chapter 14

_1⃣4⃣-the promise♡_

Junnut itace asalin jini kuma jikar dilshad khatun na karshe A duniya wanda a yanzu babu wanda ya kai sarauniya dilshad kwallafa rai akan rayuwar ta.

Da suka zo persia A hannun jahan khatun dilshad ta damka junnut,a yanzu kamar yadda jahan Aarah take iko da khaldun sa'ood da subaya a matsayin yaya haka itama jahan khatun take da junnut da kaamil a mtsayin yaran ta.

Toh tun ranar da aka miko junnut persian,a kingdom din dilshad khatun ta tsara mata sabon rayuwa mai cike da gata.

A karkashin kulawar jahan khatun take ana nuna mata son uwa da uba sai suka hadu duka su ka maida ta tamkar yar kwai.

Komai ana mata ne cikin yelwata da tsari tamkar da asalin princess,gashi tayi farin jini sosai musamman a farkon zuwan ta daulan da shike junnut din ta zoda sauran tarbiyan mahaifiyan ta na sanyin hali da kyaun zuciya,sam bata cika surutu most time zuciyan ta a cike yake da tunanin kawar ta bahiyya.

Gashi Kaamil a America yake aiki yake kuma zama dan haka bai wani cika zama anan ba amma a halin yanzu babu wanda ta fi shakuwa da shi kamar sa.

Toh A watan ta na farko a persia dilshad takan ja ta gefe tana nuna mata hotunan khaldun sa'ood wanda mafi akasari duk ta sa anyi sihirin muhibba mai karfi akan su.

Dilshad tana alfahari da jikar ta junnut,aganin ta junnut kyakkwar mace ce ta ajin farko dan haka Burin ta na farko akanta bai wuce ta dora ta akan fuskan mijin da take hango mata zama da shi na har abada ba.

And For junnut ranar da ta fara dora ido akan hotunan khaldun saood ta fahimce cewa it was love at first sight.

Jahan khatun ne dai bata bada hankalin ta anan ba,
Dan kuwa tafi bada karfi wajen goge ta tass dukiya da kwalliya ta yadda zata yi level up dai dai da irin rayuwar da suke yi.

A hakan kafin ayi rabin shekara aka nemi tarbiyan junnut aka rasa shi gaba daya.

Sai aka rasa Laifin jahan ne koko laifin dilshad khatun duk dai bazaka iya banbancewa ba

Domin kuwa Junnut gaba daya ta dawo wata sangartacciya Idanun ta sun soma budewa sosai

Bata jin bari,Badon komai ba sai dan tarin dukiyan da aka zuba agaban ta kuma gashi an bata cikakken dama akai tana facalin ta inda ranta yake so babu kuma mai hanata.

Most times a chan wajen kaamil take zuwa hutun bude ido a US inta dan gaji da zaman kingdom din.

Gashi Duk wani na miji na daban acikin maza inhar ba wanda ta zaba ma ranta ba toh ko maye ne kuwa sai ta wulakanta shi.

A rayuwa ita Soja take so,shiyasa ma suke mugun shiri dan uwanta adm kaamil hamood.

Da shike anan US din yake aiki sai ya zamto shine close quardian din ta ba acika tura ta kasar da kowa ba ma in wajen sa zata zo

A iya zaman shekara da tayi dasu Kaamil  hamood Shi yake bata tarihin rayuwar big brother sa wato khaldun sa'ood.

By now Junnut tasha ganin zaratan sojoji tsakanin us da persia amma har yanzu bata ga wanda zata hada shi da tasirin da hoton khaldun yayi azuciyar ta ba,ita tun da aka mika mata pics dinsa a kingdom kullum ta zo bacci sai ta kalle shi ta koshi.

