BABI NA ASHIRIN DA BIYU
BABI NA ASHIRIN DA BIYU
Sagir ya tafi ofis, Aisha da Aneesa suka je suka dauki kayanta, ta hada kayanta sosai a babban akwati ta kwashi takardun da zata bukata. Sannan sukayi gaba, Sagir kuwa tun safe ya rasa me daya yake masa dadi.
Komawarta da kwana biyu Sagir ya je makaratarsu, yayi magana da principal a kan Aneesa kasancewar hukumar makarantar sUn san da aurenta, gashi tana fama da laulayi hakan ya sa yace zata bar zuwa har sai lokacin jarabawa ya karato tazo ta zana.
Lesson teacher ya sama mata, tana zuwa har main house suyi karatu.
Hajiya da kanta ta sa Aneesa a mota suka wuce asibiti ta mata booking antenatal. Aneesa ba abun da yafi mata haka kwanciyar hankali.
Washegarin randa suka dawo daga asibiti ne Sagir ya shiga dakin Hajiya, nan ya sameta tana kwance tana jin shigowar Sagir dakin amma tayi kaman tayi bacci don haka ya kyaleta.
Kullum Sagir sai yazo gidan da dare a nan yake hira sannan ya koma gida amma ko fuska baya samu a wurin Hajiya bare ya samu ganin Aneesa, kullum suna manne bare ya samu ya mata magana. An dauki sati a haka, wannan yasa Sagir ya samu Abba.
"Abba daman maganar Aneesa ne, tunda na ga ta dan samu karfin jikinta batun komawarta gida" Duk sabon shi da sakewarsa da Abba ta maza kawai yayi ya yi magana.
Abba yayi kamar bai fahimce shi ba "Ah, har sun gama jarabawar ne?"
Sagir yayi tunanin daman wai suna shirin rike masa mata har sai tayi jarabawa ne?
"Abba jarrabawa kuma?"
"Ka san a wannan yanayin nata tana bukatar hutu sannan ga karatu a gabanta, duk da akwai mai tayata aiki idan ta koma ina ga stress zai mata yawa, saboda haka inaga ka dan kara barinta a nan ta kara hutawa."
Cikin jin nauyi Sagir yace "To shi kenan Abba."
Ya kula kaman wani hadin baki sukayi masa ga uwa uba kwata-kwata wayar Aneesa a kashe ya rasa me yake masa dadi.
Ranar ya gaisa da Hajiya a daki fitowarsa falonta ya samu Aneesa ita kadai ce a nan tana karatu don haka yayi tunanin amfani da wannan damar don ya mata magana, amma cikin ikon Allah ya zauna kenan sai Hajiya ta sa baki ta kira Aneesa wai ta tayata sa kaya a wardrobe, ran Sagir ya baci ita da tazo hutawa bata da lafiya kuma wani aiki kuma za a sakata, sannan mutum da matarsa an haramta musu ko da magana ne bare su kebe. Haka ya mike ya bar gidan jiki ba kwari.
Randa Aneesa ta cika sati biyu a main house ne Sagir ya yanke abun yi don ya kula idan ba ya dau mataki ba abubuwan sa gaba daya zasu daina ci gaba, don yanzu haka ma ya daga tafiya zuwa kasashe biyu saboda rashin sanin madafa.
Aneesa ta gama hira da su Aisha da Hajiya ranar Kamaal ma yana gida sai wajen karfe goma tace musu sai da safe.
Shigarta bangarenta taji mamaki kasancewar a kashe ta bar wutan cikin daki gashi kuma ta same shi a kunne. Don haka sai ta bari akan ta manta ne bata kashe ba ta fita. Ta nufi jikin wardrobe don daukar kayan baccinta ne sukayi ido hudu dashi, da sauri taja da baya tsabar tsoron da taji.
"Subhaanallah. Ka ban tsoro, me kakeyi a nan baka tafi ba?"
"Yaya za ayi na tafi matata tana nan." Ya fada yana duba wani littafinta da ya dauka a durowar gefen gado.
"Idan su Hajiya suka san kana nan..."
