Chapter35
_Monday/11/019_
_3⃣5⃣-Tort♡._
Bayan angama case a kotu atare suka dawo gidan gaba dayan su da sharadin bazasu bude maganan ma kowa.
Jikin kaaamil nee ya tsanan ta,da alaman high fever ke damun shi dan babu abunda yake yi sai surutai yana kiraye kirayen sunan bahiyya.
Fannin jahan khatun kuwa Banda bacin ran halin da kaamil yake ciki ji take kamar zatayi hauka jin ance jahan Aarah ta iso gidan..
Sukam da suka iso gidan a site din su hjy indirah suka yada da zango,.
Khaldun dake jin kanshi daban yau duk sai ya rasa ta inda zai fara gyaro ta da bahiyyar sa,hira kadan yayi da su ya fice baima san meke faruwa a fannin su kaamil ba..
bayan fitar sa,jahan Aarah tace ma subaya kuje ku huta,nima zanzo namu shashin daga baya...ba laifi suka bar wajen su ukun bahiyya ta mata jagora har zuwa site din ta ant murja na biye da su suna ta hirar su abun sha'awa..
Acikin sirri jahan Aarah ta gaya ma hjy indirah duk abunda ake ciki,jiman tawa take yi sosai tana jin mamakin halin kirki irin na bahiyya sai ga alhaj hamood ya shigo..yayi musu sallama yace Aara,ashe kaamil ba lpya..yakamata muje ku duba shi
.. dama ita kam bataje ta gaishe da dilshad ba,jin ance kaamil na kwance yasa suka debe jiki ita da hjy indiran suka nufi wajen san atake..
Sarauniya Dilshad da ahalin ta duka suna cikin dakin..
Daga yin sallamar su jahan Aarah tuni iskan wajen ya sauya tsari,Wani kallon banza aka watsa ma juna
kasan ido jahan Khatun ke duban su daya bayan daya acikin wuya take ansa gaisuwar jahan Aarah..
Jahn Aarah tayi kamar bata san ma tanayi ba ta haishe da sarauniya dilshad bayabo ba fallasa ta amsa tana mata sannu da zuwa..
"Kaaamil?...Ya jikin ka...Very soft nd calm take shafa kanshi tana duban shi da kulawa..,har cikin ranta take kaunar sa as much as yadda take son danta saood,jikin sa yayi zafi sosai har jira ake yadan sassauta kafin doc ya shigo ya masa Allura..hjy indirah tace meke da munshi babu wanda ya ansa ta atake ta juya ta sauke haushin hakan akan su hilda da junnut da suka ki ficewa su basu wuri..
Tace wai ku bakusan manyan ku ba?..maza ku fice ku bamu wuri..
Tsuliya azage suka fita sum sum kamar yan matan bin kida basu ma gaida kowa ba.
Tuni Jahan K ta bata ranta ta fara kukuni,tace ciwon maita aka laka mashi,...
ina zaman zaman na ankawo ni wata kasa marar dadi daga yau wannan yaxo maka gida sai gobe wannan yazo
..rabon kaamil da yayi ciwo yana kame kamen suna tun da chan da aka saka min ido a persia..ko Mena tsare ma mutane oho
Har ta gama mitan ta babu wanda ya daga kai ya dube ta
hjiya indirah ta budi baki kenan alhaj hamood yayi gyaran murya cikin nitsuwa yayi maganan sa...jahan Aarah kam duk hankalin ta nakan kaamil don batace musu uffan ba matar tana da tausayi sosai..
Jahan khatun kuwa ba dan jan numfashi sai ta shiga fetsa magana tana cewa mayya aka kawo gidan ta...ita so take a kore bahiyya ta ko sa ma ta bar mata gida..tun abun na wasa har maganan dai ya dawo babba awajen hjy indirah
Ranta ya baci bataji dadi ba, .tace way shin wacece mayyar,?bahiyyan ce mayya koko wata daban?..ai naga duk yaran ki ne agidan nan,cin maita kuma ai sai tsoffi...
