Babi na daya


"Uwani! Uwani!" wata mata ta sa baki sai kira takeyi, matar bazata gaza shekaru arba'in da uku ba a haife, tana zaune cikin madafin da ke cike tirim da hayakin da ya fito a sanadiyyar hada wutar da take ta kokuwar yi da fitinanniyar itacen da aka samo mata wanda ya riga ya jike. Tari takeyi ba kakkautawa, idanunta cike taf da hawaye ta sake daga muryar ta "wai shin Uwani bata gidan nan ne?"

"Na'am Inna" yarinyar ta amsa da sauri hade da ajiye kayan da suke hannun ta tana nadewa, akan gadon bonon ta, da gudu ta fita daga dakin nata, ta nufi Innar ta tana haki.

Inna ta mata duba daya, ta gyara itacen da ya fito daga murhu bayan ta samu wutar ta hadu da kyar "yanzu ashe bazaki hanzarta kije gidan Baba ki musu sallama ba, banda aikin saibi ba abin da kika iya. Ko kuwa sai motar ta iso ne sannan zaki fara guje-guje kina shiga kina fita?"

"kiyi hakuri Inna, yanzu zan wuce" ta fada idanuwanta a cike taf da hawaye. Dan karamin dakinta ta koma, ta dau mayafi sannan ta wuce gidan kakannin ta. Gidan da ya zamewa Uwani tamkar gidan su.

A hanyarta ta tafiya ce ta karewa yanayin kauyen nasu kallo. Duk da kauyen su wani karamin kauyene a inda ba a san da shi ba, shine kawai inda ta sani kuma take so har cikin ranta. Ba abin da ta fi so irin yanayin sanyin garin, koren ganyayyaki, ihun yara suna wasa. Ba abin da baya burge ta a dan karamin kauyen nasu, amma sai gashi yanzu a cikin kankanin lokaci zata bar shi ta bar komai a baya.

Uwani yarinyace mai sakin fuska da son walwala, a fagen walwala irin ta karkara. A shekararta ta goma sha tara, tayi zarra wajen shafe fagen kyau, siririyace bata da nauyin azo a gani, sai zara-zaran gabbai da take dasu saboda yanayin tsawonta. ba wai zakwal ta tafi ba tana da sura da diri mai kyau, da kuma manyan idanuwa da sukafi kama da tafkin madara da aka musu digon bakin tawada, ba fara bace sol, amma idan ta dau wanka zaka ga haskenta. Uwani takan burge mutane da dama musamman kannenta wadanda suke bata girmanta matuka. A bangare guda kuma takan ci karo da kyara da hantara irin ta mutanen kauyensu, kai ba ma ita kadai ba har kan Innarta da babanta duk don saboda sa'o'inta suna dakunan mazajensu ita kuma ta zabi sai ta yi karatun boko da na muhammadiya, ta taimakawa innarta ko ta wani bangare ne. Amma kash! Mafarkin Uwani guntulalle ne, kasancewar yanda mutan Kunuwal sukayiwa Innarta caa hakan yasa aka lankwasa rayuwarta aka jefa shi a walagigin da har yau tana biyan kudin fansar ta.

Kunuwal garine da mutanen cikinsa galibi fulani ne, sana'arsu na yau da kullum noma ne da kiwo da karatu, domin kuwa akwai malaman addini a garin masu koyar da karatu, da dama ana bada karfi wajen ilimin addini a garin, sai dai karancin na bokon. Garine da ya samu wayewa da ci gaba ta fannin makaranta, wutan lantarki, wayar hannu da kuma asibiti. Sau da yawa sun fi yin auren dangi a garin sannan mace tana shekaru goma sha uku to za a mata aure. Wannan yana daya daga cikin dalilan da yasa da zarar kin wuce wannan shekaru ba ayi miki aure ba to da ke da iyayen ki za a saku a gaba.

"Assalamu alaikum" ta fada a sanyaye.

Mama ta fito kenan daga bayi da buta rike a hannun ta lokacin da ta ga jikarta tan.

