5&6

.https://chat.whatsapp.com/DgTUlodRcp2AHM4rmfKTqK

AHALINA

    (Siblings of different Father's)

(Book two in Aure uku series)

            By

   CHUCHUJAY ✍🏽

Gamasu san a tallata masu hajarsu cikin farashi Mai rahusa 09058191213 .

EPISODE 5⃣➡6⃣

    A hankali Nameer yake tuki a yayin da motar ta ɗauki shiru cos tabbas idan yayi magana shi kansa yasan bazai iya mayar da ita bakinsa ba duba da yarda zuciyar sa ke tafarfasa ,

Murmushi Anisa dake gefen sa tayi tace"Baby tunda muka taho bakin ka shiru kaƙi magana amma wani abu da baka sani ba shine ,ni a kowanne yanayi naganka burgeni yake ,shafa kan jaririn hannunta tayi tace "bashi da suna fa har yanzu cos dama uba ke bawa yaran sa suna 'dan haka wannan lokacin ma akan yarona hakan ne zai faru ,ka bashi suna and trust me DNA test ɗin Chan da zai fito 99% positive ne ,ni banga menene amfanin wahalar da kai ba. "

    Wani irin wawan burki yayi Ya Kalleta cikin fushi mai mutuƙar yawa yace "fita a motar nan ,"

Kallan sa take tana wannan murmushin wanda yake ji kamar ya yagesa a fuskarta ,hannunta ta kai ta ɗora a nasa tace "Nameer Stop trying ,mene amfanin ƙokarin da kasan babu wani outcome Mai kyau da zai fito a cikinsa?"

Kazo mu rufawa juna asiri muyi Aure mu bawa yaranmu rayuwa Mai kyau da inganci,babu wanda Ya gani babu wanda yaji please,

    Hannunta da ta saka Akan nasa Ya yakice da ƙarfin gaske kana yace "ke duk wani guntun haukaki fa inaji dashi,kila ma yafi na kanki ,sannan nasan duk hanyar da zanbi naci maki mutunci wallahi fiye da yarda baki zato 'dan haka kafun na wulakantaki ki fitar mun a mota tunda bata ubaki bace."

Ƙaramun murmushi tayi Mai ci masa rai kana tace "Cool down Man,"Bude murfin motar tayi ta fita tana Mai faɗin ,mu haɗu a gida uban ƴaƴana,

Wani irin figar motar yayi wanda Ya sakata saurin ja da baya tana Mai darawa tana juya wayarta da tayi recording abunda ya faɗa yanzu nayi mata rashin mutunci kana ta danna numbern uwar ɗakinta,

Kira ɗaya ta ɗauka ,murmushi tayi kamar tana kallanta kafun tace "uwar ɗakina ina fatan kin gama da Asibiti?"

Licking lebenta na ƙasa tayi tace "Allah yabarmu tare ,sannan a yanzu maganar da nake maki na samu wata hujja da babu yarda iyayen Nameer zasuyi dole su yarda,

Lokacine da yakamata ace sun girbi abunda suka shuka musamman Imam paki da matarsa Umaimah Bulama,ina jin suna jin labarin kiyayya da fansa amma bana taba tunanin sun tab'a ganin irin tawa ƙiyayyar da fansar dake dumama acikin zuciyata da b'argona wadda nake ji kamar na soke dukkanin acting ɗin da nake na kashesu a zuwa ɗaya,kin san nayi training wajen yin kisa ko wacce irice ballantana kuma akai ga maƙirici,

Dariya tayi kana ta kashe wayan tana Mai faɗin"Wallahi da ni yarinya ce Mai hali na gari,amma dukkan wannan halayyar ta gari ta ƙare ne a lokacin da na rasa mahaifiyata kuma kash sai Ya zamana kafun ta tafi ta sanar min da waɗanda sukayi silar mutuwarta,dukkan godiya ta tafi gareta da ta barni da ƙyautar fansa da ƙiyayya,wadda na rantse da Ubangijin da na yarda dashi bazan tab'a gushewa ba sai na ƙarar da zuri'ar Paki da duk abunda suka mallaka. "

    Da haka ta nufi gidan 'dan shirya saban tuggunta.

