x13&14

https://chat.whatsapp.com/DgTUlodRcp2AHM4rmfKTqK

     AHALINA

(Siblings of different father's)

Book 2 of Aure uku series.

              BY

CHUCHUJAY.

EPISODE 1⃣3⃣➡1⃣4⃣

Shigo da Evan Nadiya tayi tana Mai welcoming ɗinsa kamar ba baƙo ba,

Da gudu Arifullah Ya tako gaban su yana Mai rungume Evan sosai yace "Im a big Fan sir,please picture and your Autograph a pouch ɗin na ,da gudu ya shiga cikin ya haura sama yana Mai faɗin,just give a moment sir,

Murmushi yayi yace "i like him,"

Zama yayi a kan kujera yace "why do you ask me to come here,?

Yana nufin Na ƙarbu?

Dining Area ta nufa taga komai anyi arranging ɗinsa ,kallansa tayi tace "i dont like eating outside and yanzu maganar da nake maka 'im famished so ka taso kazo kaci abinci then ko mene zamuyi magana later,

Kafun yace wani Abu Arifullah Ya sauko da gudu yana mai faɗin Evan sir im here.

Murmushi Evan yayi Ya ƙarbi wayar hannunsa da permanent marker ɗin da Ya ɗauko ya saka EH,

Sannan Ya kalli Nadiya dake zaune tana kallansu yace "ki mana hoto mana."

Sakin baki Arifullah yayi yace "Adda Hausa fa yayi,innalillahi For real?"

Dariya Evan ya saka Ya jawo sa yace "ina jin hausa mana ,amma im looking forward na koyi more a gurinka,.

Tafa hannu Arifullah yayi yace"God im Happy,Adda wallahi sosai,zo ki mana hoto,."

Tasowa Nadiya tayi tamusu hoto kana tace "oya Kama gabanka,

Cike da murna Ya fita yana Mai Faɗin Thank you sir.

Dariya Nadiya tasaka tace"celebrity life"

Juyawa tayi 'dan komawa kan dining ,batayi Aune ba taji Ya kamo hannunta ya jawo ta,

Daf suke da juna har suna jiyo numfashin juna,

Saurin Hankaɗesa tayi ta juya tana Mai sauke ajiyar zuciya kana ta haura kan dining step tana Mai jin zuciyarta na mata wani irin lugude ,

Smirking yayi Ya haura shima yana Mai jawo kujerar dake kallanta Ya zauna,

Plate ta jawo tafara serving ma kanta chicken Basmati rice d'in da taji Haɗi ,Salad ta jawo ta zuba a gefe kana ta kallesa tace "Stop being touchy with me,kar ka sake gwada abunda kayi dani.

    Ajiyar zuciya yayi yace "Im sorry,bazan sake ba,i just cant help it,i love you so much to the extent that nake san na jiki kullum a kusa dani and at least ko hannunki na riƙe i feel content.

Ƙaramun murmushi tayi tana jin kanta yana wani irin girma ".

Plate ta jawo tana zuba masa tace "idan Ya isa kayi magana,"

Bayan ta gama zuba masa komai ta tura masa plate ɗin a hankali tace"How much do know about My religion?"

    Rufe idanunsa yayi yana addua kafin yiyi crossing a jikinsa Ya ɗauko spoon yayi lomar farko yayi chewing a hankali,kana yace"its delicious ,"

Cigaba tayi daci tana Mai yi masa murmushi tace "enjoy yourself "ba tare da ta damu da ƙin amsa mata tabayanta da yayi ba Tunda tasan muddin yana san cigaba da tarayya da ita dole makamanciyar tambayar nan ta shiga tsakaninsu,duk da kuwa tama san Alaƙar ba lallai ta kaisu inda zuciyar ta ke san kaita ba,na farko dai Addininta bai yarje mata Ahlul kitabi ba muddin bai karbi musulunci ba wanda bata ganin Evan cikin sahun masu ƙarba saboda a addininsa Ya shahara,mutum ne shi Mai san Addinin sa a yarda ta lura,

    Bayan sun gama cin abinci ta kalli lokaci wurin taƙwas na dare 'dan ma Allah yasa ba sallah take ba amma tana bukatar washing up,

Yana zaune suna kan hira da Arifullah tayi excusing kanta 'dan zuwa ganawa da Auntynta ,

A falon sama ta tarar da ita tana danna wayan ta,

Zama tayi gefenta tace"Aunty kina hutawa ke kaɗai kenan"

    Murmushi tayi tana Mai aje wayan tace "to Ya zanyi ,Mai taya ni hirar ma yau Ya gudu ga dadynsa da gida sai Next week kinga kuwa Ya zama dole na zauna ni kaɗai,house help ma nake tunanin dauka tunda Allah yayi Arif ne kaɗai har yanzu.

    So let talk about it ,ina kika samu Guy ɗin nan and i hope you're not engage with him romantically?

Ɗan shiru Nadiya tayi kafin tace "Aunt just pray for me and insha Allahu bazan yi abunda zai baku kunya ba,Nasan cewa tsakani na dashi a addinina haramun ne,insha Allahu zan kiyaye ."

