x23&24

AHALINA

(Siblings of different father's )

Book two 'in Aure uku series.

             BY

CHUCHUJAY✍🏽

EPISODE2⃣3⃣➡2⃣4⃣

 

بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيمِ

  Zazzaune kowa yake domin cin Abincin da Anisa ta dafa ,amma a zahiri kuwa dukkan su fargabace sukeyi dan baza suce ga wanda aka sakawa poison ɗin ba,

Nadiya ce ta kalli Mami tace "Mami we are risking this im sure ba ko wanne abinci Anisa ta sakawa guba ba cos ba shine plan ɗinta ba,yanzu babu mai cin abincin nan sai ta fito,duk abincin da tayi insisting bawa Mami shine poison,she's not that fool enough da zatayi poisoning namu duka,

Nasan cin Abincin abune Mai haɗari cos wane Ya sani everything can happen ,zata iya sake plan ɗinta a koda yaushe but this time around im sure tayi making mistake wanda Mami ne kawai target ɗinta.

    Nadiya na rufe baki Anisa na Takowa zuwa dining Area ɗin tana Mai Washe baki tana faɗin"baku fara ci ba,?"

Hannunta dukkansu suka kalla wanda yake ɗauke da ƙaramun bowl,a Take kowannensu Ya gane inda gubar yake for sure,

    "Ai abincin nan basshi ciyiwa babu in law ɗaya tamkar da dubu kamar ki yarinyata. "

"Papa Ya faɗa yana Mai danne urge ɗin cin ƙaniyar Anisa "

    Zama tayi tana Mai faɗaɗa murmushinta tace "Allah sarki,ina Chan ina making wa Mami basise ne ,dan a al'adarmu sirika takan haɗa kir da hannunta ta kaima surukarta taci ita kaɗai."

    Karamar dariya Nadiya tayi tace "Ai kuwa bakiji yarda Yawuna ke yawo ba,ba tasting ne ,"

Yatsa Anisa ta karkaɗa tace "no wannan na mother in law ne,Kema naki yana nan zuwa Zan maki Mai daɗin gaske,yanzu dai na Mami ne,

Murmushi Nadiya tayi tana Mai ciro pin ɗin dake kanta tace "Abdallah Action,"

Tasowa Nadiya tayi kamar zata leka cikin Basise d'in,tana zuwa ta saka silver pin ɗin cikin Bowl ɗin yayin da Abdallah Ya riƙeta gam gam ,

Wani irin back kick ta bashi wanda Ya sakasa faɗawa yana Mai rike cikinsa,ciro pin ɗin Nadiya tayi ,kamar kuwa yarda tayi expecting Ya zama baƙi alamun akwai guba kenan a ciki,

Tasowa Nameer yayi yana Mai tafa Hannayensa guda biyu yace "Your game is over Anisa Idris meta ,you've come to the end of the game Ya kamata ace munyi maki rounding up tunda naga Alamu bama kisan inda zaki kai wasanki ba,"

    Cikin leda Nadiya ta saka Pin ɗin tana mai faɗin "Ai brother baka san funny abun ba shine yarda ta Zama fool gaban mu tana tunanin ita kaɗai ta iya wasa ,to ga iyayenki,kinsan dama turawa sunce two heads are better than one,idan Kina ganin ke assassin ce dake kisa anyhow ba Tare da tunanin hakkin rai ba to yau kin ɗauki mission Mai wahala dan mu da kike gani AHALINE wanda babu wanda Ya isa Ya taka mu idan har muna da goyan bayan juna,"

    Wata irin super Anisa tayi ta ɗauko table knife ta saka dai dai wuyan Mami kamar gilmawar iska,

Saka gurin tsinin tayi Akan wuyanta ta saka wata irin dariya tace"yes kun samu lago ne ta hanyar yaudara,amma sai me?"

Nasan iyanzu kunsan wacece ni sannan menene Ya kawoni gidan nan,wani babban abu da baku sani ba kuwa shine ,cikin kiftarwar ido Zan iya ƙarar da AHALIN da kuke burga akai ,duk yarda kuke tunanin wallahi na wuce nan,

Dukkan ninku ku haɗe mun a guri guda,idan ba haka ba yanzu zaku rasa tsohuwar banzan nan and i wont think twice lokacin da Zan saka wannan wuƙar cikin jijiyar nan Mai Motsi ta wuyanta and trust me bazata ƙara wani shurawa ba zata baƙunci lahira.

