chapter29
For you sis Ayusher moh'd._
_3⃣0⃣-evolution♡_
Wani shakurarren kuka mai kakarin rudewa ta fashe dashi duk jikin ta sai da ya dauki rawa..
Dafe kirjin ta tayi cikin numfasawa tana furta innalihhi wa inna ilaihi rajiun
Tsaban bugu catake zuciyan ta zai fito daga kirjin ta,ji tayi kwalwwlkta na ce mata komai ma mafarki ne.
Dan Har yanzu Ta kasa yarda da cewa abu daya suke so ita da junnut din ta,"dama ashe har sa'ood yana son wata?...to what about me?i truly loved himm hala shiyasa yake wasa da hankali na, bai ma taba jin nayi masa ba,..but why junnut...why my besfriend, meyasa zuciyata ta zata so abunda kike so kuma yake sonki.
Dan pause tayi tana jan numfashi idanun ta gaba daya sunyi jazir..yace ya aure ni,amma yaki yace ni matar sace?..,bisa ga abubuwan da junnut tace mata ayau..ba tantama ta kawo cewa maybe suna matukar son juna...maybe he dosnt even want hurt junnut for my sake..
Kuka kawai takeyi tana birgima akan floor cikin tsananin tausayin kanta
Tayi ta maganganu daban daban amma bakin ta ya kasa furta mata mafita guda daya akan lamarin
What is even upseting her more bai wuce wani azaban wutar kishin sa datake ji ba...abun ya mata yawa har taba mamakin kanta
Ji takeyi kamar bazata taba iya hakura da son shi ba Dan ance junnut zai aura,bai fi damun ta kamar yadda junnut din take bada labarin sa ba
Ayanzu Wani Haushin sa takeji kuma tasan son shi da mummun kishin san suke tada mata haka
Takune kanta tayi akasa a tsakar dakin cikin kunci ta ta kife kanta da gwiwa feeling so lost and confused
Tunani takeyi ko zata iya rayuwar ta acikin su a haka?
Beside bata san me yasa ya aure tan ba
Wasu hawayen ke sauko mata,sad and trembling voice dinta yake cewa
In har junnut ce ka zaba tuntuni why did u marry me?wai ko ce masa akayi ne ina sonshi yake neman wulkantani?... To wazai fada masa sirri na?...is that why he call me cheap...in zata iya tunawa babu wanda yasani daga sadat dai sai su jasmine su kadai suka san yadda take kaunar khaldun
Tace gaskiya bazan iya hada miji da junnut ba,tunda yace ai ba so na yake ba why not ni ka sake ni na koma gida nayi rayuwa ta?..But can she? a take wani zuciyar yace mata meyasa bakiyi tunanin haka tuntuni ba sanda kikaji maganan kishiya,kin amince kin zama matar sa duk da abunda yake gaya maki,to kenan zaki sadaukar da mijin ki sabida yayi alkawari da wata?
Dan Shiru tayi tana duba da lamarin can ta jingina kanta da bango slowly ta runtse idanun ta..
Tasan dai har yanzu khaldun shine abu mafi soyuwa aranta wanda take ganin kamar rabuwa dashi abu ne wanda zai iya mugun azabtar da ita.
Sannan A Duniya tasan junnut ta fi karfin komai awajen ta,not even a guy that is mistreating her feeling,bisa ga maganganun junnut na dazu a yanzu kam ta amince khal ba ta ita yake ba,to ita ma me zatayi da shi?
Gani take kamar itace matsalan yanzu data kwallafa shi aranta
Tace Ko ma ta fada ma junnut komai ne dan suyi shawaran yadda zata rabu mata dashi kowa ya huta?.
Ayanzu gaskiyar ta shine Tasan bazata iya hada kishi da junnut din ta ba kuma tasan bazata taba iya daurewa akan soyayyar shi ba...
What a strange world..tayi ta juya tunani,ta bada kwalwalta dalilai amma har yanzu dai bata gane komai ba
Takance dama ace banyi aure shi ba da sai ince zan yanke wani hukuncin na daban
Shiru dai tayi tana maganan zuci,a hankali tana sauke ajiyan zuciya...Ganin kamar numfashin ta na neman daukewa sai tayi saurin sulalewa ta mike kafafun ta akan floor din tayi tsam da idanun ta na aikin zubar da rudaddun kwallla
A duk tunanin datayi sai take Jin kwakwaltar kamar shirme yake mata
She is in extreme shock and pain,bata ma san lokacin da wani hutaccen bacci yayi awon gaba da ita ba.