Gashi dai basu taba ganin juna ba  but she is just wondering A Kullum in kamil xai bata labarin saood sai ya nitsu sosai toh abun na burge ta na kuma shiga zuciyar ta matuka.

duk iya yadda ta san kaamil bata taba ganin shi ayanayin da yake shiga ina yana maganan khaldun sa'ood ba

Basai an fada mata ba tasan a duniyar  Kaamil kam khaldun sa'ood na daban ne.

Bayan wani lokaci ta dawo gida daga hutun bude idon data je, Ana daf da gamawar ta secndry schl ranar da safe dilshad khatun ta mata sammako suka tafi har kasar india

Da alaman Hankalin dilshad khatun yayi matukar tashi dan ko murmishi bata iyawa,ashe abu wanda ya sani tun jiyan aka aiko mata sakon cewa anyi duba an gano cewa tauraron junnut dana khaldun saood basu hadu ba dan haka aure zaiyi matukar wuya tsakanin su..
Aranta tace bazaiyuwa ba

Gidan wani mutum aka kaita Gidan kamar temple din bautar gumaka duk an sakaya shi da jan kyalle an kuma ajiye wasu halittu ga hayakin dake tashi daga manyan kaskon wuta wanda  batasan me  aciki
Ba.

Wani tsohon ba indiye ne ya fito kirjin sa babu riga ya daura farar kyalle a kugun sa ,goshin sa an zana farin layi har zane biyu

Yaren su yake yi dan haka ba sujin meyake fada .

Wani daki ya nuna mata anan aka shiga aka fito da ita daure da jan yadi
Ta fito narai narai
Ko dan kwali babu akanta.

Ita dai binsu take amma badon taso ba domin kuwa idon jahan khatun akan ta yake ya kuma hanata yin komai

wani shirgegen bath mai fadi da sakewa mutumin ya mata nuni yace ta shiga har sai da ruwan dake ciki ya rufe mata goshi

Aciki ta nitsu,ba abunda take yi sai yatsine, Sau uku mutumin yana sata tana nitso tana fitowa daga bisani sai yace ta fito ta zauna akasa

Tana zama ya shiga wasu irin addaoin irin nasu ma india,yana turara ta da wani irin hayaki..

Jahan khatun tana zaune tana kallon su haka ma sarauniya dilshad .

Haka akayi ma junnut wannan wankan sau uku har na rana uku kafin nan suka fara shiri zasu dawo gida.

Junnut tayi jahan khatun ta fada mata menene wannan din amma sai shiru wani bin sai tace bazata gane ba.

Haka suka dawo persia babu wani kwakwaram bayani
Daga bakin su Da shike ma yau wata 10 kenan rabon kaamil da little lorestan sai ya zamto ita kadai ce a kingdom din Tana ta baza mulkin ta bata da madakata

Her dreams of beign a high level slay queen sai ya bayyana mata sosai a tafin hannun ta  yanzu sai yadda tayi da rayuwar ta.

A duniya abu daya ne kawai bata iya ketare shi kuma shine dokokin jahan khatun ko na sarauniya dilshad khatun in sun furta.

Dan ayadda suke tarbiyan tar da ita cikin tsananin gata da so Zaka rantse jahan khatun din itace mahaifiyar junnut na asali ba yar uwan ta jahan zainobia ba.

Duk wani bururrukan junnut iri daya ne da tsarin Jahan khatun akan hidimar rayuwar ta

Wani bin in kaji suna hiran duniya zaka iya cewa tabbas jini daya ba wasa ba ne,don kuwa yadda junnut take da tsantsan burin taga ta kai wani level a duniya haka ma jahan khatun ta saka aranta game da ita sosai.

Toh Da ra'ayin su ya zo daya sai komai yake tafiya musu dai dai.

A Yanzu da junnut ta kai sha shekaru sha shida cif,A United states inda kaamil yake ake ta shirin tura ta cigaba a karatun gaba da secondry

Dama zuwan khaldun sa'ood ya dakatar da saka ranar tafiyan ta university sai gashi shiru baizo ba.

