49&50
AHALINA
(Siblings of different fathers)
Book two in Aure uku series
By
CHUCHUJAY ✍🏽
Episode 4⃣9⃣➡5⃣0⃣
Bayan barin hafsa Asibitin kai tsaye gidan su Nadiya suka wuce domin sama musu abincin da zata ci cos tana buƙatar kwana Biyu gaba a asibintin 'dan ta sake hutawa,
Kallanta Nadiya tayi tana tukasu tace "uhum ina saurarenki Hafsa Ya maganar ƙanina fa,ni dai ko Abdallah bai faɗamun ba ya faɗa sanki 'dan haka bari na fara Mana neman iri ,
Ƙasa da kai Hafsa tayi tace "kai Aunty nifa ba soyayya muke ba tukunna."
Dariya Nadiya tayi tace "na fahimta kenan dai za'ayi ne amma ba a fara ba,shikenan nayi shiru bari na bashi dama Ya dama da kansa.
Ita dai hafsa ƙasa tayi da kanta tana murmusawa tana Mai jin wata irin kunya kamar ƙasa ta buɗe ta shige,murmushi itama Nadiya tayi tana Mai Addu'ar Allah yasa Hafsa rabon Abdallah ce domin ta yaba da hankalinta mutuƙa.
Suna isa gida horn ɗaya tayi aka buɗe masu gate ,parking motar ta tayi tana Mai jiyo kamar hayaniya cikin gidan,bata kawo komai ba ta buɗe motar yayin da hafsa ma ta buɗe suka fara takawa a tare bisa jagorancin Nadiya,turus Nadiya tayi lokacin da ta cigaba da jin surutun na mutum ɗaya daga sashen baya Na baƙi yayin da gefe ɗaya kuma taji kukan Maminta tana faɗin"'dan Allah bilal kar ka fasa idan ka isa ka haifu,dama Ai imam na faɗa maka bani san magana dashi amma kayi masa jagora cikin gidan mu ,Kana tunanin ana wa ɗan iska hallaci ne".?
Kallan hafsa Nadiya tayi tace "kin buɗe kofar chan zata kaiki falo ,ki jirani anan ina zuwa babu daɗewa,"
Babu musu hafsa tace to yayin da itama kunnuwanta suka jiyo mata abunda na Nadiya suka jiyo amma tayi ƙokarin ɗauke jinta daga garesu domin daga gani magana ce babba ganin yarda idanun Nadiya suka kawo ruwa.
Cikin nutsuwa Nadiya ta fara takawa gurin tana ƙokarin saita kanta ,babu wani alert ko notice ta shiga ɗakin,zaune ta tarar da Mami gefenta kuma Papa Ya ɗora hannunsa kan kafaɗarta yayin da Mahaifinta Bilal ke tsaye wanda da alama tafiya zaiyyi amma bai daina surutai ba,a tare dukkaninsu suka Kalleta ,bilal ne yafara cewa "Alhamdulillah gama Nadiya ɗin nan Ai,ki kalli yarinyar nan fisabililahi yanayin shigar dake jikinta,kinyi duk ƙokarin da zakiyi umaimah kin mayar da yarinya Yar iska mai ciyar da kai da tallata jikinta ,sannan a yanzu Kina neman haɗata da tubbabe,wanda da banji bakin babana ba haka nan zaki cuceni, dama tana sana'ar modeling ina zata ɗauki hankalin musulmi?,dole sai arne to wallahi indai ina numfashi babu wanda Ya isa Ya Aurawa ɗiyata Kafuri wallahi,Dan haka ki shirya kamar yarda na faɗa miki sai kotu ta bani custody ɗinta , "
Tashi Papa yayi ransa na mutukar suya domin duk yarda yaso Ya danne fushin nasa Bilal na ƙokarin wajen ganin Ya turasa bango,cikin saita kansa yace "Alhaji Bilal kamar yarda na faɗa maka mun kai karshen zance zamu haɗu a court idan alƙalin sakarai ne Ya baka custody ɗin Nadiya "
Juyawa bilal yayi ga Nadiya yace "kar ki damu Nadiya nasan Kina cikin damuwa kuma zan cire ki daga ciki insha Allahu".
