x11&12

AHALINA

(Siblings of different father's)

Book two 'in Aure uku series

           By

Chuchujay

EPISODE 1⃣1⃣▶1⃣2⃣

   Tun Daga soron gidan kake jin shesheƙar kukan Hafsa wadda tayi sa har ta gaji,

Rarrafawa tayi dai dai ƙafar  Mama Laure tace"Mama 'dan Allah kiyi mun rai kiyi hakuri,wallahi bazan iya Auren Idi mai faskare ba wallahi 'dan iska ne ,babu irin lalatar da baya yiwa yara duk da tsufansa ,ki tausaya mun ,bani ba hatta babana Ya haifa ,'dan Allah kar ki bari rayuwata ta lalace kamar yarda bazaki so ta hasiya ta lalace ba kiyi mun rai 'dan Allah,Baba ka saka baki,"

Ta ƙarasa maganar tana Mai mayar da kallanta gurin mahaifinta wanda yayi saurin ɗauke kai,

Sake maido da ture kaga tsiya ɗin dake kanta tayi tace"lalai ma yarinyar nan,zakiyi ki gama ki gaji kiyi shiru ,'dan Idi ne sai kin Aura,dama mene kuke wa ke da ubanki,Karatu ko,sannan baku san tallah,shine nayi maki gata ,ga Aure nan Zan maki sannan babu ruwan Idi da karatunki, ke dai kawai ki buɗe masa kafa yayi maki ciki ki haihu,shine amfaninki,sannan na faɗa maki ba lusarin ubanki ba,idan duniyar nan ce zata hadu baki daya babu wanda Ya isa Ya hana na Aura maki idi nan da sati Mai zuwa ,

Tashi tayi a gurin tana Mai faɗin "ni kinga ma fita zanyi hasiya zata fitar mun da hura ,ke kuma ki ɗora tuwo, ".

    Da sauri hasiya ta ɗauko bokitin hurar tana Mai fadin dole nayi ma amaryar malam idi wannan karar ,

Suna fita ta koma tayi zaman dirshan tana kuka,bayan wasu lokuta Malam balarabe Ya tashi yayi hanyar zaure ,bayan mintuna Kaɗan Ya dawo gida yana Mai saka masa sakata ,

Ɗagota yayi yace "bari kukan nan haka Ɗiyata ,banyi lalacewar da za'a Aura maki malam idi ba,maza tashi kije dakinku ki haɗo kayanki da komai na amfaninki,"

Kamar wadda bata fahimci abunda yake nufi ba ta miƙe ta shiga ɗakin ta haɗo yan irgaggun karanta cikin tsohuwar jakar saka kayanta ,

A tsakar gida ta tarar da mahaifinta da jakar kuɗi ƙarama Mai Ɗauke da kuɗaɗe ciki,sai wani abu cikin leda a kulle, miƙa mata yayi yace "wannan kuɗin gashi nan zai isheki wani abun ,sannan karatun ki idan Kinje chan kya ɗora ,ledar dake riƙe hannunsa Ya saka cikin kuɗin yace ,wannan ledar zinaren mahaifiyarki ne a ciki wanda ta mutu ta bar miki nake ta maki ajiya ina san sai kinyi Aure na baki,

Cikin shesheƙar kuka tace "baba ina zanje na barka ,."

Shafa kanta yayi yace Hafsatu babu abunda zai sameni, ke dai yanzu ki tafi ,kije ki zama wadda zanyi Alfahari da,sannan ki riƙe mutuncinki kar kiga 'dan bana nan mahaifiyarki bata nan kiyi tunanin Allah baya nan,

Yana nan yana ganinki duk wani abu da zakiyi mara kyau,

Nayi magana da Inna ta Adama jiya wadda na sanar mata da zuwan ki ,tana nan Adamawa Unguwar dawa"

Kije chan Zan na kiran ku a boye a waya ina jin yakike,

Kuka ta saka sosai tana Mai tunanin tafiya tabar Mahaifinta,

Hannunta ya Kama yace "kar ki damu ,muje da kaina zan kaiki tasha na sakaki a mota ki tafi,ƙaramar wayarsa Ya bata yace gashi nan da layina ciki Zan kiraki,"

    Cikin kuka tace "Baba dame zaka kirani idan na karbi wayarka,?"

Shafa kanta yayi yace"kar ki damu Hafsatu na zan kiraki ke dai,gaba Ya sakata suka nufi tasha A sace da jakarta cikin hijab.

