51&52
AHALINA
(Siblings of different fathers )
Book two in Aure uku series
By
Chuchujay
Episode 5⃣1⃣➡5⃣2⃣
Baki dayansu sun hallarci zaman kotun kafun belal da iyalan sa wanda ya haɗa da mahaifiyarsa kakar Nadiya da kuma sabuwar amaryar sa wadda yayi bayan rabuwa da matarsa ,
Inda suke Nadiya bata kalla ba ,tana ji kakar tata na mata magana ta mata banza 'dan ta fahimci tana ɗaya daga cikin masu ƙarasawa wutar dake ci fetur.
Bayan an saurari shari'a biyu aka kira tashi,
Belal da umaimah alƙali yakira gaba yayin da magatakarda Ya zayyana ƙarar da suka zo domin ta,akan cewa" Alhaji Belal Ya kawo ƙarar tsohuwar matarsa ,Dr umaimah akan ɗora yarinyarsa da suka samu tare akan hanyar banza saboda kiyayyarsa sannan daga bisani take san salwantar mata da rayuwa ta hanyar Aurar da ita ga kafiri wanda suke ƙaryar Ya musulunta dan haka yake neman custody ."
Lawyern Bilal ne Ya tashi Kana na Umaimah bisa umarnin Alƙali kafun shariar ta fara gudana,
Lawyer ɗinsa ne Ya tashi Ya fara da cewa"Dr Umaimah kowa Ya santa da halayyar biye biye koda lokacin tana da Auran bilal shekaru ishirin da takwas da suka gabata domin silar rabuwarsu Ya farune dalilin kamata da yayi da wani a ɗakinsu kan gadon su na sunnah ,sannan ba wannan kawai ba shekarun da suka gabata Yaɗuwa na clip na tsiraici yayi yawo a yanar gizo wanda ya wanzo tsakanin Dr umaimah da Mijinta da take Aure Dr Imam ,kukan wanda nake karewa anan shine Alhaji bilal Ya tabbatar da cewa umaimah diyarsa ce sannan yana gudun cigaban zamanta da mahaifiyarta saboda a yanzu ta ɗauko hanyar sabawa addini mutuƙa ,gudun cigaban lalacewar ƴar tasa yake roƙon wannan kotu Mai alfarma akan ta karba jagorancin rayuwar Nadiya Bilal daga hannun Dr umaimah bulama domin shine Ya chanchanta matsayin sa na uba da Ya cigaba da kulawa da ita har Ya aurar da ita gudun cigaban lalacewarta nagode Ya Mai sharia"
Samun guri yayi Ya zauna yayin da Lawyern su ya tashi domin fara Nashi aikin ,cikin kwarewa a aikin nasa ya kalli Bilal yace "idan kotu zata Bani Dama ina San zanwa Alhaji Bilal tambayoyi biyu ."
Kada kai judge din yayi yace an baka.
Godiya yayi kana ya juya ga Bilal yace "Alhaji Bilal ina San na maka tambaya akan shin ka taba ganawa da shi wannan saurayi na Nadiya da magana ta fara ta kansa tayaya ka gane shi din ba musulmi bane? "
Dan shiru yayi kana yace"ni ban taba ganin sa ba ido da ido,amma ba Sai an fada,mun ba musulmi bane tunda dai ai yana ghanian film wannan kowa yasan arene ne.
Karamun murmushi lawyer din yayi yace "a Sanina a lokacin baya kayi tantamar kasancewar Nadiya yarinyar ka menene yasa a yanzu ka dawo akan ita din takace har kake barazana wajen ganin ka kwaceta haka nada hadi da san zuciya ?
Lauya din bilal ne ya tashi yana mai fadin Objection my Lord,barrister salik yana kokarin waje wuce iyakarsa.
