x29&30

AHALINA

(Siblings of different father's)

Book 2 'in AURE UKU series

           By

CHUCHUJAY ✍🏽

Episode 2⃣9⃣➡3⃣0⃣

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

    Cikin Yauƙi Jamaimah ke takawa dan zuwa motar da Nameer Ya shiga ,ganin Ya wa motar key tasan tabbas idan bata hanzarta ba zai tafi yabarta Ya saka ta ja akwatinta gudu gudu sauri sauri ta nufi motan tana Mai faɗin "Baby mana wai menene hakan?"

Buɗe bayan motar tayi ta saka akwatinta dan kit din kana ta koma passenger seat ta zauna,

Tun kan ta rufe ƙofar da kyau Ya fafareta dan har sai da ta saka ƙara saboda yarda ta tsorata,

Tunda suka fara tafiyar har suka isa gidan bai ce mata komai ba hakazalika itama dan ganin yarda Ya haɗe rai kamar an aiko masa da saƙon mutuwa,

Bakin katafaren gidansa dake cikin GRA ya tsaya yana Mai yin horn,sau ɗaya yayi Mai gadin gidan yazo da gudunsa Ya buɗe masa dan yasan motar Nameer sarai,

Bai tsaya kula gate man ɗin ba Ya nufi ma'adanar aje mota Ya aje,

Shi Ya fara fita Kana ita ,

Get man d'in da Ya tako garesu ta kalla da wani yauƙin wulaƙanci tace "kai zo ɗauki min akwatina ka shiga dashi ciki sannan kabi mun shi a hankali dan yayi costing salary dinka sau goma."

    Da mamaki Nameer Ya juyo yana kallanta dan a haife Mai gadin Ya haifeta,

Hannayensa Ya saka a kugu yayin da Mai gadin Ya nufi akwatin dan dauka amma Ya tsaya a lokacin da Nameer yace "Baba sulaiman bari mata akwainta ka koma kan aikinka dan aikinka yafi ɗaukan akwatin nan."

Babu musu Baba sulaiman Ya juya yana Mai faɗin Angama ranka shi daɗe.

    Buɗe baki tayi tawani shagwab'e fuska tace "yanzu dan Allah Baby mene hakan,Mai zaisa kayi humbling ɗina gaban Mai gadi kaskantacce,wannan ai salan kaja mun raini ne ina matar gida.

Karamin murmushi yayi Ya Kalleta a kyau yace "Jamaimah kenan,kina bani mamaki,ke gani kikeyi kamar ke kinfi kowa a duniya saboda kawai an haife ki gidan sarauta ko?

Ku gani kukeyi kowa ma banza ne saboda kuna da mulki ko?

Bari kiji da kyau ki kuma saurareni,abunda kikayiwa iyayena Yau yana daya daga cikin abunda zaisa bazan tab'a sakinki ba sannan bazaki tab'a samuna miji ba muddin ke wulakanci shine jigon rayuwarki,sannan zan nuna maki ke ba kowa bace face mutum wadda idan kika mutu kasar da za'a saka kaskantacen almajiri kema nan za'a sakaki ,kilanma nashi kabarin yafi naki idan yafiki aiki mai kyau domin abinda baki sani bs shine wulaƙanta dan adam kawai zai halaƙar dakai,.

Abu Mai muhimmanci kuma da nake san ki sani shine  a kasarki ne kike gimbiya amma a ƙasata a gida na a matsayin Matata ke bakowa bace sai wadda zata zauna tayi mun biyyaya tayi ibadar Aure,idan kina so fa kenan,amma duk ta inda kika bullo nima na iya bullawa ta gurin ni dake kuma shege Ya fasa,kina wannan wulƙancin kuma wallahi zanyi Aure har mata uku musha soyayya ke kuma ki sha wulaƙancinki ke kaɗai tunda shi kika zab'a 

    Yana kai ƙarshen zancen sa Ya juya dan shiga cikin gidan,binsa tayi da ido tana Mai jin zuciyarta na mata wani irin zafi musamman da Ya kawo mata maganar Aure,Cije leb'enta na ƙasa tayi tace "ina sanka Nameer sannan kai nawane ni kaɗai ,bakuma zaka chanza ni daga yarda nake ba ,haka nan zaka karb'eni domin wannan sarautar a jinina take babu wanda ya isa Ya cire mun wannan izzar ."

Da haka tabi bayansa da kayanta,

A falon dake ihun Naira ta tarar dashi tsaye hannunsa cikin aljihu ya juya mata baya wanda ya tabbatar mata da jiranta yake,

Aje akwatin tayi ta taka garesa ,cikin wani irin salo ta saka hannunta ta ƙugunsa ta rungumesa ta baya wanda sai da Ya saka shi ajiyar zuciya,idanunsa Ya rufe gam yana Mai jin jikinta kwance a nasa kamar dan shi akayi,

Lafar da kanta tayi a bayansa cikin wata irin shagwab'abbiyar murya tace"Baby ban iya faɗin im sorry ba da na fada maka koda zuciyarka zatayi sanyi,a jininmu yake faɗar Kalmar haƙuri tana bamu wahala,amma komene nayi maka bazaka iya barinsa Ya wuce ba idan ka tuna saboda kai na baro  komai nawa nazo gareka ,i love you very much Nameer sannan ni banyi tunanin zuwana gidanku zai jawo abunda Ya jawo ba da zan nemeka ne ko ta yayane na sanar da kai tunda address ɗinka  ma a company dinka na samu,kar ka saka na shiga wani Hali ,ka kalleni mana da kyau,nasan kaima kana jin abunda nake ji akanka gareni,cos ni macene da babu Mai ganina da tayin soyayya ya dauke ido,please Baby."

