chapter9
_9⃣-mr sadat Adeel♡_
This page for only u wattapad love u guys
Ni kadai a kitchen din inata sake sake don tunanin khaldun na cigaba dayi har na kammala hade haden abinci na.
Da shike dinner ne ban dafa abubuwa masu nauyi ba,i left the kitchen unkept sai naje site dina,ina shiga daki ban wani bata lokaci ba bayi na shiga na dauro alwala nayi sallahn magrib da isha kafin na nazo na gyara ma simple make up dina zaman sa.
Misalin karfe 7.55pm na sauko da serving trays na aje kan dinning dinsa ko gama jerawa banyi ba na tsinkayo
sallamar sa da tamkar ma kanshi yakeyi.
Na gaishe shi kasan wuyar sa ya amsa with his face bayabo ba fallasa
Direct ya taho zai zauna kan dining chair kamar yadda ya saba,so i quicky compose my self na tara dan karfin hali na ja masa seat kamar sarki ya zauna gently still bai kalle ni ba..!
Plates na shiga jerawa gaban sa na bude wata mayyar girki mai dadin qamshi, rich spaghetti shingella jolloff mai dauke da fresh brown meat meals..
I notice how he look at the food da gefen idon sa sai nayi boyayyen murmushi
Spagehtin na zuba dan dai dai sai na zuba meat balls guda hudu manya aciki.
Redberries na zuba a wine glass,nasan yana matukar kaunar fresh mango juice shima na aje masa shi agefe.
Daga nan tsayuwa nayi a gefe yana ci,sai dai yau din na lura kamar he is not comportable da hakan daddaya ma yake ci kamar wanda abincin bai masa dadi ba.
Qamshin jiki na ne ya ruda shi,nikuwa Ko kadan ban kawo araina cewa na birkita ogan da qamshin turare na ba,nasan zai iya yiyuwa yana son qamshhin lavender sabida jahan Aarah shi take yawan amfani da shi.
Bandai kawo tunanin komai araina ba,don nasan turarrukan sa aduka arabian designers ne daga qatar, saudi arabia, dubai ko kuwait,
Idan bai saka su ba toh clive christain ne ajikin shi hardly yake shafa made in srilanka duk dama yana dasu kuma sun hadu.
Kusan rabin awa yau nayi agaban sa ababu ababu sai da yayi rabin cinye duka abincin dake warmer ahaka ma Baima sha beries din ba naga da kanshi yau ya mika hannu ya zuba mango juice ya sha,da cup din ya nufi dakin shi bai sake duban inda nake ba.
Nikuwa a Kullum burge zuciya na yake i so much love his hard nature..
khaldun Namiji ne mai ji da control, karyan ka kagano abunda ke sa shi farinciki cikin sauki bare kuma weak point dinsa.
He is one of a kind,bazan boye muku ba har mafarkin fuskan sa nakeyi most times ko da ba a bacci ba.
Haka kawai Kwana biyu Sai na lura da na dage da aiki na na kula dashi,toh da shike ma yasan yanzu nima yar gida ce kona yi mistake baya ce min komai.
Sai ya dawo tsakani na dashi We are back in the era of few words and blatard queitness.
Yau Kwana biyar kenan ina zuwa site dinsa amma baifi sau daya yayi mun magana sentence daya ba.
Ko ajiki na musamman da na tursasa zuciya ta tunanin sa a kullum
Gashi inata shirin rubuta waec next month,tunanin khaldun sa'ood gaba daya ya hana ni lura da duk wani abun dake gaba na.
Har da Sadaat mijin anty subayah da kullum sai naga ya zuba min shanyayyun idanun sa yana bina da kallo.
I begin toh dislike him,ban cika ganin yana tarairayar big sis ba amma sai naga sis subaya kamar wacce bata da aikin yi sai nashi .
He is a demigod to her,as she practically worship him.
tsaban so da nuna biyayyar ta a gareshi har bacci abinci bata iyawa sawa abaki inbata gansa ba.
Shikuma babu ruwan sa,in gaka yana wasa da dariya mai tsayi da da ita to yace taje ta kira ni ne kuma nazo din..
