chapter28


_Thank you very much special fans,good friends,hajiyas, momys,and the very humble writers that sympathise with me on ma recent ill health condition,i feel blessed._

_2⃣8⃣-friends reunite♡_

Acikin motar nasu ma a matse take,Banda jahan data matsa sai ta raka su babu abunda take daga ido tagani wanda zai sauya mata radadin datake ji azuciyan ta

Khaldun baya ma kula su ba dan baima hade mota daya dasu ba shikadai ake jansa ana shi motar yana biyo su daga baya

Da suka isa airpot taga lallai jahan tafiya zatayi ta barta dashi bata iya boye fargaban ta ba sai ta dai daure ta yi mata magana sosai akan subaya.

Jahan dai ta saurarae tane amna ita kanta bata gane komai daga abunda tace ba gani take kamar bahiyyan tana cikin tension,aure babban al'amari ne and this whole thing is new for her ahakan dai ta barshi ta shiga lallabata da maganganu masu sauki

Tace kar ki damu da subaya.. .she is very emotional, hala idan batayi hakan ba bazata iya rabuwa dake ba ne..i know how much she cherish you ni zan kula maki da ita and da ta sauko ita zata zo miki first visit a abuja! Ok?

Hakan yasa taji dan dama dama jahan ta bata wani warm and cormfoting hugs...sannan ta damka ta hannun shi with her eyes directly odering him ta take care of her .

A haka suka bar kano suka dauki jirgi zuwa garib abuja,kowa na harkan gaban sa bata kallon inda yake shima baima san da ita ba .

Da suka isan ma Awani private lodge mai tarin sojojin navy na da kasa ya fara sauka sai ya aje ta a wani daki ita daya yayi gaba abunsa

Anan tayi ta zama tana juye juye Babu abinci babu ruwan sha babu komai kuma Bata sake ganin sa  har sai chan data gaji ta dan fito ta aika a aka kawo mata abu tasa abakin ta

Anan take ganewa ashe ma meeting yake yi da chief security adviser un behalf of sub marine security operation na kasa

Tabe baki kawai tayi ta koma ciki,snack din da aka kawo din tasa abaki taci sosai dan shi ya dan bata karfin giwa har tayi wanka tayi sallah sannan ta cire kayan jikin ta tasauya da wani simple material gown baki mai laushi, dan karamin roll dinshi ta yafa tayu zugum yanayin bakaramin daukar pale mood din ta yai ba

Ta na zaune a hakan jin kadan sai ga wayar ta na kara,ganin jahan ne yasa ta dauka da wuri tana mai sauke ajiyan zuciya ... sunyi magana ba mai yawa ba,anan ma koda ta tambaye ta akan subaya jahan ce mata tayi ai subaya ta fita a gidan dan itama ta dawo bata same ta ba

Haka dai suka kare wayar,cikin ranta cike da tunani kala kala,tunowa da cewa dija na abujan yasa tayi hanzari daukar wayar zata kira taji Just as she was about to call,sai ga budewar kofar shi

Kashe wayar tayi da sauri ta dago sabida jin shin akanta datayi bazata ya dan buga mata zuciya,baice mata uffan ba itama haka

Suna hade ido ta kau da nata sai taga har yanzun fushi yakeyi,and she just can stand his furious looks.

Ko gama juya maganan batayi ba taji voice dinshi yana cewa  "Inkin ga dama sai ki fito,..am leaving now... Ta dago kai kafin ta ansa shi har ya bar wajen,tabe baki kawai tayi ta mike kayan ta kawai ta daga ta fito dashi waje masu aiki suka karasa sawa a booth dinsa

Duka a bayan seat suka zauna Tana daga gefen sa kanshi na kallon dayan side din ta waje

She just wonder whats wrong with her own sa'ood amma haka kawai yanxun itama take kallon shi da abunda ya gaya mata jiya..

Cheap,i hate you
Tayi siririn asirtaccen tsaki.
 
A haka Har suka kai bakin wani katafaren gini irin ginin gidan jahan sak amma yadda aka tattale shi da uban kwalliya zaka san kwanan nan ma aka shige shi

The house is full of law and oder .

kowanni maid  namiji da na mace suna sanye ne cikin wani yadin atamfa blue da dankwalayen su yadin fari kamar kuyangan gidan sarkin gabas wanda Dinkin ne kawai Yake banbata su da kuma matsayin su.

Da haddadiyar GTR din su ya tsaya tun kafin su sauka akayi anoucing isowar su achan sashen jahan khatun ,her majesty dilshad khatun din ma tana cikin gidan,itama tazo zaman wucen gadi ne dan wannan karo ne na farko da suka taba banbanta gida da kasa tsakanin ita da yarta jahan khatun

Dan haka babu tantama The atmostpher is filled with reams of oficiality and
Royal sophiscation.

