TUSHEN LABARI

*🅱RILLIANT WRITERS ASSO🖊*
_Pens of freedom,home of exceptional and magnificient writers_

*🍒🌺AJALIN SO🌺🍒*
      _XPLICIT ROMANCE_
 

*WATTPAD@SURAYYAHMS*

_Dedicated to ummerheny nersallah_

_Disclaimer_
*In the name of thy lord almighty..All right reserved.Wannan labarin gaba dayan ta mallakin surayyahms ce,any resemblence of story or lifestyles shud pls be considered as a coincedence,ban yarda a dora shi a kafafan siyarwa..karantawa bugawa ko a juya min shi  ba tare da izini na ba,yin haka bazai sa nayi fushi ko na kama ka da zagi ko cin mutunci ba amma tunda brain dina da time dina ne zan ja maka Allah ya isah a zuciya ta lol it might contain matured scene and chapters rated under16 copycats karma is a bitch fa#beware..*

_Shafin farko sadaukarwa ce ga members brilliant writers association_

_Tare da mrs maryam sae'ed maman areef._

PAGE 1


*AJALIN SO TUSHEN lABARIN*

UR VOTES AND COMENTS BUYS NEXT CHAPTER

_Mattmacmillan street condominum07 10am:UK_

A cikin nitsuwa yake tahowa sanye da farin rigar sport designer ta companyn NIKE mai dauke da cap da dogon wando alaman daga street warming execise ya ke.

perfectly tailored  into his body size yayi matukar kyau kamar kullum"

Tsarin muhallin sun Condominium ce wato jointed rent apartment mai shashi shashi wanda gaba dayan ta na mutum daya ne amma kowa  yana da right ya iya siyan part dinsa kamar yadda shima yayi..

Gaban sa kawai yake kallo Ya dauke idanun sa.

Ko ina ya dauki shirun safiyar ranar ga sanyi ya sauko sosai don haka a gurguje ya bude kofar ya shiga..

"ko da ya shigo ya tsaya Da kwalayen picanto,dominos,da clipart pizza su ukun duka ya soma cin karo a kasan floor

ba shakka wanda aka ci jiya ne aka barsu nan don ko da asuba daya fito sallah ya gani kafin ya fice..

"daga jikin kofar ya jingine yana kallo,All three packs din an tattaba ne sama sama ba wani ci sosai akayi ba aka barshi a bude kuma a wulakance.

Dan karamin Tsaki ya ja don ya gama lura ma ba wannan bane ba dai dai ba anan,ga wine glass na drinks da botles hatta trow pillows dake chairs din idan suka zube kasa bata iya dagawa every where is unkept and scatterd ko kadan babu kimtsi

"a hakan ya dauki kusan 5mints yana browsing ko ina da idanun sa "duk dama yasan shiya bada purnishement din hana masu aiki amma ya sha mamakin da babu abunda ya sauya "He's just tired of being her servant....yawan complain din ma ya ishe shi...

Ajiyan zuciya yayi ya dada haurawo bedroom don ya tarkato ta ta taho
Ta tattara gidan dakanta as usual yasan is eida tana bacci ne ko tana kwalliya..

"is a normal size room so Yana bude kofar dakin yaga wayam alaman ba kowa ...nan ma ya ci karo da nitien ta akan gado rabi jelar sa na kasa komai dai yadda ya ke haka ya dawo ya same sa..

"Nimrah!!!!..nimrah ya shiga kwala kira da geek voice dinsa mai dauke da masifa...

Shiru shiru yasa ya shiga bude kofofi yana dubawa amma shol har sai da ya hakura ya dawo ya soma tattara kayan dakin  yana ajiye wa mazaunin su.

Sai anan yayi gamo da letter ta agefen drawer inda ta makele shi"

_"Hey mr mohan,kafin kafara cizo na da early morning masifan ka..im sorry,ni natafi..bazan iya jiran ka ba i need to cacht a flight ...mum dakan ta yau tazo she's now in hongkong..,so,ni na tafi wajen ta kawai..call me later kkk?..bye..nimrah._

Tsaki ne ya kufce masa....Zama ya koma yayi daga bakin bed din domin kuwa letter da kanta ta zame daga hannun sa ta fada kasa

A lokacin basai ya furta he was very annoyed ba, sosai yanayin face dinsa ya nuna..."wai meye wannan yarinyar ta dauki aure ne?so she thinks she can just leave bazama ta jira na bata go ahead ba...tsaki ya dada yi yayi shruging kafadar sa alaman zaki dawo ki tarar da ni..

Nan ya sauya zuwa comfy white towels ya shiga batrum..
ya dade anan jingine da glass wall din shower yana tunanin yanayin rayuwar auren sa for the past 2years da suke zaune anan UK this was not even his idea mahaifin sa ne ya sa suka xo nan..

