brainwashed

*🌺🍒AJALIN SO🌺🍒*

WATTPAD SURAYYAHMS

47
_Brainwashed_

Mohan sai da ya gama dariyar sa sannan ya dago ya kalle ta"sharrin shedan ko? Hmm ai sai kije ki fada mata..Sai ya Kuma Ya hade rai

Durkushewa gaban sa tayi A hankali ta ke share hawayen tsoron dake tahowa dakan su a fuskan ta"

Cikin ranta tana tunani ya xatayi ta bada Nimrah hakuri'

Ganin ya mike ya bude kofar zai fita ta taso itama ta biyo bayan sa

Dakin nimrah ya nifa ya turo kofar ya Tsaya kallon ta,

zaune take akan gado ta cika fam tana karkada kafa,yace wai fushi kikayi?Wani wawan hararar ta juyo ta balla masa

...Tabe baki yayi dariyar ta nacin Sa arai Amma sai ya make

,Nan ya juyo ya kalle banafsha dake boye abayan sa yace ohh baxaki bata hakurin ba?

Banafsha kamar wacce xata yi kuka ta fito tace"anty dan Allah kiyi hakuri nifa bada ke nake dariyar ba"

Wani shiru wajen ya dauka dama ita nimrah bata san da shigowar ta ba.
Ganin sun hada ido
juya kansa yayi gefe don kuwa
Dariyar su yake ji har ransa, irin ok ba ma ita kike dariyar ba ma aljanun abinci ne ko?

A firgit nimrah ta mike tsaye cikin fusata tace,ohh biyo ni ki kayi don Kin isa?

Da Sauri Banafsha ta girgixa kai sai xurr hawaye suka sako kai shikuwa mohan ganin yadda Banafshan tayi lumui kamar kamilan kyanwa ta marairace Fuska gwanin tausayi
Dariyar daya ke kintsewar ya sake yayi musu Sosai

...cikin dariyar Yace haba anty nimrah tafa baki hakuri,.
Hararar sa tayi ta sa masa Kuka tace ni nagaji da wannan wulakancin naka mohan, ni nagaji,
Dariyar sa yake,..yace itafa ba abincin da kika ci ya dame ta ba,wannan aljanun naki ne yasa ta dariya

Ko bahaka ba? ya juyo ya kalle Banafsha...a hankali tace ehhh

Aiko jin haka wani sabon rusa kukan nimrah ta fara ta shako fuska kamar xata kashe Banafsha,
Cikin zafin rai tace Kikace ehhh?.

Banafsha da sauri ta toshe baki"Anty Bansan nafada ba wallhy sharrin shaidan ne....
haba mana
mohan daya kafa dariya awajen shi bai san sanda yayi zaune gefen gadon ba.

Shiru Banafsha tayi tana sadda kai kasa dan itama abun ya bata dariya sosai musamman yadda taga nimrah na kuka kamar wacce aka dake ta

Sam nimrah batajin dadi,..She's actually ashame,
sosai taji kunyar abun da ya faru
don bayan bata mata plan din ta na jan aji da yayi,gashi taji kunya sosai agaban mohan
Datake cika masa baki.

Sai da yayi  mai isar sa,sannan ya hadiye dariyar ya juyo yana kallon nimra me kukan kamar taji sakon mutuwa"
Dagota yayi ya aje ta kan gado

sai ya juyo yana kallon Banafsha...
Yace sake bata hakurin"
A hankali Banafsha tace kiyi hakuri anty.

Wani mugun kallon da nimrah ta dago ta mata da jajayen idanu yasa ta hadiye  yawu....kallon Banafshan yayi yace mata get out,
A sadade ta juya kamar munafuka tayi waje,

Bakin gadon shima ya xauna ya jawo nimrah jikin shi ya shiga bubbuga mata baya cikin rarrashi "yace hey girl,tace fa badake take ba besides meye na xuwa dukan aljanu bayan ta riga taganki kinacin abincin ai ce mata xakiyi ta xubo miki tunda kema gidan naki ne
.tare da murmishi ya karasa maganan ,rinannun idanun ta ta dago tana hararar sa a fusace tace toh kai dariyar da kake yimin ta mene ne?...maimakon ka mata fadan abunda tayi min shine xaka biye mata kuna min dariya tsaban wulakanci ko?