Nan ne ya dago kan shi yana dubanta "wai me kika fadawa Hajiya ne take goyon bayan ki haka, me yasa baza kiyi hakuri ba, ban san meyasa kike hukuntani haka ba. Please ya kamata yanzu ki bari haka nan ya isa"
Aneesa ta kankance idanunta, abun da Sagir ya mata laifin sa daban, amma ya rinka daukar laifin ba a matsayar komai ba shi yafi cusguna mata rai. Don haka tace "Ni kuma me nayi? A gaban ka Hajiya tace na taho nan na huta kafin na samu kwarin jiki, har zuwa lokacin da zan gama jarabawata."
"Amma idan kika nuna zaki iya zama a gidanki ba me cewa ai ki zauna a nan, me yasa zaki biye musu?"
Ranta ya gama kai kololuwa wajen baci, cikin kankance murya kasa da nashi tace "Biye musu? kasan me kake fada kuwa, kana magana tamkar ka manta komai. Ko don kana tunanin ka boyewa su Hajiya abun da yake damuna ni zai buya a wurina? So kakeyi na bika ka karasani da hawan jini ko kuwa ciwon zuciya kake son ka bani wanann karon?"
"yaya za ayi ka manta irin zargin da ka min Uncle Sagir? Ko bakayi tunanin illar da hakan zai haifar a rayuwata ba? Na sakankance na yarda da kai na baka soyayyata, na amince da kai koda kuwa yin hakan ba karamin abu bane a gareni ka nuna min kana tare dani bai kamata naji tsoron rayuwa ba... lokaci daya ka rusa komai ka nuna min bani da wani matsayi ko daraja a rayuwarka, Sagir kana sane da halin da nake ciki ka dauki hannu ka mareni, cikinka ne a jikina ka taba lafiyata, da wani abun ya same ni kai kam ba ruwanka tunda bani a bakin komai a rayuwarka. baka da asara.
Nayi wa kaina alqawarin bazan auri mijin da yake daga hannu a kan matarsa ba sai dai ka sauya dare daya ka canza kamanni ka sa na maimaita kuskuren da Innata tayi. Akan me yasa kake tunanin zan saurare ka? Ka san yanda mutum yake ji kuwa idan an masa mummunar zato? Baka sani ba ni zan fada maka. Gari guda sun juya min baya akan mummunar zato kai Sagir kaine ka fiddo ni daga wannan ramin da na fada na firgici da tsoro da kin rayuwa. Ka fada min yanda zanji lokacin da wanda ya bani SABUWAR RAYUWA ya kwace a lokaci guda?" Aneesa ta karasa maganarta cikin kuka mai shiga rai hawayenta suna zuba ba kakkautawa. Sagir ya matso kusa da ita a hankali yasa kanta a kirjinsa yana shafawa.
"Hakika ni mai laifine sosai a gareki, laifin da ko ni bana iya kallon kaina idan na tuna shi. Na san na muzanta sunan yarda, nayi miki mummunar zato sannan na yanke hukunci cikin fushi. Amma duk abubuwan da nayin nan Aneesa ina son ki san daidai da rana daya zuciyata bata amince da zargin da take miki ba, wani fushi marar amfani ya kaini ga aikata abun da na aikata. Rashinki a gareni ba karamin gibi ne a rayuwata ba. Duk son aikina bana jin dadin yinsa, idan ina dakin taro banda kuncin rashinki ba abun da yake gabana. I lost my essence, ina matukar bukatarki a tare dani Aneesa please come home."
Aneesa ta kara sa kanta a jikin Sagir tana kuka, ya dago kanta hawaye ne shar shar a hankali ya sa baki ya sumbaci fuskarta dai dai inda hawayenta ke zuba, ya goge mata su.
"Ki daina kuka haka, ya isa, Sagir ya daina sa Aneesa kuka in sha Allah"
Murmushi tayi cikin wani annashuwa mai tarin yawa. Tace "Har yanzu kana sonta?"
"Ina sonki Aneesa" Kanta ta girgiza alamar ba ita take nufi ba, ya dubeta cikin rashin fahimtar me take nufi "Ummi, har yanzu kana sonta? Na san zafin abunda tayi da gudan kar abun ya sake faruwa ya janyo mana matsalar mu, da kuma duk wani janyewa dakayi daga gareni tun farkon auren mu. Shin sonta ke saka..."
"Aneesa, ban taba tunanin bayan auren mu zan canza sosai ba kamar yanda na canza, da har sonki zai zame min jiki ya kuma juya min al'amurana, wanda har zai sa bazan iya rayuwa ba tare da ke ba face cikin kunci. Ina so ki manta da Ummi kaman yanda na zabi na mance da ita a rayuwata, KE NAKE SO kuma wannan bazai taba canzawa ba"
Murmushi tayi mai dauke da nishadin jin maganganun Sagir. "Me tayi maka ya haddasa maka wani abu a rayuwarka?"