    Ajiyan zuciya Aunty shatuh ta sauke tace "Allah yasa cos kinsan irin waɗannan mutanen kaiɗinsu yana da yawa musamman ,ba wuya zasuma yarinya wayau,"

Dariya Nadiya ta saka jin abunda tace,inda ta sake assuring dinta babu wata damuwa ,

Sai bayan zasu tafi ne ta sauko suka gaisa da Evan wanda ko a fuska bata nuna masa wani abu ba.

    Bayan fitarsu waving masa hannu tayi ta nufi motarta ,

Tana shiga shima Ya bita Ya zauna a kujerar Mai zaman banza,

Kallansa tayi tace "baka gaji da gani na ba kenan,?"

Hannunsa ya ɗaga kamar zai tab'a mata fuska sai kuma ya fasa yana Mai tuna kashedin ta,

Murza sarƙar wuyansa yayi yace "naji daɗi da kika bani dama naga mutanenki,it really means alot to me and bazan daina hoping akanki ba"

    Dubansa tayi tana Mai zaman da zai kallesa kana tace"wa Ya koya maka hausa?"

And for your information wannan mutanen nawa is My Aunt not My birth mother.

"I learned hausa 'in Ghana so dole kijishi weird attimes and it doesnt matter idan Aunt dinki Nagani ,watarana zanga mom ɗinmu"

Yafaɗa yana Mai saka serious face kafin Ya ƙara da"dazu you asked me yanayin abunda na sani a addininki,well Bansan komai ba,abu ɗaya na sani wanda shine ina san Ɗaya daga cikin Addinin nan,"

Dafa saitin zuciyar sa yayi yana Mai kallanta cikin ido yace "zan mutu idan baki zama tawa ba Nadiya i mean it,idan ina duniya na ga kina ciki kika zama iyalin wani zan kashe kaina nima na huta cos i can't handle it ,so just tell me maine zanyi na sameki ki zama tawa ,komai kika ce na daina Zan daina ,idan hannunki ne baki so na tab'a bazan sake ba sai da yardarki,

I want to marry You please .

    Kwallar da ta zubo daga idanunsa itace babban Abunda ya ɗagawa Nadiya Hankali,

Tabbas soyayyar da yake ikirarin yana mata tana neman jefata cikin ruɗani,

Tayaya zai mata irin wannan san da yake nunawa a fuskarsa bayan a saninta zaiyyi wuya Christian namiji yaji yanawa yarinya mace Musulma soyayya a matsayin mace da namiji,

Ita dai tasan Yarda Allah bai musu lamani ba hakazalika iyayensu bazasu taba masu lamani ba,

Babban tashin hankalin ta kuma ɗaya ne ba biyu ba yarda take jin zuciyarta nayi masa duka tana Mai jin tsantsan sansa a cikin ko wanne lungu na jikinta,

Shin ina zata kai wannan baƙon Al'amarin da tasan babu inda zai kaita sai wahala saboda tasan koda sun gina soyayya Akan tafarkin da suke yanzu a ƙarya zata ƙare domin yaudarace kawai suke gwadawa kansu.

    Rumtse idanunta tayi tana Mai san kamo al'amarin dake gabanta tayi masa tufka,

Kallansa tayi da kyau taga yana mata kallo irin na marairaicewar nan ,take taji Ya bata tausayi,

Hannunsa da Ya haɗe guri ɗaya gudun kar Ya tab'ata ta kamo ta rike cikin nata tace "Evan akwai wani Fence dake tsakanina da kai wanda munaji muna gani dole bamu isa mu rushe sa ba,"i Feel something towards you i wont deny it,amma nafi jingina sa da Attraction ɗin da bazai tab'a cika ba,"

We have different religion ,Culture,beliefs da bazai tab'a barinmu tare ba,bazan iya Aurenka ba not because Bana sanka sai dai 'dan Addinina bai yarda na Aure ka ba muddin baka musulunta ba,

Sannan ni bazan boye maka ba,"i will never convert to Christianity dan mutanenka su karb'eni ,bazan iya ba,wanda nasan kaima bazaka iya barin Addininka ba,so im begging you,dan mu yiwa kanmu katanga da heart break lets end every desire we have towards each other ,and banyi worthing kayi commiting suicide saboda ni ba,i know a Addininka ma haramun ne so please kar ka sake faɗan haka,

And yes i suggest we be frnds With No string attached ,i promise zaka samu wadda tafini, i know it ,

You're handsome,rich,And kind. "

    A hankali Ya zare hanunsa daga riƙon da tayi masa,

Kallanta yayi da wani irin yanayi na rashin jin daɗin conversation ɗin da ya shiga tsakaninsu kafun yace "Good night cikin sassanyar murya kafin ya buɗe mota Ya shiga nasa,"

A yanayin yarda Ya figi motan ta san zuciyarsa babu daɗi,

Ajiyan zuciya tayi tana Mai karawa kanta ƙwarin gwiwa Akan abunda tayi shine dai dai.

