chapter37


_3⃣7⃣-Brave heart♡._

Jahan Aarah ta dake tana ci gaba da masa mugun kallo tace "akan wani dalili?" Ya dago kai yana kallonta xai yi magana ta rigasa tana girgixa kai tace "to ban amince ba, in kuma ban isa da kai ba sai ka nuna min yanxun nan in ga,Aaban,fita ka ban waje"

kallonta kawai yake ya ma rasa me zai ce mata,a dan fusace tace"to ko dukana xaka yi irin wanann kallo haka, ban da ka raina mutane meye dalilin ka da yin auren nan ina shirme ba,salon ka ja min magana a gari yarinya karama na zaman ta lafya ka tashi ka ce xaka azabtar da ita?

abokiyar xamar da kuke shirin kawo maka wato kenan ku hadu kuyi ta cutan ta ko, to baka isa ba kayi kadan, in kanwarka aka yi ma haka ai ba zaka ji dadi, plss leave"...khaldun ya kuma sunkuyar da kansa kamar karamin yaron mwi shirin yin kuka yace

"to amma mama naga da amincewar ta a farko kuma wannan abun naga ba haramun bane bare ace rabuwar shi yafi..

..."Wani tsawalellen kallo ta banka masa,wa ni xaka kawo ma wanann maganar? Dan kaga ban yi fushi dakai da kake sata dole ta amsa ba Kana wasa da nine?
Toh in ka isa ka je kayi zaman auren nan muga, get out in daina ganin ka a dakina, baka tunani kawai"

Wani kasalan xuci zancen nata ke dago masa, a lalace ya tabe baki mikewa  yayi yana shafa kansa bai kuma cewa komai ba ya nufi kofa kamar zai fita..

Alhj hamood ne ya shigo dakin yana ma jahan mugun kallo sigar zolaya yace"sannu, kin yi kokari..wato kamar yanda ki ka hanani ni yi ma mijin subaya ta hukunci,shine da na ma xaki hanasa abunda yake so?

Anan kam baki isa ba,gyaran auren sa babu fashi ni nayi wanann alkawarin"

Khaldun dake rabe agefen shi yayi murmushi jin dadin wannan kalma yace " A'a dad abun bai kai ga haka ba, tunda mama bata so kawai ni na fasa bana son abun da xai bata ran Sarauniya ta,a bar maganar auren kawai har sai ta amince"wani kallon banza Alhj hammod ya ke masa yace "sannu me uwa,

wato ni xaka watsa ma kasa a ido na zo tare maka bakin rai koh,yayi maka kyau..

ficewa Alhj hamood yayi daga dakin, Khal yayi murmushi ya dawo kusa da jahan dinsa dake zaune ko kallon inda mai gidan ta yayi bata yi ba.

Cike da sanyin jiki ya durkusa kusa da ita a hankali ya fara magana

"mamah, kiyi hakuri idan na bata maki wllh na bar batun auren tunda ba ki so,kila hakan ne yafi min alkhairi,ki kwantar da hankalin ki na rufe zancen daga nan wllh"

jahan ta dago tana kallonsa shikadai yasa ta ina zai iya sace xuciyar ta tace

"Ka turo min bahiyyar gobe sai in ji ko da gasken da amincewar ta tin farko dakake fada. in tace ehh,to baxan hanaka zaman auren ka ba tunda nima ga abinda uban ka ke cewa a kaina,in kuma tace bata san da zancen ba to ko me zai faru baza ka cigaba da xaman auren dole da yata ba..noor ta sha wahala sam baku da tausayi wallhy"

Khal ya girgixa mata kai yace"No mum ni na bar maganar in har ranki bai kwanta akai ba" .

Jin kansa kawai tayi akan cinyar ta yana mai sauke wasu nannuyan ajiyan zuciya kamar mai shirin fitar da kalmomi masu nauyin gaske daga zuciyar shi....

Mum...i want the marriage.

I know,abunda nayi ban kyauta ba,but i do care about he...rrr.. I swear...

Kuma Kinga sai inkin amince zan iya cigaba da zaman aure da ita..

Nidai Pls ki duba ki gani i wont repeat such mistakes..im sorryy ummah..

Yadda ya karasa maganan hwanin tausayi yana wani nokewa cikin maraice murya,yasa gaba daya jikin jahan yayi sanyi

jahan tace "ni ka tashi ka ban waje kayi abinda nace maka bana son dogon magana" ya dan Marairaice mata yace "wai  fushi kika yi da ni, wallhy har xuciyata na fada maki bazan karaba..mum kar ki raba auren nan"

Data ga ya daga hankali...sai ta dan sake ranta ta shafa kansa tace "to shiknan naji kar ka damu,sai kasan yadda zakayi na baka 3 days kusasanta idan noor tace bata aminta ba sai dai fa kayi hakuri,..ya dago zaiyi magana ta riga shi tace jeka kayi yanda nace maka kawai,ni banyi fushi ba".

mikewa yayi yace "to shikenan,nagode ya dora mata kiss a goshi yana mikewa Bari in tafi site dina

tace "to Allah shi kiyaye" bai bar nan ba sai da yayi ma dad dinsa sallama sannan ya fice daga site din yana murmushin irin amsawan da dad din yayi masa.