Yace hey It's ok,yanzu ai na sata baki hakuri next time i will deal with her..

Jikin ta take son faucewa ya dada janyota yace hey It's enough..ya isa haka.. im sorry Toh   kece duk kike fushi da ni ai da ba haka ba.."dagowa tayi xatayi magana ya tsare ta da rikitatun idanun sa wani lamo tayi,cikin kissa tace"tunda kayi ma yarinyar nan ciki sai ka rika min irin wayannan abubuwan agaban ta bayan kasan bna son raini..murmushi kawai yayi ya janyo jikin shi suka fado gadon tare"wani xiriya yake da hannun sa akan wuyar ta,tana jin wani shocking,ya furta to lets change,..wai daga na samo karuwar arxiki sai Ke ki yaye ni?..,wani duka takai masa akirji.. Yayi dariya ya fixgota cikin wani irin romatinc kisses suka lume agadon. Washe gari da safe anan yayi wanka daure Da towel a kugun sa ya fito nimrah nakan bacci
...dakin Banafsha ya nufa straight,yadan turo kofar kadan ganin ta yayi kn prayer mat alaman ta idar da asubahi ne amma bata tashi.
Dan karamin murmushi yayi yayi gyaran murya cikin neman tsokan yace gata nan gata nan...a firgit ta Mike tayi kan gado,sai dai bata karasa ba ta fado kasa...wani dariyar yayi kafin ya iso kanta ta riko kafa tana wassssh...gaban ta ya tsuguna y riko kafar" sorry yace. .yana dan matsewa cikin masifa"mutum sai shegen tsoro amma ga Shegen neman tsokana,idan xakiyi abun ki ni dai a dakata min sai baby na yazo duniya wajen baban shi,inyaso ke ki cigaba Da neman tsokanan Thank god u know my wife xata koya miki hankali...zumburomai baki tayi cikin masifa tace ai nabata hakuri. Bai ko kalle ta ba bare ya amsa,cewa yake duk randa shirmen ku ya taba min baby na zakuga real joke agidan nan daga ke din har ita...sai tayi shiru tana binshi da ido har Ya dago ta suka zauna kan gado"

Lie down. ya fada yana mikar ta kan  pillow,rigar ta ya daga ya shiga examing din cikin yana mata ayuverdic massage  da palms dinsa har bacci  mi dadi ya sungume ta,tare da dora mata kiss a goshi ya fice.

_8months leave_ .
 
Haka rayuwar su ke tafiya,Tsakanin ta da Nimrah sai manakisa da munafurci,"har yau bata mance maganan da Nimrah ta fada mata cewa,"ba ita mohan yake so ba Abun cikin ta ne Kuma tana haifa ta xama Masa banxa,"

...most time Banafsha zata dau abun da xafi aranta wani bin kuma in taga yadda yake bauta mata sai taga kamar karya ne ba babyn shi kawai yake so ba har da ita. .ita kanta tasan ya dora buri mai girma akan abunda ke cikin ta,zumudin sa  ya dadu ne tun ranar daya soma ganin motsawar halittar babynshi a computer,

In tana jikin shi hannun sa baya rabuwa da cikin ta,a kullum cikin tarairayar ta yake yana praising din ta akan cikin ,kowani lokaci su kaje asibiti sai ya bata karfin gwiwa.

Duk Da haka Abubuwa na damun ranta she's geting confused Kullum, tana so tace masa kar ya zanca mata bayan ta haifa mishi Abun cikin ko dan  son jin mexai ce..amma kuma sai taji ta kasa furtawa
",kawai Sai ta sa yayi mata alkwarin bazai kyale ta ba inta je haihuwa.

...wani bin har ya tsokane ta,cewar sa ma farida xai barta ta karbe haihuwan ba shi ba

Ana cikin haka rana guda aiki ya taso masa,yayi kwana biyu baya dawowa gida.

Yan adawa ne suka taso sa agaba da kalubale iri iri,
musamman yan stock market na medical reviews Masu siye da siyarwan magani

Basu yi tsammanin dan mohan ya rage kudin magani da expenses na asibitin sa xai kawo masa daukaka da cigaba a fannin Kasuwancin  ba
.
Sai suka Hada Kai suka watso wani maganin da aka laka masa side effect mai wuyan sha'ani
,Sun san wajen shi xa'afi siya, Idan kuma baisan yadda xaiyi managing ciwon ba,daga nan asibitin Sai ya rage value

Hakan kuwa ya soma faruwa coS Mutane Sai suka yi yawa sosai kuma kowa na neman taimako a asibitin sa.

