chapter 1
Page 1
_the HORN OF AFRICA_
This is how our bahiyyah looks like!
Misalin karfe 6 na safe ne,Juyi nake ina kikkiftawa salon kwace baccin gajiyar da har yanzu yake bibiyan idanu na.
"Yau ma Daga inda nafi kwanciya a chan dungun daki na tattaro karfi na duka nayi mika don na watseke,da kyar na waro idanuna dan kuwa Bibbiyu nake gani har wani jiri ke deba na,hakan kuwa bai hana ni daddagewa na zauna tsam ina muzurai ba sai dai duk da haka idanuna sunyi dishi dishi kamar wata mai kallon gajimare.
sanda na dauki mintuna uku da hannun dama na ina yarfe su kafin suka dawo min normal sai dai har yanzu Basu nuna min abbu na ba.
'Wani irin faduwar gaba ne ya taso min"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun! Na furta acikin zuciya na.Wani mugun fargaba ne naji ya rufe ni atake,a hujajan na mike tsaye ina dube dube dan bansan sanda sanyin sautin murya na ya fidda sautin sunan sa ba'..cike da damuwa na fito ina cewa
ABBUH...!
...jiya cikin dare Abbu ne akwance kusa dani kamar gawar da yaki kabarin sa.
Dan Daga ni har shi bansan ya akayi safiyan yau ta riske mu ba.
duba shi na shigayi sai dai ina dora kafata bakin dakin daya raba jingar karar dake tsakar gida sai na hango rayawar karan masara har an sakaye kofar bayi dashi alama nacewa da mutum aciki yana zagaye.
'Bayin nadan bi da ido na dan wani lokaci domin na tabbatar ko shine aciki,bayan kamar minti biyu nayi ajiyan zuciyan tare da sauke boyayyen nishi nan na juya na koma cikin dakin dana fito.
"...Yagaggen Tabarman kajinjinin dabinon da muke kwana akai na dora hannu na akai na jawo shi batare da na nade ba na karkade duk kasan dake kai na fito dashi waje.
A jikin dangar kara daya suturce mana asirin jimammiyar muhallin mu na tsaya,sanda na zare kararen da suka rage mana na hura wuta sannan na yarfa tabarman akai na juyo tsakar gida.
Daga nan A Gaban wata dakilalliyar ramin murhu nayi tsugune,Hura wuta na shiga yi da gaske domin sanyin safiyar mu ta sha banban dana kowa a yankin mu.
"Sunana Bahiyyah Ahmadu Alba.
ni Bansan daga ina muka fito ba bare nace na san asalin mu amma yanzu haka a wata katafaren yankin jeji mai tsananin sanyi da duhun itacuwa muke zaune nida iyaye na da jinsin zuriar wasu fulani wanda su ba bakake ba kuma su ba farare ba.
Nan din Yanki ne
Daya tsaga tsinin kahon nahiyar africa,Kenan mu ba acikin wata kasa muke ba.
A cikin kasashen afurka da suke zageye damu kuwa sun hada da ethiopia,somalia,djoubuti da cibiyar bahohin ruwa guda biyu wato quardafui da somalian sea,sai kasar kenya dake gudu maso gabas.
Shiyasa ma idan anka duba yankin mu da kyau sai inaga kamar muna cikin wani tsauni ne a chan Cikin dajin daya ya raba gulf of eden da kuma bahar maliyar(red sea).
Tsawon shekaru na a duniya na dauka acikin wannan yanki aka haife ni,Sai dai nasha mamaki sosai a lokacin da ammu wato mahaifiya ta tazo gaban ta na mutuwa.
Anan ta take sanar da ni cewa ita cikakkiyar yar kasar somalia ce.
A somalia jinsin yare biyu ne,ko ka kasance arab ko dan somali.
Toh Ammu na balarabiya ce tar dan cemin tayi bata ma jin yaren su na somali a duk dama larabci da somalin suka dai ne yaren da ake yi a kasar..
Tace min Abbuh wato mahaifina kuma dan yankin ethopia ne gaba da baya,A wajen cin kasuwanci a boader chan mahadan su dake wajen kasar djibouti ta hadu dashi.
soyayya mai tsananin karfi yayi sanadiyar auren su.
Daga nan A takaice Iyaye na sukayi zaman aure a kasar ethiopia wato garin mahaifina sai dai Rayuwa na shudewa dangi suna ta mutuwa,kafin a hankara rayuwar iyaye na ta koma garin mogadishu wato state capital na kasar somalia nan inda aka haifeni.
Anan ma Ko shekara guda banyi ba Koluluwar Yunwa
Da jarabar tsiyan talauci irin na kasar somalia ya sa akayi wata karamar yakin daya rabamu da kowa da komai namu a duniya.
Dan haka muka yi hijira muka bar somalia,dan tun ina Jaririya hijirar ya kawo mu wannan dajin inda muka hadu da jinsin zuriar fataken fulani mu kayi zaunen mu a cikin su muna rayuwa.
Gashi har Yau shekara ta goma sha hudu bamu bar nan ba.
A shekaran daya gabata ciwon daji yayi sanadiyar mutuwar Ammuh kuma tun mutuwar ammun Abbu ya kamo da mummun ciwon zuciya wanda nikaina na rasa gane wata irin tsaninin so da shakuwa ne ke tsakanin su,my dad cannot live without my mum
shakuwar su tasha banban da irin shakuwar masoyan zamanin yanzu.
A da chan,Allah ya bama abbu na baiwar magance cututtuka da sanin warakan ciwo ko da sanadiyar mutum ne koko na aljani.
Abbu na yana da baiwar shiga jeji yayi farauta kuma ya tsinko ganyayyaki,itacuwa da saiwa kala kala,yana kuma iya sarrafa su ta yadda yake so domin a samu sauki,da waraka akan kusan ko wani irin cuta.