Kowa na dar dar,  juya kai ta glass bahiyya tayi tana kare ma ta wajen gidan kallo

Dayaga ta bashi bayan alaman hankalin ta bai wajen sa wabi takurarren tsaki yaja bai bari ya sake  juyowa ba yace mata
Ke,sanda ta waigo a razane ta daga ido tana kallon daurarren fuskan sa

Wani warning taji yana kashe mata yana cewa saura kije ki gaya ma wani cewa ke matar aure ne,sake maimaita kalman ure nothing but my maid din shi ya sake buga mata zuciya ta tsaya duban shi ranta a dan bace har ya sa kafar sa ya fita bata ko tanka masa ba

Cikin ranta tace Kar nace ni matar ka ce?Akan me...inji dai ance nan ma gidan naku ne..to ai muddin auren nan ya auru i think yan uwan ka ma sun sani

Ita tayi tunanin hakan ne amma Ko  kadan bata san jahan ma tace kar khal da alhaj hamood su fadi auren yanzu da wuri ba

Jahan tasan halayen su dilshad sarai,zasu iya daukar dumin da zaisa a cutar da su duka, sai ta yanje shawarar cewa to su bar komai a rufe har sai an hadu gaba daya awaje daya sai a warware maganan

Kowa dai acikin su na dan fargaba Musamman akan alkwarin saood da junnut,duk dama sunsan dan saood ya aure bahi ba haramun bane
Anma ko kadan basu so ace dilshad tana musu kallon kamar sun hade kaine sun ketare dokan ta

Toh Da shike dukan su ayanzu kowa nada nashi uzurin kusa,alhaj hammod sai yace ajira khal yana dawowa daga mission din shi shima zaizo har kano ya taho da su jahan Aarah abuja sai ayi maganan 

Yanzu dai a matsayin Su yasu suka san abunsu

Awajen subjgan aarah auren sirrin akayi ma khaldun saood da bahiyyah.

khaldun tuni ya fita a motar ya barta ciki yana takawa security sukayi yuuu suna biyo bayan sa ana taka mashi baya,shika dai yasan abunda ke damunsa dan bai ko daga ido ya kalle kowa ba Cikin takun sa na kasaita da jan aji ya nufi wani part na daban wanda ma ba a asalin main house din bane

Ita kuwa bahiyya Tun daya tafi ya barta a motan ta rasa mezatayi guda daya,dan Leken  shi takeyi har ya bace ma ganin ta,kafin ta farga sanda taga yan mata biyu sanye da unirfom agaban ta suna mata fadan ci kamar zasu cinye ta

Ure welcome ur highnesss...

Wannan ya rike nan wannan ya ja nan
A Tun bata son daga kai har suka fara bata takaici

cikin ribibin gaisuwar nasu tuni aka Rabata da duk wani kayan ta aka kai side din khal da bata ma sani ba

To da ta fito sarari babu wani bayi mata She was quiet confuse on where to go strght ahead,sai ta yanke hukuncin bin inda taga ya shige in dazu,kowani gyara mayafin doguwar gown din tan batayi ba ta rike sauran a hannu tana takawa ladaf ladaf cikin tsarin da bazakace wani abu yana damun ta ba

Gaban katoton golden gate din ta isa bayan amsa gaisuwa batace da kowa uffan ba ta shiga daga ciki,kallo ta kare ma wajen aranta tana mamaki sai taga a ta Wajen ne dai kawai akwai security amma tana sa kafarta cikin farfajiyan gida taga shiru ne babu kowa sai lafiyayyar fili da home street layout masu tsananin fallasa tsafta

Tana daga ido wani sharbeben kuma boyayyen mansion ne ya bayyana mata kansa,amma da alaman ya bata baya dan babu kofofin dayayi kama da na shiga

Dan juyi take yi tana dan kifta idanun ta..."Wowww...zuciyan ta dake bugu slowly ya fada gashi wajen ya dada yankewa da tsitttt babu ko kuda sai tarin qamshin garden flowers da sanyin pure breeze

Ta dan duba setin mansion din ko zata ga doors bata gani ba hakan yasa ta tabbatar nan ta baya ne ko maybe tayi missing hanya.

Kaamil daga chan saman benen yana amsa waya shiya fara hangota tana tunani tana dan dube dube.
Wani irin dakatawa yayi ya kare mata kallo sosai

Maids sunce masa khaldun ya iso da wata yarinya dama shima sauri yake ya je site dinsan su gana...but seeing this angel rogjt now akasa yasa ya kashe wayan sa da sauri Ya sauko a guje ya bullo ta kofar main gate dake kasanr benen da bata lura dashi din ba har ya shiga asalin cikin gida

"Jayyyyy...jaaay..junnuttttt..junnut..ya shiga kwalla mata kira yana cewa kizo kizo kizo

Yadda ya zaburo yake kwala mata kiran tana chan sama ne amma Sanda taji ta tsorata

A gurguje take kokarin saukowa  tun kan ta karasa cewa menene!
Ta ji ya cakumo  hannun ta feeling so excited yana dan dariya

Yace mata junnut ques what,?

Batace komai ba Sai ta tsaya kallon shi tana turo baki

" mutumin ki is around kuma yazo mana da wata kyakkwar angellllll. .
Ke kinga kyauun ta?

U know what!i just cant wait to meet her kema fa dole ne muje yanzun ki ganta

Dan dariya junnut tayi tace what nonsense kay,yanzu akan wata yar mace kake kwalla min kira!
Tace hmm ai nasan ruwa bata tsami a banza,.