Gashi shi in har yayi aiki to fa daga bookings dinsa ne,a asibitin sa baya aikin komai sai administrative protocols dinsa.

"but this time yakasance wannan cuta Kusan shi kadai ne ya iya da shi A asibitin.

He spend a day yana training doctors dinsa amma sun kasa gane komai,sai Wani dr javeed (long time obsessed lover  nimrah)wanda ahalin yanzu ota ta sa mohan ya bashi aiki a asibitin sa sukeyi tare.

Dr Javeed yana matukar kaunar nimrah lamar yadda take kaunar mohan in return itama bata kaunar shi kamar yadda tasan mohan baya kaunar ta,

Duk abunda tafada ma javeed zaiyi,shiyasa data ce yaxo asibitin yasa ma mohan ido akan wasu abubuwan bai ja ba,shi ya sanar da ita komai game da farida da yadda ya lura da relationship din mohan azuciyar ta,..itako farida bata yin javeed sosai a kullum cikin fada suke,mohan har ya dauka ko ta samu mijin aure,baisan ta hango yadda javeed  yake son shige masa bane

A wannan yanayi ma Dr javeed shiyayi ruwa yayi tsaki wajen taimakon mohan akan cases din
Ba karya mohan yaji dadi aransa sosai.

Ita ko Banafsha bata jin dadi gashi ita kadai ne
Ranar da zai fitan ma urgently aka kira shi bata san meke faruwa a asibitin sa Ba gashi Nimrah taje port

Bata kuma tashi sanin wayoyin sa na gida ba sanda taje dakin sa da daddare,
Daya akashe dayan kuma a kunne shi ta daga taga 56 miscols" open ta bude taga suna iri biyu,daga "sweet bird,"..sai "my Comfort' bayan nan babu wani contact ko Da a cikin phone book Ne Tunanin ta bai zo mata numbers din ta bane,sai data duba ta gani.

Hakan ya sa ta murmushi har ta ji sanyi ya shige ta,late in the night saiga kirar sa ta land-line,inda yake mata bayanin abunda ke faruwa...bai dai ce mata bazai dawo gidaba amma yau 2 days kenan bai shigo gidan ba

A tv take bibiyan labarin,da abubuwan dake tafiya,abun ta dame ta sosai  sai ta fara jin bugun zuciya,she knew mohan is in deep shit Don kowa yagani yasan ansa masa ido,

Uxurin data bayar kenan na rashin dawowar sa Kullum dn sau daya sukayi waya basu sake yi ba,a kwana na ukun,Tunanin sa ya hanata sakat
Da sassafe bayan ta idar da asubahi wanka tayi ta shiga kitchen ta hado breakfast ..a cooler ta xuba shi dan dai dai
,fried rice wanda yaji kayan lambu da grilled pepper chicken da plantains da boiled egg buding,sama kuma ta xuba pepper soup na cowleg komai dan dai dai ta kimtsa..har da water flask dinta wanda nikaina bansan me aciki ba

As early as posible ta nufi asibitin,He actually mises her more than yadda hankali zai dauka,amma ganin yadda rayuwar bayin Allah  ke cikin hatsari yasa ya daure shida  dr javeed suka tackling matsalan fiye da zaton kowa.

Kowa saida yasan babba yasa hannu a aikinga inganci ga tausayawa don kuwa sisi bai karba ba na kowa daga cikin wansa iftilain ya haura kansu,

6.50Am motar gidan ya sauke ta ta inda yake shiga dasu,driver ke bin ta kayan abinci don kuwa cikin ya fito sosai,.

Tana shiga site din sa sai taji an tsare ta da hey,

Karban kayan tayi security suka sallame driver shikuma javeed ya karaso.

Baisan ta afuska ba sai asuna,dan haka yake Tambayar ta ina zata je

She can't just say wajen mijina nazo cos all eyes on her ga abinci ga kuma katon ciki,itama kallon su tayi,batce koma ba tukun da alamun zallan manyan likitocin asibitin ne a dai dai wajen sun kai su shida tana kallon su ta glass kowa na gaban wani abun.

