x35&36
AHALINA
(Siblings of different fathers )
Book two 'in Aure uku series
Episode 3⃣5⃣➡3⃣6⃣
GARABASA GARABASA BONANZA
2024 Shin kuna sane da ban bada garabasa ba?
To ku kwantar da hankalinku ga chuchu dai tazo maku da garabasar sabuwar shekara,
Shin kin fara kin fara karanta YAR AREWA labarin captain Jasmine Bilal shareef da captain Shuraym Sadauki,
Ta tashi da mafarkin zama pilot a yayinda shi da yake kan aikin yake kusheta Akan tayaya ɗiya mace Yar Arewa zata zama matuƙiyar jirgin sama?
Soyayyar da ta shiga tsakaninsu ba tsammani wadda take ƙokarin danne kiyayya .
Ko kuwa kin fara karanta littafin ABLA ADNAN ne labari na matashiyar budurwa wadda bata barin taƙwana ,budurwar da tazamarwa masu kuɗin gaske barazana ,
Shin baki fara karantashi ba ko kin fara kin tsaya saboda kuɗin Ya maki yawa?
Maza zo na maki sauki ki ji yarda soyayyar ABLA take farawa da PRINCE WASEEMUDDIN,kowa na kiranta karuwa harda shima Shin ita ɗin karuwarce?
Maza garzayo gareni ka samu amsa,
Normal price na YAR Arewa book 1&2 N700
ABLA ADNAN N700 complete amma a wanann lokaci na garabasa kuzo na baku ,Yar arewa 1&2 da ABLA adnan Akan farashin naira N600 dukka biyun ɗari shida kacal 🥱ragin N800?
Kamar yayi yawa amma a haka dai Ya zanyi na baku wannan garabasar ta sati,maza kar ayi baku.
0264267657
Gt bank
Amina jamil adam.
09058191213
Dm me
بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ
Kwana gidan Nameer ƙwana ne akayi na yunwa kar ma ace Jamaimah domin shi yaci abinci a waje ,
Kamar yarda Ya shaida mata za'a kawo kayan abinci haka akayi,komai saida aka kawo mata har kifi da naman da zata bukata amma taƙi soya koda ƙwai ne dan bama tasan ta inda zata fara ba,
Washe gari da safe tana tashi wanka ta ɗanɗasa ta shirya cikin ɗinkin doguwar riga Mai A shape na atampa,wani figeggen gyale ta jawo yayin da cikin ta ke mata faman ƙungi yunwa ,Atm card ɗinta ta take saving kudin da ita kanta bata san nawa bane ta ciro ta saka cikin Jakarta dan dole ta siyo junks,
Main Atm Card dinta ta kalla tasan a yanzu tabbas mahaifin ta yayi freezing mata Account ɗina cos duk lokacin da tayi wani rashin jin abunda yake mata kenan,
Sakashi tayi shima cikin jakar tace "kilan wannan karan naga akasin haka ,who knows ,"
Takalmi flat ta jawo ta saka tana Mai sake touching fuskarta kana ta ɗauki hanyar fita ,sai da taje tsakiyar falo ta kula dashi zaune hannunsa ɗauke da mug ɗin coffee yana sipping a hankali,
Turo baki tayi saboda fushin da take dashi,
Har ta juya zata cigaba da tafiyarta taji miryarsa yana faɗin"Ina zakije baki tambayeni ba?"
Ba tare da ta juyo ba tace"zan je neman abinci ne tunda Allah yasa ina da kuɗi ba mitsiyaciya ba"
Cigaba da tafiyarta tayi inda ta tsinci muryarsa yace "ina jin ba'a koya maki tambayar miji idan za'a fita ba a gidan ku ,amma nasan kinsa Menene hukuncin miji yace ma matarsa bai yafe ba ko?"
To idan kika fita gidannan bada izini na ba ban yafe miki ba,tunda ban rageki da komai ba
Kafun tace wani abu ya tashi Ya wuce kitchen dan samawa kansa abinda zaici,
Binsa tayi kamar zata fashe ta tsaya bakin kitchen ɗin tace"wai menene damuwarka ne Nameer ,Mai yasa kake san bamu wahala a zamantakewar Auren mu,ni ban tab'a jin inda akace wai dole mace sai tayi ma mijinta girki ba dole,beb we have money,dan me akayi guraren cin abinci?"
