3

Page 3

Wannan shine view of royal rustic  home

Royalty meet elegance

Qarar da wooden door din ya saki ayayin da ake budewa shi ya daga ni a dan baccin bayan sallajn fajr dana keyi.

'begham sahiba ce ta shigo Wato kyakyawar matar nan da Aka danka ni hannun ta jiya da daddare.

"..Tun Bata karasa sake handle din door din ba ta kafe ni da ido sai dai batace uffan ba anan nima Sai na dan dago na kalle ta Wani haske da taushin murmushi nagani akan cikakken dattijuwar fuskan ta daya sa naji duk baccin dake idanuna sun washe.

Gyaran murya tayi tare da cewa sallam

Na ansa ta a nitse na mike na karbi kayan dake hannun ta cikin ladabi na gaishe ta da "ina kwana" sai ta amsa min tare da miko min package din dake hannun nata
Tace min
Open!.babu bata lokaci Sai na bude.

Wasu jajayen doguyen Riga ne da dan kwalin su nagani ba ayi musu adon komai ba dana warware sai naga size dinsu dai dai kamar gwada ni akayi.

Begham Tace baccin ya ishe ki kuwa bahiyya? Nayi saurin gyada mata kai

to ina waje Maza ki shirya da kayan hannun ki sai ki taho ki same ni.

Nace toh cikin mikakkiyar yanayi na tashi tsaye da kayan a hannu na kamar ba wacce ta taso daga baccin gajiyan ba.

nan na shiga toilet na wanke idanuna na fito na shirya cikin kayan Data zo Min da shin din tsaf na fito na biyo bayan ta muka fara tafiya.

Akan Wata shimfidadiyar titi muke takawa

cikin wata katotuwar black and golden gate wanda bazan iya misalta tsawon shi Ba muka dosa.

Ba shakka shi nagani ajiyan da muka shigo cikin dare sai dai ayanzun nafi ganin girman sa,..tunda muka hau tafiyar nake raba ido nidai sai kalle kalle na keyi begham tana a gaba na tafiyar ta Cikin nitsuwa Wanda Daga ganin ta kasan ita din babban Mace ce

..,duk dama a jiyan cikin dare muka shigo wani Mamaki ne ya cika ni ganin yawan mutanen dake haraban gidan ana ta kaikawo kowa cikin samfurin kayar aikin sa.

Tun Daga tsarin kofar wannan katoton golden gate zaka iya cewa gidan wani babban mashahurin mayakin soja ne tsaban yalwataccen security armed forces dake kare gidan ta kowani fuska.

masu aikin tsaron gidan suna da yawa Wanda akallah uniform din jikin su ne ya banbance su da sauran tarin ma'aikatan dake shawagi wasu sunsa clayed brown uniforms wasu day wears,kowa na hidiman gaban sa.

Ina dauke idanu Na a kansu na ci karo da wasu irin dirarrun storey buildings guda biyu masu kama da ancient building of rustic architecture,to be honest,gidan babu maraban shi da gidan sarauta its huge, 8000 to 10000 times bigger than gidan dana fito.
...kuma kowane storey buiding yana da personal golden door dinsa wanda suka kere tsayin na farko dana fara gani yanzu

Da aka bude mana gate din farko wata haddadiyar parking lot na fara gani,acikin ta babu mota kwara daya da za'a baka wanda bazai fidda ka talauci na har abada ba.

Bayan manyan driveways dake wajen, a Kusa da shi akwai katoton horse stalls wanda zai iya daukan dokuna dari zuwa dari biyu wajen is kind of grassy its like masu lura dasu ne kawai ke shawagi anan wajen.

View din ginin gidan gaba dayan ta is just like that of a royal kingdom amma Kuma ba haka bane kai tsaye,sai ina ga kamar tsantsar tarin dukiya ce kawai take ambaliya bana wani sarauta ko Mulki ba .

anan Shashin ma gani nayi kowani ma'aikaci na yawo cikin specific tsarin uniform din aikin sa

Wata tsaftatacciyar iskan dana shaqo Ta ramin hanci na yasa ni noticing reference to nature dake zagaye da dogon Shararren streets din daya bada Undulating contours da layout din gidan cikakken tsari,its a Cool decorative greeny vegatation of palm trees sun jeru sunyi liff kamar da hannu aka zana su.