Bangaren khal kuwa haka kawai ransa ya bashi cewa duk inda bahi take ayanzu tana cikin rudani dan yasan bazata ji dadin abun ba
Shikam yasan yana son ta,kuma Duk da abubuwan da yake faruwa har yanzu bai cire rai ba Yasan xai iya yuwa itama tana son shi,sanin hakan ne yafi tasiri aransa fiye da duk wani laifin datayi masa .
kuma Yana da yaqinin da wata na dabance ba junnut ba da abun zai zo mata da sauki,but her best friend?.
yasan is not gonna be easy for her to asimilite...toh a duk da yana tuno hakan amma yake tursasa zuciyan sa jin dadin da hakan ya faru da ita
Gani yake wannan al'amarin shi zai rama ma kanwar shi azaban da ta dandana mata akan sadat somehow
Dama shi da kaamil ne awajen to da junnut ta iso sai ya share su ya tsunduma kanshi gaba daya cikin tunanin bahiiyar sa baiya ma sauraran hirar su
Kaaamil is so intrested in her,dan tun daya ganta zuciyar sa take faman harbawa
Koda junnut tazo wajen ma hirar bahi kawai sukeyi
Khal Jin tace ma kaamil ai hira sukeyi bahin tayi excusing dinta ta tafi tuni sai yaji zuciyar sa ta amsa
Ba bata lokaci ya xame ya wuce bai tsaya ko ina ba sai site din sa sauri yake kamar wanda ake tunzira shi,bude kofar dakin ta yayi da sauri daga idanun shi ke dawuya ya hango ta dunkule akasa tayi laushi har abun tausayi hawaye sun gama bushewan su akan kuncin ta
Dan karamin ajiyan zuciya ya sauke Ya dafe kansa...."Mixed feelings na damuwar ganin ta Ahakan da wanda yake so ya ji na dadi daya ganta hakan duk su suka dama zuciyan shi..."
Kallon yanayin ta ya tsaya yi almost 20minut bai daga idon shi ba,dan kuwa ba sai angaya mashi meyafaru da ita ba jikin shi sosai ya bashi halin datake ciki
Sai yace Duk dama amanar wata take shirin ci now she is jelous dan ance ina tare da kawar ta
..what is wrong with dis girl,ya dada kare mata kallo...xuciya nawa take da shi?Allah ya tsine ma zuciyar da zai so ni ya so wani wawa kamar sadat
Daure fuskn sa ya dadayi Har wani kikkifta ido yake yana Kallon ta Shi sam bai fahimce ta
***
Farkawan ta ke da wuya suka hade ido dashi amma bata tashi akan floor din ba ta lafe
Wani kallo suka maida ma juna yana binta da wasu zafafan harara fuskan sa a daure
Itama Hade rai tayi cikin jin kishin sa tana mutsuka ido tana dan turo baki a shagwabe sosai taji dadin ganinshi akanta....
"..Yace Whats all this?...baki da hankali ne zaki kwanta ma mutane akasa...will u get up before i crush you..
Wani share sa tayi,tana dan kau da kai maganganun da suke wanzuwa azuciyar ta su suka fi dauke mata hankali har ya tashi ya fita waje bata ma sani ba yana dawowa kuwa wani shahhhh taji ana gwaro mata ruwan sanyi tun daga kan tsakar kanta har cikin jikin ta
A mugun fusace ta mike tana huci ruwan na bin fuskanta mikewa tsaye tayi zumbut har ta hayyako zatayi magana ya wani daka mata tsawa yace...
"...Ina wasa dake ne da zanyi maki magana ki zauna ki namin shiru,ni sa'ar ki ne?
Wani kuka ta fashe masa dashi Tace ina ruwan ka dani?
Shiru yayi ya kure ta da ido tana famar komar da kukan amma Wasu sabbin hawaye ne suke sauko mata dan Tsaban fushi bata san sanda tace masa hakan ba..