Anyisune domin mu masu kuɗi waɗanda basu san menene wahala ba,dan mene Allah Ya bamu sauƙi muce mu bama so bamu gode ba?
Murmushi yayi wanda Ya bayyana ƙyawawan haƙoransa kafun Ya buɗe cikin crete ɗin kwai Ya ɗauki guda biyar Ya fasa cikin bowl Kana Ya dauko ledar sausage wanda yake a yayyanke Ya zuba a ciki Ya yanka albasansa yasa spices Ya fara whisking ,frying pan din da Ya zuba mata butter Ya juye kwan kana ya bisa da cheese yana soyuwa yana ƙarawa a haka har Ya bashi omelet ɗin da yake so,
Tana nan tsaye tana binsa da ido Ya gama abunda zaiyyi Ya juye a plate ɗaya yazo ta saitin ta zai wuce,
Ganin tayi bake bake a ƙofar yasashi kamo hannunta Ya maidata ciki Ya fito dan zuwa bawa cikinsa hakkinsa ,
Da mamaki ta bisa da kallo Kana ta mara masa baya tana Mai faɗin"Baby magana fa nake amma kayi kamar baka jini ba,sannan bana san Kana cemun baka yafe ba cos wata rana zan fita azo kuma ana wane yace wane Ya faɗa,please ka zauna muyi magana cos yanzu ma maganar da muke im mad hungry sannan naga omelet ɗinka na mutum guda na. "
Bai kula ta ba still Ya wuce Ya zauna kan dining table Ya fara yankan omlt ɗinsa yayi bismillah ya kai baki,
Zama tayi a kujera Mai kallansa amma Ko inda take bai kalla ba ballantana yace mata bismillah yayin da ita kuma zuciyarta ta gama ƙwaɗaituwa da abunda yake ci ga uwa uba yunwa na ƙwaƙwular mata ciki,
Wata irin ƙara cikin ta yayi na yunwa wadda taso saka shi dariya amma Ya maze sannan yaki kalanta,
Licking lips ɗinta na ƙasa tayi tace"Baby im hungry fa"
Bai kulata ba still har saida Ya tabbatar babu ko anini a plate ɗin kana Ya Kalleta yace "Baby yunwa kuma?"
Bai kamata ace Kina jin yunwa ba a cikin gidan nan bayan komai na abinci akwai,amma nafi tunanin Yunwar bata ciki ba da yawa ,ni kinga yau ina tashi da baƙar yunwa na tashi shi yasa kikaga babu shiri na nemawa kaina mafita.
Yana Mai kai ƙarshen maganarsa Ya tashi da plate ɗin ya kai kitchen Ya wanke Kana Ya wuce ɗakinsa dan shirin fita aiki,
Har Ya gama abunda zaiyyi Ya shirya tana zaune kan dining ɗin ranta a bace cikinta kuma na ihun chiroma,
Kamshinsa kawai Ya tabbatar mata Ya fito ,Takowa yayi inda take Ya ɗuka yayi kissing gefen kumatunta yace "to Baby ni zan wuce aiki and inaso kar ki manta abunda nace "muddin kika fita cikin gidan nan ban yafe miki ba Ko kaɗan idan kuma kin yarda kin shirya ƙarbar tsinuwar malaikun Allah to kije duk inda kike so,ni dai nace Allah ya isa,ki kula mun da kanki.
Yana kai aya Ya saka kai Ya wuce yana Mai juya Key ɗin motar sa,
Kukane Mai sauti Ya Ƙwace mata,ko giyar Wake tasha bazata fita ba saboda tasan girman Allah ya isar tasa ,amma wanne irin wulaƙanci ne Nameer ke san yi mata haka?
