chapter33
_3⃣3⃣-Villain 1♡_
Sa'ood A Reality yake ganin komai agabansa amma Duk da haka sanda ya ga kamar a mafarki ne.
...a take idanun shi suka sauya kala suka dawo jajir,wani zazzafan huci ne yake taso masa tun daga kahon zuciyar sa mai zafi sai yakeji kamar ana hura masa wuta ne akansa..
"So this is the real truth?..toh meyasa bata fada min ba...meyasa bata fada ba, wani dunkule hannun shi yayi cikin tsananin radadin jin haushi..wani tasss kake ji a kasan floor na karar saukan wayar sa dayayi firo dashi baima sani ba.
Yau Bayan yaji mugayen boyayyun sirrikan sadat akan subaya,a Duka videos din dayake kallo na cin mutuncin da sadat yayi ma bahiyya yana razanata duk su suka fi komai tsuma shi
Aynzun ko daya baiyi tunanin zai bace a kwakwalwar shi ba har sai yaga ya rama mata..
Daga jin saukar numfashin sa zaka gane cewa Hankalin sa a matukar tashe yake,..biting his lips slowly ya cusa hannun shi cikin lallausan suman kanshi yana shafawa kamar me naxari.. She was my sis ..and now she is my bby my wife..
..tsikar jikin shi har harbawa suke suna tasowa.. a idanun shi yana imagining yanayin yadda zai cire ma sadat farinciki a rayuwar sa.
Duk da halin da subaya ke ciki nai hanasa karasa kallon videos din ba
He is very intelligent dan haka abubuwa dayawa sunzo mind dinshi a wannan lokaci
Wani dabara ne ya fado mashi dan yasan ba iyakar abun ba kenan"idan har wannan videos din agida ne gaban subaya to meke nan yake mata idan bata gidan?..wayar shi ya daga ya binciko tun sakon da da dija ta turo masa na rashin lpyar bahi, then he call the number amma sai yasmine ne ta dauka...
Yasmine Tasha mamakin data ji shine akan layi,but da shike baya cikin hankalin sa sosai so bai tsaye gaishe gaishe ba ya fara mata tambayoyi,ita kuwa bata bata lokaci ba ta gaya masa hakan yana faruwa a schl..ya lura she cant give all details sabida tana jin tsoro sai ya mata godiya ya katse wayar..
Subaya Tasha mamakin furucin yasmine dan tana jin duk tambayoyin sa da kuma amsar dayake samu..
...."yasmine ta basu hints,tun daga farkon bakin zaren ta kamo musu su kaji komai xuwa har lokacin da yake kiran bahi yake mata barazana kala kala agaban su.
Subaya bata dena nishi ba dan tayi kukan har ta gaji,ita aynzu ma dukiyar bai dame ta ba,abubuwan data gani bahiyya ta fuskan ta under her roof bata sani ba su suke zautar da ita..,a hankali cikin jimantawa take cewa ya cuce ni...sadat ya lalata min rayuwa ta..
Ta yaya zan kalle yarinyar nan...ashe har zata iya zama cikin kunci da bakinciki dan ta kare ni daga wannan babban al'amari?
"She is just a little girl,me tasani da zai dauki hakkin ta haka..?ko dan yaga marainiyace bata san komai ba
...hannu ta daura akan kirjin ta tana wani irin kuka mai ban tausayi..khal har ya iso gaban ta yana rirrike ta mma bata sani ba,cike da sanyin murya da sanyin jiki yace subaya ki nitsu kiyin min bayani ..wai
A ina kika samu wannan videos din?
Ina son nasan meya faru did u know anything about this kar ki boye min dan Allah.
Cikin kuka tace wallhy ban sani ba..
I just found out now...kukan sosai yaci karfin ta
,..pls get up ya dagota da kyar yana mai tausaya mata,tallafo ta yayi ya aje ta agado dan har wani luu idanun ta suke jikin ta yayi sanyi sosai
Bata iya komai sai sauke ajiyan zuciya idanun ta har sun kumburo sun haura kamar wanda aka aika ma sakon mutuwa...
Zama yayi agefen ta yana dan calming din ta har tayi shiru
da kyar tayi masa bayanin yadda videos din suka shigo hannun ta komai ta fada bata rage ba..tace khal babu lokacin dogon bayani,bana son mum taji komai har sai munji sauran bayanin daga bakin bahiyya...xaka kawo ta?ko binka zanyi muje abujan.
