BABI NA BIYAR
BABI NA BIYAR
Gaba daya gidan ya hautsine sai kace yau take sallah, banda murna da farin ciki ba abun da ke tashi a gidan Malam Habu na Kunuwal. Yau ga Uwani ta zo daga birni kowa sai cicirondon zuwa ganinta yakeyi, wasu an ce musu Uwani ta dawo tamkar balarabiya don kyau, wasu ko ce musu akayi sai sunje su ga yanda fatarta take sheki kamar an canza mata fata. Ko ma dai menene Uwani dai uwanin da suka sani ne 'yar Inna da malam Habu, wayewace kawai ta kawo wannan canjin.
Yana zaune a kan tabarmar gindin bishiya, inda suke taruwa su rakashe suna hirar banza da wofi, wani sa'in a kawo maganar gidan makwabtansu wani sa'in na gidajensu, a nan ne aka fasa kanun labaran.
"Ai Nata'ala, na gaya maka sai ka ga yanda ta dawo wanke hannu ka taba, ni wani kalan yadin da na hango a jikinta alqur'an ban taba ko mafarkinsa ba. Kai kaga wata dalleliyar motar da ta dawo da ita? tafi wacce ta dauke ta a kyau da girma da komai
Iro yace "Ai ba zancen sanyi, kawai abun da za ayi gobe ka shirya da farin safiya, ka cafko kajin ka guda uku kaje kayi barka da sallah ko za ayi dace"
Nata'ala ya hakimce duk yana jin jawabin abokan nasa, yayinda shi ya gama nisa a tasa duniyar...
Bayan ribibi ya lafa ne suna zaune ita da Inna a tsakar gida Aneesa ta dubi Inna tace "Inna Daddy, ya miki bayanin komai ko?"
Inna ta tabe baki tare da gyara bakin zanin ta sannan tace "Uwani kenan, ai ni magana ta fatar baki ta dade bata hadani da mahaifinki ba, bare kuma abun da ya shafe ki. Ko tafiyar kin nan ma da Malam aka gama komai kafin na amsa."
Aneesa ta gyara zamanta tace "Inna don Allah ina son na san takamammen laifin da Daddy yayi miki, ko kuma abun da ya raba ki dashi. Don ni kam zuwana naje da tsanarsa sosai a raina amma na tarar da shi ba a yanda na dauke shi ba. Na san mun muzanta an zarge ki kuma ta dalilinsa amma don Allah ina son ki fada min."
"Zan fada miki a lokacin da ya dace, yanzu ki fada min, shin kin amince da zabin da ya miki?"
Kan Aneesa a kasa, wannan wani abu ne da take dadewa wajen kashe lokaci don ta samo amsar shi amma a kullum sai ta gano cewa bata sani ba, amma kuma meye amfanin sanin ma?
"Inna don Allah ki fada min?" Aneesa ta shagwabe fuska amma sam Innar ta taki, don haka suka shiga hirar shirye-shiryen sallah. Aneesa ta ja bakinta tayi shiru da niyyar washegari idan taje ganin jinjirar Mairo zata tambayi Mama kuma tasan a can kam za a bata labari.
Da wannan zumudin a ranta tayi bacci.
****** *********
"Yanzu haka zaki fita da sassafe?"
"Inna yanzu zanje na dawo, hala kuma daga gidan Mama ta can zan wuce gidan Falmata."
"Idan kin gama sai ki zo ki sa min hannu a miyar sallar ko?"
"To Inna." cikin dauki ta fice daga gidan. sauri take a hanyarta, duk da kowa ta gani yana son gaisawa da ita a hanya, sabanin da, da kowa yake gudun a ganshi tare da ita.
"Ai ke kam yarinyar nan a gaishe ki da iya doka sammako."
"Mama kar kice min bacci kikeyi, sai kika tuna min da Abuja, sai ki ga mata har taran safe bata tashi a bacci ba."
"wai wai wai, ina ni ina kai tara a kwance, ai sai jiki yayi ciwo. Mun ga tsaraba jiya kaca-kaca, Malam Sule ya shigo har nan muka gaisa ya ajiye mana. Allah ya amfana."
Muryar Baba sukaji ya shigo cikin gidan "a'a baba yau bakaje kasuwar bane?" Aneesa ta fada.
