chapter15


Here is how our junnut looks like beautiful ko?i know team bahi wll chock right now lol

_1⃣5⃣-east meet west♡_

Sanye take da plain red material irin dinkin nan na jahannama ga fasinja yana da shape sosai ga zara zaran eagle wings hands an tsaga tsakiyar sa kusa da dunduniyar elbown ta ya bi jikin ta ya mata das.

Zararrun idanun ta ta sauke akan maid din dake biye da ita kafin ta iso jikin entrance din ita kadai

ajikin kofar shiga ta labe tana jin duk wani maganganun su batare da kowa ya lura ba

Ahankali Cikin yatsina fuska tace Aure? Wani garas maganan ya zo ya doki zuciyar ta daya kuma nanata mata aure?a gaskiya ita kanta tasan babu maganan aure aranta yanzu duk dama tana da tsananin burin zama da dream guy wato khaldun sa'ood din ta.

A yanzu kam rayuwa dadi yake mata ta so ace  sai ta gama duk wani karatun da zatayi kafin ta aure sa.. Tunani take tana cewa kanta to whats the rush?

Wani sauke ajiyayyen nunfashi tayi ta gyara tsayuwar ta cikin yanayi na zurfin tunani,chan dai ta dago da wani irin takun kasaita sannan ta yi sallama a falon ta shigo

Kamar walkiya bayin dake fifita ma dilshad suka watse aka barsu su ukun, inda junnut ta ru suna tayi gaisuwa.

Jahan khatun ne ta dan kalle ta sai ta shafo fuskanta ta tana mata kallon nitsuwa mai cike da buri.

"Junnut tace Jahan ina fata lpya dai ko?....da murmushi jahan Tace lpya lau yar gata,har kin fito?.

Gyara zama junnut tayi kusa da kakan ta dilshad tace eh.,

Batare da bata lokaci ba mikewa Jahan khatun tayi ta fara mata bayani babu wani boye boye 

Tace junnuta kina sane da cewa my son,ina nufin khaldun sa'ood zai zo kwanan nan,so u most be ready to welcome him kinsan ranar ne zaku fara ganin juna ko?

A nitse Junnut tace yes..jahan...amma me kuke so nayi in yazo din..cikin son ta saya imanin su ta dan sadda kai cikin ladabi:

"Tell me any thing and i shall do it.

"..dan Dafa kafadun ta dilshad khatun tayi tana wani sake uban murmushi,sai da ma tasa mata Albarka kafin tace ma jahan khatun kin gani ko?yarinya yar albarka thats my girl,"her majesty princess of persia...!
Murmushi Jahan khatun tayi dilshad sai ta cigaba da magana

"Ai Babu abunda zakiyi illah ki nuna masa ke jinin dilshad ce zuriar Albarkatacciya  dawlat khatun.

Sai ta dada riko hannun junnut cikin idon suke kallon juna ta furta mata

...ina son sa'ood ya aure ki,but u most control the game.
Ina so ki dawo zuciyar sa, tunanin sa, da dukan shaukin sa.

Jahan khatun itana ta marmatso tace Yes!! And He is also a prince in this kingdom kamar yadda kike karki ce zaki shagala da wani soyayya, arayuwa komi da lissafin sa akeyi Zaki ga ma yafi soyuwa a raina fiye da dan ciki na kaamil,sa'ood yaro ne mai jinin mulki da kasaita uwa uba kwarjini ga baiwae ilimi kuma Shi daban yake acikin maza..
..Shiyasa muke so kiyi da gaske sosai a kansa..

Dilshad ta dan gyada kai,ta dafa ta junnut kisani Indai mune,toh zamu iya aurar da shi A ko ya amince ko bai amince ba Amma kuma ba ta hakan muke so ke kiyi rayuwar ki ba

Khaldun sa'ood shine matakin nasarar da zanso ace nice zan kafa alkalamin tarihin rayuwar sa ba uwar sa ba.
Dan Uwar san muguwa ce.

Dan Mikewa tsaye junnut tayi cikin nazarin kalaman su,cikin wannan yanayi sai da tayi taku dayan biyu har kusa da jahan khatun sannan ta tsaya.

