x25&26

AHALINA

(Siblings of different father's)

Book two 'in Aure uku series

       By

CHUCHUJAY ✍🏽

EPISODE2⃣5⃣➡2⃣6⃣

   Cikin takunta na ƙasaita da isa ta fito daga bayan Baba Mai gadi wanda suka gama rigima kafun ta shigo,dan tsabar isa har cewa tayi sai tayi silar barin sa Aiki a gidan ,

Tsoro yasaka yayi mata iso jin tafara maganar sanadiyar barin sa Aiki gidan tunda bai san menene matsayinta a ciki ba .

    A zabure Nameer Ya tashi yace"Mai kikeyi anan?"

Cikin mamaki Nadiya ma ta Kalleta tace "Nima dai abunda nake shirin tambayar ta kenan Hamma ka rigani,ina kasan wannan rasa kunya beran tankar ,dan wannan matar a gamon da mukayi na farko nasan bata da ɗa'a and im sure bibiyata take yi wanda shine yasaka ta zo gidan nan,gashi ni kuma a yanzu bani da lokacin ta dan Allah ka fitar da ita daga gidan nan dan ban shirya ɗaukar models ba im sure gurin zama ta rasa,"

  Murmushi tayi ta karaso ta zauna akwatinta da kit ɗin ta wanda baba Mai gadi Ya dauko mata gabanta,hannunta kuma ɗauke da lollipop tana tsotsa,

Ajiyar zuciya tayi tace "Nadiya kalli ya wuce mana ,abunda Ya faru tsakanina dake a airport rashin sanin juna ne,na tabbata da ace munsan juna a lokacin farin ciki zamuyi na haɗuwa da juna,amma yanzu tunda na gano wacece ke ina farin ciki na samun sister Mai irin taste dina ,komai Ya wuce,"

Kallan mami tayi tana Mai faɗaɗa murmushinta tace"daga gani wannan ce mom ɗin mu,ga dad,barka da gida."

    Cike da mutukar fushi Nameer yace"JAMAIMA watch it sannan kafun ranki yayi mutukar b'aci kizo ki bar gidan nan,"

Kallansa Mami tayi tace"menene Haka NAMEER?"

Saboda mai ranta zai b'aci and wacece wannan d'in daga gani kasanta ,yanayin ka kawai ya nuna mun you're not pleased da ganin ta,meke faruwa?.

    Mutuwar zaune Nadiya da Abdallah sukayi jin sunan da NAMEER Ya ambata,so wannan ce Jamaimah,

Nadiya na ƙokarin magana Jamaimah ta rigata ta hanyar faɗin"Mom kiyi hakuri da yarda na zo maki baku gayyace ni ba cos im high class nasan yarda zuwan baƙo uninvited yake ,amma Mom ni ba baƙuwa bace ba,ni ƴarkice saboda tsakani na da NAMEER akwai igiyiyoyin Aure guda uku,."

    AURE?

Mami da Papa suka maimaita Kalmar da mutukar mamaki.

Cikin yanayi na ko 'in kula Jamaima tace "uhum,bai faɗawa kowa ba kenan,"Juyowa tayi tana Mai kallansa yarda yaka tafarfasa kamar zai ƙone tace "baby na faɗa maka lokacin da mukayi Aure Akan Kagama gujegujenka da duk wani abu a zakayi idan ma Aurene kayi amma kasani 'ina nan Zan dawo rayuwarka,which im sure a yanayin da na sameka baka da Aure wanda hakan yana nufin ka rike mun alƙwari ,menene abun boyewa yan gidan ku, tho nima na boyewa mahaifina maimartaba Rais amma mahaifiyata babbar gimbiya tasan da maganar ,magana ake tayi min aure nikuma bana san wanda za'a Aura mun,infact bani da niyar bautawa ko wanne lamido da sunan sarauniya wadda ta basa mulki bugu da ƙari kuma bana san aikata laifin Aure Akan aure tunda dai niɗin matar Aure ce kuma ina san mijina so na hakika 'dan haka na yanke shawarar barin kowa da komai Nazo gareku,"

Kallan mami da Papa tayi waɗanda suke speechless tace"ina fatan zakuyi haƙuri dani ku ƙarb'eni a yarda nake ta bangarena kuma nayi alƙwarin zanyi iya bakin kokarina wajen ganin na ƙwantar da kaina gareku a matsayin ku na surukaina duk da abune wanda ban iya ba,"

Gyara zamanta ta sake tace "kuyi haƙuri ban samu damar gabatar maku da kaina ba,sunana Jamaimah Rais ,yar asalin garin cameroon haifafiyar masarautar Dilah,"

Ni kaɗai nake gurin iyayena sannan nice ke da hakkin nada lamido Ta hanyar Aure,haka al'adarmu yake ,ni kuma ina san ɗanku shi yasa Na bar komai domin sa.

    Hannunta NAMEER yakama yace "tashi kibar gidan nan Jamaimah kafun raina yayi mutukar baci naki Kema Ya b'aci,kizo ki koma inda kika fito."

Tsawar da Mami ta daka masa itace ta saka Ya saketa ,

Kallansa tayi ranta a mutuƙar bace  tace"samu guri ka zauna ,Bana san iskanci yanzu Zan b'ata maka sosai da sosai."