Gefe da wannan waje akwai jerarrun pebles back splashes wanda suka Dada fallasa tsafta da nitsuwa Da kuma kwanciyar hankali dake muhallin wajen

a karshe dai
Wasu manyan multi purpose wood /metal furnitures zaka gani inda aka sarrafa su a wani open space kamar lambun shakatawa

AHakan ma ba a bar cikin wajen haka ba sai da aka saka royal ottoman walls da relaxing benches hala ko dan Organisational functions.

Gidan dai duniya ce

Ido na ya gaji ne dan Bazan iya daukar komai da komai ba, dana bayyana muku tsarin,basket ball and handball court,swimming pools,arch statues,water splashes,da luxurios garages and gym din dana gani.

Domin kuwa iya kallo nayi,amma Ni kaina bazan iya Fadan komai tsala tsala ba har muka shiga wata hall way daya miko mu wata tsaleliyar royal palour,kai wannan ya wuce nace dashi palor bari akira shi da royal hall kawai

Wata mata ce ta shigo ta same mu nan suka gaisa, begham tace mune baqin albarkarciya jahan Aarah Allah ya sa bamu iso mata cikin takurawa ba"...

Matar tayi mana murmushi da gefen idonta ta kalle ni sannan Tace"barkan ku da zuwa begham ai dama ku take jira amma kujira ni anan ina zuwa.. sai ta koma ciki Babu bata lokaci..

Nikam cigaba da kallon duniya nayi,..duk kauyanci na yau saida ya fallasa kansa

design din cikin gidan ya wuce mahadar Da za'ace dashi luxury Meets royal elegance.

Domin kuwa an hado tarin lush materials in bold colours like turquoise and ornate patterns

chairs and sofas anyi sune da wani irin design din silk and velvet.

Sannan an hada tsadaddun setin gadgets and kuma daidaita marching textures kamar su velvet couches din,metal light fixtures,wood tablets and glass decors.

A takaice dai duka Furnitures Dake Ilahirin gidan an kera su ne da elm, marble,hickory and chery,sannan dukan handles din furnitures din su anyi shi ne da Tsadaddun brass knobs wanda ya hada da hannun drawers,cabinets da tuff boards ga kuma airmores.

A gefe dani kadan akayi ma zaunin wasu shegun hand crafted brass and copper lanterns dake fidda wasu irin launin haske daya dada kara ma wajen touch of royal sophiscation and warm elegance.

Ban san Sanda na karkato wuya na leka Sauran hallways din ba its like A saman kowani hall Dake gidan akwai crystal chandellier Mai mugun dauke ido Then finally The wall scounces.

Shigowar wannan matar ya dakatar dani Daga duban wani Iri ne,as expected da murmushi kan fuskan ta tace mana ki shigo bismillalh sannan tayi gaba Muka fara binta abaya.

Tun Kafin muyi nisa begahm ta dan dube ni, wani Kallon gyara kimtsi tayi min wanda ya jefa ni cikin nemowa kaina nitsuwa Da kama kai.

dan haka Ne ma ban kara kallon sunnah ma komai ba har muka iske wata amazing royal palour Bazan iya Fadan me ya kumsa ba Tsabar haduwan shi.

Tuni matar da ta kawo mu ciki tayi gefe ta tsaya

Ni kuwa alokacin Wata kyakkwiyar mata ce ta dauke min ido, i bet she is in her early fifties azaune agaban full size screen tv take xaune tana amsa waya tana dariyar ta mai cike da nuna kasaita da aji.

Kallo daya zaka mata kace sarauniya ce
domin kuwa jikin ta sanye yake da wani tsadadden grey gown mai dauke da ratsin black diamond stones kanta tamke da Nadin turban Shi kuma baki.

Haka muka jira ta gama amsa wayar ta,data juyo ta kalle ni wani Murmushin dana gani shimfide a angelic face dinta yasani naji ciki na yayi kugi har gabana yana dif dif shi kadai

A duniya Bayan mahaifiya ta wannan mata to me She Is the most beautiful creature anyone can think of.

Ido kawai tayi ma dayan matan ta fice ta bar mu da ita MU ukU.

Sai naga begahm sahiba ta rusuna da sauri cikin girmamawa tana cewa,

Allah ya ja zamanin ki jahaniyah mai Tarin albarka ga nan yarinyar da aka bani na kawo ta wajen ki.
A Nan ma murmushi kawai matar tayi
mikewa tsaye tayi cikin Salon kwarjini da kasaita ta iso gareni.