I reall..i really want to meet my sister khal... i want to make sure if she is ok...ko baga yadda yake dukan ta bane?...this is a sexual assault... abun nashi yayi yawa.. yayi tamin karya akanta and i do scold her batace min komai bayan kuma bata da laifin komai....wani matsanin cin kukkan datake dannewa ta sake fashewa dashi,tace dana san abunda yake mata kenan wallhy wallhy da na bashi dukiyar duka an rabu lpya..
He lied to me dan ya raba ni da wacce take kaunata
Ashe ma karya yake mana dayace tace mashi tana son shi? Wayyyo Allah na bahiiya ta kiyafe min..im sorry for judgin u my litle sis...im so regreting this.. i just cant take it anymore.
Khal shikadai yasan meyake ji aransa amma haka ya daure ya dinga lallabata musamman dan kar ciwon nata ya tashi
Magana sukayi na fahimta
,..da kyar subaya tayi masa alkwarin zata danne zuciyar ta dan kar jahan ta sani yanzu sai sunyi bincike
..shikuma yace ta bashi kwana uku zai gama da komai..
A Cikin daren ya fita ya bar gidan daga subayan babu wanda ya san da abunda ke tafiya.
Bangaren su kaamil kuwa ba irin dabarar da baiyi bahi ta gaya masa watake aure ba amma sam taki tace mashi komai,bai so ba amma haka ya barta ta xame ta tafi ta barshi awajen ...
Yayi ta xubda hawaye saboda wannan karon ne farko da zuciyar sa yaga abinda ya biya masa sosai,he want to respesct her decision tunda tace mashi aure ne akanta amma sai yaji bazai hakura ba sai yaji wanene mijin bahi..
Bahi kuwa abun bai wani dara ta chan chan ba,taji wani iri kam amma bata zafafa komai aranta ba
Washe gari da sassafe,dija na gida taji sammaci cewa ana neman ta a waje..da kyar ma ta fito dan babu wanda ya taba mata irin wannan sammakon
Ganin khal har bakin kofar gidan su yasa ta sha mamaki sosai,bakin ta har na batan kalma ta ushering dinshi ciki cike da mamaki da girmawa
Comfortably ya zauna akan sofa,da shike its 7 oclk sai ta kawo masa hot coffe,just one sip yay..badon komai ba sai dan ya kwantar mata da hankali ya lura ganin shin ba karamin tsorata ta yayi ba..
Ta tambaye shi lpyar bahiyyar..ba yabo ba fallasa ya amsa da cewa tana lpya..anan ya shiga kawo mata tambayar sa kamar hira tun daga lokacin da ta fara sanin bahi a schl..har ya kawo ta inda yake son yaji
Toh Daya fito fili ya nuna mata yasan labarin sadat..,sai taji kawai bata da option face ta bashi labarin duk abunda yafaru..
Khadija kam bata ji tsoron komai ba,evry little details tagaya mashi na abunda bahi ya fuskan ta ..
Duk dama tayi kuka sosai,amma she was brave enough to say that in har xai raba bahiyya da sadat to zata taimaka mashi ta duk hanyar da zai bukace ta.
Hakan yasa ya nemi alfarman mum din ta,ya dauke ta ..by 9.30am suka nar nigeria zuwa kasar london..
Da kwararrun yan bincike tunda daga military base ya fara dora salon sa..
acikin ranshi Tsaf ya shirya irin kalar hukuncin da zaiyi ma sadat da duk wani mai hannu da bada gudumawa acikin case din
Sam baya son bacin ranshi yasa yayi garaje ko kuskure
Yana dai so ya tara manyan shaida akansa,yasan yana bukatar ya aje hankalin sa waje guda yanemi taimakon dija.
Da suka isa london Basu kuwa samu duwawun zama ba dijan Ita ta kaishi duk inda sadat yake hada shirin sa,har wannan wood house din daya gallaba masu azaba sanda ta kaishi yayi binciken sa sosai
Kwana daya da rabi sukayi a london ya gama binciken sa,nan ya hada ta da wrist wacht mai dauke da security trackers da audio recoder yasata a jirgi ta dawo nigeria batare da sanin kowa ba...
Dija Tana so ta gaya ma bahi amma khal ya mata warning akan haka..m most time ma kashe wayar ta take yi dan tsaro .
On the that 2- 3rd day da asubahi khal Ya wuce USMC base,da uniform din sojan nashi ma ya shigo fuskansa adaure kamar malaikan mutuwa...
Anan ofishin wanda suka san case din basu fi mutane biyar ba,biyu daga kwararun masu bincike daya daga laboratory sai computer scientist din su mai gaba daya..