Yace ohhhh,to doka ne ba a kwanciya min akan floor dina
Duk randa kika sake kwanciyar sai na karya kafarki
Ciikin kakarin kukan Tace ai ba dakin kaba ne sai ka fita..
Bai kulata ba yace ni dai na fada maki,kar na sake ganin ki a kasan flooor dina Unless u want me to trow out.
" wani harara ta jefa mashi A dan fusace ta dago cryn balls din ta cikin sanyin murya mai nuna firgici tace mashi throw me out now...ni wallhy nagaji..i just want to go home Ai ni bance ina son zama da kai ba
Shiru yayi cikin hade rai yanajin ta sanda ta gama maganganun nata kafin ya matso kusa yasa hannu ya jawo ta Har gabansa kamar wanda yake shirin cakumo ta...
"U aint going anywhere,gidan nan shine prison dinki..
Zaki ta zama dani har sai na auri kawar ki,she is the only one i want...
..ke Baki da amfanin komai,and dont you dare say ure my wife to her dan nikam nafi karfin ki
Ko kallon shi batayi ba,A duk abunda yace "sai na aure kawar kin shiyafi mata zafi"hannun ta take shirin kwacewa ya ki ya sakar mata,..wani Cizo ta danna masa a hannun A mugun fusace ta shiga firgici zata kwace jikin ta daga nashi,shikuwa bai sake tan ba sanda ya gama karance duk wani hawayen dake sauka akan fuskan ta
yasan wannan duk borin kishin sa ne...dan yau ne ranar daya fara jin tana maida masa magana cikin fushi da firgici
Shikansa ayanzu ta gama ruda masa tunani,dan kuwa balain son shi da kishin sa yake hangowa a yanayin ta just like shikadai ne a zuciyan ta babu wani
Cikin ranshi sai yace wai kam Ba sadat take so ba?meyasa take fushi dan ni nace zan aure kawarta,wato ashe ba dadi take iya ma wasu?
Wani murmushin mugun ta yayi aransa yace ai Allah ne ya kama ki"da zan iya gaya maki laifin ki amma duk abunda zai faru dake shine dai dai ke..very stupid girl sai ya sake ta ya futa abunsa.
Itakam Kuka ta cigaba dayi,daga nan tunda ta wanke fuskanta sai bata sake lekowa tsakar gidan ba Har sanda tayi kwana biyu masu kyau a dakin ta bata kuma kira kowa ba.
Dama in bawai ta fito bane babu mai shigowa site dinsa dan haka bata sha mamakin da taga ko junnut bata leko ta ba
Wani bin in ta zauna har mamakin kanta take yi sosai,a duk sanda taji zimman cewa zata yanke hukuncin gaya ma junnut komai toh wani azaban fargaban rasa shi da kishin sa shi yake saurin danneta
Most times sai taga kamar ma babu amfanin soyayya ko auren da ke tsakanin ta da khaldun amma har yau ta kasa bari zuciyar ta ya cika furtawa mata hakan bare kuma ta kai maganan gaba
Sosai sonshi yayi nisa acikin ranta har ya zame mata numfashi da abinci ma ruhin ta
Washe garin yau bata jin daidai ajikin ta, amma sai ta daure ta fito dan su hadu da junnut din ta..hira kadan sukayi
Junnut tace dana ga kwana biyu baki fito ba sai nayi tunanin na barki ki huta kawai
Most time bahi sai dai tayi murmushi
Dan inta kalle junnut bata iya daurewa
...sai taga ko magana mai tsayi bata cika son yi da ita,..gaba daya ta dawo wata shiru shiru komai tana yi ne tana dan jan baya akai
ita kuwa junnut sai rawan kai take xuba mata surutai
Ita kuwa bahiyya A duk zumudin sake haduwa da aminiyar ta datayi bata kawo cewa cikin sauki zataji komai ya fita mata akai har haka ba..