Wani nitsatsen Kallo ta bini dashi A sanda take faman daidaita Kasaitacciyar tsayuwar ta agaba na

Karkwawa hannu na ya fara yi dakanshi duk Tsoro da fargaban inuwan ta ya cika min mara tam da fitsari sai Zaro ido waje nake ina sadda kai.

Da shike batace mjn uffan ba Wajen wani shiru ya dauka kamar an kashe maraya,nidai ko da ba'a gaya min ba a irin wannan kallo Nata Nagane Cewa ta takarance ni tsaf daga sama har kasa Babu ragi

..sai da taja sight relieve kafin tace min "Ure most welcome"..ta na fada Da sauri na dago Na dan kalle ta dan kuwa sautin muryan ta mai mugun tsada ce sai dai barin baki ya hana ni amsata

Tace Begham ki kira min adama kuzo tare In 5minutes.

Begham Tace toh angama ranki shi dade sai tayi waje ta barmu Atake.

Matar Bata sake kallo na ba ta Juya ta koma kusa da tsakiyar hall din,Sai da ta dan bani Rata tukun ta juyo tace yarinya Meye sunan ki?

Ban bata lokaci ba na dago Cike da dauriya Nace"sunana
...bah...i..yyah
Bahiyyah...

Sai Tayi Shiru Bata sake cemin uffan ba But She was looking at me closely like a true royal queen of dynasty

yadda ta nade hannayen ta da su kaji jan qunshi da kwalagwalai yasa naji tamkar ina gaban wata sarauniyar matan duniya ne Gaba daya

Ita kuwa kallo na takeyi har Sai da ta lura na natsu kafin ta sake sauke ajiyan nunfashi

Cikin nitsuwa da sanyin kalami ta fara min magana.

Tace sunana jahan Aarah nice matar wanda kika taimaka a wancan daren da baiyi da manufar alheri a cikin rayuwar mu,miji na Ya fada min sunan ki bahiyyah But na sake tambayar ki ne sabida waka daga bakin Maishi yafi dadi...

Anan Wani nitsuwa maganan nata ya sakamin dan cikin kasaitaccen yanayi ta karashe shi,sai Nayi shiru na bata full attention Sai ta cigaba Da cewa

Mijina ya fadamin komai Game dake,dan haka Zaki zauna anan gidan tare dani kafin nan ya kammala sauran jinyar shi ya dawo.

Fatan kin fahimce ni?

Da sauri na gyada kai na tari numfashin fargaba dake neman shake min wuya na da beam smiles

Shigowar su begham kenan jahan Aarah,tayi nuni da Matar da ta shigo Damu mai suna adama Wanda kowa A gidan yake kiran da Sunah ammuh,Anan Jahan tace Mim wannan zata nuna miki duk abunda ya kamata ki sani.

Wani kawataccen box naga ta sa adaman ta dauko mata,ba bata lokaci naga ta miko shi ma begham
Ita kuma ta rusuna tana godiya

...a haka har tayi mana sallama ta bar gidan mu uku aka barmu a faloun

Inda Nan din gidan sarauta ne Da zan iya Cewa Adama ce jakadiyar jahan Aarah but no.

data dan dube ni sai Tace Ranki shi dade fatan zamu iya tafiya Ko akwai wani bayani Ne?

Kawai sai naga matar ta min hannu Alaman na matso,murmushin data keyi yasa na dada tahowa a sanyaye na tsaya daf da ita.

She knew im nervous and soo scared,hannu na ta fara kamawa sai tace godiya ta tabbata ga yarinya mai jin kai irin ki.

Karki razana da mu babu abunda zamu miki,kwance tashi ai baya hana ruwan rijiya sabawa da guga ko!just relax
..u will get use to this place Its ur home now.

A hankali na dago na dube ta naga murmushi ma takeyi still,Kirjina ne ya shiga bugawa Amma dana samu na kauce ma hasken idanun ta da kyar na iya furta mata nagode.

Tace zaki iya aiki agidan nan?

Nace eh na kuma na gyada kai a ladabce

Tace toh adama gata nan Zan gaya miki Sauran details din aikin ta anjima.
I think she will fit in best ma aikin dana zabar mata.

