chapter 20
_2⃣0⃣-the venom♡_
Tun Tana daga serving spoon ya dakatar da ita ya amsa yana cewa let me have this..
A sanyaye ta sake mashi tana bin shi da kallo dan maganan kawai yayi amma bai wani kalle ta ba.
Bowl din Abincin ya sauke kasa ya aje kan lallausan chinesee rug carpet,a hankali taja mashi center table din gefe dakyau sai yace mata sit ta zauna,Serving Plates guda biyu ta jera amma da guda yayi amfani a nitse har yayi serving din su,kallon shi take satan yi but to avoid being cought sai ta yi kokari ta shiga zuba musu smothie a two cups kowa da nashi
Wani shiru Wajen ya dauka da suka fara cin abincin,its feels like heaven dan yayi kewar abincin ta sosai,shikam babu wani alaman jin kunyar ta dayakeyi dan cin abincin shi yake yi normally itace inta kai loma daya sai ta dan jira kafin ta kai na biyu.
A farkon wanda ya zuba musu ya kare sai ta dada kara musu Taga gogan bai dakata ba har suka ci abincin sau biyu..Dan kadan ya rage sai ya jawo smoothie din ya kai bakin sa..,itama dan tura abincin gefe ta yi niyyar yi ya wani balla mata harara bai ce komai ba
Bata daddara ba ta dan tura kadan,zata aje spoon yace"eat up"..duka zaki cinye..wani yamutsa fuska tayi cikin sautin shagwaba tace nifa na koshi ne..
Bai kula ba ya tura mata abincin ya dada balla mata harara,"u most eat all of it,baki da ido?baki ga kin rame ba?kaiwa nan ya kau dakai ya cigaba dashan abunsa shiru.
dan shirun itama tayi tana kallon sa a sanyaye ta jawo plates din ta tuttuura sauran abincin acikin ta badon taso ba,sai da taji tayi dam har ta kasa mikewa.
Shikuwa Tashi yayi da cup din a hannun sa ya koma kan cushion ta mike kenan xata tattara plates din ya mata nuni da remote akan ta miko masa
kallo ya kunna ya hakimce,nan taje kitchen ta gama tsaftace ko ina ta goge wajen tsaf..
A hankali ta bude door Tana dan lekowa suna hade ido
,sai yadan kau dai ba yabo ba fallasa yace fatan kinyi sallah?
Ta danyi shiru sai shima yayi shiru cos baisan ko ya dace ya mata tambayar ko bai dace ba
Doguwar Rigar material ne dama ajikin ta fari mai manyan rose flower pattern,a sadade ta wuce shi ta shiga bathrum ta wanke hannu da fuskan ta tsaf sannan tayi tsarki tayi alwala,data fito kallo daya yabita da shi,batare da yace uffan ba sai yaga ta canko in da direction din gabar ta tsaya, dan hair scarf din tan ta dada lullubawa akanta ta tada sallahn azahar.
Toh Dama karfe uku na yamma ya dan wuce Almost 10minutes tana zaune a position din da niyyar jiran lokaci dan ta hada da laasar,tunanin yaushe ne ya dace itama ta fada mashi zata tafi?
Sai yanzu ma tafara tunanin nashi tafiyar,she just dont know why he dint say anything again
Daf lokacin sallahn ya mike tsaye shima Tana gani ya nufi bathrum din a lokacin ta fara nitso cikin tunani kala kala ciki kuwa harda tunanin yadda zata fayyace masa abubuwan dake faruwa tsakanin ta da sadaat da big sis subaya.
But its becoming hard a zuciyar ta,sosai abubuwa daya na waswasi suke shigowa,bayan su dija da suka san komai kuma suke ganin komai bata tunanin akwai wanda zai yarda cewa sadat na mata haka.
"...game da maganan sirrin dake makale da auren sadat da subaya kuma bata san ya khal zai dauke maganan ba"...
,banda yau counting as an unsual moment har cikin ranta bata taba tunanin khaldun dakansa zaizo inda take ba bare har ya bata lokacin sa haka ba.
Ahaka ma Ita sam Bata san me nufin sa ba,yazo musamman dan ita kanwar sace koko wani dalili yasa shi ya waiwaye ta?
taga yana tausaya mata kuma ya biye mata fiye da yadda ya saba da chan amma ko kadan bata aminta da komai daga gare shi ba.