But Murnan jin ance khal dinta is arond ma kawai ya sa mata dadi da nishadi So ita Bata damu da yarinyar da yake magana akai ba amma danta biye ma shirmen nashi sai ta bashi hannu suka sauko tare har waje suka shigo ta dayan mansion din Suna surutu suna takowa daga matakalan dake cahn sama basu ma lura ba

Da kuwa har sun zo zasu wuce inda kaamil yake tsaye dazun da ya hango ta,sake ganin ta awajen da yayi yasa ya dawo baya sai ya jawo junnut baya itama yace heyyy heyy Look at her,gata chan wallhy har yanzun bata bar wajen ba

Da sauri junnut ta waigo,suka isa  ta Jikin balcony stand suka kama dukan su suna lekowa kasa amma sai basu ga fuskan ta da kyau ba

A lokacin bahiyyan itama ta juya tana magana da maid din da ta kai mata kaya ne akan ko zata kaita masaukin ta da khal maids din kuma ta turje akan doka ne basu shiga side din sau biyu saida cikakken izinin sa

Bahi sai ta rasa me ma zata ce ma maid din ta saduda ta kaita,gashi ya hana tace ita matar sa ce sai kwana take mata sabida bata san ko ina ba

Ganin haka yasa junnut ta dan ja tsaki tace nikam mu tafi kawai....
Look how She is just talking to a maid bana tunanin tana da aji

u know i really miss him ni shi nake son gani ba wata babe ba....

Shikuwa kaamil ba yadda ya iya ne kawai amma haka kawai tunda yagan ta yaji zuciyansa yana ta zumudi

yace ok ok muje mana junnut sai ta shiga gaba...Aikuwa suna juyawa wani karamin short gesture ya wuce walau ta idanun ta ya nuna mata kamar barin gefen fuskan bahiyya

Wani dum dum taji a zuciyan ta atake taji tana neman tsayawa chak

Kaamil da ke gaba sai zame sai yaga junnut ta dakata sai yace ke ya haka?mu tafi ba basauri kike ba?

Ko kula shi batayi ba ta koma kan step din da gudu again tana dada kare ma bayan bahiyyar kallo,bata san me ya sata ba kawai sai taji bakin ta ya furta bahiiiii?

"The feeling was so  increasing...sai ta dada cewa Bahiyyyahhh...ita ma bahi tuni jikin ta ya bata kamar wani abu na daban zai faru amma sai ta basar
aikuwa 2secnd bata kara ba ta juyo not looking up  ita dama environment din tafiye kallo cos har yanzu bata lura da mutane achan saman ba

Da junnut taga ita dince Wani electric shock ne taji ya bi jijiyan ta agigice ta ware idanun ta,..asif she was dreaming in a broad day ligh

Atake jikin ta ya fara rawa dakan shi
Tana wasu irin  kakarin kukan murna

mamaki ya sa kaamil ya dawo gaban ta yana ta binta ido

Sosai ta kafe ido tana kare ma bahi kallo dan ta tabbatar ba mafarki takeyi ba.

bahiyya tana juyi zata bi bayan maid din itama dan ta nemi mafita makanta

A haukace Junnut ta wani daka tsalle in clean exctiment takarkrewa tayi ta kwala kira
bahiyyyahhh...bahiii.
Kamar wanda zata cire magwagoron ta

Jin karar yasa bahi ta dakata Wani rassss kanta ya buga Tuni ta waigo a tsorace dan ba tantama ta gane muryan junnut din ta ne

Da ta waigo bata ga kowa ba Sai ta yi saurin lumshe idanun ta ta rike kirjin ta dake faff gaff da sauri duk abunda take yi alokacin junnut na sama tana kallon ta

Hawaye ne suka wanke fuskan junnut Wani birkicewa tayi cikin murmushin murna da ko kaaamil bai taba gani akan fuskn ta ba

Sai ya riko hannun ta a slow. ...yace junnut dama kinsan ta ne,..batayi saurin amsawa ba sabda ta wani lumshe idanun ta data itama

She saw how bahi is reacting righ now ta kuma gamsu cewa lallai bahiyya bata mance da amana ba.

Kamar wance ta haukace ta xabura ta tsala ihun murna  tana kuka at same time,after five years of silence and pain,tuni tabi ta kankame sa tana cewa kaamil bahiyya ta ce fa,..she is mine...what im i even waiting for...

Jin sautin ihun da murnan junnut ya dan dada jan hankalin bahiyyar sai ta shiga zulumi tana dan dube dube har wani abun naso yace mata ta dube sama amma tana daga kai taga babu kowa nan ba dan Tun kan kaamil  yayi gaining balance ya rike junnut ta ture sa ta arce aguje tana saukowa she dint even know  when ta zubdar da takalman kafafun ta
Bata tsaya ba sanda ta iso kasan ta ganta da kyau atsayen

Lokacin ita kuwa Bahiyya har tagaji da dube dube ta dauka ko kunnen ta ne kawai yake neman haukatar ta sai ta juya zata fita

One good step ta dora sai ta taji muryan kuma still a kusa da ita,. 
Cikin sanyi ake kiran ta

Bahiii...bahiyya..

Duk da daukewa chak datayi bai hanata wani irin waawan juyowa

Sai charaf suka hade idanun su su,wani irin shock ne ya debe su na mamakin ganin juna da kuma mamakin irin wajen da suka hade ayanzu

Sunfi minti ashirin a haka har  kaamil ya karaso wajen suna ta kalloin junan su

Wasu rikitattun hawayen kewa mamaki da kauna duka ya wanke fuskan su

Junnn....nut???..bahi ta fada da kyar muryan ta kamar zai rabu da jikin ta dan rawa

Wani kasallalen murmushi junnut tayi tana dan kokarin share tears din tace yess yess nice bahiyya.... please come ....sai ta ware arms dinta duka biyu ta fashe da kuka...

