chapter4
♡this is how khaldun looks like
VOTES PLS
_4⃣-Coincedence♡_
A daskare na tsaya chak kamar wacce akayi freezing dan ko iya juyowa banyi ba.
and y are u in my room?Ya sake fada muryan sa emotionless
Wani runtse ido nayi for the moment ina sauraran bugun zuciya ta..ohhh ya ilahi"...his voice... shi kadai ma ya isa yi ma zuciyan mai sauraro hisabi..
kakkauran sautin muryan shin ya daki tsakar kwalkwar ta har yasa na saki siririn nunfashi, ji nake tamkar kirjina zai fado kasa tsaban tsanan ta bugu,..not withstanding sai na daure na amsa cikin sanyin murya nace... um..umm dama damm..a ..nice mai aikin ka,mai kulawa dakai..
Wani Shiru naji yayi bai amsa ni ba
Banji mamakin hakan ba sabida yadda nayi maganan kasa kasa cikin tsoro da fargaba nasan ba lallai bane yaji.
Shud i just turn around and look at him?na tambaye kaina anma sai naga nakasa yin hakan...
ayau ko da ace ban fara mallakar hankalin kaina ba dole ne na fahimci cewa wannan gayen ba kalar masu maimaita magana bane.dan haka Bani da wata mafita face na maimaita ansar tambayar shi
A take na kuma taro confidence na dan bude baki nace"nice mai aikin ka mai kulawa da kai.
Still naji yamin shiru,
Nace im ur personal house help sir....sai nadan daga murya na kadan tunani hala baiya ji nane ashe ba haka bane.
Hasali ma juya kanshi yayi yana tsime akan pillown sa yayi banza da maganan kamar da icce nake tare ba da mutum ba,"hmm ashe gwara ma da ban juyo na kalle shi ba sai na cigaba da tsayuwa ta..
Chan dai dana ga abun nasa so i started panicking,
Gashi kafa na har zafi ya soma min tsaban tsayuwa waje guda nakai minti 10 ina maimaita abu guda azuciya ta,da kalmomi iri iri na ansa shi ko zanji yace wani abu
Still yana shiru.
"can nima nayi tsit still dai ban juyo na kalle shi ba,cikin tunani na nace Oh Allah,ko kashe ni zaiyi ne kam! Maybe is time to walk away...halan ranshi ne ya baci...
Sai nayi yunkuri fast foward zan fita sai dai Ko daga kafata banyi ba naji ya daka min wata dakakkiyar tsawa wanda dirinta ta nane min kafata ta kuma daskarar da gangan jiki na,
waje daya na tsaya sanda kunne na ya jiyo tambayar na daban dayayi min again'
Meya kawo ki daki na?
Lokacin da baki na ya furta tea tea tea dink...a na zo ajiyewa banma sani ba..My tongue was seriously sluttering har kalmomi suna neman kasa haduwa abaki na.
Dan shiru yayi cahn naji yace did you know who i am?...!yana gama rufe bakin sa
Immidietly na girgiza masa kai alaman ah'a
Words!!!
Yace yan mai daka min wata fusatacciyar tsawa
Lokacin da baki na da kanshi ya furta amsar"ah'a,ban ma sani ba.
Gaba daya sai naji na tsorata sai na rasa meyasa yake min masifa to ni menayi masa?ba shayi kawai na kawo ba?
Ji nayi yace aikin ki ne kizo ki dame ni ina bacci?
Na girgiza kai da sauri nakuma cewa ah'a da sanyin murya..
Yace kinzo kin tashe ni ina bacci baki ji ne ko baki gani?...kirji na dada bugu na girgiza kai na gefe da gefe na kuma cewa ayi hakuri.
Tsimewa yayi,Bai kulani ba cikin makokwaransa yayi kwafa yace both i quess...toh daga yau kar na sake ganin mai kama dake a dakin nan dont you ever come into my room.
Ever!!! ya dada jaddada min.
Kaina akasa na amsa shi A tsorace ina kan jiran next action.
Get lost!!!
Comanding voice dinsa yayi wisphering chan kasan wuya kamar bada ni yake ba,aiko da uban sauri na fice adakin na koma kitchen rike da kirjina ina haki.
