chapter16


_1⃣6⃣-london♡_

Bayan kusan kwanakin wata guda junnut ta kammala jarabawan ta na gaba da primary.

Anan suka sata agaba da huduba marasa amfani,domin kuwa babu ta inda kalaman su yake karkata taje face rudin duniya

Jahan khatun ce ta dada zurma zuciyan junnut har ta amince cewa ita dib mace ce mai tsananin daraja da mulki dan haka bazata ta cika sauke kanta
Kamar sauran mata ba

Musamman da akan nuna mata hoton khaldun sa'ood ake kuma jaddada mata cewa nan gaba shine fa mijin ta.

Doka ne junnut in taje america bazata yi saurayi ba dan haka kudin sosai aka sake mata wanda shi kadai ma ya isa ya dauke mata duk wani sha'awan rayuwa da wani wanda bai kai ta ba dukiya.

Toh A Washe gari da asubahin fari jirgi ya tafi da ita xuwa chan united states.

Bangarena kuwa tun ranar da nagama waec jahan Aarah ta gama min bayanin komai a nitse.

Big sis subaya is all excited cewa zan koma zama da su amma sabida mijin ta sadaat sai kwata kwata bana jin wani dadi

Dadin karawa ban taba tunanin son da jahan Aarah take nuna min zai yi tasiri a zuciya ta ba sai da muka shiga jirgi muka taho gidan big sis subaya a saudi arabia.

Gaba daya sai naji ni cikin shaukin rabuwa da ita

I was quiet for sometime,bana fiye motsawa kamar ba yau na fara zuwa kasar waje a rayuwa ta ba.

Duk wani zumudi da jjc yaki zuwa min,big sis ce take ta famar jana ko ina tana nuna min wurare.

Saudi arabia its a perfect place but i just cant wait to go to my new school in london.

Zaman sati guda danayi da su sai da naji nagaji sosai,sadat is alwys on my nerve ga big sis gaba daya bata da gane abu,abun nata ma sai gaba gaba yake yi.

Yanzu gashi har ya tursasa ta muna cin abinci tare har dashi a tsakiyan mu.

Haka zaiyi ta jefo min silly looks,ba dama na dan kware da ruwa sai yafi kowa daga hankali awajen yi min jaje.

har naji nagaji nafara ina shiga kitchen ina taya mai aikin su girki,toh daya gane hakan ba karamin masifa big sis ta sha a hanun sa.

Big sis sai tace min ki daina yawan wahal dakanki tunda kinsan darling sam baya son bacin ranki And i also do not want to see you suffering,"

Ni kuma wanann ba irin kalar rayuwar da zan iya bane
tun ina ma big sis bayani har na dawo inta na min maganan sadaat yace kaza akaina saii dai in yi shiru ina jin ta.

I just wonder when she wll realised all this.

Washe gari da aka ce zan tafi london ji nayi kamar an saka zuciya ta a kankara

Here comes my freedom,Atleast zanci abinci,nayi yawo nayi duk abunda nake so batare da sa idon wannan mijin big sis din ba,araina har na fara harsashen hala idan yaga bana nan zai fi bada hankalin sa akan big sis bani ba.

Da safen da jirgi na zai tashi tare da su duka muka je london din,ga wani uban shoping din da suka mun,tsaban abun takaici sadaat har da kokarin sa wajen siya min inners.

A hakan kuma duk big sis bata dauke sa wani abu ba.

Babban universityn dake london din aka saka ni,inda zan karance full 3 +1yrs nutrition course!

Im just 15;16 dan haka aka damka ni wajen university maiden,don fir naki shawaran sadaat na cewa akama min hotel ko apartment ba hostel ba.

Bansan nufin sa ba amma Har kuka sanda nayi ma big sis sannan ta dan tsaya min har ya amince aka barni na zauna a hostel din.

Besides bansan komai game da london ba,and i need my space.

So nake na bude idanuna dakaina na batare da sa idon kowa ba ko dan domin nasan abunda ke min zafi

Kwana biyu big sis sukayi min kafin suka koma saudia,a hakan ma bata gamsu ba sai da ta nemo min student mate dina musulmai daya daga nigeria sunan ta Khadija daya kuma daga instanbul frm turkey sunan ta jasmin itama duk musulmar ce.