Shidai alhaj yana mugun son auren nan..shiyasa ma tun farko ba a samu matsala wajen samun hadin kanshi ba..

Karfe tara da rabi na daren ranar Khal ya shiga dite dinsa,

Yau dakansa ya kashe wutan main falon as usual ya nufi sama zai bude bedroom falonsa a hankali ya zura key yana yi dai yana kallon kofar dakinta

Yana shiga bedroom dinsa ya nufa kai tsaye ya tsaya da mamki yana ta kallon dakin.

yanda ya fita ya bar shi haka ya dawo ya same shi sai dai bata kan gadon a yanzu.

Baiyi wata wata ba ya fice a fusace ya nufi dakinta ya bude ya shiga kai tsaye,bata dakin jin zuban ruwa da kamshin soap ya gane wanka take,

tsayawa yayi a dakin yana jiran fitowarta fuskarsa a daure ta fito daure da light purpl towel tana saka gashinta cikin wet net din dake hannunta,

Data waigo sosai ta tsorata ganinsa tsaye a dakin don bata ji shigowarsa ba,ta juya da gudu zata koma bayin tana cewa"Innalillahi, ya riko ta ya dawo da ita..wani gullutun hadiyar yawu tayi dama tun safe take avoiding dinshi dan tasan hala gamuwar su yau bazai mata dadi ba

kai ni nashiga uku da wanann jaraba...cikin ranta ta fada amma bata sam ta furta hakan ma a fili ba

Shikuwa kallon ta yake yama tasa me zai ce mata

maganganun mum dinshi kadai ke masa yawo a lokacin kwana uku ta bashi baisan ya zai fara da ita ba,sai ya juya hannun ta acikin nashi saukan numfashin sa taji a wuyanta yana mai sake mata kiss da damshin lebbansa duk a lokaci guda,

ta gwalo ido a tsorace zata fara ihu ya matso ta jikinsa ya toshe mata baki da hannu daya sanann ya zamo fuskarsa a hankali zuwa kan kirjinta,bahiyya da ta ji kamar numfashin ta xai dauke don tsabar tsoro ta shiga kiciniyar kwace kanta a hannunsa jikinta na rawa amma ta kasa

wani ihu ta fasa masa a gigice ganin abinda yake shirin yi,a take ta shiga tuno warning dinsa data saba dazu agaban jahan Aarah
Ai dama yace zaiga karshen ta inta fada

Tsoro ne ya rikita ta sosai ta shiga zare ido kamar zata yi kuka, Ita bada wani nufi tace hakan ba,she just want him to feel
Extly how he felt da soyayyar shi a lokacin dayake basarwa

..ta labgwame masa sosai bata gama rufe baki ba taji bakinsa cikin nata, ya shiga mata kiss mai dagula lissafi, daga ita har shi kasa tsayuwa suka yi duk suka zube nan kasan bayin kamar da sannun su suka fara..

daga jin irin numfashin da take yasan ba karamin tsoro takeji ba amma duk da haka bai kyaleta ba sai da ya ga jini yadan silalo kadan a kasan kafarta sai  sann ya gane al'adan ta yazo mata

  ya turata ya mike da sauri ya fice daga dakin nata mai gaba daya ya nufi dakinsa,wani azababben yanayin son kasancewa da ita ke deban shi da kyar ya fada bathroom ya kintsa kanshi

Bahi dake jin zuciyar ta na cuskunewa ta fashe da wani sabon kukan har lkcn jikinta na rawa don ba karamin tsurewa takeyi idan yana taba ba, ta kusa awa daya tana abu daya sanann ta mike da kyar ta gyara jikinta ta dauki wani towel din ta daura ta fito cikin dakinta a sanyaye

rigar baccinta odd grey kawai ta zura ta kwanta kan gadonta a hankali tunani kala kala na mata yawo a ka,to wai me yake nufi da abubuwan dayake mata..

Batayi nisa cikin wannan tunanin ba junnut ta fado mata,atake ta mike da sauri daga kwancen data ke waje ta nema ta zauna ta rafka tagumi tana tuno da cewa yau ma kwata kwata junnut bata bar kofar ta abude ba bare ma taje suyi maganan 

Tun ranar Zuciyar ta ke dunkule dawannan azaban damuwar amma su big sis subaya da aunt murja gaba daya sunki su bata lokacin saka damuwa aranta

Sukam dagewa sukayi Suna ta shirye shiryen su kamar basu san me ake ciki ba.