Domin kuwa iya daurewa da nazari tanayi amma har yanxu bata gane kan komai ba sai ma dada rudewa da tunanin su yake sa takeyi
Bangaren khaldun kuwa duk yana sa idon sa akanta a boye amma bata san da haka ba
Aranshi Yakanji ya takura ma rayuwar ta akan junnut tunda yaga kishi na damun ta sosai..
amma idan ya kalle yanayin tarin hadarin son data ke masa a kwayar idanun ta sai yaji gaba daya jikin shi yayi sanyi da al'amarin..game da subaya da sadat yasan tayi ma zuciyar shi laifi..but he stil respect that kowani dan adam yana da ra'ayin shi akan wanda zaiso da wanda bazai so ba
Yana matukar kaunar ta yar hanzu....He hate those tears
...he feel that bazai iya cigaba da dauriyar ganin ta ahaka ba duk dama laifin datayi ma zuciyan san is still unforgivable.
And Besides ya tsani raini,kuma Baijin zai iya cigaba da sai insa da ita bare ya gaya mata sirrin zuciyar sa
Dan a kwana biyun ya lura yaga cewa gaba daya mood din ta ba adaida yake ba
Hakan ya dada sawa yayi watsi da tsabgar ta bata ma ganin shi sosai a hidima gidan amma shi yana lura da ita sosai
Kaamil da junnut din dai suke kokarin debe mata kewa duk dama kwata kwata yanzu mind din ta baya wajen su duka
Ita ayanzu Tafi tunanin yadda zata fuskance
al'amarin,shin zata daure ta gaya ma junnut komai ne koko zata nemi mafita ta wani wajen.
Akan hakan ma ta kira dija yafi sau agirga amma ta kasa gaya mata asalin meke damun ta,gashi har yau subaya taki daukar wayar ta bare suyi magana,kuma duk sanda suka hadu da junut har ta kawo mata maganan khaldun din ta toh bata iya yin bacci mai dadi Wani bin ta dinga kuka kenan
A Haka rayuwar ta kasance mata na har kusan sati biyu sannan ta fara jin sassauci aranta
musamamman data gane cewa ayanzu bata da wani madogara face ta bar ma Allah komai.
Idan tayi wani tunani sai taga kamar bazata iya zuba ido taga komai na tafiya a lullube ba,duk dama yanzu kam junnut ta cike mata brain da karerayi akan soyayyar su da khal
But tunda ta dan aje hankalin ta waje guda ta soma lura da banbancin lafuzan junnut da na kaamil akan abun sosai sai ta fara gane cewa kamar abun duk daya ne babu wani banbanci. .
dada nitsuwar datayi sosai yasa ta gane cewa wasu zantukan junnut din duka karya ne
Hakan ya fara bata karfin gwiwa har ta dena jin karfin cutarwan lafuzan ta a zuciyar ta kusan kowani lokaci
Gashi ta gama lura ayanzu kamar rayuwar su ya dada banbanta,dan babu yadda batayi da junnut ta dena saka guntayen kaya tana yawo agidan ba amma haka sam taki..
Ita tunda khal ya sa tayi islamiya a london ta gane cewa ko wata mace a duniya kamar sarauniya ce,yaanzu ita dakanta ma bata son cika barin jikin ta abude haka kawai...
Junnut Takan dai ce mata bahiyyya ke kam bazaki taba wayewa ba,tunda kika zo gidan kike lullebe kanki kamar wata kwai...bazaki sa kaya kisha iska ba?wasu designers din are terrible
Design dinsu is alwys revealing amma dan dai tasan su din ta saka bata damuwa da yanayin tsarin su
Shikuwa kaaamil yanayin bambancin tarbiyan su yana daya daga cikin abunda yake sa shi yake jin bahiyya na burge sa sosai.
Ya lura duk iya surutun junnut da tsiyar d zatayi ma bahiyya,bahi taki sam ta biye mata akan irin sabbin tsarin rayuwar da ta debo makanta.
Ana cikin haka washe gari da safe bahi ta farka da niyyar zata kai ziyara ma dija dan kuwa tunda ta karbe adress din bata bude ba sai yau
Sanye take da hot pink nitie ta sake suman kanta duka sun zubo mata a baya
ganin safiya yayi yawa ba lallai akawo mata abincin akan lokaci ba yasa ta shiga private kitchen dinshi ta shiga dora indomie
Wani irin hadin alfarma takeyi ma indomie yana ta zuba qamshi an shake shi da ingredient kala kala tamkar ba ciki za'a kaishi ba
Tanayi ne tana tunanin masoyin ta,musamman take so ace yaci ko da zata ji dadi aranta for once
Dan haka Bayan ta kammala tayi serving a plate sai ta gangaro tabiyo ta kofar dakinsa,tafi minti biyar a kofar dakin batayi knocking ba kuma bata ce uffan ba..
