chapter5
_5⃣-Formal♡_
VOTE PLS
Tsabar bakin ciki Da kyar nayi bacci ko iya bitan karatu na banyi ba gashi malami na yace min na dage sosai da don kwanan nan zanyi jarabawar waec.
da safe ko da na tashi fuskata sam babu wani cikaken walwala
But still i know i have to forget abt it to meye ma a ciki dan yace na jefar da riga? Ba ringan sa bane ai shi zaiji dashi..
Cikin shirin fitowa aikin safiya na bude kofa ta na nufi kitchen dinsa na fara aikace aikace.
7.28 na fara takowa xuwa kofar dakin shi nasan 2 minute zai isar dani wajen ajiye mashi shayi
Thank God he is sleeping,da alama bazai je ko ina yau ba.
Haka nayi ta hanging a wajen kamar marar aikin yi sabida bai fito a dakin sa kamar yadda ya saba sai yaje ya dawo kafin yake cin break fast dinsa ba.
Atakaice dai yau ban samu lokacin gyara mashi daki da hada masa ruwan wanka ba
By 8.30 sai gashi ya fito fuskan sa still ba sauki,nidai nayi tunanin ko dan bai kimtsa bane.
As usual baiko kalle ni ba har na gama serving dinshi,ko gajiyan tsayuwar jiran sa yanzu banaji tsaban yadda kwakwalta ta dau cagi wajen tunanin yadda zanyi sneaking na karasa sauran aiki dake jira na a dakin sa
Jim kadan da farawar cin abincin sa sai ga Wani kurtun soja ya shigo yana masa magana kasa kasa with full respect bana gane komai but alaman kamar ana neman sa awaje ne.
I was happy daya fita,sai na tattara kayan abincin nakai kitchen na wanke na jere su tsaf na yi mopping ban kuma bata lokaci ba na dawo kofar dakin sa
Anan Don na tabbatar bai dawo ba sai na kwankwasa kofar s har sau uku,toh dana ji shiru A hankali na turo na shigo duk da haka ina famar leke, zuciyata kuwa har tambayata take akan me nake wani sneaking kamar marar gaskiya?
Ganin bakowan da gaske yasani na sake na shiga karkade makwancin sa na sauya beddings na aje ma masu loundry a inda nasaba ajewa,na share ko ina tsaf tsaf na kammala vacuing beige rugs.
Tsaye nayi rike da kwankwaso na a gajiye ina dada duban lokaci,
Tare da sauke ajiyan zuciya na bude kofa na shiga bathrum dinsa
Anan ma ban ko kallo gaba na ba nayi tsaye gaban tap dinsa na kunna ruwa na tsiyaya ina bi da kallo
Hankali ma har ya fara kaini wani tunanin Kamar daga sama naji ance waye wannan?. A razane na farga na juyo da sauri sai charaf muka hade ido dashi
"Wayyyo Allah na shiga uku.
He is in Towels babu ko riga ajikinshi.
Wani tsorattacen hadiyan yawo nayi mai shake magwagwo to wallhy bansan yaushe ya dawo ba bare ma nasan ya shiga bathrum yana wanka.
But Could it be lokacin ina kitchen ne ya dawon?sai na daura hannu aka ina bada kaina laifi...toh meyasa ma ban fara gyara nan dakin nasa kafin naje kitchen din ba?
Gaba daya jiki na ya hau rawa gashi na kasa sake daga ido na kalle shi.
Shikuwa Wani tsawa ya daka min that i can't help but to stammared
Nace Ka...yyiiii haku...ri...na zo hada maka ruwan wanka ne
Da wani irin muryan bacin rai yace meye sunan ki.
His voice kamar wani tsawa haka naji acikin kunne na yau
Cikin rawan murya nace masa sunana BAHIYYAH
Bai ko kula ni ba
"How dare you stand when im standing ke wacece haka?
Da sauri na sulale nayi kasa Allah ya so ni toilet din san ma yafi wani dakin tsafta,so batare da na ansa shi ba na zuba gwiwowi na akasa nayi kneeling.
Who send you huh?Kashe ni zakiyi ?waya aiko ki..
