BABI NA HUDU
Assalamu alaikum,
Here is the continuation of Al'amarin Zucci, please do share, vote and comment.
Lots of comments will be good. Press the share button, pretty please. 😌
BABI NA HUDU
Tunda Aadil yazo yace masa bai sameta a gida ba, hankalin sa sai ya kwanta, ko ba komai zai bawa Hajiya uzurin cewa basu gama tattaunawa da yarinyar ba. Don haka da karfin gwiwarsa ya nufi main house, don a can yau yake da shirin shan ruwa. Yawancin lokuta idan dai yana gari yafi shan ruwa a Main house, wannan Ramadan din kuwa har an kai uku amma bai je shan ruwan ba, sai yau.
Hannatu ce ta shigo dakin su Sameeha ta sanar da ita akan tayi bako a waje, don haka ta dauki wayarta cikin mamakin ko waye ne, don ita kam bata barin kowa ya iso gida nemanta. Yau dinma ta fita ne don taga waye me shirin tono mata asiri yasa Daddy yayi mata maganar aure. A kan kujerar harabar gidan ta same shi. Ita dai tunda ta iso taga ba wai ta san me shi bane.
Shi kuwa Aadil tun fitowar ta ya tsaya yana mamakin kodai yayi batan gida ne, to amma yaushe ya zo, ba ana gobe za akama azumi bane? Gashi yau azumi an kai uku kenan, yaya za ayi ya manta gidan. Lalle nan ne sai dai hala ba Sameeha... kafin ya karasa tunanin yaga yarinyar da ta keta mutumcin atamfar nan da wani dinki dakyar take numfashi ta ja kujera ta zauna, duk rabin krijinta a waje.
"Lafiya dai Malam, ban gane ka ba"
Aadil yayi murmushi "Ai kya maida wukar mu gaisa ko?"
Ta dan saki jiki kadan. "Sunana Aadil, kwanaki uku da suka wuce na zo ban same ki ba. To sako ne nayi mantuwa ban bada ba shiyasa na kara dawowa yau, da fatan banyi laifi ba."
Sameeha tayi shiru tana tunanin abunyi, kafin ta nisa tace "kaga Aadil na farko, ni bani da ra'ayin jin sakon ka, kai asalima wanda ya turo sakon baya gabana ina da wanda nake so don haka ka bashi hakuri."
Aadil yayi shiru cikin jimamin yanda akayi wannan yarinyar tayi batan kai ta fito a gidan da yake tunanin gidan mutumci ne. Don haka sukayi sallama, ya isa gurin mai gadi ya mika masa sakon, ya fitar da takarda da biro yayi wani rubutu sannan ya bayar yace a hada da sakon a isar cikin gida.
Dalleliyar motarsa ya fada ya kama hanyar gida, a zuciyar sa kuwa ya gama shirya abun da ya dace yayi.
Bayan sati guda da yin wannan al'amari ne Alhaji Mahmoud ya nemi ganin Aneesa a falonsa, da jin hakan Hajiya Juwairiya hankalinta ya tashi tasan asirinta kam yau zai tonu, dama niyyarta idan anga Sameeha, sai ta cewa Daddy din anzo anga Aneesa amma shi yaron yace Sameeha ce ta masa, amma sai hakan bai faru ba. Yanzu kam dai bata da sauran dabara tanaji tana gani 'yar da tafi tsana a duniya ta wuce falon mahaifin nata ba tare da tayi komai a kai ba.
"Aneesan Innarta, yaya karatun dai ana ganewa ko?"
Kanta a kasa tace "Eh, Daddy wanda ban gane ba munayi da Khazeena amma tace itama basuyi wasu ba a makaranta sai dai na tambayi Zaheeda."
"To yayi kyau, kinaga zaki iya jarabawar tare da su Zaheeda ko dai a bari sai wani shekarar ayi miki register?"
Ba abun da ya fadowa Aneesa a lokacin irin yanda har zata iya kara wata shekara ba tare da taga Innarta ba.
"Zan gwada yi yanzun ma, ai da dan sauran watanni"
"Allah ya baku sa'a." bayan Daddy ya dan yi shiru ne sai kuma yace "Ni mamana, baki fada min yanda kukayi da bakon ki ba." ya fadi hakan da alamar jiran bayani daga gareta.