Tace nifa Ban fahimce ku duka ba!
Khaldun sa'od din yace zai aure ni ne in yazo?

Dan murmushi su kayi dukan su
Jahan khatun tace Ai ba sai kin fahimta ba,ke dai kisa aranki zaki aure sa kuma dole zaki mallake zuciyar sa ke kadai.

Mirmishi Dilshad tayo confidently bata ce komai ba.

Dan rusuna kai junnut tayi Alaman ta ansa ta kuma gamsu,sai ta dago tace yaushe ne auren!

Jahan tace this month zaku hadu amma aure sai ya iso dakansa ya ganki,Ko ba ki shirya bane?

Da mamakin su sai junnut ta gyada kai

Toh menene shirin kuma? Dilshad tace tana binta da ido.

Gaban dilshad din junnut tazo

Cikin sanyin murya Tace ur highness my grand ma Allah ya taimake ki...

your grand dougher is very scared ni gaskiya ina jin fargaba,Shin kina ganin ina da kasaitar da zanyi saurin mallake  namiji wanda har ke kika yaba da kasaitar sa kuma har ayi aure cikin wannan lokacin?

nasan dai kina hankalce da komai,nikuma domin in faranta muku rai zan yi muku komai

sai dai akan shi ne Ni ina ganin aiki ne mai girma a kaina  duba da shekaru na ga ambition dina ga kuma kula da miji
Auren ne naga kamar yayi min sauri..amma in nayi ganganci A gafarce ni,sai ta ja gefe tayi tsuru tsuru.

Sunyi shiru suna sauraran ta sai Dukan su sai suka kalle juna,jahan ne ta maida mata murmushi cikin yabawa tunanin ta sai tace ai bamuce zamu daura maki duk wannan nauyin ba,shekarunkin nawa ne ,sha shida ko?in A sha shida kike ai baki isa aure ba ma.

Ke dai auren ne zamu tabbatar da tubalin sa tin yanzu kafin ki gama dawowa cikakkiyar mace

Ai tsananin kyau kudi ilimi da wayewa shine kasaitar mace kuma duka kin mallake su

Junnut tace toh Soyayyar sa fa!?sai ta sunkuyar da kai alaman kunya

Wannan karon dilshad ce tayi mata bayani.

Tace ai zuwan su
India da akayi akan hakan ne domin kuwa shirin da aka mata a duk lokacin da ta hada ido da khaldun ko da bata masa ba bazai taba iya wulakantata ba.

Sosai junnut taji dadin wannan zance duk dama akwai abunda aka bata ta hadiye acahn toh kyankyami yasa bata hadiye ba kuma sai tace ma jahan din ta hadiye.

ita dama ta dade da fargaban samun karbuwan soyayyar ta a zuciyar shi,tasan dai tana son shi amma bata san ko zata iya nace ma namiji tana binshi ba barin ma da akace yana da shegen kasaita da mulki.

Haka dai aka watse a falon junnut ta koma site din ta

Ita dai dilshad azuciyar ta bata wani ji dadin meeting din ba dan kuwa taso ace khaldun yana zuwa a daura auren sa da junnut inyaso zata karasa karatun ta agabansa.

Amma sai gashi tunda suka hada kai akan maganan da jahan khatun sai ta shiga kawo mata tsare tsare cewar ta

"Zanso ace auren yayi yuwa da gaggawa amma kuma Babban kuskure ne mu bashi yarinya daga yanzu wanda ko sec schol bata mallaka shaidan sa ba

Gashi ni dake duk mun tsara mata rayuwar ta duka,kuma muna so ta mallake zuciyar shi sai yadda tayi dashi

Sa'ood fa ya girma Toh Idan junnut taje gabansa a yarinya me ta isa ta gaya masa yaji?mother tunda kin hada su a spirit world nasan ko shekara nawa junnut zatayi tana makaranta saood bazai kufce mata ba

Toh Wayannan bayanan  jahan ta bayar aka sauya tsarin maganan auren.

