chapter 24

_2⃣4⃣-piousness♡_

A cikin jirgi Da kanshi ya makala mata seat belt ya dada ruriffe mata kunnen ta da head warmers ta zauna daf dashi batace uffan ba,shikuwa babu abunda yafi daga masa hankali a yanzu kamar yanda yaga duk ta rame ta jigata tayi fayau..

Thats not how he left her few month ago,tunani yake yi kala kala Har bacci ya sungume ta bai daina aikin kallon ta ba,Cikin ransa ji yake kamar yay wani magic ya bude zuciyar ta ko dan  yaga asalin mene ne damuwar ta.

After just few hrs ta bude idanun ta Tsintar kanta kawai tayi acikin wani white monochromic theme bedroom jikin ta a lullube da wata lallausan comfoter

banda edges din funitures komai fari kall ne a dakin, dan salati tayi tana mika Kanta nakan mata wani irin juyayi..

Daga kanta ke da wuya taga wall clock,kusan karfe 7 na dare.

Batare da bata lokaci ba ta yaye bargon ta aje kafa daya a kasa tana shirin saukowa cikin sauri musamman da tuno da sallolin tun azahar dake kanta

tana dira ta fara jin motsin mutane
Jim kadan aka murda kofar dakin da sallama aka shigo ,khaldun ne a gaba doctor na biyo shi a baya..

Wani kallo suka maida ma juna nauyin idanun shi ya sata ta suke nata idanun kasa,yana tausayawa amma ganin ta a yadda take,daga ita sai riga da wando ga suman kanta yabi gadon bayan ta babu ko mayafi a  take sai yaji ransa baiso ba.

Wani mugun kallon ya dada binta dashi duk da ma yanzun yasan ba kallon sa zata sake iyayi ba

sai ta koma bakin gadon slowly ta zauna ciki hadiyan yawu tay saurin sunkuyar da kan ta kasa kamar marainiya...

Tun kafin doc din ya mata magana ya juyo kanshi ba yabo ba fallasa yace ma doc din pls
Excuse me..,doc yana matsawa kuwa sai ya taho kusa da ita cikin galla mata harara "lay back".. ya furta kamar bada ita yake ba slowly ta koma saman gadon..sai ya gyara mata pillow ya ja bargon wanda ya dada sata mike kafa da kyau,tana kuwa shiga Ya lullube mata jiki har izuwa kan kirjin ta ita da kanta ta maida hular ta,...anan gefen gadon yayi zamansa bai tashi ba..

Quietly Doc din ya shiga duba ta_to ya dan manyan ta dan haka bai fara daukar matakin komai ba sanda yaga report din past medical history ya dan mata tambayoyi..

Her blood presure is quiet high..sannan tana bukatar bacci da abinci masu rage tunani,...duk bayanin shi ma khaldun yakeyi ita kuma tayi shiru bata da aiki sai binsu da ido..

...doc yace zai mata allura wanda zai taimaka wajen sata cin abincin,ita kuwa tin kafin yagama hade ruwan ta shiga taro hawaye tana kau da kanta slowly....gashi ya tsani hawayen nata,kuma sam ba baya son ya barta da wani su kebe...

Da hakan sai ya wayance ma doc akan,kar ayi mata a ko ina sai a hanu cewar sa ai intravenous din ma zaifi bin jikin ta akan lokaci.

A hakan ma shi ya taimaka aka mata Alluran,yana gamawa ya maida mata kanta kan pillow ya rako doc din waje.

Bai sake shigowa ba sai da ta mike ta shiga bathrum ta da niyyar alwala ruwan yayi mata dai duk suman kanta saida ta jika,dayawa suka manne agefe gefen fuskn ta,ta fito da hular a hannu tana famar zazzarewa sai gashi ya shigo...

Kallon juna sukayi na 2minutes kafun ya sake kofar ya karaso,..yanayin daya tsaya cikin dakewa yana binta da muzurai yasa ta kasa motsawa daga bakin bathrum door tana ta sunkuye sunkuyen kai ga wani shegen jiri dake famar sandan ta...

Aikuwa tana kara one step zata karaso tajiyo ta zube ajikin sa,ba abunda take yi sai numfashi sai layi..yunwa ga rashin karfin jiki duk su ka nakasa ta,ko lips dinta dakanshi yke rawan dari duk ta sake mashi nauyin ta tana luoi da ido..

Dago ta yayi tare da damke hannun duka biyu,he is tensed
,..Wani masifan karfin hali ya shiga mata tun daga kan fitowar datayi a bathrum din babu dan kwali har zuwa kayan dake jikin ta ayanzu..U love to keep it open..Ni banaso..waya ce miki ma ki tashi...bakince bakki lpya ba?Zamu bata idan bakijin gari...