Yace malama ina tanbaya ko kin bata hanya,
Dan kadan ta kau da kai ta dada kare ma wajen kalllo sannan tace "i want to see mohan,"..pls where is he? Galala yayi da bakin sa irin what?. .mohan gatsau,who is this woman?
Yadda take basar
Da shi ke dad amusing dinsa Itama yadda yake kure ta da ido kamar shine mamallakin aSibitin ya bata haushi

Dayan doc Dake wajen yaso ya gane wani abu,but da shike mohan privately yake shigowa da ita yayi abunsa su fice sai duk basu dago fuskn ta Ba
Buts its sound awkward to javeed,yasan dai babu mai green card din zuwa nan site din sai wani babba,
Farida ce ta bude kofa ayayin da duka suka maida hankalin su kanta
Suna hade ido da Banafsha sai data ji wani mugun bugun xuciya don sosai cikin Mohan ya zauna ajikin ta gwanin sha'awa...

Murmushi ta kwaKwlo haka itama Banafsha
,ure welcome mrs.   Banafsha tace thank you..pls can you take me to him?yaya mohan naxo nema....javeed was like woah,sai yace ma farida dama ita sister sa ne. Dan kadan ta harare sa tace no "wife"
Abun hannun banfshan ta karbe suka barshi tsaye wajen yana shafa kai. So this is the Banafsha? Hmmm ya sauke ajiyan zuciya yana shafa keya.

A kofar office dinsa Knocking farida ta farayi,
Ba ace su shigo
Ba dan haka suka dan tsaya

Dr Umar  ne da dr aliyu aciki,sun sa shi agaba suna cin tarar sa na kin kirar su su taya shi aiki,

Surutu sukeyi yna defending kansa cewar baya son ya kwaba musu aiki,yasan being one of the best medical doctors a kasa is not easy...mohan kamar knock ake Aliyu ya fada.. Yace ok Sai yayi shiru..aliyu ne yce come in...

As he expected farida ce ta soma shigowa,ganin dr umar ya mike tsaye yana murmushi sai yadan leko suka hade ido da ita,..

mamaki ma taba shi..but yaji dadin ganin ta har ransa,a gefe farida ta ajiye  kayan abincin da suka shugo shi

Faridan xata fita tace nagode sis

itama sai ta mayar mata da murmushi..

Xagowa yayi xuwa inda take ya na murmushi ya kamo hannun ta zuwa gaban sa"ba yabo ba fallasa yace musu look who's here"....
Aliyu yace amarya bata laifi gaskiya kin sammace mu,bata ce komai ba ta gaishe su aladabce..cikin fara,a da jin dadi su aliyu suka amsa gaisuwar ta
Kin biyo kayan ki?ai munce yaJe gida yaki ne,,ai gwara da kika zo..ta sunkuyar dakai tayi murmushi,
...dr
umar yace Baxaki xe komai ba?
ahh to
To bari mu tafi mukam ko?aliyu..

Dariya sukayi mohan yace kar ku ma fara ba aikin zakuyi ba?,thank God Kunga anzo dauka na  school over,"
dariya sukayi har da ita dR Umar yace amarya kin amince muxauna tayi saurin gyada musu kai tace ehh,..sukuwa suka hakimce,dama sune masu yawan nuna soyayyar su ma matar su this is the First time  a bangaren mohan

wani hararar ta yayi da gefen idon shi,giran shi ya daga mata cikin murya da ba lallai su ji shi ba yace ni baza'a gaishe ni ba ne?
Lumshe ido tayi kadan don sosai take jin nauyin su dr umar din ita kanta bata san meyasa tace su xauna ba din ba...ina kwana",..yace inche dai lpya na ganki am i safe? Ya juyo yana duban basket din abincin? bata amsa ba,sai ya dago ya dora hannun shi akan cikin nata yayi feeling,take tayi saurin sunkuyar da kai bai damu sai da ya kwafi idanun ta yace aliyu kunyar ku fa takeji...