Nishi yake saukewa a hankali domin kuwa Abubuwa dayawa sunyi crosing mind dinsa marasa dadi musamman idan ya tuno da abu biyu zuwa uku

"Yasan Dole ne yayi zaman aure da nimrah sabida umarnin mahaifin sa ne hakan Duk dama yasan a da chan bai taba kaunar ta ta sigar aure ba
But who cares now,shes his wife now..kuma  yasan tana son shi sosai

A wajen sa Zama da nimrahn tamkar kashin kifi ne a wuyar sa wanda baisan ranar fitar sa ba maybe hala Sai inyayi ra'ayin fita da kansa..

Shi dai Bawai baya jin komai aransa game da ita bane tunda suka yi auren nan ma yake jin wani yanayi na daban aransa na musamman domin ta..

Sun samu shakuwa shakuwa irin na ma'aurata,infact wani bin yadda yake biye mata  bazaka ce asalin auren dole aka masa da ita ba abu daya ya rage wato masifa da rashin da'ar ta,
Shikuwa Sam baya son raini ita ko nan tafi kwarewa

Da a chan baya ma Tare da nimrah suka taso da budurwan sa na yarinta mai suna aysha..

tun aysha tana da shekaru 15 yake son ta shikuma yana first year a medical schl india

Aysha da nimrah ajin su daya a sydney anan suke fafatawa.

Sai ya kasance Bayan ayshah...nimrah ce abokiyar sa na kusa amma Tunda ta kashe masa ayshan yaji ya tsane ta a duniyan sa musamman ma da aka ki daukar matakin komai akan lamarin.

"Toh yau gashi nimrahn ce ta dawo matar sa,in ya tuno haka sai yaji zuciyar sa ya sake shiga damuwa sosai,amma da shike yasan babu ranan da zai samu mafita ko abunda yake so ma ransa sai ya hakura ya kaucar da tunanin tare da sa wa zuciyan sa shaukin accepting cewa qaddar aure dake tsakanin sa da nimrah ya riga yayi AJALIN SO A duniyar sa

Shi dai yana nan ne kawai amma shika dai yasan damuwar sa ta asali.

Ita kam bata damu ba domin asali ta girma ne da mummunan kaunar shi,..shi kuma sam baya yin ta Hakan shiyasa bata iya controling kanta akan sa ba ko kadan..

da suke kananan ma tayi kokarin ganin ta kwace sa wajen aysha amma da ya zo ya nuna zai iya tsanan ta akan son da take masa sai tayi saurin dawowa mace mai fuska biyu kuma a hakan ta kashe aysha ta tafi scot free akace accidently ne

Gashi Ko yanzu agaban sa idan tayi ba dai dai ba  ya nuna bacin rai sai tana saurin neman sulhu duk dama babu wanda zai iya kwatanta kasaita da girman kanta awaje

Nimrah ya guda ce wajen wata hamshakiya kuma isashhiyar minister tsaro na kasa wato LADY ZINETA ADAMS, She's a doughter of a royal generation from kingdom of zazzau.

Lady zineta mace ce mai ji da kwarjini

Kasaitacciya ce Azzaluma mai tinkaho da zalunci da mugun ta,don musamman take da dakin tsafin ta a babbn mansion din ta...

Sune irin matan nan na siyasa masu dauke da political powers din da ke take duk wani mahalukin da ya sha musu gaba.

A Shekaru 8 da suka wuce Abin ciken wani mutum mai suna journalist farasat da matar sa dr arjumand saeed...

sun gano gaskiyar wani babban sirrin da aka binne dangane da rayuwar alhaj muamar wato mahaifin dr mohan wanda ya so yayi ajalin sa

Alhj muamar haifaffen dan nigeria ne amma yayi aikin soja na kasa  a matsayin babban arc comander na yakin dake ci a kasar syria da pakistan

A cewar jounalist farasat  dr arjumand saeed matar Sa halfcast ce amma mahaifin ta indigene na ibadan state ne kabilan yorubawa...

mahaifiyar ta kuma spanish lady ce,so ta mutu kafin suka dawo nigeria da zama da shi da yarsu karama guda daya mace.

sai ya kasance duk da dr arjumand ta auro dan nigeria gaba da baya bata da burin da ya wuce ta ji ana speaking yaren maman ta wato espanol don hakan yana sa taji zuciyan ta ya samo kusanci da mahaifiyar ta a koda yaushe.

Jounalist farasat shine  namiji na farko da ya cika mata wannan burin nata na iya yaren da bana shi ba kuma ya bata dama ta koya ma yarsu mai suna BANAFSHA dake da shekara ta 5 zuwa 6 a duniya

dr arjumand sosai ta rike abun aranta don yayi mata dadi marar misaltuwa.