Bansha mamakin fushin sa ba don nasaba dama he is always angry at me.
Naji tsoro sosai dan haka na fara tattaro nitsuwa dan na samu na amsa tambayar sa da kyau batare da yamin wani abu ba.
Har wani tsoro nake kar yace zai mare ni
Gashi akai na ya tsaya yana hushi obviously waiting for my reply
Gani nayi yana min kallon rainin hankali irin kamar ma bai taba gani na a rayuwan sa ba sai yau,hmm bakomai bane i know tsaban rashin m ne kawai irin nashi.
So i started talking calmy da kyar na nitsar da harshe na...
Nace jahan ce ta sani aiki,aikin kulawa da kai da site dinka...nayi shiru ban kara cewa uffan ba.
I have to repeat myself sau uku kafin ya san ma nayi magana..
"And she gave you rights ki shigo min bathrum ina wanka.?
Nayi saurin girgiza kai na jiki na duk yayi sanyi yana shaking
Tsaban tsoron sa danake ji i was seriously strugling with my tears amma duk da haka saida suka sauko kaca kaca akan fuskata.
Shikam ma Haushi na bashi Sosai sai daya buga mirror cubord tayi kara da tafin hannun sa.
Are you deaf?
A fusace ya firta hakan sai na girgiza kai ina hawaye. .wani mugun harara ya jefa min
I said,Words!!! Ki bude bakin ki kiyi min magana
Use your freaking godam voice and respond to me when im asking.
Bazan iya ba,Kuka mai sauti ne ya kufce min ina yi ina toshe baki na a tsakure sai na shiga cewa
Nifa Jahan ce ta sani aikin dan Allah kayi hakuri
Daya ga dai na birkice sai ya basar
Baice uffan ba ya tsaya kallo na
Sai jan shessheka nake ina neman hadiye kukan dana keyi amma nakasa
Get lost! Kawai yace ya juya abunsa.
Bansan sanda naruga aguje na bar dakin shi ba,da kyar na isa katifa ta tsaban yadda nake ganin dishi dishi kuka nakeyi cikin tunanin abunda zai biyo baya.
bacci barawo shi ya dauke ni..
Shi kuwa yana kammala shirn sa ya nufi part din mahaifiyar sa,simple green rigar army yasa akan wata dakilalliyar drenched jean cikin takun sa mai dauke hankali
Anan harabar shashin tun Daga masu jigilan aike aike har manyan security Kaf aka fara watsewa kamar sunga malaikan mutuwa, kan kace kobo waje ya dauki shiru
A falon ta na uku ya dakata
Jahan Aarahn ce a zaune akan wata Asian block rimmed chairs,Wanda Shikadai ya cinye rabin falo an kawata shi da huge and bold trow pillows
Kawataccen murmushin ta mai narkawar ta tare shi da shi ayayin da ya karaso gaban ta daf ya rusuna cike da ladabi yace ina kwana mamah?
Bata amsa tana dai kan murmushi chan ta dago kanshi da tafin hannun ta ta zuba masa idanun ta
Kallon ta yake shima baice uffan ba don a cikin sauki yake jin duk duniya babu murmishin daya fi kauna kamar wanda take mishi
Ayanzu.
Bata cika kiransa da asalin sunan sa ba dan haka Tace angel ..KHALDUN!my very own son....ta kuma dafa kafadan sa cike da kulawa,Allah ya raya min kai..ta shiga mashi addua kala kala saida ta gaji kafin tace tashi ka zauna.
Ba musu ya mike ya dawo ya zauna kusa a gefen ta
Har ya juyo Zaiyi magana ta juya cikin taron mumfashin sa tace shushhh
Shirun yayi sai ta furta
Deep breath!!!!
Sai ya sauke nunfashin Slowly Yayi rolling idanun shi,sannan Ya wani sake ajiyan zuciya ya nayi yana maimaitwa slowly har sanda yaji dai dai
Watoh His mum,ita kadai tasan yadda take bi dashi,shikan sa ji yake agaban ta kamar dan karamin yaro yake.