Hannun matar Naji A kafadata Ta dafa ni sai na dago kai Amma Nakasa hade ido da ita,But i can feel it while smiling at me tace Daga yanzu Zaki zama mai kula Min da dana shima yana nan agidan nan

..Yadda tayi maganan nasan This statement is neva a request Bare na samu filin MUhawwara da zuciya Ta akan ina so ko bana so

Nidai Wani irin faduwar gaba naji tun kafin ma na ce Komai,naji ammuh Adama ta yi korafi tanacewa amma ranki shi dade,anya bata kasa a matsayin personal maid din khaldun ba?

Dan karamin miskilallan murmushi matar tayi tace mata a'ah,
I think shes 15 ko?Ta dube ni Sama da kasa in a quick body inspection

nikuwa nayi saurin sauke kai na kasa Nayi Shiru.

Sai Tace zata iya mana,beside a matsayin alfarman da tayi mana ta wuce wanda zan bata aikin kula da dawainiyar dana.

Adama

Da saurii adama tadan rusuna kai tace yes jahan

Just Do one thing,teach her everything and everywhere.

Idan kuka kammala nida kaina zan gaya mata dokokin aikin ta

Adama ta dube ni tace kinji ko?

Cikin barin baki mai dada bayyana innocent heart dina na amsa da eh naji.
Nagode

Nan Jahan din tayi murmushi ta sallame mu hannu na adama ta kama muka nufi wani site.

Nidai bin ta kawai nake yi amma
Bansan cewa jahan din tafada ma adama akan Gwajin hali ta daura ni Shiyasa tabani wannan aikin ba.

Chan da yamma Bayan waje yayi liff ana ta shirin himman kirayen sallahr magriba

Matar ce a kwance akan wata sculpted black tuned soffa a wani purple tinted mini palour Har ta sauya Kayanta zuwa royal orange arabian jallabiya.

waje yayi shiru sosai don kuwa nan waje ne da ta saba amsa wayar mijin ta wato retired,navy admiral 5 stared army general,a reknwn political beurocrat,and the 39th chief security adviser to the united states legis.

Rtr adm gen alhj hamood mufaddal clive sunan shi..

Shi mutum ne karfaffa mai tsayi da jiki curently in his late 70s.

Duk da wayannan matsayin na shi
He Is still a son from an ancient royal palace of iran anan ma wata sarauniyace ce ta haife shi.

Da tarihin Zuria yabi zuria a nan asalin tarihin sa ya bayyana cewa ajinsin dawlat khatun ya fito karkashin jinin wasu bi-Queens of the persian empire paticularly jinin sarauniya badi'atul jamal waccce ta fara kafa tarihi nadaban a labarin sarki sayful maluku tun a lokacin kasar iran yana amsa sunan sa na land of aryans a duniya.

A yanzu inda ta kwanta babu abunda take Tunani kamar maganan da su kayi da mijin ta akaina tun kafin nazo,shiru tayi cikin wani nazarin daya sake jefa ta cikin jimamin abunda ya faru da shi a cikin kwanakin nan yare da lunshe idanun ta ta sauke wani sassayan ajiyan zuciya.

Asalin sunan ta Aarah,amma ana kiran ta da Jahan Aarah itace matar sa na farko,duk dama ita ba daga dangin shi bane amma Soyayya sosai su kayi kafin sukayi aure

...rtr hamood ya kasance Shine hasken zuciyan ta cikar burin ranta,farin cikin ta da duk wani sadaukar wan ta,sai dai inta Tuno cewa badon yarinyar nan bahiyya ba da babu shi a duniyan yau
Sai taji kamar ta sa a kira mata bahiyan tayi declaring dinta yar cikin ta kawai dan nuna godiyan su,.

Da dai Sun tsara hakan tun a farkon jin labarin ta,sun fahimci cewa ita abun a tausayawa ne, yarinya karama Marar uwa da uba ne a duniyan nan.

Sai dai she can't Do That just yet,bazasu iya aikata haka agagauce ba domin kuwa su manyan mutane ne wanda rayuwar su ke tafiya da tsari da dokoki wanda dole ne su bishi ko dan samun tabbatcen tsira daga makiyan su.