Ya zauna kan kujerar sa mai kwanceccen baya "Bayan an sake ni anyi sabon miji kuma ina naga ta walwala bare zuwa kasuwa?"
Aneesa tayi dariya sosai sannan tace "Ai ba a daura ba, idan kana so ba sai nace na fasa ba." haka dai sukayi ta barkwance daga bisani suka gaisa, sannan ta wuce sashin Mairo don ganin jinjira, wacce aka sanyawa suna Hauwa'u amma Inna wuro suke ce mata kasancewarta mai sunan uwar Mairo.
Komawarta ta samu Baba ya fita kofar gida don haka ta bajewa mama bukatarta na son sanin ko meye maqasudin rabuwar iyayenta da kuma ma'anar kalmar da aka dade ana caba mata wato "Uwani 'yar Halima ai gado tayi." Nan ma Maman cewa tayi Innarta ta fada mata. "ni kam sai gwarani kukeyi ku taimaka ku fada min"
"hmmm idan kin sani akwai abun da zaki iya gyarawa ne? komai ya wuce, ya ci gaba da rayuwar sa itama ta ci gaba da tata"
"Ina son na sani ko akwai abun da zan koya a cikin labarin da zai sa na kiyaye yin kuskuren da dayan su yayi a rayuwar aure. Tunda nima ana shirin nawa"
Jin haka Mama tayi ajiyar zuciya "Ki je dai Innarki ta fada miki ai waka a bakin mai ita tafi dadi."
Haka dai Aneesa ta tafi gidan Falmata jiki babu kwari. Falmata na son jin hirar birni irin Abuja yayinda Aneesa take son jin tarihin iyayenta.
Ranar dai batayi bacci ba sai da ta sake samun innarta akan lallai tana son sanin ciwon da Mahaifiyarta mama, take alhinin fada mata da bakinta don gudun tuno bakin cikin wancan lokacin. A nan ne Inna ta daddara.
"Hakika ni Halima na ga rayuwa, wanda nake farin ciki da shi da wanda ko a mafarki bana fatan sake ganin shi. Tun ina cikin kuruciyata kanin Babanmu baban su Zainabu da yake Gombe ya zo ya tafi dani saboda ya sani nayi makarantar zamani tare da yaransa, kasancewar hakika yafi Babanmu rufin asiri, a wancan lokacin. Munyi kukan rabuwa da su Mama yayinda mutanen gari kowa yayi ta aibanta abin da sukayi da rashin godiyar Allah, tunda ai 'ya mace anyi ta ne don ta yi aure ta kula da miji da yaranta don me yasa su zasuce tasu 'yar tayi boko?"
Aneesa ta gyara zamanta.
"Basu canza shawara ba, su ka barni har na kammala karatuna na firamare. Nakan zo lokaci-lokaci na gaida su mama da Baba a gida, a haka ne baban su Zainabu yace ya sama mani makarantar kwana ta Doma inda zan ci gaba da karatu, to nan ne akayi takun sak'a da babanmu, domin kuwa ya k'yakishe kasa yace 'yar sa ta gama boko. Da kyar dai aka shawo kanshi, sai da yayan mu yasa baki ya barni yace amma yana sama min miji zan dawo ayi mani aure.
Na koma da wannan yarjejeniyar, ai kuwa ko shekara biyu ba a rufa ba, sai ga baban su zainabu ya taso keyata a gaba, A lokacin da na hadu da Mahmoud a gidan wata yar su Zainabu wai shi kanin mijinta ne yazo daga Zaria, kafin kace meye zance yayi nisa har kunnen baban Zainabu. Wannan yasa ya sakoni a gaba don na bayyana komai gaban baba a san abun yi. An yi bincike mai tsawo, kasancewar sa mutumin Zaria, sai da aka hada da jama'armu na can tukunna sannan aka gano gidan su da kuma ko shi waye." Inna tayi shiru tana murmushi kaman wanda take tariyo lokacin a kwakwalwarta "a wancan lokacin na dade banga mutum mai son kyautatawa nasa ba da na kusa da shi irin Mahmoud, wato mahaifin ki. Ba aje ko ina ba, aka daura aurena da Mahmoud muka tattara muka koma Kaduna inda yake aiki a lokacin.