Suma a kunyace sukayi dariya,..dr aliyu yace ai tunda akace mu xauna muna zaune komai ayi gaban mu....wani kunya taji
"Ni dai kidena jin kunya aike kanwa ce waje na.
..yanzu ya takura miki xan rama miki...yanayin yadda suke yi na saka ta nishadi a hankali tace ohh nagode yayah....
Suna hade ido dashi yace yaya ko?ta dan turo masa baki..tace yaya aiki? brot u breakfast ko har kaci abinci?
Yace ah'a,..im soo famished ganin ki ne yake sa naji na koshi,banda
Murmushin kan fuskan ta
Bata ce uffan ba sai Ta dago abincin ta fara zuba musu kowa na tofa albarkacin bakin sa.

Inda ya dage sai ta bashi abincin abaki.."zagewa yayi yana karba ciikin kewar ta soyayya mai sanyi ke fallasa kansa atsakanun su..He was soo proud of her,a idon kowa yau for the first time Friends dinsa sunsan akwai mace mai nuna damuwar ta da soyayyar ta akansa...

Dan haka ya sake ranshi kamar ba shi ba,har suka rakota cikin mota aka jata tayi gida

Bangaren sa da Nimrah kua Tun daga ranar da  ta samu hankalin Sa sai ta dawo masa normal amma sai dai bai san tsakanin ta da Banafsha ba.

Ita ko Banafsha tun tana tsoron nimrah zata mata wani abu har ta dena ta shiga cikin wani halin nazari,cos all she tots was nimrah tana fushi da ita da mohan ne baki daya

Amma Sai babu abunda take gani kamar sabanin tunanin ta,yadda nimrah ke nunawa boro boro a tsakar gida shine mohan ya fifita Banafshan ya barta.
 
Cikin salon makirci babu ta inda Nimrah bata bullo  dan ta nuna ma Banafsha cewa mohan fuska biyu gare shi ba, most times sai ta faki idon ta sai ta fara wayar karya tana maganganu kamar" ai namiji?  Hmmmm barshi kawai agidan nan na dauki darasin rayuwa,itama bari kiga ta haihu ya samo abunda yake so share ta zaiyi.

Wani lokacin kuma sai taji tana cewa," mohan ya gama cin duniyar sa Dama haihuwar kawai Yake so,the moment ya samu aka sauke masa,wasu zasu gane koran su agidan nan.

Mutumin da baice yana son ka?ke fa inba ma rashin tunani ba har zaka sake da shi  da zuciyar ka dan kawai yana nuna maka kulawa?
Sai tace Jamila kin ganni nan,yanzu bana fada da kowa
Ni tausaya ma Wasu ma nake yi is possible dan Bana kaffara dan cikin Kawai yake bata time dinsa sa Da ta haifo mishi yaro shikenan .

"wani bin Very ridiculous hakan nan Banafsha ke daukar maganan amma sai abun ya zo ya fara fin tunanin ta,

Kwana biyu,shikuwa mohan duk iya kokarin sa zaiyi akanta,ko yana wani wajen tace tana son abu haka zai turo ko ya kaita da kanshi,..sai dai hr yau bata san meke faruwa Na gaskiya tsakanin sa da nimrah ba,tunanin tako ya dena ma nimrah adalci sabida ita tana dauke da cikin sa yake kulata ita kadai.

Wani bin bata sanin Nimrah tayi tafiya,inta ganshi kullum ajikin ta yana kulawa da ita sai ta fara jin wani iri aranta..so haka halin maza yake? Idan kayi sai suyi dakai..idan baka da shi su juya maka baya?ita wayannan abubuwan suka fara juya mata tunani,duk kalaman so da tarairaya dazai furta mata most times in tana jikin shi gani take kawai yaudara ne.

Da shike hjy mahnoor ta dan ja baya da shi,Shikan sa baisan nimrah inta fita kasar waje tana zuwa
Mata ba..a  haka xata yi ta koke koke tana zuga hjy mahnoor,

Ita kuwa dama  ta dan huce Har tana tunanin ganin jikar ta wajen Banafsha But da nimrah ta Xo ta yanko wani manakisar sai taji ta haura.