Wasu files khal ya karba daga wajen dayan repotern
Daga nan Yayi 1hr indoor secret meeting da manyan generals da officials dake wajen ba wanda yasan meya ke nuna musu
Yana fitowa A hujajan ya wuce torture room ya aika mugayen sojojin sa guda biyu har izuwa lab din..kowa anyi dismising dinsa aka bar doctor barak adeel
...barak adeel yana ta aikin shi kamar mutimin arziki ya dauka ko irin mission din su na gaggawa ne ya taso ma khal ake bukatar taimakon sa
Da suka tsamo shi yaga an nufi torture room da shi abin ya dan bashi mamaki aransa sosai...
..yana budan baki zaiyi magana.. khal ya tsare su...oder kawai ya basu da idanun shi,bajira suka fara dukan sa ta ko ina da wasu irin kakkauran rubber mai irin kaurin belt din engine din nan
Kowani saukan duka,thy wll make sure kayan jikin sa ya beke,doc barak adeel yayi ta ihun radadi ga azaban rudanin rashin sanin laifinshi,khal bai motsa ba yana ta kallon shi har ya bar zuba ihun ya shiga fade fade,yana neman afuwa duk jikin sa saida sukayi tambari da jini..
Sanda ya galabaice khal yasa aka barsu su biyu..barak is his private doc so ya san waye khal sosai
..duk dashi ba sojan yaki bane amma yasan khaldun din nan da ake gaya masa ba wai bane there is alot of bad and scary stories behind it.
Ayanzu ji yake Da ace khal yayi handling dinsa gwara ya gwamaci mutuwar sa,dan haka ya zube kasa jikin shi na rawa kuka har da majina yana rokon shi gafara tun kafin ma yaji laifin shi
Khal baima ji shi ba...tambaya daya ya masa nacewa ko ya san waye sadat adeel?..jin haka ya dada sa doc ya rude yana inda inda...to khal baima barshi ya amsa ba, ya matso bakin sa da hannayen shi ya karya masa yatsu ya tsoma su a tafasashen ruwan zafi
...tsaban zafin azaba da kanshi ya rasa setin brain dinsa yana kuka yana bari ya shiga gaya masa duka duka sirrin sa..harda yadda suke boye ma duniya cewa su basu da iyaye bayan suna dashi ashe ubansun ma gagurumin cocaine seller na yana chan prison a rufe a russia am masa daurin rai da rai...
Khal yace masa ina Alluran daya ke cewa xai yi masa yaje yanzu ya dauko ya masa....he was scared to the core amma haka aka kwashe shi aka kaishi lab a ragwabe ya dauko alluran mugun tan nashi da hannun shi
....khal yana zaune yasa shi agaba akan cewa maza ya hada ruwa Alluran batarr daya rage ko one drop ba which is over dose.
...doc adeel dake fama da radadi yanayi jikin shi na rawa,ga khal agefe ya na dada birkita shi da tsawa akan yayi sauri... yau sai ya mashi allurar.. ga shi duka ya sa shi ya ja ruwan syringe ya cika fam har yana fetsuwa
..duk da tsawan da khal ke masa ana tsoro ya hanashi iya matsawa..
Haka yana ji yana gani khal ya karbe allurar ya tsiyaya masa gaba daya a hanyar jinin sa baiji dandanin tausayin shi ba
Doctor dayaga mutuwar sa kiri da kiri birkicewa yayi
Yana cikin radadin zafin mutuwa da axaba khal ya bata rai yake gaya masa laifukan sa na asali
Sanadiyar wannan ruwan allura daya hada yake mugun ta da shi Binciken su ya nuna cewa other high rank leutanants da manyan sojojin da suka mutu ba asan couse din mutuwar su sun duba sun gani ashe wannan alurar ne ya kashe su..and that means shi ya musu tunda allura nashi ne shiyake hadawa bawani ba..
Then maganan daya fada ma bahi na cewa zai ma khaldun shiknsa allurar ya fito a camera hade da personal issuren sa akan sadat
Khal yace masa yayi kuskure da haukar sa ya shiga ryuwar matar sa,he told him dat duk wanda ya taba mashi bahiyya henceforth baxai rayu a duniyar ba..last word din da doc barak ya ji kenan Allah ya karbe ranshi
Imidietly khal yasa aka saka gawar sa a motan da xaibi da shi airpot kafin kace kobo gaba daya gawar ta sauya hallitar zuwa wani irin mummunan abu babu kyan gani..