Na lura da shi Yana so muyi ta hira anma nikam jinina bai hadu da shi ba sam
Akwai indian serie da nake yawan kallo na mance sunan sa but akwai khushi da arnav toh babu maraban wannan sadaat din da mijin anjali wato shyam.
I just dislike his looking attitudes
Shiyasa idan big sis subaya bata kusa nakan yi sauri naje daki na na rufe kaina na ina karatun dole,bana sake saukowa sai ta dawo Haka ma da safe ko da daddare a site din khaldun zan bata lokaci na.
Nidai Sam naki na sake fuska ta wa mijin big sis,har ya kaiga ya fara sata tana biyo ni kitchen din khaldun tana ganin mena keyi
I love her soo much yawanci sai naja ta muyi ta hira har tana tayani girki,ita kuma burin ta bai wuce inna gama muje tare wajen mijin ta muyi hiran ba.
Hakan da sukeyi na takurani amma sabida saukin hali irin nata sai na kanje haka zaiyi ta kawo min hirarra ki shidai yana so yaji labarin yadda nake so na gina rayuwata nan gaba
Like makarantar da nake so nayi,my future career and stuff.
Subaya is the lit ana hirar ma sai kaga tana ta dariya abun ta,kullum zuciyar ta daya ne,sam bata lura da cewa mijin ta ya kamu da yaudarraren so na bane a zuciyar sa
Nikuwa ayadda nakejin bana son halayen sa,ko a kafata aka daura min shi yarwa zanyi,badon bai cika namiji ba,sadaat ma mugun kyakkwar namiji ne ajin farko kawai halin sa ne sam baimun ba.
Cikin wannan zaman namu
Kwasam sai ga Convoys na motoci suna shigowa .
Dama mun fito mu biyu da big sis raka sadaat din ne wai zaije aiki
Riga da skirt na saka na trim orange satin shirt na yafa karamin mayafi da flair royal blue daga sama na har kasa D&G ne.
I look queit and spoilt,kyau na ya saje da matsayi na.
Muna tsaye daga farfajiyan gidan Agaban mu Aka jera convoys din motoci
A jerin farko Motocin jeep kirar ford ne dukan su hudu da sojoji
Na biyar din Aka bude kofar Jahan Aarah ce ta fito
Duka murmushi mukayi muna karasowa big sis
Subaya ta riko hannu na muka rungume ta tare muka mata welcome
Jahan AarahTaji dadi sosai Like she was longing to hear my voice cike da wani irin sanyin murya irin na manya kuma kasaitatum mata ta dan dago haba na.
tana murmushi tace bahiyatul Noor,i hope you miss me? naji dadin ganin ki haka..may ur happiness sway on the wings of eternity
Murmushi na sosai ya fafadada na amsa ta da ameen ina mata godiya,
Tanbayar ta nayi yaya hanya?
,..wani murmushin tayi ta dan shafa cheek dina kafin ta amsa ni da kar na damu.
Wani lokaci sai nayi ta kallon ta haka kawai...this woman is killing me,gaba daya sanyin dake tafe da Ajin ta na burge ni.
She talks like a real queen yo ko Alhj hamood daya kasance jinin sarauta bazai gwada mata kasaita ba.
The second version of the convoy was motoci masu kofa biyu kirar cadillac xi farare Kar su uku.
Wani saurayi aka bude ma kofa ya fito,baima jira an gama rufewa ba ya taho gaban jahan da murna sa ya rusuna ya fara zuba mata kirari da girmamawa itama cike da jin dadi take yabon sa tana tambayr sa lpyar iyayen sa.
But Who is he?
Na kare masa kallo daga sama har kasa ina tambayar kaina
Naga big sis subaya ma murmushi take
Har gayen suka gama gaisawa da jahan ya juyo gare mu.
Wani jahilin murmushi suka exchngin shida big sis He hugged her lightly,tace welcome Huh?Ashe a duniya zan sake ganinka...?
Sai yayi dariya yace of course bagani ba.
Dogo ne fari kar kamar bature but he is very handsome yana da pink lips blond hair da manyan idanu.