Sarauniya dilshad ta kalle hjy indirah da wani irin sigar baraxana..bata kula ta ba itama ta bata rai abun ta
alhj cikin rashin jin dadi yace dan Allah ya isa hakan nan abubuwa dayawa ne agaban mu
...da yaren su na persians dilshad Tace mashi ai tunda kaamil ya kwanta ba abunda yake cewa sai bahiyyya...
Yaya baza ace da ita mayya ba?
Cikin bacin rai hjy indirah tace to kenan ita tasa mashi ciwon dan gidan nan duk basu da idanun gani?
..normal high fever ke damun shi..,ta juya ta dube shi kaamil bayya ma jin su,tace to wllhy zaka ma warware ..
Jahan Khtun tace in be warware ba mu mun san me zamuyi,dan haka kowa ya jira yagani
..kuma kowa ya sani babu dana babu zaman waje guda da mayya
Jahan Aarah batace uffan ba har sanda taga hjy indirah ta kasa dena amsa su,.
wani haushin hjy indirahn su junnut sukeji dan basu tafi ba labewa sukayi abakin door suna eaves droping duk abunda akecewa suna so suji..
Gashi junnut din bata so tayi wani abu anan din, ai ance mata dayan matar itace jahan Aarah mahaifiyar husban tobe din ta wato khaldun..
Dilshad ta matsa tana son taji dalilin daya sa tagan su agidan,dan so take maza su tattara su tafi dan adena haniyar ma gaba dayan shi
Hakan datace sai ya ma jahan Aarah zafi..aganin ta tunda gidan na mijin su ne bai dace dilshad tana iko ba amma sanin halin ta yasa batace ufffan ba
Kamar kuwa tatabo ma Alhj hamood abunda yake masa kaikayi daurewa yayi yacire nauyi yace ma dilshad akwai muhimmiyar maganan dayasa su dole suka zo baki daya inta bashi dama xaiyi ta anan
Dilshad tace mashi tana jinshi ya fade ta
Kamar yadda ya saba,cikin ladabi da iya bayani...yace mata dama yazo ne ya gaya mata cewa qaddara tayi halin ta,aure ya shiga tsakanin yar rikon su bahiyya da khaldun sannan auren subaya ma ya lalace a yau kotu ta raba su.
Aure?...Wani dumm maganan ya doki kunnen su duka suka kalle shi with intense suprise
Ba dilshad ba har su junnut dake tsaye ji sukayi kamar an sauke musu bomb a kunne
,..khal ya aure bahi? Jin kafarta ya kasa daukar ta Junnut sai tayi luuiii da zata zube kasa..da sauri hilda ta riko hannun ta tana mata ido akan kar tayi reacting dan kar asan dasu.
..suna ji alhj yace ai dama ana yin auren ne suka taho abujan..
..Amma ga dalilin daya sa shi yace sujira shida kansa zai zo ya mata bayani,yace kiyi hakuri ur majest aure da mutuwa abu ne na ubangiji idan sunzo ba yadda dan adam zaiyu da shi,..yace indai akan auren saood da junnut ne to a shirye yake ya karbi duk wani zabin da sukayi ma dansa a kowani lokaci
..shidai fatan sa suyi hakuri suyi accepting wannan auren sabida abun da dansa ya nema daga gareshi kenan.
"Tun kafin ya gama suturta maganan Jahan khatun ta wani daka musu tsawa ta tuma tace wai menene kake cewa ne..?
"Wai mena keji ne hakan?Sa'ooddd din ne aka aura mashi wata na daban,da izinin uban waye..ta fada a mugun zafafe har tana tsumayi
wani asararren kallon banza hjy indirah ta bita dashi tace da izinin uwar sa da ubansa ince kin jini?...
Dilshad tayi sauri ta tsare su,tace dakata min...ni banji dadi ba sam,hamood ace ayadda nake da yaron nan har zaka masa mace bazaka jira inbada amincewa ta ba
Wannan yarinyar ?Ko ba itace kaaamil yake cewa yana so ba?...