Ita kuma kanta sai ya kulle bakonta kuma? Hala dai bakon da ya zo wurin Sameeha Daddy yake nufi.
"Baki ce komai ba, kun daidaita ko har yanzu baku gama tunanin ba"
"Daddy ai da yazo bai samu Sameehan ba"
"Shi kuma me ya hada shi da Sameeha, Sameeha zai aura ko ke?"
Nan take taji gabanta ya yanke ya fadi, duniyar da take kuma yana neman ya hadiyeta. Wai me take shirin ji? Ina ita ina auren dan birni? Dan birnin ma mai ilimi wanda kuma Mummy taso Sameeha ya aura. Don su kam dai ce musu akayi Sameehace ke da bako.
"Mummy tace Sameeha ke da bako, ko da bakon yazo ya bada uzuri akan abokin sa bai samu isowa ba saboda ayyuka amma zai sake juyowa, sai muka bashi hakuri saboda Sameeha ta tafi makaranta zana gwaji"
Daddy yayi shiru cikin alamar nazari "Ba komai to tashi kije, idan kin shiga kiyi wa mummy din naku magana"
"Na gode Daddy."
Jikinta a sanyaye, ta koma daki tana isa ta bude marfin wardrobe dinta mai dauke da ledar da ta adana shi wuri guda. Hannunta na rawa ta bude takardar ta sake karantawa.
"Sannu da dawainiya, mun gode da tarbar da kikayi mana, kuma mun yaba da halayenki na kwarai, ki sa mana rana sai abokina yazo domin ku kara tattaunawa, ki huta lafiya"
Ta nade takardar a bayan takardar dai sunantane rada-rada a rubuce, tunda Baba Saratu ta mika mata wannan sakon ta boye da kyau don gudun rikici sai dai yanzu kaman itace ta rikice.
"Shin dama ni aka turo a zo a gani ko Sameeha? To tunda basu sami Sameeha ba me yasa suka amince da ni ko kuma wani rudani ne daga wajen su?" tambayoyi fal a cike a ran Aneesa, ta shiga bude abubuwan cikin ledar nan, kayan shafe-shafe ne irin na mata masu tsadar gaske da turarurruka taga an rubuta YSL a jiki sai kayan makulashe. A kasan kayan ne taga kwalin wayar Nokia a ciki.
Gumi ne ya keto mata, wai shin sun san wa Uwanin Malam Habu suka tarkatowa wannan shirgi kuwa? sun san me rayuwarta ta Kunuwal ta kunsa? sun san cewa duk inda ta shiga babu farin ciki a wurin kuwa? Nan da nan ta shiga tara kayan a leda tana maidasu, harda 'yar guntun wasikar ma ta jefa a ciki.
Hajiya Juwairiya da taji kiran Daddy hankalinta idan yayi dubu to sun tashi. Ta shiga jikinta na rawa, amma ga mamakin ta bai dago mata zancen 'yar Halima ba bare tasha tashin hankalin da ta yi zato.
****** ******** ***********
"Abba, munje mun tattauna da yarinyar, yanzu dai jira mukeyi ta bamu lokacin da za muje muji ko me ta yanke game da al'amarin, amma munyi na'am da hankalinta, da kuma tarbiyyarta" Aadil ne ke ta kwararo zance, Sagir kuwa kansa na kasa don ba yanda za ayi yacewa Abba bada shi aka je ba, don haka ya bar Aadil da aikin kwararo bayani.
"Ah to yayi kyau, duk abun da ake ciki dai sai na sani saboda a sa manya a maganar. Allah ya tabbatar da alheri"
"ameen, mun gode Abba."
"Kaima sai kayi kokari ai ka samowa kanka, ko sai ka jira abokin naka ya soma tukun?"
Aadil yana dariya ya dan sosa keyarsa sannan yace "Yallabai, muna ta kokari dai."
Bayan sun fita ne suka nufi ofis don akwai sauran ayyukan da suka saura musu na hada rahotannin kamfani da sukeyi da sauran ma'aikata, akwai wadanda suka ware zasu kara musu kudin aiki sai su dawo bayan isha zuwa karfe sha daya su rage aikin kafin kowa ya watse.