A gurguje na shiga hada abubuwan dana shirya
Koda na fito na aje masa breakfast din sa sai naga bai ko sauko ba ma bare yasa lokacin yaci.
Haka naci tsayuwa akan abincin har nagaji,so i tot ko dan na bata masa rai ne bayason ma ya kalle fuska ta
inayi ina dan komawa kitchen hoping to see him seated amma shiru har na kammala komai na dawo na dauki abincin na mayar kitchen.
Ashe har yayi wanka ya shirya kansa ya fice ban ma lura ba.
I was kind of pissed duk dama banda wani dalili,lokacin aikin na kaucewa na tattara komai a kitchen din na tsaftace shi tsaf kafin na fito ina sb tambaye tambaye har nagane ashe ma ya fita ne agidan baki daya.
Yau a sace kamar wata munafuka na gyara mashi daki na wanke bayi,na kuma jera masa wankakkun kayan sa a closet...
Ina kwance akan gado na,zuciya ta tana mugun sha'awar ganin ammuh adama amma kuma bansan ina zanje kai tsaye na same ta ba
Ni kaina nasan ina muhallin da aka gina shi da dokoki da tsari Tsoro na kar naje na shiga inda bai dace ba nayi laifi.
And I do not want to miss this chance,ko ba dan komai bama nakan tuno da mummunar rayuwar dana fito daga ciki dan sati biyu da suka shude
Shin waye zai bani aiki awaje kamar haka?inacin mai kyau ina saka mai kyau ina bacci akan gado mai kyau..a rayuwa dai nasan na taimake mutane da dama amma babu wanda ya taba tunanin biyana ta wani fanni sai anan gidan.
Speaking of secrifice,in na tuna da hakan kirji na ne ya kan buga,a take naji wani shauki mai karya zuciya ya shige ni ya min rawaya a kirji na
Juyi nake faman yi ina juyayi cikin azaban radadin kewa da son in taurara zuciya ta
Sam sam bana so na tuno da babbar aminiyata junnut bare ma na tuno da iyaye na wanda suka riga suka bar duniyan nan suka barni nikadai.
Sai dai karban qaddara ga mumini ba kasawa ko gazawa wajen nuna soyayya bace,inka ganni wata rana zaka dauka bana tuna kowa aduniya nan,but deep inside me i know no one can eva replace my parents and my dear friend junnut.
Wanda ayanzu na karbi qaddarar daya rabamu wanda kuma babu alaman zan iya ganin ko daya daga cikin su har abada,wannan shaukin ya sa sai na dena saka komai a raina ma game dasu ina dai fatan so na riki duniya ta fuskar da a duk inda suke bazan taba basu kunya.
A Yau na yanke wa kaina hukuncin jajircewa wajen aiki na batare da na sa damuwar halin ogah na araina ba..
Tun safe da yamin maganan Ban sake ganin shi ba har sai da dare yayi a dinning dinshi wajen serving dinshi dinner.
Riga da skirt royal orange mai tsafta da sanyin qamshi na saka dauri na simple babu hayaniya tsaye nayi a agefen shi na shiga serving dinshi in varieties Crispy fishrolls,offals pepper soup da
tamarind juice dayan wamer din kuma tuwon shinkafa ne mai laushi da miyan eforiro yau ban jero abinci dayawa ba dan bana iya taba zubarwa kuma nagaji da neman masu cin ragowar.
Ina serving dinshi tsaban fargaba jiki na har rawa yake amma duk da haka ban fasa gulman sa araina ba,hmmm yau naga abun mamaki So finally he decided to fully show me his face!
kanshi ya dora akan chair din yadan jingine Babu karya gayen ya hadu,kai kalman haduwar ma is an understatement.
Kamar yadda nayi harsashen kamannin dirin jikin sa da indian actor john Abraham Sai naga fuskan nasu kusan kwatance daya ne, aga nina ma yafi shi haduwa da hasken fata the guy is faultless and flawlesss.
Sanye yake cikin wata kasaitaciyar collection na kananan kaya ta kamfanin dior hormes white shirt and a very soft black trosers.