"Whats wrong my khaldun?naga kamar ranka abace
Yace mamah,who is she?wancan yarinyar dake shiga min daki...
Tun kafin ya dora wani kalma ta juya ta kalle shi tana murmushin daya dakatar dashi..
Sai bai sake cewa uffan ba shima
Ya sakalta mata fuskan sa ya sauke kansa kasa
Jahan Gyara zaman ta tayi kafin tace toh mika min,ta masa nuni da tarin fresh dates(dabino)cikin pantray dake gaban glass center table nan ya dauko ya kawo mata gaban ta,ya kuma deba a hannun sa ya bata ta kai baki.
Kafin ya koma ya aje tray din akan table ya juyo tana kan taunar dabinon cikin nitsuwa sai tace yarinyar ba kamar kowa bace my son,she is your personal help ni da kaina na zabe ta ta kula min da kai.
Shima Baice uffan ba Sanda Ya zauna cikin kasaitar sa baima kalle ta ba "mamah,"is it necessary?
Itama jahan din Bata amsa ba sai tace cmon my angel addua ta fa yana tare da kai kullum dan Allah kar ka damu da komai,..nan sai ta jawo hannayen sa cikin nata a saukake Wani sweet and calming hand massage ta shiga bashi tana kure shi da kallo mai dauke da motherly sooths
cikin kwarewa ta rusunar da zuciyan shi yadda tasan dole zaiyi calming sosai,a tsanake ta ke massaging thumps dinsa ...
Khaldun was already cool amma bai ce uffan ba,lura da hakan yasa tace can i formally introduce her now?
Ba bata lokaci Yace ehmm..
Daga nan suka cigaba da dan hirar su...
Ni kuwa Ko wani minti 30 banyi da runtsawar ba naji ana buga min kofa
A firgice na sauko kaina na min ciwo
tuno da yau ban je na karbe kaya daga landry man na shirya masa su ba yasa kirji na bugawa
Sai dai ina bude kofa naci karo da ammu adama
Nasha mamakin ganin ta sai dai kafin na budi baki na gaishe ta ta jawo hannu na tana cewa u have to come quick Jahan na neman ki a falon ta cikin gaggawa
Nace toh,sai dai Kirjina kamar zai fashe tsaban tsoro da fargaba
ban iya cewa komai ba na bita har muka isa palourn jahan Aarah.
Muna shigowa shima fara hangowa,a sadade nake tafiya crushing and falling for his gesture duk dama nasan bada ni yake ba,For the first time eva yau naga wata kawataccen murmushi a fiskan sa daya sani jin zuciyata ta yafe mashi duk abunda yake yi mata.
Toh Lallai yana kaunar Mahifiyar shi,wannan yanayi nashi ko amafarki akace xan gani bazan taba yarda ba.
Sai da ammuh adama ta rusuna tace ma jahan gata nan kafin ma ya dago ya kalle ni,atake na ga ya sake daure fuskan sa
Ban damu ba na rusuna cikin sanyin jiki da ladabi nace ina kwana jahan?
Tayi min murmushi tace bahiyya ko?
Nayi sauran gyada kai tace
Taso ki tsaya anan.
Sai ta sallami ammmu nikuma na tashi tsaye agaban su duka daga gefe kaina na a kasa.
Inajin ta Sai da tafara bashi hakuri kamar wani sarki, sannan tace masa sunana bahiyyah nice zan dinga kula dashi for the main time..
"Tsaban yadda kirji na yake bugu bansan sanda ya amsa ba Ji kawai nayi ta saka masa albarka
Ta kuma jaddada min Dokokin aiki na agaban sa.
Nace insha Allah xanyi..
Nan ta sallame ni na koma site dina na fara shirin jiran malamina.
Washe gari da safe,tunda jahan tayi clearing tsakani da shi akan maganan aiki sai bani da wata fargaba na cigaba.
A kullu yaumin zanje na samu yana bacci haka nake kammala komai cikin sauki
Sai dai kamar an dauke masa magana baki yau kwanan mu 10 kenan bai taba budan baki yace min uffan ba"
I was happy tho atleast babu tsawa babu tsiwa
Ranar juma'a da yamma na baje littafan biology ina dubawa kawai naji an taba kafada ta.
