medicine

*🍒🌺AJALIN SO🍒🌺*

_WATTPAD SURAYYAHMS_

Brilliant writers association

_50 medicine_

Tun daga fitar ta ta kira layin maryam tace mata tana nan A hanyar zuwa maryam Tace Toh Kizo gidan ummah Kawai ina wajen

Nan Din ta wuce  driver ya aje ta,
Bakowa harabar gidan Sai ta shigo Falo da sallamar ta,Maryam din ne a zaune Ganin ta yasa ta mike da fara'a tana cewa maraba Da xuwa, ta bata wajen zama
..gidan shiru kamar ba kowa sai su biyun...aje maysam Banafsha tayi gefe tana sauke boyayyen ajiyan zuciya Don har wani iska na daban ta ke ji naratsa ta

Maryam tace kaga amaryan doc hjy Banafsha...,sai wani pale pale kike kinyi haske, Banafsha anya ba wani katon kwallon kika chabe ba?

Murmurshi kawai tayi tace wannan ai sai ku yaushe zan iya mantawa da azaban danaci a nakuda?

,. . yah Yaya ameer ango na Fatan kuna lpya?

maryam Tayi Murmushi tace lpya Lau fatan dai zaki zo min, dan nan dai ba gida na bane.....sukayi dariya Banafsha tace Ke kadai ce?naga bakowa Inche Lpy?

..tace eh fa daga shiga kitchen nafito sai banga ummah ba,bari dai na duba mana abincin sai naxo..

Sai Ta gyada mata kai,bby maysam ke Neman fara kuka sai ta dago ta ta aje ta kan cinya tana bata nono

,...yadda yarinyar tayi shiru ta nitsu tana tsotsar ta sai ya sa takafe ta da ido tana ganin kamannin mijin ta,.ranar ma tanaji hajy na fada cewa mohan bai wani sha nonon uwa ba sabida hjy mahnoor ba ita ta raine shi ba
...tace hjy mahnoor ta samu cikin shi ne a lokacin da take kokarin fara kafa career ta na fashion and desing a duniya kuma tana so yayi karfi sai kawai ta fi bada muhimmanci achan fiye da shi.

Sometimes idan hjy na bada labarin yarantar sa har abun dariya yake bata,yanzun ma wani abun ta tuno zatayi dariyan amma saiga hawaye sun sako mata

...wani mugun mugun son mijin ta da kewar sa ke neman mata illah,'dan kadan tahade goshin ta dana maysam tana kallon kamannin sa anan tana kukan zuci.

Maryam Tray din hannun ta ta aje Ra karaso kusa kanta tace Banafsha?...
Bata ma ji ma ta kuma cewa
nafsha... adan firgit ta dago cikin sauri Ta kuma sadda kai tana goge hawayen ta

..maryam da shiKe ta dade tsaye kusa da bayan ta tana kallon abunda take tuntini tuni ta karbe baby ta ajiye gefe ta Dawo ta tsuguno gaban ta

tace Banafsha lpya kuwa,meya sameki kike kuka? Bata  Amsa ba Tayi shiru...ko maysam ne bata da lpya Kin  fada ma doc?what's going on....

Da maryam ke tambayar ta A haka sai taji She cudnt hold it anymore,wani matsanancin kuka ta fashe da shi tana cewa babu komai kawai wani abu nake tunawa..sai kuma tayi shiru Ta cigaba
..hankalin maryam Kuwa tuni ya tashi,but she's very tactfull dan haka ta nitsu ta riko hannun Banafshan gently Tace kawata"..kar kice min iyayen ki kike tunawa...ko su hjy sun bata miki rai ne?...Tayi saurin girgiza kai

tace ah'a Maryam...tun daga nan bata Sake cewa komai sai kuka...

Gefe da ita maryam ta Dawo zauna ta jawo ta jikin ta Tafara rarrashin ta,Maryam duk wani kalma na hakuri ta fada mata da kyar ta dago Ta hadiye kukan tace Mata maryam Im not happy....my marriage,... ni bansan ya zanyi Da shi ba,It s alwys hurting Me..what shud i do pls..?

sosai maryam ta shiga halin tausayin ta Data ganta a hakan ayanda suke rike da amincin junan su itama tuni ruwan hawaye ya taro a idanun ta,tace Banafsha dama yaya mohan ne?Kar kice mun fada kikayi da shi,Pls talk to me Nasan ki da boye damuwa Aranki,Kuma ba yadda xaki rike abu aranki ki samu saukin shi...pls whats wrong?meya faru ne nafsha kefa ta Yaya Mohan ne shi kadai, shima naki ne ke kadai.

Cikin shessheka Banafsha Tace ah'a kam, yaH mohan baya ma kula ni yanzu Ni tunda na haifi maysam na dena gane kansa,i just wonder if he care about me or not he changed alot
....i think he doesn't like me Anymore..Dan yamin abu nayi fushi Then he dosnt want to talk to me again,kuma wallhy ina son shi Bazan iya jure hakan ba..

Yanzun haka anty Nimrah tanada ciki,hanklin sa gaba daya yake so ya maida shi chan..naga ko maysam din ma yana so ya dena kulawa Da ita kamar da.
.shikenan Ni Sai na dawo musu hoto agidan Ko?
Wani kukan ta saki Ta hade kanta da gwiwa,
.
Maryam sai ta danyi shiru chan ta kalle ta tace toh kiyi hakuri Banafsha,but i can't believe that haka kawai yaya mohan zai canza miki bayan kin haihu masa..,ni a yadda nake gani yake tarairayar ki gaskiya inaga kinyi masa wani abu ne.. So fada min..Banafsha me kika masa?

Dagowa tayi kamar zatayi Magana amma sai tayi shiru

Maryam tace "look Kar kiyi min shirun nan naki, idan ma baki sani ba we have to think right  now,bazan iya barinki acikin kuncin nan ba..

Banafsha Share hawayen ta tayi
Ta gyara zama tace inaga Fa tun akan lokacin da nafara nakuda ne,anan tayi highlighting ma maryam abubuwan da suka faru,ta Karashe da cewa ni Da farko dai sai naga kamar babyn sa Dama ya so bani ba...maryam what do you think am realy confused About him,kuma fa kinji abunda anty nimrah tace min
...kafin maryam tace zatayi magana sai su kaji gyaran murya akansu

Ummahn ta ne tafito daga bayan gida a daki, toh data jiyo abunda Banafsha ke fada sai taki tayi interupting dinsu
Komai aka fade shi a kunnen ta..