"Suman kanshi is silky black and shiny babu wani sanko ko cinkai,gashin sa acike take luff dai dai misali sannan babu maraban askin kansa dana world best foot baller wato cristiana ronaldo.
Bakin shi dan dai dai,Daidaituwar shape din Karan hancin sa ya samo kyakywan diri ne daga Shatin kerarren Sajen sa wanda yabi cikakken giran shi masu dauke da dogayen eye lashes dinsa.
Nasan hala bazan taba ganin murmushin shi ba sai dai Allah cikin ikon sa ya bayyana shatin lotsawar kyawawan twin dimples dake gefe da gefen kuncin sa,
He loves keeping straight face ban taba ganin mutun mai son bata rai kamar wannan gayen ba
Hannu na sai rawa yake a hankali amma bandamu ba haka na gama serving dinshi.!
Ina gamawa nayi sauri zan Juya da niyyar basa waje sai naji yace na dawo na tsaya!
Tun daga nan baice min uffan ba,ina kallon shi yana cin abincin a tsanake,well pampered yatsun
Hannun shi da suka ji gyaran manicure su suka dauke min hankali he's goddam porschy sosai yaji wankan aji.
Dan kadan yataba offal pepper soup yasha tamarind juice din ya aje spoon abunsa.
Baice min uffan ba kuma bai tashi ba,wayar sa ya cigaba da latsawa yana kira ana kiran sa.
Tsaban na gaji Baya na kamar zai karye amma hakan na daure na jira bai kuwa tashi barun wajen ba sai da ya wargaza min ka'idan lokacin aiki na.
Da sauri na tattara dirty dishes din naje kitchen ina wankewa ina maganan zuci.
This guy is kind of mean wallhy,wasu mutanen dai haka suke,shegen iya wulakanci da fi'ilin tsiya.
'..Washe gari da safe hakan na tashi da niyyar cigaba da aiki na as usual abincin shi nafara dafawa duk dama nakasa motsawa sosai.
Gaba daya tunanin Abubuwa dayawa sun cirke min zuciya,duba da yadda jiyan yace kar na sake shigar mai daki"
Shin yanzu maganan wa zanbi?
dokokin aikin da Jahan Aarah da ammu adama zan dauka na cigaba da aiki na koko na wannan mutumin da ko sunan shi ma ban sani ba?
Wannan rudaddiyar muhawwara da zulumi yasa na dan ja lokaci banje dakin sa akan lokaci ba.
Sai chan anjima dai na taro caurage na iso,Ko da nayi shahada na turo kofar sa a sadade na leka sai naga wayam babu shi akan gadon sa
...cikin mamaki na tsaya baki na abude.
hmmm seriously
I was surprise ai na dauka doka ne baya tashi akan gadon shi sai akan tsarin lokacin sa.
I waited,haka nayi ta jiran tsammani dan naga ko zai shigo amma shiru har karfe 8 ya gauce toh nasan lokacin cin abincin sa yayi Sai nayi sauri na sauko
cike da sa'a kuwa na ganshi yana kokarin shigowa part din
A gurguje naje na fara shirya masa abincin,gani danayi ya zauna bisa kujeran dinning din ya dada bani karfin gwiwa so i served him kamar yadda nake yi,yaci abincin kadan ina tsaye akan sa har ya tashi ya bar wajen kallo na baiyi ba bare yace min ci kanki.
Haka ma yau da daddare dana zo serving dinshi dinner wani azakzalan masifan danaji yana yi ma wasu agaba na sai danaji hanjin ciki na ya kada ya gamutsa kansa.
Mennhn gayen is quiet tempera mental masifaffe ne babu karya.
Dan haka nima nabi shi sau da kafa har muka rabu lpya na koma dakina batare da ya sauke min ba
Washe gari da safe tsoro ya hana ni aiwatar da komai mint tea din dana dafa mashi ma ban kai dakin ba
ajewa nayi na hada tare da abincin shi akan dinning tunda nasan yanzu ya hanani shiga dakin sa,Jira nake inya fita naga me zan iya yi,.
Ina tsaye sai gashi nan kuwa ya fito cikin shirin sa tsaf da alaman fita ma zaiyi ,da sauri na dan rusuna kai na gaishe shi duk dama nasan bazai taba amsa ni ba.