"Sagir, kai yaushe kake da shirin mu koma ne? Naga Abba fa ya sa wuta har maganar sako manya yakeyi."
"Naga alama kai dadin abun nan kakeji,"
"Ni naga yarinya nace maka tayi sosai, ka shirya kawai muje muji me zata ce ya gagare ka?"
"To ba shikenan ba sai kai ka aureta."
Aadil ya juya ya kalli Sagir "kai sai ana maganar gaskiya sai ka koma wata maganar daban,"
"Na ji, idan mun kammala wannan aikin gaban mu zamu je India inaga bai wuce muyi kwana uku ba idan Allah yaso, muna dawowa sai muje nima ko zan huta da wannan damuwar"
"Zaka gode min, muna nan da kai". Sagir ya adana motar a ma'adanar motar shugaban kamfani sannan suka shiga.
Daggash-Adebayo and sons katafaren wurine sosai wanda ya kunshi kamfani da ofis-ofis na ma'aikatan, harda gidajen ma'aikata yawanci masu kula da ayyuka, akawu, mataimaka, masu bada shawara masana ilimin fannoni da dama nan ne ofishin su yake. Sagir shi ke kula da ofishin su na Abuja, kasancewar sa mutum mai hannun jarin da ya fi kauri shine shugaban kamfanin (CEO), sai Ahmad Adebayo wanda yake kula da kamfanin magungunan su dake legas, sai dai zuwan Sagir kamfanin ne suka kirkiri bangaren kerekere da gine-gine a tsarin kamfanin. Sauran ofisoshinsu kuwa suna garuruwan daban-daban kaman Ibadan, Kogi, Kaduna, Bauchi da Kano.
Ranar wata Asabar ne gidan Alhaji Mahmoud sukayi manyan baki, wadanda suka shigo da kayan arziki iri-iri. Bayan duka matan nan sun gama shigowa falon mummy ne, aka fara gaisawa kasancewar Azumi ne, ba zancen kawo kayan ciye-ciye. Hajiya Juwairiyya dai da ganin su ta san daga babban gida suka fito, tana bin kowaccen su da kallo, har sai da suka shararo bayanin abun da ke tafe dasu.
"Da farko zan fara bude mana wannan zama da addu'a cike da fatan alkhairi, ayi salati ga annabi, a karanta Fatiha da qul a'uzai." bayan an kammala ne wannan matar tayi bayanin kanta "Ni sunana Hajiya Munnira, wadannan duk 'yan uwa ne da abokan arziki, daga gidan Alhaji Mustapha Daggash muka taho, wannan kayan dai na toshin 'yar ku kuma 'yar mu ne tunda yanzu an zama daya."
Hajiya Juwairiyya ta nemi numfashinta tana neman ta rasa shi saboda yanda yake fita a gaggauce. Hankalinta ya tashi aure kuma?
"ina 'yar tamu ne tun shigowar mu bamuga amaryar ba."
"Ai kin san yaran, suna can wurin karatu." Ta samu ta fada da kyar tana yake.
"To ba komai, tunda kina nan, sai mu miki bayanin komai"
Nan fa su Hannatu suka shiga jero kaya ana ta bayani wai duk kayan toshi ne.
Ita dai inda kanta ya kulle Alhaji Mahmoud bai ce mata za a zo kawo kaya ba, sannan bai sanar da ita cewa ga 'yar sa da ya bayar ba, daya zuciyar tace mata maganar Aneesa fa da ya miki? Nan da nan ta kau da wannan zancen, yaya ma za ayi su dauki 'yar kauye su zuba mata wannan arzikin ai yafi karfin ta. Kudin dinki ma fa da suka sa a kasan akwatin dubu dari biyu. Tab ina yarinya ai baki iso nan ba tukun.
Tana ta yaken dole dai, har ta samu bakin suka tafi, ta umurci 'yan aikin gidan su jido kayan a jibge a falon Daddy.
Ai kuwa yana shigowa gidan da kayan yayi arba, murmushi yayi ya wuce dakinsa. Bayan sun gama buda baki ne yaran duka sun shiga ta same shi da maganar.