Tunda muka tafi lafiya kalau, ba abun da yafi farin ciki a gurin su mama irin hakan. Don hankalin kowa ya kwanta sun aurar da yarinya lafiya, ba kaman yanda ake zaton zan dawo ba daga birni a lalace. An ce wai idan an ji shiru ma lafiya ne, a tunanin su kenan. Amma a nawa bangaren labari ya sha bambam anyi auren mu da Mahmoud da wata goma sha daya sai gani niki-niki da tsohon ciki da akwati guda, kana ganina kuma ka san nasha wahalar tafiya.
Sai da na natsa komai ya lafa tukunna babana ya sa ni a gaba da tambayoyin ko lafiya? banda kuka ba abunda nakeyi haka dai suka hakura suka barni har washegari tukun. A hankali na shiga warware wa mama abun da ya faru.
Wato randa muka bar garinnan mun tafi cikin farin ciki da daukin juna, mun sami watanni biyu masu kyau cikin zaman lafiya kafin komai ya juye akasin hakan.
Wato kwatsam ganin Mahmoud nayi sun dawo da wata mata gida ko kadan ban kawo wani abu a raina ba, ban kuma tambayesa ko wacece bakuwar tamu ba, na tarbe ta da kyau, sai da yamma ne ya kira ni, gaba daya yanda naga ya daburce na san akwai matsala don ban taba ganin sa cikin wannan yanayin ba. Cikin dai kame-kame ya hau min bayanin wai wannan bakuwar tamu amaryata ce. Iyayensa dama sun bashi mata, to amma ya riga ya ganni kuma ni yake so don haka ne ya aureni ya kuma basu hakuri akan zai auri zabin su daga baya.
Bazan iya fayyace miki halin da na tsinci kaina a ciki ba a wannan dare, nayi kwanan bakin ciki a wannan rana amma kuma mijina ne dole na zauna nayi masa biyayya. Sai dai ni nake kidana nake kuma rawana, domin kuwa tun zuwan amarya ba zaman lafiya tsakani na da Mahmoud, yau an daura mini sata gobe an mani sharrin hana mutanen gidan abinci wato amaryar dai, duk na zauna na hadiye gaba daya. A haka har na samu juna, ganin haka ya kara tunzura amarya wurin sake sabon shiri, ba gaira ba dalili sai Mahmoud ya dawo gida da wani zafaffen fushi ya hau jibgata kaman an aiko shi, wani lokaci haka zai fita bai bani kudin cefene ba, sai dai nayi 'yar dabara na samu wanda zan ci, wai ni a gidan Mahmoud akwai randa na jera kwana biyu ina jika garrin kwaki ina sha, ran na ukun ne naji jiri na dibata na san lokacin neman mafita fa yayi. Amma menene mafitar?
Har ya kasance ni da na sa Mahmoud a ido sai ayi sati yana wurin amarya, kasancewar ya kamawa amaryar sa gidan gefen mu. Haka na zauna nayi ta renon cikin jikina, cikin kunci da bakin ciki gashi ba halin tafiya gida saboda a lokacin ko kudin mota bana maganinsu. A haka ne dabara ta fado mani na soma shiga makwabta ina musu kitso saboda na samu na abinci. A wancan lokacin gilmawar motar sa kawai ke tsakani na da Mahmoud, daga zuwan amarya zuwa watanni biyar sai da ya zamana bani da girki a gidan. Ni nake ciyar da kaina na kuma biyawa kaina bukatun yau da kullum, gashi dai mutane suna yi mun kallon ina hutawa ne, mijina mai motar yayi, gidan mu mai kyau na zamani amma basu san ba nan gizo yake sakar ba, raina a cunkuse yake.
Wataran idan nayi wa mutane kitso ma bai wuci a bani sabulu ba ko mai, duk da suna taimakawa amma nafi bukatar kudin ko ba komai zasu tare wani abun. A hankali na kula Mahmoud kaman ma bai san ya ajiye wata abu a gefe ba bare ya tuno da abun da yake cikin ta.
Ranar da naga abu ya isheni ne na sabi gyale na shiga gidan amaryata, bata ko bari mun gaisa ba, ta taso. "lafiya zaki shigo kan mutane babu izini?"