Danne duk wani abu dake zuciyarta tayi ,ta faɗa jikinsa tana Mai faɗin "Daddyyy,"
Petting bayanta Ya fara yace "karki damu Nadiya babu wanda Ya isa Ya Aura miki kafiri,"
Kaɗa kai tayi ,kafun Ya farga tasa hannunta a bayan gashinsa daga baya wanda Ya tasa taja gashin sa da ƙarfi wanda sai da Ya saka ƙaramar ƙara,
Murmushi tayi tace "da zafi kenan,abunda nake so kaji kenan,sannan wanene yace maka bana san kafirin da ka raɗa masa?"
Shi nake so fiye da kai sannan wannan da kake gani Shine mahaifina ita kuma kafi kowa sani itace mahaifiyata ,sannan zan zabesu sau dubu a kanka,kar ka manta ni kaina kayi doubting zamana jininka So dont play this With me zan baka darajar kai ɗin kai kayi donating aka samar dani shima abunda yasa na gasgasata saboda mahaifiyata ba mazinaciya bace ba ,amma idan ka dage da maganar custody ɗina to mu haɗu a court ɗin,kar ka manta im an adult 29 for that matter ,so ka shirya faɗanka a kotu sannan kasa a ranka bazan taba zuwa na zauna ƙarkashinka ba domin nima a shirye nake ,and trust me munsan shari'a ta yarda a yanzu abunda kake sunansa harassment kuma zamu iya ɗaukar mataki akan hakan.
Tana kai karshen zancenta ta fita a ɗakin tana Mai sake rike gashin data figa gudun kar Ya faɗi.
Tana fita mami ta kallesa tace "ina fatan ka gane karatun,zaka iya tafiya ko kuma na saka a fitar da kai babu daɗi,idan kuma zaman nan ɗin kake so bismillah,"
Gaba tayi Papa ya mara mata baya yana Mai faɗin "sai mun hadu a gaba"
Cike da balai bilal yace "Ai dama nasan za'ayi haka,wato kin bata wani abu da zaisaka Tamun rashin kunya ko,to wallahi ko kiƙi ko kiso Nadiya tawace halak malak kuma wallahi sai an bani magajiya ta,bazai taba sabuwa ba yarinyata guda ɗaya tilo a duniya ta Auri kafiri"
Ganin sun fice sun barsa yana ta faman hargagi Ya sakashi shima fita yana mita da surutai Ya bar gidan.
Kai tsaye Nadiya na komawa ciki tayi ƙokarin saita kanta gudun kar hafsa ta gano da wanin abu,Mahmood tagani a hannunta tana mashi wasa,zama tayi gefensu tace "wai kaima kasan Mai kyau ko"
ɗan murmushi Hafsa tayi inda yana ganinta Ya fara miƙa mata hannu kan ta ɗaukesa,babu musu ta karbesa tana Mai faɗin"yaran kirki maine kaci ne naji Kana ta ƙara nauyi haka,faɗa mun sirrin"
Mami dake tsaye bakin kofa tana Mai jin hawaye na tausayin Nadiya da mahmood ce ta ƙaraso tana Mai faɗin"kulawan Mami ce kawai da Papa wanda bai gajiya da siya masa daɗi ta sakashi ƙiba,yana jin muryar mami kuwa Ya fara zillo yana ihun ta ɗauke sa,dan turo baki Nadiya tayi tace"a'h wato wai kai kasan Maminka ko,Ai shikenan abun bana faɗa bane jeka,"
Zama Papa yayi yana Mai faɗin "Ai mahmood idan yaga maminsa hatta ni da nake bashi abun daɗi mantawa yake dani saboda ƙauna".
A zaune Hafsa ke a ɗari ɗari na haɗuwa da iyayen Abdallah wanda bata tunanin ma Sun kula da ita suna ta yaransu abun sha'awa,cikin ladabi tace "Ina wuni"
A tare mami da Papa suka kalleta Kana suka amsa inda Mami kecewa "ina muka samo damsel haka'.
Murmushi Nadiya tayi tace "Ai wannan damsel ɗinta..."
Da sauri Hafsa ta katseta wajen faɗin"ina aiki gidan Aunty shatuh ne ."