    Ƙaramun murmushi yayi Mai sauti da tagama maganarta ,tabbas yana san Jamaimah amma soyayya bata rufe masa ido ba Ya zauna yana kallan wanann rashin tarbiyar tata dan hatta a kalami bata da tarbiyya wanda dole Ya gyara mata zama tasan cewa mulki ba hauka bane,sannan sai Ya gasa masa aya cikin ruwan sanyin da bazata taba sanin lokacin da zata faɗa masa sorry ba mara iyaka,

Duk da yana jin kamar yayi ripping duk wani kaya da ke jikinta saboda irin rungumar da tayi masa amma ya danne lust dinsa Ya kama Hannayenta Ya b'anbare su daga jikinta Ya juyo yana kallanta yace "Gimbiya Jamaimah Rais,tashen ki yana burgeni,wato baki iya faɗar sorry ba sannan kike ikirarin Kina sona ,okay barka da zuwa rayuwar Nameer Babu gayyata , "

Ɗaki ɗaya Ya nuna mata cikin ɗakuna biyar d'in dake jere da juna yace "ga ɗaki Chan ki kai kayanki sannan kiyi amfani dashi,"

Cike da mamaki ta juyo ta kallesa tace"ni bazan zauna ni kaɗai ba a ɗaki idan Babu kai sannan naga gidan dagani sai kai ,ina yan aiki dan ni wallahi bazan iya aiki ba",

    Baice mata komai ba Ya juya dan shiga ɗakin dake nasa yace "idan bazaki iya aiki ba gimbiya JAMAIMA zaki iya komawa gidan ku ,amma ki sani da Aurena zakiyi ta yawo dan wanann karen nima yin kaina bazan sakeki ba.

Yana kai karshen maganarsa Ya shige ɗaki na huɗu dake daga Chan ƙarshen corridor Ya barta tsaye.

    Tab'e bakinta tayi taja kayanta tana mai faɗin"zaka biyu ne indai muna gida ɗaya".

    Bayan shigar Nameer shahararren ɗakinsa kan gadonsa Ya faɗa yana Mai duba lokaci ƙarfe Ɗaya da rabi na rana,wayarsa Ya ɗauko yayo ordering pizza dan bashi da komai na abinci gidan sannan pizza ɗin yake sha'awa amma yana fita zai siyo mata kayan abinci duk da kuwa yasan ba iya girkin tayi ba amma a hakan sai Ya gyara mata zama tasa ita ba kowa bace.

Wayarsace ta fara ruri,Nadiya ke kiransa, kira ɗaya Ya ɗaga,conference ne su uku,daga ɗayan bangaren Nadiya tace "Hamma are you okay?"

Ajiyar zuciya yayi yace "im Okay Nadiya and nasan yarda zanyi da Jamaimah Yes i was planning to talk about her da su mami idan komai Ya lafa cos ina santa ,we made mistake amma Aurenmu a ko ina Aure ne wanda ya ɗauro,amma yarda tazo wa su mami dole ne nayi da gaske wajen ganin na gyara mata zama."

Daga ɗayan bangaren Abdallah yace "Hamma ka dai kula kar ka shiga hakkin ta cos tun ranar da aka ɗaura maku Aure hakkinta ya hau kanka.

    Rufe idanunsa Yayi kamar yana gabansu yace"Insha Allahu bazan cutar da ita ba ,Ni dai alfarma ɗaya zakuyi mun wanda shine ku tayani wa mami magana da Papa dan Allah."

Assuring ɗinsa sukayi inda Abdallah Ya fara fita a wayan Akan zaije wani taro da aka gayyace,

Yar hira Kaɗan suka taba da Nadiya wadda duka akan lallashin junane kafun sukayi hanging Call ɗin .

    Pizza ɗinsa ce tazo ya fita ya shigo da ita,

A ƙaton dining table Ya zauna bayan Ya ɗauko holandia da cup,

Ya buɗe zai faraci ta fito a dakin nata cikin buguwar riga mara Nauyi baƙa wadda ta ɗauki farar fatarta sosai,

Saurin ɗauke idanunsa yayi akanta yana Mai gutsurar pizzan da Ya ɗauko,

Cikin wani irin Yanayin ta tako garesa tana Mai yarfe hannu tace"Baby pizza God abunda nake craving kenan."

Zama tayi tana Mai ɗauko cup d'in da Ya zuba hollandia ɗin tayi sipping,bai hana taba sanann shima bai hanata sha ba ,a haka suka fara cin abincin suna shan hollandia ɗin a cup ɗaya yana Kara masu,

Bayan sun gama Ya kalleta yace "anjima zan kawo Food stuffs zanki fara girki".

    Wata irin dariya ta saka har tana ƙwarewa tace"amma wasa kake ba?"

I mean hatta ruwan wankan kaimun ake a gidan mu ,ni ko ruwan zafi bansan Ya zan ɗaura ba.

Tashi yayi bayan ya goge bakinsa yace "Ai kin iya kunna data dan haka kiyi browsing,"

Wayarta dake gefenta Ya ɗauka yasa numbernsa yayi dialing tana shiga Ya kashe yana Mai aje mata yace "Ni zan fita ki kula mun da gida sannan bathroom ɗina yayi datti kije ki wanke mun,bana san na dawo nagansa haka nan."

    Kafun tace wani abu Ya fita a gidan,

Murmushi tayi bayan fitar sa tace "abu na technology ,kafun ka dawo na samo yar aikin da zata wanke maka bayin amma ni kam sai dai a soni a lallab'a ni. "

    CHUCHUJAY ✍🏽

*

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top