Akwana biyun da suka wuce Subaya bata samun shi awaya,gashi damuwar ya nuna boro boro a fuskan ta,boye kanta ma take dan tasan jahan tana ganin ta shikenan dole asiri ya tonu
A wani fannin zuciyar ta har tsoro take dan tasan jahan Aarah kam bazata dauki maganan da sauki ba
Ta nemi yasmine awaya bata same ta ba...amma da dija ta dawo da shike tana da nunber ta sai ta kasa hakuri ta kira ta sukayi dogon video call
Anan itama ta ji duk sauran bala'in da suka fuskan ta wanda bata sani ba
Dija fadar maganan takeyi kamar wanda dama ta dade tana jiran ta sauke nauyi,anan subaya taji cewa khal da bahiyya suna son juna, sannan khal yakanje london domin yaga bahiyar sa..
Abun ya dame ta sosai, Kenan ta raba yardan dake cikin soyayyar wayannan masoya?
Daga nan wani silent zazzabi ya shige ta. ,tafiya take acikin gida kamar mace amma ita kadai tasan ba a dai dai take ba.
To kafin nan a gidan su bahi tun ranar da tagaya mashi tana da aure,kaamil ya ki ya fito daga room dinshi har na kwana biyun sai abun ya fara daga masu jahan khatun hankali
Anyi anyi ya bude kofar dakin yaki,rabun su da su kagan shi awani hali irin haka tun lokacin da khal yaje prison a ta dalilin shi..
Jahan khatun tuni ta daga hankalin ta sosai dn tasan babu lpya acikin lamarin
Nan aka shiga bincikawa har dai junnut ta ce ko akan bahiyya ne?
She tot ko dan basu samu daidaituwa bane, but taga bahiyya lpyar ta lau bata masan wai kaamil ya kulle kanshi a daki yaki fitowa ba
Junnut tayi iya kokarin ta dan taji daga bakin shi amma yaki,she has no choice than ta gaya musu cewa ita tana ganin cewa akan bahiyya ne ya kulle kanshi
..tunda ita last maganan datayi da shi kenan
Toh Aranar da safe bahiyya ta farka da mugun bakin cikin rashin sanin ina mijin ta yaje kwana biyu,tana fitowa daga room din shin suka yi ido biyu da jahan khatun
Tace good mrning maam tana dan rusunawa aladabce..jahan khatun ko amsawa batayi ba
cikin wani irin wulakantaccen yanayi ta jawo ta ...tace mata biyoni. .Nan suka iso har sashen kaamil,suna kaiwa tasa ta agaba tace sai kice mashi ya fito tunda ke ce munafukar
Bahi cikin mamaki ta dube jahan anma batayi musu ba,ta shiga knocking kofar tana rokon shi ....hilda da jahan khatun din kamar zasu mutu....dan su kam basu ga abin so ajikin bahiyyar ba
Jahan din ma jira take kaamil ya fitoo tayi masa kaca kace ta tura shi us ayau din nan..
Da bahiyya ta dage na magiya sai gashi kaamil ya fito...gaba daya ya galabaita idanun shi yayi ja.
Ita kanta bahi sanda taji kanta ya sara data dube yanayin shi
...ran mahaifiyar shi ne ya dada harzuka data ganshi Ahakan...ta daure fuskan ta sosai batace masa uffan ba
Bahi ne take masa tambayoyi cikin nuna kulawar ta tace ko baka da lpya ne?..to lokacin yanaji da radadin zafin rasata...baiji kunyar su ba ya fara tambayar ta meyasa tace bata son shi again?
...shidai yanzu ji yake yi kamar yaki yarda da maganan auren nata..gashi bata so ta furta agaban kowa cewa khaldun ne ya aure ta..
Jahan is already murmumring..su junnut kuma sun sa ido suna kallon su kowa da abunda yake rayawa aranshi,hawayene akan fuskan kaaamil wanda ya sako shi ma bahi yana ta famar marairaice mata..
Kunya da fargaba duk sai ya hanata sakat
Dan Jan shi gefe tayi ta daure tayi masa maganganu masu sanyi
...cike da nuna mashi gaskiyan lamarin ta sake xayyana masa cewa wallhy da auren wani akanta so babu batun soyayyar su...
Yace wanene mijin?
Tace a gaskiya sirrin ta ne kuma in har yana son ta dagskiya to ya shirya rike mata sirrin ta
..wani hawayen ya sauke mata,zaiyi magana sai ga jahan ta iso kan su sai ya share hawayen sa yayi shiru
...tace ke wacece haka da zaki zo gidana ki shiga rayuwar dana?