Wuce ni yayi kamar mai iska nima sai na dago kai na biyo bayan sa
'Zaman sa yayi agaban table din baice uffan ba ya kama shan shayin dana ajiye baiyi korafin komai ba,.araina naji dadin haka
Sai nayi serving dinshi abinci na tsaya a position dina ina jiran shi ya gama cinyewa na koma kan aiki na
akan empty seat dake kusa da shi ya aje Jacket din Bakin fitted Tux din daya saka ajikin shi sai ya bar pure white shirt dinsa a bayyane
Sai naga gogan ya dage yau dayawa ma yake deban abincin yake ci,.
This guy is too perfect,i cant deny that zuciya ta har ta fara crushing akan haduwar sa in ina kallon sa har bana jin nagaji.
25 minutes of chewing ya aje spoon yana kokarin goge baki slighty da food napkin bai mashi ba ya ajiye
Mango juice!!!
Ya fada baiko kalle ni ba
wata tsadadiyar transparent glass na rarumo na shiga zubawa toh bansan meya faru ba sanda nake haba haba na debo na mika masa
Shin nice ban rike da kyau ba ko shine ya buge ni all i saw was dukan juice din ya subuce daga hannu na ya kwarara masa akan farar rigan sa
Sake kofin akan table nayi a slow motion Da sauri na lumshe ido baki na bari na firta innalillahi waninna ilaihi rajiun
wani mugun kallon barazana ya bi ni dashi ayayin da yake kokarin mikewa yana exclaiming da bacin rai afuskn sa
Ban bari ya gama tashi tsaye ba na raromu napkins arude na taho zan fara goge mashi.
"dont you dare touch me" ...
Cikin wata irin tsawa yace min
A gigice na koma baya ina neman hado kalman hakuri.
Ko saurara ta baiyi ba ya haura sama a fusace, kusan minti talatin wajen ya dau shiru chan sai gashi ya sauko da rigar a fuskata ya wurga yace
"I want it the way it is".bai jira na amsa ba Ya sa kai ya barni a tsaye
Yana fita nayi saurin deban komai na bar wajen.
Sai da nagama aiyukana tass sannan na fara wanke rigar .
Ba wani stain din kirki ba ne amma Na wanke na wanke yaki fita tass har Raina ya baci.
..wannan wata irin material ne haka?,i used evrything in the loundry sai kace wani kayan sarkin aljanu?to meyasa tabon juice din bazai goge ba?
Yau kam danaga babu mafita sai na fice na shiga asalin haraban gidan ko zanga ammuh adama na nemi taimako
I cudnt find her sai nahadu da mami fatima":
Tasha mamakin ganina awaje amma saukin kai da iya ladabi na yasa ta amsa min bukatuna
Cemin tayi bata san inda ammuh adama take ba amma indai dan fitar da stain ne a riga tana da abun da zata bani na yi amfani dashi.
I was happy sai nabita ta dauko wani concotion ta bani,daga ji lemon tsami aka tula aciki..
Godiya nayi mata na dawo dakin wankin,ba bata lokaci na tsoma rigar da wannan abun na shiga dirjewa yayi kumfa sosai har ina murna ko kayan zai fita
Ban tashi shiga uku ba sanda na dauraye naga duk stain din rigar bai gogu ba infact ya sauya kala ne ma daga orange stain ya dawo kalar bacaccen bula duk yayi layi layi
Ya ilaahiiii.. .i was not happy amma haka na daure na busar na kuma goge shi da kyau tunani na ko zai ragu amma ina kamar ma kara fito da shatin abun nayi.
Haka nayi ta fama har nagaji ya yanke hukunci kai masa rigar sa hakan inyaso na bashi hakuri.
As usual bamu hadu ba sai wajen cin abincin dare
Har nagama serving dinshi yaci abincin baice min komai ba sai ma naga kamar shirin mikewa yakeyi zai shiga daki
Ohhh Alhmadullhi Kenan ya mance da batun rigar?
Tuni naji sanyi na neman mamaye cikin raina Sai dai fa Kan na sake wani motsin sai naji yace min ina rigar shi?
Dumm na tsaya kamar wanda aka kira mata kalman mutuwa....