    Ƙokarin matsawa gurinta Papa yake cikin fushi Nadiya ta rike sa tana Mai ɗaga hannayenta sama tace "kiyi hakuri zamuyi yarda kike so,"

Alamu tayiwa su Nameer da Su matsa ,babu musu kowannensu ya matsa suka haɗu ta gurin dining a yayin da Anisa ta bawa kofar da zata sadaka da Falon Baya ,

Riƙe Mami tayi tsam tace "ina jin daɗi idan naga mutum a gabana jikinsa na rawa sai naji kamar an sakani cikin aljanna,a yanzu ma abunda nake ji kenan musamman idan na kalli wannan shegiyar yarinyar Nadiya wadda ke ganin tafi kowa ,naji kina da komai,ga kuɗi ga family Mai kyau,amma yau da kike ƙarƙashina fa ?

Sai yarda nayi daku sannan ina san ku sani dole ku zabi wanda zai mutu ko uwarku ko kuma mijin uwarku ,dan dole guda ɗaya ya mutu,

A lokacin da mahaifiyata na gadan mutuwa bata gushe ba saida ta sake jadada mun yarda imam paki da karuwarsa Umaimah suka wulaƙantata suka tozartata bayan yayi mata fyaɗe Zuri'ar gidan su suka juya mata baya suka ƙaryata ta ,suka mata korar kare a lokacin image ɗinku da reputation ɗinku yafi na kowa ko?

Ku godewa Allah ni dana tashi zuwa maku da case ɗin fyaɗe na ban bata image ɗin gidanku ba a duniya amma na b'ata na zuciyarku ".

    Dariya Mami ta saka duk da yarda take jin wuƙar a wuyanta amma bakinta bai mutu ba,cike da tsana irin ta sameera tace"banyi mamakin maganar da kika faɗa ba wadda ta fito daga bakin sameerah ,dama Ai maƙaryaciyace ,amma abunda yafi bani mamaki shine yarda tana ƙokari komawa gurin wanda Ya halicceta amma sai da ta durawa ƴarta gubar ƙaryar da ta saba ,

Bance kiji nawa ba amma inaso ki sani babu wanda yayi wa sameera fyaɗe sai dai ita da ta takurawa rayuwarmu har Allah yayi mana maganinta,"

    Danna wuƙar Anisa tayi da karfi wanda Ya saka Mami saka wata irin ƙara yayin da yaran da Papa sukayi ƙoƙarin tasowa amma kowa Ya tsaya sakamakon Tsawar da Anisa ta daka tana maiyi masu alamu da su koma su zauna inda suke,

Kama jelar gashin Mami tayi wanda akayiwa All back tace "idan bakinki Ya sake faɗin sunan mahaifiyata tabbas sai na baki mutuwar da zaki roƙeni na kasheki lokaci ɗaya ki huta,duk wani makircinki da iskancinki da kikayi a lokacin yana tafin hannuna sannan ina san ki sani lokacin ki Ya wuce yanzu namu ne ,ko ince nawa saboda hatta ita tsagerar yarinyar da kike da ita yau tana ƙarƙashin ikona saboda ina rike da weakness ɗinta,

    Cikin kwantar da hankali Nadiya tace "what on earth do you want Anisa ,Mai kike so ayi maki?"

Nuna Nadiya tayi ta wuƙar tace "Good question ,ina san mijin Umaimah babban munafukin nan Ya dawowa da Mahaifiyata budurcinta da rayuwarta da ta rasa ,idan kuma bazai iya ba sai ku zaba ko shi ko ita ,dole za'ayi ɗaya cikin biyun nan shine abunda nake so."

    Tasowa Nadiya tayi tana Dariya wadda ta ɗauki Anisa da mamaki,

Tafi Nadiya ta fara tana Mai Takowa inda Anisa take,

Nunata Anisa ta fara da yatsa tana faɗin"kar ki kuma gangancin Takowa kusa dani,"

    Murmushi Nadiya tayi tace idan nayi zaki kashe Mami ba?