Ammuh adama nagani tare da wani mutum cikin uniform din aikin sa.
Ban bata lokaci ba na sauko karasowa nayi cikin girmamawa na gaishe ta nan ta shiga min bayani
Akan cewa na shirya yanzu khaldun zaiyi tafiya dani kuma za'a je.
Sai da naji kaina yayi bugu na secnds kafin na dago murya na a karye nace ammuh har ibadan?
Tace min yes baahi,and you have to get ready now,daga nan ta tashi ta fice sojan na biye da ita
Wani sauke ajiyan zuciya nayi na shiga bathrum Haka dai na tattara kaina a sadade duk dama banajin dadin abun amma haka na shiga shirya kayana
Ko wani minti 10 daga fitowa daga wankar banyi ba aka kwalla min aika daga waje na fito.
Ammu ne kawai agaban manyan motoci kirar GTR i8 bakake har shida da aka shirya zasu kaimu aiport dan haka ita ta rungume ni tana min Allah ya dawo damu lpya.
Ayayin da ogana ya fito kowa ya shiga hankalin sa,motar dake kusa da tsakiya daga karshe ya shiga nikuma aka kaini na farko tare da security arm da driver har muka kai aiport
Duk da private plane ne kuma babu kowa daga ni sai shi Anan din ma ina daga bayan seat din shi shi kuma yana zaune agaba air hostess tana famar jigila da fitinan shi.
I was like chan muku,jim kadan sai gashi mun sauka a oyo,ibadan state.
Anan ma wasu bakaken motocin kirar mesarati su suka zo suka dauke mu.
Munsha nisan tafiya daga nan kuwa dan
Ba a tsaya ko ina ba sai da muka kai wani haddaden estate wanda ake masa lakabi da white house.
Tsaban kalle kalle na Ban lura da kyau ba har sai da driver na yace min mun iso
Anan ma cikin wata katafaren gida aka sauke mu,nikam sai danayi kallo mai isata.
Dan kuwa its a huge transitional building,wato gida mai dauke da both modern and traditional structures.
Masha Allah as we walked in mutane daban daban ke wulgawa cikin uniforms dinsu kowa na harkan gaban sa.
Ji nayi an dafa ni ina waigowa naga wata mata tana murmurushi nima sai na mayar mata.
Tace bahiyyah?
Nace yes maa..
Tace ok zo nan,banyi gardama ba dan kuwa ta kusan kaiwa ammu adama agirman jiki da dattako,
nan dai na bi bayan ta zuwa wani shashi,inda ta kaini cikin wani daki mai shegen kyau
Tace ni sunana aminah u can called me nanah A..im the chief maid here.
And This is ur room..
Nayi murmushi,
na amsa ta ganin kind gesturen ta nace ok nanah A nagode.
Murmushi itama ta sake min"
Kiyi da jikin ki ki fito pls,u have alot to do hala ku koma kanon gobe"
Da sauri na ansa mata da toh na shiga kimtsa kaya na Daga nan ma Bathrum na shiga na watsa ruwa
A Lokacin yunwa kamar zai kashe ni dan banci komai ba tunda muka dauko hanya,nan na fito na sanya simple jallabiya ina neman hanyar kitchen ina kuma dada kare ma gidan kallo dan shima ya hadu babu karya
Sai dai har yanzu ba damuwa ta bace Nasan me muka zoyi gashi tunda muka zo ban ma ganshi ba.
Ina sharo kwana kuwa Cikin sa'a muka gamu da nana A tana haurowa site dina.
Na dada gaishe ta,itama jawo ni tayi muka shiga wani shashi mai girma sosai.
"...Ashe ma a private part nake ban sani ba maybe ko dan anan shima ya sauka so babu hayaniya.
'Da muka fito sarari yanzu ne nake ganin asalin mutanen dake gidan...
Its actually one of his mums personal houses, ita ma idan tazo wani abun a ibadan anan take zama duk dama gaba daya estate din da sunan shi tayi signing.