"wa alaikumussalam, sannu da zuwa, lale" Mama ta fada hannun ta rike da habar ta cikin mamaki "ina kika fito da sassafen nan? na san innar ki ce ta turo ki ko?"

Uwani ta rike habar mayafin ta tana wasa dashi fuskar nan a turbune, "ba inna bace ta turo ni wai na muku bankwana, kafin motar daukata ta iso?"

Mama tayi murmushi "to kuma shine ranki duk yabi ya baci haka?" Tsohuwar ta mika mata hannun ta alamar tazo kusa da ita.

"Mama, ko karyawa fa bata bari nayi ba, ban san me yasa take daukin taga ta rabu dani ba zuwa rayuwar da ban san yanda take ba."

Mama ta kare mata kallo ba tare da tace komai ba sai can tace "me ya sa zaki ce tafiyar da bata da amfani a gareki, Allah ne kawai ya san abun da yafi alkhairi a gareki, saboda haka shi zamu ci gaba da roko alherin Sa a garemu. "

Uwani ta dan yi murmushi hade da yankwana fuska cikin shagwaba sannan tace "yunwa nakeji , me zan samu a dakin ki mama?"

"Shiga ciki zaki samu danwake a roba, yafendon ki Mairo shi ta dafa"

Cikin jin dadi Uwani tace "Kai Allah yayi wa Mairo albarka, kamar ko ta san abun da nake ta marmari kenan tun jiya." taci sosai, tayi kat! ta sude sauran mai da yajin da ke kasan kwanon sai da ta gama sannan ta dubi mama tace "Mama kin san ko me ya sa Inna yanke wannan danyen hukuncin ba tare da ta nemi shawarar ku ba?"

Mama ta kalleta ta a fusace "ke yarinya! ki iye bakin ki wai bakya cikin hayyacin ki ne kam? Ashe akwai abun da Halima zata miki har ki bincike ta ko ki bi diddigi? A zatona ko wuta ta hada tace ki fada ke me shiga ne bare zuwa birni. Zaki zauna cikin jinin ki ba wai bare ba ko kungurmin daji." Mama ta nisa. "ai Halima mutumce tamkar ya goma, mace mai kamar maza ba wai ina fada miki wannan bane don tana matsayin 'yata, a'a sam. Na zauna da ita a gidan nan kuma naga abun da ta fuskanta na bakin cikin rayuwa. Ke kan ki kin san irin rawar gani da ta taka da kuma abubuwan da ta bari don ta inganta miki rayuwar ki. Banga dalilin da zai sa ki tuhumi duk wani abun da ta umurce ki da yi ba. Dole ki koyi juriya a al'amuran rayuwa" Mama ta mayar da kwallan da suka ciko mata idanu.

Uwani kam barin su tayi suka zubo, bata tare nata hawayen ba. Yaya ma za ayi ace ta manta abun da Innar ta ta fuskanta a dalilin ta? yanda ta tsaya tsayin daka ta kare mata mutumcin ta. Dalilai da dama da fushi da yarinta suka hanata gani a da, yanzu ya zama lallai ta yi yanda Innarta ta umurce ta.

Wajajen karfe sha daya na safe ta shiga bangaren kawunta wanda yake gida daya ne da su Mama can ma ta musu sallama, da zuciya mai radadi da nauyi ta bar gidan, a kullum zata kasance mai kewar lokacin da ta debe a wannan gida mai dimbin tarihi, oh yanda ta rinka yiwa Mama fitsarin kwance da take karama, da yanda ita da su Falmata suke satan gyadar Mairo idan bata nan . Bata jira kawun nata da Baba suka dawo ba saboda sun riga sun wuce kasuwar dabbobi bazasu dawo ba sai bayan Almuru.

Tana barin gidan Mama rafin kukanta ta tafi ta masa kallon karshe, nan ne wurin kebewarta da Falmata suyi ta labarai iri iri na rayuwa, suyi kuka idan abun bakin ciki ya same su su kuma dara su sha iskar damina idan suna cikin nishadi.

