Finale
AHALINA
(Siblings of different fathers)
Book two in Aure uku series
By
CHUCHUJAY ✍️
FINALE
Baki ɗaya kwanciyar Hankalin da suke nema sun samu domin kuwa kowa a gidansa idan ka kalla suna zaune ne cikin zaman lafiya mai daɗi,
Idan kana kallan rayuwarsu bazakace akwai wani abu behind it ba karma ace yarda Haɗin kai na AHALIN yake, idan ba wai an faɗa maka ba bazaka taba cewa wai yaran Umaimah Shida kowa da ubansa ba,AURE UKU da tayi ta yarda babu daɗi amma ta gamsu da cewa duk wani abu da ubangiji 'ya tsara maka shine gaskiya,babu wani abu bayansa sannan baya taba ɗora maka abu wanda yafi ƙarfin kanka,sannan every failure' is a blessing domin kuwa mutanen da suke jiran ganin failure' na Aurenta sunfi masu fatan ya ɗore.
Taro ne suka tsantsara na Family bayan Wata guda da Auren Su Nadiya duba da yanayi na kowa zai tafi,Yan uku zasu koma makaranta Abdallah kuma da matarsa Adamawa domin Gaida iyayen Hafsa daga nan kuma zasu wuce mecca domin Aikinsa yayin da Nameer Baba Bulama ya yanke masu ranar zuwa Cameron wanda tafiyace yake san suyi baki ɗaya domin kwantarwa da iyayen Jamaimah hankali akan tana cikin hannu mai kyau,ille kuwa ranar saturday da 'ya zamana weekend suka dugunzum wajen tafiya masarautar.
Tun da jirginsu 'ya tashi kirjin Jamaimah ke dukan tara tara wanda Nameer 'ya kula da yanayinta,cike da kulawa 'ya kama hannunta yana mai shafa hannunta a hankali cikin sigar lallashi,ajiyar zuciya tayi tace "babe im scared bansan 'ta inda xan fara da iyayena ba,sake rubbing hannunta yayi yace komai zai daidaita ,insha Allahu babu wata babbar matsala,kar ki manta da Gradnpa Bulama a wannan tafiyar da Abuh da Papa da Mami da ummuh ga nan su Abdallah, su kansu zasu san guduwanki mai amfani ne after all ga ɗan Abbah a ciki ,
Tsintar kanta tayi da murmusawa tana mai faɗin"stop joking a moment ɗin nan abunda nayi musu ba dai dai bane ba".
Kaɗa kai yayi yace"na gamsu ba dai dai bane ba amma Abun daɗine da 'ya zamana kin dakatar dasu daga aikata ba dai dai ba domin kuwa da kin zauna zasuyi miki Aure ne wanda haramun ne saboda kina da Aurena wanda koda babu iyayen mu halsataccene duk da wata mazhabar kance babu aynayin waliyyai bai hallarta ba amma a musulunce munsan ya hallarta tunda an shaida kin karbi sadaki an daura wanda dama Aure shaidu yake buƙata ,dan haka ki kwantar da hankalinki komai zaizo da sauki da ikon Allah."
A haka Nameer 'ya ringa assuring Jamaimah har suka isa kasar,already dama kafun isar su Granpa Bulama ya saka an sanar da sarki RAIS maganar zuwansa ta hanyar connection,duk da babu abunda 'ya taba haɗasu amma mahaifin Jamaimah ya saka aka shirya tarbasu tunda shi din sanannan mutum ne wanda zuwansa gurin mutum bazai taba zama sharri ba ,
Koda suka iso sarkin da kansa 'ya Aika a daukosa a airport',kallan Jamaimah kawai Drivern da aka aika 'ya ɗaukosun yake dan bazai taba manta fuskarta ba duk da kuwa baƙone shi,fuskarta tayi mutuƙar yawo domin mahaifinta lokacin batanta 'ya saka Milliyan biyu a kuɗin Nigeria ga duk wanda 'ya kawota,kasar ta dauki kara akan wannan offer da sarki rais 'ya bada hakazalika matasa sukayi chaa wajen neman Jamaimah , tashin hankali kuwa babu irin wanda harith bai shiga ba domin wannan gangancin shi Jamaimah tayiwa dan haka har a ranar bai daina nemanta ba a duk inda tunaninsa 'ya kai masa zataje,karshe kuwa da yayi yinkurin kashe Sarki Aka ɗauresa.