******************************************** 

  Bayan Rabuwar Nadiya da Evan ta daɗe tana saka da warwara a cikin zuciyarta kafun ta nufi gida kai tsaye dan ko office bata san zuwa,

Abu guda ɗaya ya tsaya mata a zuciya wanda shine yarda Evan yasan Abubawa da dama akanta ciki kuwa har da inda take zama,

Babu abunda yake sake b'ata mata rai da damunta kamar idan ta binciki zuciyarta taji har a lokacin akwai wani Abu tattare dashi wanda bazata iya fassarawa da baki ba ,

Tana shiga gida Motar Nameer Ya tabbatar mata da sun dawo ,ajiyar zuciya tayi atleast idan nata matsalar baiyyi working out ba na Hammanta ta tabbatar da yayi,

Tana Mai koƙarin fita a motanta bayan ta fakata a mazauninta Anisa ta buɗe ta zauna a mazaunin Mai zaman banza,

Wani banzan kallo Aneesa ta bata musamman da taji yarda Annoying kukan babyn da bai ji bai gani ba yana tashi,

Baki ɗayanta a foul mood take wanda idan Anisa ba tayi wasa ba zata iya juyewa akanta ,ɗaukar Jakarta tayi tana Mai faɗin"Get out of My car".

    Wata irin dariya Anisa tayi tace"na daɗe da lura Alhalin gidan nan arrogance ɗinsu abu ɗayane kamar yarda suke abu ɗaya,kamar kuma an tsinkuleta ko irin ka faɗin abu ba dai dai ba tace"a'h Afuwan fa ashe dake da Nameer ɗina da Abdallah zaman agolanci kuke a gidan nan,'dan naji sirikina da Ya haifi Nameer har Porn clip ɗin mahaifiyarki da Mijin ta na yanzu ma'ana mahaifin su Fawzan Ya ɗora wanda kuɗi yasa aka kashe maganar aka ƙaryata alhalin babu wanda bai san iskancin da suke yi a city hospital ba,

    Dafe bakin ta tayi tana Mai Kallan Nadiya da murmushi rainin hankali tace"amma fa rumours ne nima' wai 'naji suna iskanci a 'da amma bana tunanin jita jita da ya tashi a lokacin baya na kama mahaifiyarki da Mahaifinki Bilal yayi da gardi Akan gadonsa ƙarya ne ,sannan naji ance yana ƙokwantan kasancewar ki ƴarsa,After All baya nemanki " .

Sake dafa baki tayi tace "a'h shima nafi yarda da jita jita ne 'dan mother 'in law na batayi kama da Mai rabawa maza Pun@ ɗinta  ba duk da kuwa ta raba ga maza iri huɗu da sunan Aure.

Family ɗinmu nada reputation gaskiya .

    Buɗe murfin motar Nadiya tayi ta fito kana ta zagaya inda Anisa ke zaune ta buɗe ta finciko ta,kafun Anisa tayi Aune ta sharara mata wani irin zazzafan mari yayin da babu abunda bakinta keyi sai karkarwa ,ƙokari sosai tayi wajen danne kukan da yake san zubo mata 'dan sosai maganganun Aneesa sukayi mata zafi,tana ƙokarin sake marin ta sakamakon dariyar da Anisa ke Mata taji an riƙe mata hannu,

Juyawa tayi 'dan ganin wanene,Papa ne tsaye gefensa Mami,kaɗa mata kai yayi yace"No My princess bana san ki Aikata mistake ɗin nan ,"

Hawayen da take ƙokarin zubo mata ne suka fara neman hanyarsu ,ba tare da ta boye ba tace "Papa kalli yarinyar nan na tabbata ko Abdallah ƙanina Ya girmeta and trust me idan kaji maganganun da ta faɗa mun kai zaka mareta Bani ba,amma tunda kace na Bari Zan bari,nuna Anisa tayi da hannu tace "ki sani i will be your downfall sannan lokacin da Zan wulaƙantaki a gidan nan na maki koran kare lokacinne Zan baki amsa dai dai da abunda kika faɗa mun ,Stupid freaking Gold digging bitch .

    Ta juya dan barin gurin ta tsinci muryar Mami na faɗin"stupid freaking Gold digging bitch ɗin nan ina san kisa aranki babu ranar da zaki koreta,ki wulaƙantata cos zaman ta da Ahalinku yanzu ta fara cos tana ɗauke da ɗan da yake jinin gidan nan,"

    Wata irin murmushi frustration Nadiya tayii jin Abunda mami tace sannan sarai ta fahimci abunda Mamin ke nufi ma'ana dai Dna Ya nuna yaran dan Nameer ne,

Juyowa tayi ta kalle su kana tace "ban san menene kuka yarda dashi ba amma ni abu ɗaya na sani na yarda dashi wanda bana tunanin kun fahimce sa wanda shine"wannan yarinyar is fake and a cheat cos ada kokwanto nake amma a yau maganar da ta faɗa mun bana koƙwanto sannan sai na kawo ƙarshen maƙiricin ta cos naga Alama ni ta zab'a a gidan nan na kawo mata ƙarshen ta"