Kuma a haka aka shiga tsara rayuwar junnut,da zimman cewa za ahada su amma tana gama karatun ta baki daya za daura aure babu fashi.

Haka rayuwar ta tsaya har Bayan wata guda zuwa lokacin da khaldun saaod yayi alkwarin zaizo persia


Washe garin da zaizo din tunda asubahi aka fara shirin tarbon sa yau kusan shekaran sa uku rabon sa da kingdom dan haka har site dinsa sai da aka kwashe komai aka sake cikewa da sabbi 

Jahan khatun da kanta take kula da komai uwa uba junnut da aka kawo masu kwalliya na musmman domin su gyara ta.

Ita kam ma game  take tayi da wayan ta Dan yanzun ji take babu abunda yasha mata gaba tunda dai ance azai taba wulakanta ba
yanzu rayuwa
Sai yadda ta so zata
Yi.

Washe gari Da misalin biyar na yamma mai shela ya sanar da lokacin isowar sa

A filin da private
jet din masarautar yake sauka aka jera motoci kirar mercedez benz farare kall

Khaldun yana saukowa sai ga wani jirgin ya aje kaamil

Khal Yasha mamakin ganin sa sosai duk dama yaji dadi aransa sosai

Anan gida ma Babu wanda ya san da zuwan kaamil din sai junnut domin har iyayen nasu basu fada musu.

Ita Tun jiya da take dan jin fargaba,sai kawai tayi amfani da shawaran zuciyan ta na ce  cewa ta fada ma kaamil komai tunda shi yafi kowa sanin waye khaldun in yana kusa kuma zata iya cimma burin ta na kalmashe shi

Dan haka ta sashi ya iso gida a gurguje batare da ya fada ma kowa ba

Su kuwa da suka shigo palace din abu inda suka dosa sai babban fadan dilshad kakar su

A tare jahan khatun ta gansu sun shigo khaldun rike da hannun dan uwansa sun rusuna agaban dilshad kamar yadda suka saba cikin tsananin nuna biyayya suna masu miko gaisuwa

Hakan ya matukar sa jahan khatun farin ciki marar misaltuwa babu abunda take sanya musu sai albarka

Sunyi sunyi kaamil ya fada musu reason dinsa na zuwa unanouced amma sam yaki.

Khaldun kam kowa ya san shi dan tsari ne bayan gaisuwar ma baifi sau biyu ya sake magana ba don tunda ya samu wajen zama dilshad tana famar musu bayanin ta akan komai shi ko motsawa bai sake yi ba Hasali ma shi abun bai wanj dara shi,maganan  mahaifin sa ne ke masa yawo a kwakwalwa

Sun tashi sunga yana matukar biyayya ma dilshad khatun dan haka bai sa aransa zai bijire ma maganan auren nasu ba

bayan 40 minutes suka nufi site din su inda kowa ya shiga kimtsawa

Anan kingdom komai yi musu akeyi dan haka masu aiki suke faman jigila da dawainiyar abinci,aiki, da sauran su.

A jerin masu aiki dama na khaldun saood daban suke,hatta uniform dinsu ma ba dai sai yake da sauran bayi ba

Kwata kwata yan mata uku ne a site dinsa ka kowacce da irin aikin da takeyi

Daga nan babu wanda ya sake neman su sai washe gari da safe,aikan dilshad ya iso kofar dakin khaldun cewa ya shirya  zatayo introducing dinsa ma bride to be dinsa.

Shidai bai iya nuna alaman komai  fuskan sa ba,sai dai yana da tabbacin cewa ba lallai ne ya so abunda suke so ba.