To kashe ta mana indai zaki iya,

Sake danna wuƙar Anisa tayi cikin ciwan da tafara jiwa mami tace "One step Nadiya just take one step and im gonna kill this old hag.

    Kafun Anisa tayi Aune taji an kamo dukkan Hannayenta ta baya an murɗesu,

Da sauri Nadiya ta taro mami dake ƙokarin faduwa inda take Papa Ya taso yana Mai kiran sunan Mami a kidime,Kallan Abdallah yayi yace "maza Abdallah je dauko first aid box".

Da gudu Abdallah ya tafi ɗaukowa yayin da Nameer Ya saka saban hanky ɗin dake aljihunsa gurin ciwan.

    Takawa Nadiya tayi tana kallan yarda Anisa ke ƙokarin ƙwatar Kanta daga hannun ƙatti biyun da suka rukunkumeta,

Tafi Nadiya tayi Mai sound biyu a gefe ɗaya ,yayin da ta sake wani Mai sound biyu ɗin a gefe ɗaya ,matsawa tayi daf da Anisa tana Mai ɗago hab'arta da hannu ɗaya tayi wani sound na tausayi da bakin ta tace "Ya kika ga yarda nawa wasan Ya juya ,"Hannunta ta ɗaga sama tace "Allah sarki,kina tunanin zamu zauna ne Akan hannunmu ki kashe mu ki wuce sai kace wasu kaji? "

You must be a fool idan har koda sau ɗayane kin yarda da hakan,

Duk gogewarkanki baki kai karfi da girma na yan uwan taka ba.

Kuskure guda ɗaya kikayi wanda shine nuna mun ke ba mutuniyar Arziƙi bace tun farko,

Dama i had My doubts amma kikayi min Clearing a ranar da kike sake jadada mun mu agololi ne .  

    Wata irin dariya Anisa tasa tace "Kina tunanin kun ci galaba akaina ne?"

na yarda kun sameni off guard amma ku sani bazan je prison ba ,i refuse to go,ba ku san kungiyar da na fito daga ba ko,muna karkashin Strong Mafians wanda a yanzu idan nayi commiting suicide sai sunyi wiping duk zuriar ku .

    Dariya Nadiya tasa kafun tace be My guest,

Kafun Anisa ta farga Nadiya ta ɗauke ta da mari,bata bari ta fito daga shock ɗin marin ba ta ɗauketa da wani tace"wannan marin Na disrespecting Mami nane da kikayi ,ɗayan kuma na yiwa Papa sharri ne ,ƙara mata wani tayi tace"wannan kuma nayiwa Hamma na ƙazafi ne da kuma kawo yaran da baki Chanchanci kawowa duniya ba,you're a disgrace to All mothers ,sannan inaso ki sani wannan karan tunda zaki prison ta hannun mu sai na tabbata kin samu sentence na life 'in prisonment sannan Mafian da kike taƙama da Babu abunda suka isa suyi cos you've messed with the wrong people ,

Kiyi ta addua kar su bibiyeki a Chan dan yanzu haka maganarsu da kika fara anyi recording dan bada hujja akanki a kuto,

Mu haɗu a court,saseen take her out.

    Handcuff aka saka mata a hannu yayin da matar da ta saka mata handcuff ɗin ta kaɗa ƙeyarta ,

Tirjewa tayi tana Mai kallan Nadiya tace"kafun naje prison ɗin sai da na tabbata na bar maki tukuici,"Yarona Mahmood kila da dake akai DNA za'a samu Positive result ,cos ƙaninki ne wanda na samu da Ubanki Belal ta hanyar zina .

Tana kai ƙarshen maganarta ta juya ta cigaba da tafiya tana Mai kece dariya.

    Wata irin juwace ta ƙwashi Nadiya,Tana ƙokarin faɗuwa Nameer ya Tare ta,wasu irin hawaye Taji suna mata yawo a kunci ɗaya bayan ɗaya,

"Kamata Ka kaita kan kujera Nameer tayaya yazama tukuici a gurinki bayan wanda take ikirarin Ɗansa ne baki da alaƙa dashi,

Mami ta faɗa duk da tana cikin raɗaɗi.

"Haka nan taji kirjin ta yayi mata wani irin zafi bata san lokacin da ta fashe da wani irin kuka ba.