    ***********************************

    Bayan dawowar Nadiya daga Abuja kai tsaye Abdallah ta kira inda Ya ke shaida Mata yana Office dinsa,

Kai tsaye ta nufi office ɗin nasa 'dan gana wa dashi cos dole maganar nan tayi da wani wanda tasan wani ɗin nan ba kowa bane face Abdallah,

Shine kaɗai zai bata shawarar mai zatayi ,yaya zatayi,

Tana shiga office dinsa ta samu guri ta zauna tana Mai yin ajiyar zuciya,

Kallanta yayi yace"Addyna a kawo maki abun shane mai ɗan sanyi?"

Kaɗa kai tayi tace "malt please,"

Intercom Ya kira wanda Babu daukar lokaci Mai tsayi aka kawo mata ,

Bayan ta sha Mai isarta ta aje tace "Abdallah guess What?

Cike da ƙaguwa yace "What ,just tell me ,"

Cike da damuwa tace "wai kasan Hamma yayi aure a china babu wanda Ya faɗawa ,i mean it seems kamar bet ,like sun dauki abun wasa,"

Ƙaramun dariya yayi yana Mai gyara tie ɗin wuyansa yace "bari wasa mana ,badai hamma ba ,ni ina da yaƙinin cewa Hamma bazaiyyi abu makamancin wannan ba,

Wayarta ta jawo ta kunna masa recording ɗin tayi tace "listen ,nasan duk sauran Abinda Ya faɗa ƙarya yake ,amma maganar Aure 'fa akwai sa cos da kunnena naji abokinsa Fadil yayi maganar Auren ,amma who is this Fadil?

Yakamata mu nemosa duk inda yake shi kaɗai zai iya Clearing mana Air ɗin nan."

    Shiru Abdallah yayi bayan ya gama saurara yace "indai Fadil ne kike magana Akai wanda na sani to akwai kishin kishin na ƙamshin gaskiya a maganar Auren ,amma yazo da sauki indai Fadil da nasani ne yana garin nan cos sun fara aiki tare da hamma,."

Tashi Nadiya tayi tace "please Abdallah kayi abunda zamu hadu dashi ba tare da sanin hamma ba ,Ya kamata muyi magana dashi musan menene gaskiya ASAP please,

Cos ina jin dole tafiya cameroon Ya kamani ,dole musan wacece wannan Jamaimah ɗin,

    Wasa da Pen Abdallah keyi da hannunsa kana yace "kar ki damu gobe Zan san yarda za'ayi mugansa,sannan for your information jiya da Mami ta je da sameera gidan iyayenta an ɗaurowa Hamma Aure da ita, "

    Komawa tayi tace "Dont tell me this,"

Fuskar damuwa yasa yace "Im telling you Adda,ɗazu da safe har grandpa ya kira meeting duka anje harda Ummu da Abbi,

Allah sarki Nana,har na hango tana da rai akayi abunnan,sai mun ɗora hannu akai munce wayyo Allah,nasan cikin three years ɗin nan da bata kowa na missing ɗinta".

    Dariya Nadiya tasaka for  a moment da yayi maganar Nana,sai da tayi Mai isarta tace "muna cikin damuwa Nana ta saka mu dariya,babu abunda nake tunawa sai tsallen ƙwadin da tafara lokacin da Abbi yayi tafiya Ya dawo tace "Su Fauza suka sakata saboda kawai mami ta  bata wahala da cikinsu ,bata san idan zaka gina ramin ƙeta ka gina sa kaɗan ƙwananta biyar bata takawa ,su kuma babu abunda aka musu,sun dai sha zagi,

Kai Allah dai ka jiƙan Nana kayi mata rahma,banji mutuwar ƙaƙanin Mami ba kamar yarda naji na Nana.

Dariya suka sake sakawa a tare suna masu tuna moments ɗin su da ita ,suna dai shan gori da kiran su Agololin gidan imamu.

     A magana ɗaya suka tsaya na ganin Fadil Washe gari,Sannan koda an ɗaura Aure da Anisa ai baƙaramun abu bane tsinkesa,

Kallan Agogo Nadiya tayi taga har magreeb Ya kusa,

Ɗan Cije lebenta tayi tana Mai dialing numbern da Evan Ya kirata dashi,

Har yayi ringing biyu bai ɗauka ba,ajiyan zuciya tayi tace "i know bazai ɗauka ba wanda ke faɗa mun yayi fushi,ɗaga kafadun ta tayi tace "its okay"

Tana ƙokarin tada motan ta kiransa yana shigo mata,tsintar kanta tayi da murmusawa kafun ta ɗauko wayan tana Mai Clearing Voice ɗin ta tace" hello"

Ɗan shiru yayi daga ɗayan bangaren kana yace "i miss you"

Ɗan sauke wayan tayi daga kunnenta kafun ta yi ƴar ƙaramar dariya sanann ta mayar tace"im Sorry i left you waiting ,i had an emergency that needed My attention ,"

    Murmushi yayi kamar tana kallansa kana yace "i don't mind waiting for you My whole life,but How are You going to make it up for me,Dinner?"