Sagir ya nisa ganin Aneesa ta sa shi a gaba yace "Ta canza, ta soni kafin auren mu, ko kuwa abun da nayi zato kenan, sai dai kuma bayan ta aureni ta ga irin dukiyar da nake dashi dani da iyayena, sai suka canzata, ta sa buri a rayuwarta ya zamana ba abun da take so illa kyale-kyale, ta canza kawayenta da yanayin shigarta abun har ya kai ga..."
Sagir yayi shiru kaman yana fafutukar fadin abun da yake ransa, Aneesa ta sa hannunta ta rike nashi hannun. "ya zamana ko auratayya bazatayi dani ba sai ta san akwai abun da zata samu a ciki, daga baya ta daina kulani duk juyin duniyar da zanyi, ga bin wasu kawaye da takeyi marassa kan gado, duk a tsawon wata nawa da aure, mamakin ta ya kamani, abu na karshe da tayi naji zaman mu ya kare shine kwana ta komayi da wuka saboda kar na zo kusa da ita. Ta nemi rayuwata saboda ba ni take so ba kudina take so. Wannan yasa na ji tsoron sake son wata 'ya mace na ji tsoron sake aqalar rayuwata a hannun kowa, har nake ganin kowace mata haka take, amma kuma kasancewata da ke kin nuna min kaman yanda ba duka aka zama mata na gari ba haka ba kowace mace bace take da makarkashiya a tare da ita. Kin gwada min menene hakikanin so, you made me believe again"
Aneesa tayi ajiyar zuciya cike da tausayawa rayuwar da Sagir ya gani na rashin so daga matarsa ta sunna, wato dama da dalilinsa na kin sakewa da ita tun farko, a tunaninta jijji da kaine yake gwada mata. "shi ke nan komai ya wuce"
"ko ba komai yau an kirani Sagir, ba uncle." Tayi murmushi, shi kuwa ya kara janta jikin sa kafin ya rike hannunta ya zaunar da ita a bakin gado, "yaya babyn mu, kina ta fushi dani ko labarin baby an daina bani." ya shafo cikinta.
"Lafiya lau. Ya fara motsi"
"Da gaske?" ya fada hade da kawo kunnen shi kan cikin.
"Ai ba za ka ji ba sai ya dade yakeyi."
Ya daga ya dubi fuskarta sannan yace "I am so sorry, yaushe zamu koma gida? Nayi kewarki sosai, gidan mu ma na bukatar ki"
"uhmm sai Hajiya tasa min rana na koma"
"Don Allah ki yi mun rai kice mata kin fara jin karfin jikin ki."
Sagir yaso ya bata dariya, "yaya zan fara ce mata ina so na koma bayan tana ganin yanda kake sintiri a gidannan ta san meye kake so, amma bata ce min na tafi ba."
"Ni dai ki san yanda zakiyi idan ba haka ba kuma zan tattaro na dawo dakin nan."
"Ka rufa min asiri, ba ruwana."
"Ba ruwanki? Ba ke kika jawo mana ba, da kika fada mata komai."
Ta kwantar da kai sannan tace "Ina kake so naje to?"
Yayi murmushi yace "Gida, wurin mijinki"
Aneesa tana cikin jin dadin hirarsu kenan ta ankara da agogo da sauri ta mike "lah, karfe sha biyu fa, ka tashi ka tafi gida"
Sagir ya jawo hannyenta zuwa gareshi yace "Gani ga gidana ina zanje? yau a nan zan kwana."
Ta kama baki hade da zaro idanu "Ka rufa min asiri ka tafi don Allah" ta firfito da idanu har ta so ta bashi dariya.
Abun da Sagir ya shiga yi mata ne ya nuna mata cewa tabbas zama yazo yi ba tafiya ba.
Ana kiran sallah ta farka, gani tayi yayi alwala ya fito daga bandaki. "yanzu yaya za ayi ka tafi masallaci? Idan ka hadu da Abba ko Kamaal fa ko wani dan gidan nan ya ganka?"
"Sai meye suma sun san sun rike min mata. Na zo tayata hira ne."