Tayi shiru,tana dan lumshe ido cikin shagwaba tana dan riko shi,. Daurewa yayi dan ya  tsani yayi magana ayi masa shiru..sai ya jawo ta duk nufi gadon..a hankali ta firta ni fa sallah zanyi...

Tsaban baima san meke asalin bashi haushi da ita ba,sai ya fita shaanin ta yayi zaman sa bakin gadon yana kallon tana layi tana zaro kaya daga travel kit din..yasan tana neman wanda zatayi sallan da shine,shikansa ya baza ido duk baiga wanda yayi masa ba kawai sai ya mike yayi waje...

Kota sake kallon inda yayi,Wani half gown ta dora akan
Jean din ta lullube kai da mayafi ta jero duka sallolin dake binta.

Kamin ta idar gaba daya tayi laushi,zama tayi agefen bed din a kasa kanta kife da gwiwar ta tana sauke numfashi a hankali....
Har ya shigo bata lura ba,sanda yayi gyaran murya..

Dago ido tayi adan gurguje ganin ba shi kadai ba yasa ta dan kau da kai...

"....mai aiki kuwa tuni ta aje farantin abincin agaban ta tayi waje...yana tsaye bai motsa ba daga wajen yace..u need to take something..taji amma bata amsa ba dan tunani duk ya cike mata zuciya,she just want to sleep now...sosai take fargaban abunda sadaat yaci alwashin zaiyi akansu in ta sake kwana agidan shi..

After five minutes of silence ta jawo abincin ta fara ci a hankali kamar bazata ci ba .

Hannayen sa rungume da kirjin sa ya kafe ta da ido ko zama bai iyayi ba.,.gaba daya bata jin dadin abincin sabida shi take tutturawa...tasan idan ma tace ta a koshi masifa zaiyi mata dan haka ta dage tana ci,karshe zuciyan ta ne ya shiga tashi yana mata suya tuni taji cikin ya hautsina kafin kace kobo wani makallen amai ya fara yunkurin turo kansa waje. 

"Get up...ya fada batare daya motsa ko y taimaka mata ba,..da kyar ta tashi ta iya mikewa ta nufi batrum din da sauri ta zube kasa ta shiga fitar da duk abunda taci

Idan Ga yadda ya tsime ya hade rai daga nesa yana kallon ta zaka ce haushi take basa
Amma kuma cikin ransa tsantsan tausayi ne da azaban damuwar halin da take ciki

yasan bazai iya lallabi ba ,tsayuwan shi ya cigaba dayi baice mata uffan ba saida ta karaci aman sannan ya taho ya daga ta,..wasu irin silent tears masu zafi take saukarwa bai ko kalle ta ba,nan ya kunna mata tap ruwa mai sanyi ya fara kwalala sai ya umarce ta da wanke bakin ta da fuskan ta,..ba musu ta sa hannu ta shiga tare ruwan tanayi tana dan layi..,shikuwa kamar wanda yake jiran ta akan wuta.."bai ma bari ta kashe tap din ba ya dago ta bayan 2minute looks daya bita dashi ya dauke kai wani irin fizgo hannun ta yayi suka fita a bathrum din suka koma dakin...sit down...ya dangwala ta kan gadon ya tsaya yana kallon ta ya mugun hade rai

Tunanin me kikeyi?
Ta danyi shiru..

Dont keep ur silence on me...whats all this...meke damunki kina karama kina deban makanki hawan jini..?

Wasu hawaye masu yawa su suka sauko
Mata zirrr ta shiga tarewa a slow jikin ta tuni ya dau rawa...

Wani karin haushin ta bashi a Baiso ya daga voice dinshi ba amma haka kawai yaji ransa na tafasa sosai masifa ya cigaba da azalzala mata kamar bai damu ba....

Akwai wanda ke takura maki ne?..is it ur friends... hooligans..cultist...a makarantan ne ko agida?...just start
Talking now....ya dan daka mata tsawa.

A tsorace ta fashe masa da kuka mai sauti,jikin ta ne ya dada tsanan ta rawa...

Yace ni kimin shiru....batayi ba ta takune kanta kamar wanda take so yasan yana bata tsoro her shivers is making him feel quilty

jikake wani karan tass tasss a kasa
Dan da yayi wani firo da bedside lamp sanda ta birkice ta firgita ita kanta batasan sanda ta sulale kasa ta dukunkune waje guda ba

Rakubewa tayi cikin wani irin tsumayin sautin kuka tafara cewa "dan Allah kayi hakuri ai zan fada maka..dama nifa babu komai..kawai banda da lpya ne.
Kuma...kuma..

A zuciye Yace karya kike min...kinga ina lallabaki ko?...did u think am stupid yaushe na fara wasa dake..