Waskewa Nadiya tayi tace "okay baki So a faɗa kenan ,to Ai shikenan tunda kin gabatar da kanki nima bari nayi nawa,Mami,Papa sunanta Hafsa and tana taya Aunty shatuh aikine So sai ta ɗan aikata gidan Nameer akan maganar nan da na miki kwanaki yanzu haka ma matar Nameer ɗin tana asibitinmu a akwance,munzo mu kai masu abinci ne"
Tabe baki mami tayi tace "Allah Ya sawaƙe inda Papa kuma yace "subhanallah hope ba wani serious abu bane,"
"Eh ba wani serious abu bane sosai Bp ne yayi shooting amma ta warke yanzun tana dai hutawa ne"Nadiya ta bashi amsa,
Sake Tabe baki mami tayi tace "Ya tabbata ya aje kuɗin gado zan kira asibitin ai,sa'arsu ɗaya ina leave da ko tab'ata baza'ayi ba sai Ya aje kuɗi ,mara kunyan yarinya kawai,ga yam porridge chan na dafa ki dauka ki kai mata.
Tana kai aya ta yi sama da mahmood tana masa wasa,dariya Nadiya da Papa sukayi Nadiya na faɗin"Mami duniya ".
Dariya Papa Ya kuma sawa yana Mai faɗin "and she cares fa,matana akwai rigima
Tashi yayi yana faɗin "Abdallah fa yana cikin gidan nan wai baya jin dadin jikinsa amma He's okay yanzu ,After All parents ɗinsa likitoci ne kuma suna gida,kinsan rakin yarona idan yana ciwo sai mu ɗin in akaje waje dariya za'ayi masa,matarsa zatayi fama,which na ƙosa Ya kawo mana cos nagaji da ko budurwa baya da"
Dariya Nadiya tasa tana Mai faɗin"ka kwantar da hankalin ka Papa she's closer than you think,"
Gumtse dariyar ta tayi jin Hafsa na zungurinta ,kaɗa kai yayi da ya kula da idan da Nadiya keyi masa ga hafsa,murmushi kawai yayi Ya barsu nan,kallan Hafsa Nadiya tayi tace "uhum yanzu dai kinji Abdallah bashi da lafiya ba,nasan kinji kina san zuwa ki dubasa,ƙasa tayi da kanta ta miƙe tace"ni dai mu tafi nasan hamma yana chan yana jiran abinci akai musu dama ko karyawa baiyyi ba muka fito,"
Tashi Nadiya tayi tace "Ai shikenan bari ni naje na dubasa na dawo sai mu wuce,"
Haka Nadiya ta nufi sashen sa yayin da Hafsa take ji kamar ta bita ta ganshi cos maganar rashin lafiyan nasa da akayi tabbas yayi mata wani abu ,
Tana nan zaune Nadiya ta dawo tace "habibin naki bacci yake yi sai mu tafi".
Bayan sun kai masu abinci suka tarar da Jamaimah na rigimar ita gida zata je ,dole doctor Na'im Ya sallamesu yana Mai jadadawa Nameer Ya samu isashe hutu dan haka a tare suka wuce gidan Nameer ɗin banda Nadiya wadda tace musu tana da muhimmin abu da zatayi a asibitin ,
Suna isa Jamaimah ta shiga wanka saboda yarda take jin jikinta babu daɗi,bayan ta fito ta tarar da Nameer zaune bakin Gadon ta,tun daga ƙasa Ya fara kallanta har Ya kai kan fuskarta,dan tsuke baki tayi tace "ka daina kallona haka cos nasa koda babu kaya jikina bazan ja ra'ayinka ba saboda halayyata gareka,na sani you don't lust for me domin da ace Kana sha'awata a lokuta da dama dana taba ka da Ya nuna ".
Murmushi yayi yana jinjina rashin filtern Jamaimah a baki ,bata kunya magana muddin tazo mata baki,
Tasowa yayi Ya tako inda take hannunsa Ya saka kan exposed cinyanta in a seductive manner ,jawota jikinsa yayi da dan ƙarfi yana kama butts ɗinta ,buɗe bakin ta tayi ganin yarda ya riƙeta ɗin ,zatayi magana Ya saka finger ɗin sa a kan lips ɗinta yace "shhh,kar kiyi magana cos idan kikayi bazan iya riƙe kaina ba,komai naki abun sha'awane da ɗaukar hankali,your lips,boobs,butts,flat tummy,sexy eyes da komai da kika san ke kika mallakesa jikinki,nayi faɗa da kaina sau da dama wajen ganin ban ripping duk wani tufafi dake jikinki ba nayi taking ɗinki a duk inda kike,Kinsan yarda nake rike kaina,ina hukuntakine amma kaina nake hukuntawa,abu ɗaya zai hanani nuna maki irin sha'awanki da nake wanda shine rashin lafiyar da kike and kikaji Dr yace ki samu isashen hutu wanda nima nake san ki huta ɗin domin bazan barki ki huta ba and trust me im the sexiest lion da zaki sani."