Banafsha A sanyaye ta rusuna tace ina wuni ummah ashe kina ciki..

Ummah da tuni tadade da shiga kundun nazarin abun da tajin bata ko amsa ta ba A masife tace
Mena ke ji haka Banafsha,dama A haka kike rike auren ki?ashe ni ba uwa bace da baxaki kawo damuwar ki waje na ba?

..wani hawayen ne suka zubo mata kirjin ta na Bugu,.. tace ummah Kiyi hakuri, baya bari na fita ko ina Ne yau ma dan baya kasar ne na fito Bai ma sani ba"
...ummah tace yimin shiru awajen,ai kin bata min rai Banafsha,
Banso naji haka daga gareki ba.

nan ta hada su Biyun tayi musu fada tana cewa bawani uxurin da kuke dashi a wannan lokaci,

ure just 16-17 ai tunda kuruciyar ku zaku ji dadin aure ba sai jikin ku yayi nauyi ba,

ga yan mata nan ire iren ku sun bude ido sunsan meye duniya take ciki
'Yara yan 16-20 duk ina ganin su suna xuwa nan siyan kayan gyara,wani bin mu manya ma sai su nemi sufi karfin mu Ta Fannin Rike miji da tattalin shi,amma wai ku da kuke yara na Har zaku zauna kuna shirme  ana cin tuwo akanku haka?
..Banafsha ko dai baki son shi ne?

Tace ah'a ummah,..ina ....... .. son shi..

Ummah tace Banga alama ba, To tashi maza ki biyoni daki, ke kuma maryam ki kula min da jika na.. tace toh ummah.

Ayayin da Banafsha ta bi bayan ta daki ummah tana zama Banafsha ta nemi Waje itama kusa da ita ta zauna A kasa ta sunkuyar da kai..

Dan shiru ummah tayi tana kallon ta,cikin nitsuwa da lallashi tace,ba fada nake miki ba yata Share hawayen ki muyi magana ki dena kuka kinji!?

A hankali ta dago jajayen idanun ta tace kiyi hakuri ummah nasan nayi kuskure Aure na ya lalace min.. wallhy bansan yazanyi bane Shiyasa.

Ummah tace um um Banafsha Kidena fadin baki san ya zakiyi ba...,ke kuma fisabillahi haka akeyi!? Da kika haihun shi yafada miki baya sane dake?ai Wanda yaso abunda ka haifa yana son  ka Ne..Wato ke duk wannan baki gani ba ko, kishi zakiyi har da Yar cikin ki?Banafsha Lafewa tayi kadan ta sharo fuskan ta Cikin jin kunya

...."umma ta cigaba da Cewa haba Banafsha ta, Ina kike kai tunanin ki Ne? kefa Ya mace ce,keda nake ganin kwarjinin ki afili ashe har akwai kishiyar da zata xuga ki Kiji ta? yanzu fa kin girma, ke ba yarinya bace da zaki tsaya ki kafa hujja da maganan kishiyar ki kowa takansa yake a gidan miji ko cemiki Tayi Ita  bata Kishin shi?,mijin ki might be having problem somewhere else wanda baya son ya shafe ki a condition din da kike a lokacin da kika haihu,kece yaka mata ki dinga bada uxuri kafin ki yanke masa hukunci,shi aure ai ba wasa bane he is ur life partner,alwys stay put and be open to him Kifadi masa damuwr ki,kar kiyi shiru da abu aranki dan wata rana zaki tafka mummanan kuskure.

Sannan The very next time naji kin korashi ajikin ki da sunan kina fushi dashi har gidan zanzo na same Ki naci kaniyar ki,dan baki da hankali Mijin kin xaki raba gado da shi wayace miki ana haka..

Ummah tace,Toh kar nakara jin kinyi hakan dai, don ba tarbiyar mace mai kamala bane,..aure ai bautan Allah ne don haka bason ranki zaKi rikayi ba,maza ki sa ma zuciyan ki ruwan sanyi ki san me kikeyi
go back to your man now, ki bashi hakuri kar ki yadda Ki kyale shi har sai ya hakura

Dan Siririn hawayen ta ta share Kafin tayi magana umma tace Oya Tashi kije ki dauko maysam kizo..ina tana dai karban nonon ki da kyau tace eh ummah
",yawwa to dauko ta..
A sadade ta mike ta fice kafin ta dawo ummah ta fito dawasu special packages daga cikin kayyakin siyarwan ta Ta aje Domin ta,tace goya ta maza ki koma gidan ki kar ki kara makanki laifi,Babu kyau fitowa haka kibari yabaki izini Sai kizo kuyi hiran ku

Tace toh ummah nagode...

"nan ummah ta debo kayan tace Ungo karbi Wannan Turaren da kin gama wanka kizuba a clean water ki shiga ciki na minti 10,Ga Kuma wannan kije ki shanye yau da gobe duk sun ishe ki..Banafsha Abun ta karba tana juyawa a hannu Wani hadin kutungwila na pure zuma dabino kwakwa  da sauran hadin da bata san me ajiki ba,ansa shi well packaged agoran yoghurt tsaban Abun ya tsumu har oil Din fruits din kwakwan dake jiki na kama goran gashi coffe brown Yana gamshin dadi kamar Wani Yummy chokolate,sai wasu tsumin Suma agora anma tace mata kar ta bari Ya kwana ta shanye shi A yau Din..

Banafsha Har bata san kalman da zatayi godiyan da shi ba Don kuwa sosai taji sanyi aranta

,rarrashin ta ummahn maryam ta Dada yi zuciyan ta cike da tausayin ta"
tunanin ta itama shine yanzu da ace bata duniya wazai rike mata mata nata yar?

Ko da taga Yanayin rayuwar Banafsha da sauran Kananan Yara Irin ta  wanda Suke rayuwar auren Kuma Basu da uwa a duniya,

takan jinjina masu Sosai tasan Hrdly suke sanin inda xasu aje kansu a kafadar wani suyi kukan damuwar su..