"agarin gulma na unknowlgly His eye caught mine ban kuwa dauke ba ina kallon shi sama da kasa har sanda ya dage min gira,sai yace ma subaya wace ce wannan?
Ya juyo again"Heloo pretty bird..ya mika min hannun shi kamar yaga babyn rubber nikuwa naki mayar masa sai nayi durus da fuska ina kallon shi
Kamar naga tababben zombie.
Wani unxpected hadiyan tawu yayi ya maida knsa yana sosa keya
Ko jahan saida tayi dariyar mu subaya ta dafa kafadu na tana murmushi tace masa hey shahrul easy.. She is my sister fa..
Jahan tace yeah...enough now.
Ya kamata mu shigo ciki ko m,duka muka ansa da yes
Gaba jahan din tayi sai nabi bayan ta da sauri Na bar big sis subaya da mutumin yana tambayar ta irin taya akayi na dawo sister su shi bai sani ba
Inaji take wasa da hankalin sa suna dariya bata gaya masa komai ba dai tace ai dan ya dade baizo bane shiyasa baisanni ba.
Nikam Asalin Site din jaahan naje nayi zamana dan ko kadan bana son hayaniyar kowa.
Sunan mutumin shahrul,he is a medical doctor dan gidan uwar gidan shugaban kasar Oman Best and childhood friend din khaldun sa'ood
Tsaban amintakar su ne yasa shahrul yake yawan yin hutun sa a wajen
Khaldun a camp har ya iya hausa sosai.
Amma tunda aiki da career ya raba su sai kowa yayi wuyan gani.
As usaul Site din khaldun din subaya tayi da shi.
Khaldun was happy to see him amma bazaka gane hakan ba sabida yanayin sa.
Hira kawai sukeyi tsakanin su ayi larabci ayi turanci ayi hausa
Big sis dataga abun nasu nayi ne,kawai sai ta fita ta barsu ta dawo muka cigaba da hidimar mu wajen jahan.
Jahan is atill worried da maganan girkin da aikin da nake yi ma khaldun,nikuma naki ji sam
Sai da big sis subaya ta bata labarin cewa khaldun yafi cin abinci na fiye da yadda taga yake ci a ko ina kafin ta saduda
Chan bayan isha'i sadaat ya dawo suna tare da big sis
yau ma shi ya bata min raina
I was not happy da big sis take cewa ai daya dawo gidan ni ya fara tambaya.
Yanzu haka nasan anata tunanin tana murnan cewa mijin ta sadaat yana haka ne sabida ya gwada ya na son duk abun da take so.
Wai shin wani irin zuciya take da shi ne da bata ganin wannan tsarin nasa matsayin cin fuska?
A gaskiya bazan ji dadi ace miji na baida wani aikin yi sai maganan wata ba ko da kuwa sister nane..
Atleast there is limit,..not always...na sadaat yayi yawa har abun haushi.
Da wannan tunanin nake girki my face isnt looking so cool
Duk dama yau shigar hausawa nayi so na fito daban,atampa koriya shar riga da skirt tamin kyau sosai.
Godiyan Allah ma yau abinci dayawa zan dafa ma khaldun tunda bashi kadai bane Sai nasa araina yau kam bazan biye ma big sis ba bare ma na bada sadaat daman kallon fuska.
So i quickly made dinner,offal pper soup,crispy jollof rice na hada da soyayyen kaza sai na shirya simple brown yamballs mai shake da flake fish.
Kunun gyada mai madara da mango juice as usual.
Toh nakai abincin dinning amma banga ya fito ba
Sai da big sis ta zo dubawa ko nagama sai take cemin a dakin sa zanyi serving dinsu tunda bashi daya bane.
Tana tafiyar ta na kwashe abincin na je bakin kofar dakin nasa
I knocked for 20seconds sannan aka bani izini na shigo,Sake hade ido mukayi da shahrul saiya kau da kansa da sauri kamar bai gane ni ba nikuwa tsaf na kalle su duka.
Shi Ya sauya kaya zuwa wata tsadadiyar velvet engilan cow bow style baki da ja.
