BABI NA ASHIRIN DA DAYA
BABI NA ASHIRIN DA DAYA
Komawarsu gida da kusan Sati Inna ta kula Aneesa bata da shirin komawa sannan kuma direban da ya kawota ma ta sallameshi, hakan ya kara ankarar da Inna tun zuwan Aneesa bata kula tana waya da mijinta ba sai dai tace yana mika gaisuwa. Don haka ne ta kirata tace "Uwani, ina fata dai ba matsala kika samu ba da mai gidan naki?"
Sai da gaban Aneesa ya fadi yaya akayi Inna ta gano ta?
Shirun da tayi yasa Inna ta hada daya da biyu. "Yanzu uwani ashe baki dauki duk abun da nake fada miki ba? Mutumin nan yana iyaka kokarin sa akan ki shine har zaki iya daga kafafu da sunan yaji ki bar gidansa? sannan ki shafe kwanaki ba tare da sanar da mu abun da kike ciki ba?"
"Inna ba yaji nayi ba, gidansu na koma kuma Hajiyarsa ta san nan na taho ita tace ma na zauna na huta tukun."
"Ita Hajiyartaku tace ki zauna ki huta? Haka ake aure? Ashe baza kiyi hakuri ki zauna a dakinki ba? Mu kinga muna kokawa kowa damuwarmu ne? ko kina tsamman kowa zaman lafiya takeyi da mijinta? Wannan ai rashin hankali ne kin kwashi kafa kinje kin zube a gidansu, an fada miki ita Hajiyar bata son danta ne, da zaki budi baki kiyi ta fada mata laifinsa?"
Aneesa taji ranta ya fara baci yaya Inna zata mata fada maimakon ta goyi bayanta?
"Inna fa ni ban fada ba, itace ta dage lallai sai ta san me yake faruwa"
"Da kinyi zamanki a dakinki, akwai wanda zai san kin samu matsala da mijinki bare har a so jin meye matsalar? watakila ma war haka da kun shirya komai ya wuce"
"Inna fa baki san me ya hada mu ba, har mari na sai da yayi fa"
"Sagir din ya mareki?" hankalin Inna ya tashi amma ta danne tace "Ba dole ya mara ba, tunda ke kowace magana aka fada kina da amsarta."
"Inna ke dai kawai kina goyon bayansa ne, amma yaya za ayi nayi shiru bayan yana zargin cewa wai ni da abokinsa muna soyayya."
Inna ta sa salati ta sanar da ubangiji "Uwani! me nake ji haka? me zai bashi wannan tunanin da har zai dau mataki a kai?"
Nan Aneesa ta bata labari tun daga zuwan Mummy gidansu abun da ya faru.
"Ashsha, komai ai dan bincike ne da bin diddigi, kafin a yanke hukunci ko a zartar da tunani." Ita dai Aneesa maimakon ta zo gaisuwa ta koma ta kara jibgawa marar lafiya damuwa. Shigowar malam Habu Inna Halima ta masa bayanin abun da a ke ciki, wannan yasa ya kira Aneesa yace "Innarki ta min bayanin komai, amma ina son ki san cewa kece kasa da mijinki, hakuri zakiyi ki koma idan yaso a dakinki sai ayi muku sulhu, amma tahowarki gida ba shi zai yi maganin matsalarki da mijinki ba, don haka kiyi hakuri ki shirya ni da kaina zan maidake sai a zauna ayi magana"
Aneesa ta hada rai tana tuno duk abun da Sagir ya fada hade da marin da ya wanka mata, nan ta tuno zaman yunwan da Innarta tayi a hannun Daddy a ladabce tace "Baba, kayi hakuri amma ni kam bazan koma gidan Sagir ba har sai ya zo da kanshi."
Inna ta kama baki tace "lallai kuwa kina da aiki, da wannan taurin kan naki kike so kiyi zaman lafiya da miji? An gaya miki mu abokanan wasan ki ne? ko kuwa so kikeyi kema ki zauna ki haihu a gaban mu sunan mu ya sake baci a gari?"
"Inna naga halin rayuwa da kika fuskanta, kin kuma ban labarin wanda ban gani ba wannan yasa na dau alqawarin bazan bari na miji ya wulaqantani yanda ya faru dake ba, don haka idan har na bar gidan nan to cikin kima da daraja Sagir zai zo ya daukeni."
Inna Halima ta zabura zata kai wa Aneesa duka malam Habu yayi saurin riketa "Halima kar ki taba ta mana, ai abun baiyi zafi haka ba sai ki illata abunda ke jikinta. Tunda tace haka sai a saurara a ga zuwan shi Sagir din." ya juya kan Aneesa yace "Amma ina son ki san da cewa muddin nan da kwana hudu Sagir bai zo ba kafarki kafata zan maidake gidanki." Cikin tashin hankali Aneesa ta dago kanta amma da taga bata da wani zabi sai ta amince.
Dadinta daya shine Mama tana jin abun da ya faru ta tirje kasa tace ba abunda zai sa Uwani ta koma "Ina Haliman? Wato ita har ta manta wuyar da ta ciwo wurin namiji ko to ai kuwa mudddin ina raye sai na ji dalili, haka kawai yarinyar kirki ita ayi ta wulaqanta ta. Yi zamanki Uwani naga wanda ya saki komawa a garin nan"
Hankalin Aneesa yayi matukar kwanciya jin maganar mama ko ba komai ta san zata kwatar mata 'yancin ta, amma haka kawai Inna ta dau zafi, ita bata ga laifinta ba a wannan lamari shi yasa taji zuciyarta ta kara kissima mata jin haushin Sagir, gashi karatu yana ta wuceta.
Har tayi niyyar komawa gidan Mama saboda tana goyon bayanta sai kuma Mama tace mata "kiyi zaman ki a can, ni dai ina garin nan sai naji dalili ai kudi ba hauka bane, kema kina da gata wannan irin kazafi da me yayi kama?"
Hakan yasa Aneesa ta koma gidan Inna, tana shiru abunta, jira takeyi su Innan su mata maganar komawa ta tattara inata inata ta koma gidan Mama abunta, don ko baban Halima bai ce komai kan lamarin ba.
Har dai Abba ya dawo yaji abun da ya faru da farko ransa ya baci kan abun da Sagir yayi, amma sai Hajiya ta bashi hakuri tace ita ta san maganin abun.