Kallan barrister salik Babban alkali yayi kana yace "ka gyara salan tambayarka"
Cike da girmamawa ya karbi gyaransa kana yace"ya mai girma mai sharia,gudun zaunar da kotu da bata mata lokaci yasa nake san na kawo hujojina na nuna lallai Alhaji Bilal bai chanchanci Zama wanda yake da hakkin rike Nadiya ba,ba wai ina cewa ba mahaifinta bane ba shi amma ina tsoran sanar da kotu cewa a suna ne kawai domin kuwa tun daga yarintar Nadiya zuwa ga girmanta Alhaji Bilal bai san hakkin koda da siyan Kwayar shinkafa ba,sannan ina mai san sanar wa da kotu mai Alfarma akan cewa shekaru da suka wuce,Alhaji Bilal ya sadaukar da custody din Nadiya ga mahaifiyarta inda a wannan document din da nake shirin gabatarwa ya saka Hannu akan tabbas idan yazo da maganar san s bashi ita a kamasa ayi masa hukunci.
Sannan magana akan halayyar Dr Umaimah duk karyane"
Zazzare ido bilal yafara yana mai fadin"karyane ya mai sharia ban taba saka hannu a abu makamancin wannan ba,
Murmushi barrister Salik yayi yace idan kotu ta bani dama zan shigo da shaida wanda na tabbata bazai ma Alhaji Bilal karya ba.
Dama aka basa inda ya bada izini da a shigo da Shaidar.
Shigowar mahaifin Bilal shine abunda ya sake bawa Bilal mamaki wanda nan take ya tuna yarda akayi ya saka hannu a wannan document da ake magana akai.
Shaida maihaifinsa ya bada akan tabbas shi da kansa ya bawa Bilal wannan file ya cike kumaa a cikin hankalinsa ba a maye ba sannan ni mahaifinsa shaidane akan hakan bazan taba bada shaidar ƙarya ba .
Haka Lawyer din su shima ya tashi suka cigaba da fafatawa kowa na kokarin kare wanda yake karewa cikin iyawa da gwaninta,
Hutun awa daya alkalin ya bada akan idan an dawo zaiji ta Bakin Nadiya kana ya yanke hukunci.
Sun fita mahaifiyar Bilal ta kalli mijinta tace "Amma Alhaji baka duba wannan al'amarin ba domin kuwa kasan cewa Nadiya ita kadai ce jinin Bilal kuma dole ne yau mu tafi da ita gida.
Ajiyar zuciya yayi yace"ke dai shaidace akan abunda Bilal yayi ma umaimah ke ganau ce ba jiyau ba,sannan ina san ku sani Alhaji Bulama a shirye yake da ya fafata da duk wani wanda zai taba masa iyalinsa kar ma ace kai Bilal ,so dole nazo da kaina Kafun shi yazo da kansa wanda kai Bilal kasan cewa wallahi idan yazo babu dadi,shiru baki dayansu sukayi yayin da kowa ke saka da warwara akan al'amarin amma tabbas suna bukatar Nadiya a tattare dasu.
Bayan lokacin da Alƙali ya yanke baki daya suka koma domin jin wanda yayi nasara cikinsu , fitowa Nadiya tayi bisa umarnin Alƙali mahmood a sabe a kafaɗarta,
Cikin girma irin na Alƙalin yace "Nadiya ga dai shari'a anayi dominki kuma shari'ar tsakanin iyayanki ne guda biyu gasu nan ,wane kike san zama da a cikin su?"
Kalan iyayann nata guda biyu tayi tace"mahaifiyata ta daukeni a cikinta tsawan wata tara ,tayi dauwaniyya dani tun ina ciki har zuwana duniya wanda a cikin rayuwata da ita ban taba sanin babu ba,duk wani abu da nake So a rayuwata ita tayi mun shi,itace uwata itace ubana sannan a wannan zama na rayuwa ta sama mun uba wanda bani da ya shi a rayuwata,
Gefe guda kuma wanda ya bada gudunmawar irinsane aka samar dani wanda tun fari yana kokwaton kasancewa tasa shin idan na zavesa sama da mahafiyata duniya baza tayi Allah wadai dani ba?
Shin menene gudunmawarsa a kasancewarsa mahaifina?
Babu ya mai girma mai shariah, mahaifina bai bari mun komai ba face kayan kunya da kayan gori,
Nuna mahmood tayi da hannunta tace"wannan yaran dake hannun a cikin halayyasa marasa kyau ya sameshi,yaro abun tausayi wanda bansan taya zan fara masa bayani menene ainahinsa ba a lokacin da ya biɗa yasan hakan,"
shiru gurin ya dauka lokacin da Alkalin ya bukaci hakan,kallan Nadiya alkalin yayi yace kina nufin kice shima wannan din ɗansa ne.