"Da rana kawai sai ga baki." Tana fadan haka ta dake. Yayi murmushi wato sarautar ta motsa amma bata san shima da 'yan mulkin ya shigo ba.
"Na sha'afa ban sanar dake ba, sun koma lafiya dai ko?"
Baki a bude cike da mamaki tace "Da ka sanar da zuwan baki ai inaga da an shirya musu tarba ta girma, amma ace anzo gidan Alhaji Mahmoud guda ba tare da an koma da abu mai kauri ba ai bai dace ba"
"Na san Hajiya tana nan, ba abun da zai kasa"
Taga alama ya na neman ya manna mata ne don haka tace "Sai dai ban san wace 'yar tawa aka bada ba batare da sanina ba"
"Kina da wata 'yar da ta kai ayi mata aure ne yanzu bayan Aneesa?"
Ai yana tabbatar mata da zargin ta taji komai ya kwance mata, yanzu duk kokarinta na ganin Halima da zuri'ar ta sun tozarta ya tashi a banza kenan? eh mana, tunda ba yanda za ayi wannan yarinyar ta shiga wannan daular ta bar uwarta a kauye, nan da nan taji cikinta ya juya.
"ko kuwa kina da tacewa ne wannan karon, ba sai daga baya ki zo ki bi ta bayan fage ba." da ya kula bakin ta ya mutu ne sai yace
"A tunanina, an riga an zama daya zaki dauki yarinyar nan a matsayin 'yar ki, ko da a rashina ke mai riketa ne, amma har zan kawo maganar aurenta ki juya ki maidashi kan 'yar ki. Allah da ikon sa na fahimci hakan. Don haka an kammala magana aure kuma ba fashi da yardar Allah, idan kin isa kuma ki hana shi mugani." ya mike ya shiga daki. A nan ta buga tagumi na rashin sanin mafita.
Aneesa kuwa zama cikin mutan gidan ya gagare ta tunda aka kawo kayan toshinta, sai ta fara kula da canji wajen mummy, ko ta gaisheta ba lallai bane ta amsa, don haka aikin gaban ta kawai takeyi. Ranar Daddy ya ce ta shirya ana jibi Sallah zata tafi Kunuwal gaishe da su Inna har sai an gama bikin Sallah.
Wannan labari ne ya kunsa mata farin ciki a tare da ita marar misaltuwa. Tana komawa daki ta hau kimtsa kayan da zata tafi dasu. Su Baba Saratu kuwa an cika su da hirar abun da za a farayi da an isa.
Da dare ta gama goge kayanta tana jera su ne a cikin jakar tafiyarta. Sai ga Khazeena ta shigo tana haki
"kefa lafiya nagan ki haka?"
"ke kam ki tashi ki shirya kinyi baki"
"Baki ni kuma?" Aneesa ta dafa kirji, to ita wa ta sani kuma?
"Ke dai ki shirya, kin tuna Uncle Aadil da yazo ranan?"
"Eh, na tuna shi. me ya faru?"
Khazeena taja hannaun ta zuwa kofar wardrobe dinta ta ciro kaya tana zaba mata "Yazo dashi da abokinsa Uncle Sagir, wanda naji daddy yace shi zaki aura"
Nan take jikin Aneesa ya hau tsuma. "To ni kuma naje nace musu meye?"
Khazeena tace "Nima ban sani ba, amma dai ki shirya suna falon Daddy, bari naje na hado musu abun sha"
Tunda Khazeena ta fita a nan ta bar Aneesa ba tare da ta iya yin komai ba, yau ta ga ta kanta me zata ce masa? Ita ba iya zancen mutanen birni tayi ba.
Wata zuciyar tace ki gaishe su kawai ki tsuke bakin ki.
Hakan ko akayi, bayan minti goma ta sa kayanta, fes da ita, ta gyara fuskarta daidai gwargwado ta daura dankwalin atamfarta blue mai ratsin fari da bakin layi sannan ta yafa mayafinta ta karasa falon inda ta same su zaune. Kanta a kasa ta nemi wurinta na kullum a bakin kafet kamar an zana sunanta a wannan wajen.