Bayan mutuwan iyaye,ayanzu abu mafi daraja arayuwan jahan Aara shine Mjin ta
Daga shi kuma sai yayan ta Guda biyu mace da namiji

Gashi Haka kawai Bahiyyar ta shiga ranta,har ta Kuma furta hakan ma gen hamood M tun ma bata ganta ba

Toh Lokacin ne suka hadu sukayi nazarin rayuwa Mai zurfi akaina harda hadun bakin yar uwan sa begahm sahiba

acewar su tunda an tabbata bani da kowa a duniya toh Kafin su maida ni official adopted child zan zauna a matsayin mai aiki da hidama da dansu

Wanda Duk cikin zuria suke ganin kamar babu irinsa a wajen wahalar zama,shi mutum ne mai murdadden yanayi,muddin har na iya zama dashi to babu tantama zan iya zama da kowa.

Kuma Ahakan suke saran sanin wacece ni kuma da Wacce irin zuciya nazo Musu dashi.

Cikin su jahan tafi kowa Fatan na Kasance ta gari Inda zatayi saurin yanta ni ta dawo da ni tamkar yar cikin ta domin ita mace ce mai tsananin tausayin nakasa da ita Ga son maida Ladan alheri akan lokaci..tunda ta ganni yau take faman tausayi na aranta.

She is already thinking of so many ways to repay my kindness.

Ni kuwa tun Ranar da muka fita a shashin jahan Aarahn ba a sake bada izinin dawowa dani ba

Achan wani sashi muke Jibge,tare da sauran dattijan mata Su hudu wanda suka kasance manyan masu lura da ma'aikatan gidan kowa dana shi fannin Daya kware.

Ammuh adama itace general Chief maid Na gidan,Sai mami fatima tana kula da harkokin siyayya Da harkokin Kowani irin store Inde nagidan ne, Mami hafsa Itace mai Lura da duk wani shige da ficen kowa dan haka tana da Masifa Sosai.
...Mami jamila Kuma Itace kunne da idon gidan babu karya Wajen Aikin ta na gano munafukai da warware matsala Tsakanin Mutane.

Sam basu da matsala domin kuwa akwai wadatacciyar arzikin da komin Salalan Tsiyar mutum dole zaiji shi ajikin sa.

Yanayin Tsarin dokan da aka shimfide ake bi da ma'aikatan gidan Shi yake nuna sakewar su da dattako da girmamawan su wajen Aiwatar da dutyn su.

Kwanaki goma sha biyu kacal Ammuh adama ta dauka tana saita ni

Farko sai da ta zagaya dani kowani sashi lungu Da sako na gidan kafin muka dawo muka fara daga kan koyar salon magana
girmama Nagaba
kwajin tsafta,iya tafiya,Kayan Amfani da girki,hatta yadda ake serving da yanayin gyaran gadon su duk ta nuna min

hazaka da kaifin basirah ta yasa yanzu zaka sha mamakin yadda adama ta sake dani,dan sau daya zata fadi abu na dauka,daga ta koyar dani tofa za taga nayi dai dai koma fiye Da hakan, kuma bana da saurin mantuwa.

Ammuh Dai ta dawo min kamar wata uwar daki don kuwa tun zuwa na ba wanda ya taba daure min fuskan sa Agidan..

Yanzi har na Saba a gidan Karfe 7.00 Na kowani rana ake bude gate Din waje gaba dayan ta sannan babu mai fita agidan har sai karfe 9.

Anan inda nake Kwana kuma 6.oopm na safiya ake buga musu workers alarm Daga jikin wata katuwar agogo dake Chan sama tsakiyar gidan dan haka kowa lokacin yake tashi ya shiga hidiman aikin sa

Yau Ina zaune akan sallaya Ammu adama ta tada ni nayi wanka na fito na saka wata riga da zani ruwan madara Da simple flat shoe na biyo ta.

Ni dai bakowa bace amma a yadda naga suke min nasan indai karamci ne to ana yimin.

Site din jahan Aarah muka nufa da shike babu hayaniya har muka shiga banga kowa ba Sai ita a Zaune Akan Beige rug Wanda yaji Floral patterns

Rusunawar Gaisuwa ammu tayi Bayan ammun ta mike Nima tuni sai Na bi sawon ta na rusuna."Nace Allah ya taimake ki ina kwana?
Jahan tace lpya bahiyyah ko!.
Nace eh nice...sai dai bandago kai na ba

Yadda na gaishe Da Jahan din cikin ladabi da girmawa ya matukar burge Ammuh adaman barin Ma aje kan jahan Din dake sake min faffadan murmushin ta mai Saurin Tausasa yanayi

Daga ganin kalar biyayya ta,She's now very sure that zan iya aikin da suka daura ni akai Duk dama tasan Task ne mai matikar wuya.