Kuka ta sake fashewa dashi saida tayi Mai isarta Kana ta jawo wayarta ,tama rasa uban da zatayi tunda dai ita kasar nan ba wasu frnds gareta ba,duk waɗanda suka gama makaranta tare ta ɗaukesu ne matsayin masu mata bauta da maula shi yasa koda aka gama makaranta babu wanda ta sake nema,dan kada kowa kuma Ya dameta Ko yasan ina take ta cire layinta na ƙasarsu ta karya ,koda ma tana dashi babu abunda zatayi da mutan cikin layin dan ta gama da cameroon kuma ,ba dai yanzu ba,dan da rayuwar da zataje tayi achan ta ƙwammace ta zauna da Nameer tunda tana mutuwar sansa kamar ranta yanayin life ɗinsa ne kawai damuwarta,
Data ɗinta ta kunna tayi searching yarda zata dafa indomie kana ta shiga kitchen ɗin da wayar a gefenta ta dafa indomie ɗin da ta chabe,
Tsaki tayi ta soya ƙwai kamar yarda taga yayi kana ta haɗa black tea shima according to recipe online,bata tunanin rayuwarta da gyara saboda mene aibun rayuwar hutu?
Itafa saboda mulki bata tab'a koda takawa kitchen ɗinta ba ballantana ta kai ga dafa wani abinci,
Kira ɗaya idan tayi za'a gama mata komai jiki na rawa,idan baiyyi mata ba ta saka a kulle mata mutum har Ya manta ma ta kullesa,amma wai yau itace tayi girki ma cikinta wanda duk ta hanyar dafawa ta kokone hannunta.
Fara cin indomie ɗin tayi ,wani rashin daɗi da Ya ziyarceta Ya saka tayi saurin firzarwa saboda tayi mata wani yum yum a baki,
Bata san abinci mara daɗi Ko yayane dan haka ta ƙi ci,shima ƙwan da ta fara ci yasha maggi a haka dai ita tutturasa badan yana mata daɗi ba saboda yunwa dai,
Bayan ta gama nan ta bar ƙwanikan ta koma kan kujera ta zauna tana tunanin yarda zata nema wa kanta mafita,
Tana wannan zaman taji ana knocking ,ɗan tsaki tayi cos itafa bata san wahala sannan takawa ta buɗe kofar gani take kamar taci baya ta kuma kaskantar da kanta,abune fa wanda bata taba ba,cigaba da latsa wayarta tayi yayinda knocking ɗin kuma yaƙi karewa ,
Nadiya dake tsaye tana faman bugu ce ta zagaya ta backyard ɗin gidan inda karamar ɗoor ɗin da zata sadaka da kitchen ta nufa tana Mai Murɗa handle d'in wanda cikin sa'a ya buɗe ,kai tsaye ta shiga tana tunanin ko lafiya cos tasan Jamaimah na gidan sannan adadin knocking ɗin da tayi ko me mutum yake yi zaiji sai dai idan ba lafiya ba wanda tunanin hakan Ya sakata shigowa ta ƙofar bayan,
Da mamaki ta kalli Jamaimah lokacin da tayi shigo Falon ,a ɗan razana Jamaimah ta Kalleta jin mutum babu zato babu tsammani kana tace"wallahi har kin ban tsoro nayi tunanin aljanace yarda kika shigo ɗin nan babu zato babu tsammani,dama kece ke ƙwanƙwasa kofa,"
Ƙaramun murmushi Nadiya tayi kana ta tako ta zauna kujerar dake kusa da ita tace "nice sannan nayi mamakin yarda na shigo na ganki zaune kamar bake ake ƙwanƙwasawa kofa ba,"
Gyara zama tayi tace "wallahi na tashi naje na buɗe ɗinne aiki,kinsan abunka da mutum bai saba ba"
Kaɗa kai Nadiya tayi tace"tabbas kuwa abunka da mutum bai saba ba dole ne ayi masa uziri,to Ya za'ayi an maki,
Tashi tayi tace nufi kan dining ɗin tayi ƙwashe komai ta kai kitchen kana ta zubar da indomie ɗin ta gyara kitchen kana ta ɗora sanwar jallof rice wanda dama shine babban abinda Ya kawota,lokacin da Nameer Ya kirata a waya sukayi magana tayi Alƙwarin taimakawa wajen koyawa Jamaimah hankali da sanin mutuncin ɗan adam ,
Kafun kace mene gidan Ya cika da kamshin party jallof ɗin da Nadiya ke dafawa,babu abunda Ya damu Jamaimah ko tace dan me zatazo mata gida ta kama girki ko makamancin haka illa ma daɗi da takeji yau zataci homemade Food dan ƙamshin abinci Ya fara dukar mata dukkan wata ƙofa dake cikin hancinta na shaƙar kamshi.