Sagir dai yana kwance a kan kujerar falon gidanshi amma gabaki daya ba wai dadin rayuwar yakeji ba. ko ina ya duba bakin ciki ne a rayuwarsa. Ba abun da yafi damunshi irin yanda su Hajiya suka matsa masa kan maganar Aneesa, a hakikanin gaskiya shima yayi kewarta amma da zaran ya tuno furucinta na ranar sai yaji ta sane masa kwata-kwata. Ya rabu da Ummi ya saba amma ya rasa me ya sa Aneesa na nesa dashi amma yake jinta a duniyar da take kusa tamkar tana cikin jikinsa.
Idan ya tsaya tunani sai ya ga ta ina ya kuskuro, sai da ya bari ya fuskanci ko wacece Aneesa, amma hakan ya faru ko da yake wannan mai sauki ne, tunda amininshi da ya dade da saninshi ya san komai game da shi ya gagara gano cewa yana son matar da zai aura har ma ya aureta bai gano me yake ji game da ita ba, tabbas yayi babban kuskure. Sallama yaji a kofa ya mike yaje don ya duba ko waye.
Aadil ya gani a bakin kofar, lalle wannan shi a cikin marasa kunyar ma na gaban layi ne shi. Sagir bai ce komai ba ya maida kofa zai rufe, Aadil ya sa hannu ya tare. Sameeha ta fito daga bayan Aadil ganin su tare yasa ya bude musu kofar suka shigo ko kallo Aadil bai isheshi ba.
"Sameeha, sorry gidan ba mata ban san me zan kawo miki ba I hope you don't mind" Aadil ya kalli Sameeha duka sunga yanda damuwa ta bayyana karara a tare da Sagir. Duk da dai a bayyane bai bari hakan ya nuna ba amma da ya bude baki zai yi magana zaka fahimci yana cikin kuna da bacin rai.
"Uncle Sagir meye ne yake faruwa na samu labarin cewa Aneesa bata nan"
"Ina tsamman mijinki yana da amsar komai, ko kuwa shi ya turo ki ki tamabaya masa inda rabin ranshi take?"
Aadil yace "Sagir, me yasa kake hakane, maganar nan gudace ka tsaya ayi ta a tsanake mu fahimci juna amma baka bada hanyar yin hakan ba. Ta yaya kake tsamanin za a warware wannan matsalar?"
Sagir ya gyara zaman shi hade da harde hannayensa cikin juna tamkar yana sauraren Aadil.
"Naji na gode." ya amsa a karshe bayan Aadil ya kai aya.
Sameeha ta dubi mijinta sannan ta dubi Sagir "Uncle Sagir tabbas nice babbar silar wannan fitina da ta auku, kuma na gane kuskuren yin hakan da nayi da na rike sirrina da mijina mun zauna mun maganace wannan matsalar shin kana ga har wani zai san cewa a da Aadil ya taba son Aneesa? kar mu manta fa zuciya bata da kashi kuma ba yi da ikon juya AL'AMARIN ZUCIyarsa. Wai meye laifin Aneesa a wannan maganar? Ita da bata san hawa ba bata san sauka ba da zaka juye dukkan laifi ka daura mata? A ganina ya kamata ka kara tunani kan wannan maganar." Aadil ya mike Sameeha ta bi bayansa suka bar Sagir a zaune, ko kala bai ce musu ba.
Suna fita Sameeha tace "Kana ganin zai sauko?"
"hmm ni na san Sagir aje-aje zai sauko sai dai kuma wannan lokacin ne ban sani ba. kar ki damu gobe zan sake masa magana kafin nan abun da kika fada masa yau hala ya masa tasiri."
"to Allah ya kaimu"
Washegari Sagir na ofis tare da wani ma'aikacin sa "Yaya zaka yi min wannan shirmen, haka ake rubuta report, ina sauran bayanin? idan baza ka iya aikin ba akwai dubbai da suke nema, saboda haka ko ka gyara aikin ka ko kuwa na nemi wani" ya fada hade ta buga file din hannun shi a kan teburin, yana huci. shigowar Aadil ofis din ne ya sa ya sallami ma'aikacin, ya daga ido ya dubeshi. "Akan meye zaka zo kana huce haushinka akan wanda bayi da laifi?"
Sagir yayi kwafa "Ziyara biyu a awa ashirin? da fatan dai komai kalau"
Aadil yayi murmushi sannan ya ja kujera ya zauna "Sagir kana bani mamaki idan har na duba naga wai abu daya da bai dameka ba a rayuwa shi ne zai yi sanadin shiga tsakani na da kai"
"hmmm direct to the point ina son haka." Sagir ya fada hade da ajiye biron hannunshi mai dauke da logon kamfaninsa.
"Wai shin kana ga da na so Aneesa wa kaina Sagir, kuma tana cikin qaddarata kasan da cewa ko saninta baza kayi ba?"
"Hakan kuwa zai fi dacewa kaga duka zaku fi fahimtar juna tunda kauye kuka fito tunaninku iri daya ne, ko kuwa?"
"Ai ina tsamman babu wanda tushen sa birni ne tunda haduwa akayi aka tada birnin. Maganar dai ba daga nan take ba. Maganar da nake so ka fahimta a nan itace Aneesa bata da laifi. Tabbas na so ta, amma tunda aka sanya maganar auren ku na san dole na tsayar da kaina don kai ne mutum daya a duniya da zan iya rabuwa da komai saboda tsakanin mu ya kai haka. Nayi mamaki kwarai da har zaka bari son mace ya shiga tsakani na da kai. Ka bari karamar yarinya tana juya maka tunani yanda take so bayan ka taki matsayin juya mata daban-daban a sako-sako na kasar nan dama wajen ta. Me akayi akayi Aneesa da zata shiga tsakanin Aadil da Sagir?"
Sagir ya mike a fusace ya daga hannu tamkar zai kai wa Aadil mari sai kuma ya fasa "Ya isa haka bazaka shigo har inda nake kana fada min abun da yadace ba, ko kuma wace mata ya kamata na aura, idan kana da matsala da matata wannan damuwarka ce amma ina son ka san matsayarka a kan Aneesa zan iya fada da kowa don haka ka tashi ka fita min daga ofis."