Bata iya mance shi amma bayan sa kuma har yau tana tuni da hallacin da tsohon soja alhj muamar ya mata da chan tana karama

a cewar ta shine sojan daya tseratar da musulamai ayankin syria da yake boader da turkey...
A ranar,Mutane bila adadin sun samu rayuwa ciki har da nata familyn shi baisan ta ba amma ta rike sa sosai arai.

Hakan yasa suka sa karfi da karfe ita da mijin ta jounalist farasat akan gano gaskiyar sa wanda aka riga aka rufe sa da chan.

Kowa yasan Minister of defence Lady zineta gadon mulkin tayi,domin kuwa yace wajen wajen wani shaharran ministern tsaro na kasa wanda da makirci da mugunta ya daura ta akan mulkin bayan mutuwar sa

..lady tana da mulki da iko da kudi na takama.

amma duk da haka ko kadan bata da dukiya da tarin murdaddun connections din da alhaj muamar ya tara ma kansa a duniya bayan sauka dayayi daga aikin sojan...

yana da kashin arziki sosai da farin jini
He's filthy rich and influential.
He's now a co-founder of many power rersouce and industries a zageye da duniya komin sa na tafiya smooth ba matsala

Hakan ya sa lady zineta ta sa masa kahon zuka..

So,a farkon hawan kujeran ta na mulki sai ta so su hada kai da shi suyi harkokin kudi da arziki

"...amma sai ya ki sam sabida zaluncin ta da danne hakkin talakawar ta abu ne wanda baya so yayi arayuwar sa ko kadan.

Abun ya mata zafi duk dama shine mutum na farko da ta nemi abu wajen sa ya gaya mata gatsau bazata samu ba

Amma sai Bata tsoratar da shi da barazanar mutuwa ko ikon ta kamar yadda take ma sauran ba cikin lumana ta barsa ya tafi.

Bayan kwana biyu har an mance rayuwa na tafiya ma kowa Lokaci guda sai kawai yaji sammaci a kotu da laifi manya manya wanda ya nuna hannun sa dumu dumu aciki

Wato kisar babban ogan sa na soja"arc major salem iftiqham wanda aka rufe mutuwar sa da drug dealing business na cocaine da wiwi.

Sai ta sa aka juya case din da cewa retired ac comander muamar shi ya kashe ogan sa ya kuma juya kudin sa na drugs ya gina kansa har yayi kudi haka ba asani ba.

"alhj muamar da ogan sa sun shaku sosai duk da halayen su ya banbata

Sai ta samu gurbi Da ikon power ta ta hade masa gadar zare mai karfi ta bada shaidu akansa ba tare da ya san ita ta aika ta masa hakan ba

Sai da ta ga yana cikin halin ha'ula'i ga ciwon buguwar zuciya da sharrin ya taho masa da shi ga mutanen sa sun fara ja baya da shi..
is a matter of strict international concern sai kowa yana zame kansa a hankali

Har sai da familyn sa ya fara zubewa kasa suna neman taimakon kota halin kaka ne..for the first time kudin su sam bai musu amfani ba...

Toh Anan Gaban lady ta sa hannu akan zata taimake su,nan batare da bata lokaci ba ta nuna ikon mulkin ta a kotu aka rufe maganar da sunan ita ta taimake sa ta rufa masa asiri ya dawo kan kafar sa

Sai ta rufe zargin lamarin akanta ta hanyar amfani da mumumnan son da only doutherr ta NIMRAH take ma only son dinsa MOHAN duk dama lokaciin basu wani girma ba

In exchange of that homage,sai ta nemi alfarman marriage proposal to his only son DOCTOR MOHAN muamar wanda tun da aka fara case din yana india sam mahaifiyar sa ta hana a fada masa komai daga case din gudun kar ta bata masa future sa..

Lady tace'akan idan suka kara girma sai ayi bikin su.

Lokacin mohan yana da shekaru ashirin da wani abu a india ita kuma nimrah ta koma London tana cigaba@18yearz.

A lokacin alhj muamar bai ki mata ba amma sai ya ce lallai sai dansa ya amince da auren kafin ayi masa

Ko da suka hada ranar gabatar wa sai mohan ya nuna bazai yi zaman aure da nimrah ba.

Acewar sa sabida darajar abunda ke tsakanin su yanzu zai cigaba da daukar ta abokiya amma banda matar auren sa sabida baiya son ta kuma harga Allah shi bai yafe mata kashe ayshah datayi ba

Abun yayi musu zafi sosai barin ma nimrah da dama tayi zumudi sosai akan haka har take burin barin karatun ta ta dawo nigeria domin sa.

kin amincewar mohan akan auren nimrah da bin bayan sa da mahaifinsa yayi anan ya sa lady zineta fushi da fusata
Amma agaban su Sai tayi kamar abun bai dame ta ba

So Bayan tafiyar su da yan kwanaki sai ta  ta shigo ma alhj muamar da business deal dinta boro boro tare da masa baraza wajen bayyana duk abubuwan data kulla masa a fili akan case dinsa na kotu batare da kowa ya sani ba..