More than anyone tasan halinshi ta dde da sanin cewa a murde yake,tsoron ta anan shine kar ta fara gaya mashi damuwarta yayi misunderstading dinta har maganan ya dawo musu wani babban matsala
Aganin ta wannan Maganan babba ne,
Ko ba don cin amanan da sadaat yake shirin yi akan subaya da ita ba,tunanin ta Ta yaya khaldun zai dauki maganan asalin mugun burin sadat akan subayan cikin sauki batare da wani kwakwaran shaida ba..
Bata da komai a hannun ta da zata iya nunawa
Not even phone calls or mesges sabida sadat always has his ways bai taba kira da number sa ko in anyway ya farmata da real identityn sa ba kuma kullum acikin razanar da ita yake da barazanar sa na cewa tayi duk abunda zatayi he is evrywhere.
Cikin juyayin tunani tace"How can she explain all this to khal?He is not a little child,..tsakanin ta da shi daban bancin duk tsiya tasan subaya ce jinin sa na asali ba ita ba,magana da fatar baki kawai wont be so easy for him to take..
gashi anan dai su biyu tasan babu mai karban ta inta kwafsa
Gyaran muryan shi akanta ya hankarar da ita,fuskan sa da alaman ruwan alwala alamane na zaiyi sallahn la'asar.
Mikewa tsaye tayi ta dan kurkura baki tafito sai ta samu ya juya mat din itama sai tayi sauri ta hau ta gyara zaman mayafin ta
Bayan ya tada ikama,cikin nitsuwa ya fara jansu tare cikin wani kamilallen sallah mai cike da tarin abun duba,dan kuwa sosai ta gane cewa ashe shima A ne ta wannan fannin.
Gashi daki daya ne a gidan ba ta inda zataje tayi wani abun ita kadai... aranta kuma tana mugun son taga ta fayyace masa komai.
Bayan sun idar,shikam kan cushion ya koma yana amsa waya da mr pilot anan takejin yana cewa sai gobe zai tafi.
'nitsuwa tayi adan dofane akan gadon ta shiga texting din su jasmine ko da zata ji yadda suke ciki sannan tana mugun son su tayata yanke shawara akan maganan
Hakan ya dauke mata hankali for the main time,musu sukeyi kowa na bada point dinsa in one way or the other confusion har ya shiga hidiman sosai.
Cikin nazari har ya zame ya fita bata wani lura ba sanda wajen ya dada daukar shiru ta dago taga wayam babu shi a dakin..dan kwafa tayi ta mike kafan ta akan gadon,wani story book irin bedtime short stories ta dauka tana karantawa a nitse yana dan debe mata kewa
"..har sai chan 10pm na dare toh da bata gansa ba sai ta dada sakewa a kan gadon tadan kwanta ta jingine tayi shiru
Juyi take Cikin wannan yanayi wani iska mai karfin bala'i ya huro drape curtain a firgice ta juyo rike da kirjin ta daya buga lokaci guda..,tana kuwa juyi kallon bakin windown idanun ta suka kafe sukayi fari, a Wani duniyar ta tsinci kanta.
Sai ta ganta gata nan tana tsaye da kayan jikin ta daga nesa tana hango wasu mutane bakake kirin zaune agaban wani katon tukunya mai ci da wuta
Tayi ta lekowa tana dube dube amma Bata gane fuskan kowa ba,sai dai tana jin abunda suke fada sarai.
Wanda ke zaune gaban tukunyar hannun sa dauke da wani bakar muciya yana tuka wa shi yace ma bakar kurwan sadat"...na kira ka da gaggawa ne sabida yarinyar tana da taurin kai zata bata maka sa'ar ka,. Zata tona maka asiri,dole ne kasan yadda zaka yi da ita yanzun nan.
Wani magana akayi kasa kasa bataji ba kuma ita bata gane cewa sadat bane awajen sabida babu kamannin sa a jikin halittar
Kafin kace kobo har sun iso gaban ta kamar kiftawar bismillahi,..cikin wani yanayin tsoro ta ja numfashi jikin taya hau rawa tun kan ta dawo daga firgitan da tayi mutumin ya takarkare ya doke tsakar kanta da karfi da wannan muciyar sai battt taga ta dawo dai dai bakin ta yana furta
Innalihhi wa inna ilahi rajiun.
wani mumunan tsoro ne ya shige ta,ta rike kai kamar zata tuno abunda ya faru yanzun amma minti 2 baiyi ba ma ta dawo normal,komai ya goge kamar ba ayi ba,Tsikar jikin ta ne kawai ya ke tashi.