"kiyi hakuri nayi sallama, amma da bata kama na shigo bangaren ki ba ni ba me yin hakan bane, ni na shigo na roke ki ne kiji tsoron Allah a al'amuranki, ki bari mijin mu ya kwatanta adalci a tsakanin mu, meye ribarmu yau ace muna kai shi ga halaka bayan koda ba ya tara mu don yana son mu bane ai a karkashin sa muke, kuma bazamu so cutuwar sa ba. Kiyi wa Allah ki rinka fada masa gaskiya, don yau ya fifita ki akaina ba karamin abu bane a wurinsa gobe ya fifita wata kuma a kanki." Sai da ta gama karemin kallon banza tukun ta daura
"ki je dai kiji da tsiyarki, ko an fada miki ba musan asalin ki bane, kin fito daga kauye futuk kinga maiko kin manne, ko zuciya babu miji ya daina shiga wurinki amma baki gane jirwaye yake miki ba, nice ke da tuni na wuce inda nafi kauri."
Ni Halima wai akeyiwa gorin Mahmoud yau, haka dai na bar gidan jiki a sanyaye, duk wannan bai isa ba ranar na dawo daga gidan wata wacce nake zuwa yiwa kitso na samo sabulu, da omo, ledar na rike a hannuna na sa dan mabudi zan bude gidan sai naji kofa a bude. A tsorace na sa kai na shiga, ina lekawa kuwa ashe Mahmoud ne ya shigo wai yaji dalilin da zai sa na je na tayarwa matarsa da hankali. Mamakin sa ne ya sa ban bashi amsa ba, sai tambayar kaina da nayi, shin kuwa Mahmoud din da na aura ne wannan, a lokacin ne shi kuma idanunsa suka kai kan ledar hannuna ya wabta ya bude.
"Meye wannan kuma?" cikin in ina da kidimar da tsawar sa ta haddasa min nace "sabulu ne da omo" a fusace ya jefar da ledar yace "A gidan uban wa kika samo su?"
Maganar tayi mani ciwo amma na daure nace "sana'a nakeyi na samu, shin ko ka damu da sanin ci da sha na a cikin wannan watannin ma kuwa Mahmoud? ka mance da abun da kabari a tare da ni? ka mance da alkawarin da ka min na kula da kaunata har karshen rayuwa? ashe haka kaunar take na wata biyu Mahmoud?" mari ya kai mani sai da na ja da baya. "Tukun ma da izinin wa kike fita a gidan nan? da har zaki ce min sana'a" yayi mini dariyar da tafi kuka ciwo wato na takaici sannan yace "wani sana'a ma kika iya da har zaki je ki samo kudi?"
"Wato manufarka, kai baka kawo ba sai na zauna na kashe kaina da yunwa alhalin hakan ba gagarar ka yayi ba? kasan hakkina da kake tauye mini kuwa?"
"Baki san ina tauye miki hakki ba sai kin nemi matsuguni da tufar sawa kin rasa tukun" ya bugi teburin tsakiyar falon.
Tsoron kalamansa da kuma halin da zan shiga idan ya ida aikata abun da ya furta ne yasa na gagara fadin komai, har ya fice. Da yamma na koma shagon unguwar mu, na kai wa me shagon omo na da sabulu nace ya taimaka ya canza min da suga kulli daya da taliya. Ina kallon irin kallon da mai shagon nan ya soma mini tunda ya kula da halin da nake ciki, na tausayi amma ba yanda ya iya, kuma yana tsoron tambayar ko me yasa yana kallon mijina a gari amma kullum ina sintirin kayan masarufi? Ranar dai da ya gaji da wnanan shirun sai Umaru mai shago yace min "Ba komai lokaci ne komai zai wuce." ya kara min karfin gwiwa a wannan ranar.
Haka na kara wata guda cikin lallama rayuwa, cikin uquba da kewar gida, cikin ma sai ya dade yake motsawa saboda rashin koshin lafiyata da kuzari, ban san zancen awu ba kam haka nake jabe a gida cikin tunanin maganar malam Umaru mai shago.
Sai dai ban san haka komai zai kare ba, randa Mahmoud ya dawo gida yana ta ihun fada, na shigo falon na same shi. "yau kam Allah ya tona asirin ki, wato daman kin san me kikeyi a gari kina zubar min da mutumci zaki wani zo ki ce min sana'a kikeyi don ki ciyar da kanki. Ashe sana'ar taki daman haka take?"