Haka Banafsha tayi sallama da su ta koma gidan ta ko kiran driver ma bata yi...'

'Wanka ta fada tayi sallahn magrib,tunda ta samu taci abinci kadan ta shiga kundun tunanin abunda ummah tace

.. After 9 na dare ta kwantar da maysam,abubuwan da ummah ta bata ta  shanye sannan ta bi gado n ta ta kwanta,

Ji Take kamar ta gama saita tunanin ta akan komai,Sai dai har yanzu Tunanin salo da yadda zata bi ta bashi hakuri ke damun ta, by 8am na safe  dama ranar monday ne a tsanake ta gama komai har ta yi breakfast ta shirya maysam cikin all white baby set na jimmy chuu yarinya ta fito  angelic as usual

Tunda tayi amfani da turaren  wanka da umma ta bata qamshi ne kebin ta a dik inda ta tashi ko ta zauna"

Da safen Dakin sa ta nufa ta bude tana kallo Daga bakin kofa,

kwana biyu da bata zuwa nan akai akai sai da taga banbanci

nan ta shiga kintsawa tana buge kura,within some minutes ta share ko ina ta goge, wani hadadden bedding set  ta fito da shi pure sea blue mai laushi ta shinfede gadon sa da shi,bata fice ba sanda ta tabbata har toilet din dakin na qamshi da sheki

Sai chan da yamma wajen karfe 3 saura taji driver ya ce shi xai je dauko
Shi a airport...

nan ma ta sake wanka ta shirya kanta cikin wani pingelin gown marar hannu pink da ita babyn Ta suka zauna a daki..

Bata sani ba ashe tana shigowa daki Nimrah ma ta shigo gidan

agurguje ta haura sama Dan dama ta riga ta gama setting plan din ta. .

Dakin mohan ta fara lekawa Taga ko ya dawo ganin an sauya komai an tsaftace yasa ta fashe da dariyar mugun ta"irin wato har anzo dubawa ko ya dawo ko?
Tabe baki tayi ta Shigo
A Kan kujeran dakin ta zauna ta aje wani magani In form of pill  akan stool nesa da ita

..,dama wanda tasha na abortion din already ya fara aikin sa tuntuni Don har ta fara serial bleeding,dama lab scientist din ladyn tace mata muddin ta sha wancan karamin pill din jinin zai zubo mata dayawa har yabi kafar ta and is very risky duk da haka bata damu ba..

Wayar ta ta daga ta kira faisal,shi sam baya son muamala da ita amma tsoron ta yake ji,.
nan ta tanbaye shi inda mohan yake,shi ya kayyade mata
Cewa nan da minti goma ma driver zai iya shigowa da shi Gidan,

Tana katse wayar ta mike ta bude kofar dakin San
sai ta wani irin sake shi da karfi yayi kara kamar an shigo ne aka rufe....

Sau biyu tayi hakan,kafin Banafsha ta ji,Ita Kuma sai ta dauka ko shine ya dawo

ba wani bata lokaci ta taso dan ta zo ta tabbatar Da hakan,

Wani malak nimrah ta kwanta kan cushion dinsa ta sake takalma da jakan ta akasa ta riko cikin ta tana wash wash,..

Wani dada kara sautin nishin ta tayi ta rikota kasa musamman data ji sallamar ta...

Itako Banafsha mamaki da tsoro ne ya cikata,tace antyy lpya kuwa. .?

Wani munafukin
Kuka nimrah ta sake,tace ciki na kemin ciwo Banafsha .. Can you Pls help Me ga magani na chan dauko min nasha.

Arude Banafsha tace ok, sai ta aje babyn ta akan gadon sa ta dauko pill din,

gefen condenser tabi ta tsiyayo ruwa ta zo gaban ta rusuna tace sannu anty ga shi nan na kawo miki,

Ba laifi Nimrah ta karba ta hadiye agaban ta Tasha ruwa.

Cup din ta mika mata tana rike dashi tana kallon yadda take wash washhhh,jim kadan kawai Nimrah tasa ihu sai zirrrrr jini yafara bin kafar ta.

A rude Banafsha tadafa kafadan ta tana furta innalillahi wa enna ilaihi rajiun..sorry
sannu

Nimrah Tace sake debo min ruwan zansha,ba jira ta mike tana dawo mata da ruwan,Ta karba ta sha..

Cikin tausayawa Banafsha tace
Anty Ko na kira driver akaiki asibiti"

Dan gyara zama nimrah tayi Ta Kalle Banafshan,

"ita dama already anyi inducing mata pain reliever,duk murde murden munafirci take Kawai dan ta zulma ta, tana jin zafin Dai amma is bearable"Sai tace bazan je asibiti ba sai dai Za'a Akaiki,dan kuwa yanzu xaki samo Ciwon tabin hankali

Cike da mamaki Banafsha tace mene?Ki kace me

Nimrah tayi dariya tace Yes u heard me Right,Dago rigan ta kadan tayi ta Gwada ma banafsha jinin Dake bin ta. ,tace Wawiya Kawai Toh This is all planed Dama so nake Kisan kin bani magani da hannun ki...,Ni zan fada ma Mohan kin bani maganin zubda ciki a ruwa Nasha Cikin da yayi min ya xube,

So mrs Banafsha Can you Deny it?tayi dariya Mai shake da tsegeran ci

Ganin Banafsha ta shiga shock tayi durus Cikin rashin sanin Zatace, yasa ta kyabe baki Tace

"ki ce masa karya ne Mana, or are you two fighting?ta sake fashewa da dariya,

well basai kin amsa ni ba nasan komai tunda nina hada ku,amma kinsan makomar ko kuwa? mohan Zai ki ya yarda dake sai ki dawo mahaukaciya Ya kora ki agidan sa. .simple.

"nan Banafsha ta dago kai Wasu takurarrun zufa ne suka fetso mata Cikin tsananin mamaki ta sake karamar dariyar takaici tace
Hmmm Heheheh"
..Lallai fa, So What do you mean now anty?kina nufin sharri Za kiyi min Yanzu yanzun nan ko? Toh Menayi Miki haka? Ko duk sabida yaya mohan ne? I tot ure in pain Ni sam ban fahimce ki ba Fa are you for real?..,Tayi kwafa ta na kallon nimrahn Kanta har na mata kaikayi

Nimrah tace i am,ba wasa nake miki ba,kwanan ki ne ya kare..gwara Ki Sake ki fadi abunda ke ranki Don gida na xaki bari yau,.