Itace fa,. yes ur majesty ai itace ma mayyar..jahan khatun tayi blurting azafafe hankalin ta a matukar tashe
...hjy indirah tace ah a..kece mayyar dai khatun..daga yaro ya kamu da high fever sai alaka masa soyayya?nifa bangane muku ba ..ta juya tace hamood?kayi ma bakin matar ka linzami tafara wuce gona da iri
Jahan khatun to! tace daga fadan gaskiya?in karya nake akira ta aji meke tsakanin ta da dana...
Tsaki mai sauti hjy indirah ta sakw tace"..To yarinya dai da auren ta bawani kaamil din nan saood shine mijin ta na sunnah.
Sannan Bamu son maganan banza inkya nema ma danki hayakin tsoffin mayu...u better do that...
Can u excuse me?alokacin idanun ta sunyi tsaban bacin rai,Nan gida nane kisan agaban waye kike furta furucin ki..Wacece tsofuwar mayyar? .
Mikewa tsaye hjy tayi tace mayya kam ke kika sani ni bana tsoron uban kowa bare uwar sa,yarinya da aure akan ta,bazaki laka mata danki ba.
"Ko da ba auren ma Bata son shi..
baiyi mata..bahiyya Ahmad hamood saood sunan ta..
Gaba daya sai suka kule da furicin nata
..,nan wani zazzafan muhawara ya kaure akan kaaamil da bahiyya da kyar akayi setling zance tsakanin hjy indirah da jahan khatun as usual kowa cikin su ranshi abace ya koma ya zauna
...cike da saukar da kai alhj ya dada ba da sarauniya dilshad hakuri ya nuna mata lallai auren qaddararre
Bawai dan araina zabin ta ba
..abun ya mugun yi musu zafi... a very big blow to sarauniya dilshad
Tunda suke a duniyan su Alhaj hamood bai taba mata haka ba sai yau..
"...Anan bakin door Junnut tayi hawaye har ta gaji..hilda tayi tayi su bar bakin door inda suka labe sunajin sauran zancen amma tsaban firgici da tsananin kishi yasa junnut ta kame tana jin komai har iyayen su suka sauko suka warware maganan kuwa a tsanake
Bacin rai matuka ya bayyana kansa akan fuskan jahan khatun kamar itace junnut din da aka aure mata saurayi
...gashi gani take kamar ba ataba raina mahaifiyar ta kaman na yau ba...duk dama jahan Aarah bata tanka ba amma duk laifin akan ta suka sauke
Suka ce itace ta sa hakan ya faru,. ta juya kan miji dan ta nuna musu cewa ta isa da shi da kuma dan ta.
Cikin zuciyar jahan khatun Tace ai dama daga jin ance bahiyya yar rikon jahan Aarahn tasan bazai yuwa ta hada hanya da yarinyar ba
Kaamil tuni yayi bacci,dan surutun nasu bai amfane shi da komai ba
Da shike su dilshad din tsoffin mugaye ne kuma munafukai duk jani injaka da akayi akan maganan,daga bisani sai suka juya suka amshe sa hannu biyu sunayi dai suna batsarwa.
Sarauniya Dilshad tace toh dole ne asake yin bikin a idanun ta,tana so ayi musu royal wedding irin na al'adan su,biki take so ayi na dukiya da dukiya wanda zai sa kowa ya san dacewa dan su na farko wanda suke ji dashi shi yayi aure
...as for junnut sarauniya dilshad tayi nazari tace an tsayar da maganan akan sai ta gama schl za'a aura mashi ita as first but second wife..
A hakan aka bar zancen kowa ya watse naciki na ciki..
..,jahan khatun bata fasa mita da kananun magana ba, tana so ne ayi fitina sosai awajen hidiman bikin...burin ta ta nuna ma jahan Aarah cewa tafi ta iko da Saood din duk dama tasan ba danta bane.
tsaban fitina ta hana alhj hamood motsawa daga jikin su wai zasuyi discusing new royal weding date din babu bata lokaci
jahan Aarah kuwa ko ajikin ta suna fita suka koma site dinsu na asali dake chan dayan bangaren gefe da inda su hjy suka sauka.
A Cikin zuciyar Subaya tana famar da hrtbreak din abubuwan da ya faru da ita,amma bata cika nunawa badon komai ba sai dan taga farinciki akan fuskan bahiyya...ko aunt murja sanda ta shaida subaya sosai take son bahiyya...