Gefen junnut kuwa tun safe da tafito daga shashin motsa jiki ko sport wears din bata cire ba ta nufi site din kaamil,its private dan haka acikin ruwan wani katoton pool dake bayan apartment dinsa same shi,sai ta zauna a chair suna hirar sirrin su

"Kaamil dirarren namiji ne,fari mai mugun son kara'i, shi babu ruwan sa da komai kuma dai duk abunda zaiyi da yan mata har yau ba ayi macen da ta burge sa  har yaji ta sa  masa sha'awar aure ba

Ko da yaji ance ma khaldun za abada junnut,sosai ya gode ma Allah dan shikam har cikin ransa ba sosai yake ganin zai iya cigaba da biyayya ma dilshad da dad din su ba

"He likes beign free ya tsani abun takuri arayuwan sa,ita kuwa junnut badon ta riga ta ga zabin da dilshad tayi mata yafi ba, da ko kaamil akace ta aura ba zai dame ta ba

Shima irin mijin datake burin aure ne,ga shi da kyau,naval captain uwa uba dan kara'i ne.

Ya kanyi harkan sa da duk wacce ta masa but just for flirting sake,akan party da mata kaamil zai iya kwana baiyi bacci ba.

Sai dai in ka ganshi ba lallai ka gane hakan ba,most of times sai yana hutu yake ballewa, sannan shii babban soja ne to inda yake shiga yayi karain sa ba waje bane na zuwan kowa da kowa.

A us wani bin ko junnut bata iya binsa party,inta gansa da matan turawan nan somtimes she just wonder how
And Why har yau kaamil baijin sha'awar yin aure.

Anan dai tagama deban lectures dan ya gaya mata duk wani salon da zatayi muddin tana so tayi magana mai tsayi da khaldun.

By 10 in the morning lokacin an tabbatar da kowa ya kammala breakfast din sa

Kowa yana expecting yaga khaldun ya futo cikin dressing mai kyau da nuna kasaita ko burgewa,amma sai gashi ya fito cikin simple white jallabiya wanda hatta takalman kafar sa plain ne.

Zaman sa yayi kusa da dilshad wacce already ta sa an kere wajen ya haska sosai ta inda duk wnda zai shigo zasu ji dadin kallon sa

Chan sai ga kaamil shima ya shigo bayan ya gaishe ta direct ua dawo gefen bro dinsa wani murmushi suka sakar a tare don A ko yaushe suka jalle juna ji suke kamar mutuwa ce kawai zata iya shiga tsakanin su.

Anan daki kuwa jahan ne a tsaye tana dada jaddada ma junnut abubuwan da ya kamata tayi domin ta samu karbuwa wajen khaldun

Gashi har ta fara dagowa cewa junnut ta riga ta shiga zumudin soyayyar khaldun tun ma bata gansa a ido sa ido ba

Toh aya kenan zata dauki wannan risk din auren wurin bayan tasan irin zaman da suke so junnut tayi a gidan khaldun Ba abu bane da zasuyi wasa da shi.

Bisa ga wannan dalilin jahan ta yanke hukuncin dada ganat da junnut.

Tun kafin ta fito da ita sai ta nuna mata cewa ita asalin burin ta akan ta shine sai ta kammala karatu ta rike abun kanta kafun ta shiga rayuwar aure da khaldun.

Anan ma Sosai junnut ta fahimce ta sabida dama abun na ranta itama sosai kuma ganin bata kai inda take so takai arayuwa yanzun ba shiyafi saka mata fargaban fuskntar sa ayau

Jahan khatun Tasan sarauniya dilshad tana mugun tsoron lamarin ne, Kar suyi sanya ne abun ya xo ya kufce musu shiyasa da chan ta matsa sai anyi abun yanzu .

******

Da asalin sumar kan junnut aka mata nadin kwalliyar jeweries din gold yan dai dai masu kyaun gaske.

Kayan ta fitted mermaid gown ne brown mai tail har yana dan jan kasa dakansa sai dai kwalliyar manyan mata aka kwaba ma fuskan ta wanda yaso ya karkata kamannin ta baki daya.

Sanda zata shigo har wani sanarwa  jahan ta sa akayi,bayi shida ne suka rufa mata baya tana taku kamar bazata taba kasa ba,duk dai tayi musu kyau amma  khaldun baiji abun yaje masa ba

Tana zama tayi gaisuwa su jahan suna yabon ta,..duk dama kirjin ta dukan dari dari yake amma haka ta daure bata ko kalle sa ba

Shikam idon sa ya zuba ya kare mata sama da kasa
...She's not bad huhn?