Idanun Banafsha take sukayi ja cikin rawan murya tace akan me?zamanki nake ne..

Nimrah tace ai ba mai zamani Dani dama,I have neva liked you Kuma kin sani,dokar zama na dake shine duk abunda zanyi na tarwatsa rayuwar ki sai nayi shi.....

Wasu hawaye Masu zafi ne suka sauko mata tace anty Shine Har da kashe dan cikin ki?Ure this wicked? No wonder kikace yaya baya so Na abun ciki na yake so,so it was all your plan right. Muryan ta har na rawa ta karashe

Wani dariya Nimrah tayi tace Hmmmm Banafsha kenan Ure dump,stupid blind..Wato wannan kawai kika sani ko?It's ok,wasa Dai ya kare Kinga wanda yaci baya zaiyi ouuuuut...

A zafafe banafsha tace Wallhy Baki isa ba,munafuka kawai"Allah ya tuno asirin ki,ashe Dama hada mu kawai kike dan ki raba ni da shi?

"Basar da harzukan tan Nimrah tayi tace
Deny it Mana bake kika Ban magani nasha ba?

Wani Kukan Fushi da takaici Banafsha ta fashe da Shi Cikin ranta ji take kamar Ta kashe Nimrah dama ashe Haka take?
Tace toh,In na fice Anan ai zanga wa zaki lakama sharrin akace Miki kike kadai kike da bakin sharri,zan fita kuma ba Wanda ya isa yace nazo nan na baki wani abu

Banafsha nasa kafa Nimrah ta shake ta

Charaf sai suka ji sallamar sa
Wani Ihu Nimrah ta sa Tace wallhy baki isa ba Sai kin fada min meyey kika saka min aruwan ciki na ya xube

Wani baru jikin Banafsha Keyi kuMa ita ce ta fara daga ido ta kalle shi shima Kuma kallon ta yayi

Kai Lpyar ku kuwa?Ya fada da dagon murya Yana kallon yanayin su...

Cikin wani munafukin kuka mai kunshe da sinadaran makirci Nimrah tace Mohan na shiga uku,ohhh thank god ure here, walllhy
Matar ka zata kashe ni.

Cikin kuka Banafsha Ma tace karya kikeyi zaki kashe kanki dai

Wani sake baki Nimrah tayi har yana bari Yana zubda yawo, tace Daga cewa ta taimake ni tabani pcm shine zata hado min da wani maganin?

Cikin kukan tace mohan Look at me,i don't know what's happening Sai bleeding nakeyi,mohan i think lost my baby ..jinin dake bin kafar ta talakato a tafin hannun ta tana kukan fitan rai tana kallon shi kamar ta zare.

Tunda Banafsha taji me take cewa ta shiga shock Tana kuka bata farfado ba A durus ta tsaya ta waro ido tana kallon nimrah ji take kamar Komai a film

"anty Ki kace Ni Banafsha na baki wani magani?Ta iso gaban ta a hargitse,are you mad or something?Inaga fa baki da lpya ke Ki fada masa abunda kika ce min Mana?
Why are you implicating me For god sake

Sai Ta dawo gaban sa tace
Yayah She's lying To you,ai tace plan takeyi Dan ta raba ni da kai,  yanzun nan Fa Ta ce na bata magani bata jin dadi what will i gain da har zan baki maganin zubda ciki..? A mugun fusace Banafsha ta fada dan bata masan ta fada ba,.

Mohan shiru yayi yana mamakin su,he was like so sun ma zubar da cikin?

Banafsha kuwa kirjin tane ke bugu tuni taji hankalin taya tashi dayayi mata shirun

Ga Nimrah sai tsuma take Agaban su tanacewa cikin ta cikin ta ancuce ta

Cikin takaici mai tafe da bacin rai,Tace Kema Baxaki  fa fada masa gaskiya Bako? ni bansan meke damun ki ba kuma baxan dauki alhakin komai ba

A haukace Nimrah tace shut up bitch,muguwa kawai azzaluma walllhy nafi karfin munafurckin Banafsha

u cannot cheat me twice,ga asaran ciki ga munafurci da karya ?yaushe nayi miki magana

Ai dama nasan baki kaunata,komai xaki iya cewa,Wato dan kin san nafiki gindin da zai haifo Da namiji shine bari ki cika mumman burin ki akai na ko?

Wani yunkuri Nimrah tayi kamar zata tashi ta cahkomo Banafshan sai kuma ta xube akasa ta kara sa da ihu tuni jinin ya fetso sai gashi tafara karkawa

"Shikam tsaban mamakin su sai ya zamto musu dan kallo,nimrah najin jiki amma haka ta zake tana cewa Banafsha ta zubar mata da ciki dan bakin cikin zata haifo da namiji..

haka itama Banafsha ta zage tana cewa bata san da hakan ba,karshe kuka Kawai ta fashe da shi Bata iya cewa Komai
Nimrah ta xautar da ita tasa ta bayani har makokoron ta na mata zafi Har ciwo kanta ya soma yi tasan inda da halin da zuciyar ta zai fado kasa Shima da tuni ya sauko,

Yana shiru

Sai da suka gama musun su Sukayi shiru,ya tsuguna gaban Nimrah yana observing zuban jini,

kafafun ta ya dan ware kadan sai ya ciro handkerchief daga aljihun sa ya dan share jinin da suke biyo sawun kafar ta
Ya Bashi critical look...