Komawarta gida taci gaba da hada 'yan tsummokaranta a cikin akwatin gwangwaronta, wanda kyauta ce daga mijin Innar ta malam Habu. Ita kam ta gode Allah zata bar jama'a masu dimbin kaunar ta zuwa cikin jama'ar da basu damu da su san kasancewar ta ba ko rayuwarta, amma idan ta tuno maganar da Mama ta fada mata sai taji sauki.

Malam Habu, da yake tsaye a jikin kyauren ta amma bata ma san da shi a wurin ba yace "A'ah wai Uwata ce ke ta faman kuka tun dazu?" Ya dago dan kyallen da tayi labule da sauran duniya dashi, da sauri ta juya gefe da taji shigowan shi, amma ta gagara tsai da hawayen ta. Malam Habu ya samu kujerar tsuguno, ya jawo ya zauna, wanda banda ita sai gadon bono sune kadai abun da ke dakin..

"ni na zaci an wuce nan, haba ina 'yata mai kwazo da himma da juriya? ki goge hawayen nan haka"

"Baba, me yasa Inna zata tura ni? me yasa ta bar sona kaman da?"

Malam Habu ya gyara zaman shi ya fuskanci Uwani. "Uwani, na san ke yarinya ce mai tarbiyya da natsuwa, sannan ina da tabbacin cewa kin san yanda mahaifiyar ku take ji game dake. Gidan nan da zaki je, da 'yan uwanki zaki zauna, Allah ya kaddara rayuwa daban-daban zaku samu ke kin girma a kauye su kuma a birni." malam Habu da ya tabbatar ya samu hankalin ta sai ya ci gaba, "yanzu, akwai dalilin da ya sa Innar ki yanke wannan hukuncin, ina son kisan cewa addu'o'in mu na tare da ke kuma addu'a bata faduwa kasa, na san idan kinje zaki fahimci wannan dalilin da yasa inna take son ki tafi. Allah ya miki albarka."

"Na gane Baba, na gode. Allah ya bar mana kai domin kaine ginshikin rayuwar mu."

"Yauwa Uwata ko ke fa? yanzu ki gama shiryawa ki zo ki wuce kar kuyi dare, kin san ban cika son tafiyar dare ba."

Uwani ta sabi akwatin gwangwaronta, tana kokawar daurawa a kanta, malam Habu ya karba mata "Je ki samu Innar ki tana daki". Uwani tayi murmushi sannan ta bar dakin zuwa na innarta. Ta same ta sai faman ninke kaya takeyi. Ko da taji shigowar ta bai sa ta bari ba saboda tana tsoron kar ta kasa jure rabuwa da 'yar ta. Uwani dai tana kula da Innar ta, don kuwa dakin tsab yake, saboda wataran ita har tsabtar innar tata na damunta, don haka ta san kawai ta damu da batun tafiyar tata ne. to idan bata so na tafi me ya sa zata tura ni? kai tambayoyin nan sun isa haka, wannan zai iya kasancewa karo na karshe da zata hadu da innar ta a cikin lokaci mai tsawo, bazata kuma yi amfani da lokacin wurin tambayoyin da basu da amfani ba. Da gudu ta karasa ta rungume innarta "na san zakiyi kewata, nima haka zan yi kewar ki da Muhammad, Suhail da kuma Amina. Don Allah inna kina shan maganin ki kan lokaci, sannan kar abar Amina da Suhail su rinka bin su Madu, suyi karatu sosai saboda su samu ci gaba a rayuwa. Bana so su bar karatun su a rabin hanya kaman yanda na..." nan da nan tayi shiru domin toshe wannan madacin da ya taso mata a duk lokacin da ta tuna wannan bangare na rayuwar ta. Wannan wani bangare ne wanda da akwai yanda za ayi ta manta dashi kwata-kwata da ta manta.