Gashi dama ban san cewa begham sahiba kafin ta tafi ranar Har ta fada mata na iya girki kala kala ba.

Im just a teenager but with lots of focus and energy ni bana son saibi bare sanyin jiki ayadda naga mahaifiyata na Kazar Kazar Akan aiki Nima haka na taso da spirit din.

Jahan Aarah tace ki saurare ni kiji abunda zan fada miki duk abunda baki gane ba call my attention ok?

Kaina a tsunkuye nace yess Jahan.

Tayi murmushi Tace'..aikin ki na farko karatu ne zaki zauna a koyar dake domin ki samu good secondry school cert,duk wanda kika gani agidan nan yana aiki toh yana da abun da zai nuna na matsayin matakin karatun sa, but yours is gonna be afternoon sessions a site din maids Thats in kin kammala duk wani aikin ki.

Game da ayyukan ki kuma Ya kamata kisan cewa.

Dana Shi kadai yake cin Break fast dinshi dan haka akan lokaci zaki na kasancewa a kitchen din dake section dinsa Wanda ke Kusa da dakin kwanan sa...
Adama tafada miki kitchen din nashi ne shi kadai ko?

A Dan Sanyaye Nace eh.

Tace good to Kar ki sake Kiyi masa abinci awani wajen inba A nashi kItchen din ba Doka ce

Cikin gamsuwa Nace yess maam

Tace By 7.30Am na Ko wani Safiya zaki shiga bedroom dinshi,do not wake him up kedai ki tabbata kin aje mishi fresh mint tea,and dont forget No Sugar honey Za kisa Masa 2teaspoon.
Zakiga oak side table anan zaki bari sannan sai ki fita

Inya tashi Zai fito karfe 8.00 Dai dai dan haka kiyi kokari Yana bada baya ki shiga dakin ki canza bedings Dinsa ki tsaftace dakin,kar ki manta zallan dakin baccin sa ne aikin ki,sauran part din san akwai masu kula dashi.

Sannan Karfe 9 zai taho dinning dinsa cin breakfast.

Sai ki tsaya ki yi serving dinshi ki Zuba mashi ko wani nauin abincin da akwai ba tare da kin tambaye shi mai yake so ba

Bayan kin kammala da nan sai ki koma ki hada mashi ruwan wanka akwai instrument so set it at exctly 39 degrees,yana wanka ke kuma kina tsaftace kitchen din sa.

Kar ki damu da serving dinshi abincin rana
a wajena yake ci.

sai dai Idan ya dawo zaki kawo abincin daren shi dining dinsa da misalin karfe 8.00,sauran lokacin da kike free zaki iya amfani da shi kiyi sauran ayyukan Daya dace

Nidai kallon bakin ta kawai nake,nace Ikon Allah!shikuma hakan rayuwar sa yake?Hmm tabb di.

"Baahi...adama ta dakatar da tunani na da kiran ta Afirgit na amsa da naam..

Tace Kinji abunda aka ce miki ko?

A dan birkice nace naji insha Allah zanyi Duka..

Nan Jahan ta sallame ni Fuskar Ta dauke da Wani irin Weak smiles.

Dana fice Adama ce ta matso cikin saukar da kai tace ranki shi dade jahan.

kiyi hakuri da shisshigi na amma sai naga kamar daman Da kika bata yayi yawa khaldun sa'ood bazai so ace.....

Bata karasa ba jahan ta daga mata hannu..Tace
Karki damu Da wannan adama
Nina haife shi kuma Nasan menakeyi sarai

Shin ya kike ganin hankalin yarinyar a yanzu?ko akwai abunda kika gano game da ita wanda zan iya sani ne?

Nidai Nayi nazarin Mai zurfi Akan tarihin rayuwar Ta dana jiyo Muddin Yarinyar nan ta wuce wannan jarabawar dana dora ta to ba shakka zan kaita wani matsayi mai kyau arayuwa...