Har Fargaba yasa taji ta juya kawai ta bar wajen,one step ta kara sai taji kyat an bude kofar dakin daga bayan ta
Wani gafff taji kirjin ta ya amsa,a dan sadade ta juyo ta gama daukawa shi zata gani kawai sai suka hade ido da junnut,...
Saurin dakewa tayi ta tsaya...She cant hide the remorseful look dan ko murmushi ta kasa mayar mata,ita kuwa junnut sanda ta gama kare mata kallo sannan tace bahi?me kike yi anan haka..tayi mata maganan ne tana kallon dresing din ta Irin kofar dakin husban to be dina ne kike zuwa mashi da hot nity?
Junnut Batayi tsammani ba sai taji bahi ta mayar mata da irin tambayar,tana cewa ke me yakawo ki nan din,im suprised..naga baki tashi da sassafe sai 10 ko...
Tace ohhhhh dear,bari kawai khal ne fa..kinga wai miji zaiyi tafiya shine nazo muyi ban kwana kinga ma har ya tafi ya barni a dakin ban sani ba...
Wabi shiru Bahi tayi dan bata san sanda ta daure fuskan ta ba,tana jin duk surutun junnut din amma bata sake cewa uffan ba
Imagining takeyi cewa ita da suke shashi daya tayi kwana biyu kenan bata ganin sa amma sai yau junnut ne zata gaya mata cewa yayi tafiya?
And what is chocking her up bai wuce cewa da junnut tayi tazo wajen sa har cikin dakin nasa ba.
Ita sam bata ji dadin haka ba,duk dama bata taba ganin junnut a site din ba yau kishi ya sataji kamar dama idan tana daki junnut din takan shigo wajen sa ma bata sani ba.
Wucewa kawai tayi ta nemi waje ta zauna cikin danne zuciya ta bude abincin ta fara ci a tsanake kamar bata damu ba,but Tsaban bata jin dai dai ko tayin abincin bata mata junnut din ne tagaji ta sa hannu suka karasa ci tare..
Da ta dan kawo hirar iyayen sun ne ma bahi ta sake nata fuska ta sa baki,.junnut ke cewa ai abincin bahin har yau babu maraban shi da na mahaifiyar ta...
Bayan sun gama cin indomien,wayar junnut tayi kara sai ta fita tayi excusing dinta
Daga nan wanka ta fada ta yi alwala tayi karatun qurani haka kawai dan ta rage zafin kishib datake ji aranta game da kawar ta wanda bata san da shi ba
Wani bin takan rasa gane dalilin daya sa ta kwallafa gayen da bai damu da ita ba ..
Tasan dai Allah yana jin kukan ta
Amma rashin samun sassauci akan son data ke mashi yasa ta dadajin ta bar ma Allah komai
Dan kadan ta tattale fuskan ta da make up,ta shafa turare marar karfi
Riga da skirt tasa na plain ember sai ta dora kakkauran bakar kimono jacket ta rufe sumar kanta gaba daya da veil shima baki...
Fitowar ta ke da wiya suja hade da kaamil,waya yake yi amma daya ganta sai ya dakata ya iso har inda take yana yaba dresing dinta
Takan ji kunyarshi sosai duk dama most times dan yasa ta magana yake damun ta he has a great sense of humor ..ya iya barkwanci da salon sace zuciyar mata
Ita kam bata jin komai akansa,ta kan dauka dai khal shine nadaban acikin yan uwanshi,subaya da kaamil duk taga basu da daure fuska
Sai da suka zauna
Tace masa ina junnut take?
Sai yace mata tana daki tana shiryawa kinsan kawarta zata kawo mata ziyara
Tace hilda?
Yace ehh...thank god kinsan ta ai dana baki labarin ta bata da maraba da kawar ki ..