Suna zaune suna hira,maid ta shigo tace ana kiran bahiyya ...dukan su ba tantama sun san khaldun ne..
Cikin ranta bata so taje ba amma sai Ta mike ta zari mayafin ta,tana fita kuwa suka yi gamowar kicibis da su hilda ta riko junnut riki riki a hannun kamar marar lpya tana lallabata tana fizgewa a zuciye..
..da sauri bahiyya ta iso gaban su zata rike junnut din itama musamman ganin guguwar bacin rai har da hawaye a idanun ta..cike da mamaki tace junnut lpya kuwa?
Junnut ta wani sauke numfashin fushi,Wani firigitaccen tsawar tsana hilda ta daka mata
..da Allah matsa
hang on...witch munafuka kawai
..muguwa azzaluma dont you dare touch her...ta bita da harara kamar idanun ta zai fado
Bahi ta tsaya galala tana kallon su xata sake budan baki kenan hilda ta wani ture ta gefe azafafe...cike da masifa tace
Yau Allah ya tuni asirin ki bakar muguwa mai fuska biyu..husband snacher..witch.
ran bahi ya baci matuka amma bata kula ta ba takai hannu zata taba junnut,..da mamakin ta sai taga junnut din ma ta wani irin bangaje ta,..cike sa mamaki tace junnut?tayi mata shiru ta wuce da sauri bata kulata ba kuka ta fashe dashi
..arude bahi tace junnut meyafaru
?..junn...hilda tsaki taja..da sauri
Bahiyya ta bi bayan junnut din tana shiga dakin ta same ta akan gado ta kife kanta da gwiwa tayi shiru tana hawaye
..tace junnut pls meyasame ki?
Nan hilda ta shigo itama ja tayi ta dora hannu a kirji daga bakin door tana duban su..
junnut am talking to u...dukawa kusa da ita bahi tayi kamar zata dago ta agaggauce ....a mugun fusace junnut ta mike tsaye batace uffan ba ta fixge zata bar mata dakin
Bahi ta riko arm din ta da sauri..Junnut meye hakan?
...meyasa bazaki ce min komai ba
Anan junnut ta juyo da wani irin bakin zuciya tana mai qasa mata harara tace ke din kinfada min komai ne da kika zo gidan na?
bahiyya meyasa zakiyi min karya..u lie to me..kin munafurce ni..
Wani rassss gaban bahi ya fadi,
munafurci?..har muryan ta na rawa tace wani karya nayi maki?ta dafa kafadun ta..junnut meke faruwa meya kawo wannan maganan
Ture ta hannyan tayi ta jiya tana share tears din ta....ba kin zabi ki munafurce ni ba ai saikije kiyi tayi
..niki fita min a daki na.
..daga nan
Tayi mata shiru,sai famar sharar hawayen takeyi ta hade ranta sosai,
Bahi ma shiru tayi kamar me nazari...sosai hankalin ta ya tashi idanun ta suka cicciko...tace junnut kema kinsan babu irin haka atsakanin mu..nayi maki laifi ne?dani dake munwuce shafin da zaki tsaya gaya min magana a cikin duhu..meye matsalar?
Junnut tana juyowa Wani tassss ta sauke akan fuskan bahiyya..
A mugun firgice bahi ta dafe kuncin ta
,...wasu hawayen bazata masu zafi su suka biyo..dukan su cikin su sai tsuma yake suna kallon kwayar idanun juna
..muryan ta na tawa tace menayi maki junnut ..
I said U lied to me. .cikin zafi da dacin rai junnut ta furta...
Ashe kin aure shi..?
miji na ne ni kadai kum nafda miki.. meyasa xaki aure shi sannan ki boye min?ashe haka kawancen yake
..nafada maki komai nawa amma da shike kin maida ni wawiya shine bazaki gaya min aure ne tsakanin ki da mijin da zai aure ni ba
..u make me look like a fool...cikin tsaban yanayin zafin kishi ta dada kawo hannu zata mare ta bahiyya tayi saurin riko ta jikin ta take yayi sanyi
...Adan firgice tace junnut pls..calm down junnut walhy wallhy ba abunda kike tunani bane
..ban boye maki dan na munafurce ki ba pls listen i wll explain... a tsawace junnut tace bana so keep ur freaking explanation to urself..shut up...ni babu abunda zaki ce min...u just ruined my hapinesss..ure stealing my deam
...ki fuce min a daki na.