Dare na dada yi Lokacin hanjin cikin ta ya gama kadawa da tsoron shirun da wajen ya dada dauka
haka kawai taji wani fiirgici da fargaba ya nakasa zuciyan ta bayan ta ga lokaci yayi nisa sai ta fara kai kawo tsakanin waje da cikin compound din gidan amma shiru bata gan dawowar sa ba.
"A Maimakon ta cigaba da tunanin yadda zata fada ma khal matsalanta kamar yadda sukayi shawara da su jasmine Sai ta tsinci kanta da jin wani tsinannan mantuwa game da issuren mai gaba daya bata iya gane komai....
ayanzu Damuwar ta bai wuci tuninin How can she sleep outside schl ba dan Ko da wasa bata taba skipping kwana a wani waje ba inba dakin su a hostel ba.
Karshe dai dawowa dakin tayi ta koma kan gadon ta zauna
Da Har zata bude book din again sai ta bari ta kife shi abude wani Lumshe ido tayi ta jawo pillow zuwa karjin ta kamar mai bacci tayi tsammm tana kokarin regaining memoryn ta amma duk abanza.
Jim kadan dayin hakan taji saukan wani lallausan hannu akan goshin ta,tana dawo wa cikin senses din ta kuwa ta fahimce cewa shidin ne daff da ita yana kallon fuskan ta..,wani kara kulle ido tayi gam gam batare da tasan dalili ba har ya gaji da kallon fuskan na ta ya zame ya same waje ya zauna daf da ita akan gadon
Dan kadan ya juya ya kalle ta,cike da kulawa yace Bahiyyah!
Taki ta motsa sai yayi tapping gefen gadon da palms din sa,r u sleeping? sorry for keeping late ... ya furta a takaice
Dan karamin boyayyen ajiyan zuciya tayi Tana bude ido a slow sai suka hade ido da shi tuni wani yanayi ya jefa su cikin kallon idanun juna
ya gama lura da halin tsoron datake ciki,...hakan na damun sa amma sai ya basar..
Sai Ta gaishe shi ya amsa yana dada gyara zama kan bed din Yace Bahiyya..
Tana juyawa zata amsa sai yace i kept u waiting ko? sorry..
Ta dan kauda idanun ta,. .Babu komai....its ok ta sunkuyar da kai,wani direct look yake mata batare daya lura da komai ba,ita kuma kanta na kasa kamar wanda hankalin ta na kan book din ne..
Jawo book din yayi shima ya bude,five minutes scrolls ya dube ta ba yabo ba fallasa yace can you read stories?.
Tace yes..cikin sanyin sautin jin kunyan shi..
Hawa gadon yayi mai gaba daya,ayayin data mike ta zauna sabida faduwan da gaban ta yake yi.
Read it for me...ya mika mata book din yana gyara kwanciyar sa just beside her Babu musu itama ta karba
Dan shiru ne ya ratsa wajen ta kafa book din har ido,sai ta rasa wanne labarin zata karanta mashi a halin yanzu da presence dinsa yake birkita ta
Yana kwance agaban ta tana zaune agefen sa with the book still covering her face
tasan duk dama ba kallon shi take ba amma da alaman jiran ta yake ta fara
Which story will u like!..she manage to say in a very calm voice tana dan satan kallon shi ta kasan book din da wayo.
A bazata ya sa hannu ya sauke book din sai ta runtse ido da sauri ayayin da ta sake mashi gaba daya cikin jin kunya sosai
,.murmushi kawai yayi yace
"read story 7...
bai bata book din ba ya rike,tasan jira yake ta karba a hannun sa dakanta
Amma sai ta kasa
Murya na dan
Rawa ta langwame masa wuya so cute tace pls can i have it,...shagwaban ta sosai ya dauke masa hankali,sai ya dada gyara zaman pillown yadda zai fuskance ta da kyau idanun shi still kafin nan ya mika mata book din.
Ba wani bata lokaci ta bude story 7,its a short love story wanda bai wuce rabin shafi ba,..sweet and slow ta fara karantawa wajen ya yanke shiru,tun tana kauce ma pircieng looks dinsa har ta dan basar ta saje kamar bata san yanayi ba.
"Even after her death Sultan neva forgets his maid turn lover, asiyah".
karshen labarin ya karashe da wannan kalman,a hankali ta furta....the end
Wani ajiyan zuciyn
Ya sauke kamar da gaske yaji duk abunda tace,menene sunan labarin ma?
Tace"he is royalty.