*** *cigaban labari*
Cikin masarautar khorshidy

Karfe 12 da dan dori wata classic private jet ta sauka a makeken super huge lane dake khorshidy mansion.

Daga focal view dinka zaka iya hango wasu twin gambrel roofs akan kowani edge na flat dake cikin gidan

Tsarin gidan gaba dayanta ya tsaya a theme din 1920s art decor ne.

Daga waje zaka anyi exagerating undulating contours  an kewaye ko ina da flowers bishiyoyi da shukoki

Komai kuma anyi shine da sleek metallic finishes,
stainless steel,sai kuma glasses and chrome Inda ko wani shashi cikin gidan akayi higlighting dinsa da floral patterns
,jagged and pointed edges,rugs da featured graphic masu linens print kamar sun burst da zigzag.

Duka duka Chairs,dresser,airmores, headboad da duk wani funitures din su yana da girma sosai sannan dukan su dark colours ne.

Ahakan ma Dai dai kun wajaje ne zaka ga ana kawata su da white or brown decors bayan wannan bazaka taba ganin wani colour ba a masarautan ba.

Isowar gen hamood wannan gida yasa dilshad khatun ta hada wani babban feast inda aka ci aka sha tsakanin ta da shi da matar sa jahan khatun da kuma junnut da sai yau ya  ganta da idanun sa

Agaban su ya yi cikakken bayanin cewa khaldun saood bazai samu halin zuwa ba sai bayan wani lokaci.

Da shike sunji ance aikin sa ne ya rike sa sai basu damu ba sai kawai suka sanya albarka.

Toh ana washe gari gen zai koma  inda ya fito,Kafin tashin sa ne dilshad khatun take kawo masa maganan hada Alkwarin aure tsakanin jikan ta junnut da babban dansu khaldun sa'ood .

Cikin nitsuwa nuna isa da kasaita take maganan

Cewar ta junnuta jini tace,idan muka yi wannan hadi Ba xallan zuriar mu hatta ubangijin mu zai bamu ladan karfafa wannan zumunci.

Gen kam ya sha mamakin wannan magana dan aganin sa yanzu ai ba kamar da chan bane amma da shike ya lura ta mugun nuna damuwar ta sai ya ce to abar maganan har sai khaldun ya kammala ya zo dakansa sai ayi komai ..

Cike da wayar da kai Ya kara mata da bayanai cewar sa
Tayi hakuri,Shi tun bayau ba yasan tsakanin sa da yayan sa akwai banbancin wajen biyayya sabida yanzu yaran zamani idanun su a bude yake.

Aranshi kuma ya bari cewa Aure hurumin rayuwar dansa ne,bazai so kuma ya tursasa masa auren wanda baiya so ba.

Sarauniya Dilshad tace haka ne taji ta kuma gamsu,ta kuma amince za ajira khaldun ya zo sai Ayi magana amma itama aranta sam bata so jin sabawar amsan daga wajen gen ba .

taso ace ya bi akalar ta kai tsaye kamar yadda ya saba amma da shike tana sane da irin shirin datayi akan khaldun din toh tasan inhar ta ce mashi ga junnut bai isa yace mata A'ah ba,Haka dai aka bar magana tsakanin dilshad da gen hamood.

To duk ana maganan hadin auren nan ne amma dilshad bata fito fili ta fayyace ma jahan khatun komai ba sai dai inzatayi abu ta bata umarni wanda dole ne suke cikewa babu tambaya.