Inna ta juyo ta fuskanci Uwani, ta share mata hawaye. "ina son ki kasance mace mai kamun kai da sanin mutumcin kanki, rayuwar birni rayuwace ta daban da wanda kika saba da ita. Ki san matsayin ki a ko da yaushe ki kuma ji tsoron Allah, Allah ya kaiku lafiya" tana fadan haka ta juya ta bar dakin. A nan gaban kwabar dakin Inna, Uwani ta zube tana ta rusgar kuka, Muhammadu da Amina suka shigo dakin suka rungumi 'yaruwar su, gaba daya suka dunguma zuwa rakata bayan Malam Habu ya sake rarrashin ta,a waje suka tarar da kusan rabin kauyen sun taru domin ganin tafiyar ta a wata zankaleliyar mota,

Direban yana jiran ta a mota, inna ta tanada masa abinci da sha irin na mutanen karkara sai da yayi kat.

Shi ya karbi gwangwaron ta ya sa a bayan motar, Uwani tun da take bata taba ganin mota mai kyau ko kuma dalleliya irin wannan ba, motocin da ta sani kawai sune a kori kura da first lady, wanda ake zuwa cin kasuwa a ciki. Duk makota sun taru, haka Uwani ta rungume babbar kawarta Falmata da kyar aka banbare su. sun sha bai-bai kam har sai da hannun Uwani ya soma ciwo tukun ta bari, daga bayan tulin jama'ar da suka taru ta hango fuskar Innar ta tana lekowa daga cikin gida. A take a wannan lokacin Uwani ta yanke hukuncin koma me yake jiran ta a birni zata fuskance shi, saboda ba za ta bar dimbin jama'ar da take so suke kuma son ta haka siddan ba.

Suna tafe ta tuno maganar da Baban ta ya fada mata "kar ki damu da Inna, ina nan zan kula miki da ita da kannen ki, kiyi karatu sosai sannan ki dage da addu'a, idan mun samu dama zamu zo mu ganki kin ji?" Uwani kuka kawai ta sa mai tsuma rai don ita dai kawai ta san ya fada ne me zai sa wani yazo gidan mutumin da ko fadin sunan sa an haramta a zur'ar su?

Ta riga tayi zurfi a tunani kaman daga sama taji direban yace "yarinya, ki bar kukan haka kar kiyi rashin lafiya, zaki saba a hankali, kinga nima daga kauyen na zo gashi har na saba." A hankali ta daga idanuwan ta da sukayi luhuluhu don kuka.

"Sunana Mallam Sule" mutumin nan ya fada

"Ni suna na Aneesa amma kowa Uwani yake kirana"

"Malam sule yayi murmushi yace "Ah ashe babban suna ke gareki, to ai da karfin hali aka san manyan mutane. Ina tabbatar miki zaki ji dadin zaman ki a can a hankali."

Uwani dai murmushi tayi kawai tana dariyar rashin sanin Malam sule domin da ya san irin shaquwarta da innarta da bai fadi haka ba.

Bata san iya tafiyar da suka yi ba akan titi, saboda tayi zurfi a tunani wani lokacin har gyangyadi ya dan sace ta, idan ta bude idanu sai ta gansu a wani gari.

A karo na karshe da ta bude idanunta ya faru ne saboda wani irin kara da ta ji na karfe a kan karfe, a birkice ta zauna tana kifkifta idanu saboda razana.

"ki kwantar da hankalin ki" malam sule ya ce mata, "kofar get ne, mun iso yanzu kam".

Uwani tayi zuru tana kalle-kalle kaman wani abu zai taho ta bayan ta ya cinye ta, a hankali ta kawo fuskar ta jikin tagar motar tana karewa masarautar kallo. An kawata masarautar da shuke-shuke daban-daban na furanni kala-kala, arewa maso gabas na masarautar anyi shine don adana motoci manya-manya kaman masu shirin numfashi. A tsakiyar titin da suka biyo kuma wani shataletale ne wanda ruwa yake bulbulowa ta tsakiyar sa, abun da ya kidima Uwani shine yanda bata ga wani dutse ba da ruwan yake bulbulowa a jiki. Malam sule ya bude mata kofa, saboda yayi ta kiranta amma ina tsabar nisan da tayi bata ko ji shi ba tana duban abun al'ajabi iri-iri. Da ta farfado ne ya kara kiran sunan ta. "me kike tunani haka? ga Saratu zata kai ki cikin gidan, za a shigo miki da sauran kayan ki yanzu."