Tace mum kisa baki su hjy sudena sa mohan yana nuna rashin adalci tsakanin mu,. Ni ban san menayi musu ba,.
Dikan su Sun tsane ni...
Sai ta fashe da kuka.."mumy,nayi hakuri ina kula da Banafsha,nasan dai akoi xafi da kishi ,but she's just a girl ga ciki,duk rashin jin ta haka nake fama da dawainiyar ta,mohan ba zama yake alwys ba,amma sai kiga Wata rana dn aci min fuska Sai su aiko Wai ya kai musu ita cahn gidan su tayi hutu..

"Nifa ranar hjy mamah ce min tayi mena sani game da kula da mai ciki bayan ni nikasa yi...abun ya dame ni mum

Shikuma bansan meke damun sa Ba kwata kwata mohan ya sauya halayen sa,baijin maganan kowa sai na hjy...

Sai ta fadi hakan
Sai ta durkufe kai kasa kaFar hjya mahnoor tana sheshesheka,.
tana cewa
Kiyi hakuri in nafadi wani abu marar dadi,i know mohan dan ki ne..but i also consider you my mother bani da wanda zan gaya ma damuwar gida na in bake ba.

I  do not want to tell my family lady Z xata ga laifin miji na,kuma bana son haka ..ba laifin shi bane nasan ba halyyar sa bane

Nimrah inta na hakan sosai take sa hjy mahnoor cikin wani hali,

Sai taji tana mugun tausaya mata har cikin ranta,

Many times takan gaya mata Ni zan dauki mataki sosai akan mohan,tunda su hjy suna ganin sunfi karfina,this time tsakanina da dana ne duk sai sunji ajikin su

Taso ta kira mohan taji kan maganan amma Nimrah tayi babakere wajen juya mata tunani, hade da itama hjy mahnoor bata son alhaji ya sa baki sai tayi burus ta xuba musu mugun ido..Dadin karawa,lokacin cikin Banafsha na 6months sai laulayi ya juya salo,most of the time bata cin abinci agida ko yaje hjya tayi ta bashi ya kawo,ki a aiko su mufida da shi
Duk abunda ke faruwa nusaiba na fada mata,musammn ranar da daya fitar da su shan ice-cream,.toh ita nusaiba bata je ba da mufida da ahmd ne sai Banafshan.

Hakan yasa ta gaya ma hjy mahnoor yanzu yayah mohan baya dauka Ta sister shi su mufida kawai yake so don kawayen Banafsha ne Sai tace duk ya tsane ni sabida ita,
Itama da guntun munafurci haka zata rika juya hjya mhnoor tunani,lokaci guda suka cika mata kirji da maganganu masu kama da Gaskiya amma ba gaskiyan bane.

,anan kuma bagaren mohan Nimrah was normal to him shikan sa ya fara respecting din ta dayaga tun fada da hayaniyar da suka yi a azumin basu sake aikata wani ba.

Sai ta nuna masa ta huce,bazata taba Banafsha ba kuma bazata sake shiga harkan ta ba,for the first Time eva thinking matured sai yaga kamar Nimrah tayi abun kai tayi hankali sosai.

A bangaren sa Dai dai gwargwado yake adalci tsakanin su,wani bin ma yana shan mamaki yadda ta furta cewa ai abun shi nata ne,so she's gonna accept his baby,but din karya gane ta sai ta nuna masa still  ita bata yin Banafsha kishin nan na nan,jinin shi dake jikin ta kawai take so

He was ok with that, a tunanin sa ko soyayyar sa yayi rinjaye ne aranta shiyasa ta sauya halayen ta

ko kadan bai san agaban sa kawai bane Agaban Banafsha nunawa ma take ya share ta,baya mata adalci,sannan ba abunda yake jira wajen Banafsha sai babyn shi.

Bayan sati biyu

Nimrah farkawa tayi taji labarin cewa cikin dare  nakuda mai zafi ya turke Banafsha.

Mohan Bai taba sanin akwai abunda zai daga masa hankali ba sai wannan
,.hawaye kawai take mishi tana murkusu su tsaban fitinan baurin data keji ko sauti bata fitarwa,a asibiti suka kwana yana kanta a tsaye gashi yayi alkwari makansa cewa shikadai zai kula da ita privately.