Koda suka isa masarautar babban sashen dake daukar baki akayi dasu,gurin 'ya gaji da haɗuwa da girma ,kafun isowarsu kuwa makil aka cika ɗakin da kayan cima na alfarma domin tarbar su,basu dade da zuwa ba sarkin 'ya bayyana domin girmama bakin nasa,fadawa suka fara shigowa kana Sarki Rais a baya,
Koda ya shigo idanunsa basu sauka akan kowa ba sai batacciyar ɗiyarsa,wani irin abune 'ya daki zuciyarsa wanda bazai iya fasalta menene ba domin kuwa yanayin rabon sa dashi tun lokacin da aka sanar masa da sarauniyarsa ta haifi Jamaimah,
Take ruwa 'ya kawo a idanunsa,a hankali Jamaimah ta tashi ta nufi garesa tana mai fashewa da kuka,ganin haka yasa fadawan darewa domin basu guri,kan gwiwowinta ta zube tasaka kuka sosai,saurin goge ƙwallar dake kokarin kunyatasa yayi ya duƙa 'ya Kamota 'ya rungumeta,kafun kace mene Mahaifiyarta tazo gurin wadda tun tafiyar Jamaimah bata kuma lafiya ba amma da labarin Zuwan Jamaimah ta risketa Babu shiri ta taso tazo,tana kuwa shigowa bata ma kula da mutanen dake gurin ba tace"yarinyata,jin muryar ta yasa Jamaimah raba jikinta dana mahaifinta ta nufeta tana mai faɗin "Uwata"
Wani irin kuka mahaifiyar tata ta saka kana ta rungumeta,
Kafun kace mene maganar dawowar Jamaimah ya zagaye gari kamar bonfire.
Zama sukayi domin tattaunawa da sakewa iyalan Bulama godiya domin kuwa dawo musu da Jamaimah da sukayi yafi masu masarautarsu da abunda ke cikinta.
Cike da nutsuwa Grandpa Bulama 'yayi musu bayanin duk wani abu da 'ya faru kama daga Auresu a china har izuwa zuwanta NIGERIA,hakuri 'ya sake basu da cewa,munyi maku ba dai dai ba damu sanar daku kai tsaye ba lokacin da tazo garemu duk da kuwa tazo da halayya mafi munin da Babu wanda zaiso ɗiyarsa mace ta kassance dashi dan haka muka hukunta su ta hanyar watsar dasu su gyara tunda Auren da sukayi Babu manyansu shine babban Laifi,to Alhamdulillah a yanzu ɗiyarku watace daban domin kuwa an samu chanji sosai a yarda tazo yanzu abu guda 'ya rage wanda shine kuyi hakuri ku karbi Aurenta domin kuwa a tare da ita akwai rabon shi Nameer din,gashi nan bayan wautar da suka aikata bashi da wani aibu sannan ba wai dan yana jikana Bane kuje kuyi bincike idan kukaga halayyarsa ta banza to ni da kaina zan saka 'ya sauwakewa ita Jamaimah ɗin,a yanzu kuwa gata nan yarda kukace haka za'ayi domin hakkin ku ne.
A yarda sukayi tunani iyayen Jamaimah zasu dauki abun ba haka Bane domin kuwa sosai suka nuna farin cikinsu da 'ya zamana Jamaimah ta faɗa hannunsu sannan suka
Nuna mutuƙar dana sani wajen hanyar da suka ɗauka na nuna mata soyayyar banza da izzar mulki wanda 'ya so kaita ga hallaka.