Daya fito zai tafi Toh Jahan khatun din ce ta masa rakiyar har bakin inda jet dinsa inda zai tashi

Daga nan Tafi mintuna goma tana tunani Bayan tafiyar san babu wani bata lokaci ta juyo a haukace dan kuwa har yanzu
Kanta bai dena juyawa da abubuwan da mijin ta ya gama fada mata game da maganan auren junnut da khaldun saood da sukayi da dilshad ba

Kafin su rabu Agaban sa kam  bata nuna komi ba amma ayanzun Tafiya take cikin sauri da hatsala bata ko damu da yadda jelar abayan ta yake bin kasa da shara yuuuuu yana sandarewa ba.

burin ta bai wuci taga kawai ta isa gaban dilshad  khatun ba

cikin dacin rai da bambami take sauke maganganun zici
Ya za'ayi mamah tayi min haka?
Ohh dama shiyasa ta bada junnut hotunan sa'ood ranar dan tasan zatayi nata zabin kuma bazata zabi dan ciki na ba?

Toh A gaskiya bazan iya ba,i cant let that happen jinin wancen mayyar bazai bi jikin yata junnut ba,tsaban idon ta ya rufe cikin sauri a durkufe ta saka kafa cikin babban falon dilshad babu ko sallama ko gyara dilshad din ne a zaune agaban ta akan throne tana binta da ido

Data juya ido Wani tsawa mai birkitarwa ta ma bayin wanda atake suke zame suka bar harabar wajen baki daya

Cike dauriya ta Dan rusuna kai,muryan ta har na srkafewa cikin tuhuma bacin rai da nuna rashin fahimta bata tsaya yin wani gaisuwa ba ta fara da cewa

Na kasance mai maki biyayya tunda har kika sani na so kuma na raini dan wanda nafi natsana a duniya kamar dan ciki na

tace Tunda junnut taxo gidan nan hoton saood kawai ake nuna mata why not my son kaamil.?

"MOther,..pls ki gaya min dalilin da junnut zata auri sa'ood ba dana kaamil ba

...yafi shi kyaune?aji kudi ko gata ?
Why....why mother sai ta juya kai tana hushi mai zafi

Kallon ta kawai sarauniya Dilshad takeyii batace komai ba har sanda ta gama bambamin tayi shiru kafin
Ta sauko daga kan kujeran mulkin ta tsaya da dan sauran karfin ta

tace

"Hmmm lallai Kina da yawan mantuwa khatun,.wai shin kinga laifi na dana fiye son na dauke wahalar yi miki tunani akan abunda xai fishe ki da rayuwar ki.?

Tabbas nace junnut khaldun zata aura
Ba kaamil ba

Domin kuwa Junnut da kaamil duk jinin mu ne kin sani na sani kowa ku maya sani

amma tsakanin kaamil da sa'ood
Ke kinsan waye dan halak acikin su.

Bayan firta wannan kalman Wani shiru ne ya tsinke a wajen kafin dilshad ta cigaba

Shin in na mutu haka ke zaki tafiyar da rayuwar ki babu tsari?,banyi tsammanin dan nace haka har ya dame ki ba dan kuwa gata mai girma zan miki da auren nan

Dada Matsowa kusa da ita tayi kamar wacce zata mata nasiha,tace dube nifa, na tsufa kuma mutuwa ta na ke hangowa,toh Wani amfana zakayi idan Shi kaamil ya auro junnut,cikar burin yan uwantakar mu?in na mutu ai zaynobia bata ma duniyar ai 

Ohhh my zain,yarinya ta mai tsananin biyayya
,Allah ya sa jikata junnut ma ta sha jinin ta

Ke kuma sam bakijin magana ta khatun,da kinaji da tuni kin koma chan nigeria inda mijin ki ya gina musamman domin ki ,ai ko ba komai dai tasan ba tsoron ta kike ji ba da kika ki gidan miji kika zauna agaba na.

Baga shi kin bar tan ba?Toh nidai yau naga sauyin yanayi a halayen hamood har da furucin sa.

Im sure matar sa ta fara cin galaba akansa da bin malamai da yan tdubbu,na lura ma yanzu itace uwar sa da ubansa wai bakiji meyace min ba?wai ni na jira dansa yazo da kansa kafin subi umarni na
mmmmmmmm

Toh Idan baki bari yarinyar nan ta rike mana dan masu gida ba nan gaba zamu zama tarihi marar ma'ana a rayuwan nan.