Fiskan sa a cike take da damuwa Shi kansa sai da zufa ya keto masa ba abunda yake yi sai shafa ta yana tofa mata addua,nishi take yi kamar wacce bazata kai ba..da kyar Tana sauke nishi sannan ta yunkuro nakuda mai zafi bakin ta tafe da salati

Shi yaa karbi haihuwar diyar sa inda ta santalo masa kyakkyawar ya mace mai mugun kyau Da muhibba.

A kammanin sa ba abunda ta rage face siffar idanun sa..

Fara ce sol da dogon hanci
,cheeks din ta  masha Allah dauke yake da irin lotswar dimples din mahaifin ta...kanta mai yelwataccen baqin qashi da kwantaciyar gira
shikan sa ya shagala wajen kallon jinjirar bai lura da sumewar da matar sa tayi ba..Godiya yake ma Allah Sosai domin kuwa a duniya  yasa Ya mace  aranshi gashi Yau Allah ya bashi

Sai sannan daya fita ya bada farida ta kimtsa babyn sannan ya dawo ya kula da matar sa cikin tsananin so godiya da Nuna kaunar sa

Sai dai Ita duk bata sani ba sabida dogon suma da tayi mai hade da gajiyan nishi da nakuda Datayi overnight
.
dama Ajiyan ya kira mum dinsa,amma ji datayi yace ya kira su hjya mamah First Sai Ta bata ranta.

Tunanin shi bata dawo ba, baisan ajiyan cikin dare ta iso ba.

anty rawiya ce  ke jigila A asibitin don ta riga ta fada mashi su hjy mamah suna gida suna shirin tarban sabon bakuwa,Banafsha na Kan bacci bata farka ba..chan da waje ya lafa
,iAnty rawiya sai ta wuce gida dan ta sanar da hjy mahnoor In person Tasha mamakin data ji Shiru Daga fannin su

"anan tana shiga Site din ta tarar da mahaifiyar ta Wato kakar mohan  hJy zaynab Itama taxo,
ko da tayi musu bayanin abunda ake ciki,kalaman hjy Zaynab sai ya dada sa hjy mahnoor taurin kai da izgilin cewa bazata lamunci wannnan juyin karan ba,ita a dole danta ya fifita wasu akanta ace har sai da matar sa ta haihu sannan zata sani? Ai dama fushi take da shi don haka taki sam ta taka kafarta zuwa asibitin,ita da hjy Zaynab haka  suka tsigale anty rawiya Ta fita zuciyan ta babu dadi.

Mohan kuwa yana office Yana zumudin yarsa tare da  abokan sa da su hjy mamah tun a waya.

BanafshaTunda ta fita a suman Datayi sai bata gane kata sosai,shima Jira yake Banafshan ta farka daga Dogon Barcin da take Ta yi sannan ya kai musu ita gida.

  Suna cikin haka saiga Anty rawiya
Ta dawO,

Agefe suka ja take gaya masa mahaifiyar sa ta dawo Tun jiya  kuma ga abunda take fada Akan sa..

Basosai ya daga hankalin sa ba don yana ganin muddin taga jinin aa aduniya xata saduda..dan haka babu bata lokaci ya Sa Anty rawiya ta rike masa babyn Suka nufi gida,suna fita Nimrah tana shigowa dakin haihuwar,
Me ta haifa? Ta tambaye farida Sai tace mata baby girl 

not minding Her presence ta tuntsire da Wani mugun dariya
"favourite wife ta haifi na mace'?..Hmm

Hakan yasa Farida tayi Waje Tana kada kai, Sai dai kassh Banafsha Tana farkawa a idon nimrah."cikin layi take kiran sunan sa,a wahale alaman allurar Da yayi mata Bai gama sake ta ba

Inda kishi da Bakin ciki ya Cakke Nimrahn,

Tasowa tayi tsaye hannun ta daure a kugu tace Gwara ma Ki farka don ke kadai ce Anan nidin da kika raina nice anan,

Mohan Ya dauki babyn shi ya tafi..

Cikin wani irin ajijiya da ciwon kai Banafsha ta Lunshe ido ta kuma budewa Ta kalli Nimrah"Tace
Karya kike Yi anty,yaya mohan baxai tafi ya barni ba..Wani mugun dariya nimrah ta fashe da shi,tace Ko?
#followAcct@
#SURAYYAHMS
Ur comments are what i read and gain that little strength to write despite my busy days SHARE YOUR VIEWS and votes pls

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top