Aadil yayi murmushi yace "Exactly, abun da nake so ka gane kenan Sagir, Aneesa itace rayuwarka shin kana ganin zaka iya bari wani fada kalilan tsakanin ka da tsohon aboki ya raba ka da abun son ka, jigon rayuwarka? Macen da kake tunanin ta zamo uwar 'ya'yan ka? ni dai Sagir Mustapha Daggash da na sani ba daga nan yake ba. Don me yasa zaka bari kuskuren da kayi a rayuwa guda daya yayi ta juya al'amuran sauran rayuwarka. Idan Ummi ta yaudareka ta ci amanarka wannan ba shi yake nufi duka mata haka suka taru suka zama ba"
"Aadil bana so ka sako min maganar Ummi"
"Don me yasa baka son na sako maka maganar Ummi, ka san da cewa ta dade da tafiya a rayuwarka amma har yau ita ce matsalarka a rayuwa, me yasa kullum kake kauce magana akanta? Idan har da gaske ka wuce shafinta a rayuwa me yasa kake making decisions saboda abun da ta maka a baya? Kar ka bari ta ci galaba a kanka. Duk da ban san me ta maka ba amma na san da cewa idan baka mance ba ka ci gaba da rayuwa tabbas zata hanaka gina kyakkyawar rayuwa da iyalinka da suka fi kowa muhimmanci a gareka"
Sagir ya zauna jiki a sanyaye kanshi a cikin tafukan hannunsa. A cikin ransa yace "Ya Allah, me na yiwa Aneesa me zata daukeni? Na rabu da ita da karamin ciki, Allah kadai yasan me take ciki a yanzu ko a wani hali take, tsorona daya kar ta kauracewa abinci na san ba karamin aikinta bane..." dago idanunsa da yayi ya hada da na Aadil yasa, yaji tamkar an zare masa tausayin Aneesa a ransa wani fushi ya kara harzuka sa abunka da AL'AMARIN ZUCI yana huci yace "Naji abun da kace, don Allah idan bazaka damu ba ina aiki."
Yana fada ya mike ya bude kofar ofis alamar Aadil ya fice. Ba tare da cewa komai ba Aadil ya fita daga ofis din.
Aadil yana fita Sagir ya dauki makullai da wayoyinsa ya fice daga ofis din, saboda a wannan lokacin bayi da natsuwar yin aikin ma gaba daya, komai ya ishe shi na rayuwar. Main house ya wuce bai tsaya ko ina ba sai dakin Hajiya, amma ya tadda shi a rufe.
"Yaa Sagir?"
"Aisha, ina Hajiya take?"
Aisha dai da ganin yanayin yayanta ta san yana cikin damuwa kwarai "Dazu ta fita zuwa asibiti gaisuwa."
Shafa kansa yayi cikin damuwa ya fita ba tare da cewa komai ba, Hajiya kawai yake son ya yi magana da ita ko zai samu saukin damuwar da yake ciki. Gida ya koma yayi shirin masallaci tunda ko ya fita bai koma gida ba, sai da aka ce masa za a rufe masallacin.
Kai halin da zuciyarsa ke ciki a wannan lokacin baya ji zai iya jira har zuwa washegari ba tare da ya sata a idanu ba, domin ya rasa natsuwarsa gaba daya. Madaidaiciyar jakarsa ya dauka ya sa kaya kala uku a ciki da abubuwan da zai bukata na amfani, domin ya yanke shawara zai je ya taho da Aneesa.
Har ya daga waya ya kira Malam Hassan saboda ya shaida masa batun tafiyar sai kuma ya fasa saboda bai san iya lokacin da zai dauka ba. Kamar gari bazai waye ba yake ji, daga sallar asuba ya kama hanya.
****** **********
Tana kwance a daki duk duniya ba abun da yake mata dadi, gashi a daren jiya ta fara jin cikin jikinta ya fara motsi, duk sanda ya motsa sai ta tuna Sagir, wai shin me ya hana shi zuwa? Har yanzu fushin yake yi da ita? Yanzu ashe da gaske Sagir yakeyi yana tunanin zata iya son wani da na miji musamman abokinsa? Mamakinsa kwarai takeyi idan tana tuna kalamansa. Idan yana tunanin ya iya fushi ya tsaya tukun yaga nata kalan fushin, zai ga HUKUNCIN 'YA MACE. Duk randa yazo ko kallon shi bazatayi ba, idan ya ga dama ya koma ba ita amma ba ruwanta dashi. Haka kawai ya hadata fada da Innarta sannan ya hanata zuwa makaranta.
Ita kadai sai kunkuni takeyi da zuciyarta sai ga Muhammad ya shigo da gudu cikin dakin. Yana shigowa ta tashi da niyyar yayyafa masa fada amma yace mata "Adda Uwani, ga nan Uncle Sagir yazo yana dakin bakin Baba"
Kaman a mafarki taji kanta, ta bude idanu ta lumshe alamar kawar da tunanin da ya zo mata, sai taji Muhammadu yace "Naje nace kina zuwa?"
Da sauri ta rike hannun shi tace "Kaje kace ka samu ina bacci."
Muhammadu yaje ya dawo yace "Wai to yaji nace miki ki kunna wayarki"
Aneesa ta riko hannunshi tace "Me kace masa?"
"Cewa nayi kince kina bacci"
Aneesa taji kaman ta make keyarsa "wa ya ce maka haka ake aika? ka tafi kaje kayi karatunka." Tana zaune tana auna zuwanta da zamanta ne Inna ta dago labulen dakin nata tace "Ashe ba tun dazu nake jin Muhammadu yana ta sintiri a dakin nan ba? Ko ba mijinki bane yazo? Ni zan kai masa ruwa kina kwance bayan ya taso daga nesa?"
Jin Inna zata tada hankalinta yasa Aneesa ta tashi ta dauki mayafinta ta nufi dan karamin falon Malam Habu.
Idanun Sagir suna kan kofa yana sauraron shigowarta gaba daya ya kagauta da son ganinta har yake ji da zata kara wasu mintoci bata fito ba zai iya shiga cikin gidan.
Tana shigowa ta samu wuri ta zauna, amma abun mamaki ta nemi duk abun da ta shirya fadawa Sagir ta manta don tsabar fushi da haushinsa da take ji komai ya shallake tunaninta. Taki cewa komai gudun kar garin magana ta fadi asalin abun da take ji a wannan lokacin.
"Uwanin Inna yau ko gaisuwa Uncle Sagir bazai samu bane?"
Aneesa ta kara hada rai ganin bata da niyyar magana yace "Da alama dai yawan yin fushina ya shafe ki, amma amin afuwa. yaya kike da baby?"
lalle ma wannan ya ma gama raina mata hankali ya dauka zai dauko kafafunsa ya cika ta da surutu sannan tace ta amince dashi ta bishi zooo kamar wata rakuma?
"Babyn ka lafiya kalau, idan ka gama zan iya shiga? Dama Inna ce ta sani kawo maka ruwa."