Kukan ta cigaba dayi tana bobboye fuskan ta..

Gaba daya Tension din ganin ta ahakn ya gama nakasa shi gashi taki sam tace masa wani abu mai ma'ana,kuma yasan akwai abunda ke damun ta,..karshe ma juyawa yayi ya bar mata dakin..

Kuka tayi tayi sosai,tana tuno da yadda zata bullo ma al'amarin...tasan khaldun yayi zuciya..she knew in yasake birkice mata hakan bazata iya kin gaya masa komai game da sadat ba..

Amma kuma hatsarin ciki take duba,its the same as daba ma
Cikin ta wuka dan fargaban sadaat har yanzu yafi komai jan karfin ta

A wajen ta zauna ta rungune kanta da hannayen ta tun tana kuka mai sauti har ta dena sai  hawayen kawai ke zubda kansu.

Around 9.30pm wayar ta ya fargar da ita,dada share fuskan tatayi sannan ta dauko call din su dija ne suke kira dan haka ta danna conect after 1sc ya kama suka ga junan su,..video call its easier for them to console each other..duk abunda take ciki tagaya musu

Yasmine ne ta dada bata karfin gwiwan cewa ta cire tsoron komai aranta sadat bazai san suna tare ba,..she dosnt really believe in magic amma yadda suke bata asurance yasa dan dole ta amince..

Dija tace sun baza idanun su akan komai yanzu suna da masu taimaka musu wajen bibiyar duk abunda sadat ke ciki batare da kowa ya gane su ba..

Alfarma daya suka roka wajen ta kuma shine akan suna son ta sake ranta ta warke kodan ta dawo akan lokaci su shirya ma promotion  exams dinsu.

Yadda takejin tausayin su yasa ta amsa da cikaken amincewa...atleast sune agefe wanda zata iya gaya musu asalin damuwar ta kuma su fahince ta..

Bayan ta katse wayar Wani lunshe ido tayi tana sauke ajiyan zuciya cikin tunanin yadda zata je ta lallabosa.

Tasan bazata iya gaya masa komai ba,muddin basu cimma burin su akan sadatt ba..she knew she cant risk it..amma kuma dole ta gaya masa abunda xaisa hankalin sa ya kwanta sosai..

Mikewa tsaye tayi ta tattara wajen duk broken glass din tayi disposing,rigar data sa akan jean din tayi sallah shi ta mayar ta hada da mayafi ta fito a sadade tana neman inda zata gansa.

Data murda kofar ta fito sarari ajikin  step na karshe Tayi tsaye kusan Minti 10 tana kare ma gidan kallo

evrything all white hakan ya dada haskaka mata idanu har ta hango wani chef dake tahowa gaban ta da tray din abinci..

Har ya karaso batace mishi uffan ba,shikuwa yana isowa gaban ta ya dan risina kaii ya gaishe ta,..yace khaldun ya bada oder cewa asake kawo mata abinci..

He dint forget that anyi mata alluran cin abinci,sai tace mashi yakai dakin ya aje mata

Dan kwafa tayi cikin tunani,ohhhh duk wannan fushin da akayi dani ba a dai mantawa dani...

Chef na fitowa tayi sauri Tace pls excuse me...
Sai ya juyo.. Tace
Pls where is he..?

Ganin kamar ita din sam bata da dirin wulakanci Sai ya sa shi ya mata nuni da wani kofa dake daff da inda take tsaye,dakin yana  kallon juna ne da wanda ta fito aciki yanzun.

Ta dan kwakwalo murmushi tace thanks,chef da wuri ya sauka ita kuma ta isa bakin kofar dakin...

20minutes tana knocking  da kyar ya bada izini aka shigo

Kwance yake yayi luff ya lunshe idanu akan gadon sa ya kuma bada kofar baya

He is literally upset,jira ma yake ya bude idanun shi ga wanda ya shigo ya sauke masa bala'in masifa

...yana kuwa juyowa yaganta tsaye daga bakin kofar tayi shiru ta dauke kanta tana dan wasa  da yatsun hannun ta,he feels better dayaga babu hawaye akan fuskan ta yanzu amma shirun datayi ya sa ya kau da kansa ya bata keya...

Wani lumshe idanun sa yayi,yana kokarin 
Rokon ziciyar sa ya sauko dan yaga ko hala zai iya lallabataamma ina,kowani five minute baiyi ba yaji inuwar mutum daf dashi....

A slow ya juyo ya bita da wasu razanannun looks,idanun shi babu wasa a ciki...hawayen dake shirin cikowa ta mayar ta matso daf inda ya kwanta tana binshi da kallon itama,cikin marairacewa da sanyin shagwaba slowly ta zuba gwiwan ta akasa tace..