Tsawon shekaru yana taimakawa amma yau Sai gashi har Abbu na yakasa gano itace ko wani ganyen da zai masa maganin Ciwon son ammu na dake damun zuciyar sa.
Mutuwar Ammuh kamar faduwar wata danga ce agare mu gashi abbu yasa abun aransa sosai fiye ma dani.
"Sai Gaba daya ya dena fita ko ina,tun lokacin ya tsayar da duk wani harkan sa ta siyar da magani gashi har ciwon zuciyar yayi tsanani ya kama shi ta inda bazai ma ji maganin gargajiya akan lokaci ba.
A Yanzu Buri na na sami taikamakon da zai wadatar dani har na kaishi ganin likitar bature a chan yankin kasar egypts inda nake karatu
dan naga suma suna shigowa kasuwanci a yankin mu kuma bamu da wani nisa sosai.
Ko da nayi yunkuri sai naga Jikin abbu yaki sam,A kullum tsoro na kar abbu shima ya mutu ya barni dan bansan ina zanje ba.
..........
A haka Ina zaune gaban murhun,idanuna
sun yi lufu lufu da hayakin danyen karar dake ci Da kyar wutar murhun ta kama tana ci bal bal tashi nayi na jawo kwaryan dake gefe na,don kafin nan na dan tsaftace wajen danake zaune,sai kawai na dora sauran gasashen namar rago da muka ci jiya domin shima ya turara musamu na sawa a bakin salati.
Asali dai Bamu cika cin abincin da ya shafi ganye ko itacuwa ba,,dani da iyaye na gaba daya We are not much of vegetarians.
Dana zo daga baya ma na san asalin tarihin ammu sai na dena bata lokaci na wajen nazarin yanayin cin abincin mu.
Ammuh tace min a chan somalia haka nan suka saba iyaye da kakanni,suna nomar turmeric wato(kurkurm) curry da kuma corriander,abincin su kuma daga namar rago,
namar shanu kaza da tinkiya,
Sai basmati rice.
Hakan ya dada bayyana min tasirin halin talaucin da kasar somaliar take ciki,amma tunda muka dawo nan alhamdullhi zamu ce,duk dama munsaban amma Abbu wata rana yakan sa muci zallan yayan itacuwa ko ganyen alaihu,tufa,cerely,gurji,karas,ibini da dabino da kuma ganyen lettuce.
Mukuma mukan bashi hadin kai ne A matsayin sa na masanin kariyar cuta sai muke biye mashi mafi akasarin lokuta muke sauya abinci.
"Ina zaune gaban murhun,Daga baya na na Ji karar sautin takun sa,mikewa nayi na juyo ta inda zan ganshi da kyau as usuall tsaye yake cikin dakakkiyar rigar jumfa wacce take suluk babu shape,rigar ya dan tsuufa amma fari ne tass wandon kuma kalar kasa ne,he is looking neat babu lifo,don a duk dama ni karama ce bai hanani tsaftace abbu na ba.
Tsaye yayi hannun sa rike da buta ya tsura min hasken fararen idanun shi yana kakalo murmushi kamar bashi bane mai sani kukan tausayin kaina ko wani dare.
Domin son yaga nayi murmushi sai ya yabani da kalman larabci yana mai cewa Saiiqah...yah noori...!
Nikuwa Yadda ya furta kalaman nan naga kuma yana kallo na yana murmushi sai ya sani naji wani tsananin kaunar sa da tausayin sa ya tsuma ni...a take na mike tsaye ina kallon shi
Hannun shi naga ya ware duka biyu ya buda min,ni kaina Bansan sanda na taho kusa da shi na rungume sa ba..gam ya dada matso ni tamlar wanda zai maidani cikin sa"wani sanyin hawaye mai shiga rai shi ya kufce min ayayin dana kankame sa nima jiki na dik yayi weak a haka na furta ABBUH ban karasa ba....sai naji ya shafa kai na,A hankali na kuma furta ABBUH NA, HAMMAM dina,
Wano Dada kankame ni yayi jikin sa sai rawa yake alaman shi kadai yasan meya keji ajikin nasa,a haka ya dago fuska ta zuwa nashi yana min murmushi mai taba zuciya da sa sanyin rai...
Yace yata shin waya koya miki kalmar "hammam" bacin nasan ke baki iya larabci ba?..hakika kalman tayi min dadi...bayan matata zaynah,a duniya ke kadaice zaki iya gayamin wannan kalma mai dadi kuma naji dadin shi.
Share guntun hawaye na nayi ina murmushi sai Na sunkuyar da kaina na seconds biyu..
Cikin farin cikin da bansan na meye bane na furta.
"Abbu,ranar a kasuwar kofar gidan modibbo naji wani balabaren egypts yana fada ma sarki 'hammam" shikuma sarki yaji dadi sosai har ya masa kyautar azurfa.
Shine Sai na tambaye shi ma'anan kalman shine yake cemin kalma ce ta girma kuma ba'a cewa kowa hammam sai mutumin da ya cika abun Alfahari,abun koyi,abun kauna kuma abun tinkaho..
Hannun shi na kama fiska ta na sake wasu irin disasshun murmushi:
nace Abbbu..kai ne abun alfahari na Allah ya baka lpya abbu na.
Dan Shiru abbu yayi,Sai Na lura tsaban farincikin abun da nace yanzun yasa abbu na baice komai ba.
Nidai karamar ajiyan zuciya nayi
Hannun shi dake famar sacewa da tsaninin sanyin dake busowa na riko cikin idonshi na furta
...wai shin yaushe zaka warke muje jeji ne,..?abbu na
Ina so na raka ka deban magani kaga kwana biyu kudin mu duk sun kare..ko ka mance lokacin da kake dauko ni akafada muna tsintar ganyen mu?ko dan ammu ta barmu shikenan kai zaka dena rayuwan ka dani?.