Sagir shiru yayi ya koma cikin kujera yana kare mata kallo. Wannan ya nuna masa Aneesa ba yanzu zata sauko ba, amma sannu a hankali ya san zata bude cikinta. Don haka yace "to ba laifi tunda bakya son muyi magana zamu karasa idan munje gida, baki san da zuwana ba don haka zan barki ki gama kimtsawa da safe zan dawo sai mu tafi."
Aneesa tace "oh, ni na ce maka zan bika? ina tsamman baka fahimceni ba tukun ba da kai nazo ba haka ba da kai zan koma ba don haka zaka iya tafiya"
Ta mike zata bar falon Sagir yayi saurin mikewa ya rike hannunta ba shiri ta juyo ta hadu da jikinsa.
"Tunda har na taho kina tsamman zan koma ni kadai ne? lalle yarinya har yau baki san waye Sagir ba"
Aneesa tayi kokarin kwace hannunta da ta kasa tace "Ni kuwa na san waye Sagir da abun da zai iya yi don haka bana buqatar kasancewata tare da shi."
Murmushi yayi sannan ya riko fuskarta zuwa nashi. Ya mata abun da ya saba yi idan ya so rikitar da ita. Yana saketa ta juyar da fuskarta cikin jin haushi. "Sai da safe ki zauna cikin shiri karfe takwas ina hanya."
Abun da ya mata ya bata haushi matuka hakan yasa ta gagara ce masa komai, haka ta koma cikin gida.
Bata cewa Inna komai ba har sai bayan isha ana zaune ana hira a tsakar gida, Inna tace "Ni Uwani banga kin gama shiri ba, Malam yace sunyi da maigidan ki zaku koma da safe ko"
Aneesa tace "Inna fa ba haka mukayi dashi ba"
Inna Halima ta fusata tace "Sagir din ne zai yi karya ko malam? Bana son shashanci idan zaki mike ki je ki karasa shiryawa gwamma kin mike idan ba haka ba kuwa gobe yana zuwa ko da kayan jikin ki ne kawai haka zaki bishi ku tafi. Kaji min shirmen banza."
Jiki a sanyaye Aneesa ta shiga daki ta fara hada kayanta, can kuma ta wurga zani a akwatin ta zauna ta sa kuka, sai da tayi son ranta sannan ta hakura don kanta. Sannan su Inna ko su dan hora shi suce sai daga baya zata koma, amma daga zuwan shi harda amincewa ta bishi, gobe kam likida ta zai yi da duka tunda yaga ba a daukar mata fansa, dadin karawa kuma ta rasa me yasa Sagir yake dawainiya da rayuwarta? Idan tana tare dashi taji babu wanda ya kaita sa'a idan ta rasa shi taji babu wanda ya kaita asara.
Gashi Falmata tayi mata nisa da taje sunyi shawara, da sassafe ta faki idon Inna ta hada duk abunda zata bukata ta fice daga gidan bata tsaya a ko ina ba sai wurin da ya zame mata abokin hira lokacin da abokai suka mata karanci, wurin da ta kan samu kwanciyar hankali da nishadi, sai dai kuma tana isa wurin ba abin da ta tuna illa zuwanta da Uncle Sagir inda ya lallabata saboda ta bishi su koma. Ya zauna a bakin gaba a lokacin, Rafin kukanta ke nan. Nan tayi zamanta a gindin wata bishiya, me yasa duk inda taje a rayuwarta sai Uncle Sagir ya bita ne? Nan ta zauna ta bude jakarta, idan taji lokacin sallah ta bude jakarta ta fito da abin sallah, ta debi ruwa tayi alwala, idan ta ji yunwa kuwa daman da guzurin biredinta. Ta gama shirya plan dinta tsab cikin dare, don da ta koma da Uncle Sagir ya dake ta ko ya zage ta ya kala mata son abokinsa gwamma ta zauna a rafin Kukanta.
Karfe takwas a Kunuwal yayi wa Sagir, kai tsaye ya yi sallama gidan malam Habu. Kasancewar Inna ta san da zuwanshi ta tanada masa abun karyawa Amina ta kai masa, sai dai fa hankalin Inna ne ya tashi da ta shiga daki bata ga Aneesa ba. Ta duba bayi nan ma babu ita ba labari, don haka tayi tunanin tana gidan mama.
Sai da suka gaisa da Sagir ne tace "Ina ga Uwanin tana gidan Mama na sa Amina ta kirata."
"Ah, ba komai Inna zan karasa can saboda ta can na gaida su maman."
"To ba laifi, sai kun dawo."
Sai dai abu mai daure kai canma da yaje su mama sukace basu ga Aneesa ba tun wayewar garin yau. Da Inna ta samu labari sai abun ya dameta "To ina Uwani zata je? Ke Amina je gidansu Falmata ki duba Adda Uwani, kice mata maza-maza ta taho nan mai gidanta ya zo."
Suna zaman jira ne sai ga Amina ta dawo tana haki "Inna wai inji Innar Falmata wai itama bata je gidansu ba"
Inna ta kama haba cikin damuwa "Yau ina Uwani ta shiga zata jawo min magana, ban san wani irin taurin kai bane yake damun yarinyar nan."
Hankalin Sagir ya fara tashi ganin duk inda ya dace a je neman Uwani anje ba a sameta ba.
Wasa wasa har yamma ba labarin Uwani, don haka Malam Habu yaje ya samu mai gari ya fada masa abun da ake ciki, nan ne yace zai sa yara su dubata.
Aneesa kuwa tana ganin yamma ya kawo kai ta san cewa zama a rafin kukanta ya kare dole ta nemi wurin kwana. Don ta san har yanzu sarkin nacin nan bai tafi ba. Kai tsaye ta san inda zata je kuma ba wanda zai neme ta a can, ta kama hanya fuskarta a lullube bata tsaya ko ina ba sai gidan Fatu kanwar Na Ta'ala.
Hankalinsu Inna kam yanzu ya gama tashi, saboda harda Sagir a yawon nema amma sam ba sa'a, don haka malam Habu ya same shi yace "Ina ga ya kamata, kaje haka ka huta zuwa safiya mu san abunyi in sha Allah. Tunda mai gari ya sani to in sha Allah za a sameta cikin gaggawa"
Sagir ai baya jin zai iya barin Kunuwal ba Aneesa don hankalinshi dubu ya tashi , Ina zata je? Duk ni na jawo, girman laifina yasa ta gujeni har ta gwammace tasa Innarta a damuwa saboda ni. saboda bata son ta bini mu koma. Please Aneesa where are you?" Nan abun ya fado masa, rafin Kukanta, yes!