"Junnut ...jun...bahi ta birkice tana rirriko ta tana ture ta,..kuka duka suma fashe da shi...junnut bazaki saurare ni ba?..
ni ki fice min..wallhy banson ganin ki..
Junnut m sorry pls listen
dadi abun yake ma hilda dake tsaye tsam tana kallon su...,bahi na hawaye junnut gaba daya kishi ya rufe mata ido taki saurarar komai...ni ki fice min...i said just get out ta jawo ta azafafe...har bakin door ta kai bahiyya ta tura ta rufe kofar,
wani kuka mai cin rai ta fashe dashi tana jin bahiyyar na bubbugawa tana neman gafarar ta tana kuka..
Ita kadai tasan kalar wutar dake ci aranta,agaskiyan magana shine yau da ace ba bahiyya bane ta aure saood..tana ganin zata iya daba mata wuka acikin tsaban kishin dayake damun ta ayanzu..
ya ma azaayi ace namijin data dade tana kiwon sa rana daya sai ace mata wata na daban ya aura?
Tana da tsananin kishin da tasan ba bahiyya ba koma waye ne muddin akan khal ne bazata iya ba.
Tana kuka,tana jimami hilda ta karaso kanta da maganganu,ai dama na fada maki..kece baki ganin halin yarinyar
Munafukace,gashi yanzu ta miki mai kankat ta aure shi, in har dama da gaskiya ta rike ki da tuni ta gaya maki cewa ta aure miki miji...
junnut dake jiyo kukan bahi abaki door wani toshe kunnuwan ta tayi cikin wani yanayi tace...hilda kidena cewa hakan pls
..bahiyya fa ba haka take ba...im just angry right now..meyasa bazata fada min ba ta barni a duhu suna min kallon shasha sha
... Ohho ashw kinsan ta maisa ki shashasha,shine har yanzu kike cewa ba haka take ba? Lallai ma junnut...ni wallhy inice mun rabu kenan har abada ..kuma wallhy bazata sha ta dadi,zaman auren nan sai ya mata daci
Noo...hilda namiji bazai raba ni da bahiyya ba
gAskiya bazan iya yi gaba da bahiyya ba...nasan tana so na..sosai. Kawai
i just dont understand why she hide things from me now ne,yanzu sikenan ta aure min shi?wani sautin kukan ta kara fashewa da shi tace wayyyo Allah na nashiga uku..wallhy bazan iya bar mata shi ba nevaaaaa ta wani zube akasa tana kokarin zata yi birgima
Dago ta hilda tayi tana rarrashin ta dan bakaramin azaban kishi ke nunawa akan fuskan junnut ba,sit pleas.. ta zaunar da ita akan gado red wine mai sanyi ta zuba a glass cup ta mika mata..ta karba ta sha..lumshe idanun ta tayi a slow ta mike kafafun ta akan gadon kamar wata marar lpy..
Lokacin bahiyya har ta gaji da knocking da magiya tayi shiru bayan ta jingine da door da shike ma bata jin su sosai idanun ta sunyi ja ta lumshe su..
Tana san budewa zata ja nunfashi,tun daga dayan benen tagano wulgawar jahan Aarah da subaya alaman suna tahowa zuwa site din kaamil
Hakan ya sa ta share hawayen ta da sauri ta shiga saukowa daga kan steps din dan ta bi bayan su dama itama bataje ba,.