Kaamil ma anashi bangaren yna ta kai kawo,in 14daya za yi hidamar amma sabida wani kasaitacciyar shirin da akeyi ma bikin yasa ba tsaida rana guda ba har yanzu.

Hjy indirah ta dade tana tsabgogin su na manyan mata
,agoben ake saka ran karban bakin ta tun daga maiduguri masu gyara taste din amarya
masu gyaran jikin ta ma larabawan sudan ne

Duk an gama tsara komai,site guda aka ware out side the main mansion,anyi ma hall din kwalliya da soft traditional couchs،.,lush leather cushions da irin tambarin zaman amaren nan na garjajiya mai kaman trow pillow round and tufted daga ganin nasu kasan mai tsada ne sosai,ko ina awajen an sakaya shi da kwalliyar gold da pepper red drape curtains

..5 days akasa wanda za dauka ana decorating dakin da zaayi gyaran amaryan wanda ahalin yanzu ya fara kintsuwa matuka tamkar anan zaayi hidiman bikin mai gaba daya.

Fannin jahan Aarah da dilshad kuwa babu abunda basu ce ba,sai dai basu fitowa fili suyi magana a sirrince suke hada makarkashiyar su.

..sun fi kowa tsanar auren,kuma sun tsani bahiyya matuka amma a fili sai suke nuna ma kowa sune akan gaba da komai kuma sunfi iko da saood ko dan su jahan suji haushi

Toh Daga jiya zuwa yau Tasan ayanzu junnut tana cikin wani hali dan haka
Bata son cika damun ta sai dai ta sai maasu aiki suna duba ta suna gaya mata halin da take ciki.

So take sai junnut tayi sanyi kafin taje mata,tasan suna da kishi sosai,so is not advisable taje mata da shawarwarin da take sakawa aranta har sai ta dawo hayyacin ta.

Bahi na tashi da asuba ta nufi windown site din gym dinsa don ganin ko ya dawo amma bata ga alaman haka ba, ta tabe baki ta koma tayi kwanciyarta don ba sallah take ba.

After 25minute  tana na kwance n tana tunanin ko me ya hana junnut zuwa mata har yanzu,nan taji an bude kofarta ta Mike da sauri don tasan ita kadai ce a site din..ya tsaya daga bakin kofar fuskarsa a dan daure yana kallonta,

kasa kallonsa tayi ta koma tayi kwanciyar ta ta juya masa baya,jin takunsa cikin dakin yasa ta kuma mikewa xaune da sauri kamar xata yi kuka tana kallonsa,

ya balla mata harara yace "tashi ki dauko hijab din ki"

mikewa tayi a hankli fuskar ta daure ta bude wardrobe dinta ta ciro hijab ta saka, karasowa kusa da ita yyi yana mata mugun kallo,"gaban su dad zamuje zaayi miki tambaya saura naji kina maimaita abunda kikace ma mum jiya..

Kawai gyada mashi kai tayi a tsorace dan tun jiyar daman take jin shakkun shi.

Sai suka fita Yana gaba tana biye da shi,bayan ya gaida iyayen nasu itama ta zauna...,kaamil ne yayi sallama ya shigo shima.

Dad ure needed urgently ...alhj hamood ya kalle jahan yace ok carry on,duk abunda suka yanke sai a sanar dani...

Hakan ya dada sa gaban khal ya fadi amma sai ya matse ya hade rai yana saurar yaji me za'ace

Jahan tace kaaamil nemi waje ka zauna kai zakayi mana shaida..

Ya nemi waje shikam,yana ta satan kallon bahiyya.

da suka hade ido,wani Murmushi suka sakar ma juna sunyi kifi kifi suna comunicating da idanun su

Nan jahan ta shiga tambayar bahiyya ko tana so ta cigaba da zaman auren..

Tace kwana kadan ya rage a yi hidimar, kinga tun kafin iyayennku sugama riritawa is better ku yi magana daya sai ayi ta ta kare.

Khal ne ya fara magana cewar sa shi yana son auren sa
..thou bayadda suka so ya fada ba ya fada..shi sam baiya don cika sauke kansa

Bahi ta maida kai kasa,tayi ajiyan numfashi...

Cikin sanyin murya tace mum,ai nagaya maki nikam bana so..ta turo baki

Jahan taji wani iri aranta amma ta fuske tace ok noor di na
..tunda baki so Allah ya kawo wanda ya dai dai Kwanan nan sai ayi naki bikin ko?

Ta gyada kai a slow...jahan tace hope is soon dan bana son ki zauna hakan nan..bahi tayi saurin gyada kai

...khal kallon su yake amma aranshi ya gama jin kamar ya shakure su...

Dai dai nan aunt murja ta shigo da tsokonar ta,da dai bata san kan maganan ba kaamil ya shafa mata a kunne,khal ne cikin su ya tsime baya cewa uffan bai cika daga kai ba,hirar bahi da jaahan na mugun kona shi..ga nan kaamil da aunt murja sun fara wani irin annoying site talks agefen sa suna yi suna matse dariyar su,aunt murja tayi gyaran murya,.Kamar bata san da shi "mum,ashe noor ba rabon Aaban bane..