"Dan Allah Kayi hakuri. ..

Wani sanyi yaji aranshi,amma bai ce uffan ba ya dauke kansa

.. Ta fade hakan sau uku yayi kamar bai ma san da shi takeyi ba sanda ta dan kara sautin crack voice din ta
Sannan Ya juyo da kyau..

Dan Allah kay...yace
stop nan ya dakatar da ita da wani irin kallon kulawa..

Kinci abincin dana tura maki?

Sai Ta dago grey eyesballs din ta  kadan Nan suka hade ido,cikin sanyi jiki ta girgiza mai kai tace ah'a banci ba

shi kansa baisan meyasa shi tsaki ba, mikewa yayi ya mata nuni da hanyar waje..

Nan ne hawayen da take dannewa suka fito,..rabon ta dataga ya tsime haka tun lokacin datake matsayin maid dinsa,..bata jin tana da karfin daukar fushin sa ayanzu dan haka ta mike a sulale ta nufi bakin kofar niyar ta inta ci abincin saita dawo,..bata hankara   taji shi daf,karasa turata wajen yayi ya slaming door dinsa gaban idanun ta...

Shock ya bar mata bakin ta a bude,sam bata san meyasa yake da fushi sosai ba,...goge tears din tayi tana sauke ajiyayyun ajiyan zuciya...tasan bazata iya jure hakan daga wajen shi ba...jikin kofar ta koma kamar zata sake knocking

amma batayi ba sai ta jingine bayan ta cikin nitsuwa ta fara rokon shi achan cikin wuyar ta...

Pls open the door...
Da kyar take furta hakan, i want to tell you evrything..pls open...very weak hands dinta ke bubuga kofar lighy tamkar bata san metake ba

After 10minutes of silence taji kyat alaman budewa.,wani disashen murmushi ne ya kufce mata sai tayi saurin goge hawayen sannan ta tura ta shigo,,dashi ta cikaro gumm a gaban ta bata kara one step ba inuwar sa ya dakatar da ita ,..a tsaye ta same shi abakin door din ya rungeme hannayen sa a kirjinsa..

Wani irin quick and passitionate looks sukayi exchanging sannan ta sauke idanun ta kasa a hankali ta shiga rero masa labarin data shirya.

Tafara ne da bashi hakuri,a cewar ta itama bata san sunan ciwon dake damun ta...Ta kuma tabbatar masa da cewa babu abunda ta nema ta rasa na kudi...

Wasu nannuyan hawayen suka kufce mata Sai tace ina ga fa mafarki ne....

A slow yace mafarki?

Sai ta gyada masa kai kaman dagske ..

Ai kullum inayin shi,I kept seeng it...
I think im scared...ni fa tsoro nakeji

Yace tsoron waye?

Ta dan yi shuru,sanda ta sauke wani ajiyan zuciya tace,ni bansan shi ba,shine  sai yana tsoratar da ni..kusan kullum yana zuwa min bana iya bacci...i dont know what to do..i keep getting sick...kuma ina fada babu mai yarda dani,.a hankali ta karashe karyan nata cikin sautin kuka

Wani lumshe  idanunshi yayi cikin jin tausayin ta,a baya cikin hankalin sa ya jawo ta jikin sa ya wani rungume ta sosai saida ta aje kanta akan kafadun sa itama tana sauke wasu fitinannun ajiyan zuciya...

Its ok...ya fada very calmly agefen kunnen ta yana dada kamkame ta itama zagewa tayi tana lumewa jikin shi tana dada sauke ajiyan zuciya 

A tsaye dai sun kai mintina talatin,
sanda ya tabbatar ta dawo hankalin ta kafun ya tattaro fuskan ta da hannyen sa ya shiga kare mata kallo
,..sauran tears din dake fuskan ta ya goge,yace zakici abincin?wani waek smile ya kufce mata sai Ta gyada mashi kai suka fita..

Agaba ya sata tana cin abincin chef din rashin lpyar yasa take taunawa very slow har ya fara tunanin ko abincin baiyi mata bane

Cikin sanyin kallo ya tambaye ta me kike shaawar ci,kamar zata ce babu komai but ganin idon shi yasa tace mashi mint tea...

Toh Shi dakansa ya hado tea din y kawo tana gama sha tayi kwanciyar ta shi ya fita..bata sake ganin sa ba sai da asubahi.

Doc zai sake dawowa dan haka ya taimaka mata ta yi sallah. .

Magungunan bacci dana cin abincin daya dinga samata har na tsawon kwana uku shi yake dada rike mata jiki.

Cikin kwanakin kaamil ma ya kira shi but sabida halin datake ciki sai yace masa kawai yana london ar yanzu bai dawo ba.