Nace "Ban gane ba Mahmoud, me kuma ya kawo wannan tashin hankalin, ni ban taba cewa ka bani wani abu naka dole ba, alhamdulillah, Allah gatan kowane, kuma Shi yana sane da komai Shi da Yasani a wannan yanayi da nake ciki shi zai cireni."
Ban tashi jin komai ba sai saukan belt a gadon bayana "Ni zaki cewa Allah, kinje kina yawon iskanci, har zaki kawo min ciki kice min nawa ne?"
Bakin cikin da wadannan munanan kalamun suka haddasa min ne suka rufe min idanu da kunnuwa naji kamar bana duniya, wato abun ya kai ga yau rashin mutumcin Mahmoud ya tashi a kaina ya koma shegantar da cikin jiki na.
Ban san lokacin da na wanka masa mari ba. Sai da nayi, na koma lungu na dunkule rike da baki na, nan ya rufe ni da duka ina dunkule don kar ya samu cikin jikina. Yana gama jibgata son ransa, ya ce na nemi inda dare ya min ya sakeni. Kuma bashi bani bare kuma wannan abun ya fada tare da nuna cikin jikina. Cikin kuka na kwana, da safe na tattara komatsaina, na dauki sarkar da ya saya mini farkon auren mu na wuce kasuwa na sayar da ita sannan na nemi motar Gombe, bana ko jin ciwon da ya haddasa min a jikina. Zuciyata garin mu kawai take so kuma naga iyayena. Haka na iso da burin samun kubuta daga waccar rayuwar. Amma sai kuma ga magana ta bazu a gari, ai nayi cikin shege ne mijina ya gane ya kuma hadoni da abu na, ban san yanda akayi aka murda labarina ya koma hakan ba."
Aneesa cikin kuka irin mai zafi a makogoron nan take tuno wasu abubuwan da ta fuskanta a rayuwarta, nan take taji ta kara son mahaifiyarta a ranta.
"Innata to me yasa ki ka yarda na koma hannun wannan azzalumin mutumi..."
Nan take Inna Halima ta katse ta "kul, kar ki kuskura ki fadi mummunar kalma a kan mahaifinki, wanann yana daya daga cikin dalilan da yasa ban taba baki labarin nan ba, saboda bana so ki tashi da kiyayyar mahaifinki a ranki, hakika na yi yaki nayi fama da jama'a har Allah ya kawo Malam Habu garin nan a matsayin malamin makaranta, ya samu labarina kuma ya amince ya aureni alhalin ko auren fari bai taba yi ba, tun ina tsoron sake jiki dashi gudun abun da ya faru a baya har dai ya nuna min shi dan halak ne.
A hankali ya fahimtar dani idan aka cutar da mutum kuma yana da daman ya rama cutar da akayi masa amma yayi hakuri to lallai shi ya rabauta. Da wannan dalili ya ci galaba a kaina lokacin da mahaifinki, ya nemi magana dani akace masa nayi aure, ya nemi malam Habu ta gurin mai gari akan yayi nadama kuma yana so ya gyara kuskuren da yayi a baya, tun ba yau ba yake bin mu da maganar amma naki amincewa sai lokaci daya, da naje gidan suna aka yada magana wai wasu yaran haka aka shigo mana dasu gari ba a san ubannin su ba. Ganin cewa na san sarai waye mahaifin ki kuma na san yana neman ki idanu a rufe ya sa na amince rikon ki ya koma hannun shi kaman yanda hakan ya dace a shari'ance."
Ranar dai Aneesa kuka Inna kuka, haka suka raba dare kafin Malam Habu ya leko yace "koke-koken nan ya isa mana, ko sai ruwan idanun naku sun kare ne a dare daya har ku rasa nayin kukan rabuwar auren Uwanin?"