To mudai bazamu yarda abawa bare ba  Kawai ayi
Yar gida tunda second angon yana shirye

..kaamil dauke kai yayi kamar anbarshi a duhu bayan shirya hakan sukayi yanzun nan..

Ayayin da jahan ta kalle su kaamil ya kashe ma bahii ido..Cike da mamaki jahan tace
Second angon?..

Aina kenan,..khal ya dada daure fuskan sa sosai kamar zai fashe...

Aunt murja tace mum baki sani ba?

Ai abun dayasa ni baxan damu ba sabida na hango fa kamar angon namu agidan nan yake

..jahan tace nonsense bana son maganan banza

...tace ohhh mumy what if bahi rabon kaamil ne..ai sun dace ko

Tsaki mai sauti ya kufce ma khal,...
Dukan su sun sha mamaki

Nidai ayi araba auren nan noor nake so nagani cikin sabon kayan auren ta
...ko bahaka ba noor?

bahi ta dago da murmushin ban mamaki tana washe baki..suna tayi

nothing is funny  akan fuskan saood,mikewa yayi yabar wajen a sadade,...

jahan tana binsu da kallon tuhuma...

Dariya kaamil yayi yace mum wallhy wasa take miki..

Jahan tayi scolding dinsu,hira mai dadin gaske sukayi kan bahiyya na kafar jahan tana lailaya ta cike da nuna mata gata.

Anan Har ta gaji ta barsu ta nufi site din junnut,bata fasa ba lallai tana so su fahince juna..

Site din ya dau wani shiruu na ban mamaki isar ta bakin door iya bugawa tayi amma babu wanda ya bude mata kofar
Haka ta gaji ta fice daga site din mai gaba daya

Saood Shikadai yake tafiya yana zaga saman benen site dinsa ranshi a matukar bace..

This girl is jokin with me

Wai ni zata rinka juyawa?

God pls me zanyi mata tasan ina son zama da ita har abada?
This is geting serious,bazan iya jure wannan wasan ba..

Brother?...

Muryan subaya ya dakatar da shi daga tunanin shi,sai ya wani lumshe idon sa ya sake budewa kafin ya juyo...

Subaya Tana tahowa tana magana

"What is wrong?...ya naga ranka abace"

Yayi furzan iska,duk tashin hankali ya nuna a idanun shi

Huhhh,i dont know,nidai nasan Duk laifin ki ne Subaya,..

ure very close to her amma baki ko gaya mata abun daya dace.
..,kinaji ta hada kai da mum xata raba auren nan u kept quiet wai sau nawa zan bada hakurin ne?

Subaya ta sa fuskan tausayi

"Khal..pls calm down..
Akan bahiyyar me kake daga hankali ?Ta fada da sautin damuwa tana matsowa kusa sosai
..yace ni Kar ki fada min haka..kinsan  ina son ta and right now cewa take bata son zama dani,and mum is on it..ya kuke son nayi?

Tayi sauri ta dafo shi,Khal pls listen ka kwantar da hankalin ka..ni wallhy bansani ba ma.
Bahiyya ce take cewa araba auren ku.?

Ya ja tsaki Msssw..yana mai dafa balcony da palms dinsa yana wani irin sassanyar hushi

He is really anoyed,bari ma yanzun daya hango aunt murja tana shigowa site dinsa

Sai Ya juya ya kalle subaya
Da Allah ki fita..wai ina masu aikin gidan nan..dint i said kar ana barin kowa yama zuwan min site..

Bunch of nuisance.

pls leave..
Kije subaya ni nafasa maganan dake.

Aunt murjan ta san duk da ita yake mitan nashi,bata fasa ba kuwa sanda ta iso har gabansa tana kallon yadda bacin ran nashi yayi affecting mood din subaya.

Tayi tsuka..

..Aaban wai meye wulakanci dan zaka rabu da matar ka shine kake sauke ma kowa

Ya bata ransa sosai,ta lura idanun sa na neman sauya kala yaki kulata baice mata uffam ba

"Ohon maka,yarinya is already making arrangement for her future auren soyayya..kinaji kuwa subaya,?

bahiyyan ma tace kaaamil ne next angon namu..i know thy wll look so cute together, kinsan kaaamil fa dan duniya ne,gashi hot guy ga sense of humour,a yadda noor take danye sharr ai idan akayi hadin nan kuma sai anga abun da ya nade ma buzu nadi.

Yake kawai Subaya tayi,cos taga yadda bro din ta ya tsume

A sadade tace,bahi da kaamil sharp sharp haka

Ant murja na satan kallon shi tace eh mana,..wai me zaa jira abu a gida?

before she realise khal ya kama hanyan sauka kasa yabi ta step dawowar sa ke da wuya sukaga security har biyu abayan shi,ya tsaya agefe ya dake ya hade rai..