Abinci na cikin nuna ta dawo ta zauna Falon tace"Kina jin daɗi Addanmu matar hamma Nameer ,"
Murmushi Jamaimah tayi tace "bakiji yarda kika sake shiga raina ba dan wallahi a rayuwa zan iya bada komai akan Nameer domin soyyayar da nake masa ba ƙarya bace ba yin Allah ne kawai na yarda da hakan,zan iya sadaukar da komai nawa kan Nameer.
Crossing kafa Nadiya tayi tace"ba shakka,"
Cikin zaƙuwa Jamaimah tace "na ƙosa ki Gama girkin nan bakiji ƙamshin sa yarda yake saka yawona rushing ba".
Tashi Nadiya tayi cikin saurin tace kinga na ma manta ban gyara chicken ɗin da Nagani cikin fridge ba zan yi Pepper chicken da ita,
Cike da murmushi Jamaimah tace "yaji garlic please ,wallahi naji daɗin zuwanki,dan Allah ki dawo gidan nan"
Ba tare da Nadiya tace komai ba ta faɗa kitchen ɗin tana murmushi.
Bayan Nadiya ta gama komai na Abinci ta ɗauko warmer Mai kyau ta juye jallof rice ɗin Ya zama saura ƙanzo sannan shima chicken ɗin ta juye komai saura kaya miya da wuya ɗaya ,basket ta ɗauko ta juye sannan ta fito tana Mai faɗaɗa murmushinta ,gyalenta ta ɗauka da keyn motarta tace"to ni nayi gaba zanje na kaima hamma cos jiya matar sa da zata iya sadaukar da komai dominsa banda girman kanta da izzarta ta barsa da yunwa,shi yasa ƙanwarsa kuma Mai ƙaunarsa wadda zata kawo masa matar Aure nan kusa wadda zata na mashi girki da girmama yan uwansa ta zo domin yi masa girkin cikin gidansa matarsa tasan tana wasa babban ganganci domin idan tayi wasa ba ƙanwarsa ce zata shigo gobe ba matarsa ce.
Tana kai ƙarshen magana ta fara takun barin falan,har takai bakin ƙofa ta juyo tace"akwai ƙanzo da wuyan kaza na aje miki,kinsan ance ido guba sannan gashi kamshin Ya dakeki da yawa,iyawar kenan domin Mamina duk kuɗinmu sai da ta tabbatar nasan sirrin kitchen ,indai mijin da zan Aura yayi Aure to badan girki bane sai dai dan yana da ra'ayi,"
Bata jira mai JAMAIMA zata ce ba ta sa kai ta fice tana Mai barin ƙofar Falon a kulle wanda tasan dole Jamaimah ta taso ta kulle.
Wani irin abune ya tsayawa JAMAIMA a wuya bayan fitar Nadiya domin tunda take a rayuwata babu wanda Ya taba takata yayi mata wulaƙanci kaca kaca kamar Nadiya,
Tashi tayi ta nufi kofar Falon ta kulle kan ta shigo ciki tana Mai jin wasu hawaye na bin kuncinta ,ita Nadiya zata zo ta taka har cikin gidanta sannan dan ta mayar da ita mayya ta aje mata ƙanzo da wuyan kaza,ita gimbiya Jamaimah ,ɗiyar babban gidan sarauta da kowa ke shakka cikin ƙasarsu,
Ɗakinta ta faɗa tana Mai faɗin wallahi yau idan Nameer Ya dawo sai Ya faɗa mata dalilin da ya saka Nadiya tazo Ya zage ta cikin ruwan sanyi haka,sannan Ya faɗa mata ta ina ya gwadata a gadonsa yaga ta b
Kasa da zaiyyi mata kishiya wanda zancene dama na ƙanzan kurge dan wallahi babu wanda Ya isa,dama menene auren idan ba shi ba
**
Dan Allah kumun afuwa da rashin update da baku samu kullum nakoma makaranta inaso nayi adjusting amma insha Allah zan na maku ƙokari ,sai mun haɗu idan Allah Ya kaimu..
.
Chuchujay✍🏽
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top