Ƙarasa zance yayi da kashe mata ido guda daya,wani irin yar taji a jikinta inda take dukkan wani goosebump nata Ya taso yayin da jikin ta Ya dauki Wani irin zafi ,
Murmushi yayi da Ya fahimci halin da Ya jefata,takawa yayi ya nufi kofa yana Mai fadin ki shirya ki fito kici abinci cos nasan present ɗina yana miki wani abu,
Fita yayi yana mata dariya ,da gudu ta faɗa bathroom ɗin dan sake sakar ma jikinta ruwa saboda yarda take ji kamar an zuba mata wata wutar desire .
Bayan fitowarta ta shirya cikin riga da wando na palazzo Cos bata da wani atampa ko ɗaya duk da kuwa a yanzu ganin da take yi a jikin Nadiya da hafsa burgeta suke,
Tufke Gashinta tayi tana tunanin yakamata taje saloon a gyara mata shi cos a yanzu tana san a gun Nameer ta zama fes ta ko ina ta yarda Babu wata ɗiya mace da zata burgesa cos ta yarda da kanta ta ko ina.
Bayan ta gama ta fito kitchen taji motsin hafsa yayin da shi kuma bata ji alamunsa ba,shiga tayi bakinta da sallama,cike da girmamawa Hafsa tace "Kin fito kenan,Ya jikin"?
Dan murmushi Jamaimah tayi tace "jiki Alhamdulillah,dama ina san magana dake ,nutsuwa Hafsa tayi tace "Allah yasa ba wani abun na sake yi ba."
Zama Jamaimah tayi kan stool ɗin dake kitchen ɗin tana Mai murmusawa tace "babu abunda kikayi matsoraciya,ina so ne naje gaida Mami da Papa sannan ina so idan zanje nayi musu abinci Mai daɗi na kai musu and kinsan ni ban iya girki ba ,amma ina san koya saboda yanzu inasan nayi rayuwa domin mijina da farin cikinsa to kinga kuwa barin sa da yunwa Ai bai taso ba dole na iya nima,sannan magana kuma na karshen ina so ki zauna dani na wasu kwanaki har na iya wani abu trust me im a fast leaner , "
Murmushi hafsa tayi tace "kar ki damu Adda kome kike so zan miki,sannan zanyi ƙokari wajen ganin kin iya abubuwa da dama kafun na koma gidan Aunty ".
Haka nan suka yanke decision din zata zauna ɗin,
Bayan hafsa ta gama duk wani 'dan aikace aikace da zatayi ta koma ɗakinta ta kwanta wuraren Takwas na dare,ita ba wata mayyar kallo bace ba dan bata tashi gidan da zatayi kallan bama,wayarta ta ciro ta shiga numbern Abdallah tana Mai tunanin kiransa,
Kira ɗaya Ya dauka kamar dama yana jiran kiran nata,
Cikin siririyar muryarta tayi sallama ,shiru yayi bai amsa ta ba,tunanin ko baya jinta Ya saka tacewa "hello"amma still baiyyi magana ba,cire wayan tayi a kunnenta ta kashe tana kashewa kuwa Ya kirata ,kamar bazata ɗagaba amma sai ta ɗaga ɗin da ɗari ɗari,sallama ta kuma yi masa a karo na biyu,a gajiya yace "wa'alaikis salam,Mai yasa kika kashe".
"Nayi tunanin Ko baka jina ne""
Ta Amsashi a takaice.