"Don Allah kayi hakuri kayi sallarka a gida don na yau kawai, yaya zanyi zaka sani jin kunya."
Dariya yayi yace "Na nawa kuma sun riga sunga motata a waje, don haka ki kwantar da hankalinki ba komai"
"Zaka hanani zuwa gaida Abba kenan."
"A'a, na sama mana hanyar komawarki cikin sauki ne, tunda kince ke baza ki iya ba. Kinga idan suka ga na fara kwana a nan ai zasu tattaraki ki koma." ya sauke hannun jallabiyarsa ya fice daga dakin, tamkar a gidansa yake.
Aneesa ta rike kai ta jabe zaune, sai da taji an tada sallah a masallaci ta iya mikewa tayi alwala.
Da safe bayan Abba ya gama cin abinci ne ya dubi Hajiya Khadija yace "wai ni kam me yasa baza ki bar yaron nan ya dauki matarsa bane?"
"Ah, Abba shi fa da kanshi yace a barta sai randa ta huce ta koma da kanta, kaga kenan ai bai damu ba don haka kyaleni dashi"
Alhaji Mustapha ya girgiza kai yace "ke ma dai kina tayata fushin kenan, amma ni banga me zai hana ta koma ba tunda ba a kwance take ba. Aiki kuwa basu rasa masu yi musu shi ba, don haka ni ban goyi bayan zamanta ba"
"To, tunda kace haka. Amma ai abun da yayi wa 'yar mutane bai kyauta ba, idan aka barshi kuma ya sake maimaita hakan fa? Gwamma dai ya gane banbancin rashinta da kuma muhimmancinta ina ga zai gyara al'amuran sa."
"Shin ba kya kula da sintirin da ya faye yi tun da kika dauko masa mata? ki dai barsu suje can su daidaita kan su amma idan kika takura su kuma to sai shima kiyi masa masauki don dai yau nan gidan motarsa ta kwana."
Hajiya tayi shiru tana jinjina maganar Abba, tabbas ba tun yau ba ta kula da yawan sintirin da Sagir yakeyi a gidan, amma ta ki ta bashi sararin ganin Aneesa idan dai har magana ta kai haka kam dole ta tattara masa iyalinsa ta koma.
Bayan kwana biyu Sagir ya tafi da matarsa gida, ko da suka koma Aneesa sai mita take masa na cewar ya janyo har taji kunyar su Hajiya. "To yanzu ke hakan bai fi miki ba akan kina ta kame-kame ke da mijinki?" Sagir ya fada mata cikin rashin damuwa da maganarta.
Zama dai ya mike gadan-gadan tsakanin Aneesa da Sagir hakan ya janyo kyakkyawar canji a tare da natsuwarsu duk. Aneesa dai sun fara jarabawa, Sagir kuwa ya mai da hankalinsa ga kula da kasuwancinsa da iyalinsa sai dai matsalar har yau dai alaqa tsakaninsa da abokinsa Aadil bata gyaru ba, yaki bashi fuska iyaka suyi aikin ofis shi kenan.
Ana saura Sati daya Aneesa ta rubuta jarabawarta ta karshe a NECO ne haihuwa ya taso mata gadan-gadan. Tunda ta shiga watanta daddy ya turo Baba Saratu domin ta zauna da ita, don haka ta samu kula sosai, nakuda na tashi Baba saratu ta fadawa Hajiya da mummy sannan suka nufi asibiti domin Sagir yana South Africa a lokacin. Yana samun labarin abun da ake ciki hankalinsa gaba daya yayi gida, nan yasa Aisha ta hada shi da Aneesa a video call, amma ina tana ta kanta bata san ma me yake cewa ba. Ganinta a wannan halin yasa Sagir ya kara tausaya mata yaji kuma kaunarta ya karu a zuciyarsa.
Tana kwance a gado a dakin da aka shirya mata da zatayi zaman jego cikin dakunan kasa, taga baby na motsi don haka ta dagata tana girgizawa, a hankali ta tsinkayi kamshin Sagir daga idanun da zatayi sai ko ta ganshi a dakin.
"Maa sha Allah, Aneesa sannu da kokari." ya durkusa a gaban gadon yana kallon baby a hannunta, a hankali ta mika masa. Tana kallon yanda yake kallon baby cike da so da kauna, ya tofa mata addu'o'i. Ya sa ta a jikinsa sannan ya dubi Aneesa ya hada ya rungume su. "Ba ki san irin farin cikin da kika damka min ba, Allah ya raya mana ita cikin tafarkin addinin musulunci ya kare mana ita daga dukkan sharri"
Aneesa ta share dan kwallan da ya fito mata sannan tace "Ameen."