Fuu ta wuce ciki inda Anisa ta wani langwab'e kai tana Mai faɗin"interesting a zuciyarta ,mami na kallanta ta marairaice fuska ,Hannu mami ta miƙamata alamun ta bata yaran ,babu musu ta b'ata ,kallansa sosai mami Take tana san gano da uban da yayi Kama a zuria'rsu amma babu,babban kuma abunda Ya kuma ɗaure mata kai shine yarda DNA ɗin yaran yayi matching dana Nameer, bata tunanin anyi tempering dan a asibitinsu akayi bata tunanin zasu back stabbing ɗinta haka.

    Papa ya fara barin gurin kafun ta mara masa baya Anisa na biye dasu tana Mai jin daɗin defeat d'in da ta gani a kan fuskokinsu ,

Kaɗan ma suka fara gani A cikin irin abubuwan da ta shirya masu indai itace.

***********************

    Nameer zaka Auri Anisa nan da sati ɗaya sannan a yanzu zaka raɗa ma yaranku suna dan nauyin ka ne,idan kuma ban isa ba ban kai nasaka ka ba dan Allah ka bijirce mun.

    A zabure Ya kalli mami yace "Mami wallahi tallahi wannan yaran banawa bane sannan wallahi ban tab'a ganin yarinyar nan ba ballantana har na bata cikin da zata haifa mun yaro shima kuma ta hanyar fyaɗe ,mami zaki yarda da wannan yarinyar sama dani da kika haifa ne?

Papa say something.

    Ɗauke kai Papa yayi cos duk yarda yaso Ya yarda da maganar Nameer gaskiyace sai yaji kamar baiyyiwa Anisa adalci ba sanann yaso kansa .

Jefa masa result d'in DNA ɗin mami tayi tace "Ba yarda nayi da ita sama da kai ba result ɗin da na tabbatar babu kuskure shi nayarda dashi,zaka faɗi wani abu bayan nan ne,?

Zubewa tayi a ƙasa duk juriyarta ta saka wani irin kuka Mai cin rai tace"kalle ni nan Nameer  ba sai na faɗa maka ba nasan kana da wayan sanin abubuwan da nayi facing through kafun Papanku,ko ban kai uwa enough ba wani cikinku Ya fada mu,im a not That Good enough da kuke san dole sai kun tona mun asiri,dame na rageka Nameer,i gave you a father ,gashi nan zaune wanda Ya ɗauke ku kamar nasa duk da abunda duniya ta ringa Faɗa bai damu ba,he gave you guys a Good life and d father's warmth ,bai isa ba?

Idan baku guje mun abun magana domin ni ba zaku guje dominshi,amma sai da kayi yarda kayi ka nuna mun ban isa na goge jinin Habib a jikin ka ba atleast ka gado wani abu nasa.

    Da sauri Papa Ya ƙarasa gareta yana mai hanata faɗan abunda zatayi dana sani,

Goge hawayenta tayi tana Mai Kallan Papa tace "im Sorry ,kayi haƙuri da abunda Nameer Ya jawo mana and yau bazaka shigar masa ba cos you've pampered him enough,

Goge hawayeta tayi ta mike ta nufi gurin Anisa ta karbo babyn ta ɗorasa kan cinyar Nameer wanda yayi saurin tallafesa gudun kar ya faɗi.

Nuna yaran tayi tace He's yours dan haka ka bashi suna sannan dole ka Auri Mamansa for damage ɗin da kai causing mata idan kuma ba haka ba Zan tsaya mata iya ƙarfina a ƙwatar mata yancin ta and kasani idan na shiga sai kaje jail na maka alƙawari ".

    Wasu irin hawaye ne ke bi masa kumatunsa a yayin da yake kallan yaran dake cinyarsa yana Mai jin dama wani zai zo Ya Dafasa yace masa Ya tashi daga mumunan mafarkin da yake yi.