Kokarin Sake kiran sunan shin zanyi amma ban ko karasa kalmar ba ya rufe min baki na da yatsun sa..cike da sanyin jiki ya jawo ni jikin shi Tsam sai naji ya sake rungume ni..
Wani Ajiyan zuciya na sauke Nima sai na lafe ina mai sauke ajiyayyan numfashi.
Wani shiru ne ya ratsa tsakanin mu Tsawon lokaci sannan abbu ya dago ni yana mai kallon fuskata,nima kallon sa na tsaya yi dan daga ka ganshi kasan maganar dana furta ne yayi tasiri a zuciyar sa sosai.
But Maybe am too young to understand what love is shiyasa bazan fahimce rashin dauriyar sa akan soyayyar sa da ammuh ba.
Anma kuma Ba sai an fada min ba nasan abbu yana nadaman sakani cikin halin da nake ciki yanzu sosai.
Sai da ya kure ni da ido Kafin ya numfasa da dai Kamar wani magana zai min
sai naga ya sake min hannu na da sauri ya juya dubar sa kan abunda na daura akan murhu..
Ashe namar dana daura a wutar ne ke famar babbakewa nikuwa tsaban shaukin kasancewa tare da abbu na yasa ban ma ji ba,da azaman sa ya sauke namar yana yarfa hannu...
Da sauri na matso,ina cewa mugani...tafin hannun shin na riko inda ya kone ina furawa da iskan baki na inai masa sannu cike da so da kulawa..
Ina Cikin haka Kwasam sai naga dison Hawayen shi ya digo akan hannu na daya ke cikin nashi,sai dai bai ma bari na daga ido na kalle shi ba ya goge idanun shi da sauri ya kuma zaunar da ni kan dutsin dake wajen baice uffan ba ya juya abunshi
Nidai Ina ta kallon shi Har ya gama tsatsame naman ya aje agabana,sai ya dauki kwara guda
Yace yi bisimillahi
Inayi kuwa ya kaimin namar bakina.
Mahaifi na kkyawar mutum ne sosai duk dama wahala ya tsufar dashi amma kuma farin fata,bakin gashi da manyan dim eyes dinsa su suke yawan sani Lumshe ido a hankali ina kuma sake budewa
Cikin sauki Yake sakamin ina taunawa a tsanake.
Sai da nakai kusan sau hudu kafin nima na yanka bari guda na kai mashi bakin sa..
Ya na kan ci..sai na kirashi nace "Abbu cikin son na sa shi dariya..sai kuwa ya amsa ni da na'am noor!
Sai nace wai Meyasa ka daina kira na da asalin suna na?ko ya dena maka dadi ne..
Faffadan Murmushi kawai yayi yace,ai ko bayan raina ne, nasan kuwa akwai mutane dayawa a doron kasa da zasu kira ki da asalin sunan ki BAHIYYAH ta.
Amma kinga ni? Dole na girmama ki da sunayi da yawa..
Dariya mai sanyi kawai nayi ganin murmushin karfin halin da yake min yana kuma maganan cikin raha pretending to be ok bayan nasan ba yajin dadin.
Sai ya dafe tsakar kaina with much serious tone kamar wanda zai yimin wata muhimmin addua..Yace bahiyyah kincancaci a kira ki saiiqa..sabida ke alheri ce kuma akan hanyar alheri zaki dawwama har abada.
Kece ..noor wato haske,hasken rayuwar iyayen ta...sai yayi murmushi..
Hawayen dake hargowa a idanu na na tare cikin karfin hali nayi murmushi nace
..abbu dayan fa?
Baice min komai ba Hannun shi ya sauke kawai yana murmushin sa,sai da ya sake yankar namar zai kai min baki kafi yace
Almass?(diamond)kar ki damu dashi.
Nidai Kiyi hakuri bahiyya tah,nasan Abbu sam baya kyautawa yar sa.
"Ina kan tauna na baki na, sai nace hakuri akan me kuma abbuh na?bai amsa ni ba sai yace min nayi miki Alkwari bazan sake sakaki cikin wani hali ba.
Kisani nafi kowa son ki rayu cikin farin ciki ba kunci ba.
Tirrr da mahaifin da zai jefa yarsa cikin kunci..dan juya kansa yayi dan da wani irin remorseful feeling ya karashe kalman.
...atake sai naga yanayin sa ya fara sauyawa.
Hankali na adan tashe nace abbuh?wai akan me kake furta irin wayannan kalaman,nayi maka wani abu ne?
Yace ah,a Bahiyya...ai ko kin min laifi ma na yafe miki har abada,dada riko hanu na yayi yace min
Amma bansan ko ke zaki yafe min ba,bar ganin ina cikin zafin ciwo a jiya ina sane dake araina,kina wahala dani sosai naga har firgita kikeyi cikin dare kina kirayen sunana....ina tausaya miki sosai.
Kuma Tin A lokacin na fara jin dole na na rayu ko dan farin cikin ki bahiyyah kinyafe min...?
"Dan Shiru nayi dan banma san me zance masa ba Cikin farin cikin da bansan dashi ba na gyada kai ina goge idanuna da suka dan sauya kalar su
Yauce rana ta farko danaji abbuh ya furta min hakan kai tsaye..,har abbu ne yau ya iya mance jimamin mutuwar ammuh yake cewa zai rayu dani?wani Murna ne ya mamaye kirji na sosai wanda babu misalin shi.
******
Tun daga wannan rana har cikin makon,a gaba dayan ta a haka rayuwa ta sauya mana, duk dama abbu baya fita ko ina amma bai taba kwanciya ciwo ba tun wannan rana.
Muna cikin wannan yanayi Wata ranar Alhamis na fito nayi wanka na fes,ganin abbu ya warware yana kwance shiru sai na nemi izinin sa na bar shi a gidan shikadai,ni kuma na Fito cikin garin kallon wasa a chan yankin sarkin fulani domin ziyartar babban kawata wanda ake kira da JUNNUT..