Ya kara dubanta yace "yaya kikeji, ba dai wani problem ko?"
"A'a lafiyata kalau."
"To alhamdulillah, Allah ya raya mana Khadija Khairiyya"
Aneesa tayi murmushi sannan tace "Ameen, Allah kuma yasa ta dauko halayyar masu sunan."
A nan Sagir ya zauna suna ta hira sai da Baba Saratu ta shigo tace lokacin wankan su yayi. Sagir ya mika baby shima ya mike yayi nasa dakin domin ya dan rage gajiya.
Tana fitowa daga wanka ta je ta samu Iyatu suka shirya abincin Sagir a kan table, amma bayan awa daya sai gashi ya shigo dakin da plate din abincin shi.
"Da kayi magana ai sai a kawo maka baby, na san dai ita ake ta faman bibiya"
Sagir yayi dariya, yace "ba ruwanki damu."
Shi wai a dole ranar a dakin zai kwana, amma ba shiri tun karfe sha biyu yace su kwana lafiya domin kuwa lokacin ne garin Khairiyya ya waye. Aneesa tana dariyarsa ya fita a dakin ya koma dakinshi.
Bayan kwana uku da haihuwar Aneesa ne sukayi manyan baki daga Kano, Rabi'at ne da mijinta Faruk. Aneesa tayi farin cikin zuwansu, nan da nan ta shirya musu tarba ta musamman. Sun dade suna hira Aneesa ta tambaye ta labarin su Maryam yaran Rabi'at, kafin suka ce zasu wuce Rabi'at tace "kiyi hakuri bazamu samu halartar suna ba, kasancewar zamuyi tafiya gobe. Amma in sha Allah zaki ganni idan na dawo."
Aneesa tace "ba komai, yanzun ma kun kyauta sosai da kuka zo. Allah ya bar zumunci ya kuma kare muku hanya."
"Ameen, Allah ya raya mana pretty Khairiyya" Da suka tashi tafiya Rabi'at ta bata wasu lesuka masu kyaun gaske guda biyu da 'kananan 'yan kunnayen gwal na baby. Shi kuwa mai gidanta kudi ya bata a envelope. Sai bayan tafiyarsu ta ga bandir din 'yan dubu-dubu ne. Duk ta ajiye su a dakin Sagir sai ya dawo zata nuna masa.
An daga taron suna kasancewar ranar Aneesa zata rubuta paper dinta na karshe, Anty FAtima ce ta shirya duk wani abu na tarban bakin sunan Aneesa.
Ana saura kwana biyu suna ne sai ga su Mama a Abuja, musamman Sagir ya aika mota Kunuwal yace wadanda zasu zo suna su biyo motar a kawo su. RAnar murna a wurin Aneesa ba a cewa komai, haka ta raba dare suna hira da mama. Amma wai ita fushi takeyi don me yasa Inna bata zo ba. Sai a waya suke magana tun haihuwar, ta dai shiryo mata kayan kauri an taho mata dashi.
Nan Sagir ya shigo dakin da Mama take yace "Ke tsohuwa, me ya kawo ki bayan da kin hana ni dauko matata?"
Mama tayi dariya tace "Ai sa'a kayi, ina zan bari kana min sintiri a gida ku a dole soyayya? Gata nan na tarkato maka ita kuyi ta fama, da 'yarku mai shegen kukan nan"
Ya dade suna hira a dakin sannan ya musu sai da safe.
Ranar suna da safe Sagir yayiwa Aneesa wata kayatacciyar kyauta, dakinsa ya kirata. Sai da ya gama hirar sa da Khairiyya ya fito da wani dan karamin akwati ya daura a kan gadon ya bude mata yace "Wannan kyautace ta musamman da na tanadar don wannan ranar. Ba abinda zan baki ya biya wani kyautatawa ko kuma wannan farin cikin da na samu ta dalilinki, please accept this"
Aneesa ta tsaya tana kallon abubuwan cikin akwatin tana kallon Sagir. "ki dauka naki ne." Makullin mota ta gani da wasu takardu sai wata sarka mai dan karan kyau, ita kanta bata taba ganin abu mai kyau irin sa ba.