"Dan karamin kwafa yayi,yace and is that all?masoiyar sa ta mutu sai labari ya kare ko,a bazata tayi murmushi Ta dan girgiza kai sideways,tace ai ta mutu ne amma har yau suna tare....sai ya gyara zama ..ta dauki book din ta sake bude page seven,throug this writen poem soyayyar su yake numfashi .
..hannu yasa ya karba book din yace let me see the poem..sai ta bashi feeling more comfortable ta dada gyara zaman ta daf da kan pillown sa.
Tsaff ya karance poem din aransa
,cikin zuciyar sa yana masa dadi dan ji yake kamar abubuwan dayake sha'awar furta mata kenan amma bazai taba iyawa ba,..after 10minutes of staring ya aje book din akan cinyar ta..'cikin basarwa yace read it for me ni bangane ba..ba wani tantama ta dauka ta fara bin words din..
Its actually from a song,amma dan author ya gyara labarin sa sai yace masoyan ne suka kirkiro remix din 2 stanzas..
Slowly ta fara from the moment that we met,any moment that i get,all i wanna do is dream about you....When you look into my eyes,i just hope u realised,i can neva live alone witout you.....
Dayan layin kuma
"i will neva forget you,u will always be by my side,from the day that i met you i know that i wll love you till the day i die,and i wll neva want much more,in my heart i will alwys be sure..
Jin yayi shiru sosai yana jin ta,sai kirjin ta ya shiga bugawa
Sai ta danyi shiru itama,ko tunanin meyake oho,sai ya dan motsa jikin shi akasale ya wani lumshe ido yana lumar dakansa slowly cikin pillow..,da wani irin muryan mai kamar mai jin bacci yace 'banaji' is that all,ta dan girgiza kai adan rude da sauri ta maida kanta kan book din,ta karasa few words din daya rage da dan rawan murya Tana cewa ,i will neva forget,u wll alwys be by my sad till the day i die..
Finish....ta daure ta fada tana aje book din akan side drawer cikin sauke boyayyan ajiyan zuciya.
Tana juyuwa taci karo da golden eyes dinsa dar akan nata,thank you,ya furta a kasale..sai ta sunkuyar dakai kasa bata ce komai ba,can i ask? Ya tambaye ta... cike da mamakin sa ta dago cikin sanyin murya tace yes sure..
Why must love die?....
I mean meyasa sultan zai bari maid turn lover dinsa ta mutu,What sort of love is that?
Dan sauke ajiyan zuciya tayi,cikin sanyin nazari tace
Ba bari yayi ba,"she is just scared..
Cikin dauriya ta kalli idanun shi tace...
Scared of broken relationships....
Shima Sai ya danyi shiru,kamar mai nazari kasan makoshi ya furta but one must not secrifice love..
"Tayi murmushi,
Awajen wanda yasan halacci amanan yan uwanta ka ba abu bane mai saukin karyawa,
Asiya Tana son shi amma she choose peace and relationship
Bai motsa ba dan Murmushin ma kufce masa yayi sai ya tabe baki yayi shiru for 2seconds
so you do belive in that?u believe in secrifice?
Ta gyada mashi kai tace yes..its a good thing.
So "love is a bad thing".Ya furta yana dan kokarin kau da kansa
Tace noo,ni bance haka ba.
Bai dai amsa ta ba ya fara shirin sauka akan gadon mai gaba daya sai ta bishi da wani irin kallo.
Misali,Idan ace kai ne sultan zaka ga laifin ta dan tayi haka?What wll you do?
Data furta mashi hakan shikansa Ya dan sha mamakin courage din ta,sai ya dan yi kwafa yana dan kallon ta daga tsaye..
"I don't belive in relationships,sabida babu wani kwanciyar hankali da zaki samu duniyan nan,I wont kill myself for any secrifice.
Mood din Daya furta hakan sanda taji kanta ya wani sara Bata iya cewa komai ba tayi murmushin karfin hali....
Ruwan gora ya juya ya dauko yadan kurba,gyara zaman ta tayi tace but
,The poem is actully nice"when it says from the day that i met you i know i will love till the day i die....ai kenan so bazai mutu ba.
Wani makallen kallo ya bita da shi" yace hmmm ur tots.?
abunda ya bata poem din shine"i will neva forget you"
If only baisa wannan kalman ba i will accept ur own point of view,"those who secrifice only to die in love are loosers... go to bed now..yana kallon tan ya bata comand din haka...