Murmushi yayi kamar tana gaban sa yace"Ai ina fushi ne dake da kika zo akace kizo ki dubani kika ƙi so nayi tunanin baki damu dani bane kwata kwata ashe akwai sauran damuwata a tattare dake,"
Murmushi tayi tace "ya jiki"
Gyara kwanciyarsa yayi Yace "jiki 'fa yayi dɗi musamman da na san cewa Hamma da matarsa sun shirya,kinga nima dake sai muzo mu shirya ki amshi tayi soyayyata,idan kuwa baki amince dani ba zan tayi miki naci har sai kin amince,idan kuma kika amince na miki Alƙawari zan soki fiye da jiya ,idan yau ta wuce zan soki fiye da a yau a gobe da zan tsinci kaina burina da fatana shine ki amsa tayin soyayyar narayan nan,Mai kikace "
Tsintar kanta tayi da cewa "to" kawai.
"To mene?Kina nufin kin amince da soyayyata?"
Cikin siririyar muryar tace "eh"
Wani irin ajiyar zuciya Ya saki yace "Alhamdulillah ,da ace dare bayyi ba da gudu zan zo na sakaki cikin idona domin ki faɗa mun wannan kalmar da zata sakani nayi bacci cikin walwala,nagode hafsa sannan na miki alkawari bazaki taba dana sanin amsan soyayya ta ba,Zanzo gurinki mu zauna ni dake kisan wanene ni ,idan kin yarda dani a yarda nake Zan mutuƙar farin ciki ,idan kuma baki yarda dani ba a yarda nake to Zan ta ƙokari naga kin amince dani ta hanyar nuna miki ni mutumin kirki ne".
Duk wani courage ɗinta ta nemo ta saka tayi ƙokarin cire wata kunya dake damunta akansa tace "ba sai ka faɗa mun wanene kai ba domin na riga da na san wanenen kai saboda duk wani masoyinka mai bibiyarka yasan labarinka,nima kuma ina cikinsu,tun kan nazo garin nan nasanka nake jin daɗin saurarenka,zuwana garin nan kuma nasan wanene kai da asalin labarinka,bai dameni ba kuma bazai chanza abunda nake dashi a raina dangane da kaiba ,abunda Ya shafi mahaifinka wanda baya da kyau bazai taba shafanka ba tunda wani baya ɗaukar hakkin laifin wani. "
Shiru yayi yana Mai jin wani irin santa na shigarss,dan murmushi yayi lokacin da Ya juya ilahirin maganarta ,cikin sanyin murya yace "wato dai ke kika fara sona kafun na sO ki"
Dif ta kashe wayanta wanda hakan Ya sakashi darawa a hankali cikin nutsuwa,bai sske kiranta ba 'dan yasan kunya take ji,godiya yayi wa Allah yana Mai Addu'ar faranta mata a babin soyayyarsu da suka buɗe sabo.
****
Kamar yarda Bilal mahaifin Nadiya yayi alwashin makaso kotu haka ya faru,da safiyar Allah tun kafin ko wannensu Ya fita aiki takardar shammaci ta rikesu,sosai ran Mami Ya harzuƙa,lokaci guda kuma damuwarta ta karkata kan Nadiya,murmushi Nadiya tayi tace "mami Ai ba abun tashin hankali bane ,abu guda na sani wanda shine babu sanda Ya isa Ya maida ni karkashin ikonsa saboda tun da daɗewa Ya rasa wannan ikon,kar ki Bari wani hargaginsa da na shari'a Ya baki tsoro,ni mutane biyu na sani iyayena wanda kece da Papa bani kuma da wasu kakanni bayan mahaifanki da mahaifan Papa 'dan haka duk inda suka kai da bala'in su sun rasani har abada,carrier ɗin Mahmood ta ɗauko kan couch ta karbesa hannun Mai rainonsa tace "Ya kamata ace zaman nan shima anyi dashi ,bata jira amsar kowa ba ta dauki abubuwan da take buƙata tace "ya kamata mu haɗu a court ɗin nan infact ya kamata ace mun rigasu zuwa mu tayasu buga wasan da su Kansu sun sani zasu fadi.
To bayin Allah mu haɗu a court nan da two weeks bayan exams ɗina idan Allah Ya ara mana rayuwa,ku sani ina mutukar kaunarku ❤❤kamar yarda kuke kaunata fisabililahi,sai mun sake haɗuwa. "
Nice taku a kullum
Aminatu
CHUCHUJAY ✍🏽
Bạn đang đọc truyện trên: AzTruyen.Top