Sagir ya mata bayanin takardun wai na gidanta ne. Gidan da suka taba sauka a Gombe wai dama da sunanta ya saya amma bai fada mata ba sai lokacin da ya dace yazo. Sarkar kuwa ya tuna mata lokacin da ya barta a airpot a Turkey yace ta jirashi, abunda ya sayo mata kenan. Aneesa kam ta rasa bakin magana sai hawaye taji suna bi mata idanu. Da taga bazata iya magana ba mikewa tayi ta rungume shi cikin yabawa da gode masa. Baby kuwa cika mata daki yayi da sayayyarta har ta rasa inda zata sa wasu.
A filin gidan Sagir aka shirya kayatacciyar walima, taron yaga jama'a da dama daga kowani bangare kawayen Aneesa na makarantarsu ma duk sun hallara. An ci an sha an rarraba kyaututtuka ga duk wanda ya halarci wannan taro. Mai jego ta shiryu cikin kaya na alfarma. Akwatuna tirim aka ciko daga gidan Daddy wai duk nata ne da na baby. Haka takwararta bata rage su da komai ba, har da turarrukan na musamman ta aiko wa Aneesa domin gyaran jiki, Aneesa har ta rasa bakin magana.
Wuni sukayi bayan suna da su Khazeena suna shirge kayan sunan a dakin tsakiya da bata amfani dashi sosai, ta ware wasu zannuwan ta bawa su Zahida da Khazeena wasu kuwa ta aikawa Aisha da Hamdiyya, ta daukawa Innarta da Amina ma.
Anty Sameera ma tazo sunan, don a wannan lokaci dai ta sawa kanta salama ta amince tana sauraron wani dan majalisa da ya dade yana sonta, matansa biyu. Ganin Sagir ya zakalkale baya tunanin wata sai Aneesan sa ita ma ta hakura domin zaman hakan ya soma damunta.
Kamaal ya kammala karatunsa na Masters har ya fara aiki a Kaduna.
Tun bayan haihuwarta Baba Saratu take ta aikin shirya ta, ba wasa. Ta hanata yawo ba takalma kullum kuma tana cikin sata zama cikin ruwan bagaruwa. Ga aukin turarata da takeyi. kullum kuwa tana cin romo da shayi mai kauri har saida Aneesa tayi wani bulbul tana sheki tukun. Kafin su gama jego dai har wani kamshi na musamman ya zauna a jikin Aneesa. Daga wannan lokacin kuwa Baba Saratu ta rakashe a gidan Aneesa.
Ranar wata laraba ne sukayi waya da Innarta, take shaida mata Malam Habu ya samu koyarwa a babban secondary a cikin Gombe don haka yanzu aikin sa ya koma can. Aneesa murna ya kamata marar misaltuwa.
Da dare suna cin abinci da Sagir take fada masa abun da ya faru. Yayi murna da jin labarin kwarai a lokacin ya kira malam Habu suka taya shi murna. Bayan sun gama wayar ne yace "Mun kammala shirye-shiryen da mukeyi fa na bude kamfanin mu na south Africa ina ga cikin wata mai kamawa za a bude kamfanin, in sha Allah."
Aneesa tana murmushin jin dadi tace "Lallai abu yayi kyau, Allah ya sa a bude lafiya ya kuma yi albarka kaman yanda sauran suke dashi."
"Ameen, sai dai zai dan bukaci lokaci sai na tabbatar da cewa komai ya daidaita sannan na dawo, za a min rakiya ko kuwa Khairiyya tayi kankanta?"
Aneesa tace "me zai hana. Itama dai yanzu kam ta kunsu da yawa kullum ita kenan daga daki sai falo? ko kuma idan za aje danna mata allura."
Yayi dariya yace "To shi kenan sai ku shirya wani sati sai muje Kunuwal ku musu sallama suga Khairiyya kafin mu tafi."
Aneesa ta amsa masa sannan ta shiga kwashe kwanukan zuwa kicin, a falo ta same su da ta dawo. Sagir yace "Tashi ki kwantar da Khairiyya inaga baccin ta yayi nisa yanzu kam." Ta karbi jinjirar tasa a dan karamin cot din ta mai laushi. Sai da aka gama labaru tukun tace "mu kam mun shiga sai da safe," Sagir ya kalleta yace "Ban gane sai da safe ba, ai yau kam kun koma sama ki je ki kwantar da ita ina haurowa yanzu nima." Jin haka Aneesa ta sha jinin jikinta don haka dakinta ta shiga ta kimtsa tukun sannan ta amsa kiran mai gidan nata.