Babu wanda yace mata tayi shiru dan ko ance tayi shirun ma bayi zatayi ba ,

Haka nan ta gama batare da ta cewa kowa komai ba ta wuce ɗakinta,

A hakan nan ba Tare da kowa yace komai ba suka wuce ɗakunan su inda Mami tasaka Mai aikinsu ta ƙwanta da Mahmood tunda dama ana basa madara.

    Washe gari haka nan kowa ya tashi da abunda yake damunsa ,breakfast ma kowa daban yayi ranar,Basu suka tashi haɗuwa ba dukkansu sai Wurin 10 ,

Nadiya ne ta fara magana inda take cewa"Mami saseen yace ankai maganar Anisa court amma yanzu tana kulle gobe idan Allah ya kaimu za'ayi Zama ,babu wani Complication Za'a Yanke Mata Hukunci Tunda Akwai Evidence Sosai Da Yake Pointing Kanta ,

    Mami takama hannunta tace "kar ki damu Nadiya ,babu abunda Ya haɗa ki da bilal kar ki ɗorawa kanki damuwar Abunda Anisa ta faɗa maki,and jibi nida Nameer da Abdallah da Papanki zamu kai mahmood gidansu gurin mahaifinsa"

    Kukan da take dannewa ne Ya ƙwace mata tace "Mami still jininsa ke yawo a jikina ,shine yayi silar kawoni duniya,im pretending kamar komai is okay amma Its not cos a kullum idan na tuna jininsa ke yawo jikina sai naji kamar na buɗe jikina na kwashe jininsa,"

And mami ki kalli Mahmood fa,yaro ne bai masan komai ba a duniya ,ki kalla ta hanyar da aka samesa,uwa bata gari ba haka zalika uba,har gwanda ni Zan daki kirji nayi alfahari da samun uwa kamar ki,

Kamo hannun Mami tayi idanunta na zubar hawaye tace "Mami 'dan Allah kar ki maidawa Bilal mahmood ,yaran abun tausayi ne ,koda za'a basa shi ba yanzu ba,dan Allah mami nasan da wuya amma ki taimaka ki bawa ƙanina mahaifiya ta gari da baya dashi. ,"

    Shiru Mami tayi tana kallan Nadiya yayin da zuciyarta ta karaya sosai,

Hannunta da taji Papa Ya dafa ne yasaka ɗagowa ta kallesa,

Cikin kwantar mata da hankali yace"maganar da Nadiya ta faɗa abun a duba ne ,ni kaina tun jiya da maganar na ƙwana ,we can adopt him kamar Yarda Nadiya ta faɗa gidan Bilal ba gurin da innocent yaro kamar mahmood zai tashi bane,na tabbata we can give him a Good life.,"

    Ƙwallace ta ciko idanun Mami tana Mai kallansa tace "ka karbi yarana wanda Bakai ka haifesu ba amma ka basu uba ,baka tab'a nunawa koda sau ɗaya ba Akan ba naka bane sannan yanzu zaka karbi Yaran mijina wanda ni kaina bana da alaƙa dashi,Shin wane irin zuciya ne da kai,?

Why are you this kind?"

    Cikin kwantar mata da hankali yace"kar ki damu matata,idan baya da Alaƙa dake yana da alaƙa da Nadiya sannan kar ki manta Nadiya na ɗaya daga cikin yara mafi soyuwa a zuciyata ,sannan shi ɗa Ai na kowane kika san wanda zai mana rana,kar ki damu Daga yau Mahmood Ya Zama ɗaya daga cikin AHALINMU ,insha Allahu zamu basa kulawa kamar yarda zamu bawa namu."  

    Cikin kuka Nadiya ta rungumesa tana mai faɗin"Allah ya baka Aljanna mafificiya Papa,kai babban mutum ne Mai babbar zuciya ,Allah Ya kula  maka da zuriar ka ko bayan babu kai."

    Sallamar da akayice ta katse masu hanzarinsu,

A tare baki ɗayansu suka kalli ƙofar ,Baba maigadi ne Ya shigo,

Abdallah ne yace "barka Baba lafiya dai ko?"

    "Wata lafiyarce ta ƙaraso ɗaga cameroon."

CHUCHUJAY ✍🏽

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top