Junnut ma marainiya ce,sai dai ta rasa uwa da uba ne baki daya,ayanzu a hannun yar uwan mahaifin ta wato ummah Surbajo take zama.
Mahaifin junnut da sister sa ummah surbajo asalin jinsin zuriar fulanin yankin ne.
Don haka junnut asalin bafulata ne maiji da kyau baiwa da kuma buri mai kyau na rayuwa.
Kawancen mu da ita ya samu nasaba ne tun daga kan iyayen mu,Don kuwa mahaifiya ta itace babban kawar mahaifiyar junnut
Ammuh tace min da ada chan damu ka shigo garin bamu san kowa ba
mahaifiyar junnut su ne jinsin fulanina farko da suka bada iyayen nawa mafaka acikin wannan yanki har aka karbe mu..
Iyayen junnut duka sun rasu tun kafin ammuh na ta bar duniya
Sam rasuwar sun baiyi mana dadi ba,gashi sun tafi sun bar dukiya mai tarin yawa
da shike su masu arzikin dabbobi da kudin hadadan kasuwanci da larabawan egytps da china ne toh bayan mutuwar su sai ya kasance yarsu da suka bari wato junnut bata cikin irin halin maraicin danake ciki.
...gashi a duk tsaunin wajen ummah surbajo ce kawai tayi karatu mai zurfi,tun asali ma ta dalilin ta iyayen mu suka yarda muke zuwa makarantar bature a chan kusa da egypt dama da yankin ethiopia har muka sami ilimin bature nida junnut yanzu munkai matakin ss1..
Wanda a yanzun Mutuwar ammu na da ciwon abbu ya dan dakatar da ni daga halarta kwana biyu banje ba.
Ummah surbajo tana matikar kula da junnut dan haka Ko meye junnut take so ana mata shi.
Rayuwar ta take yi cike da buri da son kawo mana cigaba...
Tun Muna yan Shekaru 4 shakuwar mu ya wuce yadda hankali zai iya dauka,ayanzu duk wani sirrin ta na sani haka itama kuma tasan nawa.
tsaban yadda muke da ita wani bin ko ciwon kai nakeyi zaka ga itama ta fara yinshi kuma bata samun sauki har sai na samu
Gashi kusan siffar fatar jikin mu da tsarin jikin mu daya, duk wani halayen mu na yaranta ma iri daya ne,banbacin mu shine ita tafi ni iya magana da mutane sabida awani wajen ni shiru shiru ne.
GAshi har munkai shekaru sha hudu,Da shike al'adan fulanin su muma muke bi,mutuwar ammu ne ya hana ayi min aure,ita kuma junnut burin ta na rayuwa ya hana ayi mata musamman data samu goyon baya daga antyn ta ummah surbajo.
Junnut tana matukar kaunar rayuwa,mace ce maison taga ta yi ilimin bature mai zurfi tayi kudi tana kwalliya tayi kyau,tana tuka motoci.
Above all babban burin junnut ne ta ga tayi aure nan gaba kuma ta auri Babban soja ko wani iri ne kuwa bata damu ba.
A hanyar mu na kasuwa Yau ma hirar data zo min da shi kenan.
Sai dariya muke fuskokin mu dauke da annuri Hannun mu sarkafe da juna.
Chan sai Tace min baahi?batare da na dago ba
Nace naam
"Daga Gobe Buri na zai iya cikawa amma kwata kwata bana jin farin ciki sabida nasan kwanan nan zamu rabu.
Nace ko?..wanne daga cikin burin naki ne zai raba mu junnut..
Tayi dariya tace min buri na koyan turanci.
Kinsan ko wanda anty surbajo take dan koya mana bazai ishe ni na wanku har na auro soja na ba ko?
Murmushi kawai nayi cikin nuna mata rashin fahimta nace To wanne kenan?ai Nima sai inbiki ko?
Junnut idan kika tafi kika barni bansan ya zanyi ba..
Dan Kallo na junnut tayi,dan Salon danayi maganan ya sata taji wani iri. jawo ni tayi muka koma gefe muka jingina da bayan mu.
Wani Ajiyan zuciya tayi,Tace ashe babu dadi?
...,bahiyyah kinsan me naji kuwa a lokacin da abbu yake ciwo kika daina fitowa muje karatu kwata kwata ma na daina ganin ki?
To Walhy ji nayi kamar nikadai ce a duniyan nan..
Ni Gashi ina nan Bansan wani halin kuke ciki ba gashi umma surbajo ta hanani zuwa yankin ku...wai its too far"cikin rigimammen gurgun turancin ta takarashe maganan Duk dama Damuwa ne sosai akan fuskarta.
Sai nayi Murmushi nace ai babu komai junnut,nasan bazaki barni cikin wani hali ba,ba gashi abbun ma ya warware ba
Dan karamin Nishi junnut ta sauke tace eh,Mungode ma Allah..
Amma kinsan me?nace mata a'ah..
Tace "inada yaqinin cewa bazamu taba rabuwa ba bahiyya, nidake shakuwa ce na har abada na
Amana,soyayya na rai da rai..ina matukar kaunar ki kawata.
Anan muka juyo duka muna fuskan tar juna cikin shauki mai nuna kaunar gaskiya dake tafe da kalaman zuciyar mu
Nidai Bance komai ba don tausayin ta da nake ji,junnut is kind of emotional don ko ni nasan nafita karfin xuciya da jarumta.
Cikin sanyin murya tace bahiyyya
.
Na dube ta nace naam junnut
Tace dama naji umma surbajo ne tana cewa gobe zasu zo su dauke ni..
Hannun ta na sake garan gatsau Cikin tashin hankali Nace su waye kuma junnut?wai Ina za kije ne?