Bayan sadda zumunci wanda 'ya wakana tsakanin AHALIN biyu iyayen, da samun daidaituwa iyaye Nameer suka wuce suka barshi nan da matarsa akan su kwana biyu inyaso idan zasu koma NIGERIA iyayenta su bisu suga inda ɗiyarsu take.
Bayan komawarsu gida tafiyar Abdallah da matarsa Hafsa ta kama zuwa saudiyya inda 'ya saka ranar zuwa Katsina domin gaida iyayenta duk da kuwa mahaifinta yace kar 'ya damu amma ganin chanchantar hakan yaga 'ya kamata ace sunje ɗin,
Yan uku suka fara wucewa Newyork kana Abdallah da hafsa da Aunty shatuh suka tafi garinsu Hafsa,
Sanin zuwansu 'yasaka Malam Balarabe yin nan da nan ganin 'ya nemawa yarinyarsa mutunci dan bayan bikinta har gyaran gida yayi,abinci 'ya bada akayi masa a waje sanin wacece laure matar da bata sake hali,habaici kuwa da zage zage Babu wanda bata saki ba amma yayi mata banza tunda yasan a wannan gejin sai dai tayi zagin domin kuwa yafi karfinta sannan duk wani abu da take masa kuwa ya karye domin ɗiyarsa yake san dama 'ya nutsar gidan miji yayi Aure kuma burinsa 'ya cika Alhamdulillah Auren kawai 'ya rage masa 'dan har mata 'ya samu.
Tarba ta mutunci yayi musu kamar shine macen gidan ,kafun kace mene labarin Zuwan Hafsat 'ya karaɗe gari wanda 'ya jawo yan tsurku zuwa ganin ta,Hasiya dake zaman zawarci gida kuwa babu abuunda take ma Abdallah sai shisshigi tanan addua Allah yasa cikin shishshiginta tayi wuff da wani abokinsa,
Motel Abdallah 'ya samawa kansa da kyar duk yarda kuwa Malam Balarabe yayi ya kwana gidan 'dan suna da masauki amma yarda Hasiya ke shige masa hankalinsa bai kwanta da yarinyar ba 'dan haka 'ya tafi akan da safe zai dawo inda a ranar dama zasu wuce,Ƙawayen Hafsa da dama sunzo ciki kuwa harda hauwa da Lawisa da tayi aure a doro,tsokananta hauwa ta ringayi akan ta kwace mata crush dama shi tabi Adamawa.
Washe gari da rana suka wuce bayan sha tara ta arziki da Abdallah yayi ma yan gidan da yan gari,bayan komawarsu Adamawa kuma da kwana biyu suka wuce Mecca inda suka bude sabuwar rayuwarsu cikin Aminci da ƙauna.
****************************
FOUR YEARS LATER.
NEWYORK CITY.
Green Sea palace .
Organized gurine wanda Sai ka tara zaka kamashi saboda tsadarsa,ammaa a guri na zuri'ar Tasu its just a piece of cake ,baki daya AHALINSU na gurin wannan ƙaramun taro da Grandpa Bulama 'ya haɗawa yan uku dan murnar gama karatunsu a cewarsa "a kasar 'da suka kare karatu anan 'ya kamata a tayasu murna ba wani guri ba dan haka suna gama taronsu na makaranta wanda kwansu da kwarkwatarsu suka je suka nufi Green Sea ,Nameer yazo da Twins ɗinsa"Afra da Afreen,Abdallah yazo da yaransa Muhammad,Nadiya tazo da yarinyar ta Fatima,yayin da Abbu,Ummu ,Affan da Afnan ƙannen Imam paki baki daya suka halarta,ciki kuwa harda gayyar gidan Grandpa Bulama da masu so da wanda babu yarda zasuyi amma a fuska bazaka ce ba,dama ko wanne AHALI ya ƙunshi hakan addu'ar mu kawai shine Allah ya sake haɗe mana kan zuri'a baki ɗaya, "
Washe gari suka wuce Nigeria baki ɗayansu .