Da wani irin force of atraction suka taho jikin juna aguje suka kankame kansu cikin wani irin mugun shauki.

Dada kankame juna sukeyi juyi juyi bakajin sautin komai sai na muryan su

Kaamil yayi still ya nade hannun shi a gafe shikam yana kallon su in total confusion har sanda abun ya dan sake su

A hankali bahiyy ta zare jikin ta dago junnut din tana kallon ta hawaye ne masu nauyi ke sauka akan maraitaccen fuskan ta ta dora hannun ta ta shafa fuskan junnut din gently...murya na rawa tace junnut ashe kece...ya ilaaahi.....dont tell me this a dream..sai tayi saurin sake ta ta juya mata baya tana lumshe idanun ta..

A hankali junnut ta karaso ta wani kwnto akan gadon bayn ta tarre da knkame ta

ji kawai tayi ta zagaye jikin ta tsam da hannun ta cikin yanayin shauki ta rungumo  ta baya..

Tace ba mafarki bane kawata nice ....junnut dinki ce.... I missss you soo much bahi,..banyi tsammani zan ganki anan ba. .nor now

What are doing here
Sai ta juyo da bahi suna kallon juna kowannen su na kokarin controling emotions dinsa..

Dan ajiyan zuciya bahyy ta sauke tace Nima yanzu nazo...
Bansan nan wajen ba...i came with..

Junnut tace its ok,ko waye ya kawo ki yau dai bazan dena gode masa ba
Cos he brough me back to bein who i am when i use to be with you

Come,Meet my brother ...sai ta jawo hannun ta zuwa gaban kaaamil wanda ya dade yana ta kallon su kansa adaure. .

Acikin nitsuwar da baisan junnut dashi ba tace Kay..wannan itace zuciya ta..bahiyya ta.. my best and childhood friend infact my blood sis...

Sai Ya danyi smile a hankali yana binsu da kallo Yace yeah i can see that.,ure welcome zuciyar junnut ....ya mata murmushi itama ta mayar mashi...i love this ur bonds fa,. Like ouchhhh junnut kece?...ai saura kiris kusani kuka ..

Yanayin yadda yayi maganan cikin shaukin kwaikwayo da unserious feeling sanda suka danyi masa dariya suna jin kunya

Zo muje ciki...ta ja hannun bahiyyar suka fara  fita gaba daya daga shashen

Kaamil shima yana tahowa yana binsuu da ido yana wondering irin yanayin shakuwar su

Bai taba sanin junnut zata dawo wata daban lokaci guda ba sanda yau yagan ta da wannan yarinyar!

Those innocent tears,the bonding and pure respect,its get to him har brain dinshi yaji lamarin su

Yace kai wannan yarinyar She must be very speacial one...junnut tana matikar kaunar ta...gata kyakkwa Uwa sarauniya

Su kuwa tafiya suke rike da hannun juna junnuta tana cewa

Nan gidan mom dina ne kanwar mahaifiyata muma ai jiya muka dawo kasar nan,,yanzu dai bana so na cikaki da surutu kinga kakata na nan lets go and meet them first kafin naji lpyar ki ko?

Murmushi bahiyya tayi suka wuce basu sake tsayawa ba sanda suka shiga wata albarkatcciyar waje mai mugun dauke hankali

Thy are two colours that speak of royalty..

"purple and black"

Ko ina ya dauki white wall with dark edges,daga gani ba tanbaya tasan nan kam ba arziki bane kawai harda mararin sarauta

Bayi da maidens na ta kaikawo junnut na rike da hannun ta har suka kai gaban wata hamshakiyar mata dake kime akan wani jahilar royal puple chair mai haddaden golden grown crown head

Ganin ta ma kawai ya isa gaban ka ya fadi sau dari,dan haka bahiyya ta zame hannun ta a slow ta dan ja da baya tana kallon yadda junnut da kaamil suka isa gaban ta.

Ur majesty..
Grand ma ...matar cikin mulki da nuna isa mai sanyi tayi murmushi ta dan shafa kansu

Junnut tayi nuni da bahiyyya,at same time tana gayyatar ta tayi gaisuwa...har kasa kuwa ta rusuna ta gaishe da dilshad .   .wanda tsaban son ta san wacece wannan din ya sata dasa mata kasaitatun idanun ta

Grand ma wannan itace bahiyya,kawata ce tun muna gida chan tare da ammah

Tun kan Dilshad tace ohhh sai sukaji muryan jahan khatun akansu alaman ta shigo ne unxpected
,Aina kuma lika samo ta...ta fada da wani irin muryan da bai nuna saukin kai...

A dan tsorace bahiyya ta juya ta kalle ta,sai taga suna mugun kama da junnut din,babu bata lokaci ta rusuna tayi gaisuwa

Wani kallon sama da kasa tayi mata kallon raini da kaskanci kafin ma ta amsa cikin wuyar ta..

Haka kawai taji yarinyar bata mata ba musamman tasa idanun hasada da kallon baki isa ba..