Ita ma shiru tayi ta kure ni da idon don kuwa a
Ba zata naji kirji na ya buga.
Nan ta fara min bayani a tsanake don kuwa yau babu fuskan wasa a tattare da ita.
Tace"Yan uwan mama na ne daga chan wata kasar zasu zo,ummah surbajo tace awajen su zan koma zama na har abada,
bahiyyah ance suna da dukiya da duk wani abunda zaisa buri na na rayuwa ya cika kinga bama sai na tafi da gado na ba,wai dama jira suke na kai sha hudu ko sha biyar sai suzo su tafi dani..
Ruwan daya taru min a idanuna na sake cikin sanyin jiki nace dagaske kike yi junnut? Gyada min kai kawai tayi Wasu zafafan hawayen Junnut ta fashe dashi ta rungumeni, sai gashi jikin ta duk yasaki yana neman fara rawa nima Bansan sanda na kankame ta na fashe da kuka ba.
Rungume da juna Sai da mukayi mai isar mu kafin muka rarrashe juna,nan junnut tayi min alkwari cewa ko ta tafi bazata taba mancewa da rayuwar da muka gina tare ba
Don sanadiyar burirrika irin na junnut nima naji ina son nayi karatun baturen nan ko dan na taimaki abbu na, a duk dama bani da buri masu yawa irin na junnut,Nima Alkawari nayi mata cewa bazan mance ta ba,haka ma nace ni zan zamto mata mafaka na farko wajen ganin ta cimma burin ta duk rintsi duk wuya.
Tsananin amintar dake tsakanin mu yasa nake jin kamar duk wani cigaba ko karuwa da duk wani al'amarin rayuwar junnut nima nawa ne.
Gani nake kamar mani zataje tayi sabuwar rayuwar data samu achan din.
Haka dai muka waske da kyar muka goge hawayen mu cikin karfafa ma juna gwiwa har muka isa kofar filin wasan samari da yan mata da aka saba yi..
Da mamaki sai ba muga kowa ba don yamma ya fara rufawa sosai waje yana neman yin duhu
Junnut ce ta yi tambayar meya faru taga nabu kowa a fili yau,sai ake sanar da mu cewa ai yau din nan sarki modibbo ya sake SABBIN samarin AHUMAGGAH a daji don haka ne yasa kowa ma ya shiga gida da wuri..
Tabe baki kawai mukayi muka juya muka dauki hanyar komawa gidan su.
Muna tafe muna hira,nake cewa junnut ni Sam al'adan nan bata burge ni.
Sai Tayi dariya cikin raha tace akan me? don sosai muke da samari kala kala masu crushing akan kyawun halitar mu,junnut farar fata ce,sai dai ita tana da pale brown eyes ba irin nawa daya kasance grey ba!..,sosai tsarin halittar mu ya kere idanun dul wani maigani,dan tun tasowar mu samari ke buga kansu akan mu wai suna son mu.
musamman ma ni da ban cika son abun ba,muna cikin hirar ta mu sai junnut tace mon "kodai kin dade baki fito dandali ba ne gashi yau kin fito gayu basu nan ko?
....hade rai kawai nayi sai naga tayi dariya Tun kan na amsa tace kar ki damu tunda bamu samu wasa ba sai muje gidan ku na yi sallama da abbu halan gobe bazan samu zuwa ba.
Dadin jin hakan da tace yasa ni murmushi kawai
Sai Muka dora niyyar tafiya wajen abbu
Hiran burrrikan ta take min nima Ina kan jadadda mata yadda raina yaki jinin al'adan Ahumaggah akan haka kuma dariya kawai take yi min.
Wato shi AHUMAGGAH wani babban al'adace ta wasu jinsin fulani.
wanda zaka ga yaro namiji tun yana jinjiri ba za'a mishi aski ko kaciya ba sai ya kai sha biyar ko sha hudu,ko ma sha shida.
Nan sarkin gari,da matsafa da aljanun sa zasu tara wayannan samaruka a tsuma su da tsumin aljanu, sannan akai su jeji abasu jawadin tsawon kwana bakwai batare da sun fito gari ba.
To Cikin wannan kwana bakwai din ake saka ran duk wani yaranta dake kansu zasu aje shi ajejin.
Da zaran kwanaki bakwai ya cika sun fito sai ayi musu aski kaciya da aure.
Sai dai kuma mummunan abu da samarukan AHUMAGGAH shine kwana bakwai ajejin nan da sukeyi babu abunda suke ayyanawa sai rayuwa iri na dabbobi da jahilai.
Da rana zasuyi fashi ma duk wanda suka ci karo da shi.
Idan budurwace haka zasu yi layi su kwanta da ita suyi mata fyade.
Haka ma idan matar aure ce zasu zabi daya daga cikin su yayi zina da ita.
Bayan nan yankin ance Akwai masu wannan al'adan Achan kasar nigeria cikin wani kauye a garin alkaleri a bauchi state. sai dai su al'adan su basu hade shi da dokokin tsafi da aljanu ba.
a wannan jinsin fulanin kuma aljanu da bokaye kusan sune ma hukumar al'adan.
Dan kuwa akwai doka mai tsanani na cewa.
"Duk budurwan da ta ci karo da Ahumaggah har yayi mata fyade toh za'a shafe ta daga zuriar,a kuma a jefe ta da baqin cursed na aljanu.
Thy believe idan saurayi bai fita a kwanakin Ahumaggan sa ba ya sadu dakai tamkar bada jinin ka ne ma shedanun aljanu ne.
Matan aure da abun ya shafa ma jefe su akeyi ko akashe mahaifin ta a shafe ta a zuria..
******
Ahakan Har muka iso gidan mu bamu bar musun hakan da junnut din ba.