Tambadaddiya..yar iska irin ki?..toh ta Allah bata ki ba..inma aiko ki akayi kiyi seducing dinsa ki cuna masa bakin ciki dana naji haushi..to wallhy nafi karfin ku..da na yafi karfin ki..
Bahi ta dagi kamar zatace wani uban..cikin hatsala tace will u get out of my sight?
..a tsorace bahi
ta zame .. jiki ba kwari ta barsu anan..
Jahan bata tsaya lura da condition din dayake ciki ba ta dinga zuba masa masifa da xagi ta inda ta shiga bata nan take fita ba.
Ta jaddada masa cewa ko bata duniyan nan badai ya auro mata wannan yarinya ba
Saidai in zai sake wata uwa ba ita ba..
Junnut ta matukar tausaya ma kaaamil
...da sauri ta bi bayan bahi dan taji kan maganan
Hilda kuwa dama abunda take so kenan tuni ta shiga sa ma jahan khatun baki suna scolding kaamil
Ita kuwa bahi ko dakin nata ma bata isa ba taga sakon sadat mai dauke da mummunan baraxana kamar yadda yasaba..
Wani siririn hawaye ya kufce akan idanun ta,ajiyan zuciya tayi tana karantawa wai
Ya bata 2hrs cewa idan bata same shi ayanzu ba zai sa ayi ma khal din ta allurar mutuwa
..gashi ta ga khal kwana biyu baya nan she just assumed that dagaske aikin yaje maybe yana hannun dan uwansa barak adeel..
"Mayafin ta kawai ta dago zuciyan ta cike sa tunani kala kala,kaamil na bata tausayi sosai,kuma bata son wani abu ya taba mata mijin ta...adai dai bakin door ta fito sai ga junnut..
Wani kallo suka maida ma juna tayi sauri ta karaso
Tace bahi we need to talk...wai Meya faru tsakanin ki da kaamail ne..bahi mesa zakice baki son shi?
Junnut look disturbed and serious
Bahi tayi shiru..cos hawayen rudani duk sun rine mata idanu kuma bata so ta bude baki har zuciyan ta yasa ta furta ma junnut abubuwan da bata da niyya.
Junnut ina sauri ne amma dana dawo zamuyi maganan
.
Kafin junnut ta bude baki bahi har ta xame ta bar ta awajen ta,quickly ta shiga mota ta bar gidan
..bata wani iya tuki ba amma haka ta daddage Straight ta isa location din daya ce mata yana jiran ta
taje Wajen babu mutane,hasali ma bayan gari ne sosai
Babu mutane dayawa sai ajiyayun motocin fa ba amfani dasu
Daga nesa Ta kare mashi kallo Ba shakka kuwa shi din ta gani zaune akan bakar motar shi ba laifi ya fada sosai...
Yana ganin ta daga nesa sai ya shiga motar ya zauna
dayaga ta iso kusa sai ya bude mata door din..bata rai tayi Tana kallon shi sai taja ta tsaya taki ta shiga...wani mugun dariya ya fashe da shi..he is happy to see her zuciyar shi sai harbawa yake dan sosai ya fahimci cewa son yarinyar ya shige jikin sa sosai..
Bahi ta hade ranta sosai batayi hawaye ba kuma batace uffan ba
Da yaga dai ba shigan zatayi ba sai ya fito yana da wani irin miskallaen murmushi taki ta hade ido dashi ta kau dakan ta.
Hannun sa ya miko kamar zai janyo ta jikin shi yana mata wani irin kallo,da wani irin muryan tsana da hantara cikin fushi tace masa What did u want?
Ya sakar mata murmushi Yace ohw woah ..haba yan mata... hush down mana,bakiyi kewa ta ba?Taja tsaki mai sauti...dariya yayi yace lallai auren nan ya bata min ke..
U no longer respect me... Cako hannun ta yayi abaxata ya matse a nashi tasa masa ihu tana finficikewa abun wuyar sa ne ya fadi ajikin ta ita tagani shi bai lura ba yanata faman kokawa da ita tayi sauri ta cusa acikin hannun rigar ta..da karfi ya hada ta da jikin car din shi ya matse bakin ta yana kokarin shakar gamshin jikin ta cikin wani yanayi,hawayen ta mai zafi su suka fetso ..,yana ta kallon inda ruwan hawayen da ke saukowa akan hannun shi..