Nan junnut ta shiga basu labarin ta sosai,she was so excited amma sukam abun bai wani dara su ba

Kaaamil ne ma yace musu ai da khaldun tazo gidan sannan dilshad tadan wayance suka dena bata cold looks

shi sai ya zame ya fita zuwa site din khaldun din dan kuwa yasan ko nan ma dukan su awajen jiran sa sukeyi

Junnut kuwa tuni taja bahiyyya takai ta chan sama dakin ta,its a very big apartment on its own, kalar tsarin kaya duniyan da aka zuba mata ido bazai iya tantancewa ba
.
A kan sharbaben tufted and heavy matress din ta suka baje,after so much conversation and happy moods..

Nan junnut take ce ma bahiyyan ai jiya suka dawo nigeria daga persia, kuma dama tana so ne idan sun huta sai taje neman ta a kaduna wajen ummah surbajo

Duk abunda junnut ke ciki arayuwa na ci gaba da cikar burin ta sanda ta ayyana ma bahiya step by step,har labarin hilda bahi taji amma bata gaya mata komai akan khaldun ba

Bahiyya ma ta bata labarin yadda destiny yayi da rayuwan ta zuwa gidan jahan Aarah,har junnut ta gane cewa ashe jahan Aarahn da bata taba gani ba itace uwar rikon bahiyyar ta

Duk dama taji labarai munana akan jahan Aarah daga wajen su dilshad,amma sai yau taji tana son ta da bahi ta gaya mata yadda suka rike ta da amana da son gaskiya.

Ashe kina london?
Ai dana sani da wallhy nima chan zan koma

Bahi tayi dariya tace ai na gama,shiyasa ma kika ganni anan

Junnut tace nikam ban gama ba ina ganin ma kamar ban fara ba...ina first degree ne yanzu....my mum tace zanyi masters kafin nan musan nayi.. .i still wanna be that girl kinganne,irin matan nan dai da idan babu su babu duniya,kuma babu sha'ani..tana ta zuba

Bahiyya tana kallon ta tana murmushi chan tace junnut Har yanzu baki ko zanca ba,Ure still that mrs ambitiuos girl..

Wani rau da ido junnut tayi ta mike tsaye tana wani juyi cikin jin dadai,tace look at me bahi ke yanzu bakijin dadin yarda rayuwar muya dawo,?ki kalli fatar jikin ki..duk dama yanzu naga kin kere ni a kyau but i do have evrything im dreaming of saura kirissssssss sauran ma jira n suke yi.

Bahi tace Allah ko? Wani dariyan sukayi  suka dan tafa

Junnut bata damu taji maye alakan bahi da khal ba tun dama taji ance mahaifiyar sa ce tayi adopting din bahi ne

....she just assume thy are con-curent siblings babu wani connection

For the main time
Bahiyya taji ta cikin sabon yanayi,tace lallai Allah shike yadda yaso..if not bazata taba kawo cewa yau zata ga junnut din ta ba

Anan junnut ta rike ta dam hira kala kala...kowa na fadan nashi damuwar

Sirri biyu ne a tsakanin su,bahi bata fadi tayi aure ba ke junnut bakice kinada mijin aure ba

Sannan A duk damuwar du da suka tada haka ma bata gaya mata ko kadan daga labarin zaman ta mai muni daya shafi sadat ko khal achan gidan
Ba

She was just awwed dayadda taga junnut ta dawo,ga guntun skirt cinya awaje,ga wasuxuka zukan nails da sukaji red tinted curtex..tasan dai junnut tana da dogon gashi irin nata amma kuma
attchement ne akanta ayanzu.

Sunfi awanni suna magana non stop,haka junnut ta matsa har bahiyyar ta yi amfani da bathrum din ta tayi wanka cikin nishadi da kewar juna suka zauna akayi serving dinsu abinci suna ci suna hira

Bangaren khal kuwa gaba daya ya rasa meke masa dadi game da yawan tunanin bahiyya,..he wish zai iya jin ya tsani bahiiya amma its not feeling like it.. Yanzun haka fushi ma yake yi dakansa amma shikan sa bai sani ba

He look down and angry,dandanin murmushi babu a fuska

Side din dama nashi ne shikadai just like yadda yake agidan jahan mahaifiyar sa

Yanzu ma Kiran ta ne ya tuno masa da cewa bahiyyar bata fa biyo bayan sa ba,.

He was like ohon mata inma taje wani abu ya same ta shi babu ruwan sa.

Wanka ya fada ya sauya kayan sa zuwa simple long sleev shirt da trousers,yana famar combing kansa agaban mirrror saiga kaaamil ya shigo

Ba yabo ba fallasa suka gaisa.. Shikam ya rasa meyasa yaketa famar zumudi akan bahiyya...

Not too long ya fara zubaa ma khal labarin duk abunda ya faru

Shida baiso yanajin maganan ta amma wannan ba karamin buga masa zuciya yayi ba..

So bahi and junnut are best friends!!

Ya maimaita wannan maganan a brain dinshi yafi sau goma..

Witout showing any major concern,ya amsa tambayar kaamil dake neman sanin hadin shi da bahiyyar.