Ita kam ma abun bai dame ta sabanin nikam dana kejin da ina da iko da na sa an dena yin shi a doron kasa.
Gani nake wannan jahilci ne da rashin tsoron Allah.
No wonder sarki modibbo da bokayen sa,gaba dayan su basu shiri da iyayen mu, haka ma naga sun tsani umma surbajo sosai..har wani suna wai kadangariyar bariki suke kiranta da shi
Sabida shi sarki modibbo babban jahili ne babu arabi babu boko sai tsafi da neman arziki wajen aljanu dan bunkasa mulkin sa da kasuwancin garin sa.
amma iyayen mu sun nemi addini da ilimin bature dai dai misali a wajen larabawan egypts da kuma yan china dake shigowa kasuwanci ta boader somalia.
Dan haka ne ma rayuwa ta nida junnut ba dai dai yake dana kowa ba..
Wayewar mu basira da ilimin mu a fili yake nuna kansa.
Tun daga bakin kofa muka doka tagwayen sallama
Muka shigo
Amma sai Shiru kakeji tsakar gidan gaba daya babu bakowa,sai nace junnut ki shiga daki ki same abbu ni zan sa mana ruwan alwala
Tace min toh ta saka kai
Niyyata su gaisa idan tayi sallah
Nake son na rakata bakin hanya ta koma gida
Ina sane da cewa Umma surbajo bata son ta cika dadewa a waje musanman ma da naga har waje ya yi duhu yanzu magrib kuma ya shigo.
Shigar junnut dakin keda wuya na kafa kai Ina famar hakar ruwa a tulun bakin rijiya..
Ko ajiyan numfashi ban yi ba wani irin firgitaccen karar ta ya dake kunne na wanda ya sani sake butar danake shirin kai hannu na na shigo cikin dakin mun aguje.
Junnut lpya?
Bata amsa ni ba
A durkufe agaban abbu na same ta
'Abbu..abbuuu....
Abbbuhhhh..cikin firgicewa ta riko rigar shi tana fada kamar zata cire ranta da kuka,sai yanzu na na lura aman jini yake,duk yayi malala a a hannun ta tana famar jijjgashi
Nima durkushewar nayi gaban ta muka shiga jijjgashi muna tallafoshi ba shakka ciwon zuciyar sa ne ya tashi gadan gadan.
Kukan rudani duka muka farayi musamman ma junnut da shike tafi ni sanyin zuciya.
da naga hakan bazai ficce mu ba,sake mata shi nayi daga bisani na mike tsaye na fito tsakar gidan neman maganin shi daya hada yake sha a kwana biyun nan.
Kwaryan shan na rarumo Sai dai kashhsssss maganin dake ciki bai kai ko rabin cokali ba.
Haka ma Duk iya bin cike munyi nida junnut amma ba muga ragowar sa ba.
Haka muka yi cirko cirko akansa muna neman mafita,ga shi dare ya rufa ga shi Hankalin mu a matukar tashe yake ganin halin da abbu yake ciki dan aduk sanda yayi tari gudan jini ke fashewa yana kuma fetsowa..
Karshen ta barin san nayi da junnut adaki tana ta kuka sai nayi kokari na sulale a zuciye na fito na bar gidan na kama hanyar jeji.
Tafiya kawai nake buri na naje cikin dajin ko zan samu na kalato magani abbuna ya sha ya rayu.
Karewar Maghriba ya shiga sosai donko gaba na bana gani sosai danake tafiyar
But I was so dertemined,ko ajiki na zuciya ta arufe take kuma duk wata alaman tsoro na kau dashi.
Sai dai Ko rabin jejin ban tsaga ba naji takun mutum abaya na ina kuwa daga ido naga aminiyata junnut faca faca alaman biyo ni tayi.
Abun ya bani mamaki,tambayar kaima nake anya junnut tasan hatsarin dake cikin wannan lokaci kuwa?.. A zuciye Nace junnut?baki da hankali ne zaki shigo jejin nan cikin dare?Idan wani abu ya same ki fa me zaki ce..
A take Tace min oho
Share ta nayi na taho zan maidata gida ta fauce hannun ta
Kallo na take yi
Don Tsaban zuciyar ta ya karaya Cikin wani birkitaccen kuka Ta tsare numfashi na da cewa wai ena ruwan ki dan nazo,wato so kike na barshi ya mutu ko bahiyya?
Abbu mahaifina na ne nima kuma
Bazan zauna ina kallon shi cikin wannan azaba ba..
Kuma Dole ne na zo na taimake ki mune masa magani..hada ranta tayi ta kame
Bance komai ba,dan Hawaye ne suka sauko minbina sharewa dana ganta ahakan sai naji na damu da safetyn ta sosai
I wish dat bata zo gidan mu yau din ba ma,a haka ma ban bari ba duk iya musu munyi akan ta koma gida kan abbu Amma haka fir junuut taki.
A haka na hakura mukaje cikin jeji neman maganin tare.
Bamu samu irin ganyen da wuri ba dan munkai kusan rabin awa muna dubawa..
Sai da mukayi nisa bamu sani ba,Finally junnut ce ta gano shi ta nuna min,dan kwazazzabi ne yabi wajen sai na mika hannu ina tsinkawa tana tara min a fallen rigar ta
"Mun ko debo isasshen a Kai hannu na na karshe sai naji an chapke ni,a tsorace na shiga fixgewa sai dai kuma lyaki sakowa..
Wani kara nasake
Cikin radadin murdamin hannun da akayi
Kafin Junnut tayo kaina,nadaga ido sai charaf mukayi ido hudu da saurayi
AHUMAGGAH..
Wani uban Ihu na tsala nace junnut ki gudu ga Ahumaggah..cikin rudani da rawan murya tace Ahumaggah?