Dan sosai  Ya dago furucin kowa gani yake kamar Yasan mai gaskiyan acikin su

Nimrah Sai wani washhh washhh take,cikin kuka tana cewa wallhy bazata yarda ba.

sai ya daga ido ya kalle ta yace Nimrah relax Pls zan kira aliyu yanzu yaduba ki ,ko kinajin jiri ne?,tace ba sosai ba Kuma wallhy sai ta biyani baby na..yace to ki nitsu kifada minene ya faru Kar kuma naji Muryan kuka

Nan ta sauya kama kamar tsohuwar makira tace"..naxo gida kaina na ciwo nace ta taimaka min da pcm bansan me tayi ba daga nasha sai nafara bleeding,Ni nasan dai aruwa kika xuba mun wani abu

charaf Banafsha ta yanke maganan tace ohon miki,nidai ba abunda nayi miki kuma kema kinsa ni,Aniyar ki tabiki abunda kike so Ya faru dani bazai Faru Dani ba, mugu..wa kawai

wani mugun kallo ya dago ya bita da shi yace waya Sa bakin ki?
Ina wasa dake ko?

hawaye masu xafi ta sauke ta dauke kanta Gaba daya jikin ta na karkawa

wallhy ciki na ya zube bazan yafe miki muguwa kawai...

Yace Nimrah, its kk muje dakin ki kijira shi anan ina xuwa.

Tallafo nimran yayi akafadan sa
suka fita su ukun
Banafsha na bin su a baya gaba daya abun duniya ya dameta

Ashe dama haka take?babban munafuka,har agaba na ma tana hada min Sherri,?kawai dama tana so yaya ya daura min laifin komai ne Ya kOre ni..

Mohan Aje ta yayi akan gado,ya nemo abu ya goge ta dashi

wayar sa ya cire yayi kira aka zo aka duba ta inda Wani doctorn daban ke tabbatar masa da lallai wani magani mai karfi tasha a ruwa ya zubda mata cikin...

Alluran da aka mata Alokacin ya na sa ta layi amma Haka ta bude ido tanace masa Mohan kaji ko?

Ko likita ya fada ita ce tabani maganin Im sure acikin ruwan ne..

Banafsha sai jikin ta yayi sanyi rungume da babyn ta ba abunda take sai hawaye

....a haka Har nimrah tayi barci bai juyo ya kalle ta ba..
Maganganun da  Nimrah tayi tayi yayi mummunan mata illah Acikin ranta

Ita hurts her to know that gaskiya yana gaban ta amma bazata iya bayyana Ma kowa yagane ba"

Tunanin makomar ta take Tayi A wajen mohan,Don tasan bai isa yace ua gane kan fadar sun ba,abu daya ne Kawai afili Shine Nimrah ta laka mata alhakin zuban cikiN ta

...sai da Taga ya mike xai koma dakin sa tayi sauri ta aje babyn ta biyo bayan sa...

Tace Yaya,...yaya mohan pls wait and hear me out"basar da ita yayi...bai tsaya ba sanda ya bude kofar dakin shi,..

Wasu mugayen kallo yabita da shi,a sukwane ta dago ta Kalle shi
Tace Wallhy ba haka bane ya faru,ita ta ce na bata maganin zata sha bansan niyyar ta bakenan da bazan bata ba"She said she wanted to ruin me...Allah kaji na rantse maka Sharri take min.

Cikin dakewa Yace ok doc ma yayi karya kenan?
Kin bata wani abu ki baki bata ba

Tace eh, ai shima baisan abunda ya faru ba..."Yaya kayi hakuri kar kace na xubda mata ciki wallhy banyi hakan ba

...da taga irin kallon dayake mata har kasa ta nemi silalewa tana kuka xata roke shi,hannun shi take da niyyar kamowa yayi saurin kwacewa ya hade rai,,a masife yace don't you dare touch me again,"kin dauka xan kashe kaina akan ki ne?...im not even surprise inkinyi hakan
Ba abunda kika
Ga dama shi kikeyi ba?,ok Allah ya bada sa'a,..and just get out of my sight....right now.... ya daka mata tsawa dai da ta razana taja gefe

a rude tace yaya no,pls don't take it that way wallhy walllhy karya anty takeyi min,i just helped her dan naga bata jin dadi kuma ita tace nayi mata hakan bansan mesa doct yace maka nabata magani ba..yanzu har ka yarda zan iya yin haka...?

Kukan Ta sosai yaKe Ruguza saitin brain dinshi Da shike hankalin sa da tunanin sa basu kusa Shikam Baima jin me take cewa kawai sai
Yace eh,and i said get lost bana son ganin ki nace ko?Tsaki yaja...zai rife kofa tasa hannu zata tare ko ajikin sa ya buga da hannun nata saida tayi kara Taja da baya..

Anan ta xube a kasa Tana kukan Tana tapping kofar sa Tace Yaya mohan Pls don't send me Away,kayi adalci ka ji abunda zan fada maka,yaya Mohan Pls Open the door...Kayi hakuri Kaji?Pls im sorry.

Haka tayi tayi har ta gaji tayi shiru,

ShIma Bai iya motsawa ba Tun tuni jingine yake abakin kofar ya lumshe Ido yana jiyo ta.

Banafsha Sosai ta zuciya Abun ya matukar kona mata rai,sai Shessheka take tayi shame shame akasa tana zaune A kofar dakin sa..cikin ranta take cewa yanzu ta hada ni da shi kenan?in ya kore ni A gidan sa fa?She's a devil,She used Me...
munafuka Ce kawai shegiya,makira annamimiya Muguwa  bazan yafe miki Ba, kuma bazan bar gidan nan ba..
Hawayen ta ta goge tas Kasan makoshi ta Furta
Ai wallhy kuwa bata isa ba,sai ta gaya min yaushe na bata maganin xubda ciki Kona xame mata Babban fitina agidan nan..a masife ta tashi ta nufi dakin nimrah fuuh ta bangaje kofar Babu ko tsoro aranta..

Gani tayi har bacci ya debe ta,bata hakura ba dan kwata kwata bata yi tsammanin haka Asalin halin Nimrah yake ba..

Yarta ta dago ta rike sannann ta shiga kallon nimrah dake bacci tana cewa

"I was respecting you sabida na dauka kin girme ni ashe ke banza ce Baki cancanci komai daga waje na ba girman ma nafasa baki

Kinyi kuskuren nuna min kazamin halin ki in rashin imani kike ji dashi wallhy nafi ki,..ashe har xaki Iya zubar da ciki dan kawai ki hada ni da miji na?,only god knows wHat uve been Saying to Fool me agaban sa Im sure that's not all,...toh da kina ji na da bakiji na
Ki sani kinci bashin da bazai Taba wuce Miki awuya ba,

I will teach you a lesson you won't eva forget...