Tana ganin kafa ya lafa gari ya soma shiru, nan ne tsoro ya kamata, a hankali ta lallaba tana tafiya ba abunda take tunani sai irin abun da yake faruwa a gida, don tunda take bata taba guduwa ba sai yau.
Fatu na daya daga cikin mutanen da suka goyi bayanta lokacin gurminta da Na Ta'ala har ta so ganar dashi amma yaki saurarenta. Aneesa ta san mijin Fatu matukin mota ne saboda haka ba ko yaushe bane yake gari, don haka fatan ta daya shine ya kasance yau ma baya gari. A sace ta shiga cikin gidan
Motsi taji ta leko tana cewa "Waye ne?"
Aneesa ta bude lullubin da tayi wa fuskarta, Fatu tana ganinta ta zaro idanu. Ta sake rage su sannan tace "Waye kaman Uwanin Inna?"
Aneesa ta gyada mata kai gami da rage murya tace "Fatu nice"
A razane Fatu ta saki labulen dakinta ta fito tsakar gida "Lafiya na ganki cikin dare? yaushe kika zo?"
"Fatu taimakon ki nake nema"
Fatu ta dubeta cike da mamaki, yanda ta samu labarin Uwani ta zama babbar mutum wani taimako zata nema a wurinta yanzu?
"fada min Uwani wani taimako zan miki? don idan bai fi karfina ba zan miki in sha Allah, lokacin da ya kamata na taimake ki ban taimake ki ba."
Nan Aneesa tace so takeyi ta bata makwanci. kuma kar kowa ya sani.
""Gidan Inna fa?"
"Ina cikin wata damuwa Fatu da ba inda zan tsira sai nan, ba wanda zai yi tunanin zuwa nan ya nemeni."
"To shikenan, ba komai, bari na miki shimfidi."
Aneesa tayi ajiyar zuciya sai dai Sagir ya tattara muguntar shi ya koma amma bazata bishi ba.
Yana zuwa zuciyarsa ce ta kame saboda bai ga abun da yake tsammani ba, don kuwa wayam ya samu wurin, sai dai yaga wani abu a dunkule a gindin bishiya, da taimakon hasken da ke hannunshi ya haska sai ya ga sallaya ce nadaddiya. Ajiyar zuciya yayi "Alhamdulillah, Aneesa me yasa kike bani wahala?" Sai dai ya duba ko ina bai sameta ba. Don haka ya koma gidan Malam Habu a falon yayi zamanshi da niyyar asuba na fari can zai koma yasan zata je neman kayanta da ta bari.
Ai kuwa sai da hankalinta ya kwanta ne ta tuno da kayanta da ta bari a gindin bishiya, abubuwanta da dama suna ciki, sai dai yanzu dare yayi sai da asuban fari zata je ta dauko kafin ta san abin yi.
Tana sallah tace "Fatu ba abinda zance miki sai godiya, baki san irin taimako na da kikayi ba, Allah ya biyaki"
"Ameen, ai Uwani munyi zaman mutumci dake, kar ki fadi haka. Amma don Allah zan san me yasa kika bar gida har su inna bakya son ta san inda kike?"
"Hmm, ke dai kawai wasu matsaloline na samu yanzu shine suka matsa min wai sai dai na koma ni kuma bazan iya ba."
"To, ai wannan babban magana ce, ki tsaya mana a warware koma menene amma guduwa ba shi bane, ina zaki je idan kin gudu? Dole ki koma gida ki fuskanci komai." nan ta tuno abunda ta fadawa Sameeha kenan da ta samu matsala da Daddy.
"Tawa matsalar daban ce, bazan bari nayi irin rayuwar da Inna tayi ba Fatu."
"To amma ni kuwa sai nake ga kamar ke kike sa kanki a wannan halin, yanzu kina wahalar da kanki ga ciki a jikinki, ina zaki shiga wanda ya wuce ki komawa mutanen da suka fi kowa kaunarki, kowa da kika gani hakuri yakeyi sai dai na wani yafi na wani."
Aneesa dai jin Fatu takeyi "Na gode Fatu, Allah ya saka da alheri. Sai kin ganni in sha Allah idan komai ya daidaita"
"Don Allah ki koma gida Uwani, na san da mijinki ne kika samu matsala ko?"
Aneesa taji mamakin yanda fatu ta dago ta "ke kam ki bar maganar kawai."
"Allah yana son ki, don yanda Nata'ala ya ban labarin mutumin na san haka, ya fada min yanda ya damu da al'amarinki sosai. Hakan yasa yace ya san zai kula da ke sosai."
Fatu bata san me take fada ba sannan bata san matsalarta ba, mutumin da yake son ka ne zai fadi abubuwa a kanka wanda basu dace ba? "Shi kenan zan duba maganarki, ni na wuce"
Nan sukayi sallama ta koma rafin saboda ta kwaso abubuwanta tayi zamanta a wurin ta san zuwa yamma zai koma idan bai sameta ba, tunda lokacinsa na da matukar muhimmanci a kamfaninsa. Tana isa gindin bishiyar ta sunkuya zata dau jakarta sai ta ga wayam, ta juya bayan bishiyar nan ma bata ga komai ba sai hankalinta ya tashi, wa yazo nan cikin dare ya dauke mata abubuwanta?
"Wannan kike nema?"
Muryar da taji ne ya matukar razana ta ta juyo tana kallon shi, jikinta na rawa tamkar taga zaki. "Uncle Sagir?"
"Kina tsamman akwai inda zaki shiga a garin nan na gagara samoki ne?"
"Ni ba guduwa nayi ba" Ta fada a dake tare da dauke fuskarta. Ga wani dan karen sanyin da ake zubawa.
"To idan ba guduwa kikayi ba, ki zo mu tafi. Don na gaji gida nake son na koma"
cikin haushi ta kalleshi "oh ka daina yawo a jirgin ne yanzu?"
"Tunda ina tare da sarauniya kam ai sai yanda tace za ayi, idan bata son shatar jirgi ai dole na na hakura."
"Na zaci saboda zaka iya ne ya sa kake yawo a jirgi me ya canza? Ni bazan bika ba"
"Kiyi hakuri ki zo mu tafi, kin san kin gajiyar dani jiya ba wanda yayi bacci a gida, Inna ma jiranki takeyi don haka kizo muje ta gama miki fada mu tafi."
Idanu ta zare a hankali tace "Mugu!"
"Me kika ce?"
"Babu, ni fa ba inda zan bika muje, gwamma ka kama hanya ka tafi."