Wani ihun na sake tsalawa..ko da junnut zata firgita ta gudu amma ina sai naga batayi hakan ba
Kokawar jawo ni
Ma Ta shigayi cikin dauriya dukan mu muna ihun neman ceto
Ahaka Har ta ci nasaran kwace ni a hannun sa muka fado kasa tare A hargitse muka mike ai tun kafin Ahumaggan yace zai zago na tura junnut kan hanya nikuma na kwaso maganin da muka debo a hannu na,..wani uban Gudu muke cikin jeji da dukan karfin da Allah ya bamu.
Gudu yaki ci yaki karewa dan Bamu san munyi nisan kiwo ba sai da hakan ya faru damu tsaga ciyawa kawai mukeyi babu iyaka...
Ayayin da shima Ahumaggahn ya haukace yana biye da mu aguje da dukan karfin sa ko kiran yan uwnsa baiyi ba....
Bana so mu rabu da junnut dan haka muka rike hannu muna falfalawa back to back..
Gashi Idon mu duk ya rufe da tsoro,sao A Chan bakin wani tsaunin itace daya fado kasa junnut bata lura ba tayi tuntube ta fadi gashi ta gaji sosai sai haki take..nayi kokarin janta amma wani Ihu tayi cikin radadin zafi wanda ya tabbatar min da cewa taji mumunnan ciwo a kafarta
A tsorace na zube gaban ta nayi kokarin dagata don jin sautin tahowar Ahummagan ya gama jefamu cikin rudani.
Agurguce dai na tallafo ta Da kyar na dago muka tsaya tana dingishi kafarta na dama har ya farke ya na zubar jini sosai.
Munajin sautin iska alaman Ahumaggan na gaf da mu anan tsananin tsoro ya sa muka sake juna
Ita Junnut tayi gabas ni kuma nayi arewa..
Gudu kawai muke yi har na samu na tsira sai na buya bayan bishiyar kuka ina ta haki ina neman dai daita hankali na.
Anan Nakai wasu mintuna goma banga wullowar Ahumaggan ba haka ma banga junnut ba
Atake naji Kirji na ya buga,kaina yayi mummunan sara,gashi ina so na kwalla ma junnut kira amma ina tsoron dada jefa mu cikin fitina.
Nasan tabbas sauran Ahumaggan ma suna nan,kuma muddin suka ji muryan mace zasu fito dukan su kuma nasan bazamu taba tsira ba.
Cikin jarumta na fito a sadade ina neman junnut ajejin.
Tafiya nake ina duban gaba da baya,har na naci kusan rabin awa banganta ba,sai da nakai chan ciki wajen gonar masarar sarki modibbo kafin naji dafff an dafa ni.
A hargitse na waiwayo dan tsoro sai kuwa muka hade ido da junnut tana tsaye kamar kungi hawaye taff kan fuskan ta.
Wani irin daskararren Kallo muka tsaya yiwa juna cikin mu babu wanda ya iya furta komai
Gaba daya Ji nayi Jiki na ya dau sanyi dan Yanayin da take kallo na sam bangane mashi ba... idanun ta sunyi jajir kuma ta riko rigarta ta cukuikuyo shi da dukan hannayen ta tana nuna alaman tsana ma yanayin da take ciki.
Innalihhihi wa inna ilahi rajiun Murya na tsananin na rawa nace"
Junnuut...jun..
Ai Bata bari na karasa ba tasake min Kukan ta mai dauke da tsumayi wanda ya dakatar da ni.
Atake naji wasu mahaukatan hawayen sun bulbulo min Cikin firgici Nace meye ne?
Nan ta riko ni tana mai dada fashewa da kuka Tana boye fuskanta ajiki na,kai kawai take girgizawa
Anan Zuciya ta tuni ta bani cewa wani abu mummuna ya faru da ita dan haka nima nabu jira na fashe da azabbaben kuka mai fitar da sautin ciwon daya fi nata ciwon zafi
Wani Kankkame juna mukayi cikin dajin muna kuka sosai da kuma dukan zuciyar mu,..batare da ta furta min ba
Na gane cewa Ahumaggan nan ya cimma burin sa ne akan budurcin junnut.
Da kyar muka rarrashe kanmu
Mukayi zaman mu cikin tsakiyar gonan bamu damu da komai ba muna tsananin jimami.
Cikin disashiyar sautin kuka Nace shikenan yau na shiga uku junnut,..maganganu nake yi cikin rudani da Har zan fara bada kaina laifin jawo ta cikin wannan matsala
Sai naji tace"kar kice haka bahiyya,ai duk abunda zanyi akan Abbu tamkar nayi ma mahaifina na ne..
Ni Damuwata yanzu ummah surbajo da cikar buri na!
Kinsan yadda nake so nayi rayuwata ko?wallhy Ina matukar son na Zama mace a duniyan nan bahiyya bazan iya jure duk wani abunda zai ranani da hakan ba!
Yau idan akaji abunda ya same ni nasan ko ummah surbajo bazata kula ni ba bare adanka ni wajen dangin mahaifiya ta.
Sai bata sake cewa komi ba dan Kuka mai ban tausayi junnut take yi cikin zafin rai da rikicewa
Gashi ba karamin zafi jikin ta yake mata ba,nikaina kukan nake yi kuma nasan dauriya junnut take yi ayayin da take min maganan ayanzu.
Damuwa sai ta mamaye zuciya ta,don Bayan tinanin hukunci da za'ayi ma junnut awajen sarki
Babban fargaba shine burin ta na rayuwa da take sa shi a ran zai fara daga gobe.
Sai naji kawai banyi mata adalci
musanman da naji cikin kukan nata kamar tafi damuwa da Cewa za'a shafe ta a zuria ayi cursing dinta inda ko umma surbajo bazata so ta hada hanya da ita ba bare taje birni ta cimma burin tan.