Tana jin cikin wayar nasa,ya sauya mata suna zuwa"twinkle"
Kaamil ya so ace an bashi ita sun gaisa amma sai dai ya dube lumshashun idanun ta yace masa tana bacci..

Da haka tension ya fara raguwa mata

Sometimes idan tana bacci bata cikin hayyacin but takan ji duk hidimar da khal yake mata na kulawa.

Toh Tunda doc ya dena zuwa Da dare inzatayi bacci shi yake yawan zama kusa da ita ya karanta mata alqur'ani..

Sometimes anan kasan kusa da gadon yake zama yana gadin ta har asubahi baya runtsawa,cin ta da shan ta duk yana lura sosai..

Kowa waya baya cika son amsawa idan yana tare da ita

After 1 full week agidan,ta mike ranar asabar da safe ta farka dawani karfi da nishadi tana jin jikin ta ya warware tasss alaman sauki ya samu..

Shikuwa da ya lura da hakan sai yaja jikin sa,trouh out the wekend bai wani je inda take ba.

Ba laifi takan fito dakanta tsakar gidan tayi ta zagaye zagaye,ranar bata ganshi ba gashi kuma tana mugun kwadayin noodles
Da taimkom chef ta nufa Kitchen ta shiga hada wata garnished indomie mai dan karan qamshi,dan rabon ta datayi girki yakai fiye da wata guda.

Tsaban yadda take jin yawan cin abinci yanzun tun kan indomie yagama hucewa take famar zara tana kaiwa baki,..

Budewan kofar kiitchen din ya sa ta farga wani gurd tagani sanye da plain army uniform yace mata ta taho khal ya dawo yana neman ta a falo

Ba bata lokaci ta fito dauke da plate din indomien ta,riga da wandon jean da hular sakar ta baki ne ajikin ta,tsavan qamshin idomine na bugata bata ma lura da abunda ke gaban ta
Tun a saman yagama kare mata kallo Da wani mugun ido ya sallame duk wayanda suke wajen,harda wanda ya kawo masa aikan da bai ma saurare sa yaji ba..

Tun Akan step na karshe data dora kafar ta zata karaso taga ya mike tsaye ya hade ranshi yana kallon ta

Wai mene ne wannan,..?

Baki a bude Ta tsaya tana dan dube dube ta gama daukawa ko ba agirki agidan ne  ita taje tayi,..wani shegen naugty face ta bashi wanda tuni ya dada ruda zuciyar shi da kishin ta

Looking at her up and down
yace wai baki da kayan sawa ne sai wannan,ni baiyi min ba..and u cant wear this in my house...

He sound weird to himself,amma sai Ya dada hade rai ya karaso ta gefen ta zai wuce ya haura dakin sa..."go and change"a iska ma ta jiyo .

Bayan ta dauke idan ta akanshi Tabe baki tayi tana kare ma jikin ta kallo ta ko ina bata ga aibun ta ba,ita dai tun nigeria big sis ta sabar mata da saka kananan kaya na english gowns materialz gowns ko jean da top,tasan baison barin kai abude kam kuma dama ita duk tsiya bata fita babu rifin kaii

Amma yanzu sam bata fahimce angern sa akan saka jeans din ta ba,..kyabe baki tayi ta karaso tayi zaman ta akan cushion din tana cin indomien kadan kadan tana wondering,to ita wani kayan zata sa masa bayan a jakan ta inbanda jeans din babu wani kaya na daban sai simple jumpsuits shima daya kawai ta dauka..

Ko rabin plate din batayi kusa ba taji karar rufe door Jin motsin saukowar sa kasan yasa ta ta mike a gurguje tare da aje abincin da sauri ta hauro kan step, din tun anan ta rakube tana dan satan kallon shi bai kula ta ba ya sauka,she is left with no other  choice than ta cire kayan jikin ta ta saka jumpsuit din duk dama yadan rike ta shima
But is beter when she cover it up da veil din nata..

Bayan ta sauya kayan

Saukowa take tana dan leko shi,bata ga meyake ba sanda ta fito sarari taga empty plate of indomie da remote a hannun shi yana kallo...

Dan kadan ta turo baki ta shagwabe,abu kamar ba maita haka kawai kuwa indomien ya biya ranta,tsabn kiriniya ko sallama bata masa ba ta sulale ta zauna akan cushiob dake kusa da nashi,da gefen idon shi..he notice her silly pouts,sai yauqi takeyi ita kadai cikin ranta tana banbami
...duk ya gane damuwar ta.

shi Jira yake tayi korafin indomie ya hada ya mata masifan,jikin nata dan baiso ace tana takura kanta.