Huɗuba yayi ma yaran a kunne na hagu dana dama kana yace Na raɗa masa suna MAHMOOD saboda ina fatan nan gaba bazai bari past ɗinsa Ya dame sa ba zai zama abun alfahari Ya mallaki ma'anar sunan wato wanda za'ana yabawa anan praising ɗin sa,

Sannan Zan Aureta nan da sati kamar yarda kikace Mami,ni nasan Allah a kullum yana tare da mai gaskiya, makirici da mugunta bata tab'a cin galaba Akan gaskiya,

Kallan mami yayi wadda jikinta yayi sanyi yace "Mami im not like Habib kuma  bazan taba zama kamar sa ba na maki alƙwari"

    Tashi yayi da mahmood a hannunsa Ya nufi gurin Anisa Ya ɗora mata shi kan hannunta cikin kulawa yace"Bansan Mai yasa kike yin abunda kike yi ba ,amma ina so ki sani Allah baya bacci ,kin sakani a tsaka mai wahala ke ƴar adam kenan wadda baki iya fidda mutum cikin matsala ,baki kasheshi in lokacin sa baiyyi ba baki rayasa,baki da wuta baki da Aljanna,

Ki shirya dan bazakiji daɗi ba lokacin da Allahn da na yarda zai fitar dani Ya jefaki cikin tsaka Mai wuya.

Yana ƙarashen maganarsa Ya bar Falon,

Haka zalika Abdallah da Nadiya waɗanda akayi a gabansu ,

Juyawa mami tayi ta kalli Anisa tana Mai murmushin yaƙe tace "ki saki jikinki sannan ki daina damuwa cos nan yanzu gidan ku ne sannan zuwa gobe ina san za muje tare dan mu gana da iyayenki Ayi magana ta fahimta,tashi kije ciki idan Kina buƙatar wani abu kiyi magana,

Babu musu Anisa ta miƙe tana Mai jinta kamar wadda aka saka a aljanna cos mission step one is completed.

Sannan bata buƙatar basu wani recording dan batayi tunanin abun zai zo mata da sauki haka ba.

********************************************

    Zaune take bakin tashar ɗan marna gefen ta robar furar da tasha daka ,kallo ɗaya zakayi ma furar kaji ta burgeka,babu abunda Hafsa ta tsana irin fita tallan furar nan da Mama laure ke aza mata duk da girmanta da mutuncin ta,wani lokacin takanji kamar tayi rebelling amma tunawa da karatunta yake hanata dan Mama laure ta faɗa ta kuma jadadawa mahaifinta muddin Ya hanata siyar mata da fura to karatunta zai tsaya duk balai kuma sai ta aurar da ita ga mutum mafi kaskanci,

Dafata taji anyi wanda hakan Ya fito da ita daga duniyar tunanin da ita shiga,dagowa tayi taga lawisa ƙawarta da suke zowa gurin tallah tare,

Goge karamar kwallar dake shirin zubo mata tayi tace "lawisa yaushe kika zo",

Gyara zama lawisa tayi tace"ina zaki gane nazo kina zaune Kina tunanin da kika saba na babu gaira babu dalili ,ni Bansan mainene duwarki ba hassatu,dan kawai kin daukowa Mama laure tallah?"Ni ki kalle ni mana,Bani ga tsuntsu Bani ga tarko,ni dake tare muka fara karatu tun firamare amma kina ganina jiya e yau banda ma Zawarci da nake a ƙanƙantar shekaruna ,ni ba wani kyau ba,wallahi nasani shi yasa kika ga ko tsohon mijinta Halliru zai fada mun mumuna ban damuwa dan shine kawai maganar da Ya fada ta gaskiya duk da karyarsa ,ki kalli bakin nan nawa,

Buɗe ƙaton bakinta tayi wanda yasaka Hafsa darawa dan dama abunda Lawisa d'in taka so kenan,

Ita da lawisa tare suka tashi,duk da ba halinsu ɗaya ba,lawisa na da rawar kai inda hafsa take shiru shiru babu wata hatsaniya amma hakan bai saka abotarsu ta lalace,suna da banbancin ra'ayi amma abotarsu gaskiya ce shine gaba,

Kamo hannunta lawisa tayi ganin tana dariyar tace"ke kyakyawace sannan ni na yarda ina gaban iyayena sanann babu wanda Ya isa yamun keta ,tanan kawai na fiki amma bayan nan ki ringa duba abubuwa da dama misali Mai zai faru dake nan da shekaru Goma idan Allah Ya nuna mana,

Wannan sana'ar furar sai dai kiyi labarin ta dan jikina na bani a ofishi Mai gilasai zakiyi aiki, idan Kika gama karatu sannan insha Allahu sai kin zama matar Malam Abdallah."

    Dariya sosai hafsa ta saka tana Mai jin lawisa har ranta sannan tana mata addu'a Allah Ya basu rayuwa Mai kyau baki ɗayasu.

Chuchujay ✍🏽

Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top