Shikuma khaldun sanye yake da wata hot pure white shirt wanda ake kira naked cashmiir ya dan matse kadan yana zaune gefen gadon shi ya wani bude button din rigar gaban faffdan kirjin sa half closed.
He looks sexy ni kaina da na dan yi gulman sa araina i was seriously tripping for him ban ma sani ba.
Dana gama gulma na Cikin ladabi na aje abincin agaban su nayi gaisuwa
Shahrul ne kawai ya amsa ni,cos tun da ya tambaye khaldun labari na yaki ya kula sa sai bai sake ba.
Ina kann zuzzuba abincin a faranti shahrul ya tambaye ni sunana,he is so cool na kanyi boyayyen murmushin da har bana amsa magana sai na aje plate na dan nitsu a hakan sai na dada burge sa shima
Ban lura ba ashw Khaldun kallon mu yake har wayar sa yayi kara,na dade banji masifar sa ba sai yanzu gaba daya duk hankali na sai ya koma kansa har ban cika jiyo maganganun shahrul din bama.
Abun da zan iya tunawa shine naji yace zaiyi mana sati agidan
Yadda na zuba ma khaldun din aka na zuba ma Shahrul kuma Ina wajen suka fara cin abincin Khaldun baice mana uffan ba
Shahrul was awwed,shi mamaki ma yake dayaga na tsaya agafe suna cin abinci,bai san wai aiki na bane hakan
Aransa Sai ya shiga tausaya min har da kokarin sa wajen sani a cikin hirar su,a wasa yace ma khaldun im such a great cook shikam daga yau wannan abincin zan nayi masa.
Watoh shi fresh brown yamball mai flaked fish din ya burge sa sosai.
Khaldun kam tsaki yayi,dan ma ya bani haushi sai yaki cin yam balls din ya tsame offals da jollof din yaci
Shahrul kuwa yana ta yaba ni,nima yake kawai nake iyayi bana cewa uffan.
So i packed the plates bayan sun gama..kitchen na nufa ina kan wanke wanke sai ga big sis
Na dan kalle ta sai naga kamar bata wani jin dadi?
Nace big sis....
Tace baahi har yanzu baki gama bane?
Kinsan darling bazai barni ba inbaki zo ba
Wani boyayyn ajiyan zuciya na sauke Nadan yi kafin na tsame hannu na a kumfa na fuskance ta
Big sis kiyi hakuri..kinsan su biyu ne,the other one.. he eats slow dole na jira shi..cikin kissa sai na dan yamutsa fuska na dafa kai,
Tace whats wrong kin gaji ko!
Nace ah'a kawai kaina kemin ciwo
Tace uhh ok am so sorry..to bar wannan abun kije za akawo miki magani yanzu.
Da haka muka rabu ta tura ni daki naje nati kwanciyata nikaina bansan ya suka kare da mijin ta ba.
Haka dai na samu wannan saran nakanbi duk wani hanyar da zan ki sam na hadu da sadaat don na lura Acikin masu min shisshigi har gwara ma abokin khaldun wato shahrul
shikam he is just a nice person babu wani attachement sai nake bashi girman sa sosai.
Most time idan naje serving dinsu ya dinga yabo na kenan duk dama abokin shi ya sha nuna masa baiya son hakan dayake min.
A dayan bangaren kuwa kwana biyu sadaat hankalin shi yayi mugun tashi da baya samun gani na.
Ga big sis ma ta dan shiga busy da aikin ta kwana biyu baya ko samun wanda zai ji labari na awajen sa.
Ita ceo ne na business companies din cosmetics guda uku wanda suka kasance natane na gashin kanta.
Haka kawai sadat Sai ya yi fushi irin fushin munafurcin nan wanda daga shi sai zuciyar sa suka sani...
Nikuwa tun ranar da khaldun suka fito wajen jahan tare da abokin sa shahrul Naji irin bakaken maganan da sadat ke jefa masa akan yaki accepting dina a matsayin sister sai na fahimci kishi da tsana ne a zuciyar sadat game da khaldun.
Arayuwar sa Komai da biyu yake yi its obvios yana fama da haushin nafi bada lokaci na ma khaldun agidan ne fiye da kowa
Sadaat shiyayi sanadiyar har shahrul ya gane cewa ni adopted child ne.