Sarauniya dishad kuwa sai kallon sa takeyi tana so taga ko zata gane wani abuda da suka hade ido da shi
Dan Yake khaldun din yayi sai jahan tayi gyaran murya.

Nan ta gabatar masa da junnut matsayin wanda zasu aura masa,and right from tarihin ta da matsayin ta acikin su baa rage masa komai ba

sannan ta nuna cewa a matsayin ta na uwa ce tayi masa wannan zabin kuma hakan shiyafi dacewa da shi.

Shikam Ba tantama ya amsa tare da nuna biyayyar sa.
  Sosai dilshad taji dadi duk wani fargabn ta dai ya yanke

Nan tayi umarni akan a basu waje domin su gana tsakanin su

Kowa na fita Wani shiru ne ya dauki wajen tsawon minti talatin junnut bata dago kai ta kalle sa ba shikuwa ya sa wayar sa agaba yana latsawa kamar ma baisan da ita ba

Hakan ya dada cusa mata fargaba a ranta amma sai ta fuske ta cigaba da shiru abun ta

...sai chan wani dan karamin tari ne ya shake mata wuya a bazata datayi sai taga ya dago ido ya dan kalle ta,...

Wani dauke kan jiji da kai tayi da sauri tana jin nauyin idanun sa,and she honestly cannot believe that duk uban shirin datayi akansa zai zamo banza lokaci guda ba..hes is sooo hot and everything she eva eva dream of

Data kare ma Kyaun shi da kasaitar sa kallo aranta sai taga kamar dama chan labarin karya ake mata

'The way she see him now,sai dataji ta raina ma kanta ga wani shegen mahaukacin kaunar sa mai zafi daya cakke kahon zuciyar ta ayanzu

Gashi yaki cewa uffan ita kuma a yanzu ma kwakwalnta gaba daya ya shafe bata ma son ta furta wani abu ta kwafsa ta fiso sai ta sami cikakken nitsuwa.

da taga dan tarin datayi dai ya ja hankalin sa sai ta cigaba da kwalowa cikin salon basarwa.

Bata ma sani ba taga ya tashi ya fita,a bakin kofar fita yaga maid  tana tsaye batare sa ya kalle ta ba  yace get her some water daga nan yabar sashin bai sake duban inda take ba.

Itama tsaye ta mike ta Wani sauke ajiyan zuciya,gaba daya damuwar ta bata sane zata ce masu jahan ba insuka tambaye ta,zaman kurame akayi sai dai kowa yasan fuskan kowa yanzu

Haka dai ta cigaba time to time ana hada su suna ganawa amma iya haduwa in zatayi khaldun baiya ma kallon ta sau biyu bare ya tanka ,daga nan jahan ta samu daman saka nata ra'ayin,har dilshad  ta soma daga kafa sosai musamman da junnut ta nuna kasawar ta wajen ja da hidimimon khaldun..

Ta dai yarda da shirin tsafin da su kayi,a duk dama bata fara ganin wani positive action ta fannin sa ba

Jahan khatun tace
Matsalan su rashin sabo ne

Kawai sai akayi akan koda junnut taje schl a us in saood ya dawo zata na zuwa masa hutu kamar dai yadda take ma kaamil

Kwanan sa tara a kingdom amma Da kyar junnut ta fara gane kansa,duk iya rigimar ta da iya kasaitar ta bata kamo setin tashan khaldun ba har sai da kaamil ya fara musu yar qwari qwari.

Shi zai hada dinner ko wani game sai ya yi inviting dinsu su biyu yana dan ja su da hira Anan har tasan cikakkrn sautin muryn sa

Da hakan har kaamil ya samu suka fara magana kadan kadan a tsakanin su,sai dai fa matsalan junnut shine tayi saurin zumudi wajen nuna cewa ita wata ce.

Karama da ita amma She is always on high Fleeky Make up ko games zasuyi bazaka ga ta bar natural beautyn ta afili ba,ga fiye tsadadun kaya da son nuna ta waye bata san kuma hakan shi yake dada sa khaldun jan baya Da hidimar ta

Dan kyau kam shima ya yaba,har yana jin alamun zai iya rayuwar aure da ita,da alaman kuma wannan wankan maganin nasu ya dan taba shi...