Ajiyan zuciya adama ta saki tace a'ah babu komai Jahan she's perfect sai dai bamusan nn gaba ba...nidai Ki barmin komai A hannu na ni zan kula ..Adaman tace.

Jahan tace Toh kiyi kokari...

Daga nan sukayi sallama kowa ya shiga hidiman rayuwan sa.

washe gari da safe Ammu adama ta taso ni agaba tace min Yau fa zaki fara aikin ki bahiiyyah

gaba naKe Yawan faduwa sabida gani nake kamar Bazan Saba ba

cikin nitsuwa da jan kunne Ammuh adama ta Zaunar dani tace kina ji na?

Nace eh

Tace to kar ki sake ki shiga bangaren shi Gatsau,bare Kuma dakinshi in har ba akan aikin ki ba

and most impotantly babu ruwan ki dayi masa magana inba shi yayi miki ba

Ki nitsu ki ji duk abunda zaice miki batare da kin sa ido kina kallon nashi idanun ba,in yana tsaye kar ki zauna domin shi ba mutum bane mai son raini zakiyi hankali dashi sosai.

Cikin nazarin abun Na kuma cewa toh naji Ammuh

Tace Tashi muje na kaiki sabon dakin ki Zaman ki anan ya kare ..da sauri na dago nace sabon daki Na kuma?Tare zamu kuma kenan ko ammuh? Dan Allah kar ki rabu dani ..

Ammuh Adama tayi murmushi cikin son kwantar min da hankali tace Bahiyyah kenan,
Daga nan dai batace uffan ba,Hannu ta mika min na taso jiki a sanyaye na fara biyo ta.

Bamu tsaya ba sai a cikin wani sashi Ta cikin gidan Mai kamar four duplex apartment Amma bashi din bane design Ne kawai

Sai da ta nuna min Wani zigzag stairs da zan bi ya Sada ni da wajen aiki na kafin muka sauko Wani daki sai ta bude min
Muka shiga ciki Tare.

Its a very Exotic sleek style bedroom So simple and elegant.

gadaje Yan madaidaita har guda biyu aka bar min Ga brass lanterns Masu fararen haske,komina design din Sa fari ne kar gwanin sha'awa.

This is ur personal room.

AmmU tafada tana Bude Min wardrob dan na ga kayan sawaN da aka aje Min,tace Min
zaki iya muamala da kowa amma aikin ki baya bukatar ki sake da sauran ma'aikatan gidan nan If posible Just stay alone shi
Zai Fi miki.

Tace babuu wanda jahan ta karramashi da wannan matsayi saike dan haka kar ki bani kunya bahiyya.

Sai na dan kalle ta dan Sosai na kejin wani iri araina,sai naji na Bi na damu tsoro na neman shiga ta sosai..all this rules..oohh ya rabbi

Haka har adama tayi min sallama ta fice,tin daga ranar kuma ban sake ganin ta ba.

Nikuwa Ba jira Da safassafe na tashi na haura site din sa,i think A rana na farko i was a bit early sabida danaje kitchen din shin sai da nayi tsayuwan minti talatin ina jiran lokaci ya daidaita kafin na hado Masa steamy mint tea na dora akan italian tea sets farare kal
Na fito dasu

A hankali nake bin ta hallway da yakai ni har bakin kofar dakin shi,cikin kula natura kofar tsoro na kar na dago shi a bacci

Dama A raina na bari cewa He must be a demigod tunda kula da shi ma yazama abun aiki
Irin haka.

Dana shigo Fully na kare ma ko ina kallo Sai naga Dakin yafi karfin Ma ace dashi normal daki don yana da girma sosai its like an apartment on its own Har da palours.

A kusa da tsakiyar dakin aka kafe Wani sharbaben king sized royal bed,mutum ne a kwance fuskan sa gaba daya a rufe Take da duvet Ba Aganin komai daga siffar sa

Ban tsaya kalle kalle ba na aje tea din akan oak Oriented table na juya na fita kamar yadda aka fada min

Dinning hall Nayi da sauri naje na shiga jera mashi warmers din abincin shi Akan dinning table.

Haka na dinga bin lokacin aikina daki daki har naci nasaran gyara mashi daki na sauya bedsheet na jejjera pillows komai akan tsari

Saura minti kadan lokacin cin abincin shi yayi dan haka na fita naje dinning area din nayi tsaye ina jiran shi ya dawo Daga inda yaje don nayi serving dinshi

..But ganin 9 yayi dot bai shigo ba nayi himma na shiga serving
Duk abincin dake wajen yadda aka koya min.