Baisan saukin nata har sosai haka bane,suna cikin kallon shiru saiga chef ya shigo da kwalayen pizza guda biyu ya wuce kitchen dashi anan ma take taji ranta ya biya akai.

Alhamfullhi After 10minutes taga chef din yana jere akan table

Wasu dadan hand made chicken shawarma,pizzan da aka siyo sai damammen oatmeal da madara mai dumi. 

A ladabce yace sir..the food is ready,
Sai ya tafi

yana dago kai suka hade ido da ita tayi saurin daukewa,kada kansa kawai yayi  kamar bazai ce komai ba chan dai yace go and eat ur meal..

Toh Ranta ya riga ya biya Cikin basarwa Ta mike a sadade abunta ta nufi dinning,tana tafiyar bata sani ba duk jikin nata ya kafe da ido yana ta kallon dresing din nata

wani siririn tsaki ne ya kufce masa sai ya dauke kai..

"Bata damu da rashin tahowar sa kan dinning ba ta bubuude abincin Ababu Ababu Babu abunda bata ci ma cikin ta awajen ba..

Cup ta jawo Tana kokarin zuba plain water...Wani phone call din daya da keyi ne yaso ya ja hankalin ta dan kiris ya rage ta gane cewa da mace yake maganan..

Bata gama tunanin ba taga ya tashi da wayar a hannun sa,wani package ne agefen sa tun wanda dazu ta gani amma batasan na miye bane but she kept suspecting that pack haka kawai,sai taga kuma ya sa ana biyo sa da shi cikin dakin sa ya nufa a alama har iyanzu bai gama ba..

Haka kawai taji walwalan ta ya yanke karshen cin abincin nata kenaan sai ta bar wajen ta dawo palour ta zauna,kallon take amma gaba daya hankalin ta bai jikin ta,she was not sure ko da macen yake magana ba amma yanayin daya ke ansawa wayar ya banbata da yadda ta saba gani,wani rau tayi da idanun ta kirjin ta na mata wani zafi she cant bliv that kishi mai zafi tajeji akan sa..

Tun tana basarwa dai har taji ta kasa hakuri rashin saukowar sa akan lokaci ya dada kara ma zuciyan ta uneaseness ..

Shikuwa sanda a shiga dakin ya samu freedom din magana da ita yadda yake so..

Junnut Ta takura cewa zata dawo us cikin satin dan kuwa tana missing dinsa..so take tayi amfani da sauran hutun ta suje chan kingdom tare

Sai yake gwada mata shi baida wannan lokacin Ayanzu haka ma tafiya zaiyi...

Gifts din dake wajen ita ta aiko da shi tun daga hungaray ita kadai tasan me tasa masa aciki,.take cewa idan ya bude yagani tana so ya kira ta in yayi haka zata ji dadi cos har yau baya daukan hannun sa ya kira ta haka kawai sai dai ta kira shi ko ta zo dakan ta.

Amma Duk iya wulakanci da iya basarwan sa inta kira kullum sai ta nace sun kai minti talatin suna wayan

A yanzun ma Da kyar ta amince ta kyale shi yana sauke wayar a kunnen shi yaji an turo kofar,tuni idanun sa suka sauka akan bahi ita kanta bata san meya kawo ta nan ba...

Duka Sunyi shiru ba wanda ya tanka,sai ta fara sosa gefen kunnen ta,wani noughty smirk yayi ya taho zai wuce ta...sai ya tuna da gifts din dawowa yayi zai kai hannu kai tayi saurin rigashi wani daukewa tayi da uban sauri tace
let me help you...tana dana masa duka idanun ta akansa kamar wacce take da degree a masifa da kiriniya .

No thanks...ya miko hannu zai karba ta ja da baya da bags din ta dauke kanta..

yayi karamin furzan iska yace Ok lets go down,nowww...sai ya fice

Haka ta biyo sa da shi suka dawo palour bata bashi ba,kowa zama yayi ya tsime

Daga Kan kujeran san in ta juyo anata sai ta kalle shi...wani kallon data ke mashi na dole a sai an bude mata pack din taga me aciki shi yasa shi ya kasa dena mamakin ta...is she mad?

tsaki yake ja aransa yana lura da ita yana bambami shi kadai,..to ina ruwan ta da gifts dina,..tasan da kishi take barin jikin ta abude kowa yana gani..yayi tsaki ajere ajere cikin wuyar sa
Yafi sau dari..itama ba abunda bata fada aranta ba,yanzu data tabbatar da mace yayi wayar tana tsaye abakin door dinshi ai taji ana cewa"she she"...slow take hararar sa da gefen ido...ita dai lallai tana so ya bude gifts bag din ai inma subaya ne tasan zata gane.