Hakan yasa naji na dada tsanan halayen sa.
Da sassafen ranan asabar ana gobe shahrul zai tafi,har nayi serving dinsu break fast na fito
Kenan daga kitchen sai naji tahowar mutum akan stairs baima lura da ni ba
Ina daga kasa ne shi kuma yana saukowa so
Tun daga kan arniyar black sport canvas dake kafar sa na soma kure kallo na har na iso fuskan sa da saura kadan facing cap dinsa ya rufe.
Shi kadai ne awajen kuma Yayi matikar kyau All in black theme adidas sport wears ko wayar sa bai dauko ba.
Badge din rigar da jan logo haka ma jikin canvas din akwai jan logo
Gefe na rabe dan nasan ko ya ganni bazai ce min uffan ba.
But i was wrong,ji nayi ya bani oder 2 glasses of mango juice da pancake sai ya fita.
kitchen din na nufa na fara kwaba pancake ina soyawa,sai ga big sis itama sanye da pink sport wear..
Bansan sanda na zo jikin ta ina murmushi ba don kuwa ko kai ka kawo kushel duniya kaganta kasan ta hadu
Ina zakije Haka?... You look so beauttfl sis i was exited sai nayi mata maganan kamar yadda take min in tana yaba ni
Kwabe fuska tayi jocklingly amused bata kula ni ba ta bi kan table din da kallo tace wai shi Aaban(angel)
bazai barki kisha iska bane?
Jiki fa kullum a kitchen,bahiyyah meyasa bazaki ce ma mum aikin ya isa haka ba?
Kallon salon da tayi maganan nayi nabita da murmushi
I knew this is not her word zai iya yuwa shawaran da mijin ta yake bata kenan so that na bar zuwa wajen khaldun sood.
Nace karki damu big sis...
Ina de basket ball court zakije?
I wll join you in 10 minutes
Tace ok ta dan shafa kaina tayi murmushi tayi waje.
A wajen kuma Khaldun da shahrul sune a katon luxurios basket ball court dake kusa da wata katoton Aqua maria pool suna game dinsu cike da nuna jarumta Suna ta hirarraki
Shahrul sport wears na kamfanin nike yasa all white shikam ya cire cap dinsa ba kamar khaldun ba..
Shi saood Kallo daya zaka masa ka fahimci Training din sojoji na jinin sa he is so full of energy ga kwarjini kamar dan sarkin aljanu..
To da sassafen ma sadaat sun gamu da shahrul khadum bai sani ba kuma anan sadat ya san cewa zasuyi sport din
Shigar sa gida sai yace ma subayah itama ta shirya suje suyi wasa.
Murna take ta yi duk ta dauka ko duk romantic treat ne bata san don zunzurutun neman maganan khaldun yayi hakan ba.
Haka suka fito sunyi kyau acikin shirin su,kallo daya khaldun ya masu ya kau dakai ya cigaba da dribbling da ball kamar bai san da zuwan su ba
shahrul kam tsayawa yayi ya dinga ma subaya dariya yana tsokanan ta.
Tunanin meye Khaldun din yake oho sai ball din ya kufce a hanun sa charaf sadaat ya chafke ya kuma bishi da dariyar mugun ta
Tsaki mai sauti yaja suka dago ido Wani banzan kallo suka watsa ma juna
Tare da sauke miskilin murmushi sadaat din ya buga masa ball din a kirji yace masa
"Lets play ...
Tsaki khaldun yayi,he got pissed ...am out ..ya furta cikin wuya zai juya ya bar wajen
Wait...Subaya ce ta taro sa cikin wasa waiit wait Khaldun.. ..
Sai ta maraice fuska tace afraid?
Toh shikenan Am going to be in ur team Aaban pleasssse let play..ta dada marairaice mashi
Haushi take bashi musamman daya lura indai akan mijin ta ne toh ko taga ya daure fuska sai ta daga kanta tayi kaman bata san ma yanayi ba..
Haka dai ya amince.
Team khaldun and subaya da team shahrul and saadat.