Zazzaune suke lokacin dinner baki ɗayasu da ƙarin jikoki domin yin break fast,Afra yarinya yar kimanin shekara huɗuce ta kalli Muhammad Wanda ke tsaye cike da iyayi tace "Ya Muhammad ijlis mana "
Baki ɗayansu suka saka mata dariya banda ita da ta haɗe rai,cike da pouting lips ɗinta irina mahaifiyarta Jamaimah cos ita take kama da ita tace"mene kuma kuke mun dariya ai kunsan ba wani hausa yake ji ba, "
Zama yayi yana mai kallanta cikin hausarsa da bata fita da kyau yace "Ummi na bani hausa"
Dariya sosai sauran jikokin suka saka suna tsokanarsa har sai da Mami tasa musu baki suka bari kana suka nutsu suka fara cin abincinsu gwanin ban sha'awa.
Rayuwar cikin Ahalinsu rayuwace gwanin ban sha'awa da zaman lafiya duk da kuwa ko wacce zuri'a ta kunshi up and downs nata amma Alhamdulillah bangaren haɗe kansu abun gwanin burgewa,a gidan Nameer Yana zaunne lafiya da matarshi da yaransa wanda bayan haihuwansu ta fara aiki a company dinsa yayin da Nadiya da mijinta Ahmad da yarinyarsu suma suke aiki cikin haɗaka,bangaren Su Abdallah kuwa bayan haihuwarta 'ya maida ta makaranta nan cikin garin Mecca inda ta cigaba da karatunta wanda ta dauko farko,
A haka rayuwa ta cigaba da tafiyar musu in which they live happily ever After.
ALHAMDULILLAH anan na sauke biro na daga kan takardar littafin AHALINA ,
Ina mai mutukar nuna godiyata gareku masoya da irin dumbin kaunar da kuke nuna mun,ina sanku fisabillilah sannan na sadaukar da wannna littafi daga AURE UKU zuwa AHALINA gareku masoya domin idan baku Babu ni,
My wattpad family mafari na ,ina mutuƙar maku godiya inda kuka kaimun AURE UKU 12.5k,AHALINA 2.2K ah cikin kwanaki kaɗan fa my series book 'ya samu view haka ,i cant thank you less,nagode.
Kuskuren dake cikin Allah ya yafe mun idan kuma rubutuna 'ya bata maka ta Wata sigar ina neman afuwa cikin rashin sanine,
Ida kuma ya amfaneka ko ya nishaɗantar da kai komai kankantarsa to kamun addua .
Yauwa kafun na manta zan amfani da wannan damar wajen sanar daku zuwan sabon littafina amma na kuɗine, amma fa a wannan karan a complete zaizo ma'ana zaka iya siyan complete idan baka san page by page ,book 1 free book 2 na kuɗi,
Sannan a wannan page din inasan jinjinawa masu tsayawa suyi comment inajin daɗi sosai Allahu ya barmu tare,wadda kuma ya cinye comment section baki ɗaya itace UMMU SUBAI'A sharhinta yana mun daɗi kuma yana karamun zeal na sake dagewa wajen rubuta abunda nake rubutawa ,daki daki sharhinta yake fita yake sani gyara abubuwa da dama,nagode sannan tukuicinki shine littafin gaba da zaki karanantashi baki ɗaya a kyauta idan Allah ya aramana rayuwa bayan sallah insha Allah.
Asha ruwa lafiya and barka da Sallah 'in advance
Nice taku a kullum
Amina Jamil Adam
Mrs Buhari
Ommu Mahnoor
CHUCHUJAY ✍️
Duk ni ɗaya🥰😁.
Follow me on my media platforms
Wattpad page:CHUCHUJAY
X:Ameenatourh_jay
IG:Chapter_green_
Fb:Ameeatourh jameel
Ku huta lafiya❤
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top