Mikewa yayi a bazata Zai haura sama,sai ya ga bata ko kalle shi ba,gift in ta dada jawo tana jira ya haura ai ta bude da kanta,yana hawa kuwa ya labe as expected  yaga ta dage karfin ta tana fincike seal tape din kamar wanda aka bata aiki.

Thats very rude of you...ya fauce abunsa ta bayan ta yana mata masifa bata ma san yaushe ya lallabo ya sauko ba.

Wayace ki bude min...naki ne..?

Sai ta dan kalle shi a sanyeye bata masan meke tunzira ta ba,jinta kawai tayi ta Wani hade rai Sai tayi masa shiru har fushin nata sosai ya ke neman ya shashi dariya.....atleast na rama..ya ayyana hakan aranshi mirmishi yake aransa amma fuskn babu sauki..shegen kishin tsiya ai sai nayi maganin ki..

Ya kwace gifts dinsa,.yana haurawa sama ko budewa yaga meye aciki baiyi ba sabida ita ya kira mai aiki ya bada shi kyauta

Washe gari da safe
Wani heavy knock ne ya dago ta a bacci,ta bude door din hannun ta akan fuska tana mutsukawa,ta duba bata ga kowa ba sai manya manyan ledojin shoping kowanne da logon arabian designer masu shegen tsada kuma na yayi..

Lekowa da kyau tayi ko zataga wanda ya aje su amma sai shiru babu kowa awajen,wani mika tayi cikin salati tana kirgo yawan su da idanun ta,manyan guda uku sai kanana da dan dai dai guda biyar biyar,..

One by one take shigarwa cikin dakin,bayan ta idar da sallah ta kimtsa sannan ta zauna ta shiga duddubawa tana zarowa waje shoes,long skirts da gowns

And Most of them are turkish gowns and Arabian jallabiyas guda daya ne ma tasame shi riga da wando da mayafin shi irin pakistani fashion din nan

Komai awajen na yan mata ne  kamar ta masu daukan ido kowannen su chic and decent

..Bakaken covers na Chador da burqan ne  ma yaso ya sata dariya,tunani take wai itace zata sa masa wannan?
Ko a mafarki bata kawo hakan ba.

Wanka tayi ta dan kimtsa kanta with very slight make up,cikin kayan ta dauko wani gown mai fadi mai open button black and white colour an matse kugun da black belt kasan kuma anyi shi mai step step har sama.

Hannun shi dogo sannan tsawon shi ya kai mata har idanun sawon ts

Tsarin rigar yasa ta tattare duka suman kanta ta masa daurin donut ta tusa su gaba daya acikin black turban ta fesa turare Sosai tayi kyau.

ita kanta data kare ma kanta kallo tuni ta gane banbamcin abunda yake son ya nuna mata tsakanin saka wayancan kayan da kuma wanda zai rufe mata jiki gaba daya sannan ya sa ta fito  kamar sarauniya..

Cikin kadadi ta dada duban kanta
Is not bad huh?

.. islamic code of dressing is way better than any other..

Idan kaga ka rufe jikin ka bakayi kyau yadda kake so ba to lallai laifin daga kaine..

Koda ta sauko a hakan ta fannin shi taga sauyin fuska,smiles dinsa mai tsadan shi ya tare ta dashi,then koda ya mata tambayar me zata karya dashi data fada shi ya shiga kitchen din ya fara hadowa dakanshi

Scramble egg,milkcustard da coissant...yana bugawa yana murmushi shikadai.

Daya gama Hakan ya sata agaba ta cinye kuwa tass...after that day suka tafi dubai halartan wani islamic family gathering na iyayen babban aminin sa shahrul

Koda suka iso shikansa shahrul baisan ita bace agefen sa sabida bayan plain bakar abayan daya sa ta kwama mayafin burqa shine ya rufe ko ina da inan ta

Burqa,irin cover din nan ne na matan larabawa wanda yake kamar hijabi mai hade da niqab shi baya kama jikin mutum kuma zallan wajen idanun ta kawai akayi da black transparent
Material agefen shi take tafiya,tunda suka gaisa shah yake ta lekowa ko zai gane gashi gogan ya tsime ya hanata kyakwan tari duk abunda zatayi yakanso tagaya masa..

Sanda suka je masauki,daya umarce ta da ta cire burqan ta ci abinci kafin shahrul ma yasan itace

He was freaking out tsaban mamaki har sanda ya sata tayi dariyar sa..

Yace Pretty girl ashe kece,dama dazai tafi yace wata rana zata zo inda yake..Sai gashi yau khal dinsa ya kawo ta yaji dadi sosai

Its a very big royal gathering hidaman addini ne ya hadu na zunzurutun ahalin sarauta da mulki na larabawa masu tarin dukiya.