Kallan su Nadiya tayi waɗanda a kallo ɗaya zakayi masu kasan cewa sun san da maganar Jamaima,ƙaramar dariya tayi tace "so its true,fuskar kannenka ma Ya faɗa Sun san komai so nida Papanku ne yan iska waɗanda bamu da darajar da zamu san abunda kayi ko,"

Katab'a zuwa kace kana san Aure munce baza muyi maka ba?

Shine har zakayi Aure a wani guri NAMEER bamu sani ba?

Yaushe zamu samu peace sau ɗaya a gidan nan ne,jiya da daren nan muka fita daga wata fitinar gashi wata ta mana sallama,

Tashi tayi idanunta cike da ƙwalla ,

Cike da tashin hankali NAMEER ya bita yana Mai faɗin"mami i can explain please,"

Da fitina cikin idanunta ta juyo tana kallansa tace"idan ka sake taku ɗaya ka biyoni sai na sab'a maka ,Zan maka abunda zakayi dana sani nima nayi,sannan bana san na fito naganka kai da yarinya Chan a cikin gidan nan ,ka ɗauke ta tunda Allah yayi kana da naka gidan ka kaita,Ai kaine ka haifi kanka baka neman shawarar kowa kaje kayi abinda kaga dama da rayuwarka."

    Durƙusawa yayi a gurin yana kuka saboda irin tsananin bacin ran da Ya gani a cikin idanun Mami,yana wannan kukan Papa ya gifta ta gefensa ba Tare da yace masa komai ba yabi bayan matarsa ,

    Tasowa Nadiya tayi ta Dafasa tace "Hamma wannan kukan bashine solution ba,Ka tashi yanzu kamar yarda Mami tace zamu san yarda za'ayi ,"

Tasowa Abdallah yayi shima yana Mai faɗin"hamma we will sort everything out insha Allah."

Tashi yayi yana Mai kallan inda mami tayi kana Ya share hawayensa Ya maida kallansa kan Jamaima wadda take mamaki zaman da yayi yana kuka,

Tasowa tayi tace "ni Bansan menene abun tashin hankali ba Akan maganar Auren nan,naji ba'a kyauta ba amma Ai the damage has been done maine abun kuka ,"

    Cikin wani yanayi na b'acin rai Nadiya Tace"na tabbata baki san menene girman abunda kika aikata ba ko nace baki san menene ake kira da mutunci family ba shi yasa zaki tambaya menen abun kuka."

Barin gurin tayi 'dan idan ta cigaba da Zama a anan gurin zata yiwa Jamaimah wulaƙancin da har abada bazata manta ba,

  Da wani iri yanayi NAMEER Ya kaleta yace "kisan inda dare yayi maki domin bana tunanin darenki yana tattare dani,"

Cikin nutsuwa Abdallah yace"hamma idan har Auranka kai da ita kaima kasan Aurene maganar ta Kama gabanta bai taso ba,"

Yarda mami ta faɗa ka ɗauketa ku tafi gidan ka 'in yaso daga baya komai zai gyaru.

    Cikin ido Nameer ya kallesa inda shi kuma Ya bashi assurance da ido,

Bai ce da ita komai ba ya shiga ɗakinsa ɗan ɗauko mukullin motansa dana gidan.

    Zama abdallah yayi kujerar dake kusa da ita yace"ni tabbata ba kisan wanene hamma ba,ta iyu kin Aure sa amma bana tunanin kinsan menene ma'anar Aure ,nuna lollipop ɗin da Take sha yayi yace "na farko wannan alawar da kike tsotsa gaban su Mami kina magana cikin kalamai marasa da'a Shine abu na farko da zai fara baki matsala,'dan a iya zuwanki yau na tabbatar ladabinki da sauki,

Ta iyu a inda kika fito kowa yana duƙa maki amma annan kuwa Babu Mai duƙa maki muddin baki sauke girman kai da yake damun ki ba dan akwai sa,

Anyi kuskure kuma ba wai ance ke kikayi ba,dukkaninku kunyi amma ki sani abunda kike taƙama dashi na Aurensa to Allah da Ya halicci Auren Ya halicci rabuwarsa ,idan kuma Kina san ƙarkonsa a dole kisan wanene Nameer da abunda Ahalinsa suka ƙunsa."

Bai jira jin ta bakinta ba Ya bar gurin.

    B'in sa Jamaimah take da kallo hannunta riƙe da sweet ɗin da bataga wani aibu ba dan tasha a gaban ko wane,wannan Shine karo na farko da wani Ya zauna Ya daddara mata,

Tabbas Family ɗin Nameer is interesting,tana san sabo da baƙon yanayi 'dan haka tana maraba da wannan.

Tana wannan tunanin taga gilmawar Nameer   Ya nufi ƙofa,

Kallan akwatinta tayi da kit ɗinta cikin wata irin shagwababiyar murya tace "baby bazan iya ɗaukan abunnan ba is heavy babu wasu maids ne around here?,"

Jin babu motsin kowa sannan yafita a Falon ya sakata yarfe hannu tana Mai jan akwatin da kit din tabi bayansa.







CHUCHUJAY ✍🏽

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top