Kafin su tafi a cikin tarairaya big sis take cemin idan akwai matsala na kira mijin ta ko ma na kira ta In babu kuma sai hutu zasu zo su dauko ni

Nace mata toh kuma A haka mukarabu.

Daki na na koma nayi kwanciya ta na dada lumshe ido dan Har Wani sanyin iskan freedom ke bin jinin jikina.
I miss my big sis amma idan na tuno
Ayanxu there is No more sadaat sai naji dadi Dan shikadai ne abun daya takura ma rayuwa ta.

Bangaren junnut kuwa a wani tangamemen condimonium na yayan manyan kasar aka kama mata.

Dogon Gidan sama ne mai hawa shida,site din ta na hawana karshe.

Sai ya kasance Ni ina kasar london,junnut Dina tana kasar America We both exist in 2 different location batare da mun kawo tunanin hakan ba.

And My first day in college was full of abun mamaki.

,sabbin kawaye na da big sis ta jona mu, wato khadija da jasmine gaba dayan su babu tayan baya

Na lura wato shi dan nigeria ko aina yake zaka samu he is naturally upgraded suna da saurin wayewa ga wayo da iya bi da mutane

Khadija yoruba girl ce tana da jikin girma kuma farin fatar ta dan dai daine,jiya da muka fito lecturs naga yadda ta ware tana takun ta hankali kwance tana muamala da kowa tamkar wanda ta san london din kawai abun sai ya bani mamaki.

Nikam ban wani sake jiki na ba,am shy and quiet,toh tunda dija ta gane hakan ta fara sani agaba tun bana so har na fara bin ta ina warwarewa

She has been encouraging to chill,tace ki mance fa nan london ne ai kalar fatar nasu baifi namu ba,and you see this big girls da suka fimu jiki da tsayi duk sa'oin mu,turawa ai girman buredi ne dasu ..

Nikuma na lura da suna da rainin wayo musamman yan first year ace sunga kai ba kalar fatar su ba.

But still some of them are cool,wasun su ma basu magana da kowa harkan gaban su kawai sukeyi.

And jasmine,ita kuma yar kinibibi ce ga shegen iya masifa da kadadi
Shiyasa ma tun a satin mu na biyu aka fara sanin mu a ajin mu,duk wanda ya gaya mana baki sai ta fada masa jaja zir.
Sau biyu tana tada hargitsi acikin filin aji

Nice dai shirun acikin su,amma sabida ina da kyau sosai kuma na fisu tsarin jiki wasu students ma sabida ni suka fiye shiga harkan mu.

Nidai Abunda ya sa na dada jin dadib tarayyar mu shine dukan su suna da kwakwalwa da kaifin tarbiya,ban taba jin sunce muje adult party ba,barin ma jasmine akwai ta da rike addini ita kuma khadija ta ta kere mu a a ilimi da baiwar gane karatu.

After six weeks aka raba mu a activites,sai kowa ya koma yin asalin abunda ya kawo shi,amma da shike same level ne kusan tare muke fitowa sai mu hada hanya nu dawo dormetry.

Su suka sa ni na dan ji dai dai,dan bamu komawa hostel wani bin sai munje yawo iri da iri acikin gari.

A haka Har muka saba sosai aka fahimci juna.

Dan idan nayi waya da jahan kuma suna kusa sai kaga sun karba sun gaishe ta.

Bangaren junnut kuwa rayuwar ta is private,ita kadai ce a apartment din ta dan haka babu mai shiga harkan ta.

At her age anan america sai bata fara tuka kanta ba,driver aka kawo na musamman wanda idan zata fita shi zai na janta ko ina.

Haka take zuwa class ta zauna,high level girl babu ruwan ta da magana da kowa,ga wani irin shegun dreses masu dan uban tsada data ke sawa,she is alwys on 5inchs rock stud,ko designer sandal hills.

Uwa uba heavy make up sai dai tana dan rufe gashin kanta da scarf.