"Show them the way..

Aunt murja ta kalle shi tana sallamewa Aaban?meyayi zafi

Bai ko kalle su ba

Subaya ta kama hannun aunt murja dake tambayar shin sikinini tace ant mutafi kawai,dan mood dinshin ya fara bata tsoro

Security sunsa su agaba aunt murja ta watsa masa hararar oho dai

Tace To muntafi..ta tsokane shi
..bazakace min gudnite bane bani na kar xomo ba rataya akaban

"Just leave me alone murja
..iskancin banza kawai.

Murmushin data sakar masa ya dada kular da shi. Ba sani ba sabo ya sa aka musu jagora har waje kafin nan ya wuce dakin sa..

Anan ma kasa xama yayi,ya juya wayar sa yafi sau goma amma ya rasa wanda zai kira ya gaya masa kalma daya mai dadi.

Wai kaamil take so?hmm msw
..kaaamil din ya kira atake..cikin mintina goma kaamil ya bude kofar ya shigo

Bro u called?

Khal ya juyo ya kalle shi babu sauki..

Yess,wai menake ji kuke fada daxu..

Kaaamil ya dan shashantar da fuskan sa alaman what? irin baima
fahimce shin nan

"Zaka maida ni abokin wasan kane..She is still married to me...can u ppl just respect that

Kaamil sai yayi shiru ya nitsu dan da fusata khal ya fadi maganan

Bro..nifa bance komai azancen nan ba..cupcake ce take ce musu wai ni take so

Cup what?

Cikin wata dalakkiyar murya yace ma kaamil din

Kaamil yana sosa gefen kunnen sa yace cup..ca...ke

"Wani banzan suna ne wannan? will u get out?"

"Im sorry..kaamil ya furta da sauri yana satan kallon shi

'out...ya masa nuni da kofa sai ya fita abunshi

Murmushi kaamil yayi yana dariyar sa aransa.

Aranar gaba daya khaldun bai gane komai ba,bahiyya tunda taji ant murja tana mita akan abin daya musu sai ta shafa ma kanta ruwa bata je site din ba

..kin shigowa part dinsun tayi har dare gashi bata ganin hilda ma bare junnut

Yau kwana biyu kenan amma har yanzu basu hadu ba

Wajejen 9pm khal bai dawo ba,gashi yau hjy indrah tana less busy,about gyaran jikin amarya da xaa fara mata a goben sai hjy ta kora ta dakin mijin ta tace maza kije ki kwanta danki tashi da wuri

Haka ta ja kafar ta zuwa dakinsa tana yi tana leke

Tana ganin baiya nan kuwa tayi sauri ta kimtsa ta lume kan gadon sa nan da nan bacci ya kuma dauketa.

Karfe biyu saura na daren Khal ya shigo dakin,kallo daya yayi mata ya dauke kansa ya kulle dakin da key sanann ya nufi inda wayarsa ya ke ya dauka ya ajiye gaban mirror,nan ya kashe wutan dakin yayi kwanciyarsa can nesa da ita,juyi yake yana lazy turns sam ya kasa samun bacci,yau anci kwana daya saura kwana biyu,bayan minti talatin da kwanciyar sa ya ga sai juye juye take, juyawa yayi yana ta kallonta can ya dauke kansa yayi tsuka,..

Ganin ta mike xaune yasa ya kuma juyawa yana kallon ta, kokarin sauka ta shiga yi daga kan gadon ya kunna bedside lamp yace "me ya faru" banxa tayi masa ta mike ta nufi bathroom din da ke dakin,yayi tsaki ya kashe wutan da ya kunna

ko da ta fito yana kallonta ta nufi kofa kamar zata fita sai ta ji kofar a rufe da key, ta juya tana kallonsa kamar mai shirin yi masa kuka, can dai ta ja dogon tsaki kasar wuyan ta tana hararansa,

A kasan tiles din dakin ta dawo ta kwanta shi dai bai ce mata ci kanki ba sai rufe kansa da bargo da yayi...

Ko da ya tashi da asuba kan gado ya ganta kwance yayi kwafa ya mike ya shiga bathroom don yin alwala.