Dan shiru tayi kafun tace "kana ina?"

#Saint guest palace,will you come over?

Ya tambaya.

    Ɗan ƙaramin murmushi tayi tace "that sound tempting But no,i will send you a location ,if you're okay with it and... "

Kafin ta sake wata maganar yace"Right away my princess ,kashe wayan tayi tana Mai jin wani irin sanyi aranta ,kamar ba itace ke Ɗauke da damuwar ɗazu ba,she had a hectic day and yes she's hungry kuma homemade food take sanci amma tasan last kuskuren da zatayi a yanzu dai shine kai Evan gida ,cos Yau mami yarda take saman nan ta shiga uku idan ta ɗora idanunta akansa ,musamma ta hango sarƙar wuyansa ,ta kaɗe har ganyenta,'dan tsaf a yanayin nan ma Mami zatace ta fita daga addinin musulunci.

    Wani idea Ya faɗo mata inda Babu wata wata ta tura masa location ,tana tura masa tayi dialing Number a wayanta,ringing ɗaya aka ɗauka,

Marairaicewa tayi kamar wadda ta kira ɗin tana kallansa tace "favourite Aunty i miss you,"

Daga ɗayan bangaren favourite Aunty tace "Nadiya maike tafe dake just say it ba sai kin gwada min yaudara ba,"

Dariya ta saka tace "Aunty Shatuh ɗan Allah baƙo zanyi and nayi missing ɗanɗanon Abincinki ɗinnan Mai daɗin tsiya ,shi nake ma baƙona kwaɗayi,"

    Cikin sigar tsokana tace"Ko dai ko dai sirikina ne ,"

Cike da kunya tace"kai Aunty ,ni dai gani nan zuwa,"

Kashe wayan tayi tana Mai murmusawa tace "i will give you a shock Maybe,"

    Bayan isarta gidan tana ƙokarin fita a motanta Ya kirata Ya shaida mata zuwansa,

Fita tayi domin shiga dashi,suna ƙokarin shiga yaranta Arifullah mai shekara sha taƙwas na ƙokarin fitowa ,yana ganin Nadiya Ya faɗa jikinta yana faɗin,Sissy ,rungumesa tayi itama tana Mai tayasa murnar cos ta ƙwana biyu bata sashi ido ba ,

Bayan sun saki juna ne Ya maida kallansa bayanta inda Evan yayi waving nasa yace "Hey handsome".

Sakaƙe Arif yayi yana kallansa Kafun yayi ƴar ƙaramar dariya yace"Adda kin ganni da wani imagination ko?

Da ace Bansan Evan Hans ɗan Ghana bane sai nace Ya akayi kika kawosa gidan mu ,amma nasan babu ma yarda za'ayi wannan Ya zama Evan,amma wallahi kamar su is over 'dan ma bai saka sarƙan ...

Shiru kuma yayi bai ƙarasa zancen ba lokacin da idanunsa suka sauka kan sarƙan wuyan Evan,

Da mamaki Ya buɗe idanunsa kafin Ya koma cikin gidan da gudu,

Murmushi Evan yayi yana Mai Faɗin i like him,

Kaɗa kai Nadiya tayi tace he's cute Bari na sanar dasu zuwanka then na kaika ciki,

Babu musu yayi mata murmushi yace "Im waiting."

Shiga ciki tayi taga Arif bakin Ƙatotuwar TV ɗin dake falonsu wadda ke haska wani film ɗin Evan,Do or Die,

Da mamakinsa Ya kalli Mamansa da Ya ƙwalama kira tafito yace "Wallahi Mama Evan Adda Nadiya tazo dashi gidannan,wannan na cikin film ɗin ,wallahi Mama shine ,ga sarƙar nan da komai,kuma a zahiri ma yafi kyau."

Kallan Nadiya Aunty shatuh tayi tace "Mai yake damun ƙanin nan naki ke ,i hope we are safe ,and wane wani Evan ,mene zai haɗasa da Nadiya ,kai dai da ka sansu kake kallansu kamar ibada kenan ".

    Dan ƙasa da kai Nadiya tayi tace "Aunty shine and muna tare nace bari na sanar dake zuwan sa"

Da mamaki Aunty shatuh ke kallanta ,kafun tace ,kije ki shigo dashi ɗin ,and abincin ku is ready cos dama yau fav ɗinki na dafa Allah yayi ku zakuci,bari ni na je sama and idan kun gama muna da magana Mai kyau cos nayi imani da Allah Adda ma bata san kunzo nan ba.

Nasan short chapter ne ,kuyi manage ,yafi babu😀

CHUCHUJAY ✍🏽

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top