Washegari aka tashi safiyar Sallah, duk gidan da ka leka zaka tarar da annashuwa da farin ciki, kowa ya kure a daka, ana ta hidimar sada zumunci, da mika kyaututtukan abinci. Da yamma bakon nasu ya iso, sai dai kowa yaji mamakin ganin wannan bako a wannan lokacin. Malam Habu ne ya fita suka gaisa tukun sannan yace "Bari a musu magana sai ka shigo ku gaisa, sannu fa kun sha hanya"
Alhaji Mahmoud yabi shi da kallon tausayi, yanzu haka suke rayuwarsu amma hankulan su a kwance, ya dubi gidan da kyau. Yanzu a nan Halima take rayuwarta? nan take yaji wasu hawaye suna neman kwararo masa, amma ya hadiye su. Sai kuwa ga Malam Habu ya shimfida masa tabarma a dan falon karban bakin sa, a hakan ma gidan malam Habu yana cikin daidaikun gidajen da aka mulmule da siminti a garin.
Inna da jin anyi bako tayi maza ta hada fura, ta sa a kwano mai kyau ta baiwa Amina ta kai, ta dan daura jalof din taliya da yaji hadi sannan ta bar Aneesa wurin duba girkin ta yayibi luffayanta ta nufi falon, sai dai bakon da ta gani ya haddasa mata mummunar faduwar gaba, wanda kuma labarin da ta bawa Aneesa jiya yana daya daga cikin abubuwan da suka dawo mata da ciwonta sabo fil.
Bata bari damuwar ta bayyana a fuskarta ba, ta zauna daga bakin kofa ta gaishe shi, ta kuma masa sannu da zuwa, shi kuwa kallonta yakeyi bata canza ba sosai, sai dai da tana cikin hutu fiye da wannan ya san zata dade tsufarta bai fito ba. Sai da ta sake ce masa yaya hanya sannan ya amsa.
"Bari yara su iso maka da abinci"
"A'a alhamdulillah, sai da naci abinci a Gombe sannan na karaso."
"Cimar mu ta Kunuwal dai ta canza ba irin wanda ka sani bane a da"
Dukan su sukayi shiru, shi ya san da gayya ta fadi hakan.
Malam Habu ya yi sallama ya shigo falon, aka sake gaisawa, Inna Halima ta mike zata tafi yace
"Zauna muyi magana mana"
Wai shi wannan ya zaci har yanzu a karkashin ikon sa nake ne? ta masa wani irin duba, tana jin fushi na taso mata, sai da ta zauna sannan ya ci gaba "Kaman yanda na sanar muku a waya, anyi tambayar auren Aneesa kuma an bada ita. Malam Habu kayi hakuri na maka katsalandan cikin al'amari don kowa ya san kaine kafi cancanta ka auradda Aneesa wato, amma ganin gidan mutumci ne suka miko wannan maganar yasa na yi tunani har na amince ba tare da na tunkare ka ba. amma yanzu da suka zo da batun aure, al'amarin sa rana da komai, naga ya dace nayi tattaki nazo domin a tattauna a tsanake."
Malam Habu ya gyara zama yace "Yallabai, ai komi kayi yayi daidai domin kaine mahaifin Uwani, mu dai fatan mu Allah ya sa ayi a sa'a Allah ya bata zaman lafiya da mijinta ya bata ingatacciyar rayuwa"
Kaman daga sama suka ji Inna tace "Amma dai an bincika bayi da mata ko? ko kuwa baya shirin yin wani auren? Don kar a zo a sashi dole ya sa rayuwarta a hatsari."
Jin hakan yasa mazan duk sukayi shiru, daga bisani ta mike taje ta dauko musu abinci ta koma cikin gida abinta.
Ai wannan ma wani salon tsiya ne sai da ka gama shirin aure zaka taho kace wai kai 'yarka 'yarka, bayan baka san wuyanta ba.
Bayan sun kammala ne, Alhaji Mahmoud ya nemi ganin Aneesa don suyi sallama zai wuce Gombe washegari jirgi zai maidashi Abuja. Gaishe shi tayi kawai ba tare da ta tsawaita hirar tasu ba, ya nemi sanin ko yaushe take son komawa, Tace "Daddy ko nan da sati daya?"
Tana ta addu'ar Allah ya sa ya amince ne a ranta, sai kawai taji yace "to shi kenan sai ki zauna da shirin ki nan da rana ita yau."
Da suka zo sallama ne, Inna ta bukaci ta sanar da shi wata muhimmiyar magana. "Sai dai magana ta karshe da ya kyautu a fadawa yaron nan da zai auri Uwani shine; Uwani fa ta taba yin aure!"
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top