Kusan duka prince da princesess na daulan islamic nations daddaya ne basu wajen kowa da tawagar sa da kuma irin kalar kasaitar sa

"Khaldun jinin sarauta ne gaba da baya amma ko da wasa abun bai dara shi ,shi yafi gane ma military stand  dinshi dan haka ne ma saudi arabian emirate suka bashi matsayi acikin manyan sojojin da zasu na taimaka ma addinin musulunci underground..

Ya hadu da malamai dayawa wanda suka koyar da su islama,dan sanadiyar shahrul ya karanci addinin sa at age of 18 ya sauke qur'ani batare da kowa ya sani ba

A da chan ya tashi ne yaga alaman kakan sa dilshad bata ko tunanin tana saka su akan wannan tafarki..

So Shiya koya sannan ya koyar da kaninshi kaamil tun a camp.

,..maids da masu kaikawo Nata famar fadanci,bahiyya tun tana wondering har ta fara sabawa da yadda ake worshiping din su ana binsu suna basarwa..

Ur highnesss..ur majesty..kadai zaka ji ana cewa

Banda shahrul daya ga fiskanta ko iyayen sa bai bata daman bude niqab din gaban su ba..

Shikuwa shahrul har ya fada ma queen of oman wato mahaifiyar shi akan cewa bahiyya itace wanda khaldun zai aura, dan shi tuni dama yake harsashen soyayya a tsakanin su...

Mum din shin Taji dadi sosai Dan haka ta ja bahiyyar ajikin ta duk inda zasuyi takan nuna ta a matsayin doter inlaw inta ma manyan attajirai da hamshakan baiks,khanuns da begahms har ma da kawayen ta queens of differn arabian nations da suka hallaci taron..

Most of them speak arabic har ta soma jin sha'awar koya itama amma nauyi da kunya ya hanata gaya ma khaldun cikin hirar su da shahrul take fada masa ,to daya gaya ma khal akan zai nema mata malami tun daga nan sai bai bada fuska ba..

Bayan kwana biyar suka koma US ta samo gifts kala kala daga waje daban daban musamman wajen shahrul da mahaifiyar sa...

Da yaga yanzu sai taji ta dan nitsu hankalin ta ya dawo jikiin ta

Nan Sai ya fara fargaban kar ta koma schl din kuma ciwon ya dawo mata gashi yasan bazata gansa nan kusa.

sai yayi ta tunanin ko ya kira subaya ya tuhume ta ne,but how can he?baya son kowa yasan yana ganin ta ayanzun .

Sannan haushi ma yake ji daya lura da cewa tin da tazo gidan acikin su babu wanda ya kira ta sai kawayen ta

Haka kawai Sai ya shiga neman mafita ta wani bangaren  yasan dolen sa ne ya taimaka mata da garkuwa mai karfi kafin ta koma school

Shiryen shiryen maidatan ne ya dauke nasa hankali,sai daya kammala komai
Washe gari da safe
A ajiye ta Yake tambayar ta ko tana mafarkin nata again..

Tasan dama karya tayi mashi,so bata dora ba tace yanzun da sauki...

Sai ya mata dan bayani akan adduar bacci da zata nayi,cewarsa zai tura ta london da wani quiding soja dan Ya kaita schl school din yana kuma lura masa da ita

Yace ta san yadda zatayi da business din ta sabida akwai schl din daya ke so ana kaiita don ta koya larabcin.

...murnan jin hakan ma ya hanata rufe bakin ta.. She dint know that full islamic school yayi enroling dinta just so that ta samu ilimin taimakawa wa kanta akan dukan abunda ke damun ta

Washe gari rabuwar su was so passionate and emotional...bayan hugs din rarrashi sanda aka daura mata peg asaman goshin ta

Ita da quiding sojan  suka koma london,same time shima ya tattara ina shi zuwa kasar russia domin comanding wani babban sea war operation mission.
#follow @SURAYYAHMS
get any information or updates

Tag ur favourite lines challenge.
Im challenging you guys,to show me exctly what u learn about this chapter that is soo special..i wll meet u a coment box.

Idan kana jin dadin labarin to Dont forget to click on the vote button fah

My dear extreme lovelies wallah ina kaunar ku sosai
amma ina son kusani cewa
Thiis story is already made up,.it obvious that nikadai ce nasan mezai faru gaba cos i have not seen any similar ques har yau,toh na muku alkwarin full week post and am gonna fulfil it this week insha Allah,All i want you to do is to stay calm and jejely analyse things say ur mind as if u wanna make us see what we havent seen,educate us with ur lines,kar kuma mu nuna son kai dan munga labari ne atleast lets be realistic so that mu samu karin sanin rayuwar duniya. Ur support is all i needed .COMENTS MORE

SHARE AND SHARE UR VIEWS.

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top