Wannan zuwan nasu gidan su na Gombe suka fara sauka, a wancan zuwan nasu Aneesa bata kula da gidan da kyau ba kasancewar shigan dare sukayi. sai a wannan zuwan ta kula duk kayan da Daddy ya mata da wanda Innarta ta mata a nan aka shirya mata su. Nan taji wani dadi ya lullubeta, ta kara jin son Sagir a tare da ita. Suna isa tamkar su Amina ita suke jira, kowa sai son karban Khairiyya yakeyi Inna tace "kaji min yara dai sai kun tumurmutsa ta ne tukun na? ku bari sai ta tashi a bacci sai duka ku dauketa."
Sagir ya shigo suka gaisa da Inna tace "Aneesa ta fada mana ci gaban da aka kara samu Allah ya sanya alheri ya kuma kara daukaka. Yayi kyau"
"Ameen, Ameen ina Muhammad ne yau ya samu baby bai zo mun gaisa ba"
"Hmm gasu can sai fada sukeyi akan wanda zai riga dauka."
"Ina ruwan Muhammad, Inna ni zan shige akwai inda zamuje da Malam zan same shi a makaranta"
"Ayya, to ba laifi. sai kun dawo"
Inna tana komawa ciki tace "ki tashi kije ko da abun da zai ce miki, wai zasu fita da malam."
Tana shiga yace "zamu anguwa da Malam zakiyi rakiya?"
"A'a ku dai sauka lafiya sai kun dawo"
"Ina khairiyya?"
Aneesa tace "tana wurin Inna, zaku dade ne?"
"A'a akwai abokina Haruna kin tuna shi ai," Aneesa ta gyada kai "zamu je ganin sa ne akwai abunda zamu tattauna"
Aneesa tayi murmushi tace "to Allah ya dawo daku lafiya."
**********
Da yamma sai ga Malam Habu ya shigo gida yana farin ciki sai kira yakeyi "Halima, ina Haliman ne?"
Inna ta fito da sauri daga daki don dai ta san wannan kira ta dabance "lafiya malam?"
Malam Habu ya zauna a bakin tabarma yace bude ki ga wannan"
Inna ta sa hannu ta karbi takarda tana dubawa "Malam wannan fa?"
"Kin san yaron nan Sagir muna tafiya muka samu wani abokinsa daga can muka wuce wani gida sai ya shiga suka gama dubawa sannan ya maida abokin a nan ne ya fito da takardar nan yace "Malam wannan naka ne, inaga tunda yanzu aikin ka ya dawo Gombe wahalar shiga da fita kar tayi maka yawa zaku iya dawowa da su Inna"
"Inna tasa salati tace "Amma lallai ba abun da zame cewa Sagir sai Allah ya biyashi da madaukakiyar gida a aljanna Allah ya saka da alheri."
Nan Inna ta sa baki ta kira Uwani suka shaida mata a abunda mijinta yayi, mamaki da dadi da farin ciki ya cika ta fal ta rasa bakin magana.
Sai da dare ta nemi wayarta ta kira Sagir.
"Ba kiyi bacci ba?"
"a'a, yanzu dai nake da shirin yi na samu Khairiyya tayi."
"lalle kin ci sa'a. Allah yasa anjima kar ta tashi miki"
Aneesa ta yi shiru sannan tace "Sagir akwai abun da zan yi maka don na nuna maka godiyata kan dawainiyar da kake dauka akan iyayena da ni kaina?"
"Aneesa kasancewar ki tare dani ya isheni komai"
Lumshe idanu tayi tace "Na gode Allah ya kara rufa asiri, ya sa ka gama da duniya lafiya. bakina bazai iya furta maka iya farin cikin da nake ciki ba"
"Ni na san abun da zai iya nuna min, ko na zo na daukeki ne?"
Aneesa ta rufe fuska tamkar yana ganinta tace "A'a wannan karon kam kayi mana afuwa mu kammala kwanakin da muka zo yi."
"To shi kenan, amma dai ki dawo da shirin ki sosai."
Haka dai suka sha hira mai shiga rai kafin sukayi sallama.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top