Karfe bakwai na safe khal ya fito daga wanka yana goge jikinsa da karamin body towel.

idonsa ne ya sauka kan bahiyya dake kwance hankalinta kwance tana bacci.

still yayi yana kallonta,aranshi jiyake kamar bai taba lura da irin hasken fatar ta ba sai yanxu don fara ce sosai bahiyya kamar wata balarabiyar egypt,

kan kafafuwanta da laps dinta masu daukan hankali ya kuma sauke idonsa,

Alokacin bata da maraba da tsaraici  don tuni gown dinn dake jikinta ya tattare sama ya kama gabansa.

wani kasala ce ta saukan Mai a lokacin sai ya karaso kusa da gadon ba tare da yasan yayi hakan ba

har lkcn idonsa na kan cinyoyinta, a hankali ya kuma sauke idonsa kan kirjinta yana kallon abinda ya kuma girgixa shi,tubarkallh.. kadai ya iya furtawa a zuciyarsa ba tare da ya ma san yayi hakan ba, yar rigar baccin dama silk ne kalar ruwan powder ya bi jikinta sosai ya maya dasss mai bra ne yayi mugun haska fatan ta.

karasa wa yayi kamar wani Mara lfya ya duka dai dai kusa da ita yana kallon kyakkyawan gentle face dinta da picht lips dinta da bata cika masa kwalliya ba

hannun shi ya daura a hankali kan kirjinta yana shafa wa,wani irin shock ya ji ya ziyarce shi

Sai ya mike da sauri kamar wanda ya tuna abu ya bar wajen bai kuma kallon inda take ba, ko minti goma cikakke ba ayi ba ya gama shiryawa ya dauki wayar sa ya fice daga dakin kamar ana hankada sa.

Akan gabar sa na zuwa fadar sarauniya dilshad suka ci karo da hilda ta dawo amma jakar ta ne kawai a hanun ta,wani kallo ta bishi da shi ya hade rai ya dauke kansa ya wuce baice mata uffan ba,shi dama inba dan junnut ba hanya ma bazai hadashi da kalar ta ba.

Tana isa ta sa key ta shiga dakin junnut,babe?..ta fada a slow tana aje jakar tan akasa

kallon inda junnut tayi fayau babu ko make up afuskan ta take abun ya so ya daga mata hankali

"Hilda...har kin dawo din kenan..

Hilda ta gyada mata kai slightly suka rungume juna.

Omg jay take it easy mana..kin ganki kuwa?

wani sauya mood din fuska junnut tayi tace

Pls Me ake ciki..mkinsan na matsu kuma kinje kinki dawowa,ur call arent even going

Hilda tace I know..matsala aka samu..

Wai priest din ya tafi holi a wani kauye..i have to follow him up wallhy na ji jiki

Ok Sorry..
To me yace?..auren xai rabu...?

Rau da ido hilda tayi  tana dan jan jikin ta,

Junnuut nagaji bari mana na huta

"Noo pls don tell me that,executive flight kika bi bawani gajiya ajikn ki

Hilda Cant yu see how eager i am,Tun tafiyar ki ban ko fita ba im here waiting on u..i just want to know..auren nan zai rabu ko bazai rabu ba? Take hawaye suka cicciko idanun ta kallo daya zaka mata kasan tana cikon damuwa

'Junnut...its ok muzauna toh Hilda Ta riko ta suka zauna daga gefen gado

"Babe kin tuna wance akace mana wai tana cikin zuciyar shi?

Junnut tace Yesss...what abt ha

"To ai itace bahiyya..

cike da mamaki junnut tace wat?

" tabe baki hikda tayi tace
Gaskiyar dai kenan priest yace auren babu rabuwa amma u can rift them apart if u want

"Rift?..,but How...ta fada kamar zatayi ma hildan kuka

Hilda ya harare ya To ai kece baki son kiga laifin ta.
Junnut Dole ne fa ki mance
Da kawancen nan naki kiyi abunda zai ficce ki

..ko priest yace ta fannnin khal kam baxaki ci nasara ba

But muddin kikayo kokari fannin kawar ki zakai iya raba su
 
Wasu zafafan tears din kunci suka zubo kan fuskan Junnut tayi shiru batace uffan ba..

Hilda Ta jawo jakar
Ta ta fito da wasu kulli gida biyu..

Ki saka su a ruwa kisha..u need to fight for what u want  naga kamar kanki kike son kashewa akansu

A sadade junnut ta karba ta riko kullin a hanu tayi kusan mintuna goma tana shiru

sai can tace ince dai in nasha bazai cutar da bahiyya ba?

Tsaki mai sauti hilda tayi,zata mike  ta riko ta da sauri

..tace pls wait..
Kingane ko hilda ?
Ina son su rabu ne kawai amma bana son wani abu ya same bahiyya ...i cant do that im serious

"Ashe baki son zaman gidan saood kenan"..
A masife hilda ta tsawatar

..wannan magani ma kaifin baki ne kawai..Is just For u to have luck and confidence,priest yace ai solution din na hannun kine kuma na fada maki
Ki tashi tsaye akan kawar ki

Tsaye junnut ta mike tsaban damuwa har jikin ta na rawa

'Hilda to ni mezan yi ma bahiyya ta bar min saood ne..

"Its simple,Ok bari na baki shawara
Bakuna son juna ba?Why not you start by emotionally blackmailing her.