"Duk abun da zaki ce dai ki bari sai munje gidan Inna tukun."
Ta dago idanunta dasuka kumbura sukayi ja sannan tace "oh saboda ka samu masu tayaka fada ko? Ai na san ba abun da zai gagari the rich SD, haka nan rayuwar kowa a matsayin wasa take a wurinka, saboda haka ba amfanin ja da kai a wannan maganar"
"Naji kawo hannunki" Hararar sa tayi sannan ta juya idanunta.
Ya sabi jakar tata, sai dai jinta yayi kamar dutse tsabar cika ta da akayi da kaya, ya dubeta 'yar ficila da ita "yaya akayi kika dauki jakar nan bata ka dake ba?"
Ko kulashi bata yi ba suka ci gaba da tafiya; tayi gaba yana bin bayanta, sai surutu yakeyi "Na fada miki ki bar daukan abu mai nauyi shine zaki kinkimi wannan jakar ki tafi da ita har rabin gari ko?" Bata ce masa komai ba sai tafiya sukeyi amma kafin ya ankara tayi wani wurin ta bace masa. Hannu yasa a goshi cikin damuwa.
Aneesa bata tsaya ko ina ba sai gidan mama, "Uwani ina kika shiga tun jiya kin daga hankalin kowa?"
"Mama guduwa nayi"
Salati Mama ta sa tana taba hannu, "Uwani guduwa fa kika ce?"
"Ni dai Mama da na koma gidan sa sai dai ku kasheni, amma ba inda zan je. Mugu ne kasheni zai yi wataran"
Ai ko nan da nan hankalin mama ya tashi ta jawo Aneesa jiki "ki kwantar da hankalin ki, Uwani. Ba inda zaki je kiyi zaman ki a nan bari shi Sangirun ya zo ya same ni haka kawai zai halaka miki rayuwa? an fada masa mu bamu son ki ne? Duk Halima ce ta biye masa"
Nan ta sha zamanta ta manta da anyi ruwan Sagir bare ma kuma ta san da shi a cikin garin Kunuwal, da azahar sai ga Inna ta sabo gyalenta, tun daga kofa take sababi "Ina uwanin yau sai ta gwada min wanda ta haifeta tunda ni ban isa ba."
Mama ta tari numfashin ta "A'a dakata Halima, meye kike ta wani tada jijiyoyin wuya?"
Inna dai ko daki bata karasa ba nan bakin tabarma ta dire, Aneesa ko na daki taki fitowa saboda ta san Inna zata tusa ta a gaba. "yanzu ke kin gwammace, 'yar ki tayi ta rayuwar wuya, irin wanda kika ciwo a gidan mijinki na da? To bari na fada miki ba inda zataje. Idan kuma dole ne to sai ya zo ya dauketa a gabana na gani. Kaji min kokari dai, haka kawai yarinya da juna biyu ya kama lillisa mata mari kaman an aiko shi? Har yau fuskar fa bata sabe ba."
Inna idanu kawai ta zuba kan tsohuwarta tasan tana biyewa Uwani ne kawai, har zata sa suji kunya yanzu wani abun zata je ta fada masa fisabilillahi?
"Mama, don Allah kiyi hakuri, ai bamu ce bai yi kuskure ba amma tunda ya gane har yazo don tafiya da matarsa ai inaga bamu masa adalci ba idan munce bazai dauke ta ba."
"Oh, so kikeyi mu masa adalci shi ya tozarta mu ko? idan yaje ya mata lahanin da yafi wannan fa? Ba inda zata koma, wani irin miji ne zai daki fuskar matarsa?"
Haka Inna tana ji, Mama ta gama bayanai kala-kala akan ita ba inda Uwani zata je, don haka ta koma gida ta fadawa Malam Habu yanda sukayi.
Hakuri ya bawa Sagir yace yaje ya huta, zasu shawo kan komai zuwa yamma in sha Allah duk yanda ake ciki da safe sai yazo ya dauki matarsa kafin nan sun mata nasiha.
Sagir yana mamakin kafiya irin ta Aneesa, yanzu a yanda taken nan duk taje tana wahalar da kanta, bata ma zauna ta huta wa ranta ba wai duk don tana gudun shi. Shin zai sake samun wuri a ranta bayan furucin da yayi mata?
Wunin ranar ne ya kunna wayoyinsa, haka yayi ta fama da jama'a amma sam hankalinsa baya jikinsa, yana gidanshi na Gombe don ya huta amma ya gagara sukuni, bare ya saurari wayewar gari. Gashi har dare Malam Habu bai neme shi a waya ba, don gajiya na tare dashi ne yasa yana wanka bacci ya daukeshi, amma can cikin dare ya farka, tunanin Aneesa ya hanashi sukuni. Alwala ya shiga yayi sannan ya soma nafilfilu.
Musamman Malam Habu ya tafi gidan Baba, domin dai wannan maganar sai ya gwada sa baki a ciki idan dai ta Mama ne to Aneesa tayi bye bye da gidan Sagir sai ko idan ita ce tayi amanna tana so ta koma. Tana jin sallamar, malam Habu ta gyara mayafinta tace da Aneesa "Uwani koma ciki."
Ai kaman dama jira takeyi ya iso tayi wuf ta mike. Bayan sun gaisane Malam Habu cikin tattausar murya ya bawa mama hakuri, akan duk abun da ya faru ya wuce tayi hakuri ta bar Aneesa.
Cikin irin jin nauyin dake tsakanin surukai ba don ta so ba mama tace "Shi kenan tunda kace, amma dai ina son ya barta ta huta tukun sannan ya dauke ta, sannan idan ya zo ina son ganinsa."
"To ba komai, Mama Allah ya kara girma, in sha Allah zamuyi waya. Ina ita Uwanin?"
Sumui sumui ta fito daga daki, ta gaishe shi, ganin haka Mama ta mike ta basu wuri. Wannan ne karo na farko da ta ga bacin ran Malam Habu sosai "Yanzu Uwani ashe haka kike da kafiya da son zuciya?"
Shiru tayi tana wurli-wurli da idanu. "Abun da bai kai ya kawo ba, kin tada hankalin kowa da kowa saboda wani dalili naki na daban? Kin azalzali ran innarki tana cikin bacin rai don haka nake son ki zabi abun da kika ga ya dace, domin dai muddin kika kashe aurenki to sai dai ki nemi wani wurin zuwa ba gidana ba, don bazan bari ki saka Halima cikin wani kunci ba a rayuwa."
Kuka takeyi sharbe sharbe har da majina yana gamawa ya kama hanya ya tafi. Haka dai ta kwana cikin juyi sai wani sarawa da taji kanta na yi.