"sannunku da zuwa"
Sagir ya juyo kallo daya ya mata ya kau da kai.
Aadil yace "Yauwa sannu da fitowa, kin fito lafiya? Mun samu an karbi uzurin kenan"
Kanta na kasa tayi murmushi. "yau kam Allah ya kawo shi, ina fatan mun wanke laifin namu?"
Aneesa tace "Daman bance kun min laifi ba, wa 'yaruwata ce"
"Ni dai ina tsamman kece Aneesa" Aadil ya fada cikin zolaya. "kuma dai da sunanki akayi tambayar nan."
Ita dai Aneesa ba abun da yake damunta illa jagorar tafiyar baya uhm baya uhm-uhm bayaga wayoyi dayake ta amsawa.
Ashe Aadil ma abun ya dame shi, don haka yace "To ni bari na dan barku ku tattauna ko?" Ya mike yana kallon Sagir.
Aadil na fita Sagir ya maida hankalinsa gareta. Ya rasa me yake damun Aadil da zai kalli wannan yarinyar yace ta dace dashi? shi Sagir Daggash da ya shiga duniya ya kewaya yaga kyawawan mata ace ya nunawa duniya wannan 'yar yarinyar a matsayin matar shi? don haka daurewa yayi yace "ina tsamman Aadil ya sanar dake ko ni waye ne?"
A sanyaye Aneesa tace "eh"
"To yayi kyau, a ina kike karatu?" Shiru tayi kafin tace tasan a rina ina ita daman ina auren gogaggen dan boko a matsayinta wacce ta tashi a kauye mai matsayin karatu iya aji daya a sekandire.
"Ba nayi" ta bashi amsa a takaice
"Baki kammala ba kike nufi?" ya tamabaya hannayensa a sarkafe cikin juna.
"A'a, ban shiga jami'a ba amma ina shirin rubuta jarabawar dai bana"
Rausayar da kansa yayi gefe guda a ransa yace oh Aadil ka cuceni, aure zanyi ko reno?
"To, Allah ya bada sa'a. mun gaishe ki zamu wuce."
Aneesa ba abun da take tunani irin Allah ya hada ta da miskilin mutum. Tunda ya fara magana ko kanta na kasa.
"ina fatan ba wata matsala ko?"
"Eh, ba matsala, sai dai idan Allah ya kaimu karshen Ramadaan zanje ganin mahaifiyata a garinmu"
Ya dago kai yana dubanta. "To Allah ya kaiku lafiya, idan kinje ki gaishesu kafin mu zo. Na dauka Hajiya ce mahaifiyarki"
"A'a ban dade da zuwa nan ba, Innata tana aure ne a Kunuwal"
Wani gari ne kuma wannan oho 'uhmm' kawai ya iya cewa, yana jira ya fita ya samu Aadil.
Ya nuna mata wata jaka yace "Ga wannan tsarabar India ce ba yawa, ki bawa su Khazeena ce ko?"
"Eh,"
"Sauran kuma sai kiyi amfani dasu."
"Ka shiga dawainiya da yawa. Mun gode Allah ya amfana ya kara rufa asiri."
Murmushi yayi iya labban bakin sa kasancewar duk da yarinyar bata masa ba, yaji dadin addu'o'in da ta masa.
"To meye laifina? bakace na tamabayeta matakin karatunta ba, mace kace na duba halayyarta kuma na dubo na yaba da halayyar kwarai."
"Yanzu tsakanin ka da Allah kayi adalci ka dubeni ka ga wannan yarinyar kamar zata karye ta dukunkune kai a kasa kaman da surukanta take magana, shin kaga dacewarta da gidana? Ka san ko sunan garinsu ban taba ji ba a rayuwata, hala ma wani kauye ne futuk"
"Me yasa kake tunanin ko matsayin mutum ne a rayuwa kawai zai taka rawar gani a rayuwar aure? kasan meye boyayyan al'amarin da yake tare da ita? ko kuwa wacce ka shaida da itan hakan ya hana abubuwa lalacewa?"
Tunda Aadil ya tabo inda Sagir baya son zuwa a rayuwarsa sai ya kau da zancen.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top