  *

     Zaune take Akan gadonta daure da towel a kirjinta hannunta dauke da wayarta,

Basai ta faɗa maka ba kasan daga wanka ta fito,tashi tayi ta nufi walk 'in closet dinta 'dan shiryawa,

Turus tayi lokacin da ta fito taga Aneesa zaune bakin gadon ta,

Ƙaramun tsaki tayi tace "lafiya?"

Mai kike mun a ɗaki.

Kallanta Anisa tayi daga sama zuwa ƙasa kana tace ,ɗakin ki?

Taƙama 'fa kike da gaibu domin ko yanzu Mai gidan nan Ya faɗi Ya mutu baku da gadon ko tsinke Ya kamata kiyiwa kanki faɗa ki nemo miji kiyi Aure ba ki ɗauki wani katon Arne ba ki kai gidan Auntynku,dan na tabbata sai dai s*x ɗin wadda nasan ita yake binki domin,

Da mamaki Nadiya tace "stalking ɗina kika fara?"

Kallanta tayi daga sama har kasa cikin yar karamar rigar baccin dake jikinta kafin ta kara da cewa"zaki iya sakawa a haka idan hakan yayi maki,jikinki kam Mai kyau,dama Mai za'ayi expecting gurin model,jiki kam zai kyau amma bamu da tabbacin HQ ɗinsu cos gurine da ake rabawa ko wanne kazami 'dan  a samu connection,gashi kuma Alhamdulillah kinsamu cos Agency ɗinki har Abroad kinga HQ ya Biya,i just hope a jiƙe yake,idan kuma abushe kike akwai wata ƙwata Mai kayan mata plug zata taimaka maki,Ni kaina idan nasha maganinta ihun da yayanki yake Ya isheki zama wet,".

    Ba tare da Nadiya tace wani abu ba ta koma koma walk 'in closet dinta ta ɗauko belt dan Baki bazai isheta tayiwa Anisa abunda take san mata ba sai dai belt ɗin,

Tana fitowa kafin Anisa ta farga ta fara buga mata karfen belt d'in,

A razane Anisa ta miƙe ta kama bakin belt ɗin ta rike gam gam,

Kokawa suka fara wanda ta Nan Nadiya ta fahimci Anisa is trained ganin yarda take binta ta hanyoyi da dama 'dan ganin ta mata illa,to itama ɗin ta san hanyoyi na self defence 'dan haka Ta Shiga kare kanta inda Allah Ya bata dama ta buga kan Anisa A bango wadda ta faɗi a sume,

Tsaki tayi da ta tabbatar suma tayi ta jata wajen dakinta ta ɗauko jug d'in ruwan da take ajjewa gefen gadonta saboda tashin dare ta sheƙa mata jikinta,

Sai da ta bari ta farfaɗo tace"Gobe idan kika ƙara shigo mun ɗaki sai naci uwarki,sannan ki fara lissafin ƙwanakin da suka rage maki gidan nan,karuwar banza yar iska kawai."

    Tana kai karshen maganarta ta bugo kofa ,zama tayi tana Mai mayar da ajiyar zuciya tana Mai sake tariyo ƙarfin da taji tattare da Anisa,Shin wacece wannan yarinyar?

Ƙarar da wayarta yayi ne Ya dawo da ita daga duniyar da ta shiga na tunanin wacece Anisa ,

Sako ne Ya shigo mata ta Email,da saurinta ta shiga jikinta na bata abun Alheri ne,ille kuwa tana shiga Biodata ɗin Anisa ne harda hotonta,

Suna:Suwaiba (Aneesah) Idris meta.

Ƙasa:Nigeria

Gari:Niger state'

Sunan Mahaifi:Idris meta

Sunan Mahaifiya:Sameera Idris Meta.

Aiki:Gungur Assassin trained for four years/killed 25 people /once a stripper in Custo Club Newyork.

Riƙe baki Nadiya tayi maganar Fawzan na dawo mata da yake faɗin yasanta  a New york ne wanda ta tabbata akwai more about yarinyar nan,

Tabbas yanzu ta fahimci daga inda karfin Anisa yake ,

To ko menene zai kawo Assassin gidansu?

Saurin dialing numbern gayen da ya tura mata Info d'in tayi,

Yana ɗauka tace "why is this girl moving the world freely When she killed 25 ,for God sake 25 people ,like nothing happened?."

Daga ɗaya bangaren yace:ma'am kungiyar da suke ƙarkashinta kungiyace da take Active for 20 years kenan wadda nake tunanin akwai manya dake ɗaukar nauyinsu wanda im sure shine dalilin da Ya saka take waje har yanzu,amma ma'am abunda nake san ki sani shine she's dangerous beyond tunaninki,just be careful sannan har yanzu muna kan bincike Akan dalilin zuwanta Nan gidan ,idan ma dai anyi hayarta ne our team is capable zamu gano dalili.

Ajiyar zuciya tayi tace "thank you very much ,Zan wiring naka sauran payment ɗinku and i will be expecting you,"

Hanging wayan tayi tana Mai cizan yatsanta tana tunanin yarda zata bullowa al'amarin.



CHUCHUJAY ✍🏽
Follow My whatapp channel
https://whatsapp.com/channel/0029Va9RLKT2P59fHSa7Ia1j

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top