A schl din su sai ya zamto babu wanda take muamala dashi,sai da aka kai kusan 4 month kafin ta hadu da wata princess yar japan.
Sunan ta princess hildah,sosai halayen su ya zo kusan daya
Gashi itama yar gidan masu shine,dan bayan hildan,junnut ita kadaice student din da ake kawo ta school da exotic sport cars kamar su jaguar,aventador,benz sport,wani bin zakaga hilda harda tuko lamboghini.

Toh Da ita kawai junnut ke fita Shan iska,da haka har suka dawo close allies

Basu zuwa wani waje in wajen bai cika sunan sa na manya bane!

Hilda it ta fara koya ma junnut dabiun saka tsadaddun manicure and pedicure irin su black and white diamond nails
Dogayen atachement na human hair da clothing fashion styles na zamani kala kala,suna deban wankan su just like real American celebritys

Kafin kace kobo,junnut ta aje al'adan ta gaba daya ta dawo wankan damammun jeans and trousers,hot lingeries,spectacles,natural gashin kanta kuwa wani bin sai taci rabin season bata ma sanda shi ban

Da ita Hilda gaba daya saida suka haukata college din su musamman da yan mata da samari suka sa ido sosai akan su kowa yana son su san dashi.

Junnut har application of friendship ake rubuta musu,daga nan sai ta koyo iya maganan banza da saurin kaskantar da dan adam,hilda kam A ce dama.

Domin kuwa babu marabar halayen hilda da zarah mj a wani hausa novel na surayyahms da nake karantawa mai suna sakamako.

Da first session ya kare junnut da hilda basu je hutu gida ba,wani extra institution na business enterpneship na yayan masu kudi sukayo registan kansu suna zuwa ana damawa da su
Jahan khatun dataji hakan kamar zata kashe kanta dan murna.

****

Nikuwa da naje hutu sai na yi gamo da rashin saa,ina zuwa saudi arabia kwana biyu kawai big sis tayi tace wai zataje califonia meeting zata dawo in 1week.
Nace zan bita,haka taki fir tace ai daga schl na dawo kawai ma huta

Haka dai na daure na zauna I have to live with that sadat mu biyu kawai a gidan

A rana na farko da ya dawo daga aiki,na fito na gaishe sa zanje dauko abunci yana ta kallo na ban kula shi ba

Dana kawo abincin zan ajiye,kawai sai naji ya kama min hannu na ya ruko a nashi har yana kokarin murzawa a tsorace na dago zan fauce Sai naji Yace...bahi?..ban amsa ba nayi kokarin kwacewa

Sai ya bini da wani shuumin murmushi,wai ke ya rayuwan ki haka ne?

Sai Na share shi Nace here is ur food. .ni na koshi

zan juya kenan sai ba ji charaff ya mike ya chapko ni,"ke zo nan ki fada min labarin london"sai ya dangwala ni akan cinyar sa da karfi dukan hannun sa sun matse ni sosai"

Wani bugun da kirji na yayi alokacin bansan sanda raina yayi mumunan bacin da sai da hawaye suka ciko min ido na ba

Blurting hurtful word na so nayi ko zanji dai dai

But Am still respecting him sabida bai taba furta min komai ba,duk dama duk wata mace mai tunani zata gane mummunan nufin sa akaina

Sai na fauce jikina a zafafe na tura sa na mike tsaye na bata raina na hade rai bance uffan ba..shima tsayen ya mike
Kamar bai san inayi ba,ya kika min shiru ina tanbayar ki,.na kau da kaina gefe tsaki ne ya kufce min,ban hankara ba kawai sai naga mutum ya dada matsowa.
Ni kam tsoro da haushi ya gama ma hatsala ni

"Wani kuka mai sauti na fashe masa da shi,yace meye akayi miki...wont you tell me?labari kawai zaki..
Tun bai karasa ba ya shiga mika hannun sa zai shafo fuska ta,turawa nayi na furta
Ni dai Bana so!!!cikin tsawa kuma a zafafe naja zuciya ina kuka, sai da ya dan ja yana kallo na cikin mamaki.
Magana yake min amma Ban kula ba,Da sauri nabi gefen sa na haura sama bayan na shiga na kulle da key har jam locks

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top