Sa tayi murmushi batace komai ba...
Yana ta kallon ta...chan yace mata yaushe zamuje...tace ina?
Yace waje...i want to take you out....ko kin fiso kita zama a gida..gwara mu muna ganin mutane am sure babu ko irin maids din nan a shashen bro..aint u bored?
A hankali Ta girgiza masa kai tace no am ok....cikin gwalo ido ya taso zaiyi magana to karar takalmin junnut ya dakatar da su.
Duka suka maida kallon su kanta sai langwasa takeyi tasha white dolce and gabana suit ya mata kyau bana wasa ba
Ita kanta bahi bata san ko kallon kishi tayi mata kona jin takaicin irin wayewar junnut din ba
...right now she dosnt even look like a muslim girl.
Tace me kuke fada baku jira ni ba?
Kaaamil ya tabe baki.. .yace yawwa kizo kisa mun baki ko hajiya kawar ki zata amince muje mu sha iska.
Zama junnut tayi tna kallon bahiyyar,cikin raha tace hajiya bahi...
Bahi Tasan da lullubin ta take yi Sai sukayi
Dariya...cikin shagwabben yanayi tace junnut ni fa ki kyale ni
Wani dariya junnut din tayi tace nikam na shiga uku,kay kaga tun ban yi korafi ba harta gane me zance..kaga dai bahiiya sam taki ta dena shake jikin ta da kaya..nikam ko aure kike so ne..?
Duka suka yu dariya...kaamil yace no its good like this nidai tayi min a hakan,chic nd beutiful...
Junnut tace whaat tayi maka ahakan?
Tabbb di..wallhy gwara ma ka cire "makan nan" she is mine...u have to pass trou me kafin ka isa gaban bahi
Ita dai batace uffan ba,murmushin dake fuskan ta kaamil yake ta satan kallo suna musu da junnut akan ta,shi yana ta yabawa junnut kuma tana komarin gano asalin nufinshi akan bahiyya
Har yace shi daga yanzu ma bazai iya kira sunan bahiyya ba cos he feel she is special...abun dai a wasa suka dauke shi. .
Da kyar yasa su suka amsa akan zai kaisu shan ice cream sabida sudan zaga garin abuja su su sha iska
Anan Sanda suka jira shi ya sauya dressing dinsa yayi kyau shima sosai..
Ba yadda junnut batayi da bahi akan ko jeans tasa ba amma taki sam
Haka kawai take jin kamar in tasa ta fita mijin ta zai ganta da shi duk dama junnut ta gaya mata baya gari but she just cant...tasan ai baya son ganin ta hakan
Su uku suka fito sunyi kyau kaamil yana tuja su a cikin wata katuwar bmw jeep formated.
Junnut ce uwar surutu,kowa na ta fadan albarkacin bakin sa akan tsarin garin abuja har suka isa babban shoping mall,Inda kaamil da bahi suke zagawa suna hira jifa jifa
Ita kuwa Junnut ta tsaya amsa wayar hilda ata bayan su.
Bayan sun fito wajaje daban daban kamil yake ta yawo dasu suna zagawa suna nishadi
,selfies,swings..mad talks...
Dan dariyar da tayi tayi Gaba daya sai ya sake jefa ta cikin wani halin tunanin khaldun
Gashi ta fara ganewa Da alaman kaamil ya aje wani special request azuciyan shi game da ita duk dama bata yi saurin kawowa soyayya bane
A fannin shi It seeems like tayi mashi sosai amma kamun kanta da banbancin ta dasauran matan daya saba gani yasa baida option din furtawa kai tsaye sai yake dai nuna mata a dan wasar da sukeyi
Just for the fun...anma har ya fara kiran ta da suna"cupcake" .
Junnut na dake dan lura takance dashi sai fa ka biya kudi sosai...wannan tsada gare ta.
Su biyun sun gane so ne amma bahi bata dauki abun da tsanani ba...
Toh Da sukaje amusement park ma abubuwan sun fi daga mata
Hankalin ta
Wani abun idan kaaamil yana mata Gaba daya tunanin khaldun shi yake dawo mata na tun ranar da yazo london ya cire ta acikin kuncin datake ciki na rana guda,wanda har yau takasa mancewa da shi.