Gaba daya na rasa ta ina zan fara dan ban shirya ba.
Amma da shike nasan bazai maimaita tambayar ba sai na shiga jero ...i..i. .na cikin rawan murya nace
Ummmmm pls im sorry sir....kayi hakkku..ri na wanke rigar sosai amma stain din yaki ficewa..
Wani irin kallo ya bini dashi
Shi dai Bai sauya fuska ba amma ya dauke kansa
.. Yace shikenan kije ki cigaba da wankewa in yafita zaki iya yin bacci yau .
Kaiwa nan ya haura sama ya barni a tsaye nayi durus kamar wata shanyayya
Haka na ja kafata zuwa dakin wankin god knows bazan iya sake wankewa ba dan na san babu abunda zanyi ma rigar ya dawo dai dai,na lura komai dada lalacewa yayi, evrtyhing become worst dana saka wannan abun da mami fatima tabani
Wani zuciyan yace na gwada takurawa wajen bashi hakuri mana ko zai fahince ni
Haka na fito da rigar a hannu na har bakin kofar sa na kwankwansa kofar kimanin minti 13 sannan ya bada izini na shigo
Yana zaune Ko kayan shi bai sauya ba,ya wani hakimce gaban tv yana kallon wresting asalin wwe raw na zamanin tun undertaker nada siffar abun tsoron sa.
'Ni wannan bai dame ni ba domin kuwa banyi kasa a gwiwa ba na rusuna kan duka kafata nayi kneeling agaban sa da rigar a hannu na nace
" dan Allah kayi hakuri sir,nasan nayi kuskure. .nayi ta gogewa yaki fita ne pls am soryy sir
Ina karasawa nayi shiru
Thank god dai murya ta batayi bari ba
Sai dai ko kallon arxiki baimin ba bare ya san inayi.
Haka na maimaita har sau uku bai amsa ni ba i was so scared and doom
Duk Sai na rasa me ke min dadi
Sanda naji wani ruwa mai gishiri gishiri nabin labba na kafin na san hawaye ne ma suke sauko min.
Duk dana yi sauri na goge sai dada tuluwa suke yi,haka kawai naji raina ya baci sai dai bani da ikon yin wani rashin kunya ko magana shesaheka ta ma a sadade nakejan ta kar ma yaji ni na harzuka shi yace zaimin wani abu.
Haka na ci kneeling har na rabin awa agaban sa rike da rigar, idanu na sun gaji da fiida ruwa dan kansu suka bushe.
Bacci ya dame ni dan nagaji sosai
Dana ga dai baiya da niyyar min magana sai kawai na tattara kaina cikin sanyin jikin na tashi na bar masa dakin sa.
Da nake fitan ma
Na dauka zai daka min tsawa ko yace nafita ban tambaye shi ba,amma shiru baice uffan ba har na rufe kofar na bar site din.
Tsaban damuwa da gajiya ban iya kai rigar dakin wanki ba dashi na kwana a gefe na.
To my surprise da safe ina idar da sallah naji ana buga min kofa
Toh yau kuma waye wannan?
Tunda nazo nan part din gidan babu wanda ya taba zuwa daki na sai ammuh adama tun aranar farko
I was Shocked and surprised at same time but ban daddara ba na taho na bude kofar
Wow...its ammuh adamah!!
Wani sanyin murmushi na saki ayayin da ta jefo min nata murmushin muka karaso ciki tare
A ladabce nagaishe ta tana daga bakin gado nikuma ina kasa akan dan karamin beige.
Tace bahiyya? Menene matsalan ki fatima tace kina nema ta jiya...
I hope ba wani abu bane Ya hada ki da shi.
Nan na dago kai na cikin damuwa mai dauke da zuciyan kuruciya
I wish that ammu adaman tana tare dani kullum dana dinga gaya mata halin wancan mutumin,so i managed to started talking calmy ina fada mata labarin abun da ya faru da rigar sa dan yanzu shine babbb damuwa ta,ita kuwa kamar bai wani daga mta hankali ba
Batace uffan ba kam amma Fuskan ta ya nuna alaman tausayawa musamn
Da nace mata he is very mean and hard to understand,
Wani bin murmushi kawai takeyi cikin ranta tana tunanin yadda zama na zai kankama agidan da alamu ta hango hakan.