Sai tayi murmushi
Babu bata lokaci ta haura kan gadon
tayi lumui kamar wata kyanwa,... zama yayi yana shan ruwan for some minutes sannan ya tashi ya rage wutar dakin,akan cushion ya mike ya kwanta ya lumshe idanun sa.
Almost 1hr suna shiru,kowa da abunda ke yawo aransa barin ma ita ta datake faman juye juye Dukan su idanun su biyu suna faman pretending da kyar tayi bacci,.
Jim kadan Shima Wani shegen baccin ne yayi awon gaba da shi,kowani awa guda baiyi ba motsin ta ya daga shi,bude idanun sa kawai yayi bai taso ba amma duk yana jin ta
She was seriously shivering,alaman wani mumunan mafarki takeyi.. sai ya kira sunan ta yaji shiru bata amsa ba,tashi yai ya iso kanta yana duban yanayin tan gashi dai idanun ta a kulle amma duk jikin ta rawa yake alaman tsorata ta akeyi
Acikin kwakwalta tana ta kokuwar fincikewa ko zata dawo dai dai ta kira masa sunan sadaat,amma wani abu mai nauyi ya riga ya toshe mata baki,ga wani tsinannen bugu da ake yi ma kanta da sanda kwata kwata bata gane meke faruwa da ita ba...
Agefen ta ya Zauna da sauri tare da dora hannun shi akan goshin ta da wuyan ta yana tattabawa,maimakon ta furta sadat din datake gani cikin wani irin firgitaccen yanayi ta furta
...Abbuhhh..Abbuh...
Addua ya shiga tofa mata hakan ya dan dada hasassa kwalwanta dawowa sarari,jikin ta tuni yayi lagwas sam bata jin wani karfi,tanaji yadda heavy hands dinsa ya tattare ta zuwa kirjin sa
Are you ok? Ya furta yana dora ta akan kafadun sa whith a very calm hug..
Gajiyayun ajiyan zuciya da Qamshin jikin sa dake toshe mata iska su suka tada ta daga baccin sosai har ta dawo cikin hankalin ta,tsaban tsoron daya rufe ta bata ma san sanda taji ta dada shigewa jikin sa ta dada kankame sa ba.
Shima Riko ta yayi gam kamar wanda zaa kwace masa ita,Wani sasaanyar muryan lallashi yasa yana dan shafa suman kanta daya yarfu hannun sa kamar wanda ya samu baby girl
"Shuhhhhh,...go to bed baby,sleep now..
.
Da taji yace mata babyn nan ma Wani sabon shaukin shagwaba da narkewa takeji amma tsoron rudadden mafarkin data yi yanzu ya hana ta sakat
bata sake shi ba sanda ya mikar da ita kan pilow ya riko hannun ta zuwa nashi yana bin inuwar closed eyes dinta da kallin yana murza fingers dinta slow..wani siririn kukan shagwaba tafara masa mai sanyin shiga rai duk saida yaji ya rude,da kamar bazaice komai ba,amma ya daure,muryan sa cike da damuwa yace Bahiyya Whats going on..tun kafin ya dora kalma
Cikin rudewar yanayi tana sauke ajiyan zuciya mai ban tausayi
Tace,Abbu na.. im just an opharn
...Abbuh... i really miss himm..
Idon ta ta rife tayi tsamm kamar bat san metake furtawa ba
Cike da damuwa Yace kinyi mafarkin sa ne? Bata wani amsa ba ta fashe masa da kuka jikin ta atake ya dau karkawa
Dada jawota ta yayi jikin sa Haka kawai yaji ta daga masa sense sosai sai ya tallafota ya aje kanta akan cinyarsa ya shiga lallabata yana mata nasiha da sanyin muryan sa.
'...Comon its just a dream kar ki daga hankalin ki,Addua zakiyi masa ba kuka ba,Everyone is an opharn too,a duniya ba a maraya sai rago,so stop putting up with all this kiyi abunda ke gaban ki. Are we clear...
Cikin sheshhekan da bata san dashi ba ta gyada kai tana jin yadda hannun shi yake dan shafa suman kanta yana aikin lallabata..
A haka har sai da tayi shiru wani bacci mai dadi ne ya dauke ta akan kafarsan ma bata sani ba..
Shikuwa bai aje ta ba Ya dade hannun sa na shafa suman kanta har zuwa fuskan ta with slow mesmerising moves yana tunani.
Cikin nazari ya shiga gamsar dakansa cewa lallai bahiyya tana cikin maraicin iyayen ta ne
Ko dai shine abunda ke damun ta tuntuni daya kasa ganewa?