Anan ba kowa sai nanah A da sauran ma'aikatan gida tsawon lokaci suna lura da komai
"He is here for an important 100 billion dolla national security meeting wanda za'ayi shi gobe da safe karfe 10 tare da taron duka wersten kings, obas and govenors of nigeria.
Muna sauka daga part dinshi nanah A tayi da ni kitchen a wani sashi,Kamar wanda take kallon hanjin ciki na
Tace am sure ure hungry"na gyada kai na asaukake.
Sai Tayi murmushi ta bude wani katafaren food store iya kallon idanu na
Tace here!!
sai dai ki tabbata ko wani abinci zaici awaje kina wajen,ki fara tabawa kici kiji, kar kiyi kuskuren sakewa har wani ya saka masa poison.
Na gwalo ido Nace ehm?Saura kadan nayi blurting out loud but i kept shut,so idan ma poising din ne nina fara mutuwa kenan ko?....
Chaii this ppl are funy.
Ban dai ce komai ba har ta gama shimfida min dokoki kusan iri daya ne da normal aikin dana saba mashi a chan gida kano
So i can quickly memorise everthing.
Kafin na daura girki muka koma ciki,
Anan ta gwada min dakin shi da sauran part din kafin ta kyale ni tayi gaba
I stood there staring ina ta kalle kalle kamar wata fatalwa,dakin Bai dai kai na chan gida a kano girma ba amma yana da girman shima sosai.
"katoton Kingsize bed ne da tufted head boards crown molding over walls tare da white ceilings sai wasu golden drapery curtains da tarin stylish funirtures.
Tabe baki na nayi na fito na shiga hade masa abinci kodan na samu nima naci ko naji dai dai ajiki na.
I did evrything accodingly babu wani matsala dan gidan sam babu hayaniya.
Its seems like Yana busy dan haka daya kammala cin abincin ya shiga daki ban sake jin shi ba.
Washe gari da sassafe nana A ta shigo daki nah,
Bayan mun gaisa take cemin
Nayi sauri na hada mashi abincin safe ta dada jadadda min karfe 10 ne meeting din shi,
Ta kuma cewa Khaldun ya bada umarni in goge floor din dake kofar dakin shi
Nasha mamakin wanan oder, dan nasan bana irin wannan aiki .
Amma sai nana A tace min ai anan gidan babu mai shiga shashen sa sai ita,yanzu kuma nine dan haka ni zan je na goge.
Nace mata babu komai Ban wani daga hankali ma ba na saka rigar material ja da baki nafito kitchen na shiga na fara hada masa break fast
Bayan nayi serving dinshi ban tsaya ba ya sallame ni sai na je hada mashi ruwan wanka
Anan sai na lura bai sha tea dinsa na safe ba,..
Nayi sauri dai na kimtsa na fito still banganshi akan dinning din ba na duba naga anan ma ko taba abincin baiyi ba..
Strange! Zuciyata tace ina faman tattara abincin zuwa kitchen.
A hanya muka ci karo dashi duk da ma nayi saurin rusunawa adaddafe bai hanashi daura min wata muguwar harara ba.
Drop it and come Yace ya wuce
Nayi sauri nakai kwanukan kitchen na dawo zan shigo dakin san sai naji a kulle yake gam gam
Dan wulakanci haka nayi ta knocking yana ciki yana ji har sanda na share mintina talatin ina tsaye kafin ya bani izini na shigo
A gaban wato sharbaben full size mirror na ganshi
Combin kansa yake da soft hair brush
Dan Baiko bani daman daidaita tsayuwa ta ba naji yace min
Almond cakes and orange juice
Daga nan bai kara cemin uffan ba yayi shiru.
Wani rau da idanu nayi I was like New breakfast oder kenan?hmmm kirjina ne ya biga
Ayayin da na ja kafata nayi hanyar kitchen na masa exact abunda yake so.
Fresh orange juice with spicy almond pan cakes na hada mashi da cool raspbery desert.
A tsanake yake ci yau kam ya taba duk abunda na ajiye masa.
Ina tsaye daga gefe ya ajiye food napkin din ya gama goge bakin shi ya kalle phatek philp din sa ya dubi time.
Kinyi aikin dana saka ki?