Chan tayi gyaran murya cikin lallami ta dada ja min kunne akan aiki na,cewar ta kar na biye mashi dokar jahan Aarah kawai zan na bi.
Game da rigar kuma wata customised apple vineger ta bani naje agurguje na jika dashi na wanke da machine nayi instant dryng nafito dashi rass
I cant believe it dan a take wanann vinegar ya wanke min shi tass ya dawo normal sai na goge ina ta jiran perfect time domin nakai mashi abinsa.
Ahaka har nagama dafe dafen abincin safen sa,whith all what ammu told me akan na rike aiki na sai na mance da dokar sa na cewa kar na sake shigo masa daki,aje rigar nayi agefe kamar wata mayya haka nayi sneaking na shiga dakin na kai mishi shayi
Yana bada baya na shigo na kimtsa ko ina nayi waje na wuce dinning ina jiran dawowar sa
Banga alaman kunya a idon gayen ba dan kuwa zama yayi agaban abincin yau kam ma bai bari na xuba mashi ba ina kawo hannu ya hantare ni yayi aikin da kansa
Not normal ya zuba da dan yawa yau ko dan jan aji da rigimar baiyi ba ya shiga ci baiya ko kallon inda na tsaya kamar wata statue
Nidai wani bin Dariyar sa nake ji har cikin raina cos yau din sai naga kamar he is eating like a horse
Murmushi na ya so ya bayyana akan fuskata amma sai na yi saurin toshe shi da dan karamin voiceless cough duk da haka sai da ya juya ya balla min harara karshe maya kora ni na bar wajen
Hakan ya bani daman hada mashi ruwan wanka kafin na dawo na samu ya gama har ya bar wajen
Bayan na tattara na kimtsa komai
I have to wait again domin nabashi rigar sa
Chan naje kofar dakin shi nayi knocking atleast 10 minutes ina tsaye kafin yace na shigo
He is all dressed in cute marks and spencer jan riga da bakar wando yayi matikar kyau.
Gaishe shi na sa keyi kafin na rusuna dan nasan ba ansa ni zaiyi ba.
Cike da jarumta da nitsuwa na fara magana clearly batare da nayi barin baki ba
Nace dan Allah kayi hakuri akan abunda ya faru jiya.
Ga rigar nan,na wanke kuma ya fita knar yadda kace....sai na danyi shiru don jiki na yayi sanyi ganin ko daga ido ya dubi inda nake baiyi ba bare ya amsa ni.
Hasali ma idanun shi nakan system dake gaban shi ne as usual babu alaman rahama ko sauki akan ta.
Ahaka Na dada taro courage nac nazo na nuna maka rigar ne,pls may i hang it in ur closet?
Ba tare da bata lokaci ba ya dago ya min wata wulkantaccen kallon daya sani na sauke kai na a sadade
"throw it away."
Yana furta hakan ya dauke kansa
Bansan sanda zuciya ta ta furta "what?ba ahujajan na dago na kalle shi sai naga kamar ba shi ya yi maganan ba
Yadda ya sa kai akan system xaka rantse da wani abun daban yake maganan bada ni bahiyya ba
.
Duk dama nasan baiya maimata magana but i have to ask again
Nace yes?sir...sirr kace na yar da rigar"
Bai samu lokacin sake dago kanshi ba ma bare har naji kamar zan sami fitowar wata kalma abakin shi
Atake Raina ya baci i was like kan uba?
Gayen nan yasan ba amfani da rigar zai sakeyi ba shine ya sa nayi ta wankewa kamar mahaukaciya?
Wannan wani irin danyen iskanci ne?nima ko sake kallon shi ban yi ba na ja rigar nayi waje dashi..
Daki na na koma na zube kan gado ina bambami
Natsani wulakanci dan haka wasu ruddadun hawaye ne suka shiga sauko min har na samu sauki a cikin raina.
Follow #SURAYYAHMS
Sharhin ku na kayatar dani sosai
Har na rasa wanda zan bashi numbar yabo nagode sosai Allah ya bar kauna acigaba sa sharhi
Share share and share.
Son so daga suriem.❤
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top