Har yanzu bata ga abu mai saurin yaye mata damuwar ta kamar shi ba..
"..Shikuwa kaamil in yaga ta bata shiru cikin tunanin tana kallon site dinshi yakan dauka ko ya burge ta ne sai yaji dadi aransa
A haka har ta gaji da abubuwan dayake mata na neman burgeta,ta koma shiru ko tana yawan jan jan musu aji
Basu sani ba ita yawon nasu a hakan tuno mata memories din khal kawai yake yi,she become all rosy acikin zuciyar ta har tanaji kamar babu abunda ya faru tsakanin ta dashi
Wajen diving zasu ce,kuma shine last wasan da suka yi da khal lokacin dayazo london graduation din ta..!
Takan tuno da yadda suka zauna daf da daf hannun shi akan nata with all the smiles on her face..sai taji kawai bazata iya sake maimaita hakan da kaaamil kowani namiji ba..
To daga cewa zata je washroom sai ta zame ta barsu..bata san ko ina garin abuja ba Da taimakon waya da adresss aka kaita har kofar gidan su dija
Its a huge flat,a anguwa mai suna osokoro ba tantama tasan dija dama ba yar talakawa bace tun fil azal
Dija ta nuna farin cikin ganin ta sosai sanda itama taji sabon nishadi ya mamaye ta,dan ma kar su junnut su neme ta sai ta sa wayar ta a silent
Hira sukayi for 2hrs dan gidan babu kowa mahaifiyar dija busy woman ce yar kasuwa ce sosai
Kuma mahaifin ta ya rasu da dadewa.
Bayan sunci abinci sunyi dam, Da kamar zata gaya ma dija abunda suke ciki da kawar ta junnut but
Ganin kirar su kaamil yayi yawa sai ta mike tace ma dija ni zan koma
Dija tace ah'a kam..yaushe kika zo...ko oga ne yake ta kira naga kina ignoring calls dinki
Tace ahh bashi bane..ai naji ance yayi tafiya ma..bata san ma hakan tace ba dija ta kure ta da ido tana jin mitar ta
Sauke ajiyan zuciya dija tayi dan babu boye boye tasan bahiyya is not ok with her life har yanzu kuma agaskiya tana mugun son taga tana taimaka mata
Tace ance maki baya nan kuma?ba auren kikeyi ba?dont tell me
Har yanzu bakuyi setling issures dinku ba..?
Sai tayi shiru...
alaman ma ta rasa mema zatace
Ma dijan
Dija tace bahi?baki tambaye shi kinji laifin da kikayi masa ba ko?
.. .kinsan dai haka kawai mutum bazai zanza maki ba..sooo wont u talk to him?ko kin masa shiru ne har yau kina ta famar wahalar dakan ki..
i know u enjoy doing that"mrs zurfin ciki...in zaki ji ni kiji ni, wata rana zaki kashe kanki am telling u
Duk dama dija bata sa fushi ko fada akan maganan ba amma Wasu siraran hawaye taji suna neman taruwa cikin idanun ta,kuma gashi tasan bata da lokacin dogon magana shes sure duk inda su junnut suke ayanzu sun damu.. kawai sai ta mike tace dija, ni zan tafi kawai Idan ya dawo zan tambaye shi sai inzo miki we wll talk about it.
Cike da nuna damuwa dija tace no way...babu wani jira a lamarin nan bahi
Nidai kawai kice kin min alkawari zaki je yau din nan ko ta phone ne ki tambaye shi matsalar, if not bazan barki ki tafi ba sai kin gaya min komai..
Adan dame tace me zan gaya maki dija...ni wallhy bansan mena masa ba..he is angry at me..fada yake mun in na tambaye shi, and he said that wai gidan shi ne prison dina kuma saiya aure ta...wani hawaye ne suka sauko mata a bazata muryan ya har yana shaking
Cike da mamaki Dija tace saiya aure ta?wacecce kenan
Sai tayi shiru tana goge hawayen ta kamar dama bata so ta firta kalaman ta ba..
#SURAYYAHMS.
Ashe haka aka rage coments a whatpad? Shafin danake so na baku is coming this week for sure..i wll see if its worth it
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top