Da sauri
Nace ah'a
Sai Ya dan tabe baki
Yace 9,45am u wll get my dresses..
Kafin na gama amsa shi yayi gaba ya haura dakin sa.
Da sauri na kimtsa komai banma iya neman wanda zasu ci abincin daya bari ba sai na juye a wani warmer na jika ruwa a mopping duck na taho inda yace na goge din
Daf da kofar dakin shi ne infact za'a iya ce ma wajen hall way ne daya ke bi in zai shiga daki..
Anan na baje ina goge tiles din da basuyi kama da sunyi datti ba Allah kadai yasan meya sa yace agoge mashi.
Ina cikin aikin sai ga sallama
Wani mutum nagani mai kama da delivery man wearing a strip army uniform baiya ko murmushI shima
box din dake hannun shi ya mika min ya juya abunshi.
Duk dama Nasan kayan sakawan shin ne but I have to open it And check Kamar Dai yadda nanah A tace inayi dan na tabbatar da komai intact.
Sai na aje mopper ta agefe Ban lurada ruwa yana tsiyaya A kasa Ba nan na bude box din cikin rawar jiki.
Wasu haddadun uniforma naci karo dasu God Knows Its amazing,Hannu nasa akan Materials din Ina shafawa Basai an gaya min tsadaddu bane kyaun su a ido da laushin su ya isa ya sanar min..
Farin rigan uniform kal ce da royal blue army trousers da cap an nade su tsaf kamar ba mutum ne zaisa ba.
Sai dai wannnan
Karon wayo na ya carke min A hanya bansan ma unifom din na soja bane ko na mai tukan jirgi"
,dan Ban ko iya karanta Ma'anan Abun da aka rubuta akan silver plated insignia da aka manna agaban white shirt din ba (wato milltary badge dinsa) dake gaban rigar ba .
Naga dai An rubuta wasu abubuwan a dakile kafin naga wata kalma kamar sunan shi reading BG SA'OOD HAMOOD MC.
Nan na Shiga tunani ina nazari,ni dai naji ana ta Ce masa khaldun amma bashi nagani ajikin rigar ba toh what does that mean?
Ko dai ba sunan shi bane?To sunan waye kenan?
Wasa wasa na tsunduma kaina cikin nazarin da baida amfani ban hankara ba naji an bude kofa daga baya na Ina juyawa kuwa muka hade ido tsaban gaba na yayi rasss sai nayi saurin fizgewa na kame
Nasan Shi din ne ya fito yayi tsaye yana jefo min mugayen kallo hannun shi rike da door handle dinsa
A sadade na shiga kokarin rufe box din ina kokarin mikewa na kalle shi na mika masa kayan sa,ai kuwa Ina daga kafa ta sai gashi tsantsi ya debo ni nayo zutttt na zame akasa Kayan sun zube duka acikin ruwan bleach din dake kasa wanda ya zubo daga mooper duck din.
A take na shiga ganin waje ldishi dishi Duk da zafin buguwan da nayi bai hanani karkarwan tsoro ba
Kokarin mikewa naki sai naji na kasa daga kafa Sau dari ina kashe kaina mentally.
Yau Na shiga uku na furta ina kokarin jan kafata da karfi dan Na mike nasan bazan iya Ma kallon Idanun shi ba.
Im very sorrry sir!!! Dan Allah kayi hakuri...
Baki na ne ya shiga furta su involuntarily
Baice min uffan ba
Hawayen tashin hankali bazata suka wanke min fuska ta ina famar tsamo kayan daga cikin ruwan bleach din dik sun baci sunyi rawaya
Bai min tsawa ba but yadda yake kallo na in a disqusiting way nasan tawa ta kare min.
Wrist dinsa ya daga ya dubo time a Agogon shi ya ce min
I have A Multi billion dollar meeting in 20 minutes.
Ki kawo min kayan da zansa na baki minti goma,ko dago kaina banyi ba wuff ya juya ya koma dakin sa ya barni da Jikakken kayan sa a hannu na.
Follow
#SURAYYAHMS
COMMENT and SHARE YOUR VIEWS❤❤
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top