Daga ni saike a Wajen yaya mohan,Daga yau sai kin gwammaci da baki Fada min Ke wacece ba bare ki hada min wannan sharrin rainin wayo,u think im a fool,toh even a fool at forty cannot be a fool forever

Uve Bring It on Ko? i will take you to the finish Insha Allah da bakin ciki na zaki bar gidan nan.

Wani zazzafn Tsaki taja a xuciye ta wuce dakin ta,akan gado ta Ajiye maysam ta Shiga rarrashin ta Har tayi bacci

Just 3months da haihuwar ta amma har yanzu babu Wani sassaucin da ya shigo mata

Mikewa tayi ta doro alwala ta yi nafila Tana rokon Allah,zuciyan ta cike take da tsoron matakin da mohan zai dauka akanta gobe,gashi ta kwallafa Son shi aran ta,ji take Kamar idan yace Ya sake ta ta bar Masa gidan zata iya zarewa.

gado Ta koma tana mai cusa kanta cikin pillow tana kukan zuci,..yau Kama tasan ranta
yayi matikar baci

Ita banda tsoron Nimrah datake ji Tuntuni ba Da babu wani mumuman zargin data ke mata akan komai tsakanin su

...sai gashi Nimrah ta bata mamaki yau ta nuna mata wacece ita boro boro

Tace uhmmm,ai daga yau ko mutuwa take Na asali bana kara yarda da ita,shima Mijin da take gadara akai  sai na kwace shi kuma nayi yadda naso dashi

Idanun ta har sun haura tsabn tayi kuka Juyi take ta furta,.hmmm she think she's smart ko har da cemin dump mswww,i maybe dump, but  im not stupid.

Da safe ma haka ta tashi da shi aranta..Sosai tayi zuciya.,sai dai ko kadan bata jin zata hakura ta karbi defeat

instead ma wani karfin gwiwa take ninko ma zuciyan ta nacewa lallai itama sai ta nuna ma nimrah irin mata salon kissar Komai ma yafaru bata damu ba

Shikuwa mohan Tun jiyan ya kasa aje kansa Waje daya bare ya yarda cewa Banafsha xata iyayin haka Ma Nimrah

But Wani zuciyan nace masa kar ka amince da mata kishi ma kawai yana Iya haukatar da tunanin su,su aikata komai

Ajiya cikin daren Faisal ya kira

Tun Kafin Faisal din ya shigo Sai yayi packaging Handkerchief din daya goga jinin Nimrah akai ya rufe Awani envelope

sai ya ce masa kayi Sauri ka kai ma aliyu Wannan sakon kafin ya bar asibiti.

Yace yeS sir Ya wuce Ya tafi

sako ya Zauna ya tura ma aliyun Mai dauke da Kalmomi kamar haka

"Dude,nasan xaka iya gane min siffar Wannan abortion din,I want everything In details And  i want the result Today Xan jira ka a kofar gidan ka by 10ocl In ka tashi.

Daga nan Wanka yayi,ya fita agidan bai sake dawowa ba sai da 10 na dare yayi ,ya nufi wajen aliyu.

Acikin mota suka xauna ,Dr Aliyu Ya mika masa report,yace Mohan What's going on Ne?Jinin waye?

Mohan Bai Amsa Saida yagama karanta result din Ya lumshe idanun sa tare da sake ajiyan zuciya yace Aliyu Nimrah ce ta zubda ciki and she was claiming that Yar uwan tane ta zubar mata

.....AliyU yace what?Nimrahn bata da hankalin ne Da Banafsha zata bata drugs harda pill Dinshi?

Yace Bar rainin wayo, i just found Out now Dama kawai gaskiyan nake so nagani
,tace wai pcm ta bukata Sai ita kuma wancen ta bata wani..

Aliyu yayi dariya ya kada kai yace But this Result isn't saying that at all,ko ba kagani bane?
Wannan Cikin nata ma anxubda Shi almost 16hrS ago..Jinin ne kawai aka ingizo

To meyasa Ita Nimrah take haka Ne?Kai mata akwai fitina wallhy

Tabe baki Mohan Yayi yace forget dama kawai nasani Ne...tayi ma kanta.

Aliyu yace pls kayi haKuri Mohan

Wata Miskilin Murmushi Ya sake yace I have to go now Saida safe Kawai Sukayi sallamah

Mohan Tunda yajI hakan hankalin sa Sai ya kwanta Sosai.

Sai dai Maimakon yayi reacting Ya nuna Musu yasan komai Sai ya basar Musamman Ma Nimrah,

sai yayi Shiru Yana kallon
Su duka kowacce da abunda take ayyanawa Domin Ya bi nata qudirin....

A ransa Yaji haushin zuban cikin amma bazaka san Da haka ba

a safiyar ranan Nimrah tayi sheme sheme tana jira yazo ya mata hidima ya kula da ita,amma sai shiru take ji har 10 Ya wuce batayi wanka ba bare taci abinci..

Mai aikin data ke kyama ita ta Koma dafa Mata shayi Ta taya ta shiga bathrum Ta tsaftace kanta

Sai tace Tunda aranar farko Ne bazata dauke abun komai ba Maybe Mohan yana bakin cikin Xuban cikin ne,Gashi ta jira taji Ko an kore Banafsha Agidan shima sai shiru

Gashi an bata 2weeks bed rest Babu fitowa

sHikuwa Tunda yasan metayi sai Motsa Motsan bakin halin shin suka Sauka A kanta gaba daya sai ta dena gane kansa

Zai  Dai shigo duba ta amma sai yaga dama sannan bazai fi minti 10 ba xai fita,sometimes Na a tsaye Kuma Duk Iya kisisinan ta baiya kulawa

Shi bai rarrashe ta ba,Shi bai mata fada ba, mata komai ba sannan hannun shi baya kaiwa jikin ta da Sunan taimaka min na tashi ko zan sha ruwa

Wani bin intana fade faden ta sai yayi shiru ya tSura mata ido Ko tana koke koke Ya basar Ya juya kai yana latsa Wayar sa

Ya Gama Lura Damuwar ta kawai shine ya wulakan ta Banafshan shi,Acikin ranshi sai dai yayi murmuShi  yace yarinya Ai kin makaro ita din ma ina nan A kanta...

a fannin Banafsha Sam Baya sake mata Itama,.shi tunda yaga ta kafe akan maganan Tana so ya saurare ta,sai ya fara punishing din feelings dinta,

A kullum xai Nuna kamar 100% ya na kula da Nimrah kuma yana tare da ita kodan ya bata haushi,.