Sai kawai Yace masa shima hadota da ita akayi,acewar sa jahan Aaarahs adopted doter ce

Kaamil was like wowww ...kace ma yar uwata ce

Ko kula kaaamil baiyi ba dan kuwa
Ba karamin zafin yake jin aransa ba musamman inyana tuno ranar daya zage yake bada kaamil din labarin ta

Cikin zuciyan shi cewa yake
She is the twinkle i wanna show you..but not anymore ...not eva..
I bet im not the guy
Nayi nadaman bude zuciyata ma wata yarinya kuma sai ta san dawa take yi

Tare suka fito dag sashen nashi kaamil na taka nashi zasu je suyi gaisuwa agaban su dilshad

Hira sukeyi kadan kadan,nan yake jin cewa ai bahiyyar tana can wajen junnut so bai wani damu ba

Isar su ya fada yayi gaisuwa,cikin so gata da nuna kaunar su suke tarairayan sa

Shima sosai ya nuna jin dadin sa game da dawowar su nan nigeria...

Musanm ma zuwan ita kakan nasu dan ita tassa shi har ya mata alkwarin cewa zai daga tafiyar sa dan ya mata kwana biyu.

Dan itama tafiyar zatayi nan d wata guda

Hira sukayi mai tsayi tsakanin su su hudu,basu ko kawo maganan junnut ba bare bahiyya

Most of their talks is eida politcal or official har dare yayi kowa ya watse zuwa site dinsa

To Kiraye kirayen  jahan din ne yasa bahi ta dan matsu dataje taga inda suka sauka da mijin nata..

Ga Junnut ma ta gama sarai zasu kwana tare amma  sai ta ki sam Duk dama yaune rana na farko da junnut ta taba mancewa da shafin khal kawai dan taga bahiyyar ta

Nan ma da kyar suka rabu,Har nite gown mai kyau ta sa ta tasa dan dole tayi mata kwalliya ta zaunar da ita ta dada gyara mata kai tun anan suka fara musun yadda kowa yayi wayewar sa
Junnut cant beliv that bahi har yau batayi irin budewar idon da ita tayi ba,...a haka dai ta hakura ta shirya akan zata raka ta zuwa site din khal

Wanda ko rabin shiga basuyi ba jahan khatun ta raba su da kira

She just dont like the girl,sosai ta raina kurwan bahi..wani gani gani take mata
Tana mata kallon kaskanci da rainin wayo

Cikin ranta tace hala ma yar bola ce aka dauko aka laka ma miji na dan tunda akace mata daga wajen jahan Aarah ta fito ta ji yarinyar sam bata mata ba

Ko yanzun ma ta dade tana kallon su daga sama Kyaun bahiyyya har yana dan raxana ta.

Haka kawai takejan tsaki,tsaki irin na hassada da nuna kyashi, badon ma khal ya bada oder lallai bahiyyar dashi zata zauna a site dinshi ba da chan wajen gidan baki zata sa akaita

and she tot that wannan kawancen nasu a wajen ta is baseless aganin ta junnut din ta bazata taba hada hanya da kaskantatun kawaye irin wannan yar ba

Bahi kuwa tsoro ma take ji in taga irin kallon d jahan khatun keyi mata .gaba daya bata do su cika hade idanun su

Datakira junnut din ko ta dan hada ta da maid,haka bahi ta lallaba dakanta ta isa Akan gobe da safe duka zasu hadu

Tafiy takeyi tana gode ma Allah tana kuma jin fargaban haduwar ta da khaldun

Ashe wai yau ne first weding nite dinta?

Tsaki ne ya kufce mata haka kawai bata san dalilin shi ba,dawowar junnut rayuwan yau ma kawai ta yasata taji wani sabon karfin gwia da  karfin zuciya

Wajen shiru babu kowa,amma da shike the same design ne da gidan su,babu tantama ta san wani kofar ya kamata ta shiga ta same shi

Tana tabawa kuwa taji damm alaman an kulle da lock ta ciki

Nan Tayi tsaye tana knocking almost 1 tana abu daya amma bata ji am bude ko an bada izinin a shigo ba

Yana jin ta dan Yana zaune akan gadon sa ne yayi shiru yana fama da tunani kala kala aransa sa

with each pain dayakeji shima so yake  ya mata wani abunda zata ji abunda shima yake ji

Ganin ta tsaya har taji ba dadi tuni Ranta ya baci ga bacci ga tsoro,chan dai wani abu ya sa ta ta zaga ta baya..aikuwa tana bullowa anan ta hango shi ta plain glass wall dake hango kan gadon sa direct wanda ya bada wajen mermaid world look mai gaba daya..

Wowwww tace aranta tana ware sleepy eyes din ta da kyau....daga dakin nashi zaka iya jan glasss ka bullo cikin backyard din room din wanda aka kawata shi da wasu marayun flowers masu gamshi da tsari gawata shekikiyar blue water pond mai shape din kwakwa white swan ne suke shawagi aciki

Bata ma damu da kallon cikin room din ba tukuna ta tsaya kare ma wajen kalllo Sanda ya ishe ta sannan ta iso gaban glass wall tana kallon ciki tana neman ja dan ta shigo. 

Its heavy ..nauyin shi yasa ta kasa motsa shi...gashi yana da yawa sosai...2 coners ya rufe...

Anan Wani zuciyar na ce mata ta masa magaña hala zai jita, but
Ganin ya diro akann gado yana dosowa ta inda take yasa ta dakatawa daga kokarwar da takeyi da dooor din ta tsaya kallon shi..