Subaya ce dauke da dan madaidaicin tray an shake shi da almond crush salad totterlini,da banana smothie mai qamshin gaske,da sallamar su suka shigo dakin babu kowa shikadai ne akwance idanun sa a lumshe..isowar su ke dawo kowa ya nemi waje
Jin qamshin jikin Jahan a kusa da shi ya sa shi dawowa daga duniyar tunanin da yake yi na sabon bikin auren bahiyyar da dan uwansa dayaji dazu iyayen nasa sunata fada zaayi
,cike da nuna kulawa jahan ta dora lallausan hannun ta akan goshin sa ba aifi jikin sa ya warware sosai zazzabin ya sauka,da sassanyar murmushi ya bude idanun sa..wani tsaban tausayi da so irin na uwa yake iya gani cikin idanun jahan wanda ma baisan da shi ba...yadade da sanin yadda ta dauki khaldun haka ta dauke shi aranta
...,amma aransa ya sha cewa tafi kaunar sa fiye da mahaifiyar sa jahan khatun..muryansa adan dishe yace Ammah??..sai tayi murmuhi ta dago kanshi gently tana duban sa da kyau kamar wacce taga farin wata...wani sauke ajiyan zuciya yayi cike da kasaitaccen shagwaba..tace my khalbim, yaya jikin?...subaya ma aje try din tayi ta karaso,tace twinny..meye haka da ciwo..baice komai ba dan bai san sanda ya aje kansa akan kafar jahan ya riko yatsun ta kamar karamin yaro yana wasa da shi ba,yace amma nifa lpya ta lau naga kin daga hankalin ki..jiyan ne kawai zazzabi ya tasomin am very ok now..in kikace nayi maki gudu ma zanyi..jahan Aarah tayi murmushi mai sauti ta dada shafa kanshi,tana mai jin dadin kalamansa aranta adduan samun lpy ta dada mashi sannan tace Alhamdullhi toh...tashi kasa wani abu acikin ka...baiyi musu ba ya mike subaya ta mika mata tray din ta bude salad din ta fara bashi abaki gently yana karba,..
Tana ta kallon shi shikam wani sabon kwanciyar hankali da nitsuwa ke famar shigo masa,jahan tace kaamil
..son...wai menene nakeji ana cewa kana son matar dan uwan ka? Atake yaji wani rass azuciyar sa bai ma iya amsa taba sanda ya kurbe smoothien ya ji sanyi
..ya aje cup din Ahankali ya kalle ta tare da cewa Ammah karya ne..ni bance ina son ta ba,misunderstanding ne kawai dan anga mun saba da ita sosai...ai bro ya gaya min matar sa ce,ni wllhy bansan meyasa sunan ta ya fita abaki na da banda lpyan nan ba i ques sabida abunda sadat yayi mata ya bata min raine ammah dan Allah kar kiyi maganan nan ya shiga kunnen saood ni bana so ...
Kalaman nasa abun mamaki cos he look disturbed an seriouss at same time
..jahan tasauke ajiyan zuciya tana lura da yanayin sa wani kiss mai sanyi ta dora mashi asaman goshin sa
tace ai dama nasan bazakayi haka ba..i know my son nasan zuciyar ka dana"my king...my hero... my pride .tana murmushi taja cheeks din sa amicably...kaamil ji yake kamar tana warware masa kundun farinciki ne da kwanciyar hankali
..u most alwys be hapy kaji?...ina nan koba yanzu ba ka tabbata kana fada min duk wani matsalar ka,i will give anything dan kaji dadin rayuwar ka..babu abunda yafi min farin cikin ku muhimmanci
..ok?..rungume ta yayi ya wani lumshe ido..
Subaya ta ce yes twinny..noor ai kanwar mu ce kayi duk yadda kake so she is our family
..abunda sadat ya mata baiyi dai dai ba,nasan dole kaji zafin abun,na fahimce ka
Dan Nima hakan nakeji har yau..
..murmushi mai sauti yayi musu duka ya dada aje kansa jikin jahan tana shafa shi calmy yana sake ajiyan zuciya mai nauyi..he know he have to let go of bahiyya ko da karfin bala'i ne
,tsakanin shi da bahi is a forbideen love story....
hira ya sake sukeyi musamman akan sabon auren da ake cewa zaayi agidan ma bahi da saood
..subaya tana ta zumudin irin karain da zasuyi..kaaamil yana dada bada shawaran yadda zasuyi abun ya kawatar sosai..