Wani irin mugun yanayi ne a fuskan sa na bakar kishi da azaban mugun ta.
"Kinzo sabida nace zan kashe shi ko?toh kisani zuwan ki bazau hana komai ba...ke Kinsan ina son ki". Amma sabida ke wawiyace kin bari har an aura maki aure da wani wawan
..toh ki nitsu da kyau kiji abunda xan fada maki..
Sake ta yayi ya fito da briefcase daga motar shi ya mika mata hawayen ta take sharewa kafib ta karba tana karantawa
Yace...this is subayas life..50% of her wealth shine anan,kuma sauran nasan inda zan same su.
Nasan kin gaji ko? Toh Shiyasa na sama mana mafita..i have the money now, saura ke bahiyya..
" tayi masa shiru cahn ta dago kamar marar laka ta kalle shi..Magana tayi kamar Jikin ta a matukar sanyaye tace ...
Sadat Am married..
dan Allah ka rabu dani..ba kasamu kudin ba?kasan ba a aure akan aure..da sauri yace mata anayi mana...ni nasan yadda zamuyi
..kisa aranki cewa sai kin aure ni idan ba haka ba ..
Tun bai gama ba Ta toshe kunnen ta a mugun zafafe tace pls stopppp
Jifa tayi da file din akasa agabn sa tace ni bazan aure ka ba..Nace maka ina da aure,bani da wata alaka dakai yanzu..ba kudin bane a hanun ka ai sai ka kama hanyar ka..go and deal with ur wicked issures....wannan
Rayuwar ka ne, kuma wallhy ka dena kira na awaya ni bana so Muryn ta na rawa cike da masifa ta juya zata tafi..
Bai tsare ta ba
Hankali kwance yayi furxan iska Yace 1 more step yarinya.... Taku daya yarage miki ki dawo bazawara matan mamaci...wani dumm taji kirjin ta ya buga amma bata juyo ba tace...r u planning to kil him dan ka aure ni?
Cike da isa da basarwa Yayi murmushi yace
A'ah,..Not witout ur permission idan kina si ya mutu yanzu zansa akashe shi..bahiyya,..na dauko dukiyan nan na zo dashi ne dan na kasance tare da ke,saura kirisss komai ya kammala
Duka arxikin subaya zai dawo nawa.
Gaban ta ya dawo ya zuba mata kasallalun idanun shi yana mai dura hannayen shi acikin aljihu...kudi ba wani abu bane a familyn hamood subaya zata sake tara wasu
But If u love subaya to be alive saikin bani hadin kai..
Ta hadiye firgicin ta tace to me kake so nayi,na kashe aure na?.... yace no..alkwari zakiyi at the expense of familyn da suka taimake rayuwar ki suka dawo dake mutum..
Ayanzu ki dauka Rayuwar saood da subaya duk suna hannun ki..
Sai Kimin alkwari zaki dawo nan gobe da yamma ki same ni.
Yau xanje na kwato sauran files din subaya,sai mujee swizeland tare dake..zan boye ki anemi ki arasa dan na samu daman tattara komai cikin nitsuwa ba tare da hankalin kowa na kaina ba..
The moment im done,zamu je wata duniyar da babu wanda zai same mu..
Auren ki zai warware idan mijin ki yayi shekaru bai ganki ba...u wl be mine har abada,bazan taba cutar dake ba
For this statement "Wani saukar tassss yaji akan malalan kumatun shi,a bazata ya dago ya kalle ta ta zuba mashi furious eyes din ta har jikin ta na tsuma ..
Yace Bahiyya kika mare ni?..dada sauke masa wani marin tayi.... zai matso kusa ta daddage ta daka masa wani firgitaccen tsawa tanace masa enouhg...
Sannu lucifer first son of the devil....ta fada azafafe cikin idanun shi ta sako zafi sosai kamar uban ta ya zaga
Ka dauka ko zanji tsoron ka ne?its over now ..bani da lokacin jin tsoron ka...ko baka san kai mahaukaci bane..?
Mamakin yadda ta birkice masa yasa shi shiga shock Zaiyi magana ta nuna mai yatsa tace ni kayi min shiru... u better Listen to me now..
Ba kabani gobe nazo nan ba?..
Dan kadan ta shafa jikin ta ta fito da magic necklace dinsa...ta nuna mashi.
To na amince zanzo..its a chaklenge kacika alkwarin ka,leave subaya and her family alone ..i assure you nima zan cika maka Alkwarin ka .
Kuyi hakuri jiya i was busy
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top