Wani irin kallo suke ma juna ta glasss din as he was coming vwry closer fuskan sa babu alaman rahma..

In yana ganin ta Zuciyar sa taba masa wani irin zafi

Son ta yafi rikita masa tsarin yanayin sa fiye da abunda ke tsakanin ta da subaya

Ita kuwa kyau ya mata sosai,duk dama tana yar tsama da shi but ta shagala tana kallon sa cikin wani yanayi...he look soo handsome and gentle acikin white pjams din shi da bai saba sabawa ba

Sai taga ya kama draw open din She tot bude mata kofar xaiyi sai ya dauke kansa tana gani yana danna wani abun god knows meyayi ma kofar amma tabbass dada kullewa yayi

Yana gamawa Ko sake kallon ta baiyi ba ya koma yayi kwanciyar sa tana tsaye tana kallon shi

Kwanciyar sa yayi kamar baisan da wata ba Looking at her straight in the eye ya danna wata remote tuni taga wasu shegun drapery curtain marasa nauyi suna haduwa da kansu suna neman mata katangan karfe daga kallon sa

She was like,kai ka aika na zo amma ka kulle ni awaje
"Wai meye nayi masa haka?cikin ranta ta furta kanta a mugun kulle...to ina zanje na kwanta gashi ko ina yayi shiru gashi batasan kowa ba

Da ta tuno da junnut har ta kama hanya zata sauka chan tsoron haduwa da jahan khatun sai y dakatar ta da ita.

Anan ta dawo ta nemi waje bakin pool din ta zauna cikin wani irin zurfin tunanin da vata san ya akayi yaci mata awowi ba..

....sanyi da rairayi sune suka fara rtsata waje ya dada yayi tsit tun bata so har Ta dan jingina kanta ai kuwa batayi minti biyu ba wani bacci mai nauyin tsiya ya tafi da ita..

Da asubhain fari ta farka a firgice,dan kuwa tsaban sanyin daya ratsa ta ji take kamar hancin ta ya toshe don bata iya numfasshi da kyau

Wajen ta dada karawa kallo wani irin tsoro na shiga ranta,da wuri ta mike ta koma jikin kofar still baija curtain din ba .

Kamar zatayi kuka ta koma gefe ta tsaya,haka ta dinga jeka ka dawo tana leke ko zai ma ji ajikin shi,amma sai taga har gari ya waye bai waiwaye ta.

She was sad and confused,dan haka tayi timing lokacin fitar sa sallah haka ta hakura ta zago yana fita ta shiga dakin

Ta bincika ashe ma ba anan aka aje mata kayan ta ba

To where is my room?...ko dama daya kawo nin banda daki ne...

Lallabawa tayi cikin dabara irin na mata ta dauro alwala ta gabatar da sallahn safiya,bai shigo ba sai ta fice ta shiga duba kayan ta dakuna uku ne asite din da kyar ta samo wanda kayan nata ke ciki

Ohh Ahamdullhi,ta fada tana zama agefen sharbeben bed din,aranta tana cewa ai da ta san haka ne da ko kadan bazata kusa da inda yake ba

Nan tayi wanka ta saka normal material gown na wata lush material
Mayafin shi tayi rolling akanta sannan ta samu damar fitowa

Allah ya taimaka ta gane hanyar dakin junnut toh babu bata lokaci ta nufi wajen

its 8.00am inthe mrning amma tayi knocking shiru

Sai can anjima aka zo aka bude mata kofar,...junnut din ne atsaye sanye da wata figigjyar nity alaman ma bata ko tashi a baccin ta ba bare tayi sallah

Da har ta dago da fuskan rashin mutunci but dataga bahiyar tane tuni ta ware ta jawo ta ciki

Bayan Kare ma dakin kallo bahi tace
"Kar kice min baki ma tashi?
Kinsan karfe nawa ne kuwa yanzu

Junnut tace Ohhh bahi,I know....nifa bana tashi sai 10 ....dokace...
Dan ma kene wallhy
Da sassafen nan mai takurani ai sai angan shi

Haka suka tsaya musu,bahi is shock again dajin yadda junnut take nuna bata wani damu da sallan safiya ba,abun ya dan daga mata hankali

Is this part of wayewar?koko wani abu ne daban ya juya mata kan junnut din ta.

Anan dai suka karace zaman su,har junnut tayi wanka ta shirya suka ci first breakfast which is always a hot coffe
Ko wani fresh prepared juice .

Gamawar su keda wiya aka aiko da cewa su fito main parlour

After like 30 minutes suka fito  Tafiya sukeyi atare bahiyya nakan  korafi akan kayan da junnut ta sa

Wani cross fold half gown ne mai tsiririn hannu,daga wuya zuwa nonuwar ta gaba daya abude suke Infact wani sabon gyaran  gashin dokin ta zuba shi ta baya platinum kamar wata lady gaga ,kafarta yaci ubar 5inches sandal ga make up bakin ya haska da red matte lipstick tsadadde

Tace bahi Nidai ki kyale ni da wa'azin kin nan,babu abunda zaki fahimta
Thank god Agidan mu kika sauka,we will definatley sort it
Kema dole zaki dena wannan dresing din

Bahi har kallon ta take Intana magana tana juya mata ido cikin kadadi,dan kuwa wani tsaban rigima junnut ta ke ji dashi

A dai dai zasu shiga fadar wasu maids suka taho kowa na binsu da gaisuwa

Mamakin yadda junnut take binsu da kallon wulakanci da kaskanci still
yasa bahi mamaki most time sai
Tace junnut why?