Bahiyya ta dade abakin door tana jin su amma ta kasa shigowa bisa mamakin daya dulmuye ta najin abubuwan da kaamil ya ke fada tun dazu...
Bata taba ganin jan namiji irin kaaamil ba,sam bata san akwai masu kyakywar zuciya a duniya kamar nashi ba
..he is rough a yanayin tsarin rayuwar sa na bin mata,zuwa party da sauran su, a fili kwata kwata banda kyaun halittar sa sam he is not perfect
amma yau ta gane cewa zuciyar sa mai tsada ce matuka..
Hawayen ta ta share ta koma gefe cikin wani dan karamin palo ta zauna ita kadai,tana tuno da abubuwa uku..
Na farko junut ne na biyu kaamil na uku khaldun saood
..kowa tana tunanin sa extensively cike da kula da nitsuwar zuci..
ajiyan zuciya kawai takeyi kamar alkalin gaskiya kowa da inda ta aje shi...
Har su jahan suka bar shashen bata sani ba,chan data farga ta mike zata bar wajen tana fitowa suka yi ido hudu da khaldun yasha kananan kaya yayi kyau sosai..
Sanda ta Ta kare masa kallo
hannun damar sa rike da door handle alaman har yafito daga wajen kaamil din shima..,rufe door din yake zai bar wajen
Da suka hade ido tayi sauri ta sauke kan ta kasa bata sake fuskan ta ba..
Wani kallo mai sanyin yanayi yake bin hallitan ta dashi,..har ya matso kusa bata lura ba...
Daga in kike?..ta dan turo baki kamar bata son magana da shi tace"daki"
Dan kadan ya cije lips dinsa ya daga giran shi na dama yana ta satan kallon sunkuyyaen fuskanta
He missed her alot,..
,...yana ta so suyi magana a tsakanin su amma sai yaga har yanzu basu samu daman kebewa ba...Sai yace yanzu zakiyi naki gaisuwar?..ta yi masa shiru kamar bata ji ba...yayi ajiyan zuciya cikin daddadnan sanyin sautin murya yace
I want to talk to u...
Dazu na aika kizo baki zo ba
...sake door din yayi ya dada matsowa kusa da ita,with much nervousness a voice dinshi..yace
ummmmm ummm bahiyya..,..can we pls go for a date?tonite ..achan sama yayi.. pointing childishly da yatsun sa bata ko kalle shi ba...Same time..? zan tura maki sako awayar ki saiki bani amsa Daga nan yayi shiru dan baima san meya ke cewa ba but yasan dai abunda ke ranshi kenan...
duk nauyin fitar maganan abakinshi ya danne ya zuba mata ido kamar zuciyan sa ba bugawa yake yi da fargaba ba..
Taga bazata iya bata lokacin ta dashi ba a hankali ta furta ok..
looking cold and unhappy ta hade ranta ta wuce shi ta bude kofar dakin kaaamil din ta shiga ta rufe abun ta..
Yayi wani ajiyan zuciya Yace hmmmmm Kallo yabi door din dashi yayi kwafa .He is very sensitive about her hakan datayi ma ya taba shi,.sai dai baya so ya sake maimaita wani kuskure akan ta har abada,yasan tunda bahiyya tayi tunanin sadaukar da rayuwan ta akansa babu abunda zai saka mata dashi face ya bata dukkan yardan sa da dukkan kaunar sa
...,kuma yana so lallai yau ya nemi gafarar ta akan abubuwanda ya mata tun farkon haduwan su,a karshe yana so ya kuma bayyana mata sirrin dake ranshi,..
..yanzu yaji kaamil yace za asake musu aure
Yana so ne yayu amfani da wannan daman dan ya bata duk wani farincikin da zai iya goge mata duk wani ciwo azuciyar ta
...ayanzu ji yake babu abunda bazai iya bayarwa sabida farincikin ta ba
...damuwar sa ayanzu bai wuce su fahimci juna ba..
#SURAYYAHMS
Follow @surayyahms
VOTE AND SHARE STORY WITH UR FRIENDs....
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top