Kaɗa kai Nadiya tayi tace"tabbas na sane wanda ya samesa da Aneeesa wadda ta bamu matsala cikin Ahalinmu a rayuwa dagaa bisani kuma bayan laifin da ya kaita gidan yari Allah ya karbeta ,kafun nan kuwa ta shaida mun Mahmood jini na ne saboda Dan mahaifinane,na tabbatar da Hakane sakamakon zuwa da mahaifina yayi gidan mu akan maganar komawata gurinsa wanda nayi amfani da hakan na cire gashin kansa Nayi DNA dana Mahmood . "
Barrister salik ya dauki file din ya mikawa Alƙalin wanda ya tabbata da ba fake bane sannan ya sake bashi document wanda Mami da Papa sukayi adopting Mahmood legally .
Bakin lawyer din Bilal ya mutu murus a yayin da Bilal ke faman rarraba ido yana kallan Nadiya da Mahmood cos 'ya tabbatar da maganarta tunda tace Anisa amma a iya saninsa rabonsaa da ita bata taba sanar masa tana da ciki ba, a zahirin yanzu kuma yana mutuƙar buƙatar jininsa a tattare da shi.
Bayan shaidu da hujoji kotu tayi facali da ƙarar Bilal sannan ta damƙawa Umaimah custody ɗin Nadiya,a Haka ƙarar ta watse.
A tare Ahalin Umaimah suka fito cikin murnar cin nasara,suna kokarin shiga mota Alhji Bilal yazo gabansu,tsaye dukkansu sukayi suna san ganin mene zaiyyi,
Durkusawa yayi kan gwiwarsa 'ya hada hannayensa guri biyu yace"Dan Allah Umaimah kiyi hakuri nasan na cutar dake,bakina ma kunyar fada yake,amma ki yi mun rai ki tausaya mu ko shi mahmood ɗiin ki bani na gyara kuskurena ta hanyar bashi rayuwa mai kyau da inganci."
Wani irin kallo mami ta bashi sannan tace,maganar banza kake Bilal,nayi imani da Allah baka da rayuwa mai kyau din da zaka iya bawa Kowa a rayuwarka ,ba Nadiya ba haka zalika ba Mahmood ba dan Haka ka dauki wannan a matsayin fansa ta akankah,wallahi bazan baka mahmood ba sannan kasa a ranka Ni da Imam ne iyayansa ,ka godewa Allah Nadiya tasan wanene kai da Bazata taba sani ba,ka shirya wata rayuwar wadda zaka rayu da sanin kana da ɗa a waje wanda baka da iko dashi,
"Aikuwa karyarki umaimah Dan wallahi babu mai sakewa tuwo suna,dole ne mu daukaka ƙara ki bamu yaranmu ,sannan abun kunya ai ba kansa farau ba ba kuma kansa ƙarau ba ehe,".
Muryar kakar Nadiya ta karaɗe gurin.
Murmushi Mami tayi tace"Allah sarki Mama Aikuwa zancenki dutse ba'a fara dashi ba kuma baza a ƙare dashi ba dan haka mu haɗu gaba idan kun daukaka karar a shirye muke fiye da yarda kuka shirya".
Basu kuma ce masu komai ba suka bar harabar gurin.
Durƙushe Alhaji Bilal yayi yana mai zayyano dana sani iri iri a ransa domin kuwa a wannan gejin 'ya tabbatar da ya rasa jininsa guda biyu wanda bincike 'ya nuna su kaɗai ne jininsa har ya koma ga Allah sakamakon hatsarin da ya samu kwanakin baya,
Haka mahaifiyarsa ta ƙaraci banbaminta suka bar gurin .
A/N
Fatan 'na sameku lafiya ,So wayata ta samu damuwa yanzu kuma dana samu nayi kokarin mayar dashi yaƙi dole 'na sake number ,
08130229878
Itace sabuwar numberta ta whatsapp sannan ina cigiyar Fatima tayi payment 'na littafi wanda nasan tayi mun magana da wancan layina,ban riƙe surname dinta ba cos nayi missing alert ɗin please idan kin gani kimin magana a layiina domin 'na baki littafin ki, nagode❤
CHUCHUJAY✍️
TBC
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top