Ki gaya mata ta bar maki shi,cooked up some words masu zafi aike kinsan ta fiye dani ko,?..kinga akwai lokaci yanzu tun kafin ace zaayi renewing auren wallhy komai zaiyi maki wuya

Jiki asanyaye Junnut Tace ok..yaushe zanyi hakan..ko
Lets go now ne?..

Cike da mamaki hilda tace now?

Tace ok no not..now
Kiyi refreshing
Zanje na same shi.

Daga nan ta kimtsa ta fito Ta fice luckly enough tajiyo muryansa acikin faloun jahan khatun

Discussing weding preparation din sukeyi,ta fito da wasu mahaukatan weding planning album tana nuna mashi irin yadda  take shirin tsara hidiman bikn auren sa

Junnut tun daga door ta kare musu kallon bacin rai da  rainin hankali,ayanzu har haushin jahan khatun take data bada hankalin ta har haka,worst part taga shima khal har yana bada nashi view din alaman yana son abun sosai.

Wani Daure fuska tayi ta shigo cikin su ba sallama ta harde hanun ta ta tsaya

Shidai sam baya son wannan dabiar nata

jahan khatun bata tsawatar mata ba sai tayi kokrin lailaiyata tana jin bakin ta salon inda xata cusa ma saood wani abu aranshi ..

Jahan K tana so lallai tanuna ma saood tana son shi in all situation

Ayanzu so take ta gwada masa komai ba komai ba ne har awajen junnut ma

Junnut kamTaki sake jikin ta sam..basar da ita dayayi ya dada sa idanun ta suka ciccciko da ruwa

Sigar munafurci jahan ta jawo ta tace zo kiga weding choices din prince,.. wai ke wani kaya xaki sa ne..

Junnut ta bata rai ta hade hannun ta batace uffan ba

Jahan ta wani tabe bakin kamar bata san metake ba

Khal?u dint say anything....
"to junnut" din ne bata karasa ba ya dago ya kalle ta suka hade ido..few second ya kau da kansa

"Mum am leaving dama nazo na dubaki..

Ya mike yana gyara zaman rigar sa

Jahan ta masa ido alaman not now,sai ya koma ya zauna

'Tayi sauri ta juya kan junnut ta riko tana zaunar da ita kusa dashi,Ohhh my gosh baby am so sorrry jikin ne,?kwana biyu naji ance baki iya fitowa ba ko?..

R u alright ne..junnut kamar zatayi kuka tayi shiru tana kallon jahan

Aka bar khal da kallon su duka yana mamakin abunda kunnen shi yaji na cewa kwana biyu junnut bata fito ba

Jahan ta shiga mata waaxin munfrci agabansa kamar da gaske.

" kowa dai yana kishin nan, ai sai kiyi hakuri dama shi babba juji ne..

Have u guys spoken yet?

Akan shi ta maida tanbayar direct sai

Ya dago yace no maam.

Jahan tace ok my boy U shud...

Baima amsa ba ya dan tsime,Ganin bai cika kulawa da talks din su ba ran junnut sai ya fada harxuka

Ta lura tun daya zauna ya jawo album din duk hankalin sa nakan weding plans dinsa

Cikin sauki Junnnut sai ta zame jiki ta fita ta basu waje.

***

Wajejen 8 na dare suka fito ita da hilda
Tafiya suke,har yanzu junnut tana complain yadda khal ya nuna rashin damuwar sa akan halin data ke ciki

Hilda tace sai kiyi tayi ai an angaya maki dama shine matsalar...wajen kawar kin nan kawai xaki iya samun sauki gwara ma ki dage

Har suka iso site din bakowa,dan yau anyi ma bahiyya wankan lalle basu ma shigo ba tukun

Sukayi knock shiru sai ta aika aka kirawo mata ita,ita kuwa bahi jin ance junnut ne tazo bahi sanda tayi hamdala gudu gudu ta iso tana murmushi.

.cikin ranta ta c ai dama nasan junnut bazatayi fishi da ni ba

Ta shigo dakin da sallama basu amsa ba, ba damuwar ta kallon da hilda tayi mata bada sauri tayi hugging junnut kamar wacce tayo shekara guda basu ga juna

Junnut dake jin dumin kawarta tuni ta lumshe ido,ta dago ta suka kalle juna..bahi ta dan maraice fuska tace
Junnut...

"Daurewa tayi ta tsare ta tace Wait bahi...nifa ba wai nazo muyi dogon magana bane

Bahi bataji dadin cewar ta hakan ba amma ta daga kai tace ok..meyafaru kuma

'Waje junnut ta nema ta zauna tana sake boyayyan ajiyan zuciya.

Bahi kin bani mamaki da kika boye min kina da auren saood..

Buts it ok..nasan ba lallai matsayi na ya cigaba da zama kamar na da chan a zuciyar ki ba.

bahi tace
"Junnut kar kice min haka..wallhy keta daban ne a raina

"Really..shine dan kin aure min miji kike min karya?..can u prove it now?