Mijin da kike takama da shi din sai mun rasa shi ni dake kuma gaba daya duniya zata zage darajar mu.

A razane jahan khatun ta dago cikin wani irin yanayin barazana,tace zan rasa mijina fa ki kace?Akan Aarah?tabbb ashe a nigeria za a fara kuwwar tashin duniya,dan kuwa tana daf da konewa kurmus. why r u saying all this wai ma Mai kike nufi ne mother

"Murmushi mai sanyi dilshad tayi tana mai sauke ajiyan zuciya,tace
Please Do not pretend khatun  nidake ne anan babu wani batun boye boye

Tuni  jahan khat ta sauke kanta ta kasa tayi tsit,wani shiru wajen ya dauka for some moment
Data dago, Eye ball to eyeball suke kallon juna

With much seriousness dilshad tace khatun
Kiyi tunanin Wata rana dole gaskiya zai fito kuma dole hamood zai san cewa Kaamil danki ba jinin sa bane jinin saurayin ki ne dan sarki maheer

Hamood zai san kin rike cikin wanda suka raba shi da iyayen sa acikin gidan sa.

kinga ke zai rabu dake haka nima zai watsar da ni dan babu cin amana a tarihin zuriar yan uwantakan mu da shi

Amma kuma akwai tarihin HALACCI da kuma SOYAYYAH da shi kuma zanyi amfani na daure tasirin auren ki kafin na barki a duniya

Yes,Idan kika ce na nuna hutun saood ma junnut dan ta so shi fiye da kaamil ne bakiyi dai dai ba.

Ai nima Ina son kaamil din amma bada junnut ba shiyasa kikaga ban hada su ba tun farko,daga yanzu junnut itace makamashin  rayuwar ki
Da babu gwara ba babu dadi
Ki dena tunanin sihiri ya binne gaskiyan maganan asalin kaamil tunda Wata rana nikaina zan mutu,kisan kuwa komai kararre ne.

Dokace Dole khaldun sa'ood ya auri jinin mu junnut kuma wannan shine kullin auren da zai baki daman zama a rayuwar hamood na har abada koda asirin mu ya tonu
Nasan hamood da matarsa bazasu so su tozarta rayuwar dansu ba kinga kenan junnut zata kasance qashin kifi a wuyar su Duk abunda zai faru bazai yi muni ba kodan darajar wannan aure,kina fahinta ta?Kinji ko bakiji ni ba?

Jiki a matukar sanyaye jahan khatun tace naji,
Lallai nayi wauta mamah! Agafarce ni

Toh tun daga wannan lokaci suka hade kai akan maganan,sai dai kuma babban abunda yasha musu kai shine yadda  auren zai kasance

Shin ayi aureb tun a yanzu a kuruciyar ta ne koko su jira sai yarinyar ta kai munzalin da zata iya murza musu kambun su da kyau?

Bayan kwana biyu junnut din ce kwance akan wata sharbeben canopy bed wanda yasha kwalliyar dark purple and silver linens.

Maid ce ta shigo ta rusuna a kasa tayi gaisuwa,junnut bata ma sanda da ita tsaban yadda tasa hankalin ta gaba daya akan game din data keyi

Haka baiwar tayi dakon jiran ta har wajajen mintina 10 sannan ta juyo tana da kyankyami dan haka ta yamutsa fuska cikin kasaita tace meye hakan?

Maid sai ta dada matsawa baya Tace Ranki shi dade sarauniya dilshad ce ke neman ki.
Follow#Surayyahms and vote
Jumuat and Happy weekends dearies
Fatan idan mun dawo da sabbin posts ranar monday naga coments din dayafi na posts din wannan satin zafii💋 i so much apreciate ur efforts lets meet in the coment section

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top