Ina gamawa nayi sauri na koma dakin shi

Nan na shiga dayan kofar da nake tunanin bayan gidan sa ne,to tunda nike da alhakin hada mashi ruwan wanka that means tsaftace bayin sa ma aiki na ne.

Haka na gama kare ma wajen kallo,Kirji na ne ya biga ganin girman complicated bathrum din da ko a mafarki ma babu kaman sa,

na dan dafe kaina na taho domin fara abun daya kawoni

A cikin bayin Wata katoton mirror ce mai dauke da handler na kayan duniya.

Gefe dashi akwai bath tub wanda ajikin shi drawers ne masu yawa da Wata full sized jaccuzi da kuma site din wata striated rectangular glass shower Tana wani kyalli kamar ba ataba taba shi ba shima gefen sa da akwai fixtures masu dauke hankali

Komai Dai a bayin Royal purple And black ne girmanshi mutane fiye da talatin zasu iya shiga ciki

Nidai Tabe baki nayi kawai na shiga hada mashi ruwan wanka at exctly 39 degres din",wai shin wani dan adam ne a duniya Wanda har yake da specific tempureture na ruwan wankan sa?
rike da themometar dake bayin a hannu na nake wannan tunani ina tabe baki.

Finally i did whats right minti sha biyar kawai na dauka na fito daga dakin walking quietly Down stairs zuwa dining area dan naga ko ya taho

Luckly enough Bayan shi kawai na hango alaman yana cin abincin amma Koda wasa banga ya kammanin shi yake ba,leke nake ina daddafa pillar Ko zanci sa'a sai dai ko 1scnd ban yi ba naga ya mike alaman zai tashi,wani uban tsoro yasa Ni back turn da gudu na yi hanyar kitchen na dauko food dismisal tray Kafin na Dawo Nan ban ganshi ba

Kallo nabi abincin dashi wanda yake kamar ma ba ataba shi Ba,i was like did he even touched It?

Sai ido na yafada kan half stained spoon wanda ya isar min da amsa ta

haka Kawai na Shiga tattara Komai nakai kitchen na Kuma tsaftace su

Haka Najira har ya fita kafin na je loundry dan ance mani za'a dinga bada gogaggun kayan shi ina aje masa a closet dinsa.

Tun Daga ranar Haka nake yi kullum babu abunda ya sauya, Nakan dai gaida jahan dik lokacin da naga sarari dan ba ko yaushe ake ganin ta ba

Tun ina dar dar da gidan har na sake na jajirce na shiga bin dokokin aiki na tsaff inayin shi

Sai dai fa har yau ban taba ganin fuskan sa da kyau ba Idan na kawo mint tea yawanci fuskan sa a arufe yake cikin comfoters ko ma ya juya fuskan sa gefe

Ko da ina serving dinshi baya zuwa har sai na kammala na tafi, bare ma nace nagan sa

Rana daya dana ci sa'a ya zauna ina zuba mashi abincin idanun sa da dukan hankalin sa nakan wayar sa.

kyakkwar motsin nunfashin sa banaji bare naga ya kamannin sa yake.

All i know is he is fair,fari ne tass irin caribean white din nan

kalar jikin shi kamar ana goge shi da madara kullum, shi baiyi dau ba amma sheqin dayake yi ya wuce misali

yana da tsayi da ginannen jiki da duk da namijin da ya mallaka zaiyi tinkaho da shi Domin Kuwa babu maraban tsarin sa dana Indian actor john abraham..

Yau sati biyu kenan amma sau daya na taba jin muryan shi ranar dana ce muku na yana latsa Waya hakan ma Cemin Yayi

"leave"

Muryan nashi ko akwai dadi,Its husky,deep yet very appealing domin kuwa har yau ban mance sautin shi A kunne na ba.

One fateful friday morning na taho da safe domin aje mishi shayin Sa as usual nayi komai daki daki sai dai Ina juyawa zan fita naji tsadadden sautin muryan shi cikin dakewa da gadara Ya furta stop!!!?
Wai wacece ke Kike shigo min daki na?
#Follow
#SURAYYAHMS

*Share share yo

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top