'Bahi tayi rau da ido..dawowa gaban junnut tayi ta risuna ta fara mata magana a nitse

"Auren a kwana daya aka shirya shi akayi shi washe gari muka zo nan garin dashi kin manta ne,thats the same day we reunite.

Junnut ban boye maki auren nan da wani nufi

"Karya ne
Ta harare ta azafafe
..stop lying baki da dalilin cewa hakan

Bahiyya nina sanki kuma kema kinsan ni,In har akwai soyayyar da kikai min da da bazaki samu dalilin boye min komai ba

Bahiyya ta sauke ajiyar zuciya 'Ok fine.. junnut na karbi laifin toh ki gaya maki kiyi hakuri..What wil i do to amend..

Junnut tayi shiru ta bata rai kamar dai tana jin nauyin furta kalamam ta..

Bahi ta dan riiiko hanun ta"junnut pls we cant go on a hakan wallhy bana jin dadi

Wani kukan munafurci junnut ta fashe da shi tace wallhy Karya kike min bahiyya .

"Bahi tace haba junnut..kiyii min adalci ki fahimce maganan nan

"In fahimce magana?bayan kinsan auren saood buri na ne?
..he is first class brigadier general kinsan da haka?

,kwanan nan zai zama babban general mai stars sai muyi aure da shi
..yanzu gashi kinzo ki bata min rayuwa da karyan ki

Ni ban yarda ba wani uzurin banza kenan?kodai kina so ki raba ni da abunda nake buri ...who else know that inada burin auren babban sojan in bake ba.

Bahi tayi shiru idanun ta sun tara kwalla sai kallon bakin junnut take alaman Maganan ya bata mata rai sosai...

Tayi hakuri dai ta danne zuciyar ta ta numfasa

"Me kike so nayi miki dan ki yarda dani akan maganan nan Junnut ?.

"Bahiyya Ki bar min shi... Junnut tayi saurin cewa

Jin hakn yasa Bahi ta dago Atake  tace in bar maki shi?akan me..whts the point

Gaskiya i cant...aure ke tsakani na dashi bani da ikon yin hakan

" Hilda ta kada kafa tace hmmmmm tabbbbb

'Junnut ta sha mamkin yadda bahi tayi maganan zafafe ta mike tsaye har tana tsuma,U cant?Ohho, ai dama na fada i will be wasting my time here

Bahi ta daure ta sha gaban ta"Listen junnut.. ta riko hannayen ta jikin ta har na rawa..

"Nasan ban kyauta ba daban gaya maki auren ba,amma beliv me bani da niyyar cutar dake..

Righ now I cannot leave khaldun for anything,ko da kuwa kece.

sabida shiya aure ni bani na aure shi ba..Shiya ke da ikon rabuwa dani a lokacin dayake so.

Nidai So nake ki fahimce ni,tunda Ni dake mun san kan mu.

Why not ki bar maganan burin kin nan kiyi auren ayanzu...

I mean sai ahada preparation din auren mu mai gaba daya that way we have him both

Noooo..

Junnut ta ce da wani gigitaccen murya tana wasu ruwan hawayen dacin rai azafefe

We cant have him both..

Bani da burin zama da kishiya Not u not any girl,I want him alone.

  in zaki barmin shi ki barmin shi idan baxaji barmin shi kawai ki fito fili ki fada min dan nasan matsayi na awajen ki yanzu.

Bahi dake jin kamar kirjin ta xai fashe saboda zafi cikin sautin maraitaccen kuka tace Junnut dan Allah ki bar wannan shirmen

...Hakan kawai shine mafita .

Wallhy baxan takura maki ke da shi ba
Ayi auren nan zaifi mana sauki.

" baxa ayi ba,,Cike da gadara da zafin rai junnut ta hayyayko gaban fuskan ta

'Baxaki barmin shi din ba?

Bahi ta dago cike da taro natsuwar ta ta goge tears din ta,..suna kallon juna

Tayi ajiyan zuciya mai cike da sanyin jiki Tace

"Junnut i cant. .kiyi hakuri..kije kiyi tunani akan abunda na fada maki

Kema kinsani Zaki iya cigaba da studies dinki in anyi auren..

tunda ayanzu baxaki fahimce ni ba ayi ta takare kawai

"Wani tasssss ta suke ma bahi a fuska ta wani hayyako cikin fusata kamar zata shakure ta

Mani kike gaya wa haka bahi..kikace Nabar burin rayuwata nayi miki aure?

Ahh i shud known  ido na ya rufe da ban dago cewa tuntuni buri na kike son ruguza min ba

Bahi ta dafe kuncin ta tana hawaye batace uffan ba

Hilda tazo ta janye junnut dake kukan bacin rai tana maganganu ,atake suka fice a dakin fuuu kamar mahauka.
Follow @SURAYYAHMS
SURAYYAHMS

Share with ur friends
💋keep sharing ur points

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top