Ai kuwa da safe tara bai rufa ba sai ga Sagir a gidan saboda ya samu sammacin Mama, tabarmanta sabuwa ta shimfida masa ta bashi abun kari mai kyau sannan ta zauna, Uwani na zaune a kan kujerar tsugunno dake bakin kofar dakin Mama, banda kunkuni ba abun da takeyi, ita a dole mai fushi.
"Kai malam Sangiru haka akeyi ne? kuma daga baka kawata sai kaje kana bata wahala don kishi ya maka yawa?"
Jikin Sagir a sanyaye yace "Mama, tabbas anyi kuskure kuma an samu sabani sosai, amma dai kam in sha Allah hakan bazai kuma faruwa ba. Kin san AL'AMARIN ZUCI mutum baya iya juyasa sai bayan ya aikata yake da na sani, amma na miki alkawari in sha Allah bazaki kuma jin makamancin hakan ya sake faruwa ba."
Mama ta nisa sannan tace "To, naji dadin hakan, don ta ni kam da yanda ka ga Uwani to haka zaka juya ka tafi bazan baka ita ba. Amma yanzun ma bazan amince ba sai kunyi magana ta yarda da bakinta sannan."
Sagir dai mamakin karfin halin tsohuwar yakeyi, amma sai yaji ta burgeshi. Daki ta ce su shiga su tattauna, Aneesa ranta a cunkushe ta kare masa kallo sai shine ya soma magana.
"Anee, ban san ta inda zan fara ba. Na san duk abun da zance yanzu bazai miki wani tasiri ba kasancewar kina cikin hali na fushi. Kin cancanci kiyi fushi dani, amma ina son ki san cewa na amince da kuskure na, kuma hakan bazai sake faruwa ba da yardar Allah. kiyi hakuri ki bini mu tafi."
Kanta na kasa har ya gama, ba tare da ta tankawa batun sa ba. Sai da yayi shiru tace "Ina son ka san zan bika ne saboda abubuwa guda biyu, na farko nayi alwqawari wa Hajiya cewa zan koma idan naga jikin Inna ya lafa. sannan na biyu kuma na kudurta a raina bazan sake barin Inna ta shiga wani kunci ba idan har ina da ikon kawar da hakan, idan banda haka ba inda zanje. Sannan abu na karshe bazan bika ba sai ka amince da sharadi guda"
Sagir yayi shiru shi dai yau yana ganin ikon Allah "Naji ina saurarenki, menene sharadin? kusan cikin zakuwa yake tambayar, don ba abunda yafi masa dadi a maganarta illa ta amince zata bishi.
"Duk randa ka sake daga hannu ka taba lafiyar jiki na ko Abuja ka kawo Kunuwal bazan bika ba, na dawo kenan"
"Na amince, amin afuwa wancan ma idanu na ne suka rufe..."
Dakatar dashi tayi tace "Mu tafi kan na canza ra'ayi na"
"To rankishi dade"
Ya fito ya samu Mama a fafarandar ta, gefe ya samu ya zauna, sai ga Aneesa ta fito da mayafinta tace "Mama na amince zan bishi mu tafi."
Mama ta kama baki cikin al'ajabi, "Ke dadi miji ko? To Allah ya sauke ku lafiya, nan gaba ki nemi gidan zuwa, daga zuwanshi har ya miki dadin baki zaki tafi ki barni."
Sagir yace "Mama, gani dai a zaune ki daina min bakin ciki mana, bayan ke baki taho ba sai kuma ki hana ta tafiya?"
"Ku dai kuka jiyo, Allah ya raka taki gona."
Aneesa dai jin su takeyi batare da ta tanka ba. Sagir ya sallami Mama sannan suka wuce gidan Inna tare da Aneesa.
Suna zuwa cikin gida Inna ta dauko muciya ta bita dashi, Malam Habu yace "Halima kyaleta, ba ta dawo ba me ya saura kuma? Ina shekaran jiya wuni kikayi kukan rashinta?"
Inna na tsuma ta hau Aneesa da balbalin bala'i. Ta mata fada har ta gode Allah sannan ta bawa Malam Habu fage, shima dai jan kunnen ta yayi akan duk rintsi kar su kara ganin ta zo gida saboda wani rikici tsakaninta da mijinta.
Tana ji tana gani Sagir ya rabata da gida, Allah kadai ya san me ya tanada mata idan ta koma, a mota suka tafi bata cewa uhm ko uhm-uhm bai nemi ya isheta da surutu ba. Ko sun tsaya cin abinci sama-sama ta taba ya nemi ya mata magana ta hade rai, haka dai yayi shiru suka ci gaba da tafiya.
Suna isa ta haura dakinta ta karkade kura ta wanke bandaki sannan ta shiga wanka. Sai da ta kammala shirinta sannan ta sauka zuwa kicin, tana kokarin hada abinci ne ya shigo kicin din ya sameta, "Yanzu duk gajiyar hanya da kika dauko me zai sa ki shiga kicin?"
Bata ce masa komai ba ta ci gaba da aikin ta zuwa yayi ya kashe gas cooker din ya riko hannunta "Magana nake miki, kuma idan ina magana saurarona akeyi saboda haka ki saurareni."
Duk da cikin tsattsaurar murya Sagir yayi maganar amma Aneesa tayi kwafa tace "Don kowa yana sauraronka sai kayi tsammani nima zan saurareka? Kar ka manta kudi fa ba shi bane kiman dan adam."
"kina stressing kanki, na fada miki ki kwantar da hankalinki. Yanzu ba lokacin da zamuyi magana bane"
"Ni bance maka zanyi magana da kai ba, kalen ka min mummunar fassara?"
Aneesa ta sa kai ta bar kicin din, Sagir yayi ajiyar zuciya yana binta da idanu. Tana barin kicin din daki ta koma ta kama sana'ar kuka, ga wani matsanancin ciwon kai dake addabarta kwanaki hudu kenan a jere. A daddafe ta sauko kasa wurin da suke ajiye magunguna saboda ta samu ta sha ko zata ji saukin juyawar da kanta ke yi. Tana tsakiyar falon Sagir ne taji wani jiri ya kwasheta, ba shiri ta zube kasa. Ta dauki kusan minti ashirin a gurin kafin Sagir ya zo kashe wuta, nan ya sameta a zube. Hankalinsa ne yayi mummunar tashi
"Inna lillahi wa inna ilaihirraji'un, Aneesa!" ya fada yana taba kuncinta, amma bata motsa ba. Da sauri ya nemi ruwa ya watsa mata a fuska, wayarsa kawai ya dauka da makullin mota ya zuba a aljihu sannan ya dauko hijabinta ya zura mata, ba tare da ya jira ta karasa farfadowa ba ya sunkumeta sai mota.