Nikam ina ciki ina hada masa oder sa bansan me ake ciki ba.
Wasa ne mai zafi ya fara wakana
Musamman tsakanin khaldun da sadaat domin kuwa karfi suke gwada ma juna Har An ture subaya a kasa yafi sau a kirga sai kawai ta ja gefe tayi shiru tana lura da su.
She dont really like their hidden hatred.
Amma ya ta iya khaldun kusan kowa ma ba so yake ba.
Tayi nisa cikin tunanin kawai sai na katse ta,tray ne a hannu na na cinnamon flavoured pancake da 2 glass of mango juice .
Subaya tayi min murmushi na mata alaman bari na aje tray din nazo...
Dan wulgawar da nayi gaban su sai sadaat ya ganni a yunkurin farko da gangan ya sa elbow ya buge shahrul a hanci fa wani irin mummunan bugu har sai da ya fadi a kasa yayi kara.
"Shah"...khaldun ya furta da sauri yayi kansa yana duba shi ransa ya dada hadewa kamar wanda zai tashi ya rama masa
Big sis itama ta taho tana tambayar sa are you ok?
Sadaat din sai ya sa fuska kamar bai sani ba ne yayi hakan sai ya shiga ce ma shahrul
Im sorry dude..
Nidai Tsaye nayi da farantin,ina kallon ikon Allah
Nasan dai shahrul ya basar da zafin dayake ji ne don kar khaldun yace zaiyi reacting..
Shikuwa khal Sai yace masa su shiga gida kawai amma haka shahrul yaki fir yace kawai suyi wasan ai he is ok..
Nikuma Khaldun bai ce min komai ba sai na aje Juice da pancake din akan ottoman
Bench kusa da ruwan pool na dawo na tsaya nida big sis.
Kana ganin fuskn ta kasan She is worried for shahrul dan naga fuskan nata dauke yake da damuwa
.ita kanta ta gane cewa shahrul baice komai ba ne sabida baya son khaldun ya dau abun da zafi
But It neva worked don kuwa ana fara sabon game din khaldun sai da ya nemi dai dai setin bakin saadat ya zuba mashi gwiwan hannu dagangan sai da yayi tumble din bazata yasa ihu.
Kowa yasan khal baya bada hakuri ahaka ma riirike shi shahruul yayi cikin harshen larabaci ya na dan masa masifa cewa meye haka?
Subaya tuni ta dago mijin ta a birkice tana dubasa,tsaban haushin da zafin da bakin sa yake sai yana tutture hannun ta ajikin shi
Bata ji dadi ba sam ta dago ta kalle khaldun daya tsime,shahrul ne kawai yake ce ma sadat yayi hakuri is a mistake.
Sabida ni sadaat ya waske yace musu bakomai besides ai shima yayi mistake din dazu.
Haka aka bar magana Kamar da gaske sun fahimce juna Aka sake komawa sai dai dukan su da abunda ke ransu.
Subaya tace ma saddat su koma daki ita kam game over kawai muje gida bai amsa ta ba
Nan khaldun ya min ido akan na kawo drink ma shahrul,
banyi kasa a gwiwa ba na dauko farantin ina tafe
Ina daf dasu na daga kafa ta kenan naji kwal abu mai karfi ya ture ni tsundum na fada acikin ruwan pool
Sadaat ne ya sake ball ya gangaro bazata naci karo dashi kowa yaha hakan
Amma dukan su basu motsa ba
Big sis subaya zata zo ta cire ni sadat ya finciko ta,yace bazakije ba yanayi yana kallon khaldun alaman tunda sunfi kusa dani to su cire ni mana
Nikuwa inata wutsil wutsil cikin ruwa
Hankalin subaya ya tashi tana ta kira na tana ce musu su taimake.
Sadaat Haka yaki ya sake ta,khaldun ma ya dauke kansa ya hade rai.
Shahrul hankalin sa ya mugun tashi da irin wasan banzan da ke wakana tsakanin sadaat da khaldun sai kallon su yake yi cike da mamaki.
Haka aka barni
A cikin ruwa ina kokarin fitowa the pool its too big dan haka da kyar nake diving.