But she have everything,muhalli mai kyau, kudi ga kuma kulawar su subaya.
Dan tabe baki yayi cikin ransa yace
Ko da shike komin dadin iyayen wasu naka naka ne,shima Kanshi ya fara sawa a position din ta gaba daya sai yaji tausayin ta ya kashe masa jiki
.
He just wonder in haka take bacci to waye xai tsaya mata har ya dinga calming dinta!..
Wani shaukin son ya cire ta a dukan damuwar ta a take ya ziyarce zuciyar shi
Sai ya gudira aransa cewa muddin ya bincika ya ga cewa bata jin dadin london,batare da sanin kowa ba ma zai dauke ta zauna agabansa don ya cigaba da kula da ita achan america.
Kwantar da ita yayi akan gadon ya rufe ta,idanun sa gaba daya nakan gajiyayen nunfashin ta dake sauka har tana bipping slowly
She looks more alluring,kywun ta ne ya ke dada haske kwayar idanun shi musamman daya ke babu kwalliyar komai akan fuskan zallan halittar Da Allah ya albarkace ta dashi ne
Yanayin yadda ya dan shafa gefen fuskan zaka san kyaun ta ya tafi dashi wani duniyar
Koda ya koma ya kwanta tunani yake to meyasa wife to be dinsa bata da qualities masu saurin burgewa irin na bahiyyar sa?
Baisan meyake ji ba amma a duninyan sa inda duka mata zasu dawo masa ita bazai damu ba
Da safe Ita ta tashe shi sallahn asubahi dan Da kyar ya runtsa kowani motsi
Tayi Idanun shi nakanta
Ayayin da suke sallahn He was bit louder tanajin daddan kira'ar sa,wanda ya kasance tamkar mafifici ma rudewar dake cin zuciyan ta
Duk abunda yake yi na mata dadi matuka,sannan har yanzu bata ji da alaman wani abu ya ragu aranta game dashi ba
suna idarwa,ya shiga tambyarta lpyar ta,sam bata so ta nuna mashi kamar tasan abunda ya faru jiyan sai tayi masa shiru komai yace zata amsa masa da alhndllhi ko da sauki
He is atill feeling sleepy sai ya kyaleta ya kwanta akan cushion still,itama baccin yayi sugesting mata amma sai ya riga ta yi.
Hakan ya bata daman yin wanka..
Sai Ta dan shanya rigar ta dan ta samu daman maida shi jikin ta kafin ya farka su tafi
Da White towel daure akan kirjin ta tana jira har ta shigo
a kasa inda yake bacci akan cushion din ta rakube daga gefe, ganin bai farka ba sai ta dada matsowa kusa da shi,tana ta kallon sa har bacci mai nauyi yatafi da ita itama.
Almost 1 hour suna famar shakar nunfashin juna ,sai cahn daya motsa jikin shi yayi juyi kan fuskan ta ya fara sauke gajiyayyun idanunsa dake kwacewa suna rifewa suna bude kansu,..gashi yanzun mafarkin sa ya nuna masa kansa yana kissing dinta
Da karfin balai ya kwace idanunsa ya dawo hankalin sa tukun Sai ya farka gata nan agabansa da towel gwanin sha'awa ya kuma gane shi take kallo har tayi bacci.
Wani bakon yanayi yake ji nabin jinin jikin sa dan haka sai Bai bar kansa yayi ta kallon ta ba ya mike slowly ya sauka akan cushion din,inda bazata ma ji shi ba
Wanka ya fada sharp sharp ya fito ya tsaftace kansa.
Ya dube ta Har yanzu tana kan deban bacci,kallon 5 seconds mai cike da unsaid feelings ya bita da shi very galant lips din ta na mugun tempting dinshi...wani bin har yaji kamar zai tsuguna yayi kissing dinta,but wani abun yanace masa is not the right din to do
So to avoid all that kawai sai ya dauki wayar ta ya sa phone numbersa yayi dialing ya goge.
Akan story 7 ya rubuta mata
"My flight is waiting on me, i hope u have a lovely day ahead_..sai ya zana round faced cryng emoji ya yayi crossing" alama ne na ce mata kar tayi kuka....ayi karatu lpya..!
ya kife book din akan gadon ya fita yaja mata door din bai tsaya ko ina ba sai united states.
#SURAYYAHMS
Sannun ku da kokari voters and comenters Insha Allah i will see this weeks coments,da shi zan duba naga in ya dace na muku full two weeeks post +weekends
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top