Ita kuwa junnut Sai ta juyo tadan mata ido irin Shusssh dont say anything gaban wayannan kaxaman zasu raina ni.

Haka ta ja ta suka shiga cikin palour

Dilshad ne a babban kujeran ita daya sai jahan  khatun  gefen ta

Kaamil da khaldun suma a kujera daya suka zauna duka sanye suke da suit din valentino garavani

Wani kallon ya kare ma hannun junnut dake rike da na bahiyya ayayin  da suka durkufa suna gaisuwa

Sai yanzu ya amince da zancen kawancen nasu ya lura duk yadda su dilshd suke bada cold attitude ma bahi junnut bata gani dan kuwa da alaman yau a sama take jin kanra

Ga khaldun ga bahiyya ga junnut

Duk wani kwarewer kwaliyar junnut mashi tayi

Anma Da shike kaamil ne a kusa da shi sai ta koma inda bahiyya take itama ta zauna babu avunda take sai kallon shi Baimaa kula ta ba

bahi kam da bata son daga kai She remain queit for some moment

Bata dago ba sanda taji jahan khatun tana tambayar sa directly akan ta

Bai wani bata lokaci ba ya mata bayanin cewa adopted doter mum dinshi ne..duk da ma bai shiga deep ya mata bayanai ba bangaren bahiyya tasha mamakin sa

So he is serious about this secret weding stuff?
Wato bazai fada ma familishi ni matar sa bace ko?.

Junnut ce tayi masa introducing bahi as kawarta good kawai yace kaamil na dan saka musu baki

Cikin haka sai taji junnut din tana kawo masa hirarrki tana masa tambayoyi wanda bata gane gansu ba

Baicika son amsa shirmen ta ba amma sabida ya zantar  da abunda ke mind dinshi agame da bahi ya sa ya dan sake yana biye mata har su jhan khatun suka ji dadi aransu

Toh Bayan sun fita  falon zaaje cin abincin safiya

To shi khal baya cin abinci da kowa kowa yasan da haka.

Junnut kuwa ganin an ragu sai ta jawo shi ta kuma jawo bahiyyar har gabansa

tace nasan kinsan shi ko?bahi tayi karamin yake tana kauce ma kallon dayake mata...duk dama bai sake fuskan sa ba

Tace dama zan gaya maki tun jiya but no time...i just want to u to oficially meet my future husband tayi nuni dashi tace shine wannan....Ina gama schol Shi zan aura

we are engaged

Da Wani irin kallon bazata mai tafe da bugun zuciya bahi ta kalle ta  tace you...rrr future husband?...bata san sanda muryan ta yayi rawan ba

junnut tace eh tana gyada mata kai tana murmushi

Wani zufa take taji na saukka mata ta ciki Da kyar ta iya furta mata congrats dan Wani mugun faduwan gaba da wani irin ciwon kai su suka taso mata idanun ta dakansu suna rufuwa ,da kyar ma ta bar zuciyan ta harya barta ta daure ta dago ido ta kalle shi dan taga reaction dinshi ko zataji yace wani abu

Suna kuwa hade ido
Ya dauke kansa ya zame ya bar wajen

Junnut tace mata shall we?

Ganin idon mutane akansu yasa ta danne firgicin dake idanun ta suka tafi kan dinning din

Bata wani iya cin abincin ba,duk dama kaamil is tryn his best yaga ta sake

Bayn sun kammala kaamil yayi excusing dinsu ya tafi wajen khal ita kuma junnut ta ja bahi sukaje daki

Bata lura da yadda bahi ta sauya atake ta dawo shiru shiru  jikin ta a sanyaye ba

Zama tayi tana bata labarin engagement din ta da khal from the start tana gaya mata yadda ma tafara son shi tun bata gansa a reality ba

Abu daya ne bata gaya mata sabida bayan hilda da kaamil bata so kowa yasan damuwar ta akan khal

All she want now shine ta bayyana shi wa bahi ta sigar da zata san tayi dace da cikakken namiji

So she lied alot akan yana matukar son ta,har zuwan ta gidan shi a us ta shafa mata
Cahn dai data ga kamar bahi tayi sanyi sai
Tace bahi kina tamin shiru,ko dai mijin nawa baiyi maki bane

Bahi dake jin kanta kamar acikin wuta bata ma iya yin kwakwarn murmushin ba,da kyar tace mata yayi
Junnut kuwa sai labari take tana  dada gwada shi

.....dan shiruuuu bahi tayi cikin rudanin zuci,ganin bazata iyaba tace junnut pls can you excuse me?

Tun kan junnut ta bude baki ta tambaye ta ina zata je tayi sauri ta isa bakin door ta bar dakin

site dinsun ta nufa cikin sauri tana shiga dakin ta ta zube akasa wani irin azaban kuka ne ya kufce mata mai dauke da radadin kishi da zafin soyayya.
#SURAYYAHMS
F

I will keep posting from monday insha Allah..

SHARE💋

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top