15days kacal sukayi anan din,amma sai ana saura kwana uku su zasu tafi kafin junnut tayo abunda ya dan bashi mamaki

A ranakun sai ta aje girman kanta tana kokarin jansa da surutu ko yaki ko ya so,ranar har tasa shi suka je garden din ta tare Suna Zagawa

sai yanzu ta samu daman amfani da  duk wani strategyn da kaamil ya fada mata wajen magana da shi..

Akwai gajiyarwa dan kuwa bata taba ganin murdadden gaye kamar shi ba

Da zai tafi Haka aka tsayar da magana cewa,khaldun na junnut ne and when the time is right za'a yi musu proper royal weding betrothal...

A yanzu junnut tana da phone number sa amma da shike kaamil ne ya saka mata awayan shiyasa bata taba dialing ba,

gashi tunda ta ganshi bata iya wani bacci mai kyau bata yi imagining din rayuwar aure ta da khaldun ba,hade da burirkan ta na nan gaba kuma sai take ga tafi kowace mace sa'a a duniya

Bayan kwana biyu da tafiyar su A kullum sai ta tambaye kamil taji ko khaldun yace wani abu akanta amma sai shiru.

Shikuwa khaldun yana sane da duk abunda take ciki,dan yana da wannan baiwar, iya kacin kure sa shine ka tafiyar da rayuwan ka batare da son nuna saika burge sa ba.

Shidai bai wani damu ya aje contact din ta a wayar sa ba,don tun aranar da suka bar kingdom din kowa sai ya koma inda ya fito sauran ayyukan sa su suka sha masa kai

kaamil din ne yakan tsula mata karyan cewa ai khldun yana kiranta baya samun ta ne shiyasa take jin sa shiru,a haka har ya sa ita da kanta ta neme shi a waya sau daya suka gaisa daga karshe ma Bai yi saving din ba

Aganin sa muddin wani abu ya taso masa na dole ya kira ta,a ta wajen kaamil yake sa ran samun hadin kanta basai ya sha wahala ba.

Haka rayuwa ta cigaba ma junnut da khaldun har Allah ya sa ta samu daman rike kasa wajen sa kewa da tunanin  shi aranta.

Gradually son shi yayi mata zurfi

Amma Tunda tazo daga baya ta fahimci cewa duk hadin kaamil ne, babu ma Ko number ta a wayar sa sai itama ta dauko dabiun jan aji irin nasa dan abun ya ci mata rai bana wasa ba,duk abunda yayi itama irinsa zata masa,gashi zatayi ta korafi adan dole jahan khatun ta cire mata tsoron sa har ta samu bakin titsiye shi cikin magana

shikuwa wani bin mamakin ta ma yake sha,gaba daya ya lura da iya nuna zagewar ta akan maganan alkwarin auren dake tsakanin su shikuma sam baya son shirme

infact aranshi yafi son yaga yaso mace sosai badai macen tafi shi zagewa ba

So most time ib tana surutu sai dai yayi mata shiru har ta gaji ta kashe wayar

amma kuma idan tayi kwana biyu bata ji shi ba sai kaga ta kira layinsa koda kuwa bazai dauka ba.

A bangaren jahan Aarah kuwa babu yadda ta iya ne da biyayyar mijin nata  amma tun bata san waye yarinyar da aka laka ma dantan ba taji abun sam bai mata ba.

Anything from dilshad khatuns kingdom awajen ta ba Alheri bane.

"Duk dama ance alkwari kawai akayi musu amma kusan kowani rana abun sai ya dame ta azuciyar ta.
Follow @surayyahms
Mutane biyu ke ban dariya aradu,those ringing bell wai yau monday ne fa,da wansa suka dau zafin basu son khal da junnuta yar gata,hahhjj ko dai na koma team khalju ne?
PLS MORE COMENTS AND MORE VOTES LOVE U SO MUCH

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top