mallakar Sagir ne, ita har tsoro kudin sa suke bata yanzu kam.

Sagir ne ya shigo dakin sanye da T shirt da jeans, "Na zaci kinyi bacci ne, kin barni ni kadai a falo"

"A'a idanu na biyu, yaushe zamu tafi?"

"Sai karfe goma na safe in sha Allah, kina da abunyi ne?"

"A'a kawai ina son zuwa gidane." Ta mike tana nade khimar dinta da abun sallah. Bata ankara ba taji wasu hawaye suna bin fuskarta "Aneesa me ya faru kuma?"

"Babu, nima ban san sun zubo ba." Ta daga kanta sama alamar neman hadiye hawayen. Sagir ya matso kusa da ita ya kurawa fuskarta idanu sannan yace "yaya kina kuka zakice babu, haka kawai hawayen ki suka zubo? Bazaki fada min dalili ba?"

Nan kukan Aneesa ya koma mai sauti ta zauna a kasan kafet ta saki kukan iya karfinta.

"kina daga min hankali fa ki fada min me ya faru? wani abu na miki? ko kuwa wani abun nace?"

Ta share ido daya da bayan hannunta sannan tace "kawai, abubuwa ne suka min yawa, na gagara sabawa dasu cikin lokaci kadan. Na tashi a rayuwar da komai kashinsa ina jin dadin sa kuma itace kawai rayuwar da na sani da dadi da ba dadi. Na zagaya cikin kauyen mu kaf da kafata, na kwana a gadon bono na tashi na taya Innata aiki sannan lokaci daya ka sabar mani da yawo zuwa kasashe, garuruwa daban daban, shiga jiragen shata, sannan yanzu ko wani gari naje Uncle Sagir ka sayi gida ka fada min ta ina zan saba da duk wannan. Sun min yawa sun wuce tunani na, a saman duk wannan ka daukeni ka mayardani tamkar daidai nake da tsarin rayuwarka bayan zai yi wuya na kamo kafarka."

Sagir ya sa hannu ya kwantar da kanta a kafadarsa "Aneesa me ya kawo wannan maganar kuma?"

Ya dago kanta ya share mata hawaye "ki daina kuka, kar ko daya daga cikin abun da kika lissafa ya shiga tsakanin ki da ni, da ni da ke duk daya ne. Kuma duk abun da kika fada ina yin shi ne saboda zan iya miki kuma ina son na miki."

"Na san zaka iya min, shine kuma dalilina; tsakani na da kai banbanci ne sosai ba kadan ba, yau gashi na gani tunda koda ni na iya zama a duniyarka kai ba mai iya jure zama a tawa duniyar bane."

"Saboda nace mu koma gobe shine yasaki tunanin zaman Kunuwal ne bazan iya ba?"

Kanta na kasa bata ce masa komai ba, "Ya Allah, me ya kawo wannan tunanin a kanki?"

Aneesa tace "Tunda kai bazaka iya zama a duniyata ba, shine ka daukoni ka dawo dani duniyarka? Ni rayuwata gaba daya a kauye take idan zaka karbeni da ni da asalina to bani da matsala amma idan zaka soni ka kyamaci asalina ..."

Sagir ya rasa me ma zaiyi a wannan lokacin ya gwadawa Aneesa kuskuren da tayi wurin fahimtar manufarsa a hankali ya hada fuskokinsu yace "Ta yaya zakiyi zaton zan kyamaci abun da ya bani rayuwata? Kunuwal da jama'ar da ke cikinta sune ke, Aneesa ni kuma kece rayuwata kina jin zan iya kinsu? Har cikin raina asalinki yake da muhimmanci a gareni, kaman yanda bana kyamarki haka bana kyamar garin da kika fito akan meye zan ki ki da asalinki, bayan nima mutum ne kuma ba dabara ta bace ta bani duk abun da kika ga na mallaka. Na yarda ina da arziki mai tarin yawa, amma ba shi zai sa na ki ki ba. Bana son kina wannan tunanin a ranki ko kadan kar ki bari kokwonto ya shigeki dangane da al'amarin mu domin ko zan rabu da tarin arzikina to ke bazan daina sonki ba."

A hankali ya sumbaci lallausar labbanta wadanda hawaye suka jika.

A wannan ranar Aneesa ta karasa sake ragamar zuciyarta ga Sagir, ta rungumi rayuwarsa ta hada da tata, ta gaskata cewa tabbas ya dauketa ya bata wani matsayi da ba macen da ta taka a zuciyarsa da rayuwarsa. Wannan yasa ta sakankance cewa ita da Sagir sun dace babu banbanci a tare dasu, AL'AMARIN ZUCI ya riga ya hadasu.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top