Daga karshe Shahrul din ne yayi tsaki ya tashi zai zo ya taimaka min
A fusace khaldun ya riko sa yace please let go in,wai kai ka jefa ta ne?
"Khaldun..subaya ta tsawatar.. amma ko ya kula ta sai Ya ma ja hannun shahrul dagske
Zasu bar wajen
Abun ya dada ba sadat haushi A fusace ya juya yace ma big sis And you too.. Ai bake kadai bace ya agidan nan,that girl is both your sister right?,idan wani banza is weak and wicked enough yana azabtar da ita so be it Get in doors.. Ya mata nuni da hanya Subaya zata yi magana..ya tsare ta rai a bace ya ce NOw..
Da sauri ta shiga gida ta barsu su ukun.
Zai motsa kenan
Khaldun ya tsare sa yace" i hope i dnt hear you calling me weak and wicked?
Shahrul dhe tsaye na kallon su yace sa'ood pls stop it.
Please let me help the girl dan Allah ku bari
Shikuwa Sadaat abunda yake so kenan yaga dai ya bata ma khaldun rai kamar yadda yagani yanzu,baisan tsawar daya yi ma yar uwansan bane ya shake sa
Lets go..shahrul y dada jansa amma yaki motsawa
sadat kaima ka shiga gida mana the game is over Comn dudes
Wani fizga khaldun yayi cikin bacin rai yace ma shahrul baza a cire ta ba,shi da baiya azabtar da itan sai ya cire ta.
Sadaat yace yess i will... zan cire ta mana,am just waiting for you to go..am human i dont enslave girls Im not like you..
Ran khaldun ya dada baci sosai Da kyar shahrul ya rike sa .
Sai ya fara tunanin meye ruwan sadat da aikin da nakeyi mashi, da chan shi yace ina masa aikin ne harda wani zai masa wannan zagin?
Bacin ransa sam babu kyan gani Wani fixge jikin shi yayi ya taho bakin pool din ya kalle ni"get out"... ya daka min tsawar da sai da na firgice na fito a ruwan batare da na sani
Go inside now..
A tsorace na wuce shi da gudu I went inside cryng my balls out.
....gaba daya tausayi na ya kama shahrul sosaii
Haka suka watse kowa yayi hanyar sa
Ziciyar sadaat kuwa kamar zai fashe dan baiso hakan ba
A daki na big sis Subaya ce tayi ta bani hakuri har nayi bacci.
Dana je serving dinsu dinner yau kam shahrul bai sake fuskan sa ba.
Duka sunyi shiru sun basar da juna
Alaman wani abun ya shiga tsakanin su kowa sai shan qamshi yake.
Little did i know that,saboda ni shahrul yayi masifa sosai ma khaldun dazu
Ba wai don ina masa aiki ba shi kin accepting dina dayayi a matsayin yar uwan sa ne ya dame sa.
Ai kuwa Ko uffan baice masa ba,Taurin kan khaldun ya wuce misali dan shika dai yasan meyasa yake yin haka
a duk korafin da shahrul yayi har washe garin ranan bai masa dai dai da ya amsa shi ba.
Da safe dana zo serving dinsu shahrul sai ya ce min zai tafi,yace na dinga hakuri and he enjoyed my cooking sosai, cewar sa wata rana zai sa akawo ni oman na na zauna dashi ko dan na dafa mashi daddan abincii shida mum dinsa.
Duk dama nasan hakan bazai yuwa ba amma naji dadi sosai,nace masa nagode'..ban ma kar a dora wani kalma ba Na ci karo da wani banzan kallon da khaldun yake mana,don kuwa hararar da khaldun din ya watsa min kadai ya hana ni amsa shi musamman maganan zuwa oman da shahrul yayi.
Today i notice a little bit of jelousy a yanayin sa sai kawai nayi shiru.
Duk dama fushi nake da shi da naga ya nuna alaman kishi na aransa a Take naji zuciyata ta yafe mashi komai.
#follow
#Surayyahms
Dama Babu post yau but yadda naga anzuba comments yasa na
Sambado keep comenting guys and
Pls sai monday zamu hade insha Allah🙏🏻
.
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top