Kallon likitan yakeyi kamar wanda ya rikide zuwa fatalwa, "Yanzu likita kana so kace min jinin Aneesa ne ya hau sosai har ya haddasa mata faduwa?"
"Eh, kwarai kuwa. An yi sa'a ma da bai taba dan cikinta ba kasancewar bayi da kwari sosai yanzu. Saboda haka sai an kula sosai. Yanzu mun saka mata ruwan allura a cikin drip dinta, zuwa safiya dai zata samu isasshen hutu sannan mu sake gwadawa mu gani. Ina sa rai magungunan da na bata zasu saukar da BP din."
Hannu bibbiyu Sagir ya sa ya dafe kanshi cikin dimuwa yanzu shi ya haddasawa Aneesa hawan jini? Wai me yake tunani ne da har zai iya cutar da dan adam haka, bayan kasancewarta mutum ma macen da yafi so bayaga Hajiyarsa?
Shi ya kwana a kanta, ga gajiya shima da yake fama dashi amma haka ya mance da tashi gajiyar, fatansa Allah ya bawa Aneesansa lafiya.
Da safe sai ga wayar Hajiya, Sagir ya daga suka gaisa. Hajiya tace "Kana lafiya?
"Lafiya, alhamdulillah." ya fada a raunane.
Hajiya taso ta karanci damuwa a muryarsa amma tasan ba a rabe dayan biyu, yanzu haka baya wuce kan maganar Aneesa ne.
"yanzu Sagir fi sabilillah, ashe bazaka hakura da fushin kan nan ka dauko yarinyar nan ba, gashi lokacin awunta na karatowa ta samu kula ta musamman, amma ka zauna sai fushi kakeyi na wofi wanda bansan ka dashi ba. Ka ga hakan da kakeyi ya dace kenan?"
Sagir yayi ajiyar zuciya yau kam bai san yanda zasu karke da Hajiya ba, "Hajiya ai na daukota jiya da dare muka shigo gari."
"Ah to abu yayi kyau, sai dai na san tana cikin wahala ga gajiyar hanya, me zai hana ka kawota nan ta dan kwana biyu kafin nan ta karasa warwarewa sai ta dawo"
"Ai hajiya gamu nan a asibiti ma bata ji dadi ba, tun jiya likita ya bata gado amma dai da sauki."
Cikin damuwa Hajiya tace "Aneesan take asibiti tun jiya, shine sai yanzu da na kira zaka fada min? Wai kai me kake shirin dawowa ne Sagir? " HAjiya ta ja tsaki domin bazata tsaya bata lokacinta a kan Sagir ba, domin taga alama ya riga yayi nisa, cikin hanzari ta shirya ta sa direba ya kaita asibitin da su Sagir din suke zuwa.
Ai tun kafin ta iso ya shaidawa likitan baya son kowa ya san abun da yake damun Aneesa.
"Gaskiya, kana ban mamaki, kaga yanda fuskar yarinya ta canza a dare daya kacal wai shine zaka ce da sauki?"
"Hajiya kiyi hakuri cikin dare muka taho asibitin, na zaci ma duba ta kawai likitan zaiyi to sai yace, bata da karfi sosai shi yasa ya daura mata ruwa."
can sai ga Aisha ta taho da abinci zuwa lokacin Aneesa ta tashi daga baccin da ta kwana tana yi. Da ikon Allah ciwon kan ya daina, sai tsamin jiki. Batayi mamakin ganinta a asibiti ba saboda ta san azabar da ta sha a jiyan. Ta yunkura zata gaida Hajiya da Abba da ya iso a lokacin ne Hajiya tayi saurin kwantar da ita.
"Sannu, ki rinka yi a hankali kinji ko?"
Kai ta gyada sannan suka gaisa. Likitan ya shigo ya sake dubata, nan ne ya shaida musu zuwa yamma zata iya komawa gida matukar zata samu isasshen hutu, amma kafin nan sai ta karasa drip din da ya daura mata da safen.
Daddy ya iso asibitin bayan Sagir ya shaida masa Aneesa na kwance, sai da suka rage su biyu a dakin yake cewa "Aneesa, wato abun da yake faruwa shine banda labari? Ashe idan kina da matsala bazaki sameni ba?" cikin jin nauyi tace "Daddy fa ba haka bane."
"To yaya ne? Sameeha ta fada min komai ai. Daga yau duk wani abun da zai tashi maza maza ki fadi damuwarki kar ki kara cewa zaki tafi."
Kai ta daga masa kawai tana shiru.
Sagir kuwa yana ta sunne kai, tsoron kar a gano karyarsa. Jin Hajiya tana ta bawa Aneesa shawarwarin da ya kamata tabi tunda ga halin da take ciki yasa hankalinsa ya kwanta. Banda sintiri ba abunda yakeyi har zuwa dare aka sallamesu.
Suna shirin fita daga dakin ne, Hajiya tace "Ai ina ganin tunda ga yanayin jikin nata, me zai hana ta koma Main house ta dan kara murmurewa kafin nan?"
Sagir yana tunanin abun fada ne yaji Hajiya tace "Aisha, saka jakarta a motar Jibrila, kice su shirya komai da kyau." Aisha ta amshi 'yar jakar da ta je ta shiryowa Aneesa, tayi waje da ita. Aneesa ko dadi fal ne a ranta ganin Hajiya tace ta koma wurinsu. Saboda ko yawan shigowarsa dakin da take a asibitin ma haushinsa yake kara mata duk da tana jin tausayin yanda ya kwazarbabi kansa ya damu da ciwonta amma haushinsa da take ji sai ya rinjayi tausayin, saboda haka tamkar ta zuba ruwa a kasa tasha taji da Hajiya ta saka ta a motar gidan Abba sukayi gaba.
Sagir dai cikin sanyin jiki aka barshi, yanzu yana tare da Aneesan ma yana samun matsala wurin shawo kanta bare an sake nesanta su kam ai sai ta Allah. Ba yanda ya iya Hajiya ta riga tayi magana. yana ji yana gani suka tafi masa da mata ba yanda ya iya, amma ta wani bangaren suna da gaskiya, don ciwonta ya tsorata shi, idan nisantarsa zai sa ta murmure to zai daure har sai randa ta sauko su fahimci juna.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top