Dan a al'adan yace muddin aka shafe ka babu wanda zai sake so ya hada zuria dakai,don gani za'ayi kamar kaidin ba alheri bane kuma darajar ka ta gushe kenan har abada
Tausayin ta sai ya kamani sosai
Junnut tayi min hallaci sosai,yau ta dauki qaddarar biyo ni neman magani ma mahaifi na rayuwar ta kuma ya shiga matsalan da bansan mafitar sa ba.
Tunani nakeyi sosai Dan haka kawai nake jin cewa dole nima nayi mata hallacin da zai dawo mata da martaban rayuwar ta cikin gaggawa.
Nace junnut idan zaki iya kawai muje gida yanzu mu samu abbu mu fada masa nasan shi zai nema mana mafita ko?.
Junnut Gyada kanta kawai tayi ta kwantar da kanta akan kafada ta cikin jimami dan kwata kwata rasa budurcin nata bai wani dara ta chan chan kamar tunanin cikar burin ta ba sai tace.
Bahiyyah ki rufa min asiri mana kinji?...
Sai na dan langwafo na kalle ta,dan ban fahimce ta ba
...mikewa tayi ta zauna tare da riko hannu na..
Tace Kinsan a duniya bani da kamar ki ko
Bahiyya!Toh dan Allah Ki rufa min asiri mu binne maganan nan tsakani na dake bana so kowa yaji.
Cikin mamaki na ware ido ,a marairaice tace
Kinga tunda naji ciwo jini na bina ai ummah surbajo bazata gane abunda nake ciki ba har sai na bar garin nan gobe ko?.toj Dan Allah bahiyya kimin wannan Alfarman,
hawaye na zubo mata sai ta marairaice min sosai gwanin tausayi
Nikuwa Cike da zakuwa Nace zan yi miki komai a duniyan nan junnut
..ina dai baki so kowa yasani ne?
Amma toh baki tsoro aljanu su tona mana asiri..
Ahumaggan nan zai fada ma aljanun su cewa yayi fyade ma budurwa,a gidan sarki kuma
zasu jira mu har kwana uku idan bamu kai kanmu ba kinsan zaki iya mutuwa ko?
Da sauri Tace eh..nasani
Anma ai basu sanin ko wacece akayi ma fyaden ba har sai takai kanta ko?
Ba tare da wani shakka ba Nace eh
Wani ajiyan ziciya Junnut ta sauke cikin sanyin tace "bahiyyah,Shiyasa nake so ki taimakeni...sai kuma tayi shiru alaman kalman ya mata nauyi abaki
Nace inajin ki junnut.. Nan ma sai ta kafe ni da ido tayi shiru abun ta
Da kyar sanda na dinga takura ta da cewa dare na dada yi mana ajejin,gashi tashin hankali ya gama mamaye zuciyar mu kafin ta shirya furta min.
Anan junnut ta nemi alfarma ta tana cewa
"Domin cikar burin rayuwa na
nake rokon ki da ki sadaukar min da darajar ki wajen sarki
Cikin kukan da bansan dashi ba Ta dada ruko hannu na tace
"Ina nufin kice masa kece akayi miki fyaden bani ba..
Zu je tare amma ke zaki dauki laifin
Inyaso koda an wanzar da hukunci akanki sai mu hada hannu mu dauko abbu mu kaishi chan inda ummah surbajo zata koma kasar nigeria sai ayi jinyar sa da dukiyata.
Cike da mamaki Nace junnut?kinsan me kike cewa kuwa
Tsaye ta mike tana dingishi,dan tun kafin na kawo korafi na tace toh nidai wallahy zan kashe kaina,daga yau muyi bankwanan a duniya bahiyya...kinsani
Idan bazan cika buri na ba gwara na mutu.
Nima tashi nayi a rikice nakai mata dan karamin mari a fuska,a zuciye nace zaki kashe kanki baki da hankali ne...
Cikin kukan bakim ciki ta sulale ta tsuguna gaba na tana mai tana kafafu na a kaskance tace bahiyya dan Allah ki taimake ni,wallhy nayi miki Alkawari zan dawo miki bazan rabu dake ba
...zamu yi rayuwar mu mai tsafta ni dake har abada..Alkawari ne.
Wani irin Tausayin ta ne naji ya shige ni sosai domin Wani Kuka mai shiga rai takeyi ayayin da nima na fashe da kukan na tsuguna na rungumo ta jiki na muka dunkule munayo tare..
Cikin tsananin son naga na yaye mata damuwar ta nace mata na Amince zan dauki alhakin yin mata haka..
Sai dai sharadi na shine wannan maganan ya kasance wata babban SIRRI l mai girma a tsakanin mu wanda ko abbu bana son yasan dashi.
Junnut ta dada rungume ni tana kuka tana min godiya
Tare da min Alkwarin duk dukiyar ta na wajen ummah surbajo zai dawo na jinyar abbu na.
Haka na dauka wannan kayan alkwarin makaina
Ni sam Bandamu da wani curses din da za'ayi min gobe agidan sarki ba.
Sannan a tunanina na yaranta na bana kawo cewa akwai abunda zai tsare ni wajen nema mahaifina gamsashen lapya,wani tsafi da aljanu duk gani nake sun yi kadan su kara da ikon Allah..
Iya kaci ne ace inhar da ummah surbajo zamu zauna a inda zata koma gobe a birni to zan iya rabuwa da abbu na. Toh Wannan shine kadai babban abun daya yake damu na yanzu..
Ta ya zan fara ma abbu bayanin haka?gashi Bantaba boye mishi komai ba sai yau da nake shirin zan boye mishi sirri na da kawata junnut..
Shin ko akwai abun da ya fi dadi a duniya kamar kasan kana da iyayen ka a raye koda kuwa baku tare?.
Follow @surayyahms
VOTES
VOTES
LET C HOW UR COMENTS WILL CALL ME BACL
_toh Fans ina jiran amsa🤣🤚🏻_
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top