Wani bin ba dakin Nimrahn yaje ba amma Inta fito zata wuce zata gansa sau dubu a kofar dakin 

Daga tayi magana Tana son ganin shi sai Yace baida lokacin sauraron ta shi Nimrah bata da lpya yana kula da ita

Haka Banafsha Tayi ta danne zuciyan ta taki tayi fushi,har abun ya kai ta makura Sai ta Dena bibiyan sa

Shi baiyi hukunci ba kuma vaice Musu komai ba,nimrah ma dataga wulakncin san yayi yawa sai tayi zuciya da shi tace Ma hasis ai Banafsha ta tsafe shi Ne ta lashe masa zuciya.

Bayan kwana biyu Dayaga dukan su sun sha jinin jikin su da shi,Sai ya shirya tafiya conference abinsa

Ranar da zai tafi da safe Banafsha tana kwance da babyn agefen ta ya shigo Bata sani ba Don Sai da yakai tsakiyar dakin kafin yayi sallamah sai ta dago Kai.....

Kallon da yake mata yasa bata iya hade ido dashi ba ta gaishe sa Cikin sanyin murya

Gaban shi na yawan faduwa aduk sanda yaga fargaba a fuskan ta Yace ki shirya,gobe zakije gida...bayan kwana biyu zamu zo.

Wani garas taji maganan ya sauka a kunnen ta Tace "Ya Allah, ko dai korata Yaya mohan yake so yayi?. ,Tuni sai taji Bugun zuciya

a gaskiya bata so taje ko ina ta barshi agidan da Nimrah,
Tace yaya mezan je yi agida? Why not na jira mu tafi tare da kai.

Yace a'a..haka Kuma yaki fir karshe ma Data takura sai yace Kawai ta tafi shixai kula da matar sa ne..

Abun ya mata ciwo Haka ta kwana da maganan aranta Tana jiyawa,da safe Data farka gani tayi an dora maysam black diamond brace a wuya mai shape din love mai kyau Tsadadae

data bude sai taga Hoton shine da na babyn sa aciki
Murmushi ta
danyi Tana kallon yadda sukayi kyau,sai ta Shiga kimtsa Kanta Amma da niyyar babu inda zataje sai Da shi

Tana sane da bayanin family function din da aka shirya gaba daya familyn za'ayi,Dama hajy tace on 23th ne gashi Yau its just 18,ita dai sam bata so tabar gidan

gashi ma ba acikin garin abuja za'ayi ba a kauyen da su hjya mamah suka taso ne..
Cikin tunanin ta sai tace toh meyesa  tun ranar tafiya baiyi ba zaice naje gida?
...tace Toh nidai bazanje ko ina ba.

Haka tayi ta zaman ta bata gansa ba Kuwa gashi yanzu basu ko ga macici da Nimrah

, shikam Tun Yana mota zaije kano Ajiyan hjy tace masa ya bataga Su banafshn ba?
Yace mata Nimrah bata da lpya amma Banafsha zata zo

Yana isa kano Driver ya Kira ya aiko Akan yace mata maza ta shirya Ya kaita,Bata ma san baya garin ba

Gashi tsaban bata so taje ba da kuka ta fita Haraban gidan Da kayan ta

Nimrah ma farkawa tayi bata ganshi ba gashi bata san da maganan family function din ba Bare tafiyan dayayi.
,Daga tsayawar ta jikin window zata daura towel sai taji hayaniyan mai gadi da driver she tot ma ko mohan ne zai fita Baizo ya duba lpyar ta ba, tana kuwa lekowa ta hango ana dura kayan Banafsha a mota,

Ita kuma ta bata rai sai jijijiga babyn take agefe

wani Kyakyawan murmushi Nimrah tayi thinking that Mohan ne ya kore Ta duk Ba'a yadda taso Din ba .

Itama xaman jiran dawowar Sa take yaxo suci rayuwar su su kadai amma sai shiru har dare ya rufa,gashi zata kira shi bazai daga ba. .

Bai tashi kula ta ba sai chan dare yayi nisa anan ma"ya turo mata sakon cewa yayi tafiya zaikai 1 week bai dawo ba.

Taji haushin haka Matuka Wai shi wani irin mutum ne Dabai damu da damuwar kowa ba? ,but tunda taga babu Banafsha a gidan bata wani daga hankali ba..

taso ace Ya kula da ita Wanka,cin abinci Abaki,Taga Dai yana lalubar ta akirjin sa kamar yadda yake yi ma Banafsha,amma Duk ina haka Nan take fama da kanta komai ita take yi makanta Ko mai aiki tayi

Kwana biyu kacal yayi a kano amma haka yake ganin miscals daga Wajen Banafsha da Nimrah wanda ko Daya baiya dagawa

  ..itako Banafsha tun data ga haka Sai ta kwallafa rai Akan Nimrah ce taja Hankalin sa yake kin daga wayar ta..

Gashi dama tunda taxo gida ta samu maysam na yawo tsakanin hjy mahnoor da su hjya Mamah sai Zama free ta kulla Tunanin mijin ta aranta..
..
A kwanan Sa na biyun Cikin dare sai taji ta kasa bacci tana ta juye juye,Ta rubuta ta goge chan kawai Sai ta tura Masa text Din"pls i want to talk to You"...

Yana gani yayi murmushi,dan shima baya iya runtsawa bata fado aranshi ba,duk da haka Sai da yaja aji after like 30minutes sai ya kira

,Ita kuwa tsaban rudani tunda ta tsaya rigiman tuno abunda zatace wayar ya yanke bai sake kira ba..
....
Da hawayen fushin hakan tayi bacci,da safe tana tashi tayi sallah Ko wanka batayi ba Ta Dura ma kanta yellow flagyll gadon hjy mamah ta dale tafashe da Wani sassaynr kukan makirci saida hankalin su ya tashi suka rufu kanta suna tambayr ta.