Sai da ta tsoratar da shi ta ko wani hanya ta kuma rufe masa kofar fita daga chawkakiyar sannan ta bashi  ultimatum akan cewa idan har basu hada zuria ba,wannan karon zata kaisa jail daga jail ta tura sa kabarin sa sannan ta wulakanta familyn sa..

Alhj muamar baiso dan sa ya kare da wance baiya kauna ba,amma da shike lady zineta ta dage akan batun ta na cutar da su da ma duk wanda yace zai taimake sa sai ya amince mata..

Abubuwa da yawa sun faru cikin shekaru takwas din nan da suka wuce har da mutuwar dr arjumand da mijin ta jounalist farasat.

Sun mutu ne akan gwagwarmayan su na fito da gaskiyan alhj muamar daga shackles din lady zineta ,..

amma tsananin iya zalunci da makirci irin na lady zineta yayi ajalin su..

'Mutuwar su yayi ma alhj muamar ciwo sosai

Amma ba yadda ya iya so,Bayan wani lokaci da komai ya lafa daga Ruguntsimin mutuwar nasu,sai alhj yasa dan sa MOHAN dole ya amince cewa zai aure nimrah witout any reasonable explanations

So Bayan sun kammala karatun su duka aka daure Auren su

Toh,Kafin nan Ko da aka zo daf za'ayi auren nimrah da mohan..

Lady ita tayi amfani da dakin tsafin ta tayi kokari ma yarta sosai wajen taya ta da shafe shafen turare da hayakin sihiri don ta samu rangwamen soyayya wajen dr mohan

duk dama tasan baisan meke faruwa tsakanin ta da mahaifin sa ba tukun Amma yanzu hakan shi kadai ne makamin yarta na zaman gidan mohan hankali kwance..

"Da zata iya cewa shima zata masa barazanan don dole ya so yarta su kuma juya shi yadda suke so"
Tasan ai Yana son mahaifin sa sosai so zai iya yarda da duk abunda zata jawo na mugun ta akan sa don ya kare sa...

Amma kassssh alhj muamar ya riga yayi mata dabaibaiyi tun ranar da aka sanar da mutuwar doc arjumand da jounalist farasat ta
inda bata yi tsammani ba

Wanda Don ta rufe zargin maganan mutuwar su jounalist farasat akanta
Sai Ta amince masa kawai..

Domin kuwa tun kafin a zo maganan daura auren ya sanar mata cewa lallai idan yar jounalist farasat da suka bari a hannun sa ta girma ta kai aure

ya riga ya nemi izini wajen iyayen ta kafin su mutu cewa lallai zai aura ma dansa mohan ko tana so ko bata so.

Babu wanda yasan haka na faruwa tsakanin su sai mahaifiyar sa hjy saddika 'wanda aka fi sani da hajiya mamah sai kuma nimrah itama har yau dai bata san da maganan auren ba..

Ita dai tunda sihiri ya samo mata kan mohan taga yana biye mata shikenan ta dena damuwa da komai tana bazata ikon ta..

Da shike alhj muamar da matar sa wato
mahaifiyar mohan basu cika zaman nigeria ba sai bai damu su su rike yarinyar da kansu ba..

Yanzu haka yarinyar ta na hannun mahaifiyar alhj muamar din a sydney nan inda mohan ya fara girma

tun tana 8years ta ke rainon ta a boye gashi har ta cigaba da zama acahn tana karasa karatun ta na primary na wanda ya sani..

To yanzu gashi har lokaci yaja anyi auren mohan da nimrah sai da auren ya cika kusan shekara daya hjya mamah ta dawo da ita nigeria tana da shekaru 13years

Anan abuja suka zauna inda family house din alhj muamar yake suka cigaba da rayuwar su

Cikin familyn alhj muamar in banda shi da hjy mamah babu wanda ya san yarinyar a fuska sai last year din ta dawo da ita nigeria

Year din da mohan yake kokarin kaiwa shekaru biyu da auren nasa
Anan kuma har an saka ta makarantar secndry ta kai jss2 tare da adopted sister sa mai suna nusaibah

alhj muamar ne ya maida masa project dinsa na farko achan tare da honeymoon treath a Uk shiyasa ko leko nigeria basuyi ba a 2years din...

Yana fitowa daga shower  shirin sa yayi tsaf cikin kana nan kaya batare da bata lokaci ba ya tattatra ina shi inashi ya wuce cape town a kasar south africa..
Follow#surayyahms

Vote
Share
Share ur views

*Surayyahms:wattpad*
*Surayyahms:instgram*





*shafin WATTPAD*
*Seach @SURAYYAHMS*

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top