Uwani ta wulwulo daga motar har ta kusa faduwa amma tayi saurin damkar kofar saboda kar ta karasa kasa. Wata mata akalla tafi innarta sosai a shekare mai mulmulallen jiki ta tunkare ta, tana zaton dai ita ce Baba saratu, saboda haka tayi maza ta durkusa don kwasar gaisuwa a wajen dattijuwar. "ina wuni?" Baba saratu da sauri ta tare ta sannan ta dago ta "lafiya kalau, 'yar nan kun sha hanya. Yaya hanya dai?" uwani cikin in-ina tace "l...lafiya"

"Don Allah tashi, kar kina durkusawa idan zaki gaisheni kinji ko?" Uwani tayi saurin girgiza kai alamar 'eh'.

"Yawwa, ko ke fa? Yanzu mu shiga ciki ki huta ko?" daga wannan lokacin Uwani taji tasu zata zo daya da Baba Saratu.

Ta sha tuntube yafi a kirga kafin su isa cikin gidan, don ita kam Allah ya gani ba kasa take kallo ba ginin kawai da kayan birni take ta zubawa idanu, wasu ta san su a karatu ne wasu kuwa ko a littafin bature bata taba gani ba. Ita dai abun da ta sani shine wannan Masarautar na da matukar kyau da girma bata taba ganin wani abu kamar sa ba, masarautar da ta fahimci ba ko ina bane face wurin da wai yanzu ita Uwani zata rinka zama a ciki na tsawon... ko yaushe oho itama bata sani ba.

Baba saratu tayi ta tafiya dasu a kan wani dan dandamali, wanda ya bude zuwa wani katon fili a gefen gidan, a nan ne Uwani taga wasu tsuntsaye masu kyau da ban sha'awa suna fidda sautin waka mai dadi, nan da nan taji tana son su. Komai na wannan gida ya dauke hankalin Uwani matuka, haba shiyasa Falmata tace birni abun tsorone. dazu-dazun nan ji tayi an tsane ta ne da aka turo ta yanzu kuwa har abun cikin sa sun fara burge ta. Hannun ta ya hau bari bakin ta na kakkarwa , yaya za ayi ta saba da duk wadannan abubuwan, anya Malam sule ba zolayanta kuwa yake yi ba da yace zata saba, kai ta fara tantaman hakan.

Haba ai na baya wasan yara ne gaba daya jikin ta ya dauki bari a yayin da ta sanya kafafu kan wani abu mai susa a kasan kafarta , ba shiri ta daka tsalle ta cafke kofa idanu a rufe tana ihu wayyo Allah, Baba saratu ta juyo da sauri don ganin me yake faruwa. "lafiya, Uwani me ya faru? wani abu kika gani?" haba ai Uwani ta gama tsorata ko idanuwanta ta gagara budewa bare magana. baba Saratu ta matsa kusa "fada min me ke faruwa?"

Haka dai ta tattara duka jarumtakar ta tace "suna bina, zasu cinye ni... wayyo kafafuwana, ki cire su" haka ta hau sambatu. Baba Saratu ta taba ta "bude idanuwan ki, ba abun da zai kama ki kafet ne, kin ga yana sa cakulkuli ne kawai saboda laushi, ba abin da zai miki" ta goga kafanta a kan kafet din don ta nunawa Uwani tace itama ta gwada ta gani. Sai da ta natsu tukun sannan Baba Saratu ta riko hannun ta ta kai ta masaukin ta.

***** ******* ******

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top