Baki Jin dadi ne tace Musu eh
Kuma lallai Yaya mohan ne xai duba ta Harda cewa ai magani Na wajen shi.

Tsoffin kam Haka Suka biye Mata,tunanin su ko dan tana cikin Inuwar jego har yanzu Bayason wani ya sa hannu akanta.
Tunda ta haihu sun san shikadai yake kula da lapyar ta

Don haka Kira akan kira,Banafsha Kuwa Sai ta haukace Musu Ta Zautar musu da tunani juya idanu Take acinyar hajy sai mashak mashak takeyi kamar mai Sabon laulayin ciki,Cikin ranta Kalau take jin kanta,"
sai tace wallhy sai kadawo Min Yau din nan, in har kana so na yau zan sani...

Haka su hjy Suka azizata magana saida hankalin shi ya tashi Ya kasa tabuka komai dake gaban sa....Gashi yana cikin mutane ne kasa kasa Ma yake maganan Na kusa da shi ma bai yaji

Yace Hjy nifa babu magani waje na',...hjya tace toh inma babu ai sai Ka dawo ka duba ta
Yarinya tun safe jikin ta Ke ciwo kamar zata mutu Baga ganta ba abun tausayi,ko nabaka ita ne kaji da kunnen ka, Yace Ok bani ita.

Banafsha tunda taji haka Sai ta yi Boyayyen gyaran murya

Hjy na miko mata   ta rufe kanta cikin bargo Dashi 2Sconds ya dauka yana jin wani munafukin numfashin ta a kunnen sa Jikin shi sai ya fara picturing masa Yanayin yadda Take a yanzun
,...Bayabo ba fallasa Yace what's wrong?Kince baki da lpya meke damun ki!?...Wani lumshe Ido mai ma'ana tayi Tana jin Shocking din Da muryan nasa Ya jona mata,

,"Itama Wani murya mai Shiga rai Ta Dasa mashi a kunne Wanda dadin sautin sa Ya sa shi mikewa tsaye Baisani ba
Cikin sanyi Da janjanin kalma Tace Yaya nah katashi lpya?Tace..uhm dama zazzabi nake ji,Kuma ina rufe ido na sai Wani mafarki Yaxo min im so scared
..Tsoro nake ji Sosai Ko akwai maganin shi??

Jin yayi shiruu bai amsa ba Sai taji fargaban ko baiya ma jin ta ne Yayi shiru Din..

Bata san sigar datayi maganan bane ya girgiza zuciyan sa yabi ya razana gangan jikin Sa da shaukin kewar ta Ba"

"Bai iya Ko tsayawa acikin mutane ba Sai ya fita gefe jingine da bango ya lunshe idanun sa Yana sake boyayyan nishi..

Cikin yauqi tace yayah? Kanaji na
Har zai bude baki yace eh Sai yaji ya kasa

Wani Fitinannan kukan shagwaba Mai sanyi ta sake mishi a kunne Mai cakki da kuma yakushi Ajinin jiki,wanda
shikan sa Baya jin motsa motsan Data ke furtawa aciki..

Yo hjy mamah dake kusa da ita Ma bata jin ko A daga abunda suke cewa

Dik sai ta ruda shi 'cikin ransa sai yaji bazai iya kara dakikai bai ganta ba Cikin ranshi yace"ohhh this girl want to kill me softly,zata jefa bawan Allah cikin wani hali

Karshen ta katse wayar yayi, A hujajan ya bar duk abunda yakeyin ta Jirgi Ma yabi ya diro garin abuja

Ita kuwa tinda taji baice komai ba ya kashe Wayar Sai ta ba hjy mamah abun ta Ta hade rai,Pillow ta matso kirjin ta ta bude Wani Sabon Shafin kuka,tun Shigar Mohan Jirgi bata dena ba sai da Taji muryan sa agidan

Gashi tsaban kukan datayi zazzabin gaske ne ya kama jikin ta Sosai ta hada dumi eye balls suka haura
Hawayen ta shiga sharewa tana murmushi,
Yayi sallamah tare da Su hjy Maman ya shigo
Hjyn birni tace gata nan ko abinci fa bata ci ba..."Dukn su biyun sunyi Tsuru Tsuru suna tsaye

Shima tsaban zumudin daya cicciyo sa Sai Ya Zauna abakin gadon,bargon ya Dan yaye Kadan Yana kallon wani Dan iskan Kwanciyar da tayi

Don kuwa wani farin skin tight ta saka A yadda bai da kauri Har Ya hango Cewa ko pants bata sa Ba, Shikan sa kasa daga ido yayi ya kalli kirjin ta, Dan dunkule wa tayi kadan sai hannun ta suka matso cikakkun nonowar tan waje
..a lokacin jitake zuciyan ta dif dif Kamar zai buga tsaban fargaba bata iya motsi ba

,Sassanyar hannun shi da taji akan fore head Din ta Yasa ta bude lumsashun Idanun ta akansa
Sunfi minti 5 a haka suna aika Ma juna wasu irin Wasu irin sakonni A tare yake ji haushin ta da kaunar ta a ransa..He just wonder why She changed"
What's wrong?Shikenan Hankalin ki ya kwanta kinsa nazo?sai yadan kamo ta Ta mike Kadan a Jikin sa,qamshin sa Ne ya dada bugar da ita Bata san sanda ta rungume shi ba,...
Shima He cudnt resist the Shock musamman da yaji kayan duniya sun goge shi Sun cike shi..
Dan kadan ya sa hannun shi A waist din ta ya kawo bakin sa setin Kunnen ta"Yace
"Hey, agaban mutane zaki cigaba da matse ni,?to Sake ni, ni ina jin kunyan su?

A kunyace ta sake shin kuwa Ta zame daga Jikin sa Slowly ta koma cikin bargo Ta dukunne,Ai kuwa sadaf sadaf Su hjy suka xame A kunyace kafin Mohan ya dago Har sun Bace.

Murmushi Yayi ya shafa keyan kansa,hannun shi ya Miko zai jawo ta, ta ansa Masa queryn sa.. wani heavy knock aka doka a kofar dakin sai ya dakatar da shi ya dago ido...
FOLLOW
#SURAYYAHMS

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top